Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   47 / 47

138K to 140.6K   out of 140.6K words

yana kallonta, cikin muryarsa mai ɗauke da aji yace.
"Yaushe kika girma, da har kike ƙoƙarin yi min wayo?."
Dariya tayi harsaida fararen haƙwaranta suka bayyana,  ahankali taɗan karyar da wuyanta gefe cikin salonta na shagwaɓa wanda akoda yaushe ke masifar ƙara mata kyau tace.
"Please ɗan kaɗan ko?."
Kansa yagirgiza, cikin silent voice ɗinsa yace.
"A'a dayawa."
Hannunsa ta kama inda ta zagayo ta bayansa, ɗan tsalle tayi tare da ɗalewa saman bayansa, kana ta  ɗaura hannuwanta akan shoulder ɗinsa, cikin jin daɗin samun kanta akan bayansa tace.
"To kaɗan yi yawo dani please ko zan dainajin gajiyan."
Wata t-shirt ɗinsa dake aje kan gado ya ɗauka tare da zura mata ajikinta, goyonta yayi da kyau kamar wata ƴar baby haka ya nufi ƙofar fita ɗakin da ita, luf tayi abayansa tare da lumshe idanunta, kaitsaye ƙofar dazai fitar dasu a part ɗinnasu ya buɗe ya fita, da sauri ta buɗe idanunta, ganinsu a falon Oummu yasa tasoma ƙoƙarin sauƙa daga kan bayannasa, amma ina yaƙi bata daman hakan, cikin yanayi naɗan tsoro takawo bakinta daidai saitin kunnensa inda ta ɗana masa cizo,  cikin yanayi na jin zafi yaɗanyi ƙara,  tare da saketa ta duro ƙasa, dariya tashiga yi masa sosai, idanunsa ya zuba mata Musamman ma yanda yaga tayi masifaffen kyau da tana dariyan, kanta yayo da sauri ta soma ja da baya baya hannu yasa zai kamota aguje tanufi ƙofar falonsu, hartakai bakin ƙofar ya cafko hannunta inda ya juyo da ita, azafafe ya mannata ajikinsa tare da ɗaura bakinsa akan nata.
Da sauri Oummu da tun fitowarsu take kallonsu tayi saurin juyawa takoma cikin ɗakinta, don dama tsaye take asama hakan yasa basu ganta ba,  tana shiga ɗaki ta sauƙe ajiyar zuciya, fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Gobe goben nan zaku koma gidanku, bazaku ci gaba dayin iskancinku agabana ba,  bansan ma yaushe kuka zama mararsa kunya ba sam!."

Sosai suke kissing ɗin juna hartakai ga tsayuwa naneman gagaransu, hakan yasa ya ɗauketa suka shige cikin falo, kai tsaye akan gado ya shumfuɗeta, rigar jikinsa danata ya zare, tare dayi musu light off na hasken ɗakin,  haɗuwar naked skin ɗinsu waje ɗaya shiya ƙara zafafa matsanancin sha'awar juna azuƙatansu.    Yau salon nasu ya banbanta dana kullum, hakan yasa gaba ɗaya suka manta duniyar da suke,  cikin wani irin yanayi mai kama da shiɗewa take fusgar numfashi da ƙyar, ahankali ta buɗe bakinta yayinda idanunta suka cika  da ƙwalla,   yanayin yanda yake ƙara shigewa cikin jikinta da kuma yanda yake groaning su suka sanya hawayen dake cikin idanunta gangarowa,  ita kanta batasan hawayen na menene ba saidai zata iya dangantasa da cewar yanayin da take ciki ne yasanyasu fitowa,  hannunsa yasanya inda ya rungumota sosai, bakinsa daya kasa rufuwa tun ɗazun ya ɗaura akan nata, lokaci guda suka sake shiɗewa,      ita kanta bazata iya misalta irin daɗin dayake jiyar da ita ba, wanda har yakai ga tanajin wani irin abu na yawo acikin kanta,  shikuwa Sooraj kwata kwata nutsuwa da tunaninsa basa jikinsa,  haka yakejinsa kamar yana swimming cikin kogin zuma, sai yaji yanason ƙyaleta sai kuma yaji sam bazai iyaba, kasancewar daɗin dayakeji ya zarce misali.
Sam bazata iya sanin yaushe kuma tayaya bacci ya ɗaukesu ba, haka sukayi bacci yana cikin jikinta, inda take ƙasansa shikuma yana sama,  bacci sukayi cikin matsanancin soyayyar juna.
Washe gari da safe kuwa tunda wuri ta shirya inda, ta ɗauki duk wani abun buƙatarta wanda zata buƙata wajen exam din,  shida kansa yabata break taci, kana ya ɗauketa suka tafi makarantar.
Awansu ɗaya da rabi acikin babban examination hall ɗin suka kammala zana jarabawar tasu ta Biology, koda suka fito daga jarabawan hira suka ɗan taɓa dasu Nasmah kafun daga bisani yazo da kansa ya ɗauketa, sosai tasha mamaki ganin sunnufi wata hanya daban bana gidan Oummu ba,  maigadine ya wangale musu gate, inda ya tura hancin motar cikin gidan, ganinsu acikin gidan dasu Oummu suka taɓa kawota yasa ta ɗan zaro ido cikin yanayi na mamaki tace.
"Mezamuyi anan?."
Hannunta yakama suka shiga cikin gidan,  saida suka kawo har tsakiyan falon kafun yasanya hannuwansa ya dafa shoulder ɗinta cikin kulawa yace.
"Mundawo nan gidan, nanne gidanmu, kuma anan zamuyi rayuwa, ko bakyaso?."
Murmushi tayi tare dayin hugging ɗinsa, ahankali tace.
"Inaso sosai"
Shida kansa yayi mata wanka inda ya samata wasu kaya marar nauyi. Gaba ɗaya wunin ranan atare sukayi inda sosai yake maida hankali wajen sauraran shagwaɓan da taketa zuba masa.
Tayaya zai misalta irin matsanancin son dayake mata? yanajin shaƙuwarsu acikin jininsa, sosai yake mata wani irin so da babu kamarsa aduniya,  akanta zai iyayin komai, yanasonta fiye da yanda yakeson ransa.
***
Sosai zamanta dashi keyi mata dadi, yayinda kullum shike kaita exam yakuma dawo da ita, inda yau sukayi geography wanda kuma shine papern ƙarshe.
Tunda ya ɗaukota a school ɗin ya lura da cewar kamar batajin daɗi, hakan yasa yaketa tattalinta,  maimakon ya wuce da ita gida, kai tsaye sai yawuce da ita, unguwar wuse zone 4 inda tuni yasayawa mahaifinta gida anan harma sun dawo, can yakaita daganan yakoma wajen aikinsa,  haka ta wuni agidan tana dariyan Inna Ma'u, don kuwa duk jimawan Inna Ma'un agidan baisa tadaina halinnata ba, haka nan take kullum ci wannan sha wancan, bakinta baya taɓa zama shiru, inta ritsa apples saitaci guda biyar atake,  sannan sai jarababben son kallon tsiya inta ɗaura idanunta akan tv, bata ƙaunar abun da zaisa ta kawar dasu.
Sai da akayi sallan isha sannan yazo ya ɗauketa.
Washe gari da safe kuwa mutanen Maiduguri sukayiwa gidan nata tsinke,  sosai tacika da tsananin farinciki, haka Aunty Ounnaisa takawo mata kayayyakin gyara na shuwa masu masifar kyau da tsada,  ita da kanta takaisu gidan Oummu dan su gaisa, sosai Oummu taji daɗin zuwansu,   haka sukayi hira sosai,  kwanansu ɗaya suka bi jirgi suka koma Maiduguri.

**
Alhamdulillah jikin Pharouk yanata samun sauƙi, inda yake samun kyakkyawar kulawa daga wajen doctors,   harzuwa yanzu nadama ne cike fal azuciyarsa, tabbas yayi danasani mai tsanani, inda kuma yaƙudurta aransa cewa, koda yagama warkewa zai cigaba da zama a Germany bazai koma Nigeria ba,  cikin ikon Allah kuma sauƙi nata samuwa masa, inda iyayensa  suka yanke shawaran cewa dazaran yagama samun sauƙi zasu ɗaura masa aure da ƴar yayan mamansa, koda yaji shawaran nasu baiƙi ba donshi yanzu rayuwa takoya masa hankali.

Ina labarin Aneesa da Yasmeen masu buri da  fatan mallakar SOORAJ? arayuwa dama ance ka shuka alkhairi saika girbi me kyau,  gaba ɗayansu rayuwa tayimusu ƙunci, inda Mahaifin Aneesa yayi mata auren dole da wani mai wanke masa motoci, kasancewar yaga al'amuranta nason fin ƙarfinsa, ita kuwa Yasmeen yawon duniyancinta take ta bugawa don ta kasa samun mai aurenta,  tuni idanunta ya buɗe inda ta gudu tabar Nigeria can America takoma da zama, tana iskanci da mazan turawa suna biyanta maƙudan kuɗaɗe, duk da cewa bajin dadin rayuwar take ba amma bata da zaɓi.

Bayan wasu watannu.

Acikin wasu watannin da suka shuɗe abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa harda auren Mas'oud da budurwarsa Aisha, da kuma auren Al'mustapha da ƴar kanwar Oummu me suna Jaminash,,  inda su Sooraj da Ziyada suka taka rawar gani sosai abikin,  acikin watannin da suka gabata ne kuma, sukayi neco da jamb, inda har result ɗinsu ya  fito, sosai jamb ɗinta yayi kyau, hakan yasa kaitsaye Sooraj ya sama mata admission a Nile University Abuja, inda taci gaba da karantar science, don alƙawari ta ɗaukarwa kanta cewa zatayi karatu tuƙuru dan ganin tazama babban likitan mata.
Alhamdulillahi tafara karatunta cikin nasara inda komai ke tafiya mata ayanda takeso,   wani babban al'amarin da ta soma lura dashi shine yanda gaba ɗaya jiki da yanayinta suka sauya,   sosai taƙara zama babbar mace skin ɗinta yayi fresh harwani shinning yake, yayinda hips ɗinta suka ƙara girma sosai, gawani irin matsanancin kasala haɗe da yawan bacci dake damunta. Hakanan yau tatashi da wani irin zazzafan zazzaɓi, ganin haka yasa RAJ gaba ɗaya ya ruɗe, shida kansa ya kimtsata inda  kaitsaye ya wuce Nizamiyye hospitall da ita.
Sosai sukayi checking ɗinta, kana suka fitar da result ɗin abun dake damunta,   fuska ɗauke da murmushi likitan ya miƙawa Sooraj result din inda yayi masa congratulation, domin Ziyada na ɗauke da ciki har na tsawon 4 month. 
Mamaki, farinciki, nishaɗi, sune gaba ɗaya suka cika zuciyar SOORAJ bazai iya misalta daɗin dayaji acikin ransa ba, idanunsa ya lumshe ahankali.yace.
"Allah Alhamdulillah! haƙiƙa baiwarka da buwayarka ta gagari misali, kaika ɗauramin lalura alokacin da kaso, kana kayayemin ita alokacin da kaso, yanzu kuma gashi ka azurtani alokacin da kaso!" hawayene suka cika cikin idanunsa, sai kawai yajawo Ziyada yayi hugging ɗinta sosai,  wani irin matsanancin ƙarin ƙaunarta yakeji acikin ransa.
Tabbas itaɗin alkhairi ce acikin rayuwarsa, shigowarta cikin rayuwarsa ya basa farinciki mai yawa, saboda ita yafarajin kansa cewa shima mutum ne kamar kowa,  cikin tarin soyayyarta ya ɗaura mata kiss agoshinta, ganin ƙwalla acikin idanunsa yasa itama nata idanun suka kawo ruwa,  tabbas taji daɗi sosai, Allah Abun godiya, wai yau itace ke ɗauke da cikin SOORAJ ajikinta, mutumin da zuciarta ke matuƙar ƙauna da bege, wanda ko da wasa bata taɓa kawo cewar zai aureta ba ma,  daga asibitin kaitsaye gidan Oummu suka nufa,  itadai kunya takeji tana Allah Allah kada Sooraj yafaɗawa Oummu wani abu, saidai kuma tunowa da tayi cewar shiɗin bamai yawan magana bane yasanya, tabisa suka shiga falon Oummun kai tsaye,  fuska ɗauke da murmushi Oummu dake tsaye a dinning table ta amsa musu sallaman da sukeyi,  batare da zato ko tsammani ba taji Sooraj yayi hugging ɗinta sosai, kansa ya ɗaura akan kafaɗanta tare da lumshe idanunsa, dame zai godewa mahaifiyartasa wacce ita tayi sanadiyar samuwar farincikinsa? haƙiƙa Oummu tacika uwa ta gari data aura masa Ziyada, yana alfahari da mahaifiyartasa sosai, hawayene suka cika idanunsa harsuka samu daman ɗiga akan kafaɗan Oummu, cikin yanayi na mamaki Oummu taɗago kansa tare da dubansa, itama hawayen ne suka cika idanunta,  cikin sanyi tace.
"Meyataɓa zuciar Jarumin ɗana hartakaisa ga zubar da hawaye?."
Murmushi yayi tare da ɗaga hannunsa yayi mata nuni da Ziyada wacce ke tsaye tana kallonsu,  kallon Ziyadan Oummu tayi cikin, sanyin daya kasa ɓoye tsananin shauƙin dayake ciki yace.
"She is pregnant!"
Idanu Oummu tazaro.cike da matsanancin farinciki, sosai abun yazo mata amatuƙar bazata, hakan yasa tayiwa Allah Sujjada tare da gode masa, nanta rungume Ziyada wacce gaba ɗaya kunya ya hanata sakat.
Haka Oummu tayita nannan da Ziyada inda take taƙira Abba tasanar masa, faɗan irin farincikin da Abba yayi ɓatawa ne, nan Oummu tashiga ƙiran ƴan uwa da abokan arziki tana faɗa musu, kowa murna yake tayata sosai.

Tattali haɗi da kulawa  ziyada ke samu daga wajen mijinta da kuma mahaifiyarsa, kowa ji yake da ita haka suke lallaɓata kamar ɗanyen ƙwai, basason duk wani abu dazai taɓa ta.

Sannu ahankali take renon cikin jikinta kana kuma take zuwa makarantarta,  sam cikin nata baihanata duk wani hidiman mijinta ba, musmaman yanda Sooraj yazame mata kamar yaro ƙarami, koda yaushe yana liƙe ajikinta, ayanda ta fahimta kuma shine idan har ya shafe sama da kwana biu bai kusanceta ba to hakanan zata ga yadawo kamar wani marar lafiya, yamaida ita abinci kuma ruwan shansa.

Cikin ikon Allah yanzu cikinta yashiga wata tara harda ƙarin kwanki,  ganin yanda cikin nata yayi girma sosai ne yasa Oummu ɗaukota ta dawo da ita gabanta, nanfa Sooraj shima ya tattaro yadawo gidan Oummun dan kuwa baya taɓa iya bacci idan baiji ɗumin jikin Sunshine ɗinsa ba.
Awata ranan larabane naƙuda ya tashiwa Ziyada gadan gadan tun tana daurewa hardai Oummu tafahimta haka suka ɗauketa suka wuce da ita asibiti, SOORAJ kam gaba ɗaya yatashi hankalinsa idanunsa sunyi jajur kamar wanda zaiyi kuka,  matsanancin tausayinta yakeji.
30 minute kacal da shigar da ita labour room cikin sauƙaƙawa irin na Ubangiji ta haifo kyakkyawan ɗanta mai azabar kyau wanda kamanninsa da SOORAJ yayi over, har kamar an tsaga kara,  nan nurses suka kimtsa ta tare dayi mata alluran bacci don su naso tasamu hutu, kimtsa yaron sukayi inda suka fito dashi, ganin nurses din sunfito yasanya su Oummu sukayi kansu, ƙoƙarin miƙawa Oummu yaron wata nurse tasomayi da sauri SOORAJ yasa hannu ya amshi yaron, duban fuskar yaron yayi inda yahango matsanancin kamanninsa akan fuskar yaron, rungume yaron yayi acikin ƙirjinsa, take kuma saiga hawaye sun silalo daga cikin idanunsa.
Da SOORAJ da yaron duka Oummu ta haɗa ta rungume, itama ƙwalla ne yacika idanunta, cikin ranta takeyiwa Allah godiya, nan nurse ɗin tabasu izini inda suka shiga ɗakin hutun da aka kwantar da Ziyada,  ƙarasawa gaban gadon SOORAJ yayi tare da yin hugging ɗinta,   cikin yanayi irin na mayen baccin da take ciki tasaki murmushi, kiss yayi mata tare da kai bakinsa daidai saitin kunnenta ahankali yace "Thank you so much My Sunshine!."
Oummuce taƙaraso jikin gadon itama tare dayi mata sannu.
Haka Oummu tashiga ƙiran mutane tana sanar dasu batun haihuwar, koda Abba yaji tuni yasa akai masa booking flight don zuwa Abuja duba ɗan jikansa, bayan yasa ayi masa ordern zazzafan mota wanda zai bawa Ziyada amatsayin gift.  

Kulawa ta musamman Ziyada ke samu daga wajen kowa, yayinda Sooraj ya ɗauki matsanancin soyayyar duniya ya ɗaura akanta ita da yaronsa.
Haka ƴan uwa suka dinga zuwa suna duba Zieyaderhn Aunty Ounnaisa  da sauran ƴan uwa ma sunzo sun dubasa, haka Hajiya Mama tazo tayi kwanaki 5 sannan ta koma, ranan da aka cika kwana bakwai da haihuwa yaro ya amsa sunan. ABDALLAH wanda kuma babansa ne ya zaɓa masa sunan,  Sosai akasha shagalin suna anyi hidima sosai, inda SOORAJ ya gwadawa Ziyada matsayinta agaresa, don sosai ya kashe mata kudi ita da yaron ta.

***

After 7 month.

Shigowarsa ɗakin kenan, idanunsa ya zubawa Abdallah dake zaune atsakiyan gado yana wasa, murmushine ya bayyana akan fuskarsa, cikin matsanancin ƙaunar kyakkyawan ɗannasa daya zarta sa kyau ya ƙaraso jikin gadon, ɗaga yaron nasa sama yayi tare da rungumesa ya ɗaurasa akan shoulder ɗinsa, hugging ɗinsa tayi ta baya tare da ɓoye fuskarta abayansa, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya hannunsa ya jawota ya zamana suna facing  juna. Sosai tayi masa kyau cikin shigarta na wata rigan net dake bayyana komai na jikinta,  sai kuma wani ɗan ƙaramin wandon jeans dake jikinta wanda iya karsa cinya, aje yaron yayi tare da sanya hannunsa yakamo waist ɗinta, cikin mayen soyayyarta dake jansa ya kashe mata idanunsa ɗaya tare da rungumeta.
Murmushi tayi itama tare da ɗan ɗaga ƙafafunta sama, bakinta ta ɗaura adaidai saitin kunnensa ahankali tace.
"I love you!."
Lumshe idanunsa yayi tare da ƙara hugging ɗinta, sosai yake shaƙan daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta.
Hannunsa yakai yana shafa hips ɗinta ahankali, ɗan ɗago fuskarta yayi cikin idanunta ya kalla, ahankali yace.
"I love you too  Sunshine."
Murmushi sukayi tare da haɗe bakinsu waje ɗaya.
Zuƙatansu cike yake da matsanancin farinciki, inda soyayya ke ɗawainiya da zuƙatan kowannensu, haƙiƙa idan zuciyoyi suka haɗe waje guda, akan samu wata irin zazzafan ƙauna mai ban mamaki,  tazama HASKE acikin rayuwarsa, yayinda ita kuma yazame mata madubin dubawa.   Soyayya wata abace dake sanya zuciya nishaɗi, haka soyayya wata abace dake gusar da duk wata damuwa, haƙiƙa SOYAYYARSU acikin jininsu take.

(Alhamdulillah, dama ance laifin daɗi ƙarewa, anan nakawo ƙarshen labarin SOORAJ!!! ina roƙon Allah  Inda nayi kuskure da ya yafemin, inda kuma nayi daidai yasa mutane su amfana da hakan,  Allah yayafe mana zunubanmu baki ɗaya Ameen.   Saikunjini acikin sabon labarin dazan gabatar muku nan gaba,  godiya mai tarin yawa agareku masoyana, haƙiƙa kunnunamin ƙauna, kana kuma kun nunawa book ɗin SOORAJ tsantsar soyayya, nagode sosai, musamman masoyana na Wattpad bazan taɓa gajiya da gode muku ba, musamman yanda kuke min comments da kuma vote haƙiƙa inajin daɗin hakan, wannan nema yasa naji ƙarfin guiwa inda zan sake zuwa muku da sabon labari mai ratsa zuciya.
Kuyi haƙuri nasan wasu zasuce nayi ƙarshen cikin gaggawa, nima bahaka naso ba,  ina muku fatan farinciki  mai ɗorewa, sannan ina muku fatan alkhairi, Allah yasa ayi sallah lafiya, Allah Kuma ya nuna mana wata sallan dama wanda ke gaban gabanta Ameen, then karku manta da Happy Sallah na please😢 am waiting............ I LOVE YOU SO MUCH MY AMIABLE FANS🧡)

*Vote*
   *and*
*comment*

*30/July/2020*

             FATYMASARDAUNA

47 / 47