Author : Maman Teddy Category : Adventure
ta ɗauka kana ta shige cikin gida. Mutane tasamu sosai acikin babban falon na Oummu, kasancewar sunyi nisa acikin hidiman da sukeyi yasanya saɗaf saɗaf ta haye sama, batare da kowa ya ganta ba, kaitsaye ɗakin Oummu ta nufa, da sallama ɗauke abakinta ta shiga cikin ɗakin nan ta iske Oummu da Aunty Muhibbat da kuma Aunty Laylerh, cike da girmamawa ta gaidasu, cikin so da ƙauna suka amsa mata, inda dukansu suka yaba da gyaran Hajiya Arabi don sosai Zieyaderh taƙara kyau, daga ɗakin Oummu ɗakinta ta wuce, nan ta rage kayan jikinta ta kwanta wayarta ta ɗauka ta shiga IG kasancewar yana ɗebe mata kewa sosai.
Washegari.
Yau takama thursday kuma yaune za'a gudanar da henna day, tun safe gidan yake ɗinke da ƴan uwan Oummu dana Abba, yayinda aka ɗauko ƙwararrun masu zanen lalle daga maiduguri wanda zasuyiwa Amarya Zieyaderh zanen lalle na musamman, su Nasmah da Shukra ma sunzo wanda bayan sungama zana exam ɗinsu na yau ɗinne suka biyo ta gidan, zuwansu yasanya damuwan da take ciki yaɗan gushe, don sun ɗebe mata kewa sosai, har kusan ƙarfe 3 na yammaci sannan aka gamawa Amarya Zieyaderh zanen lallenta wanda ya matuƙar yiwa fatarta kyau, kasancewarta fara sosai hakan yasa jan lallen ya kama farar fatar jikinta ya zauna raɗau har wani maroon colour yayi, masha Allah Zieyaderh tazama tamkar wata sarauniya banda walwali ba abun da takeyi, sai wajen ƙarfe 6 na yammaci sannan su Shukra suka soma shirin tafiya gida, Oummu da kanta tasanya Kamalu driver ya maida kowaccensu gida.
Friday.
Tun ƙarfe 6 Aunty Muhibbat ta tasheta inda tanayin breakfast suka wuce shagon saloon, gyaran gashi akayi mata mai kyau, daganan wani ƙaton mall suka wuce, Aunty Muhibbat ne tayi sayayya sannan suka dawo gida, kasancewar yau da yamma ƙarfe 4 za a gudanar da walima. Tun ƙarfe 2 Bilkh tazo don shirya amarya, kafun ƙarfe uku tuni Bilkh ta tsantsara mata kwalliya akan fuskarta, Aunty Muhibbat da kanta ta shiryata cikin wani irin tsadadden lace mai kalan fari da ratsin sky blue, wanda yaji ɗinkin riga da sket 12 pieces, sosai lace ɗin ya amshi jikinta, wani haɗaɗɗen sky blue material sari Aunty Muhibbat ta naɗa mata akan kayan, wanda yaƙara bayyana kyawun kwalliyan nata, daga kan ɗan kunne zuwa dan ƙareren sarƙan dake wuyanta har izuwa awarwaro da zoben hannunta gaba ki ɗaya na gold ne, masha Allah Amarya Zieyaderh kam taji kyau harma tagaji da haɗuwa, kowa ya ganta sai yayi santin kyawun da tayi, haka Bilkh da Aunty Muhibbat suka dinga ɗaukarta hotuna, Bilkh kuwa har ma da vedio tayi mata ta ɗaura akan shafinta na Instagram. Ƙarfe huɗu daidai aka soma ƙoƙarin tafiya da ita wajen walima, adai dai lokacin su Nasmah suka ƙaraso sun sha kyau ita da Shukra inda sukayi ado cikin wasu tsadaddun dogayen riguna masu kyau. Tsala tsalan motoci aka tanada na musamman don zuwa walima, cikin wata haɗaɗɗiyar mota ƙiran ferarri aka sanya amarya ita da su Shukra tare da Aunty Muhibbat. Ajere motocin da suka cimma guda talatin kebin dogon titin suna tafiya cikin nutsuwa ahaka har suka ƙarasa babban katafaren hall ɗin da za'a gudanar da waliman, Aunty Muhibbat da Shukra ne suka riƙo amarya aka shigo da ita cikin taron jama'an, nan fa kowa yafara ambatan masha Allah, don dayawansu basu san amaryar ba sai aranan, kowa ya yaba da tsananin kyawunta.
Walima aka gabatar mai rai da lafiya yayinda aka gudanar da wa'azi mai ratsa jiki da zuciya akan zaman aure, sosai wa'azin ya ratsa zuciyar Zieyaderh har batasan sanda hawaye suka fito daga cikin idanunta ba, wanda ita kanta batasan mene dalilin fitar hawayen ba, anci ansha sosai awajen waliman yayinda aka raba kyaututtuka, duk wanda yazo waliman sai da yasamu kyautar Sallaya da kuma al'ƙur'ani izu sittin, bayan an kammala walima ne kuma aka shiga ɗaukan hoto, abu dai yayi daɗi saidai ace masha.
Tun ahanyar dawowansu gida wani irin zazzaɓi ya rufe Zieyaderh, wanda har saida Aunty Muhibbat ta lura da hakan, koda suka koma gida Aunty Muhibbat da kanta ta haɗa mata ruwan wanka, tana fitowa awanka ta zura wata riga marar nauyi, sallah tayi sannan ta kwanta bayan tasha maganin da Aunty Muhibbat takawo mata, lulluɓa tayi da blanket tare da matse jikinta waje ɗaya.
6:00 pm daidai jirginsu ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin abuja Nnmdi Azikwe International Airport.
Ahankali yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, sanye yake da white pencil jeans and white t-shirt, sai kuma wata jibgegiyar rigan sanyi daya ɗaura akan rigannasa wanda take da kalan maroon, white facing cap ne akansa wanda hakan yasanya ba a iya ganin fuskarsa sosai, yana gama sauƙowa daga kan step ɗin cikin sauri Kamalu driver ya ƙaraso tare da karɓan ƴar ƙaraman jakan dake hannunsa, tare da yi masa sannu da dawowa.. Kaitsaye gidansa ya wuce, don bayason kowa yasan da dawowarsa, yana shiga cikin tamfatsetsen ɗakinsa ya kashe wuta, tare da cire kayan jikinsa dogon wandonsa kawai ya bari, kwanciya yayi luf akan gadonsa tare da lulluɓa da blanket, awahalce yake maida numfashi yana me ƙara takure kansa waje ɗaya, sannu ahankali zafin zazzaɓin dake jikinsa ke ƙara hauhawa.
1:00 am daidai awannan lokacin cikin kaso 90 na mutane suna bacci, kasancewar dare yakasance mahutar bawa, saidai saɓanin haka ne yakasance daga ɓangarenta don kuwa sam bacci ƴaƙi zuwa idanunta awannan dare, kuka take ƙasa ƙasa hadda sheshsheƙa wanda hakan ya haifarmata da ciwon kai, zafin zazzaɓin jikintane ya ƙara hawa hakan yasa gaba ɗaya jikinta ya ɗauki masassara, kuka take sosai, wani irin faɗuwar gaba takeji na musamman idan ta tuna da cewa gobe za'a ɗaura mata aure, tanaji ajikinta tamkar wani abu zai faru da ita. Haka takwana acikin matsanancin zazzaɓi da ciwon kai sai wajen ƙarfe huɗu na asuba sannan tasamu bacci ɓarawo ya ɗauketa.
Wayewar garin yau yakasance rana ta musamman awajen ahalin Sooraj don kuwa yau tun safe suke cike da farin ciki, yayinda gidan kota ina ke cike da ƴan uwa da kuma abokan arziki.
Ƙarfe takwas daidai tasoma yunƙurin buɗe gajiyayyun idanunta ahankali, har yanzu akwai zazzaɓi ajikinta, cikin dauriya ta jingina bayanta da saman gadon tare da rumtse idanunta, Aunty Muhibbat ce taturo ƙofar ɗakin tashigo, ganin Zieyaderh'n da tayi azaune yasa ta ƙaraso da sauri cikeda kulawa tace.
"Kintashi ya jikin naki?"
"Da sauƙi!" tafaɗa asanyaye tana me karyar da kanta gefe, Hannu Aunty Muhibbat takai ta taɓa wuyanta, zafi zau taji hakan yasa tace "Subahanallahi har yanzu zazzaɓin bai sauƙa ba, muje kiyi wanka sai kiyi break kisha magani!"
Da taimakon Aunty Muhibbat ta sauƙo daga kan gadon, har toilet Aunty Muhibbat ta kaita tare da haɗa mata ruwan wanka.
9:30 am tuni ƙofar gidan ya ɗinke da mutane manya manyan ƴan siyasa da masu muƙami harma da masu sarauta da ƴan kasuwa, kowa kagani fuskarsa ɗauke take da murmushi, Abba wanda yake cikin tawagarsa kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa yana cikin farinciki, can na hango Almustapha wanda yasha ado cikin wata blue ɗin shadda riga da wando tare da babban riga, sosai yayi kyau shima fuskarsa ƙunshe take da murmushi, duk bayan minti ɗaya yake kai dubansa zuwa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
Cikin tsananin damuwa Mas'oud ke kallon SOORAJ wanda ke zaune agaban dressing mirror yana shafawa jikinsa mai, zallan damuwa Mas'oud ya hango kwance akan fuskar Sooraj, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa 9:40 cikin ɗan zaƙuwa yace "9:40 fa RAJ kayi sauri kada mu makara"
Harara Sooraj ya watsa masa tare da cewa "Bayan ka matsamin akan cewa saina bika yanzu kuma mene zaka dameni"
Murmushi kawai Mas'oud yayi tare da cewa "Naji koma me kayi sauri."
Baki Sooraj ya buɗe daniyar yin magana sai kuma tari ya sarƙesa da sauri yasanya handkerchief ya toshe bakinsa gudun kada Mas'oud ya ji sautin tarin har ya lura da jinin dake fita daga bakinsa, ganin kamar hankalin Mas'oud baya garesa hakan yasa ya goge bakinsa tare da komawa toilet ya wanke bakinsa, da kallo kawai Mas'oud ya bisa don yaga sanda Sooraj yayi saurin goge jinin dake fita a bakinsa, yanasane yayi kamar baigani ba, wani irin tausayin abokinnasa ne yasake lulluɓe zuciyarsa.
Cikin dauriya da danne ciwon dayakeji yasanya tsadaddiyar shaddan da Mas'oud ya kawo masa, riga da wando ne ɗinkin half jumper, sai kuma gare wanda yasha aiki sosai, yana gama sanya kayan ya zura baƙaƙen takalmansa na kamfanin gucci aƙafansa wanda suke da matuƙar tsada, hulansa mai ratsin white and blue yasanya, kasancewar shaddan jikinsa white ce aikinta kuma ya kasance blue, sosai da sosai yayi kyau, yayinda gold wrist watch ɗinsa keta shinning yana ɗauke ido, baƙaramin kyau Sooraj yayi ba, duk da cewa ciwon dake cinsa arai yaɗan bayyana rama kaɗan ajikinsa, saidai kuma ya ƙara fari sosai, sannan kuma ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa ya ƙara kwantawa luf akan fuskarsa, Mas'oud da kansa saida ya yaba irin kyawun da Sooraj yayi, wayoyinsa ya ɗauka ya zuba acikin aljihun rigarsa, batare dayacewa Mas'oud ƙalaba ya murɗa handle ɗin ƙofar ya fita. Ganin haka yasanya Mas'oud rufa masa baya.
Cikin wata haɗaɗɗiyar motar SOORAJ ƙiran Buggati suka nufi unguwar Maitama inda anan za'a ɗaura auren.
Haɗaɗɗiyar motartasu ce ta ƙaraso ƙofar gidan yayinda ta ratsa cikin yawan jama'an dake cike a wajen, Mas'oud ne ya fara buɗe murfin motar ya fita, yayinda Kamalu wanda shike driving motar ya zagayo da sauri ya buɗewa Sooraj ƙofar motar, yana fitowa kallo ya dawo kansa domin sosai yayi kyau. Sam baidamu da kallon da jama'an wajen keyi masa ba, yanufi inda Abbansa yake, kan wata lallausan darduma ya zauna, fuskarsa ɗauke da mamaki yake bin ƴan tsirarun abokansa da yagani awajen da kallo, Mas'oud ne ya zauna akusa dashi tare da dafashi, ɗago da kansa yayi ya kalli Mas'oud, murmushi Mas'oud yayi masa tare da kashe masa ido, sanin iskancin Mas'oud nada yawa yasanyashi kawar da kansa gefe, yanayin hayaniyan da akeyi awajen yasanya har aka gama ɗaurin auren baisani ba, wayarsa dake ta faman ruri ya ciro daga aljihunsa, baikai gayin picking call ɗinba yaji ana shelan cewa an ɗaura auren *SOORAJ MANSOOR MAINASARA da Amaryarsa ZIEYADERH ABUBAKAR* akan sadaki naira dubu ɗari.
*Comment*
*share and*
*vote*
*fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 44*
Ahankali ta buɗe idanunta da sukayi mata matuƙar nauyi ta sauƙesu akan Aunty Muhibbat. Cikin tsananin kulawa Aunty Muhibbat tace "Sannu Zieyaderh tashi kisa kaya sai muje asibiti ko, naji jikin naki yayi zafi sosai!"
Oummu ce tashigo cikin ɗakin fuskarta ɗauke da damuwa, ƙarasowa gaban gadon da Zieyaderh'n ke kwance tayi cike da tausayin Zieyaderh'n tasanya hannunta ta taɓa wuyanta, jin zafi zau ajikinta, yasanya Oummu cikin damuwa sosai tace "Muhibbat sanya mata kaya naƙira Dr.Bashir yana hanya!"
"To" kawai Aunty Muhibbat tace tare da ɗauko wani lallausan arebian gown wanda aka tsara ado me ɗaukar hankali ajikinsa, miƙawa Zieyaderh rigan tayi tare da cewa ta sanya, cikin ɗan kuzarin daya rage mata tasanya rigan wanda yabi gaba ɗaya surar jikinta ya lafe, komawa tayi ta kwanta tana me maida numfashi ahankali, jin kanta take kamar zai rabe biyu.
Blanket Aunty Muhibbat ta rufa mata, inda tabi bayan Oummu suka fice daga cikin ɗakin.
Wani irin shock ne yaji ya kama gaba ɗaya illahirin jikinsa, take yaji komai ya tsaya masa cak, yayinda maganan maroƙin ke ƙara yawo acikin kunnuwansa yana me hautsina ƙwaƙwalwa da tunaninsa, dummmm haka yaji acikin kunnuwansa yayinda yaji tamkar an buga masa guduma atsakar kansa, tunani gami da nutsuwarsa ne suka ɗauke gaba ɗaya, haka yazama tamkar wani statue, cikin tsananin farinciki da jin daɗi Mas'oud ya dafa kafaɗunsa tare da cewa.
"Ina matuƙar tayaka murna da farincikin samun Zieyaderh amatsayin mata, Allah ya tayaka riƙo!" Mas'oud ya faɗi maganar yana me ɗan bubbuga kafaɗan SOORAJ wanda har yanzu ya kasa ƙyafta koda idanunsa ne, fuska ɗauke da tsananin farinciki Almustapha ya ƙaraso inda Sooraj din ke zaune, hug ya basa tare da cewa.
"Happy Married life my brother, am very happy to day!"
Sai alokacin Sooraj ya motsa idanunsa inda yakeyiwa Almustapha wani irin kallo me ɗauke da tarin tambayoyi haɗi da ma'anoni daban daban.
Ƴan tsirarun abokansa da suka samu daman halartar ɗaurin auren ne suka ƙaraso inda yake, kowanne daga cikinsu bakinsa ɗauke da fatan alkhairi, shidai SOORAJ tamkar wani gunki haka yake binsu da idanu, wani irin gumi ne ke tsatstsafowa ta goshinsa, lokaci guda jikinsa ya soma karkarwa tamkar wanda aka watsawa ruwan sanyi, lura da hakanne yasanya Mas'oud kamo hannunsa suka fice daga cikin taron jama'an dake wajen, kai tsaye mota Mas'oud ya nufa dashi inda ya buɗe gidan baya ya tura Sooraj ɗin aciki kana yamaida murfin ya rufe.
Da ƙarfi ya rumtse idanunsa yana mejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi kamar zata faso ƙirjinshi, wani irin sarawa kansa keyi, yayinda numfashinsa ke seizing yana me ƙoƙarin ɗaukewa, hannunsa yakai kan ƙirjinsa dake masa wani irin ƙuna, idanunsa ne suka kaɗa sukai jajur, da ƙyar ya iya haɗiye wani yawu me ɗaci wanda ya tsaya amaƙoshinsa, jiyake kamar ana watsa masa ruwan zafi akan fatarsa, yanajin kamar yata kurma ihu ko zai samu nutsuwa da salama acikin zuciyarsa, jingina bayansa yayi da jikin kujeran motar tare da cije laɓɓansa, idanunsa da suka kaɗa sukai ja kamar garwashin wuta ya lumshe tare da sanya hannuwansa duka biyu ya toshe kunnuwansa dake ta faman amsa masa amo.
Cikin mintunan da basu wuce 20 ba Dr.Basheer yasamu daman ƙarasowa cikin gidan, kai tsaye Aunty Muhibbat ce tayi masa jagora zuwa ɗakin Zieyaderh, saboda Oummu na fama da jama'arta.
Akan bedsite Dr.Bashir ya zauna tare da ciro kayan aikinsa ya soma kwada yanayin jikinnata, yana kammalawa ya haɗa wasu allurai guda biyu wanda zaiyi mata, drip ya shiga ƙoƙarin ɗaura mata don ya lura sosai take buƙatan ruwa, ganin manyan alluran dayake ƙoƙarin yi mata ne yasanya ta rumtse idanunta, cikin fitar hayyaci tare da sambatu irin na zafin zazzaɓi daya sauƙar mata lokaci guda tace. "Banason Allura, wayyo Yaya kazo kafaɗa masa banason allura, banason komai kai kawai nakeso!"
Baki buɗe Aunty Muhibbat ta kalli Dr.Bashir,
murmushi Dr.Bashir yayi mata tare da girgiza kansa cikin nutsuwa yace. "Karki damu zafin zazzaɓi ne yasanyata haka amma nanda 1 hour insha Allah zata ji sauƙi!"
Kuka Zieyaderh keyi sosai haka Dr.Bashir yayi mata allura, har ya gama yi mata alluran kuwa bata daina kuka ba, tun baigama haɗa kayan aikinsa ba wani irin fitinannen bacci ya soma fusgar ta, kasancewar manyan allurai yayi mata masu ƙarfi hakan yasa dole zasu sata bacci, lumshe idanunta wanda sukayi luhu luhu tayi, gaba ɗaya yanayin idanunnata sun sauya, yayinda suka koma kamar na wata wacce ke cikin tsananin maye.
Wata farar takarda Dr.Bashir yabawa Aunty Muhibbat inda yace anemamata magungunan idan tatashi sai abata tasha insha Allah Zata warke, godiya Aunty Muhibbat tayi masa inda daganan yayi musu sallama ya tafi, mintuna 5 kacal da tafiyan Dr.Bashir nannauyan bacci ya ɗauki Zieyaderh, ganin haka yasa Aunty Muhibbat gyara mata kwanciya tare da rufa mata blanket, rage mata gusun a.c tayi kana ta jawo mata ƙofar ɗakin ta fice, koda ta gayawa Oummu yanda sukayi da Dr.Bashir ƙiran Almustapha Oummu tayi tabashi takardan tare da gaya masa halin da Zieyaderh'n ke ciki.
Idanu Almustapha ya zaro waje cikin damuwa yace "Badai aurenta da SOORAJ ne matsalan ba?"
Kai Oummu ta girgiza masa tare da cewa "Bashi bane, don har yanzun bata sani ba, tunjiya dai take fama da zazzaɓin"
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Allah ya bata lafiya"
Da "Ameen" su duka suka amsa kana ya fice don siyawa Zieyaderh magani.
Acan waje kuwa sannu ahankali jama'a keta watsewa inda kowa ke kama gabansa, Alhaji Mansur ne ya dubi Malam Garba wanda yazo ɗaurin auren dashi da ƴan tsirarun abokansa, cikin kulawa yayi musu iso zuwa cikin katafaren falonsa, shidai Malam Garba gaba ɗaya jinsa yake wani iri, burinsa shine yayi ido huɗu da angon ƴartasa don ya damƙa masa amanarta, saidai kuma yawan jama'an dake wajen yasanya sam baiga angon ba yadaiji wasu nacewa angon yanacikin mota amma dai bai ganshi ba.
Mas'oud ne ya buɗe murfin motar ya shigo, saidai ba inda Sooraj ke zaune yashiga ba ɓangaren driver ya shiga tare da yiwa motar key, tunda ya sunkuyar da kansa ƙasa bai ɗagoba harkawo yanzu da suka kawo cikin katafaren gidannasa. Mas'oud na gama daidaita parking motar ya juyo da kallonsa ga Sooraj baikai ga cewa Komai ba, Sooraj ya buɗe murfin motar ya fita, sam bayako iya ganin gabansa da kyau hakan yasa yake ta gauraya hanya tamkar wanda ke cikin maye, kamar kububuwa haka ya wuce zuwa ɗakinsa dake sama, yana shiga yasoma kiciniyar cire babban rigan dake jikinsa, ƙarasawa gaban tangamemen glass mirror ɗin dake cikin ɗakin yayi, duban kansa da yayi acikin mirror ɗinne yasanyashi jin wani irin ɗaci amaƙoshinsa, cikin wani irin zafin nama haɗi da ƙunci, damuwa, da takaici yasanya hannunsa ya daki mirror'n, take mirror'n ya tarwatse, yayinda hannunsa kuwa yashiga zub da jini, cikin wani irin tururin ɓacin rai dake damunsa yasanya hannunsa gaba ɗaya yayi watsi da gaba ɗaya kayan shafan dake jere reras agaban mirror'n, wani irin ƙara yasanya tare da soma buga kansa ajikin bango, daidai lokacin Mas'oud ya ƙaraso cikin ɗakin, ganin abun da Sooraj ɗin ke aikatawa, sannan ga kuma hannunsa dake zubar da jini, yasanya Mas'oud ƙarasowa cikin ɗakin da sauri, cikin tsananin tashin hankali yace.
"Sooraj ka......"
"Shut up Mas'oud!!!" Sooraj yafaɗa atsawace wanda har saida Mas'oud yaɗan tsorata, cikin tsananin ɓacin ran dake cinsa azuciya yace.
"Mekuka aikata kenan Mas'oud? Nace me kuka aikata!!" Kunsan abun da kukayi kuwa?"
Azafafe ya shaƙe wuyan rigar Mas'oud cikin wata irin murya me amo, wanda tunda Mas'oud ɗin yake baisan cewa Sooraj na da'ita ba yace.
"Why do you do this to me? mehakan da kukayi