Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   42 / 47

123K to 126K   out of 140.6K words

yasanya kansa ya fara yi masa ciwo, hannu ya bawa Dr.Waleey inda sukayi musabaha daga nan yayi masa sallama, koda ya fito daga cikin office ɗin na Dr.Waleey haka Amna tabisa da wani irin mayataccen kallo harya ɓacewa ganinta, sosai yake tsananin burgeta, kama daga yanda yake dressing da kuma yanda yake aiwatar da komansa cikin nutsuwa, haka kuma sosai MISKILANCI nsa ke burgeta, duk da cewa miskilancinnasa ya zarce misali amma ahaka take kwaɗayin rayuwa dashi, saidai kuma tasan kamar yanda wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, haka shima yayi nesa da ita, don yazama kamar wutsiyar raƙumi itakuwa tazama tamkar ƙasa, dama ance hanyar jirgi daban hakama na mota daban.

Yana isa compound ɗin asibitin direct inda motarsa take ya nufa, yana shiga yabata wuta.


Gudu sosai yake shararawa akan babban titin dazai sadashi da unguwar ta Maitama, sanye yake da baƙaƙen kaya ajikinsa yayinda yasanya wata baƙar mask ya rufe gaba ɗaya fuskarsa, idanunsa kawai zaka iya hangowa, ayanda yakejin zucia da ransa na tafasa yanajin komai ma zai iya aikatawa, ayau bayajin zai iya haƙuri yashanye ɓacin ran da SOORAJ ke ɗura masa, SOORAJ ya ƙwace masa komai, a sanadin sa yarasa abubuwa da dama, asanadin SOORAJ yarasa babban matsayin dayake kai, sanadin SOORAJ company'nsa wanda yake matuƙar ji dashi ya durƙushe, akodayaushe sunan companyn ƙera abayas na SOORAJ dake Dubai ne ke yawo ƙasashe ƙasashe ba nasa ba kamar yanda yakeso, SOORAJ yasashi ya rasa abubuwa da yawa, ciki kuwa harda yarinyar dayake fatan kashe ƙishin ruwansa akanta, saboda haka baya tunanin zai iya barin SOORAJ ya rayu cikin duniya.

SOORAJ kuwa ganin ya kusa shigowa cikin unguwar tasu ta maitama ne yasanyashi ɗan ƙara gudun motar, daidai zaisha wata kwana batare da ya kula ba wata mota tayiyo kansa da gudun gaske, shima batare daya taka birkin motar tasa ba yayi kan motar, wani irin karo da sukayine yasanya gaba ɗaya motocin nasu tashi sama, alokaci guda kuma suka faɗo ƙasa, cikin ƴan mintuna ƙalilan gaba ɗaya motocin suka fara fitar da hayaƙi.


*Vote*
*and*
*Comment*


fatymasardauna

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ!!!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                   *Wattpad*
           @fatymasardauna
#romance.

*(Gabaki ɗayan wannan fejin sadaukarwa ne agareka HAMEED, ina maka fatan farinciki me ɗorewa a iya ka tsawon rayuwarka.!❣️)*

              *Chapter 53*

Sosae duka motoci biyun ke fitar da hayaƙi, kasancewar ba kaɗan ba motocin sukayi mummunan buguwa, hayaƙi ne ke cigaba da fita sosai ajikin motar kowannensu,  cikin matsanancin sauri, haɗi da gaggawa, ƴan sandan dake gadin area'n, suka taho domin bawa waƴanda ke cikin motar taimakon gaggawa, domin kuwa nanda wasu lokuta idan wani bai taimaka ba, lallai gaba ɗaya motocin zasu iya kamawa da wuta,  cikin sauri da dabara  haka ƴan sandan nan suka shiga ƙoƙarin fito da kowannensu daga cikin motar, gaba ɗayansu babu wani wanda yake da alaman numfashi ajikinsa, gaba ɗaya jini ya ɓata fuskokinsu, har takai ga baka iya tantance kamanninsu,   Ambulance ƴan sandan suka ƙira take cikin ƴan mintuna ƙalilan aka zo aka kwashesu dukansu, Kaitsaye babban privet hospital ɗin dake cikin garin Abuja wato Nizamiyye Hospital aka nufa dasu.
Direct Emergency aka wuce dasu, lokaci ɗaya aka soma basu taimakon gaggawa.

Zaune take akan stool ɗin dake aje gaban dressing mirror,  sanye take da towel ajikinta, yayinda jikinta ke ɗauke da danshin ruwa, da dukkan alamu fitowarta daga wanka kenan,   ahankali take murza sassanyan body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi ajikinta,  harwani ɗan lumshe idanu takeyi, saboda sosai ƙamshin body lotion ɗin keyi mata daɗi, har takai tanajin batason daina goga maiɗin ajikinta, koda ta kammala sama sama ta shafa powder akan kyakkyawar fuskarta, wani ɗan light pink lipstick ta goga akan ƴan madaidaitan laɓɓanta, black eye pencil ta ɗan goga acikin idanunta, mascara tasanya taɗan taje eyelashes ɗinta, take suka ƙara mimmiƙewa sukayi zara zara dasu.
Kallon kanta tayi amadubi naɗan wasu sakanni kana ta lumshe idanunta,  moment ɗinsu na ɗazu ne kawai ke yawo acikin brain ɗinta,  sosai takejin daɗin kasancewa dashi, domin aduk sanda take tare dashi takanji wani abu na musamman na yawo cikin jikinta.

Ahankali ta tashi daga kan stool ɗin inda ta nufi gaban babban drawer ɗinsu, ɓangaren kayanta ta buɗe inda ta zuba musu ido, tunanin wanda zata saka take,  nan dai ta zaro wata doguwar rigar atamfan ABC, wanda take da kalan blue wato shuɗi, sosai zanin keda kyau, yayinda aka shumfuɗa mata wata haɗaɗɗiyar straight gown  me kyaun gaske, rigar irin doguwar nance, sosai kuma aka fitar da shape ɗin ta, yayinda gefe da gefen rigar dama da hagu suka kasance atsage, tun daga ƙasa har gefe da gefen cikinta abuɗe suke,  wani dogon pencil crazy jeans ta sanya, tare da ɗaura tsagaggen doguwar rigan akai, sosai tayi kyau, musamman yanda haɗaɗɗen shape ɗinta ya bayyana ta cikin tsagun rigar, dayake jeans ɗin yakama jikinta sosai, parking dogon gashin kanta tayi  yayinda ta naɗeshi a tsakiyar kanta, wani ɗan madaidaicin blue vail ta yafa akanta, wanda ya kawo har kan cikinta,  sosai tayi kyau cikin shigarta ta, ƙarasawa gaban mirror tayi tare da ɗaukan body spray ɗinsa mai daɗin ƙamshi, wanda akullum ƙamshinsa ke ƙara zautar da ita ta fesa ajikinta,  wani flat shoe tasanya aƙafanta, cikin nutsuwa ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta fice,  kaitsaye ɗakin da zai sadata da babban falon na Oummu ta nufa,  taku biyu ya rage mata taƙarasa zuwa cikin falon taɗan tsaya, daidaita nutsuwa haɗi da tafiyarta tayi, sannan ahankali tatura ƙofar falon ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Zaune ta samu Oummu acikin katafaren falon nata,  fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata sallaman da takeyi, cikin ladabi haɗi da biyayya ta ƙaraso har gaban Oummu, durƙusawa tayi tare da gaisheta, cikin sakin fuska Oummu ta amsa mata, tare da tambayanta ya take,  cikin yanayi naɗanjin kunya Zieyaderh tayi ƙasa da kanta, haka Oummu ke ta janta da hira, itakuwa har cikin ranta kunyan Oummu takeji musamman idan ta tuna abun daya faru daren jia atsakaninta da Mr.Helper. Wayar Oummu dake aje bisa kan dinning table ne tasoma ruri alaman shigowar ƙira, Da sauri Zieyaderh ta tashi don ɗauko mata wayan, sam tamanta cewa agaban Oummu take hakan yasa take taka ƙafarta ahankali, duk dama bawani zafi takeji sosai acikin jikinnata ba.
Da kallo mai ɗauke da tsantsar nazari Oummu ta bita, wani tunani dayazo cikin ran Oummu ne yasanyata sakin murmushi mai ɗauke da tsananin jin daɗi,  daidai lokacin Zieyaderh ta dawo hannunta ɗauke da wayar Oummu'n, cikin ladabi ta miƙawa Oummu wayar tare da dawowa ta zauna,   da sallama Oummu ta amsa wayar, saidai jin abun da ake faɗa mata acikin wayar yasanya ta miƙewa tsaye, cikin tsananin fargaba haɗi da tsoro tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!." Wayar dake saƙale akan kunnen nata ne ya sulale ya faɗi ƙasa, take idanunta suka cika tab da ƙwalla,  cikin fargaba Ziryaderh ta kalli Oummu'n, ji tayi gabanta ya faɗi take wani irin tsoro ya shiga jikinta, hakanan tunaninsa ya faɗo mata arai, jikinta na rawa taƙaraso kusa da Oummu'n,  kallonta Oummu tayi take kuma saitaji wasu irin hawaye mssu ɗumi sun gangaro daga cikin idanunta, wani irin matsanancin tausayin kansune ya kamata,  ganin hawaye na fita daga cikin idanun Oummu yasanya taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta.
Hannu Oummu takai ta dafa kafaɗan Zieyaderh wacce itama idanunta sun cicciko da hawaye, duk da kasancewar ma batasan menene ke faruwa ba,  daidai lokacin akaturo ƙofar falon aka shigo, Mas'oud ne ya shigo shima fuskarsa ɗauke da tsananin damuwa haɗi da tashin hankali, Oummu naganinsa taƙaraso garesa cikin sauri da ruɗewa takamo hannunsa, murya ɗauke da rauni tace.
"Mas'oud, SOORAJ!."
Idanu Mas'oud ya lumshe cike da tausayinsu, cikin son kwantar wa da Oummun hankali yasanya hannunsa ya share hawayenta,murya ƙasa ƙasa yace.
"Muje mu dubasa Oummu."
Da sauri Oummu tajuya ta haura sama don ɗauko mayafinta.
Zieyaderh kuwa gaba ɗaya kanta ya kulle, jin an ambaci sunan SOORAJ,yasanya jikinta ya ɗauki rawa, sosai wani irin tsoro ya shigeta, bata fatan jin cewa wani mummunan abune ya sameshi, bazata iya jurewa ba, sam bazata iya jure abun da zai cutar mata dashi ba.
Oummu ce ta sauƙo daga kan mattakalan cikin sauri, ƙoƙarin yafa ƙaton mayafinta tayi, cikin kulawa ta dubi Zieyaderh dake zaune idanunta cike da ƙwalla, hannayen Zieyaderh'n ta kamo, duka suka ɗunguma sukayi waje,  cikin motar Mas'oud suka shiga, dawani irin speed Mas'oud yaja motar, kai tsaye Nizamiyye hospital suka nufa.

Sosai likitoci suka duƙufa akansu wajen basu agaji da taimakon gaggawa,   sama da awa ɗaya likitotin nan suka share akansu suna ƙoƙarin ceto rayuwarsu,  saidai kuma sunyi iyayinsu, amma abun naneman fin ƙarfinsu, duk da cewa Sooraj baiwani ji ciwo sosai ba, saidai buguwa daya samu ahanannu da kuma ƙafansa kawai, amma kuma yayi suman da har yanzu bai dawo cikin sense ɗinsa ba, shikuwa Pharouk sosai yasamu buguwa akansa, hannunsa da ƙafansa gaba ɗaya sun karye, gashi jikinsa gaba ɗaya ya kukkuje,  sannan shi ne wanda yafara farfaɗowa kafun RAJ saidai kuma sam baya iya zuƙan numfashi da kansa, dole yasanya aka wuce dashi ICU domin ciwon nasa yayi tsanani, shikuwa Sooraj sun bashi duk wata taimako da zasu iya, daganan aka wuce dashi wani ɗakin hutu bayan sunyi masa wata allura mai ƙarfin gaske, wanda aƙalla zaiyi bacci na 5 hours kafun ya farka, suna kuma sa ran idan yafarka zai tashi lafiya ƙalau insha Allah.

Idanunta ne suka sake cika da hawaye ganin sun tsaya abakin ƙofar shiga asibitin, nanfa gabanta yafara dukan uku uku, take wani irin rauni ya cika zuciyarta.
Haka suka nufi cikin asibitin kowa da abun da yake saƙawa acikin rai da zuciyarsa.
Kaitsaye Mas'oud wajen wani babban likita me suna Dr.Anas wanda awajensa case din su Sooraj ɗin yake ya nufa, nan Dr.Anas ya ɗanyi musu ƙarin bayani tare da kwantar musu da hankali,  sosai zuciyar Oummu dana Mas'oud suka ɗan samu salama jin cewar jikin Sooraj ɗin da sauƙi, har ma zai iya farfaɗowa zuwa anjima,  ita kuwa Zieyaderh tuni zuciyarta tanarke da tsananin tausayin mijinta, take taji ba abun da take burin gani daji kamar sa.
Dr.Anas dakansa yayi musu jagora har zuwa ɗakin da Sooraj ɗin ke kwance,  Dr.Anas ne ya dubesu tare da cewa idan suka shiga kar su cika surutu saboda zai iya affecting ɗinsa.
Haka suka shiga cikin ɗakin kowanne zuciyarsa ɗauke da fargaba, kwance suka iskesa flat fuskarsa na kallon sama, dagashi sai dogon wandon jeans a jikinsa, hannunsa na dama ɗaure yake da bandage haka ma ƙafarsa ɗaya itama an nannaɗeta da bandage,  sannu ahankali ruwan da aka ɗaura masa ke ɗiga ajikinsa.
Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar shigowar, lumshe idanunta tayi take saiga hawaye sun kwaranyo bisa kan ƙuncinta, hannunta tasanya ta dafe daidai saitin zuciarta da keyi mata zafi,  ahankali  su Oummu suka ƙarasa jikin gadon, hannu Oummu tasanya ta shafi lallausan sumar kansa, take kuma saiga hawaye zun kwaranyo daga cikin idanunta,  Mas'oud ma ƙarasowa yayi yaɗan shafa kan SOORAJ ɗin,   Dr.Anas ne yayi musu alama akan subiyosa zuwa waje, babu musu dukansu suka bi bayansa, aɗan wani corridor ya tsaya dubansu yayi da kyau tare da cewa cikinsu su bar mutum ɗaya wanda zai kula da Sooraj ɗin, Oummu ne ta dubi Zieyaderh, cikin sanyin murya tace.
"Zieyaderh kibi Mas'oud ku koma gida ni zan zauna dashi kafun ya farka."
Da sauri Zieyaderh ta girgiza kanta so take tacewa Oummu A'a amma kuma bata da bakin musa mata, Dr.Anas ne ya dubi Oummu tare da cewa.
"Bashida mata ne?."
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe, kana tace "Yana dashi."
Jinjina kai dr Anas yayi tare da yiwa Zieyaderh dake hawaye duban tsab,  take jikinsa ya basa cewa itace matar Sooraj ɗin, duban Oummu ya kumayi cikin ɗan sakin fuska yace.
"Inaga kubar wannan sarauniyar hawayen ta zauna idan yaso sai ku ku koma, zaki iya kulawa dashi ae ko sarauniyar hawaye?." yaƙare maganan yana ɗan Murmushi.
Duk da yanayin da suke ciki saida Oummu da Mas'oud suka ɗan murmusa,  maganar Dr.anas kuwa suka bi, inda Mas'oud ya maida Oummu gida don zataje tayi musu girki, nan akabar Zieyaderh.

Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga,  cikin nutsuwa take takowa har zuwa inda yake kwance,   gab dashi ta ƙarasa, ahankali taɗan lumshe idanunta, wanda hakan ya bawa hawayen dake cikin idanun nata daman fitowa,  hannunta ta ɗaura akan hannunsa wanda aka saƙala masa cannula,  wata ƴar farar kujera dake gefe tajawo zuwa gaban gadon, zama tayi akan kujeran tare da ɗaura kanta ajikin gadon nasa, yayinda har yanzu hannunta ke riƙe da nasa,  ahankali ta sauƙe idanunta akan kyakkyawar fuskarsa,  komai nasa abun so da burgewa ne, sosai ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa ya kwanta lub bisa skin ɗinsa, ƴan ƙananan pink lips ɗinsa ta kalla masu kalan burgewa, kana ta dawo da kallonta ga kyawawan idanunsa wanda suke arufe ruf, sosai dogin eye lashes ɗinsa suka kwanta zara zara aƙasan idonnasa,  ɗan lumshe idanunta tayi sannu ahankali takejin ƙarin zazzafar ƙaunarsa na ratsa gaba ɗaya jiki da jijiyanta.
Aje kanta tayi adai dai kafaɗunsa, ahankali take sauƙe ajiyar zuciya, sosai takejin tausayinsa na game gaba ɗaya jikinta,  sannu ahankali wani irin bacci ke fusgarta, ɗaura kanta tayi akan hannunsa, cikin sanyin yanayi bacci ya ɗauketa.

Ahankali yake buɗe kyawawan idanunsa, har ya gama waresu tas,  ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da ɗan karkatar da kansa ya kalli ɓangaren da yakejin ƙamshi irin nasa na ratsa cikin hancinsa.
Lumshe idanunsa yayi, asakamakon tozali da kyakkyawar fuskarta da yayi, ahankali yaɗan soma yunƙurin tashi,  cikin baccinta taji  motsinsa hakan yasa taɗan buɗe idanunta,  daidai lokacin shikuma ya gama daidaita zamansa akan gadon, ɗan juyo da kyawawan idanunsa yayi ya kalleta, itama kallon nasa take, sarƙewan idanunsu waje ɗaya yasanya tayi raurau da idanunta, take suka cika da ƙwalla, shagwaɓe fuska tayi tare da langwaɓar da kanta gefe, yanayin yanda tayi sosai ya bayyana zallan yarintarta,   hakan ya matuƙar burgesa sannan ya ƙarawa fuskarta kyau, wani irin ƙawataccen murmushi ne ya bayya akan kyakkyawar fuskarsa,  idanu ta zaro cike da mamaki take kallonsa, domin kuwa wannan shine karo na farko da ta fara ganin murmushin sa, baki ta buɗe tana kallon yanda yayi bala'in kyau, ashe dama haka murmushi ke yiwa fuskarsa kyau?   idanunsa yaɗan lumshe tare da jingina bayansa da jikin bango,    kusan mintuna 5 ta ɗauka tana ƙarewa kyakkyawar fuskarsa kallo,  sam ta shagala da yanayin yanda taga ya ƙara mata kyau, sosai taji wani irin sha'awan taɓa lallausan sajensa ya zo mata, ahankali ta ɗan kai hannunta  kan fuskarsa, batare da tayi aune ba taji yasanya hannunsa ya cafke nata hannun,  idanunta ta kulle ƙam cike da kunya, ita kanta batasan me yajata hartayi sha'awan taɓa fuskar tasa ba, 
riƙe hannun nata yayi da kyau, ahankali ya jawota zuwa jikinsa,  cikin nutsuwa ya tura ƴan yatsunta acikin bakinsa sannu ahankali yake sucking fingers ɗinta kamar wanda ya samu sweet, lumshe idanunta tayi tare da sauƙe wata ƙatuwar ajiyar zuciya, sosai hakan keyi mata daɗi, ahankali ya matso da fuskarsa gab da tata, iskan bakinsa ya ɗan hura mata, ahankali ta buɗe idanunta ta sauƙesu acikin nasa, hannunsa wanda aka sanya masa cannula yasanya ahankali ya jawota jikinsa, kansa ya ɗaura akan wuyanta tare da lumshe idanunsa, baisan cewa daɗin ƙamshinsa yakai har haka ba sai yau daya shaƙi ƙamshin ajikinta, cikin narkewa haɗi da shagwaɓa ta sanya tafukan hannayenta ta shafo gefe da gefen fuskarsa, so take ta tambayesa ya jikinsa, amma hakanan takejin bakinta yayi mata nauyi, shagwaɓa kawai takeji dashi.
Narkakkun idanunsa da ke kashe zucia ya zuba mata, ganin yanda yake kallonta yasanyata turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, akasalance tace.
"Yajiki?."
Bai amsa mata ba saima ƙara buɗe beautyful eyes ɗinsa da yayi yana kallonta, sosai yakejin wani diffrent feeling ajikinsa, tunowa da irin daɗin da ta jiyar dashi adaren jia, yasanya shi rungumota ƙam ajikinsa, da laɓɓansa masu taushin gaske ya manna mata kiss agefen bakinta, har cikin zuciyarta taji sanyin laɓɓan nasa, sake shigewa cikin jikinsa tayi, ahankali wasu silent tears suka gangaro daga cikin idanunta, ta godewa Allah daya tashi, domin sam batajin zata iya jure rashinsa.
Luf tayi ajikinsa tana ta faman sauƙe ajiyar zuciya, ahankali ya tura duka hannayensa ta cikin tsagun dake gefe da gefen rigarta, sauƙan hannunsa akan tattausan fatar cikinta yasa suka sauƙe ajiyar zuciya atare su dukansu, ahankali yake ƙara tura hannunsa cikin rigarta yana yi mata wani irin shafa mai tafiya da hankali, sosai taƙara shigewa cikin jikinsa, yanayin yanda sajensa ke gogan wuyanta shi yasa gaba ɗaya jikinta yayi weak, ashagwaɓe take yawo da hannunta cikin lallausan sumar kansa.
Cikin nutsuwa ya manna fuskarsu waje ɗaya, haɗuwar numfashinsu guri guda shiyayi sanadiyar faɗawarsu cikin wata duniya ta daban, ahankali ya kamo laɓɓanta, slowly yaɗan tsotsa, kamar honey haka yaji daɗin laɓɓan nata, sake manne bakinsu waje ɗaya yayi, ahankali yake tsotsan laɓɓanta, cikin mayen sha'awa haɗi da soyayyarsa dake ɗibanta itama ta haɗe laɓɓanta waje guda tare da kamo tongue ɗinsa taɗanyi sucking, atare suka sauƙe wani irin numfashi mai zafi, sake matseta yayi tare da soma jujjuya harshensa cikin bakinta, numfashi kawai suke fitarwa, yayinda suke ƙara shigewa jikin juna, wani irin daɗin hakan sukeji su duka biyu, har suna neman fita hayyacinsu.
Mas'oud ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, yayinda Oummu ke biye abayansa, turus haka Oummu da Mas'oud sukayi suna kallon ikon Allah, Da sauri Oummu ta juya tare da komawa wajen ɗakin ta tsaya, wani irin kunya haɗi da farinciki ne suka cika zuciyarta, tabbas ita tasan bataiwa SOORAJ zaɓen tumun dare ba.
Mas'oud kuwa wani irin daɗi haɗi da farinciki ne suka cika zuciyarsa, take yaji wani irin giyar daɗi na ɗibansa, sam duk

42 / 47