Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   26 / 47

75K to 78K   out of 140.6K words

faɗa tare da aje wayan.
Shima wayartasa ya aje tare da ɗaukan cover disigner shoe ɗinsa ya shiga sanyawa, iya kyau kam yayi sa, saidai kuma amma fuskar nan ahaɗe take babu alamar fari'a akanta.  
Zaune suke su duka uku akan dinning ɗin, sanye take da kayan uniform ɗinta na riga da wando,  ahakali take tsakalan chips ɗin dake gabanta, gaba ɗaya batajin daɗin zama acikinsu don haryau ganinta take amatsayinta na bare. Gaba ɗayansu  ƙamshin turarensa ne ya cika hancinsu.    Cikin ƙasaitarsa yake tahowa hannunsa ɗauke da wata ƴar briefcase me kyau,  kujera yaja ya zauna cikin ƙasan maƙoshi yace "Barka da safiya Oummu"    murmushi tayi masa tare da cewa "Barka, hope kunyi waya da commisioner?" 
Kansa ya kaɗa mata alamar "Eh" 

Mood ɗinta ne yaɗan sauya tare da cigaba da cewa "Ya faɗa maka cewa yarannan da suka harbeka sun faɗi wanda ya turosu ko? gaskiya nikam nashiga fargaba da tsoro,  indai har akan aikinka za a iya turowa akasheka, me kenan kake tunanin zai faru anan gaba? zasu iyayin komai!" ta ƙare maganar fuskarta cike da damuwa. 

Kafun Yayi magana Almustapha yace "Nima nayi mamaki ƙwarai da akace wai MR.J.J  ne yaturo ayimaka hakan, wani irin tsananin gabane ke tsakaninka dashi ne wae? Meyake nema dakai ne,  tunfa sanda aka baka BM yakejin haushinka, gaskia yanzu kam baikamata mubarshi ba!"  ya ƙare maganar cikin yanayi naɗan ɓacin rae. 

Aje mug ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa "Its Okay, anyi arresting ɗinshi  jiya" yana gama faɗan haka ya miƙe tare da  ɗaukan tissue ya goge bakinsa, briefcase ɗinsa ya ɗauka ya fice, duka suka bishi da kallo, hakanan yake shi koda yaushe baiso ayi magana me tsawo dashi, sai kace marar gaskiya.    

Ture plate ɗin abincin dake gabanta tayi tare da ɗaukan school bag ɗinta dake gefe ta rataya. 

Zieyaderh Oummu taƙira sunanta, "Na'am" ta amsa asanyaye.  "karki manta inkin dawo ki sameni aɗakina kinsan gobene tafiyarmu"  "To" kawai tace sannan ta juya tafice daga cikin falon, tana fitowa compound ɗin gidan shikuma motarsa na fita daga cikin gidan,  mota tashiga ranta duk ba daɗi.
Ko amakaranta yau bata wani sake ba, bayan sundawo break ne aka turo wae principal na ƙiranta, saida gabanta yafaɗi amma haka ta daure taje, wata leda ya bata wanda ke ɗauke da wasu sabbin uniform har kala uku yace mata daga yau su zatana sanyawa. Sosai tayi mamaki amma sai bata nunaba ta amsa kawai ta fice, koda taje aji suka duba kayan, sket ne irin high waist ɗinnan wanda ƙasansa yake da faɗi, sai kuma wata ƴar rigar makaranta fitted da hijab ɗinta wanda idan tasa zai ɗan sauƙo mata kaɗan.   Mamakine ya kashesu su dukansu.  Shukra ce tace "Wannan fa kayan bakowa kesawa a school ɗinnan ba, kodai kinzama house wife ne bamusani ba?"   hararanta Zieyaderh tayi tare da turo baki gaba cikin takaici tace "Ni bawata house wife ɗin dana zama!" dariya suka sanya su dukansu, daga haka sukaci gaba da hiransu, kaɗan kaɗan take sa musu baki.   Har aka tashi sukuku  haka takejin kanta, koda ta koma gida ko falo bata sauƙo ba, haka ta ƙare kwanciyarta aɗaki...  Washegari   Saturday.     Ƙarfe 8 daidai ta kammala shiryawa cikin kayan da Oummu ta bata tace tasanya, riga da sket ne na tsadaddiyar atamfar Vlisco, wacce taji ɗinki, sket ɗin irin pieces ɗinnan ne yayinda rigan takasance fitted, sosai kayan suka amshi jikinta, kasancewar atamfar kalan Maroon gareta hakan yasanya ta sanya maroon hijab ajikinta, sosai tayi kyau duk da cewa batayi wani kwalliya akan fuskarta ba,  flat shoe ɗinta ta sanya tare da  kallon kanta amadubi, ita kanta tasan tayiwa kanta kyau.      Saida suka biya ta wani super market Oummu tayi sayayya sannan suka ɗauki hanyar zuwa KD inda acan ƙauyen su Zieyaderh yake.  Ƙarfe 1 na rana daidai suka iso cikin ƙauyen nasu na Saminaka, tun daga lokacin ƙirjin Zieyaderh ke dukan uku uku,   da ƙyar take iyayiwa Kamalu driver kwatance har suka iso ƙofar wahalallen gidansu,  tun shigowarsu ƙauyen yara kebinsu yayinda manya kuwa ke bin haɗaɗɗiyar motarsu da kallo.    Shawo kwanan Malam Garba kenan hannunsa ɗauke da wani buhu, turus haka yaja ya tsaya yana me bin motar daya gani fake aƙofar gidansa da kallo.  Da sauri ya ƙarasa daidai lokacin kuma su dukansu suka fito daga cikin motar, koda zata shekara ɗari ne batanan bazai taɓa kasa gane jininsa ba, bakinsa abuɗe fuska ɗauke ɗa mamaki yake kallon Zieyaderh, itama kallonsa take lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, ji take kamar taje ta rungume Baban nata, amma kuma tanajin tsoro.  "Ziyada!" yaƙira sunanta muryarsa na rawa.  Kasa amsa masa tayi sai kawai ta fashe da kuka.  Shima hawayene kwance acikin idanunsa. Kamar wadda aka wurgo daga sama haka Inna Ma'u tafito daga cikin gidanta, don tuni labari yakai mata cewa wata haɗaɗɗiyar mota fa faka aƙofar gidanta.  Bakinta awangale taƙarasa gaban yarinyar da take kallonta kamar Zieyaderh, hannu tasa taɗan taɓa fuskar yarinyar dake kuka,   "Laaaaa ha'ila wallahi itace, shegiyar gari kin gama gararanbanki kindawo ko?" Inna Ma'u tafaɗa tana me ƙarewa Zieyaderh kallo, mamaki kuwa aranta kamar zai kasheta.  Ƙasa Zieyaderh tayi da kanta, Malam Garba shine wanda ya kama hannunta tare da duban Oummu dake tsaye yace.
"Hajiya kushigo daga ciki!" Babu musu Oummu ta bi bayansa yayinda yake riƙe da hannun Zieyaderh, aikuwa Inna Ma'u ma rufa musu baya tayi bayan ta tsaya ta gama ƙarewa motar da sukazo da ita kallo, harwani yawu ta haɗiya natsananin kwaɗayi dason abun duniya, musamman ma da ta hango ɗan ragowan lemun fanta dake gaban motar. 

Gudu gudu sauri sauri haka taje ta ɗauko tabarma ta shumfuɗawa Oummu baki har kunne tace "Hajiyan Birni zauna mana!"  Murmushi Oummu tayi tana me kallonta sannan ta zauna aranta tace "Kamar bayanzu tagama zagi ba"  Malam Garba da kansa ya kawo musu ruwa, ita dai Zieyaderh laɓewa tayi abayan Oummu, don har cikin ranta tana jin tsoron abun dazai biyo baya.  

Gyara zama Oummu tayi tare da ɗagawa baban Zieyaderh gaisuwa, amutumce ya amsa, kafun tasake wata magana Inna Ma'u tayi saurin cewa. "Mutanen Binni Sannu marabanki da zuwa Hajiya!"  Still murmushi Oummu  tayi tare da jinjina kanta alaman yauwa.   Batare da ta bari kowa acikinsu yace wani abuba tace "Lallaima Zieyaderh wato dakika gudu kaina kikeso na aurawa tsoho ɗan dashen? ko kuwa kina tsammanin nida ubanki muna da kuɗin da zamu biyasa abun daya kashe ne, wallahi mudai kin cucemu akan guduwarki saida duk wani ɗan abun dana mallaka ya ƙare saboda ɗan dashe cewa yayi sai mun biyasa kudin daya kashe,  kin cuceni kin cuci mahaifinki wallahi!!" Imma Ma'u tafaɗi haka tana me matse wasu munafukan hawayen ƙarya data ƙaƙalosu da ƙyar.    Sake cewa tayi "Amma Allah ne zai mana sakayya, koda yake ma ai yanzu nasan kintara kuɗi sosai ko bakomai zan fanshe asarata" tana murmushi ta ƙare maganar.   Oummu kam mamaki al'ajabi haɗi da tsoro al'amarin matar ya bata, wato dai ita ko agaban wayene bazata iya ɓoye maitanta ba.  Cikin sauri taɓuɗi baki zata sake cewa wani Abu, da sauri Malam Garba yace "Ya isa haka Ma'u, dafari ya kamatane mufara sanin ina taje bawai irin waƴannan kalaman yakamata ayi mata ba" afusace Inna Ma'u tajuya zata faɗa masa baƙar magana sai kuma tatuna da wani abu tafasa. Saita fara yaƙen ƙarya tana me ƙarewa komai dake jikin Zieyaderh kallo. 

Murmushin takaici Oummu tayi tare da kai dubanta ga Baban Zieyaderh, sannu ahankali tayi masa bayani akan cewa ɗantane ya tsinci Zieyaderh bawai yawon iskanci ta tafi ba.   Ajiyar zuciya me ƙarfi Malam Garba ya sauƙe tare dayiwa Allah godiya daya sanya ƴarsa ta faɗa hannu na gari.  Itakuwa Inna Ma'u afakaice take hararan Oummu aranta kuwa cewa tayi "Kuji ƙaryan banza, yo koma gaskiya ne wayasan abunda sukeyi dashi ɗannaki, kai banma yarda ba yanda yarinyarnan tayi ɓul ɓul da ita akwai abun da take aikatawa wata ƙilama cikine da ita"   tana gama ƙimtsa zancen zucinta tayiwa Zieyaderh ƙuri, ba inda take kallo kamar cikinta, wai adole saita gano ko cikine da ita, burinta bai wuce taga tumbinnata yaɗan taso ba ta tabbatar da zarginta.   

Godiya sosai Malam Garba ya shiga yiwa Oummu na irin riƙon amanar da tayiwa ƴarsa, don har acikin ransa yana me nadamar irin rashin kulawan daya nuna mata abaya, sannan kuma yana ƙaunar ƴarsa sosai, dan itace kaɗai jininsa aduniya, amma yazaiyi da sharri da kuma tsoron Inna Ma'u da yake, duk itace ummul aba'isin faruwar komai.   Miƙewa yayi yace zaije ya samo musu fura.   Aikuwa yana fita Inna Ma'u tace "Hajiyan birni ince dai ɗannaki daya tsinceta gidanki ya kawota ba gidansa ba?" 

Mamakine ya kama Oummu cike da mamakin tambayar tace "Mekike nufi?"  da sauri Inna Ma'u ta washe baki tare da cewa "A'a babu abun danake nufi kawai dai tambaya ne,  ke Zieyaderh cire lufayan mana kisha iska" Tafaɗa cike da zaƙuwan son ganin yanda cikar halittan Zieyaderh'n ya koma, tayi rantsuwa matuƙar taga cikin Ziryaderh yaɗan tasa to wallahi saita cucesu maƙudan kuɗaɗe.  (Chaii guys Inna Ma'u fa ta tsananta😆) 

Kallon Oummu Zieyaderh tayi, idanu Oummu ta mata alaman karta cire mayafinta, aikuwa saita yi burus da maganan Inna Ma'u. Wani irin malolon baƙin cikine ya cika zuciyar Inna Ma'u, don sarai ta ga lokacin da Oummu tayiwa Zieyaderh'n idanu.    Aranta tace "Wallahi ko zaku mutune saina laƙaba muku wani sharrin dasai kunbani kuɗi ƴan iska"     

Babu jimawa Malam Garba ya dawo hannunsa ɗauke da ƙwaryan nono, babu wani ƙyama haka Oummu ta zage tasha nonon daganan tace da Malam Garba idan ba damuwa tanaso tayi magana dashi.    "Magana kuma dashi kaɗai?" Inna Ma'u ta tambaya tana zare ido.  Babu wanda ya kulata saima iso da Malam Garba yayiwa Oummu zuwa soro tayanda babu wanda zaiji abun da suka tattauna, cike da fahimtan juna Oummu tayi masa bayanin duk wani abu dake tafe da ita, har acikin ransa yayarda da matar da kuma kamalanta saboda haka atake ya amincewa buƙatarta baƙaramin daɗi Oummu taji ba, nan suka tsaida magana cewar zata turo manya don atsaida magana, inda shikuma yace ko babu wasu manya ya yarda da ita ya bawa Ɗanta Almustapha Auren Ƴarsa Zieyaderh, duk lokacin da suka shirya kawai suzo ayi biki.

(uhhhh guys kushiryafa kuna da biki😝)


*Vote and Comment*
    
        
           fatymasardauna

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
           
             *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*
       
            *WATTPAD*
      @fatymasardauna
#romance

*This page is dedicated to you my dear @Zeety delight... heart you dear*

            *Chapter 37*

Da tsananin farinciki ɗauke akan fuskar ko wannensu Oummu da Malam Garba suka shigo cikin gidan, Inna Ma'u na ganin hakan wani ƙaton baƙinciki ya ɗarsu azuciyarta, hakanan taji ajikinta cewa hanyar ƙaruwa suka tattauna, ae kuwa nan ta ƙudura aranta cewa Oummu na tafiya sai tayi maganin Malam Garba, yadae santa ae yakuma san wacece ita.

Kallon Zieyaderh Oummu tayi fuska ɗauke da murmushi tace "Inaga ya kamata ae ace mutafi tun yanzu, kada tafiyan dare ya kamamu"   
Jin abun da Oummu tace yasanya ƙirjinta bugawa, ahankali ta ɗago idanunta tare da ɗan satan  kallon mahaifinnata, cikin rashin sa'a tasamu shiɗinma kallonta yake, da sauri tayi ƙasa da kanta, murmushi yayi tare da cewa "Bakomai kuje Zieyaderh Allah Yakiyaye hanya ya tsare, nima inanan zuwa tunda yanzu nasamu adreshin inda kuke." 
Wani irin sanyi ne Zieyaderh taji na ratsa zuciarta, sam batayi tunanin mahaifinta zai barta ta koma ba. 

"Chab amma kuwa Garba kayi banzan hali, yanzun barinta zakayi ta koma, oh wato kaidai ba ka gaji da jin zagin da mutane ke mana agarinnan ba, karka manta fa duk  akan ɓatanta sunanmu ya ɓaci,  to babu inda zataje tananan tadawo kenan!" Inna Ma'u ta faɗa amasifance, don sam bata tsammaci haka ba.

"Haba Ma'u meyasa ne bazaki sanja ba, dan Allah Kibar yarinyarnan tayi tafiyarta, tafara karatu acan birni, tsayar mata da karatunta bashida wani amfani"  Malam Garba yafaɗi haka cikin ɗan lallashi saboda yasan halin kayansa sarai ba mutumci.

Cike da kumfar baki Inna Ma'u tace "Dole kace haka mana saboda ƴar kace, ai dama ninasan banice na haifeta ba, kuma zaman birni kam wannan algungumar ƴar taka ta gama yinshi....." Bata gama rufe bakinta ba taji sauƙar wani abu me ɗan nauyi akan cinyarta,   idanu ta zaro lokaci guda tare da haɗiye maganan dake bakinta, take yanayin fuskarta ya sauya daga ɓacin rai zuwa murmushi. "To Alhamdulillah, irin wanga farare bugun can babban birni, Hajiyan Birni Allah ya ƙara arziki!" Inna Ma'u tafaɗa bakinta har kunne,   kuɗine masu yawa Oummu ta aje mata don rufe bakinta, ai kuwa lokaci guda sai ga bakinnata ya rufu .    cike da nishaɗi tace.
"To yanzu sai yaushe zaku kuma dawowa?"    yanayin yanda tayi maganan tana me ƙoƙarin cusa kuɗin cikin lalitantane yabasu daria amma sai suka gimtse, ɗauke da ɗan murmushi Oummu tace.
"Nan bada jimawa ba Insha Allah, Nangaba kaɗan kema nasan zaki kaimana ziyara!"

"Sosaima kuwa, kice  ziyarori ma ba iyaka ziyara kaɗai ba, don fa basau ɗaya zanzo ba!!" Inna Ma'u tafaɗa cikin jin daɗi, dama ita abun duniya shine kanta.

Har wajen mota suka rakasu,  bayan motar  Oummu ta buɗe wanda ke shaƙe da kaya, Kamalu driver tasanya ya shiga ciro kayan yana kaiwa cikin gidansu Zieyaderh, kayan abincine kala kala da kuma wata leda dake ɗauke da kayan sawa, atamfofi da shadda irin na maza, godiya kam ba irin wanda baban Zieyaderh baiyi mata ba, duk da yanuna mata cewa kayan sunyi yawa, amma saitace masa ba komai,  koda ta bashi kuɗi ƙin amsa yayi babu yanda batayi dashi ba amma haka yaƙi amsa, Inna Ma'u kuwa daɗine ya isheta, musamman ma ganin ana shigar da kayan abinci cikin gidanta.  Haka su Zieyaderh suka baro cikin ƙauyen zuciarta cike da kewan babanta.    Har bacci tayi a hanya kafun su iso, gaba ɗaya zaman mota ba daɗi ji take duk jikinta yayi mata wani iri.

Suna isa gida kowa ɗakinsa ya wuce, don gaba ɗayansu agajiye suke,  da ruwan zafi tayi wanka kana tabi lafiyar gado.

Sunday. 
Yawanci duk ranan weekend atare suke cin abinci akan dinning,  tun 8 tatashi tayi wanka,  riga da sket na 1million stones tasanya wanda suka amshi jikinta sosai, tayi kyau.  Wani ɗan madaidaicin mayafi ta sanya ta rufe jikinta, a kitchine ta samu Oummu cike da ladabi ta gaida ta,  fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata,  yauma kamar koda yaushe itace ta shirya gaba ɗaya abincin akan dinning.   Ƙamshin turaren Almustapha daya shiga hancinta shi yasanyata ɗago da kai ta ɗan kalleshi, ƙasa tayi da kanta tare da gaidashi,   amsa mata yayi yana me jan kujera ya zauna, sosai yau ɗin tayi masa kyau acikin shigarta,  duk da cewa bai taɓa ganin kwalliya akan fuskarta ba amma gaskiya tana da kyau sosai.  

Oummu da Almustapha ne suke taɓa hira kaɗan kaɗan yayinda ita kuma take serving ɗinsu,   tunaninsa ne kwance aƙasan zuciyartaz hakanan taji wani iri da bataga ya fito ba, tunaninta ne ya katse sakamakon  wani daddaɗan sanyin da taji yana ratsa jikinta, gefe guda kuma ni'imtaccen ƙamshinsa dake zautar da'ita ne yashiga cakuɗa da numfashinta. 
Sanye yake da blue crazy jeans and Blue t-shirt mai kyau da tsada ƙiran company'n D&G,  sosai yayi kyau kwarjininsa yasake bayyana, yayinda gashin kansa kuwa sai shinning yake, kujera yaja ya zauna, dakansa yayi serving kansa, wajen haɗa tea, ahankali yake sipping tea ɗin yayinda kansa ke ƙasa, yau babu waya ahannunsa amma duk da haka yi yake kamar hankalinsa baya garesu,   gaba ɗaya wajen ya ɗauki shiru,  kowa abincinsa yakeci yayinda akabar mutane biyu daga cikinsu da saƙar zancen zuci,  gaba ɗaya hankalinta yana garesa, so take ta ɗago idanunta ta kallesa amma fargaba ya hanata.
Tissue Oummu ta ɗauka ta goge bakinta tare da dubansu su dukansu, cikin nutsuwa tace  "Ina da buƙatar hankulanku  agareni dukanku!"  Almustapha ne ya fara aje cokalin dake hannunsa tare da duban Oummu, itama Zieyaderh ɗago kanta tayi ahankali tana me kallon Oummu'n, shikam ko motsawa baiyiba, kana bai kuma daina shan tea ɗinsa ba.

Gyara zama Oummu tayi tare da cewa.
"Sooraj da Almustapha inaso nayi maganannan ne agabanku saboda ko ba komai kamar yayye kuke awajenta, sannan awajenta zataji maganar  amatsayin sabuwace, saɓanin ku da kuka taɓa jinta"   ɗan numfasawa tayi kana tace..
"Zieyaderh!"

Tun kafun ta kammala maganganun nata ƙirjin zieyaderh ke bugawa, asanyaye tace.   "Na'am!"

Tashi Oummu tayi daga inda take zaune, tare da jawo wata kujera ta zauna gab da Zieyaderh'n, hannayen Zieyaderh Oummu ta kamo cike da son gamsar da ita tace.
"Haƙiƙa kowacce uwa tanaso ɗanta ko ƴarta su samu abokan zama na gari, burin kowacce uwa adunia shine ƴarta mace ta dace da mijin aure, haka ma kuma ɗanta namiji ya dace da macen aure,  tamkar ƴa haka na ɗaukeki Zieyaderh,  bazan taɓa son wani abu dazai cutar dake ba,  bazan miki dole ba, saboda kema kina da ra'ayi kamar kowa, halayyanki da kuma irin nutsuwarki yasanya naji ina kwaɗayin da ki ƙara zama acikin zuri'ata, duk da cewa munatare dake ayanzu, amma anan gaba ba lallaine mukasance tare ba, dole watarana aure zai ɗaukeki ya nesantaki damu, bazanyi baƙinciki ba idan kika samu adalin miji daga wani waje na daban, amma zanfi so ace daga cikin zuri'ata kika samu wannan adalin mijin, ba daga wani waje daban ba,  kamar yanda nace bazan miki dole ba, ba kuma umarni nake baki ba, saidai  ganin ya cancanta yasanya ni yin tunanin  haɗaki  aure da ɗana Almustapha!"

Dummmmmm tamkar ankwaɗa mata  katuwar guduma akan ƙirjinta haka taji, yayinda agefe guda kuwa  taji sauƙan kalaman Oummu acikin kunnuwanta tamkar almara, wani irin abune taji ya sarƙemata maƙoshi, take tasoma tari har  saida manya manyan  idanunta suka rikiɗe daga farare zuwa jajaye, da sauri Oummu ta ɗauko ruwa ta bata, cikin ikon Allah tanasha tarin ya ɗan lafa,  jingina bayanta tayi da jikin kujera tare dayin ƙasa da kanta, me Oummu ke faɗane? Kodai kunnuwanta ne basuji mata da

26 / 47