Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   28 / 47

81K to 84K   out of 140.6K words

hankalin Oummu, da sauri ta fito tare da ƙarasowa inda suke,  cikin yanayi na damuwa tace
"Subahanallahi me ya faru?"    cikin tsananin zafin dake ratsa har ƙwaƙwalwarta, ta buɗe idanunta da suka tara ruwan hawaye kana sukai ja, yunƙurin ɗaga ƙafanta ta somayi, amma zafin da takeji ya hanata, hakan yasa ta saki wani ɗan siririn ƙaran wahala,   small pink lips ɗinsa ya ɗan ciza tare da raɓawa  ta gefenta zai wuce.  "SOORAJ me kayi mata ne?" cewar Oummu tana me ƙoƙarin kama ƙafan Zieyaderh don ta duba,  fuska ɗauke da ɗan mamaki yasake ɗan waro Idanunsa alaman ni kuma mezan mata, kana ya taɓe lips ɗinsa.
"Subahanallah tayaya haka ta faru? Glass fa ta taka" Oummu tafaɗa tana me riƙe da ƙafan Zieyaderh, wanda har yanzu yake fidda jini, ƙarasowan Almustapha cikin falon kenan ya taraddasu atsaitsaye,  da sauri ya ƙaraso garesu yana me cewa "Lafiya kuwa Oummu me ya faru?"

"Fasashshen glass ta taka, please zoka riƙemin ita naɗauko first aid box sai kayi mata treatment!" Oummu ta faɗa cike da tausayin halin da  Zieyaderh ke ciki.
Babu musu Almustapha ya haura kan step ɗin tare da sanya hannayensa duka biyu ya kama kafaɗun Zieyaderh, wanda hakan yasa harta ɗan kwanto cikin jikinsa.  Sauƙe hannayensa akan kafaɗunta, yayi daidai da bugawar zuciyarsa, da sauri ya rumtse idanunsa tare da dunƙule hannuwansa, lokaci ɗaya yaji wani irin jiri na neman kadashi, aɗan hanzarce ya juya cikin azama yabar falon. 
Da taimakon Almustapha ta iya ɗingisawa zuwa kan kujera, sosai takejin zafi domin kuwa glasses ɗin sun ɗan caketa sosai,  Oummu ne ta dawo hannunta ɗauke da first aid box,  zama Almustapha yayi akan sofa tare da ɗaukan ƙafannata ya ɗaura akan wani ɗan madaidaicin stull,  da cotton yayi using wajen goge mata jinin da ya ɓata ƙafannta, hannunsa yasa ya kama ƙafan, cike da kulawa ya shiga dubawa ko akwai wata ɓoyayyar kwalba dake a
cikin ƙafar, ganin babu yasanyashi ɗaukan hydrogen  ya haɗa da auduga ahankali yake ɗan goga mata akan ciwon, kuka tasanya me sauti tare da rumtse idanunta, sosai takejin zafin hydrogen ɗin,  murmushi Almustapha yayi ganin yanda take kuka tana me cije baki,   cike da salon tsokana yace.
"Haba Bae da zafi ne?" 

Tsaida kukannata tayi tare da buɗe jajayen idanunta, samun kanta tayi da murguɗa masa baki tare da yunƙurin zame ƙafarta daga hannunsa,  murmushin daya bayyana white teeth ɗinsa yayi tare da cewa "Am sorry ai nama gama!" Kallon Oummu tayi tare da ɗan marairaice fuska, Murmushi Oummu dake tsaye tana kallonsu tun ɗazu tayi, aranta kuwa cewa tayi  "Anya abun danayi kyautawa ne?"      "Idan baizama kyautawa ba to tabbas za a ƙirasa da son kai!" Wata zuciyarta ta bata amsa. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa. "Allah shine shaidana nayi hakane don samun nutsuwa da salama azuciyar su dukan biyun, idan hakan bai yiwu ba kuwa to tabbas ko mai ya faru NI CE SANADI, sannan hakan zai zama kamar rashin adalci ne ga rayuwar ZIEYADERH!"    maganan da Almustapha ke matane ya sanyata dawowa daga tunanin da take, inda yake cewa
"Yakamata taje ta huta, daga nan zuwa da safe karta taka ƙafan muga idan babu wani matsala shikenan,  idan kuma mukaga ƙafar ta kumbura  sai muje hospital!" Ya ƙare maganar yana me ƙoƙarin rufe first aid box ɗin dake gabansa.

Da taimakon Oummu Zieyaderh ta iya ɗingisawa zuwa ɗaki,   adaddafe ta iya yin alwalan sallan magriba saboda zafi da ƙafan ke mata,  haka ta samu tayi sallah nanma saida dabara don dazaran ta shumfuɗe tafin ƙafanta aƙasa tofa zafi zai ratsa gangar jikinta.

Yana barin falon haka yaji zuciyarsa nayi masa wani iri, yanajin yanayinsa duk ba daɗi,  peter dake ta zaman jiransa tun ɗazu a waje yana ganinsa yataso da hanzari tare da buɗe masa murfin motar,  shiga cikin motar yayi ransa duk ajagule,   kallon agogonsa yayi yaga  5:50 am. Tsuka yaja tare da lumshe idanunsa da suka ɗan nuna alamun ɓacin rai acikinsu, 6 daidai jirginsu zai tashi amma gashi har yananeman yin late akan wannan stupid girl ɗin,  wani siririn tsuka yaja akaro na biyu, shikam ya lura kamar yanda take mashiririciya haka komanta ma yake, yayi imani haukane kaɗai yake wanzar da irin tsoron da yake ganinta aciki da zaran ta ganshi.  Hakanan yakejinsa cikin ƙuncin rai, suna isowa airport ya buɗe murfin motar agurguje, da sauri peter ya miƙo masa wata ƴar black trolly wanda abubuwan amfaninsa ne ke ɗauke aciki. Amsa yayi kana yashiga can cikin airport ɗin, saida ya kammala komai kafun yataho agurguje ya shiga cikin jirgi don 5 minute kacal ya rage flight ɗin ya tashi.    Yana zama akan kujera ya sauƙe wani irin ajiyar zuciya tare da jingina bayansa da jikin kujeran,  sit belt ya ɗaura kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, kamar yanda jirginsu ya tashi zuwa sararin samaniya haka arai da zuciyarsa yake fatan ace damuwarsa tayi ƙaura daga gareshi,  awannan tafiyan yanason samawa zuciyarsa nutsuwa sosai,    musamman akan sabon cutar da  ta ɗauko mai wanda yakasa sanin gabansa balle bayansa. 

Kwance take luf  akan gado yayinda  ta baza gaba ɗaya gashin kanta akan pillow,  duk da cewa anɗau wasu mintuna dajin ciwon nata amma har yanzu tanajin zafi, wannan zafin da takeji ajikinta shine zafin daya tafi har zuwa cikin zuciyarta, ko wani bugu ɗaya na zuciyarta yakan zo matane da wani sabon sauyin yanayi, akowanni daƙiƙa ji take soyayyarsa na hauhawa acikin zuciyarta,  sake gyara kwanciyarta tayi tare da lumshe idanunta.    
                  SINGAPORE
Adaidai wannan lokacin shima ya gyara kwanciyarsa tare da lumshe kyawawan idanunsa,  ako wani bugun zuciyarsa ɗaya yana tafiyane da sauye sauyen tunani da yake samu daga ƙwaƙwalwarsa, hannunsa ya ɗaura adaidai saman mararsa tare da ware idanunsa, sauƙesu yayi akan haɗaɗɗen adon zanen dake kewaye saman ɗakin,   daga gefe guda kuwa ƙoyayen wutane keta aikinsu wajen bada kaloli masu ma'ana da ɗaukar hankali, domin duk bayan ko wani second kowanne daga cikinsu yake fidda wani irin diffrent colour na haske me kyau,   daddaɗan sanyin garin da kuma iskan da ake shiya sanya yaji gaba ɗaya jikinsa yayi weak,  sake gyara kwanciyarsa yayi akaro na sau ba adadi, burinsa bai wuce bacci ya ɗaukesa ba, don zuwa yanzu zuciarsa takai ƙololuwa wajen matsawa ƙwaƙwalwarsa da tunani, bayan haka kuma gashi akwai gajiya sosai atattare dashi, sauda dama yakan zurfafa tunaninsa akan rashin lafiyansa, saidai kuma yasan komai na Allah Ne sai idan yasone zai baka lafiya, saɓanin haka kuwa kowani irin magani zakasha kodako yana maganin cutar taka sai kaga baiyi maka komai ba, yana matuƙar buƙatar lafiyarsa ayanzu saboda yanaji ajikinsa cewa nan gaba kaɗan zai cire rai da rayuwa, da kuma samun ingantaccen farinciki, tabbas ƙaddaransa babbace amma zaici gaba da ɗaukanta ahaka har izuwa lokacin mutuwarsa.

Bayan tayi sallan asuba bacci tayi sosai hakan yasa ba itace ta farka ba sai after 8. aɗan zabure tatashi daga kwancen da take tare da sanya hannu ta murza idanunta,  ganin hasken rana ya bayyana raɗau ta window'n ɗakinne yasanyata zuro  ƙafafunta ƙasa da sauri,  agurguje tayi wanka tare dayin brush,  koda ta fito sama sama tashafa body lotion ɗinta,  sauri sauri tasanya kayan uniform don tasan zuwa yanzu tayi latti sosai,  zama tayi akan bed tare da jawo cover shoe ɗinta wanda yake na makaranta, ƙoƙarin sanyawa ta somayi,  ciwon dake cikin tafin ƙafanta ne yasoma yi mata ɗan zafi sakamakon safa data sanya, shikuma ciwon baison zafi, ɗan rumtse idanunta tayi tare da soma ƙoƙarin tura kafanta cikin takalmin.  Turo ƙofar ɗakin Oummu tayi bakinta ɗauke da sallama, ganin Oummu yasanyata sakin murmushi tare dayin ƙasa da kanta cikin girmamawa tace da Oummu
"Ina kwana!"

"Lafiya lau, kinsamu tashi kenan yanzu shigowana na biyu kenan, ya ƙafan naki?" Oummu ta tambaya cike da kulawa.

"Da sauƙi Oummu, saidai yana ɗanmin zafi amma basosai ba" 

Kallonta Oummu tayi tare da cewa
"Yanaganki cikin uniform? halan dai baki san ƙarfe nawa bane yanzun ko, kuma ma ai bazaki iya jigilan zuwa school da wannan ciwon aƙafanki ba!" Oummu tafaɗa cike da kulawa

Cikin yanayi naɗan sanyi ta gyaɗa kanta, don bata da abun cewa.

Murmushi Oummu tayi tare da dafata cike da kulawa tace "To kizauna yau ba zuwa school don mahaifiyar Almustapha da kuma wasu daga cikin ƴan uwana sun taso musamman don zuwa ganin amaryarsu!" Oummu taƙare maganar tana murmushin jin daɗi.

Faɗuwar gaba da tsinkewar zuciyane suka ziyarceta alokaci guda, amma saita ɗan daure ɗago kanta tayi ta kalli Oummu, murmushi Oummu ta mata cike da son ƙarfafa mata guiwa tace "Karki damu kanki akan komai Zieyaderh,  ninan matsayin uwa nake awajenki idan kina da abun da kikeso ko abun da bakyaso duk ki sanar dani nikuma Insha Allah Zan sha re hawayenki,  nasan ƴan uwana dukansu masu fahimta ne,  so bakida wata matsala dasu nakuma san insha Allah Zaki samu ƙauna ta musamman daga garesu, karki damu kinji!" Oummu taƙare maganar cike da lallashi.

Kai Zieyaderh ta kaɗa mata alaman  "To"
Cike da jin daɗi Oummu tace "Yauwa ki saki jikinki, ki cire uniform ɗin zan turo akawomiki abinci, sannan kizauna cikin shiri don anjima zan turo meyin kwalliya tazo ta gyaramin ke"  

Kasa cewa komai tayi har Oummu tafice daga cikin ɗakin, ɗan guntun murmushin dake kan fuskarta ne ya koma, take kuma saiga hawaye suna gangarowa daga cikin idanunta, da sauri ta sanya hannu ta share cike da tausayin kanta, haƙiƙa tasan duk wannan abubuwan suna faruwa ne kawai saboda tarasa abu ɗaya aduniyarta wannan abun kuwa bakomai bane face UWA MAHAIFIYA haƙiƙa duk wata Uwa haskece ga rayuwar ƴarta mace matuƙar itaɗin takasance UWA ta gari, UWA itace ginshiƙi sannan kuma farinciki arayuwar ƳAƳANTA, hannu takuma kaiwa ta share hawayenta,  sakamakon knocking door ɗinta da taji anayi, tana buɗewa tayi kiciɓus da Nabila hannunta ɗauke da tray ɗin abinci, Nabila ɗaya daga cikin tarin ƴan aikin gidanne amma ita tana ɓangaren kitchine ne,  itace me share sharen kitchine da goge duk wani inda aka ɓata,  fuskarta ɗauke da ɗan murmushi ta amshi tray ɗin, yayinda Nabila ta juya ta koma, aje tray ɗin abincin tayi tare da soma bubbuɗe plates ɗin dake saman tray ɗin, plate ɗin farko soyayyan doya ne da egg sauce  agefe,  plate na biyu kuwa pepper soup ne na kayan ciki, ɗayan plate ɗin kuwa shawarma ne me zafi har turiri take,  duk acikin abu ukun babu cimarta, hakan yasa da ƙyar ma ta iya cin doyan, sannan ta haɗa da tea, kaɗan taci abincin ta ture gefe, bathroom tashiga ta wanke hannunta, tray ɗin ta ɗauka da niyan sauƙa ƙasa, aikuwa  3 steps kawai ta kawo sukayi kiciɓus da Oummu tare da wata ƴar budurwa dake bayanta, wacce aƙalla bazata haura 27 years ba,   murmushi Oummu tayi tare da duban budurwar  cikin sakin fuska tace
"To Bilkh gama ƴar tawa please kiyi mata irin wanda kika jima bakiyi ba!"
Murmushi wacce aka ƙira da sunan Bilkh tayi cikin hausarta me bada wani irin sauti tace "Bakomai Hajiya Insha Allah zaki yaba da wannan aikin sosai!"

Murmushi Oummu takumayi tare da ƙwaɗawa  Nabila ƙira, dama dayake tana kusa hakan yasa tataho da sauri, tray ɗin dake hannun Zieyaderh Oummu ta amsa tare da miƙawa Nabila tace takai kitchine, duban Zieyaderh tayi cike da kulawa tace "Zieyaderh wannan itace Bilkh shahararriyar me kwalliya ce,  please ki bata haɗin kai, maza ki mata jagora zuwa ɗakin ki"

Murmushi Zieyaderh tayi tare da cewa "To" itadai har yanzu kanta akulle yake don batasan menene za a mata ba.   Suna shiga cikin ɗakin Bilkh ta baje ƙaton ƙaton akwatin meckup ɗinta wanda tazo da shi.  Kallon Zieyaderh tayi tare da ce mata taje tayi wanka, musu banata bane hakan yasa ta wuce toilet, wanka tasakeyi kana ta ɗauro babban towel ajikinta wanda bazai bayyana tsiraicinta ba, tana fitowa Bilkh ta zaunar da ita tare da fiddo da wani tsadadden mai daga cikin akwatin meckup ɗinta ta shiga shafa mata, ita Zieyaderh abunma mamaki ya bata don bataga amfanin shafa mata mai ba bayan itama tanada nata hannun, tana kammala shafa mata mai ɗinne ta zaro wata galleliyar atamfa wacce taji ɗinkin fitted gown me kyau, wanda yana daga cikin kayan da Oummu ta miƙo mata lokacin da Zieyaderh ke wanka,  miƙawa Zieyaderh rigan tayi tare da cewa tasanya,  amsa tayi tare da komawa bayan drawer ta laɓe anan tasanya rigan gudun kada Bilkh taga tsiraicinta, ita kuwa Bilkh abubuwan da zata buƙata taketa haɗawa,  sosai rigan ya zauna ɗas ajikin Zieyaderh baƙaramin kyau kuwa tayi ba, akan wata kujera Bilkh ta zaunar da ita, saida tayi mata duk wani abu daya kamata kafun cikin nutsuwa ta shiga tsantsarawa Zieyaderh meckup akan beauty and innocent face ɗinta.    Bawani lokaci sosai suka ɓata ba kasancewar ba wani meckup aka mata akan fuskar nata sosai ba, simple ne amma yayi kyau sosoi,  take tsananin kyawun Zieyaderh ya sake bayyana,  tsantsara mata ɗaurin ɗankwali Bilkh tayi bayan ta nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyan kanta,  wani haɗaɗɗen sari me kyau da tsada kalan ja Bilkh ta ɗauka,  miƙar da Zieyaderh tsaye tayi tare da soma nannaɗa mata sarin ajikinta, kasancewar atamfar dake jikinta baƙine me ratsin ja, hakan yasa baƙaramin matching yayi da material sarri ɗin ba.
"Wow!" Bilkh ta faɗa bayan ta gama nannaɗawa Zieyaderh sarri ɗin, ita kanta sosai kyawun Zieyaderh ya ɗauki hankalinta, haƙiƙa ita kanta tasan ta iya kwalliya wanda zai gyara mace ya me da mummuna kyakkyawa, amma awannan karon tana da tabbacin cewa ba kwalliyarce tayiwa Zieyaderh  kyau ba, ita Zieyaderh'n ce tayiwa kwalliyan kyau. Turaruka masu ƙamshi da tsada ta fesawa Zieyaderh wacce tazama so silent.  Shigowar Oummu cikin ɗakinne yasa duk suka kalleta. Fuska faɗaɗe da murmushi tace  "Masha Allah, lallai Bilkh aikinki yayi kyau!"

Murmushi Bilkh tayi tare da cewa
"Hajiya ita yarinyar takice me kyau!"
Murmushi me sauti Oummu tayi sannan taja hannun Zieyaderh suka fice daga cikin ɗakin, yayinda Bilkh kuma ta ɗauki wayarta ta soma latsawa.  Tun shigowansu cikin katafaren falon Oummun dayake na musamman gaba ɗaya waƴanda suke cikin falon suka maida kallonsu gareta, matane su Uku zaune acikin falon kowacce idan ka ganta kamar ka latsa jini yafito tsabar fari da jin daɗi, kallo ɗaya zaka musu kafuskanci cewa manyan masu akwai ne.  Cike da fari'a ɗaya daga cikin matan wanda itace bata da yawan shekaru kamar na su Oummu ta tarbo su, hannun Zieyaderh wacce kanta ke ƙasa ta riƙe tana me cewa  "Masha Allah!" agaban sauran matan ta zaunar da Zieyaderh kan wani lallausan carpet. 

Atare duka matan suka haɗa baki wajen cewa "Masha Allah!" don kowaccensu ta yaba da kyau da kuma ƙuruciyar Zieyaderh,  duk da bata ɗago kanta sun kalleta da kyau ba amma kunyanta kaɗai ya isa gamsar dasu. Cike da ladabi Zieyaderh ta gaidasu, dukansu suka amsa fuska asake cike dajin daɗi.  Oummu ce tace taje ta kawo musu drinks da kayan fruits, aikuwa babu musu Zieyaderh ta miƙe, cikin mintuna kaɗan ta cika musu gaba da kayan fruits da drinks wanda duk tanayin aikinne cikin nutsuwarta, ba laifi sukam sun gamsu da yanayin tarbiyan yarinyar sosai, fatansu ɗaya shine Allah yasa tazamo itace matar zama agareshi.  Koda ta kammala gabatar musu da komai ɗakinta ta koma tare da ƙarasawa gaban madubin ɗakin ta shiga duba irin kyawun da tayi, don zuwa lokacin Bilkh tama jima da tafiya. Wani irin murmushi me sanyi tayi tare da sanya hannu ta shafi fuskarta daketa fidda ƙyallin kyau hancinta kuwa sai shinning yake. 

Gyara zama Hajiya Sauba tayi tare da duban ƴar uwarta cike da jin daɗi tace "Gaskiya Sulaimiyya na yaba da hankalin wannan yarinyar sosai Allah yabasu zaman lafiya!"

Da Ameen Oummu ta amsa tana murmushi.

"Nima kuwa na yaba ƙwarai Allah yasanya alkhairi, amma fa wani hanzari ba gudu ba Sulaimiyya  yakamata ace anyi bikinnan acikin watannan, saboda banga amfanin jinkirtawa ba" Cewar Aunty Laylerh.

"Wannan tunanin shine araina Aunty Laylerh, kuma Insha Allah zamusa auren nan bada jimawa ba, domin kuwa daren jiya maganan auren mukayi da Abbansa yakuma ce zasuje shida abokinsa har can garin su yarinyar!"

Murmushin jin daɗi su duka sukayi tare dayin addu'an Allah yatabbatar da alkhairi acikin auren.

(Chaiii wani gurmin sai  ranan da RAJ ɗinku yayi aure zai angwance😝  am so sorry jia banyi update ba naɗan shiga busy ne🙏🏻)

   
*Vote*
    *and comment*

           fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                *WATTPAD*
         @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 40*

Hira Oummu da ƴan uwanta sukayi sosai inda suka cigaba da tsara yanda bikin zai kasance.  Aunty Muhibbat wanda takasance itace ƙaramar cikinsu ta kalli Oummu tare da cewa "Ni aganina idan babu damuwa, zamanta ya dawo wajena saboda kinga ina tare da shuwa arab saboda haka ba ƙaramin gyara zata samu ba"   murmushi Oummu tayi tare da cewa "Hakane amma aikinsan tana zuwa makaranta, duk da ma dai muntsara kan cewar awannan year din zata zana waec nd neco ɗinta" 

Cike da jin daɗi Aunty Muhibbat tace "To Allah yasa ayi komai dai a sa'a" da "Ameen" suka amsa su dukansu, basu wani jima sosai ba suka kama hanyar tafiya bayan sun jibgewa Oummu tsarabobi masu yawa da suka kawowa surukarsu Zieyaderh.

Ɓangaren Zieyaderh kuwa jin kamar ta takura yasanya cikin nutsuwa ta shiga warware sari ɗin dake jikinta tare da aje sa gefe.  Ajiyar zuciya ta sauƙe akaro na barkatai, tare da ɗan jingina kanta da saman gadon da take zaune akai, tunanine cike fal  azuciyarta, turo ƙofar ɗakin da akayi ne yasanyata ɗago kanta ta kalli bakin ƙofan, Nabila ce tashigo cikin ɗakin cikin ɗan rusunawa tace "Hajiya tace ayi mata ƙiranki"
Murmushi Zieyaderh ta ɗanyi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye "Ganinan zuwa" tafaɗa tana me zura bedroom slippers aƙafanta.  Kai tsaye ɗakin Oummu'n ta nufa, ɗan tsayawa tayi ajikin ƙofan tare dayin knocking.  Sanin cewa itace yasa Oummu dake zaune akan gado ta bada izinin shigowa, da sallama ɗauke abakinta ta shigo tare da neman waje taɗan rusuna daga gefe.

Oummu da yawancin lokuta fuskarta baya rabo da murmushi

28 / 47