Author : Maman Teddy Category : Adventure
yatsun hanunta dake cikin nasa.
Da sauri ta ɗago golding eyes ɗinta ta kallesa, wani irin abune taji yana yawo acikin jikinta, sam batasan me yasa wani yanki na zuciyarta ke ƙoƙarin accepting ɗinshi ba, hannayenta dake cikin nashi ta soma ƙoƙarin zarewa, babu musu yasake hannun nata, sai dai kuma be janye mayun sexy eyes ɗinsa daga kanta ba. Murmushin daya bayyana kyawunta tayi tare da miƙewa tsaye, batare da ta kalleshi ba tace "Zan koma class"
Shima miƙewa tsaye yayi tare da ɗan sakin murmushin daya sanya dimples dinsa loɓawa, wani farin envelope yazaro daga cikin aljihunsa, wanda aka ƙawata bayan envelope ɗin da zanen flowers masu sheƙi, gwanin burgewa, miƙa mata envelope ɗin yayi, ɗago ɗara ɗaran idanunta tayi ta ɗan kalleshi, mumushi yayi mata kamar zai shige jikinta haka ya sake matsowa gaf da ita, yanayin idanunsa ne suka sauya, take taji wani sabon abu na sauƙa ajikinta. "Pleaseee!!" yaja maganan tare da ɗan ƙanƙantar da idanunsa. Adaburce tashiga kakkare jikinta, sam bata sabayin irin wannan kusancin da wani namiji ba, gaba ɗaya duk abun da Farouk keyi mata ganinsu take wasu daban, kowacce kalma da zata fito daga bakinsa jinta take tayi mata nauyi, takan rasa nutsuwarta idan taganshi akusa da ita sosai, domin wani irin faɗuwar gaba takeji, ganin irin mood ɗin data shiga yasanyashi sake kamo soft hand ɗinta, envelope ɗin ya ɗaura mata akan hanunta, tare da bin kyakkyawar fuskarta da ido, sam batasan da yaushene kuma ya akayi taganta tana tafiya ba, sauri tashiga yi burinta ɗaya taganta acikin class, gaba ɗaya ma ta manta da cewa basuyi sallama ba. Shikuwa Farouk wani killer smile ya sake bayan yaga shiganta cikin class, baisan me yasa ba hakanan yake losing control ɗinsa idan yana kusa da ita, ayanda ya fahimce ta yarinyace wacce take real innocent, batasan komai agame da soyayya ba, da wannan daman zaiyi amfani wajen koya mata sonsa, zai koya mata yanda zata sosa fiye da kowa, daga ƙarshe kuma zaiyi ƙoƙari wajen ganin ya sameta amatsayin Mallakinsa, sosai yake sonta, sosai yake kuma son kasancewa tare da ita. Da wannan tunanin ya ƙarasa wajen da yayi parking motarsa.
Kamar wacce aka jefo haka ta faɗo cikin class ɗin, ko izinin shiga ajin bata nema ba. da yake a bencin gaba suke kuma malamin dake cikin class ɗin, gaba ɗaya hankalinsa naga board yana rubutu, shiyasa bai kula da shigowanta ba harta zauna, kallonta Shukra da Nasmah sukayi, cikin ƙasa ƙasa da murya Nasma tace. "I hope ba wani abun kikayi ba, naga jikinki duk yayi weak"
Sai alokacin taɗan soma dawowa sense ɗinta, murmushi ta ƙaƙalo tare da girgiza kanta alaman babu komae. Nasmah bata sake cewa komai ba ta maida hankalinta ga karatun da ake musu.
Duk abunda Malamin Chemistry ɗin ya koya musu ta bayan kunnen Zieyaderh yabi ya wuce, sam ko kaɗan hankali da tunaninta ba akansa suke ba, tunaninta yayi nisa ne izuwa wani waje daban, Farouk shine wanda yayi tsaye aranta.
"I love you!!!"
kalmar daya furta mata shiketa dawowa cikin tunaninta, lumshe beauty eyes ɗinta tayi tare da sakin wani murmushi wanda batasan da bayyanarsa ba, hakanan taji wani sanyi aranta, sosai daɗin kalman ke ratsata, kulawa shine abun da ta rasa tun tana ƙarama, kalmar Soyayya kalmace da babu wani wanda ya taɓa furta mata shi, hakan yasa takejin ayanzu tamkar wani kyautan farinciki Farouk ya bata, duk da cewa kai tsaye bazata iya tantance me takeji agame dashi ba, amma tabbas zuciya koya take tanason me kyautata mata, tana a wannan tunaninne har malamin chemistry ɗin yafita batare da ta saniba, kasancewar period ɗinsa ya ƙare, dafa ta da Shukra tayi shi yayi sanadiyar ɓacewan tunanin da take.
"Lafiyanki ƙalau kuwa Zieyaderh?"
Shukra ta tambaya tana me ƙarewa fuskar Zieyaderh'n kallo.
Board ta kalla tare da ɗan waiwayawa bayanta, cikin mamaki tace.
"Wae ina chemistry teacher'n ya fita ne?"
"Da ke zai tsaya jira?" Shukra ta bata amsa tana me harhaɗa text books ɗin dake watse saman desk ɗinta.
Murmushi kawai Zieyaderh tayi tare da duban Nasmah, cikin sakewa tace.
"Gaskiya ban fahimci abun daya koyarba please Nasmah taimaka min"
Dukansu tsaida abunda sukeyi sukayi tare da kallonta.
"Bazaki taɓa fahimta ba ae tunda anzuba miki kalaman love acikin brain ɗinki" Shukra tafaɗa tana me guntse dariyar dake ranta.
Hararanta Zieyaderh tayi tare da cewa "Love kuma?"
Dariya Nasmah da Shukra sukayi tare da tafawa, kallonsu tayi kawai itama saitayi murmushi,
jujjuya envelope ɗin dake hanunta ta shiga yi.
"Lover gurl!" Shukra tafaɗa tana dariya.
Kallonta Zieyaderh tayi, cikin yanayi na shagwaɓa tace "Allah Shukra banaso fa" Dariya dukansu suka sanya, envelope din dake hanunta ta soma ƙoƙarin buɗewa, duk suka zuba mata ido.
Wani golding colour neck chain ne me kyau da tsadar gaske ne ya bayyana acikin envelope ɗin.
"Wow!!" Nasma da Shukra suka haɗa baki wajen faɗa, da sauri Nasma ta karɓi envelope ɗin ta ciro chain ɗin, saboda tsabar kyawun chain din har ɗauke musu ido yake.
Kallon Zieyaderh Nasmah tayi tare da cewa "Gaskiya guy ɗinnan ya haɗu, wannan chain ɗinfa na gold ne, zaikai 50k fa!"
"Wasa ma kike, zai iya kai 60k wannan neck chain din, gaskia guy ɗinnan ya iya bada gift" Shukra tafaɗa tana me jujjuya chain ɗin ahanunta.
Zaro idanu Zieyaderh tayi sakamakon jin kuɗin chain ɗin, cikin yanayi na tsoro tace.
"Zan maida masa gaskiya ni bazan karɓa ba"
Baki Nasma da Shukra suka sake suna kallonta, cikin nuna mata batasan me takeyi ba Shukra tace "Zaki mayar masa fa kikace?"
"Eh, bazan iya sawa ba gaskiya" Zieyaderh tafaɗi haka har acikin azuciyarta.
Dariya suka sanya su duka biyun, cikin dariya Nasmah tace
"Allah har yanzun baki waye ba babe, ae idan masoyinka ya maka kyauta baka maida masa."
Murmushi kawai Zieyaderh tayi kana ta kifa kanta akan desk, wani abune taji ya tsaya mata arai, har abada bazata taɓa manta matsayinta da kuma wacece itaba, sam bazata yaudari kanta ba, tanajin su Nasmah nata yaba neck chain ɗin tayi musu shiru,, Shigowan Islamic teacher yasanya su yin shiru, tare da bada hankalinsu gareshi. Gaba ɗaya wunin ranan Zieyaderh asukurkuce tayishi, abu biyune ke tsaye aranta, ƙarfe 5 pm daidai aka kaɗa musu ƙararrawan tashi. Amatuƙar gajiye takejin kanta, sama sama sukayi sallama dasu Nasmah, kana tanufi inda Kamalu driver ke tsaye yana jiranta, gidan baya ta buɗe ta shiga, duk da cewa tafi yawan zama agidan gaba, don bata damu da zaman gidan baya ba.
Tunda suka ɗauki hanya ta maida hankalinta kan titi, sanyin AC'n dake tashi acikin motar ne ya sanya tasomajin sanyi, hakan yasa ta duƙunƙune jikinta.
Saida sukazo gaban tamfatsetsen gate ɗin gidan Kamalu driver ya danna horn, take aka wangale masa gate ɗin gidan ya tura hancin motar ciki.
Wata Black colour jeep ce tayi parking a gefen gidan, wanda tun barowarsu makaranta take biye dasu batare da sunsan da hakan ba. Murmushi Farouk yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, key ya sake yiwa motar tare dayin reverse, sai yanzu yakejin sanyi aransa, sam bada wasa yakeson Zieyaderh ba, so yake ya mallaketa, so yake ta soshi fiye da yanda zata so kowa, aransa ya gama yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, saboda haka da confidence ɗinsa ya juya yakoma inda ya fito.
Kamalu driver na gama daidaita parking, agajiye ta buɗe murfin motar ta fice, school bag na riƙe ahanunta ta nufi hanyar da zai sadata da babban falon gidan, bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin falon, babu kowa afalon sai TV plasma wanda yaketa aiki shi kaɗai, direct sama ta wuce, kamar zata wuce ɗakinta sai kuma ta ƙarasa gaban ɗakin Ummu tayi knocking, daga cikin ɗakin Ummu dake zaune tana karanta jarida tace "Yes come in"
Tura ƙofar ɗakin tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama, ganinta yasa Ummu taɗanyi murmushi.
"Barka da gida Ummu" Zieyaderh tafaɗa cikin ƙasa da kai.
"Yauwa Zieyaderh kindawo ko, ya school ɗin?"
"Alhamdulillah!" Zieyaderh tafaɗa still aɗan kunyace, domin har acikin zuciyarta tanajin girman Ummu.
"Masha Allah, to je kicire uniform ɗin akwai abinci a dinning" Cike da kulawa Ummu tafaɗi haka.
Miƙewa Zieyaderh tayi tare da cewa "to"
Har ta fice daga cikin ɗakin Ummu bata daina kallonta ba, hakanan alkunyan Zieyaderh'n ke burgeta, sam baruwanta da rawan kai, komai nata acikin sanyi takeyinshi, tabbas zata sowa ɗanta Almustapha samun kyakkyawar yarinya kamar Zieyaderh, ta yanke hukunci aranta zata samu Mas'oud suyi magana, lallai tanason ganin iyayen Zieyaderh, don tanason nemawa ɗanta Almustapha auren Zieyaderh a wajensu, tasan Almustapha bazai taɓa ƙin zaɓinta ba, musamman ma idan yaga Zieyaderh tasan dole zai sota, dama kuma shi bai da wata matsala bakaman SOORAJ ba wanda komai nasa aƙa'idance yake.
Zieyaderh kuwa tana shiga cikin ɗaki ta soma rage kayan jikinta, towel ta ɗaura aƙirjinta tare da shigewa bathroom, da ruwa me ɗan ɗumi tayi wanka, take taji gajiyan dake nannaɗe a muscles ɗinta sun soma warwarewa, Ko body lotion bata shafa ajikinta ba ta zura wata slim net gown red colour ajikinta, wanda take da guntun hannu, sosai rigan tayi mata kyau, hasken fatanta yasake bayyana sosai, wani mayafi me shara shara ta ɗauka tayane kanta zuwa ƙirjinta dashi, ko bedroom slippers bata sanya ba haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice, wani irin yunwane ke ƙwaƙulan cikinta, kaitsaye dinning area ta nufa, food flask ne masu kyaun gaske jere a kan babban royal table ɗin, kulan farko data buɗe white rice ne aciki wanda yaji carrot da piece, ɗayan kulan kuwa chicken soup ne wanda za aci shinkafan dashi, su kaɗai ma sun wadaceta hakan yasa bata bubbuɗe sauran food flask ɗin ba, ɗiban abincin tayi ta sanya a plate, direct kitchine ta wuce don ɗaukan ruwa, sam bata taɓa tunanin zata tarar da wani acikin kitchine ɗinba kasancewar yanda taji gidan ya ɗauki shiru alamun banda Ummu da ita babu kowa acikin gidan, bata damu da gyalenta daya zame daga kanta har yayi sanadiyar fito da tsefeffen gashin kanta ba, kasancewar gyalen yana da santsi shiyasa yaketa zamewa ajikinta.
Tanashiga kitchine ɗin taga baki ɗaya wutan kitchine ɗin akashe suke, abun da bata taɓa gani ba kenan, gashi garin yasoma yin duhu hakan yasa bakomai dake cikin kitchine ɗin take iya gani ba, dayake tasan wajen da makunnan wutan suke sai kawai ta ƙarisa ta kunna wutan, take haske ya mamaye gaba ɗaya kitchine ɗin, bata damu data waiga bayanta ba ta nufi wajen fridge, buɗe murfin tayi ta ciro bottle water me ɗan sanyi. Tana juyawa idanunta suka faɗa cikin nashi, take ta sake goran dake hanunta ya faɗi ƙasa, buɗe manya manyan idanunta tayi cike da mamaki taɗan kalleshi, zaune yake akan saman wata ƴar madaidaiciyar drawer, dagashi sai long jeans ba shida ko riga ajikinsa, fresh naked skin ɗinsa sai shining take, wani cup ne riƙe ahanunsa wanda cikinsa ke ɗauke da black coffee, tun shigowarta cikin kitchine ɗin yake kallonta, harzuwa yanzu kuwa bai ɗauke idanunsa akanta ba, wani irin bugawa taji heart ɗinta nayi amma saita ɗan daure, tsugunawa tayi ta ɗauki goran ruwan tare da miƙewa tsaye, gaba ɗaya a tsarge takejin kanta, Ahankali ta juya ta nufi hanyar fita daga kitchine ɗin.
Cikin husky voice ɗinsa yace da ita. "Zoki bani ruwa"
Cak ta tsaya da tafiyan da takeyi tare da juyowa taɗan saci kallonsa, har yanzu bai ɗauke idanunsa akanta ba, zuwa tayi ta buɗe firjin tare da ɗauko masa bottle water me sanyi, cikin yanayi naɗan rusunawa ta miƙa masa, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta, da sauri yakawar da kansa gefe tare da taɓe baki, cikin rashin kulawa yace "Ajiye" agefe dashi ta ajiye, cikin sanyin jiki ta juya zata fice daga cikin kitchine ɗin.
"Waye kika ajiye da zai kashe miki wutan da kika kunna?" ƴajefo mata tambayar yana me jujjuya spoon ɗin dake hanunsa.
Tsayawa tayi daga tafiyan da takeyi tare da juyowa, jiki asanyaye ta ƙarasa ta kashe makunnin wutan, tana fita daga cikin kitchine ɗin ta saki wani wawan ajiyan zuciya, tare da ɗaukan plate ɗin abincinta da sauri ta haura sama. Shikuwa coffee ɗinsa ya cigaba da sha, sam duhun dake cikin kitchine ɗin bai damesa ba, sometimes yafison zama acikin duhu fiye da zama acikin haske.
Aƙasa ta zauna tare da tanƙwashe ƙafafunta, har yanzu ƙirjinta be daina bugawa da ƙarfi ba, hannu tasanya acikin plate ɗin, saidai takasa kai koda loma ɗaya ne na abincin cikin bakinta, gaba ɗaya tayi losing nutsuwarta, ganinsa da tayi yanzu ya matuƙar hautsina tunaninta, ba komai ke ruɗar da ita ba kamar zallan kyau da kwarjininsa, sosai takejin wani iri aduk sanda tayi gamo dashi, lumshe kyawawan idanunta tayi tare da jingina bayanta da jikin gado, shock ɗin da ta shiga lokacin da idanunsa ke yawo ajikinta tane, ya shiga yadawo cikin brain ɗinta.
(sorry am busy kuyi manage please)
*Vote*
*And comment*
fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Chapter 30*
Haka ta daure ta cuccusa abincin wa cikinta zuciyarta cike da tarin tunani, tana kammalawa tayi sallan magriba, bayan tayi sallan isha ne tabi lafiyan gado, da yake agajiye takejin kanta take bacci ɓarawo ya ɗauketa.
_SOORAJ_
Yana gama sipping black coffee tea ɗinsa, ya aje cup ɗin tare da miƙewa tsaye ya fice daga cikin kitchine ɗin, direct ɗakinsa ya wuce, toilet yafara shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala, wata blue t-shirt ya sanya kana ya wuce masallaci.
Bashi yadawo gidan ba sai ten pm dai dai, wanka ya sakeyi sannan yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi, ɗan ƙaramin towel ya ɗauka agaban dressing mirror ya shiga goge kansa, duk da cewa bai shafa turare ba amma gaba ɗaya ƙamshin sabulun da yayi wanka dashi ya cika ɗakin, wani body lotion wanda baya kama jiki sosai ya shafa ajikinsa, turarensa me sanyin ƙamshi ya ɗauka tare da fesawa, cumb ya ɗauka ya taje kwantacciyar sajen dake kan fuskarsa, ɗan kallon kansa yayi amadubi lokaci guda kuma ya kawar da kansa gefe, pink lips ɗinsa ya ɗan ciza, wani tunanine yazo ransa hakan yasanyashi sakin murmushin daya bayyana zallan Kyawunsa, shi kansa baisan da yayi murmushin ba, direct gaban drawer ɗinsa ya nufa tare da zaro kayan dazai sa, riga da wando na black jeans ya sanya ajikinsa wanda sukayi matuƙar yi masa kyau, White kambas masu kyau yasanya aƙafafunsa, tare da ɗaura hulan white facing cap akansa, sosae da sosae yayi kyau harma baka iya tantance kammaninsa saboda yanda hulan ta ɓoye fuskarsa, wayoyinsa ya ɗauka tare da ɗaukan car key ɗinsa, yana fita daga cikin ɗakin ya murzawa ƙofar key tare da tura key din cikin aljihun wandonsa, koda ya fito ko ina dake cikin gidan ya ɗauki shiru, direct parking space ya nufa, mota ƙiran kia yashiga tare dayi mata key, koda ya iso bakin gate taradda Maigadi yayi yana ta zuba gyangyaɗi, wani silent horn ya danna, take maigadi yatashi a zabure, cikin daburcewa ya wangale masa gate ɗin, ba ɓata lokaci Sooraj ya cilla hancin motar sa waje, kasancewar dare ne hakan yasa babu wani hayaniya sosai akan tituna, tuƙi yake cike da nutsuwa yayinda ya saƙala earpiece akunnensa.
Duk da sanyin AC'n dake tashi acikin motar hakan bai hanasa sauƙe glass ɗin window ba, wani irin ni'imtaccen sanyine ke ratsa jikinsa wanda har ma yafi na AC daɗi.
TRANSCOP HILTON.
Wangale masa makeken gate ɗin akayi, asukwane ya tura hancin motarsa cikin ƙawataccen compound ɗin hotel ɗin, ababban parking space ɗin hotel ɗin yayi parking motarsa.
Ahankali ya zuro da ƙafafunsa waje, cikin takunsa me ɗauke da nutsuwa haka ya nufi cikin hotel ɗin, direct babban ɗakin da zasu gudanar dawani important meeting ya nufa, gaba ɗaya kowa da kowa sun hallara shi kaɗai kawai ake jira, kasancewar shine jagoran meeting ɗin shiyasa basu fara ba dole saida suka jira yazo, aƙalla sun ɗauki sama da 1 hour suna tattauna maganganu wanda gaba ɗaya su yasu suke abunsu, Sooraj kam maganarsa bata wuce "Eh" ko "A'a" Ko kaɗan basu wani damuba domin dama acikinsu babu wanda baisan halinsa ba, 11:30 pm daidai suka kammala meeting ɗin, kowa ya kama gabansa, koda ya baro Transcop Hilton baikoma gidansu ba, direct gidansa ya wuce kasancewar gobe zai koma bakin aikinsa na Bank.
Washegari.
Kamar koda yaushe 7:15 daidai take kammala shirinta na zuwa makaranta, yauma hakance ta kasance domin tuni ta shirya kanta cikin uniform ɗinta, school bag ɗinta ta ɗauka agurguje tafice daga cikin ɗakin, bata tarar da kowa acikin falonba gashi har 7:30 takusa sam kuma bataso tamakara, buɗe ƙofar falon tayi ta fice, Kamalu driver ta iske tsaye yana jiranta, tana shiga cikin motar yaja suka tafi.
***
Tun 7 daidai yagama shirya kansa cikin wani tsadadden maroon colour suit and white long sleeve shirt, sosai yayi kyau acikin suit ɗin, wani dark maroon toms ƙiran company'n Italy yasanya aƙafafunsa, sosai kwalliyan nasa ya sake ƙawata. Agogon rolex ne ɗaure a tsintsiyar hanunsa, gaba ɗaya gashin kansa sai shining yake yana ɗauke ido, saboda sosai yasha gyara, kamar wanda akawa ɓarin turare ajiki haka yake tashin ƙamshi, sabuwar black car ɗinsa mercedes benz yashiga, direct bank ɗinsu ya nufa, tun fitowarsa daga cikin mota mutane keta kawo masa gaisuwa, sama sama yake amsasu yana wucewa, koda yakai office ɗinsa ya samu komai nead, dama kowa yasan bayason ƙazanta shiyasa always ake tsabtace masa office ɗinsa, sosai yatarar da aiki na jiransa saboda haka tunda yaje bai wani huta ba aiki kawai yaketayi a computer.
_Zieyaderh_
Tun fitowansu break take jin kanta wani iri, ga wani amai da tashin zuciya dake damunta, haka dae tayi break adaddafe suka koma class, duk su Nasmah na lure da ita, saboda ko magana sosai yau din batayi, ƙarfe 1 daidai aka fito dasu sallah, zuwa lokacin abun yasoma fin ƙarfin tunanin Zieyaderh, saboda ciwon sosai ya tsananta, gawani irin zazzaɓi daya rufeta, koda ta idar da sallah cusa kanta tayi tsakankanun cinyoyinta ta saki kuka me sauti, don bazata