Author : Maman Teddy Category : Adventure
nanma kamar gida yake, ki nutsu kuma amiki gyaran da kyau, idan kinje makaranta banda yawan yawo ki nutsu awaje ɗaya." kai Zieyaderh ta jinjina mata alaman to.
Ƙwala ƙiran wata mata Hajiya Arabi tayi nan wata ƴar dattijuwar mata taƙaraso cikin falon, nuna mata Zieyaderh Hajiya Arabi tayi tare da cewa ta kaita masauƙi na musamman domin tun yau da dare zasu fara aikinsu. "To" Matar tace tare da duban Zieyaderh tace "Muje ko" babu musu ta ɗauki trolly ɗinta tabi bayan matar yayinda Aunty Muhibbat kuwa suka fice daga falon ita da Hajiya Arabi.
Matarnan nagaba Zieyaderh na binta abaya haka suka nufi wani ɗaki, koda suka shiga cikin ɗakin ɗakine mai girma wanda ke ɗauke da ƴan madaidaitan gado har guda uku masu kyau, sai kuma sif ɗin ajiye kaya da kuma dressing mirror, ƙasan ɗakin amalale yake da wani red carpet me kyau, idanunta ne ya sauƙa akan wasu kyawawan ƴan mata guda biyu wanda ko wacce ke zaune akan gadonta, wayoyinsu ne ahannunsu da alama chatting sukeyi.
Gadon dayake shine na ƙarshe Matarnan ta nunawa Zieyaderh tare da nuna mata inda zata ajiye akwatinta, saida matar me suna Mama Ladi ta gwada mata komai sannan tabar cikin ɗakin, haɗa idanu Zieyaderh tayi da ɗaya daga cikin ƴan matan, murmushi tayi mata tare da cewa "Sannu" itama Zieyaderh'n murmushi tayi tare da ɗaga mata kai alaman yauwa.
Trolly ɗinta ta ajiye tare da warware mayafin dake jikinta, kasancewar lokacin sallan magriba ya gabato anata ƙiraye ƙirayen sallah hakan yasanya ta shiga bathroom tare da ɗauro alwala. tana fitowa ta buɗe trolly ɗinta tare da zaro hijab ta sanya, ɗaya daga cikin ƴan matan da ta samu acikin ɗakin me suna Humaira ne ta miƙo mata sallaya, godiya tayi kana ta shimfuɗa ta gabatar da salla, ba ita tatashi akan sallayan ba sai da ta gabatar da sallan Isha, tana ninke sallayan, Mama Ladi tashigo cikin ɗakin hannunta ɗauke da basket wanda cikinsa ke ɗauke da food flask, da kuma plates guda uku, dubanta takai ga Zieyaderh inda tace "Idan kinci abinci Hajiya tace ki sameta a falo" "To" kawai tace tare da cire hijab ɗin dake jikinta. Humaira ce ta jawo basket ɗin gabanta tare da ɗaukan plates ɗin tashiga zuba haɗaɗɗiyar coconut rice dake ɗaya daga cikin food flask ɗin da aka kawo, dubanta takai ga ƴar uwarta mai suna Nina cikin kulawa tace "Hajiyar chatting zakici abinci ne?"
Hankalin Nina nakan waya batare da ta ɗago ba tace
"Aa sai zuwa anjima"
Baki Humaira ta taɓe tare da zuba abincin acikin plates biyu kana ta ɗaura musu pepper chicken akan coconut rice ɗin, miƙowa Zieyaderh plate ɗaya tayi tare da cewa "Sister ga abinci kici, sunana Humaira waccar kuma cousin ɗina ce sunanta Nina, ke kuma fa ya sunanki?"
Murmushi Zieyaderh tayi aranta tace "Nasmah two" afili kuwa cewa tayi "Zieyaderh"
"Nice name!" Humaira tafaɗa tana me komawa kan bed ɗinta ta zauna, Zieyaderh kuwa kasancewar ba wani yunwa takeji sosai ba hakan yasa bata wani ci abincin da yawa ba, mayafinta ta ɗauka ta fice don amsa ƙiran Hajiya Arabi, a falo tasamu Hajiya Arabi, wani yellow'n towel Hajiya Arabi ta bata tace tacire kayanta, wani ɗan ɗaki ta shiga ta cire kayan nata tare da ɗaura towel ɗin, kasancewar towel ɗin nada girma hakan yasa ya sauƙo har zuwa kan guiwanta, wani irin kunya takeji amma babu yanda zatayi dole haka ta fita, wani ɗaki suka shiga me girma wanda keta ƙamshin kayansu humra da dai sauran kayan gyaran jiki, kujera Hajiya Arabi ta nuna mata zama tayi akai tare da miƙe ƙafafunta, wani kwalba me ɗauke da wani irin farin ruwa Hajiya Arabi ta ɗauko daga cikin wani glass, ƙarasowa gaban Zieyaderh tayi tare da buɗe kwalban ruwan cikin kwalban wanda ke da masifaffen ƙamshi ta shiga shafawa Zieyaderh agaba ɗaya jikinta har zuwa kan cinyoyinta, bayan ta gama ne tace da Zieyaderh tashafa akan ƙirjinta da kuma cikinta, hakan kuwa akayi ganin idanun Hajiya Arabi ba akanta yake ba yasanya ta zame towel ɗin tashafa akan ƙirjinta har zuwa kan lafaffen cikinta, tana gamawa Hajiya Arabi takuma shafa mata wani ruwa saidai shi kalansa yellow ne saɓanin wancan dayake white, shima balaifi yana da ƙamshi sosai, bayan tagama shafa mata yellow'n ruwan ta ɗauko wani abu dake cikin wani ɗan bowl kaman kwaɓaɓɓen dulka tashiga shafa mata saidai wannan karon harda fuskanta aka shafa, wani cup dake cike da wani irin abu kamar zuma Hajiya Arabi ta miƙowa Zieyaderh tare da cewa tatashi tsaye tashanye, cikin ɗari ɗari Zieyaderh takai cup ɗin bakinta, amaimakon taji ɗaci saitaji abun nada ɗan zaƙi hakan yasa ta rufe idanunta ta shanyesa tas, tana aje kofin Hajiya Arabi ta ƙara miƙo mata wani shima nasa kalan da ban saidai kuma shi yana da bauri bakamar wancan ba, shima rufe idanunta tayi ta shanye, still tana ajiye kofin Hajiya Arabi ta miƙo mata wani ɗan kwalba wanda cikinsa ke ɗauke da wani abu kamar zuma saidai shi danƙonsa yazarje na zuma, haka Hajiya Arabi ta dinga ɗura mata abubuwa wani yayi mata dadi wani kuwa akasin haka, saida wannan kwaɓaɓɓen dulkan yayi 1 hour ajikinta sannan Hajiya Arabi ta haɗa mata wani ruwan wanka wanda aka cika turaren wanka acikinsa, koda tayi wanka wani irin tashin ƙamshi jikinta keyi, bacci takeji sosai hakan yasa agajiye ta nufi ɗakin su, Nina nanan tana ta aikin chat, yayinda Humaira kuwa ke waya, wata riga marar nauyi tasanya tare da kwanciya luf akan gado, idanunta ta lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya, ahankali kalaman soyayyan da Humaira ke faɗawa wanda take waya dashi ke shiga kunnenta, wani irin abune taji ya daki zuciyarta take heart ɗinta yasoma beating da sauri, sake lumshe idanunta tayi kana ta cusa kanta cikin pillow da haka bacci ya ɗauketa.
Washe gari tun 7 tagama shiryawa, tun kafun tasanya komai acikinta Hajiya Arabi ta bata tatacciyar madaran shanu wanda babu ko ɗigon mix acikinta, kamar yanda ta faɗa mata tace kada tasha azaune, atsaye tashanye gaba ɗaya madaran sannan taɗanci soyayyen dankalin da aka kawo musu amatsayin break fast, bakwai da rabi daidai Kamalu driver yazo don kaita makaranta. Gaba ɗaya yau bata je ko ina ba koda suka fita break basuje ko ina ba acikin aji sukayi ciye ciyensu, su Nasmah sai tsokananta suke wai tafara ƙamshin amarci. Koda aka tashesu Kamalu driver ne yazo ya maidata gidan Hajiya Arabi, tana cire uniform tayi wanka ko abinci bata ciba Hajiya Arabi ta miƙo mata wani tsumi, saida tasha wasu haɗin magunguna kusan kala uku sannan taci abinci, kasancewar agajiye take hakan yasa ta kwanta tare da ɗaukan littafin Agric Science ɗinta tana karantawa kasancewar gobe zasuyi test, Nina ce tashigo cikin ɗakin gaba ɗaya jikinta sanye da dulka, kallon Zieyaderh tayi tare da cewa "Hajiya tace kije kina da baƙuwa"
"To" kawai tace kana ta sauƙo daga kan gadon, sosai taji daɗi ganin Oummu da tayi, da sauri ta ƙarasa tare da rusunawa agaban Oummu'n cikin girmamawa tace "Oummu barka da zuwa"
Murmushi Oummu tayi tare da cewa "Yauwa Zieyaderh ya kwanan baƙunta?"
"Alhamdulillah ta amsa tana murmushi.
Daidai lokacin Hajiya Arabi ta fito daga cikin ɗakin ta, nan tazauna suka ɗan taɓa hira da Oummu, koda Oummu tazo tafiya har bakin mota Zieyaderh ta rakata, nan Oummu ta buɗe jakarta tafito da kwalin waya ƙirar iphone 9 plus, miƙawa Zieyaderh tayi tare da cewa "Kiriƙe wannan akwai sim card aciki kuma nayi miki setting komai, zanna ƙiranki muna gaisawa, idan kina da buƙatar wani abuma ki sanar dani"
Amsan wayar tayi tare da yiwa Oummu godiya, nan Oummu ta ɗora da cewa "Naƙira shugaban makarantarku munyi magana, kasancewar lokacin da zaku fara exam zai kama lokacin biki, saboda haka nasanar masa komai yakumace ba matsala za'asa wata ɗaliba tayi miki, ki kwantar da hankalinki, idan kina da damuwa ki sanar dani kinji!" Oummu taƙare maganar cike da lallashi.
Murmushi Zieyaderh tayi tare da cewa "Nagode sosai Oummu"
Saida taga tafiyansu Oummu'n sannan takoma cikin gida, zama tayi akan gadonta tare da buɗe kwalin wayar, dalleliyar iphone 9 plus grey colour ne ta bayyana acikin kwalin, yayinda aƙasan kwalin aka shumfuɗe fararen ƴan dubu dubu wanda aƙalla zasu kai 8k, murmushi kawai tayi tare da ciro wayan kana ta maida kwalin ta rufe tasan Oummu tayi hakane saboda tasan idan ta bata kuɗin bazata amsa ba. Kasancewar komai arubuce yake kuma yanzu kanta awaye yake hakan yasa ta kunna wayar tare dayin downloading games ɗin da zasu ɗebe mata kewa. Koda tayi sallan Isha wajen Hajiya Arabi ta nufa, yau kam gyaran da akayi mata har ya zarce najiya, sai kusan wajen 10 sannan tayi bacci.
Wasa wasa yau kwananta 4 agidan Hajiya Arabi wani irin gyaran jiki ake mata na mussaman, acikin ƴan kwanakin huɗun jikinta ya soma sauyawa fatarta taƙarayin smooth yayinda face ɗinta ke shining, acikin kwanki huɗunan kullum da safe tatacciyar madaran shanun take fara sha kafun tayi break fast, wasu irin haɗaɗɗun magungana Hajiya Arabi ke bata, wanda har ƙarfinsu ya soma taɓa ta, don ayanzu takan yawan jin kanta acikin wani irin yanayi,, ɓangaren su Oummu kuwa shirye shiryen biki suke sosai hidima suka shiryawa bikin ba ɗan kaɗan ba.
*Singapore*
Kwance yake akan tangamemen gadonsa yayinda gaba ɗaya jikinsa ke lulluɓe da blanket, ahankali ya buɗe kyawawan idanunsa wanda suka kaɗa sukai ja, hannunsa yasanya ya dafe kansa dake masa masifar ciwo, yau kwanansa uku kenan yana fama da wani irin zazzafan zazzaɓi, da zaran yayi tari kuwa saidai yaga jini ta bakinsa na fita, wani irin ciwo yakeji sosai ajikinsa, yau kwanansa uku banda ruwa baisa komai acikinsa ba, ahankali yaɗan tashi tare da jingina bayansa da saman gadon, rumtse idanunsa yayi tare sanya hannunsa ya riƙe saitin heart ɗinsa dake beating da sauri, Numfashi me ɗumi ya fesar, sai kuma ga tari ya biyo baya farin handkerchief yasanya yashiga goge jinin dake fita daga bakinsa, tsabar zafin zazzaɓin dake jikinsa har karkarwa laɓɓan bakinsa keyi, cikin dakiya ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, ahankali ya sauƙo daga kan gadon, sanye yake da long jeans black colour, kasancewar baisanya riga ba hakan yasa murɗaɗɗun muscles and 6 packs ɗinsa suka bayyana, cikin dauriya tare da aro jarumta ya nufi toilet, agaban sink ya tsaya tare da kunna fanfo ya wanke bakinsa, lumshe idanunsa yayi tare da kifa kansa da jikin bango.
(am so sorry jia banyi update ba kuyi haƙuri Wallahi nashiga busy ne, zanbiyaku bashin najia gobe Insha Allah.)
*Vote and Comment*
fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 43*
Juyi take tayi akan ɗan madaidaicin gadon, yayinda gaba ɗaya nutsuwarta ke neman yin ƙaura daga gareta, ahankali take buɗe idanunta har ta sauƙesu akan Nina wacce ke zaune akan gado tana faman lumshe idanunta, wayarta ƙiran iphone ne kare akan kunnenta, waya takeyi me ratsa zucia, kasancewar ɗakin ya ɗauki shiru, sannan ta ƙure volume ɗin wayan, hakan yasanya gaba ɗaya maganan da akeyi mata acikin wayan yake fitowa fili, kalaman soyayya saurayin nata ke zazzaga mata, yayinda gaba ɗaya maganganun nasu ya ƙare akan maganan aurensu da kuma ɗokin burinsu nason kasancewa tare daya kusa cika.
Ahankali ta janye idanuwanta daga kan Nina tare da ɗaura hannunta akan maranta dake yi mata ciwo, kusan kwana biyu kenan tanajin mararta na ɗaurewa, gawani irin baƙon yanayi da takejin kanta aciki, idanunta ta sake lumshewa tana mejin daddaɗan ƙamshin jikinta na cakuɗa da numfashinta, ita kanta yanzu ƙamshin da takeyi na matuƙar yi mata daɗi, gefe guda kuwa ga skin ɗinta daya ƙara kyau yayi santsi da laushi, zuwa yanzu rabin rayuwarta cike take da kewa, wani irin son ganinsa takeyi, akullum gizo idanunta keyi mata na ganinshi, bata taɓa mantawa da kyakkyawar fuskarsa, kyawawan idanunsa masu ɗaukar hankali, harma da kyakkyawan nagartarsa, komai nasa me kyau ne, tanason komai daya dangance sa,, ahankali wasu siraran hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, kana suka biyo ta gefen ƙuncinta, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da wani irin numfashi, bata iya seccond 1 batare da ta tunasa acikin ranta ba, da tarin tunaninsa acikin rai da zuciyarta bacci ɓarawo ya sace ta..
Yau ta kama saura sati guda aurensu, sosai take shan gyara awajen Hajiya Arabi, zuwa yanzu idan kaga Zieyaderh sai kasha mamakin irin kyaun da tayi, fatarta tayi smooth yayinda duk wata halitta ta cikar ƴa mace dake jikinta suka sake ciccikowa, fatarta takoma milk colour wato kalan madara, ita kanta tasan ayanzu kyawunta ya ƙara bayyana, kuma ayanzune takejin kanta cikakkiyar mace.
Shirin biki ake sosai yayinda Oummu ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayawa amarya kayan da zata sanya alokacin biki, gaba ɗaya ahalin Oummu da Abba cike suke da farinciki saboda auren, kowa ka gani acikin Familyn burinsa shine yaga anyi auren lafiya.
***
Cike da masifa Inna Ma'u ke duban Malam Garba, cikin tsananin Mamaki tace.
"Kasan mekace kuwa? aure fa kake cewa zakayiwa Zieyaderh!"
Kallonta Malam Garba yayi cikin nutsuwa yace. "Ƙwarai Aure zanyi mata kuma saura kwanaki shida aɗaura mata aure inaso kisan da haka, yanzu ma na faɗa miki ne saboda karkice ban kyauta miki ba"
"Kam bala'i lallai Malam kacika butulu, yanzu ni Ma'u ni zakayi wa butulci? Har kasa auren ƴarka ka kuma karɓi kuɗin auren ka cinye batare da sanina ba? to wallahi bazai taɓa yiwuwa ba!" Cikin tsananin masifa Inna Ma'u ta faɗi haka.
Cikin nutsuwa Malam Garba yace "Ki kwantar da hankalinki Ma'u, auren Zieyaderh babu fashi Insha Allah za ayishi, yanzuma burina shine na saida gona ta don na saya mata ƴan abubuwan buƙata kama daga kan kayan ɗaki dadai sauransu"
Cikin mamaki Inna Ma'u tace "Gonarka kuma? Lallai ma Malam, akan auren wannan gantalalliyar yarinyarne har zakace zaka saida gonarka, to bazai taɓa yiwuwa ba!"
Kallonta kawai Malam Garba yayi tare da yin shiru, don acikin abun da yayi niyya babu wani wanda zai fasa, dole zai sauƙe haƙƙin Zieyaderh dake kansa amatsayinsa na uba.
Ganin yaƙi kulata yasanya tasa masa kukan munafurci tare da cewa.
"Nagode ae saboda banice na haifi Zieyaderh ba shiyasa kakemin haka"
Shidai har yanzu idanu kawai ya zuba mata, don sarai yasan kukan munafurci takeyi, don ahalinta babu wani abu ɗaya wanda baisani ba, ganin da tayi cewa yaƙi kulata ne yasanya tasake taso da wani sabon borin inda tashiga haɗa kayanta wai lallai sai dai ya kaita birni ayi bikin da'ita.
Shidai ƙala baice mata ba baikuma sa aransa cewa zaikaita ba don yasan zuwanta bazai zama alkhairi ba.
***
Oummu ce zaune akan gado tana ta faman har haɗa kayan ɗinkin Zieyaderh wanda aka kawo mata ɗazun, Abba ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, Oummu naganinsa ta saki murmushi tare da ƙarasowa garesa, murmushin dake kan fuskar nata ne yaɗan gushe, ganin yanayin yanda fuskar Abba ta sauya, alamun akwai damuwa.
Cikin kulawa tare da ƙaunar mijin nata ta kamo hannayensa, haɗe da dubansa tace
"Lafiya kuwa?"
Ajiyar zuciya Abba yayi tare da kamo hannun Oummu suka zauna akan gado, dubanta yayi tare da cewa.
"Sulaimiyya ina jin kamar Sooraj ba lafiya yake ba!"
Gaban Oummu ne ya faɗi take ta waro idanunta cikin yanayi na damuwa tace.
"Wani abu ya sameshi ne?"
Ajiyar zuciya yakuma sauƙewa tare da cewa. " Shine abun da bansaniba, amma ki kwantar da hankalinki nasan babu wani abu daya sameshi, kawai dai nine danakejin kamar bayacikin halin lafiya"
Cikin tsananin damuwa Oummu tace "Yace maka zaidawo ne?"
"Eh yace zai dawo jibi"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Allah yadawo dashi lafiya" da "Ameen" Abba ya amsa kana yace da Oummu takawo masa ruwa yasha.
Yau yakama saura kwana huɗu biki inda yaune kuma su Zieyaderh suka fara zana jarabawarsu na first term, wanda kuma ita bata samu daman zuwa ba, saidai kamar yanda Oummu ta faɗa ansamo wata ɗaliba ta musamman tana zana mata jarrabawar.
Ɓangaren gyaran jikinta kuwa komai yana tafiya daidai, dok sosai gyaran da akayi mata ya bayyana ajikinta, duk inda ta zauna saita raba tsaraban ƙamshi, baƙaramin sauyi takeji ajikinta ba, lokaci ɗaya ta zama wata babbar yarinya kuma cikakkiyar mace.
Kayanta take haɗawa acikin trolly ɗinta, kasancewar yau zata koma gida don sun kammala duk wani gyare gyaren su, wasu ingantattun magunguna haɗi da turaruka Hajiya Arabi ta bata, sannan musamman ta bata wasu turaruka kala biyu tace kada tayi amfani dasu sai bayan anɗaura auren tana shafasu idan zata kwanta, godiya tayi mata sosai, kana tayiwa su Nina da kuma Humaira sallama, kasancewar su ba aranar zasu tafi ba sai washe gari, inda suɗinma dukansu aure zasuyi, exchenging phone number sukayi, daganan ta ɗauki trollynta tafice daga cikin ɗakin. Cikin nutsuwa tafito compound ɗin gidan tafiya takeyi me ɗaukar hankali yayinda take ta walwali tamkar wata tauraruwa.
duk atunaninta Kamalu ne zaizo ɗaukarta amma saitaga saɓanin haka don Almustapha ta tarar tsaye ajikin mota yana jiranta, tun fitowarta da yayi mata kallo ɗaya ya kau da kansa gefe, baƙaramin kyau da cika ta ƙara ba hakan yasa bazai iya jure kallonta ba, daddaɗan ƙamshin turarenta ne yafara kawowa hancinsa ziyara hakan ne yabashi daman gane cewa taƙaraso garesa, cikin zazzaƙan muryarta tace dashi.
"Ina wuni"
Kansa ya ɗago tare da sakin murmushi cikin kulawa yace "Lapia lau amaryata!"
Ƙasa ƙasa ta hararesa tare da murgaɗa masa baki, dariya kawai yayi kana ya karɓi jakan hannunta, gidan baya ya buɗe ya ajiye jakannata , zagayawa yayi yashiga ɓangaren driver ita kuma tashiga gefen me zaman banza, tafiya suke babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu, gaba ɗaya hankalinta naga wayanta inda take chatting da Shukra wanda ketayi mata tsiya, shikuwa Almustapha gudu kawai yaketa shararawa akan babban titin, sosai ƙamshinta ke taɓasa hakanne ma yasanya yaketa sauri don yakaita gida, gudun kada daddaɗan ƙamshinta ya hautsina masa lissafi. Ababban haraban gidan yayi parking motar, kamar dama jira take da sauri ta buɗe murfin motar ta fita, trolly ɗinta