Author : Maman Teddy Category : Adventure
sauran ranaku masu zuwa."
(kuyi haƙuri two days bana baku updated da wuri, insha Allah yanzu zannayin ƙoƙarin baku update akai akai saboda inason nima na ƙare labarin soon!)
*Vote*
*and*
*Comment*
fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#Destiny.
*(Wannan fejin gabaki ɗayansa na sadaukar dashi agareki.My Aunty, AISHA ALI GARKUWA. Allah Yaƙara miki lafiya da nisan kwana, Ameen.)*
*Chapter 47*
Hannunsa ya ɗaura adaidai tsakiyar fatar bayanta dake shinning, jin sauƙan hannu ajikinta yasanya ta sakin kwalban turaren humran dake hannunta, yayinda tayi saurin juyowa atsananin tsorace, hartakai ga ƙirjinsu sun samu haɗewa waje guda,
cikin mamakin ganinsa daf da ita ta ajiye idanunta akan faffaɗan chest ɗinsa, saboda bazata iya juran kallon cikin fitinannun idanunsa ba.
Hannunsa dake kan naked skin ɗinta, ya sanya tare da ɗan jan bathrobe ɗin yayi sama, inda yakawoshi harkan kafaɗunta, ahankali ya jawota gab dashi, cikin nutsuwa ya ɗaura hannayensa akan igiyoyin da zasu haɗe bathrobe ɗin su sanya ya kama jikinta, ahankali ya haɗo igiyan tare da sanya hannunsa yasoma ƙoƙarin ɗaure mata igiyoyin akan lafaffen cikinta, kokaɗan bai bari idanunsa sun sauƙa akan ƙirjinta dake aɗan buɗe ba, fuskarta kawai yake kallo, yayinda ita kuma ta rufe kyawawan idanunta, wanda samansu ke ɗauke da zara zaran eye lashes, cikin son zame hannunsa daga jikinta, batare daya sani ba ƴan yatsunsa biyu suka gogi kan nipples ɗinta, wani irin yaaarrr yaji ajikinsa, wanda koda wasa baitaɓa jin kwatankwacin hakan ba.
Ita kuwa Zieyaderh rumtse idanunta tayi da ƙarfi, tare dayin ƙasa da kanta, yayinda wani irin kunyaya rufeta.
Ahankali ya ɗauke hannunsa daga jikinta, tare da ɗan matsawa, cikin takunsa mai ɗuke da nutsuwa ya nufi hanayar bathroom, tanajin rufewar ƙofar toilet ɗin tasaki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, tsikar jikintane ke tashi, yayinda gefe guda kuwa taji wani irin sabon abu na baƙuntan gaba ɗaya gaɓɓan jikinta, cikin jin kunyan abun daya faru, taƙarasa gaban ƙaton sif ɗinsa wanda aka jere mata kayanta daga ɗayan ɓangaren, wata dark green ɗin doguwar riga mai faffaɗan wuya ta zaro, cikin sauri sauri ta zura rigar ajinka.
Yanashiga cikin toilet ɗin yasoma ɓalle aninayen gaban rigarsa, cikin abunda aka aje a toilet ɗin musamman don ajiye kaya, ya ajiye rigarsa, makunnin shower ya kunna tare da tsayawa ruwa na dukan murɗaɗɗiyar surar jikinsa, lumshe idanunsa yayi tare da sanya hannu ya dafe jikin bango, tunowa da yanda yaji ajikinsa ɗazun ne, yasanyashi sake lumshe idanunsa,
tunowa da haka yasan yashi sake jin wani sabon abu ya tsarga masa tamkar awannan lokacin abun ya faru, cikin yanayi nason ƙaryata kansa da abun dayakeji, yaɗan soma jijjiga kansa, sam bayason zuciyarsa ta yaudaresa, tabbas yasan komai zaiji ayanzu to sharri da kuma yaudara ne irinta zuciya, koma mene bazai raɓa zama gaskiya ba.
Yajima sosai atsaye ruwa na dukan jikinsa, har saida idanunsa suka sanja kala daga farare zuwa launin ja, kafun ya kashe shower'n,
towel ɗin daya tsaya iyaka guiwarsa ya ɗaura, jikinsa na ɗigan ruwa haka ya murɗa handle ɗin ƙofar ya fito.
Jin motsin fitowarsa yasanya Zaieyaderh komawa kan gado da sauri ta kwanta, tana me dafe saman mararta wanda takejinsa kamar akumbure, gaba ɗaya kwananan batajin daɗi ita kanta batasan meke damunta ba, takan daiji mararta na yawan murɗawa, yayinda takejin ƙasan marartata acike.
ƙarasawa gaban mirror' yayi aƙagauce ya shafa body lotion,tare da body spray ɗinsa mai daɗin ƙamshi, wani blue crazy jeans tare da white t-shirt,
da kuma blue facing cap ya sanya, sosai yayi kyau ya fito acikakken handasome guy ɗinsa, makullin motarsa ya ɗauka batare daya dubi inda take ba yasakai yafice daga cikin ɗakin.
Jin motsin ficewar sa daga cikin ɗakin, yasanyata sake duƙunƙunewa waje ɗaya tare da lumshe idanunta, ahankali sabon mood ɗin da ta samu kanta aciki ke ratsata, yayinda yake ƙara shiga jikinta yana samun wajen zama, sannu ahankali ya mamaye gaba ɗaya jikinta, yayinda yasanya idanunta rufewa, tabbas ita awajenta hakan baƙon yanayi ne, kuwa sam batasan da wani irin dan batasan da wani suna zata ƙirasa ba, tunani ne kala kala acikin rai da zuciyarta, haka tayita juyi har saida aka ƙira sallan magriba, tashi daga kwancen tayi, tare da wucewa bathroom ta ɗauro alwala.
Ahankali sautin cool music ke tashi acikin ƙawataccen club ɗin, daga gefe ƴan mata da samari ne keta mu'amalansu awajen tamkar aƙasar turai, yayinda kowa ke harkan gabansa.
Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar royal chair mai kyau, yayinda ya ɗaura ƙafafunsa bisa kan wani ɗan madaidaicin table ɗin dake gabansa.
Bayansa yajingina da jikin kujeran, kana ya lumshe idanunsa masu azabar kyau, yakan zuwa club ne badon iskanci ba, haka kuma yakan zuwane badon wata manufa daban ba, yana zuwane saboda sometimes yakanji yanason abun dazaina ɗan ɗebe masa kewa, sannan kuma bakowani club yake zuwa ba, yana zuwa club ne, idan club ɗin ya amsa sunansa wajen haɗuwa, idanunsa ya buɗe ahankali inda ya sauƙe su, akan wani guy dake zaune shi kaɗai yanata cikawa cikinsa wine, kawar da kansa gefe yayi donshi sam kwata kwata ba'al adarsa bace shan wine ko alcohol, dubansa yakai kan screen ɗin wayarsa wacce ke fitar da haske alama na shigowar saƙo ko ƙira.
"Mas'oud."
Shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, akasalance yayi picking call ɗin,
cikin unique voice ɗinsa yace. "Hello."
Ajiyar zuciya Mas'oud dake zaune cikin abokan business ɗinsu ya sauƙe, cikin gane alamun inda Sooraj ɗin ke zaune yace.
"Club ko?."
Fuska Sooraj yaɗan ya mutsa cikin nuna halin ko in kula yace.
"Eh, akwai wani abu bayan hakanne?."
Cikin sanyi haɗi da kwantar da murya Mas'oud yace.
"RAJ yanzun fa bada bane yakamata kasani, yanzu bakai kaɗai bane kamar da, ka ajiye iyali, koda ace bakasonta yakamata ace kazauna da ita awannan lokacin, waima tsaya shin kama gwada abun da Dr. yace kayi?."
Wata ƴar murmushi Sooraj yayi cikin ƙosawa dajin maganganun Mas'oud ɗin yace.
"Kagama!."
Sarai Mas'oud yagane me Sooraj ɗin ke nufi, yasan hakan alamace dake nuna cewa Sooraj ɗin yagaji dajin maganansa, dama shi hakanan yake baka isa ƙiransa kuyi hira ba, magana ɗaya biyu sai ya kashe maka waya, aikuwa Mas'oud bai gama dawowa daga tunaninsa ba, ƙit haka yaji Sooraj ya kashe wayar, sake gyara zamansa akan kujeran yayi tare da lumshe idanunsa, sosai tunaninsa yayi nisa izuwa gareta, ajiyar zuciya ya sauƙe sakamakon tunowa da yanda yatsun hannunsa suka gogi kan nipple ɗinta, murmushine ya bayyana akan fuskarsa, sam tunanin da yayi yanzu baisa yaji wani abuba, sannan kuma babu wata jijiya ajikinsa da tayi motsi, saɓanin tunaninsa na ɗazu da yaji wani irin abu ya ratsa har cikin tafin ƙafansa,
dama yasani idan harma yasaka rai to ya yaudari kansa, yasani sharrin zuciyane kawai, da ace yayarda yakumasa hakan aransa to tabbas da yasake yiwa zuciyarsa babban illa, saboda yarda da gaibu babban matsalane arayuwa.
Aƙalla sama da awa biyu Sooraj ya ɗauka zaune acikin club ɗin, ƙarfe 12:15 am.
Ya baro cikin club ɗin, cikin nutsuwa haka yake murza steering motar, wani ɗan loka dake cikin motar ya buɗe, inda ya ciro kwalban maganinsa, ɓalle murfin kwalban yayi, tare da watsa ƙwayoyin dake cikin kwalban abakinsa, haka ya haɗiyesu batare daya bi kansu da ruwa ba.
Kafun ma yaƙaraso gidannasu tuni 12:26 am. Tayi cikin silently ya danna horn, Maigadi wanda idanunsa ke cike da magagin bacci ne ya wangale masa gate ɗin cikin hanzari, cikin ƙaton parking lot ɗin gidannasu yayi parking motar, kansa ya kifa ajikin steering motar aƙalla yaɗauki sama da mintuna 5 ahaka, kafun cikin salo da izza irin nasa ya buɗe murfin motar ya fito, kai tsaye cikin gidannasu ya nufa, ko ina dake cikin falon ya ɗauki shiru ba abun dake tashi sai ƙaran AC.
LHar yakai bakin ƙofar da zata sadashi da part ɗinsa, muryar Oummu wacce ta ratsa cikin kunnuwansa, ita ta tilasta masa tsayawa.
Cikin kakkausar murya Oummu dake tsaye kan matattakalan falon ƙira sunansa.
"Sooraj!"
Cak ya tsaya cikin yanayi naɗan mamaki ya juyo, makunnin ƙwan wutan falon Oummu ta kunna take haske ya gauraye ɗakin, wani irin kallon tuhuma Oummu dake ƙarasowa garesa ta watsamai, ƙasa ya sadda kansa don sam bai tsammaci ganinta awannan lokacin ba.
"Daga ina kake?." Oummu ta tambayesa cikin ɓata fuska.
Sam bai wani iya ƙarya ba hakan yasa cikin muryarsa da ta ɗan sanja amo yace. "Club."
Kallonsa sosai Oummu tayi cikin ɓacin rai tace.
"Hakan shine abun da kazaɓarwa rayuwarka ko? kabar yarinyar mutane cikin kaɗaici da kewa, amma kai kasanya ƙafa katafi club, amatsayinka na wanda keda aure yakamata ace sai 12:30 am kake dawo gida?."
Shiru yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, cikin halin ƙosawa da tsayuwan yace.
"Am so sorry!."
Baki buɗe Oummu ke kallonsa, wato ma shiko ajikinsa, dan tsabar miskilanci irin nasa ita yake bawa haƙuri, bama matarsa da ya aikata ba daidai agareta ba, shiru Oummu tayi batare datace komai ba, saima zuba masa idanu da tayi, ganin haka yasanyashi murɗa handle din ƙofar da zata sadashi da part ɗinsa ya shige,
ajiyar zucia Oummu ta sauƙe, tare da girgiza kanta, afili tace. "Allah ya kyauta." juyawa tayi ta koma ɗakinta, don dama rashin jin motsin dawowarsa ne yahanata bacci.
Ahankali ya shigo cikin falon nasa wanda keta tashin ƙamshin turaren wuta, da'alama tunda yammaci aka sanya turaren amma kuma har zuwa yanzu ƙamshin nanan bai fice ba, handle ɗin ƙofar bedroom ɗin ya murɗa, tare da tura ƙofar ciki kana yasa kansa acikin ɗakin, yana maida ƙofar ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya, tare da ɗan juyowa ya sauƙe idanunsa akanta, kwance take akan sallaya yayinda tayi matashin kai da hannunta, hijab ne ajikinta, kana cikin baccin nata da yayi nisa, ta tattare gaba ɗaya doguwar rigan jikinta yayi sama, hakanne yayi sanadiyar bayyanan fararen ƙafafunta, wanda sukasha zanen jan lalle gwanin ban sha'awa.
Ahankali ya janye idanunsa daga kanta, cikin yanayi me ɗauke da gajiya, ya fesar da wani numfashi mai ɗumi daga bakinsa, ƙarasawa gaban drawer ɗinsa yayi inda ya soma cire kayan jikinsa, wani orange towel ya ɗaura akan waist ɗinshi, kana ya wuce bathroom.
Yana gama wanka yayi alwala, kasancewar haka ƙa'idarsa take, muddin zaiyi kwanciyar bacci to saiyayi alwala, baiwani jima acikin banɗakinba ya fito, koda yafito daga cikin toilet ɗin, babu abun da jikinsa ke fitarwa, sai daddaɗan ƙamshin sabulunsa mai ratsa zuciya, wani ɗan madaidaicin towel ya ɗauka inda ya shiga tsane jiƙaƙƙen gashin kansa, yana kammala tsane jikinsa yaɗan shafa body oil sama sama, wani farin 3 guater jeans yasanya, agajiye yake hakan yasa yafaɗa kan gado, tare da kwancia luf, ya lumshe idanunsa, gaba ɗaya kwana biyun dayake kwana akan cushion, ji yake duk jikinsa nayi masa ciwo, cikin ɗan yanayin baccin daya ɗan fara fusgarsa, ya buɗe idanunsa ahankali, tare da ɗan kai dubansa gareta, dagani kaikasan bawani jin daɗin baccin takeyi ba, gashi gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sanyi, ahankali ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, ƙarasawa inda take yayi, hannunsa ya sanya ya zare hijab ɗin dake jikinta, kasancewar yaɗan shaƙe mata wuya, idanunsa ne suka sauƙa akan rabin breast ɗinta, wanda suka bayyana kansu ta saman wuyan rigar jikinta, ƙasa yayi da idanunsa, inda kalaman Dr.Waleey, suka shiga dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa filla filla, cikin wani irin yanayi yaji gaba ɗaya sassan jikinsa sun amsa,, take kuma jikinsa ya ɗauki rawa, sake buɗe idanunsa wanda suka kaɗa sukai jajur yayi, hannunsa dake rawa yasanya yaɗagota caɗak, kan gado ya nufa da ita, inda ahankali ya shumfuɗe ta, tare da gyara mata kwancia, kwanciya shima yayi agefenta tare da tsura mata ido, har zuwa yanzu jikinsa baidaina rawa ba, ahankali yaɗan matso kusa da ita tare da ɗan yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, sam baisan ta'ina zai fara ba, yanaso ya gwada amma baisan dame zai fara ba, kyakkyawar fuskarta yake kallo bayako ƙyaftawa, wani irin abu ne ke fusgar zuciyarsa akanta, yanajin itaɗin kamar wani sashi ne dake jikinsa, daga gefe guda na zuciyarsa kuwa tsananin tsausayinta yakeji, ahankali cikin yanayi na bacci taɗan buɗe kyawawan idanunta, sauƙesu tayi acikin nasa idanun, cikin magagin baccin da take yasanya take ganin hakan kamar amafarki, ɗan lumshe idanunta tayi kana ta buɗesu alokaci guda, sosai hakan ya ƙarawa beauty face ɗinta kyau, har izuwa wannan lokacin bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, ƙasa yaɗanyi da ƙwayan idanunsa inda ya sauƙe ganinsa akan tausassun pitch lips ɗinta, batare daya shirya ba, ya haɗiyi wani zazzafan saliva, daya tsaya masa amaƙoshinsa, jin yanda kansa ke sarawane yasanyashi sauƙa daga kan gadon.
Kan kujera ya koma ya kwanta, zuciyarsa ne ta tsananta bugawa, rumtse idanunsa yayi da ƙarfi tare da cije laɓɓansa, bazai iyaba, bazai taɓa iyawa ba, abun da zuciyarsa ke faɗa masa kenan, wani irin raunine ya kamasa, sake shigewa jikin kujeran yayi yana sauƙe ajiyar zuciya akai akai haka har bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
Washegari.
Tun 7:00 am.
Yabar cikin gidan kasancewar akwai babban meeting ɗin da zasu gabatar, shida abokan aikinsa, saboda haka sosai yayi kyau cikin shigarsa ta suit navy blue colour.
Ita kuwa Ziayederh sai 8 tatashi daga bacci, koda tayi wanka falo ta dawo ta zauna, yaukam zaman kaɗaicin ya isheta, hakan yasa ta kunna makeken tv plasman dake cikin falon, series film take kallo a tashan Zee wold, hakan yasa gaba ɗaya ta bada hankalinta garesu, Oummu ce ta aiko akayi ƙiranta, koda taje sashin Oummun nan ta iske Aunty Muhibbat da Oummun tsaye cikin shirinsu, da alama unguwa zasu, Oummu ce tace da Zieyaderh'n ta ɗauko mayafinta akwai inda zasuje, wani ƙaton mayafi Zieyaderh ta ɗaura akan doguwar rigan atamfan dake jikinta, haka suka fita itace ke zaune agefen mai zaman banza, yayinda Aunty Muhibbat ke driving motar, Oummu kuwa ita ke zaune agidan baya, basuwani yi tafiya sosaiba suka iso gaban wani tsararren gida wanda aka ƙawatasa, sosai haɗuwar gidan yakai haɗuwa, horn Aunty Muhibbat ta danna, take maigadi ya wangale musu gate ɗin gidan, cikin wani ƙaton parking lot dake cikin gidan Aunty Muhibbat tayi parking motar, ganin su Oummu sun buɗe murfin motar suna ƙoƙarin fita ne, yasanyata fitowa itama daga cikin motar, wani dogon ginin gidan sama dake cikin compound ɗin gidan suka nufa, gaba ɗaya tsaruwan compound ɗin gidan yatafi da hankalin Zieyaderh, don kusan gaba ɗaya compound ɗin cike yake da shukokin kyawawan flowers gwanin ban sha'awa, Aunty Muhibbat ce tasanya key ta buɗe wata babbar ƙofan dazai kaisu cikin wani ƙawataccen falo, wani irin daddaɗan ƙamshi haɗi da sanyine suka shiga jikinta alokacin da ta sanya ƙafanta cikin falon, wanda kaitsaye za'a iya ƙiransa da Aljannar duniya, falone wanda aka ƙawata cikinsa da haɗaɗɗun royal chairs masu masifar kyau da tsada, komai dake cikinsa milk colour and golding ne, da wasu irin haɗaɗɗun cottings aka ƙawata jikin ƙofa da window's ɗin falon, gefe guda kuwa wani haɗaɗɗen tv plasma ne wanda aka cika wasu new designed flowers agefe da gefensa, can gefe kuwa wani haɗaɗɗen dinning area ne wanda aka ƙawatasa, sosai haɗuwarsa ya zarce misali, gaba ɗaya jikin bangon falon ɗauke yake da wani irin magic paint mai kyau da ɗaukar hankali, sosai falon yayi kyau duk da ba a wani cika tarkace acikinsa ba, amma duk da haka tsarin yayi kyau, don sosai aka narka uban dukiya wajen ƙawatasa.
daganan falon sama suka haura, nan suka sake samun kansu acikin wani ƙawataccen falon, saidai shi wannan falon ɗin anƙawatasa ne da wasu irin kujeru irin leda sit ɗinnan, sosai kujerun sukayi kyau wanda suke da kalan light green ajikinsu, yayinda aka watsa musu ƴan ƙananan trow pillows milk colour akansu, gaba ɗaya cottings ɗin dake cikin falon light green and milk colour ne, wani ɗan madaidaicin tv plasma ne maƙale ajikin bango, sosai shima falon yayi kyau duk da cewa baikai wancan naƙasan kyau ba, amma shima yayi kyau ba laifi, 2 bedrooms ne acikin falon, koda suka shiga na farkon, ƙawace yake da haɗaɗɗun furnitures, komai na cikin ɗakin coffee colour ne, ɗayan ɗakin ma yaji furnitures saidai shi baikai na farkon haɗuwa ba, amma shima babu laifi saidai ace masha Allah. Duban Zieyaderh Oummu tayi cikin kulawa tace.
"Gaba ɗaya abun dake cikin ɗakinnan dama wanda ke cikin falon nan, mahaifinki ne yasayamiki."
Cikin mamaki Zieyaderh ta kalli Oummu, kai Oummu ta gyaɗa mata tana murmushi, wani irin hawayene suka cika idanunta take tashiga ƙarewa kayan ɗakin kallo, sai yanzun take ƙara ganin kyawun komai da komai, wani irin farinciki ne ya lulluɓe mata zuciya, ganin hawaye a idanunta ya sanya Aunty Muhibbat cewa.
"To ƴar gatan babanta badai kuka zakiyi ba?."
Murmushi tayi tare da sadda kanta ƙasa, haƙiƙa mahaifinta yayi mata babban ƙoƙari,domin sam bata taɓa tsammatan haka daga garesa ba, bata taɓa tunanin zai iyayi mata hidima mai yawa kamar haka ba. Nan Oummu da Aunty Muhibbat suka shiga nuna mata ko'ina dake cikin gidan, har kitchine saida suka shiga inda aka shaƙesa da zafafan kuloli da kuma sauran abubuwan buƙata, daganan gidan kaitsaye wani babban shagon ɗinki suka nufa inda anan Oummu ta bada ɗinkin kayan auren Zieyaderh, suna zuwa kuwa telan ya basu kayan don dama yaɗinka aƙoƙarinsa ma shine yau ɗin yakai musu, kayane niƙi niƙi har cikin wasu manyan leda guda biyu, daga shagon ɗinkin gida suka dawo, inda takoma ɓangarenta, da kanta ta shirya kayan da suka karɓo natan acikin drawer.
***
Wasa wasa yau Zieyaderh take cika sati da kasancewarta mata awajen Sooraj, cikin kwanakin da suka shuɗe abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa harda rashin ganinsa da batayi, domin yanzu, yakoyi wani salo, tun kafun tatashi daga bacci yake ficewa, haka kuma baya dawowa harsai tayi bacci, yau kwananta huɗu cif kenan bata sashi acikin idanunta ba, saidai kullum yana barmata fitinannen ƙamshinsa dake azabtar da zuciyarta, fitowarta awanka kenan cikin sauri ta kimtsa kanta, cikin wata haɗaɗɗiyar jallabiya wacce taji adon stones, sosai rigan tayi mata kyau, ɗan madaidaicin mayafin rigar tayafa akanta,cikin sauri ta fita daga ɓangaren nasu don yau Aunty Muhibbat da Oummu zasuyi tafiya, kuma tanaso tayi musu adawo lafiya, koda taje ɓangaren Oummun ita da kanta ta taya Aunty