Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   7 / 47

18K to 21K   out of 140.6K words

daga cikin motar ta shiga bin bayansa, saida suka shiga cikin wajen sannan tafahimci cewa asibiti suka zo,  ji tayi gabanta ya faɗi, aranta tace  "Allah Yasa ba allura yakawoni ayi min ba."

Tafiya suka ɗanyi sosai itadai binsa kawai take kamar jela,  abakin wani ƙofa suka tsaya, knocking ƙofan yayi, daga ciki aka bashi izinin shigowa.

"Ki tsaya anan" yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin buɗe ƙofar, tana ganin shigewarsa taja ta tsaya haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.

Dr.Salees  Yana ganin Sooraj ya miƙe haɗe da soma haɗa kayan aikin dazai buƙata, atare suka fito daga cikin office ɗin.

Murmushi Dr. Salees Yayi haɗe da kallon Ziyada.

   "Ƴan mata yajikinnaki?" yatambayeta cike da kulawa.

"Da sauƙi!" tabasa amsa murya araunane, saboda tana ganinsa taji ƙirjinta ya tsananta bugawa.

Kansa yajinjina haɗe da cewa "Biyoni muje ko"

Da sauri takalli Sooraj saidai gani tayi idanunsa ba akansu yake ba, earpiece ne ma sanye akunnensa, ya wani haɗe fuska, hakan yasa cikin sanyin jiki tabi bayan Dr. Salees.

Akan wani ɗan gado ta zauna, yayinda Dr.Salees dakansa ya soma warware mata bandage ɗin dake nannaɗe akanta, yana gama cirewa ya ɗauki auduga haɗe da ɗan ɗiga wani farin ruwa mai ɗauke da sinadarai akai, hanunsa ya sanya ya kama goshinta  ahankali yasoma goge ciwon da audugan dake hanunsa, wani irin ƙara tasa haɗe da cije laɓɓanta,   sake riƙe kanta yayi cike da kulawa yace.   "Sorry da zafi ko? ki nutsu awanke miki hakan shine zai sa ciwon ya bushe"

Sake sakin wani ƙara tayi haɗe da soma ƙoƙarin ƙwace kanta daga hanunsa, sosai takejin zafin ruwan dayake sawa yana goge ciwon,    sake kama kannata yayi da ƙarfi, haka yashiga wankewa, ita kuwa banda kuka babu abun da takeyi, duk yanda taso ta ƙwace kanta ta kasa,  saida ya wanke ciwon tsab sannan ya sake naɗa mata wani sabon bandage ɗin.   kallon innocent face ɗinta Dr. Salees Yayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
"Sarkin raki, sai ki tsayar da kukan hakanan tunda angama" 

Harsuka fito daga cikin  ɗakin Ziyada bata daina zubar da hawaye ba,  gaba ɗaya idanunta sunyi ja, fuskarta kuwa duk yayi face face da ruwan hawaye.   Wasu magungunan Dr. Salees yabata sannan suka bar cikin asibitin.

Kamar yanda suka zo haka suka tafi babu wani wanda yace da ɗan uwansa ƙala,  gaba ɗaya hankalinsa nakan tuƙin dayake, ahankali yake ɗan kaɗa kansa, sosai yake enjoying cool music ɗin dake tashi acikin earpiece din dake saƙale acikin kunnensa.    Duk abun da takeyi yana lure da ita.  Sauƙa yayi daga kan titi haɗe da ɗan gangarawa gefen hanya, tsaida motar tasa yayi haɗe da ɗaukan goran ruwa ya kafa akan bakinsa,    sauƙe goran ƙasa yayi haɗe da fitar da wani dogon numfashi.

"Kukan me kikeyi?" yajefo mata tambayar da bata taɓa zato ba.

Ɗago kanta tayi ta kallesa, daidai lokacinne kuma wani guntun hawaye dake maƙale acikin idanunta, yasamu daman gangarowa.

A fakaice ya kalleta ta gefen idanunsa...  "Inaganin lokaci yayi daya kamata ki koma ga iyayenki, saboda haka zan ajiyeki anan peter zaizo saiki nuna masa garinku zai kaiki gida" yafaɗi haka cikin halin ko inkula yana mai latsa iphone 11 pro ɗin dake riƙe a hanunsa.

Hawayene suka shiga gangarowa daga cikin idanunta kamar an buɗe famfo, murya araunane tace.

"Bansan kowa ba, bani da kowa sai mahaifina wanda kwata kwata bai ɗaukeni a matsayin ƴarsa ba, tun farko na fara rayuwata ne acikin ƙunci, bansan wani abu waishi ɗan ɗanon farinciki ba,  kataimakeni banaso rayuwata ta salwanta!" tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.

Tunda tafara maganan bai ɗago ya kalleta ba baikuma daina abun dayakeyiba, sai ayanzune ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake...   "Wani irin duhu ne acikin rayuwarki da har kika zaɓi salwantar da kanki? wacece ke?"  yatambayeta batare daya ɗaura idanunsa akan ta ba.

Hawayen da kebin kan kumatunta ta sanya hanu ta share.

"Nima bansan koni wacece ba, saidai kawai nasan tsananin duhu ne ke bibiyar rayuwata" tafaɗi haka tana mai sharce hawayen dake kan fuskarta.

Sai alokacin ya ɗago idanunsa ya kalleta, gaba ɗaya idanunta sunyi jajur dasu,  bai sake ce da ita wani abuba ya tada motar suka bar wajen.    Harsuka isa gida bata daina sheshsheƙan kuka ba.

Yana shiga cikin ɗakinsa ya zauna akan gado haɗe da sanya hannayensa ya dafe kansa,  baisan meyasa yakejin son taimakon yarinyar acikin ransa ba, sai dai tawani ɓangare na zuciyarsa bata aminta da abun dayake ƙoƙarin aikatawa ba,  sam bayaso wata ko wani su shigo cikin rayuwarsa, amma kawai yana ganin zaiyi abun daya dace.

** ** **

Ajiyar zuciya yasauƙe akaro na barkatai haɗe da jawo trolly ɗin dake gefensa, tun adaren jiya ya gama shirya kayansa, ƙarfe 6 na yamma jirgin da zai hau zuwa Abuja zai tashi, kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa yayi ƙarfe 5:20 na yammaci dai dai, ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da fitar da numfashi daga bakinsa.   Jan ɗan ƙaramin trollyn nasa ya yi haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.

Tsayawa yayi abakin ƙofar haɗe dayin knocking.  Kamar dama jira ake yayi knocking ɗin aka buɗe ƙofar.

Ganin ta buɗe ƙofar ne yasashi juyawa yasoma tafiya, batare da yace da ita wani abuba. Ganin haka yasa ta fito jikinta asanyaye tashiga bin bayansa.

Ganin yana ƙoƙarin shiga cikin motar yasanya itama tashiga ta zauna haɗe da takurewa waje ɗaya. 

Ga mamakinta sai gani tayi yashiga gidan baya ya zauna yayinda Peter ya zo yashiga mazaunin driver. 
Tafiya sukayi mai ɗan nisa kafun suka isa inda zasu,  baki hanci da ido duk ta buɗe tana ƙarewa wajen data tsinci kanta aciki kallo.  A hankali tafara bin mutanen dake ta hada hada a wajen da idanu ɗaya bayan ɗaya,  yawancin jama'ar dake wajen ɗauke suke da ƴan akwatunansu, yayinda wasu kuwa ke tsai tsaye.

"fito muje" Sooraj yace da ita yana maiƙoƙarin cire sit belt ɗin dake jikinsa. 
Tana biye dashi abaya sai wurga idanunta takeyi takota ina,  daga bayanta kuwa peter ne ke riƙe da ƴar jakan Sooraj,  tunda suka shigo cikin wajen, idanun yawancin mutane musamman ƴan mata ya dawo kan Sooraj,  suna ƙarasowa wajen ana sanar da cewa matafiya Abuja su shirya jirginsu yakusa tashi.   Tsayawa daga tafiyar da yakeyi yayi haɗe da juyawa ya kalli peter.    "Kawuce gida kawai peter sai munyi waya"  yafaɗa yana duban lokaci a gogon dake hanunsa.

Kai Peter ya jinjina alaman gamsuwa haɗe dayi masa Allah Ya Kiyaye hanya.

Pass yaciro daga cikin aljihunsa guda biyu ya miƙa mata ɗaya, amsa tayi tana mai kafesa da ɗara ɗaran idanunta.

Suna zuwa bakin ƙofar shiga yanuna pass ɗinsa, ganin abun da yayi yasa itama ta nuna ƴar takardan daya bata, dan batasanma takardan ko ta mecece ba, sannan aka barsu suka wuce.

Idanu ta ware tana bin jiragen dake wajen da ido, tunda take aduniarta bata taɓa ganin jirgi ido da ido ba sai ayau, hakanne yasa take ganin abun kamar almara,   direct inda jirginsu yake ya nufa,  har yaje kusa da matattakalar jirgin ya juyo donyi mata magana, amma abun mamaki bai ganta abayansa ba,  ɗan kalle kalle ya somayi, can ya hangota tsaye tana ta kallon jirage. (Like ƙawata hauwa lokacin da ta fara zuwa airport.Lol)   takaicine ya turnuƙeshi,  nufar inda take yayi, yana zuwa ya kamo hanunta, haɗe da turata gabansa, suka soma tafiya,   saida suka kawo ƙofar shiga jirgin, ta tsaya tana kallonsa lokaci guda idanunta sukayi raurau dasu, zuciyarta ta karye, wani tunanine yashiga yawo acikin ranta.   Da Kyawawan idanunsa ya kalleta, aƙufule yace. "Wuce muje!"   

Kasa koda motsa ƙafafunta tayi, tsanin tsoro takeji, bazata iya taka matattakalan ba.

Kamar yasan abun datake tunani kenan, ganin tana masa wasting time yasa ya kama hanunta suka soma haura matattakalan.

Direct  ɓangaren Business class suka nufa,  suna shiga ya nufi  inda kujeransa yake ya zauna wacce take kusa da window,  tsaye tayi takasa zama sai raba idanunta take, abun kamar amafarki wai yau itace acikin jirgi.   Ganin ta tsaya mai aka yasa shi ɗago da kansa ya harareta,  aibatasan lokacin da ta zauna akan kujeran dake kusa danasa ba.   Sit belt ya ɗaura ajikinsa, haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujera, kana ya lumshe idanunsa.   Gaba ɗaya Ziyada amatuƙar tsorace take, jitake kamar tazama tsuntsuwa ta fire.  Lokacin da aka soma announcement  cewa kowa ya ɗaura sit belt ɗinsa,   ɗan ranƙwafowa kusa da ita yayi, har suna iya jiyo hucin numfashin juna, sit belt ɗinta ya ɗaura mata, kana yakoma ya kwanta ajikin kujeransa, sannu ahankali jirginsu ya ɗaga sararin samaniya.

Tsananin sanyin AC'n dake ratsa cikin jirgin, shine dalilin da ya sanya tatakure jikinta waje ɗaya, sam bata saba da sanyiba ko kaɗan.


   *Vote Me On Wattpad*
      @fatymasardauna

 
#arrogant
#fantasy

[4/7, 12:02 PM] fatymasardauna: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

                *Wattpad*
          @fatymasardauna

     *Chapter 11*

Tunda jirgin su ya ɗaga bai buɗe idanunsa ba har jirgin nasu ya sauƙa a NNAMDI AZIKWE Internation airport. Buɗe idanunsa yayi a hankali tare da  zare sit belt ɗin dake jikinsa, dubansa ya kai zuwa gareta, wani babban abun mamaki ganinta yayi tana bacci, fuskarta  ɗauke da wani bushashshen hawaye,  takaicinta ne ya sake kamashi, shi sam baisan ita wace irin bagidajiya bace ba, yanzu aɗan tafiyan da bai wuce 30 minute ba har ace tayi bacci ?

Hanunsa yasa ya zunguri kanta, da yake baccin nata baiyi nisa ba, hakan yasa ta buɗe idanunta, ta sauƙe ƙwayar idanunta a kansa.

Nuni yayi mata da ta cire sit belt ɗin dake jikinta, cire sit belt ɗin tayi tana mai mutsutstsuka idanunta da suke cike da bacci.
Gudun kada tayi masa halinnata na ƙauyanci ta ba da shi agaban mutane yasa ya tusa ƙeyarta gaba suka nufi hanyar fita daga cikin jirgin.

Cikin takunsa na isa yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, sanye yake da riga da wando na jeans baƙaƙe sai kuma facing cap white colour daya sanya akansa, kalan takalman dake ƙafansa.
Kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikakken ɗan gaye ne wanda yake murza naira.  babu wani makusa  atattare dashi, komai nasa yayi hundred percent, sam a halittarsa ta bayyane bazaka taɓa kawo cewa yana ɗauke da wata damuwa ba,  saboda shiɗin irin mazan nanne masu aji da wayewa, sannan yanada cikar halitta, komai nasa abun so ne ga ƴa macen da tasan kanta.  yanada kyawun jiki data fuska, ajikinsa dai kam baida wata makusa, amma kuma saidai shikaɗai yasan menene aibunsa, wanda idan da zai bayyana rauninsa a fili,  to tabbas da sai kowacce mace ta gujesa, saboda aibun dayake ɗauke dashi, yafi tsananin kyawu da dukiyarsa tasiri wajen rugujewar farincikinsa.   idan akayi dubi da lalurar dake damunsa shekara da shekaru to tabbas kyawunsa da haɗuwarsa ba zasu amfana masa komaiba,  dama kuma hakane yawanci kowani bawa da irin tasa tawayan. 

Yana gama sauƙowa daga kan matattakalan ya gyara zaman facing cap ɗin dake kansa.  Wani matashin saurayi ne ya ƙaraso wajen da suke da sauri. Cike da girmamawa ya ce.

"Barka da zuwa Oga"
yaƙare maganar yana mai karɓan jakan dake hanun Sooraj ɗin...     

"Yauwa!" Sooraj ya amsa ataƙaice.

Juyowa yayi ya kalli Ziyada dake ta faman murje gajiyayyun idanunta, tana kuma ƙarewa haɗaɗɗen wajen kallo, domin kuwa wannan airport ɗin ya ɗarawa wanda suka baro.

"Kuje mota ina zuwa" yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin shiga wata babbar ƙofa ta glass dake cikin airport ɗin.

"Ranki yadaɗe muje ko" wannan saurayin yace da Ziyada, da haryanzu take ta kalle kalle.   Babu musu tabi bayansa, sai dai a ƙasan zuciyarta shumfuɗe take da tsoro, zuwa yanzu wata zuciyar na sanar da ita cewa "Sai da ita Sooraj zaiyi"  hakanan zuciyarta tasa mata cewa ba banza yake ɗawainiya da ita ba, saidai kuma ta wata fuskar sam baiyi kama da mugayen mutane ba, duk da bayi da sakewa, amma baiyi kamanni da mugaye ba.

Direct wajen wata dan ƙareriyar mota taga sun nufa,  buɗe mata gidan gaba ɓangaren mai zaman banza matashin saurayin da ake ƙira da Kamalu yayi,  yana mai satan kallon fuskarta, mamakine cike azuciyarsa, yana mamakin a ina ogansa ya samota, yasan Sooraj yakuma san baida wata ƙanwa mace balle yace itaɗin ko ƙanwarsa ce, ya kuma san halin ogan nasa baya neman mata, balle ko yace  wata ya ɗauko zasuyi zaman haramci,  da wannan tunanin yashiga ɓangaren driver ya zauna.

Fuskarta ta manna ajikin glass ɗin window'n motar tana mai kallon mutanen dake ta hada hada a wajen.
Kallonta ta mayar ga ƙofar da taga ya shiga, daidai lokacinne kuma ta hangoshi ya fito,  fuskarsa ɗauke da wata ƴar guntun murmushi da iyakanta kan leɓe,    tunda take arayuwarta bata taɓa ganin mutum irinsa ba,  haka kawai take ganinsa wani daban acikin mutane, komai nasa special ne.    Gani tayi wani ya biyosa abaya yana dariya, atare suka jero da Sooraj ɗin fuskar wannan ɗin ɗauke take da fari'a saɓanin Sooraj da fuskarsa ke ɗauke da yanayi irin na ba yabo ba fallasa.  Har wajen motar Ma'arouf ya rako Sooraj. (Ma'arouf abokin Sooraj ne sannan babban matuƙin jirgin sama ne)        

Buɗe gidan baya Sooraj yayi ya shiga,  ɗan ranƙwafowa Ma'arouf yayi haɗe dayin knocking  glass ɗin window'n motar ta inda Ziyada ke zaune,  a hankali Kamalu yayi ƙasa da glass ɗin window'n, atunaninsa gaisawa Ma'arouf ɗin keso suyi dashi, don yasan halin Ma'arouf akwai kirki, baruwansa komin ƙasƙancinka zai sake kuyi mu'amala dashi.

Waro idanunsa yayi haɗe da sanya hanu ya shafi fuskarsa,  "Masha Allah!" yafaɗa acikin zuciyarsa bayan yayi tozali da kyakkyawar fuskar Ziyada.

"Wow!! Raj ina kasamo mana wannan haɗaɗɗiyar baby'n haka?     i hope dai ba kayan ka bace?"    Ma'arouf yatambayi Sooraj yana mai sake ƙarewa fuskar Ziyada kallo, saboda yarinyar tayi matuƙar tafiya da imaninsa musamman ma Innocent face ɗinta.

"Kaya na?" Sooraj ya maimaita tambayar da  Ma'arouf yayi masa abakinsa cike da mamaki.

Dariya Ma'arouf yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj.  Gira ɗaya ya ɗage masa haɗe da cewa

"To ya kagani idan da ace zata zama MALLAKINA?"

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da cewa " ko zaka jarraba hakan ?" yanayin yanda yayi maganar cikin halin ko inkula,  shiya sanya  Ma'arouf yin murmushi haɗe da kallon Ziyada wacce idan da za'a kasheta bata fahimci inda kalaman nasu suka dosa ba, ita hankalinta ma ba akansu yake ba.

"Zan jarraba idan kabani dama, amma bayanzuba zaifi kyau nayi kiwonta" Ma'arouf yafaɗi haka cike da shauƙi.

"Banda enough time zaka iya jan motar mutafi?" Sooraj yafaɗi haka ga Kamalu cike da halin ko inkula da zancen da Ma'arouf ɗin keyi.

Jin kalaman Sooraj yasa Kamalu saurin tada motar.  

Ma'arouf dake tsaye yana kallon Sooraj yasaki murmushi haɗe da maida kallonsa ga kyakkyawar yarinyar dako sanin sunanta baiyi ba.   Maida Glass ɗin window'n Kamalu yayi ya rufe, haɗe da yin reverse.   Juyawa Ma'arouf yayi yakoma inda ya fito yana sakin wani murmushi.

Tunda suka hau titi ta sake baza idanunta wajen kalle kallen shukokin dake jere gefe da gefen titi, dogin gine gine masu kyau suketa  wucewa, komai gwanin burgewa.            
Shikuwa tunda ya ɗauki jarida yamai da hankalinsa akai, ko ɗago kansa baiyi ba, sai dai har aƙasan zuciyarsa yanata juya kalaman Ma'arouf da yake tambayarsa "wai itaɗin kayansa ce?"   Hmmm lallai yasake yarda babu wani wanda yasan sirrinsa, inbanda ma rashin aiki irin na Ma'arouf mai zaiyi da wannan ƴar mitsilan yarinyar? shi bayaji idan ma akwai wani abu acikin iskanci to zai samu atattare da ita, duka dukanta bata wuce 18 to 19 years ba to me zai ɗauka ajikinta? balle ma shikam mace kodaga wacce duniya tafito bazata amfanesa ta fannin mu'amala ba, saidai ko tawani ɓangare kamar aiki da sauransu.

Asokoro.

Gaban  wani tangamemen gate mai kyau da tsari Kamalu driver ya tsaya haɗe da soma danna horn ɗin motar,  da sauri wani daga cikin gidan ya wangale musu makeken gate ɗin, shikuwa Kamalu driver ya shigar da motan ciki.

Yana gama daidaita parking ɗin motar ya juyo ga Sooraj cike da ladabi yace "Ranka ya daɗe mun ƙaraso"

Batare daya ɗago kansa daga karatun jaridan dayake ba yace "Okay!"
Fita daga cikin motar Kamalu driver yayi bayan ya ɗauki jakar Ogannasa ya yi cikin gida da ita.

Ganin yana ƙoƙarin fita daga cikin motar yasa itama ta buɗe murfin motar ta fito,  compound ɗin gidan take ta kallo.

Kamar jela haka take biye dashi a baya, kafun yaƙaraso ma tuni Kamalu yasa key ya buɗe ƙofar da zata sadasu da cikin katafaren falon gidan.

Ganin ya buɗe ƙofar yashiga yasa itama ta bi bayansa Tana jefa ƙafafunta acikin falon suka soma nutsewa acikin wani lallausan carpet dake malale aƙofar shigowa falon, wani sanyin AC ne ya ratsata.   Kamalu driver na ajiye jakan hanunsa ya fita daga cikin falon haɗe da rufo musu ƙofar,  sam tamanta ma tare suke dashi, falon tashiga ƙarewa kallo, komai na cikin falon milk colour ne daga kan kujeru har zuwa kan labulaye, falo ne haɗɗaɗɗe mai ɗauke da tsari irin na mazan da suka san kansu. 

Sooraj kuwa kota kanta baibi ba direct ɗakinsa ya wuce,  yana shiga yarage kayan dake jikinsa haɗe da shigewa cikin bathroom.  Al'adansane idan yaje wanka kafun yayi wanka sai ya kunna shower ruwa ya dakesa sosai, yau ma hakance ta kasance, sosai ruwan shower yadaki jikinsa, sannan yayi wanka.

Fitowa yayi daga cikin bathroom ɗin sanye da rigan wanka ajikinsa.

Akan kujeran dressing mirror ya zauna haɗe da ɗaukan comb yashiga taje sumar dake kansa wacce take a jiƙe da ruwa.
Yana kammalawa yayi amfani da handryer wajen busar da gashin kansa, hakanan yake shi mutum ne maison tara suma akansa, sannan kuma koda yaushe, askin kansa irin na turawa ne, shiyasa always yake yanayi dasu, sosai kuma askin keyi masa kyau, saboda gashin nasa yana da laushi, ga kuma gyaran da yakesha na mayuka masu tsadan gaske.

Sosai yake son combat trouser saboda hakanema yawancin wandunansa suka kasance Combat.    Yanzu madai Combat jeans yasanya a jikinsa.   kwanciya yayi akan makeken gadonsa,  lumshe idanunsa yayi haɗe da jawo wayarsa ya saƙala earpiece akunnensa,  waƙa yakeji mai sanyin sauti, hakan yasa  duk yaji jikinsa yayi weak. 

Jin ansoma

7 / 47