Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   45 / 47

132K to 135K   out of 140.6K words

kaɗo ce baikamata ina cikakken fulani naje na auro musu ita ba,  auren ma kuma wai ni nayi gaban kaina, haka muke rayuwa watarana daɗi watarana akasin haka, awajena kaɗai Maryama kesamun soyayya, kowa bayasonta, ƴan uwana kyararta suke, har takai ga tsoron shiga cikinsu take, ahaka muka shafe shekaru huɗu da ita, acikin waƴannan shekarun babu wani ɗan uwanta guda ɗaya daya nemi sanin inda muke, sau dayawa nakan isketa tana kuka wanda na tabbata kukan nan na kewar ƴan uwanta ne takeyi, saboda akwai shaƙuwa mai kyau atsakanin su, wanda kuma ƙaddararren aurena da tayi ne ya raba hakan,  tsana da tsangwaman da ƴan uwana keyi mata ya ƙarune alokacin da muka shafe shekaru huɗu   sukaga babu alaman ciki atattare da'ita, nanfa bakin kowa akanta yake kowa sai yana ce mata juya,  sam mutane sukan manta cewa haihuwa da rashinta duk na Allah Ne, sannan Allah Yakan iya tawayan bawa ta kowani fanni, dayawan mutane ƙarancin ilimi da tunani kesa suyin gorin haihuwa, sun manta  ita haihuwa Allah Kan bawa wanda yasone ya kuma hana wanda yaso, hakan kuma bawai yana nuni da cewa Allah Ya hanaka don baya sonka bane, wataƙila hanakan dayayi shine mafi alkhairi agareka, kuma dama shi Allah Baya hana bawa abu dan haka kawai, saidai idan abun ya kasance ba alkhairi bane agareka, kuma komai na duniya yana da lokaci, sannan ƙaddara tana yawo akan kowa,  bayan munshafe shekara huɗu da ƴan watanni Allah Ya azurtamu da samun ƙaruwa, tahanyar bawa Maryama ciki, nayi farinciki sosai, duk da kasancewar awannan lokacin inacikin wani hali na takurar rayuwa, ma'ana talauci yayimin  tsanani, munzauna da mahaifiyarki lafiya koda sau ɗaya bata taɓa ɗaga muryarta akan tawa ba, munyi zaman daɗi da ita, takasance mace me tsananin biyayya da haƙuri, kana takasance me kyakkyawar zuciya, da kuma kyawawan halayya, takanci duk wani abun dana kawo mata komai rashin daɗinsa, aduk sanda bansamo ba kuwa takanyi haƙuri taɗanyi ƴan dabarbarunta wajen ganin tasama mana abun da zamuci,  sosai tasha wahala wajen rainon cikin da ke jikinta, kusan kullum bata da lafiya, amma haka take jurewa."
Ɗan numfasawa yayi tare da sanya hannu ya dafe kansa, zuciyarsa cike take da tsananin danasanin da yayi, haƙiƙa yabiyewa son zuciya, da ruɗin shaiɗan wanda yakaisa ya baro, ci gaba yayi da cewa.
"Cikin Maryama nada wata 5  nawayi gari da wani irin hali, wanda har kawo yau bansan meyasa halina ya canza ba, saidai nasan cewa hakan ma yana ɗaya daga cikin Ƙaddarata, hakanan nakejin wani irin masifaffen son ƙara aure ya shigeni, har takai ga inaji ajikina cewa idan banƙara aure ba hankalina bazai taɓa kwanciya ba,  wallahi nayi rantsuwa Maryama bata taɓa ƙuntatamin ba, hasali tanayimini biyayyya, sam kuma batacancanci zama da kishiya ba, amma saboda hali irin namu na maza hakanan naji ina sha'awar zama da mata biyu, duk da kasancewar bani da kuɗi, saidai dama ance ƙarin aure ajininmu yake mu maza, koda ana zaune lafiya, ko ana tashin hankali idan mukaso sai munyi,  haka naje na jajiɓowa kaina auren Ma'u,  babu wani fargaba bare ɗar haka nazo na tunkari Maryama da batun ƙarin aurena, ko da sau ɗaya banji tausayin halin da zata shiga ba, gashi lokacin da ciki ajikinta, sannan bata da kowa wanda ya wuce ni, akaina tabaro iyaye da danginta, ta zaɓeni sama da kowa, halacci take buƙata agareni akullum bawai butulci ba, amma kuma saidai me zuciyar ɗan adam bata da ƙashi, idanuna sun rufe ƙarin aure kawai nasa agaba, hakan yasa nadaina bata wani ingantacciyar kulawa,  ƴan uwana kuwa dama basonta sukeba, jin batun ƙarin aurena kuwa yasa suka cika da murna, nan fa suke ta yada mata haibaici, ita dai haka take rayuwarta sam bata tanka musu,  koda damuwa yayi mata yawa, saidai ta roƙi Allah Sassauci ko kuwa tashiga ɗaki ta ɓoye kanta tayi kuka, daga bisani kuwa tayi murmushi ta share hawayenta, saboda tasan ƙunci baya taɓa dauwama acikin rayuwar ɗan adam, dole watarana sauƙi zaizo.
Anyi bikina da Ma'u lafiya lafiya, inda na gina mata ɗakinta na laka agefen na Maryama,  satin Ma'u ɗaya agidana ta fara bayyana wasu halaye, sannan lokaci ɗaya yazamana inajin mugun shakkanta, idan tace eh bana iya cewa a'a, haka take juyani son ranta, saikuma taga dama nake kula Maryama.
Akwana atashi cikin Maryama ya cika wata tara da sati biyu cif, awata rana ta jumma'a ne nakuda ya tashi mata, rashin kuɗi yasa ta haihu agida, cikin iko da jin ƙai irin na Ubangiji kuwa ta haihu lafiya, inda ta haifo ƴarta mace,  wannan ƴar bakowa bace face ke Zieyaderh, haka Maryam tayi jegonta cikin rashin jin daɗi, don kwata kwata nadaina kulawa da ita, saudayawa takan sa kanta aɗaki tayi kuka sosai,    sanja halina danayi yasa gaba ɗaya ta rame ta fita hayyacinta, nikuwa ko ajikina, haka nake rayuwa ta da Ma'u, inda komai take buƙata inayi mata, tsananin son zuciya irin tawa yasa na manta da halaccin Maryama agareni.
Haka rayuwa take tafiya babu dadi, aɓangaren Maryama don ma saina ga dama nake shiga ɗakinta, haka take rainonki cikin so da ƙauna, sannu ahankali kike ƙara girma, yayinda kammanninki da Maryama ke ƙara bayyana, harma takai ga kinaso ki ɗarata fari da kyau,   sam namanta da wani haƙƙinku ko nauyinku dake kaina, rayuwata kawai nake gaba gaɗi, ɓangaren Ma'u kuwa kullum ƙara ganin ƙimarta nake, yayinda ita kuma takemin duk wani abun da taga dama,  tun kina ƙanƙanuwa ban baku kulawa keda mahaifiyarki ba, bansan meyasa zuciyata tazama butulu akan halaccin da mahaifiyarki tayimin ba."
Hawayen da suka cika idanunsa yayi ƙoƙarin shanyewa tare da cewa.
"Har mahaifiyata  ta rasu batazama mai ƙaunar Maryama ba, haka ƴan uwana suka dinga rasuwa da ɗai ɗaya,   akwana atashi asaran me rai, haka Maryama ta rasu ban zama mai kyautatawa agareta ba, sannan ko bayan rasuwarta da ƴan uwanta suka zo, sun nuna tsantsar tsana akaina saboda acewarsu talauci da zaman ƙuncine yayi ajalinta, inda suka barmini ke don sunce ke jininace sukuma bazasu karɓi jinina ba, har kawo yau kuwa basu sake nemanki ba, bankuma ƙara jin labarinsu ba, saidai akwai yayan mahaifiyarki Alhaji Ahmad Rufa'e wanda yake cikakken ɗan kasuwa, kana kuma babban  ɗan siyasa, shine ma wani lokaci nake ganin fostan sa, amma bayan haka har kawo yau babu wata alaƙa dake tsakanina dasu."

Hawayen dake tsiyaya bisa kan fuskarta ta sharce, tabbas taji ƙaunar dangin mahaifiyarta ya shigeta, saidai kuma sam abun da sukayi basu kyauta ba, baikamata ace sunyi watsi dasu har haka akan wani ɗan dalili nasu ba.
Duban mahaifinnata tayi cikin sanyin Murya tace.
"Amma Baba baikamata ace donsu sunƙi nemanmu mu muƙi nemansu ba, inasonsu Baba inason naje garesu, naji gaba ɗaya naƙosa don naga ƴan uwan mahaifiyata, tabbas nasan zuwa wannan lokacin sunyi nadama, marar amfani."
Murmushi Baban nata yayi tare da kai dubansa ga Inna Ma'u wacce keta gabzan apple, duk labarinnasu da sukeyi tanajinsu, amma dake kayan kwaɗayine agabanta, yasa komai da hankali garesu batayi ba, don koda ma tamai da hankali itace zataji kunya, don sam bata aikata alkhairi ba.
Girgiza kai baban yayi tare da duban ƴartasa yace.
"Kitambayi Mijinki idan ya baki izini, sai nayi miki jagora harzuwa garin na Maiduguri!."
Murmushi kawai tayi tare dayin ƙasa da kanta.
Sam su baban nata basu wani jima sosai ba suka tafi, dama sunzone dan su dubata, haka Oummu ta haɗa Inna Ma'u da kayan tsaraba Niƙi niƙi, amma sam haka Baban Zieyaderh ya hanata amsa, haka suka kama hanya zuciyar Inna Ma'u acunkushe sam bataso hanata karɓan alkhairin da Oummu tayi mata da yayi ba, ita aganinta kawai yana mata baƙin cikine,don ita dama asontane shine yabarta ta kwana, saboda ko kaɗan bata gaji da cin kayan daɗin da aka narka musu ba,  tabbas itakam Allah Yaga zuciarta tana tsananin son kuɗi, da kayan ƙyale ƙyalen dunia, haka dai tayita surutanta ƙasa ƙasa, kana tana wurgawa Malam Garba'n harara, can ƙasan ranta tace ɗan baƙin ciki.
***
Kwata kwata jikin Pharouk yaƙi daɗi, kasancewar yasamu wani irin mummunan buguwa acikin kansa, sakamakon haɗarin da sukayi, wanda shine sanadiyar komai,  sanadin mummunan buguwan daya samu hakan yasanya koda ya farfaɗo zai dinga yawan ciwon kai  matsananci,    yanzu haka likitoti suna iyaka ƙokarinsu wajen ganin sunshawo kan matsalan nasa, tsoronsu ɗaya shine kada abun ya shafi  brain ɗinsa, inda suka dage tuƙuru wajen yi masa aiki.

Yau amatuƙar gajiye ya dawo gidan kasancewar kwana biu yatarawa kansa aiki sosai a office, sannan ga ciwonsa dake matuƙar yi masa zafi, yana ƙarasowa cikin bathroom ɗin, ya aje briefcase ɗin dake hannunsa tare da sanya hannuwansa duka biu ya kama waist ɗinsa, sosai ya ƙarewa ɗakin kallo ganin babu ita babu alamunta, ahankali yashiga rage kayan jikinsa, inda ya buɗe drawer ɗinsa tare da zaro wani sabon blue ɗin towel,   ɗaura towel ɗin yayi akan waist dinshi, tare da nufar toilet, tsayawa yayi agaban shower tare da sakarwa kansa ruwa,  saida yaji gajiyan jikinsa yaɗan soma warwarewa kafun  ya kashe shower'n,  wani ɗan ƙaramin towel ya ɗauka, yana me tsane ruwan dake kansa.
Koda yafito daga cikin toilet ɗin sama sama ya shafa body lotion ajikinsa, kallon ƙaton agogon dake saƙale  jikin bangon ɗakin yayi, 8:00 pm daidai, drawer ɗinsa ya buɗe tare da ciro wani tree quater jeans ya sanya, da body spray ɗinsa me daɗin ƙamshi ya feshe jikinsa,  wani ɗan ƙaramin set na glass wanda aka matuƙar ƙawatasa ya buɗe, wani ɗan box mai kyau ya ɗauko tare da buɗewa, wata ƴar siririyar chain ne ta bayyana cikin ɗan ƙaramin akwatin irin ta maza, sosai sarƙan keda azaban kyau, duk da cewa siririyace kuma ta maza ne amma tana da kyau sosai,  akan kakkauran wuyansa yasanya sarƙan,  inda ya ƙarasa gaban ɗan madaidaicin fridge din dake cikin ɗakin,  kwalin fresh milk ya ɗauko, tare da bootle water wanda baida sanyi sosai, tablets ɗinsa ya ɗauko tare da ɓare kowanne ya zuba acikin bakinsa, kana yabi da ruwa, ɗaukan fresh milk ɗin yayi tare da ƙarasawa gaban gadon ya zauna, tunda ya ɗaura bakin goran fresh milk ɗin abakinsa bai cire ba, har saida yashanye sa tas, cikin durstbin ya wurga kwalin tare da shigewa bathroom ya wanko bakinsa, kasancewar yayi sallan isha tun kafun shigowarsa hakan yasa kaitsaye ya nufi kan gado, kwanciya yayi luf akan gadon tare da lumshe idanunsa, sosai yakejin gajiya ajikinsa hakan yasa bacci ke fusgarsa.

Zieyaderh kuwa tun da tayi sallan magriba tatafi ɓangaren Oummu, inda acan tasamu wata ƴar aminiyar Oummun tazo, nan Oummu tasa ƴar budurwan mai suna Zainab, ta zanawa Zieyadern jan lalle ayatsunta na hannu, domin kuwa Zainab ɗin ta iya sosae.
yanzuma can cikin ɗakin Oummun take tana shirya mata kayanta acikin trolly, don Oummun tasanar da ita cewa zata koma Kaduna yayinda su kuma zasu koma gidansu, sam Zieyaderh bataji daɗin hakan ba, saboda batason rabuwa da Oummu, Oummu ce tashigo cikin ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi, duban Zieyaderh  tayi  haɗi da cewa.
"Shirya kayan ya isa hakanan ae dai ba yanzu bane tafiyan, yakamata ki ɗan sarara ki huta, kuma ma naga dare yayi, ya kamata kije ki kwanta, dan inama tunanin yajima da dawowa."

Kunyane ya rufeta jin abunda Oummun ta faɗa, hakan yasa tayi ƙasa da kanta, ahankali take wasa da ƴan watsunta wanda sukasha jan lalle, cikin sanyin murya tace da Oummun "Saida safe."
Fuska ɗauke da murmushi Oummu ta sa mata tare da binta da kallo harta fice,  sosai takejin ƙaunar Zieyaderh'n acikin ranta.

Tun shigowarta cikin ƙawataccen falon tasamu tsaraban ƙamshinsa, hakanne ya tabbatar mata da cewa ya dawo, ahankali tatura ƙofar ɗakin tashiga bakinta ɗauke da sallama, dashi idanunta suka fara tozali inda yake kwance yayi irin kwanciyarnan ta rub da ciki,yayinda yasanya hannunsa ɗaya ya dafe mararsa, da dukkan alama bacci yake,  ahankali taƙaraso cikin ɗakin, idanu ta zuba masa, inda take ƙarewa naked fresh white skin ɗinsa kallo,  sosai komai nasa ya haɗu, idanunta ta sauƙe akan faffaɗan bayansa wanda keta shinning batare dako ɗigon zufa akan skin ɗin nasa ba,  ƙarasowa jikin gadon tayi tare da zuba masa ido, ganin ya kwanta akan hannunsa mai ciwo ne yasanyata ɗan rumtse idanunta,  ahankali takai hannunta daniyar taɓa sa, da sauri kuma ta janye hannunta tare da juyawa cikin sauri ta nufi hanyar   toilet, tana shiga tasoma rage kayan jikinta, wanka tayi tare da ɗauro towel ajikinta, sanin cewa yana bacci yasanya ta  fitowa da towel ɗin ɗaure ajikinta babu ko ɗar,  gaban mirror taƙarasa, kasancewar ana ɗan yanayi na zafi yasanya bata shafa mai ajikinta ba, body spray ɗinta  mai daɗin ƙamshi kawai ta fesa, kaitsaye gaban drawer ta nufa, wata ƴar ƙaraman sleeping dress tasanya, wanda take iyakanta cinya, gaba ɗaya rigan showing take, ganin dare ne yasa bata wani da muba, kwalban turaren da Hajiya Arabi ta haɗota dashi ta ɗauka takuma shafawa ajikinta, sosai ƙamshin turaren ya cika ɗakin, 
Cikin nutsuwa ta taka harzuwa kan kan gadon, zama tayi abakin gadon tare da kai dubanta garesa, zuwa yanzu ya gyara kwanciyarsa inda yake fuskantar sama,  idanu ta zuba masa tana me kallon  kyakkyawar fuskarsa haɗi da lallausan sajensa, sauƙe idanunta tayi akan golding chain ɗin dake wuyansa sosai yayi mata kyau, hakan yasa taɗan saki murmushi,  cigaba tayi da kallon kyakkyawar fuskarsa, ahankali takai hannunta kan fuskarsa, so take ta shafa lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa,  lumshe idanunta tayi alokacin da hannunta ya sauƙa akan tattausan sajen nasa, bazato ba tsammani taji yasanya hannunsa inda ya riƙe nata hannun, da sauri taɗan zaro idanunta waje, don kuwa koda wasa batai tsammanin idanunsa biyu ba,   ahankali ya buɗe lumsassun idanunsa, ya sauƙesu akanta, wani irin yarrr taji ajikinta sakamakon wani irin fitinannen kallo daya jefata dashi,  lumshe idanunta tayi ahankali tare da buɗewa,  cikin nutsuwa ya jawota jikinsa inda ta faɗa kan chest ɗinsa,  cikin wani irin yanayi yake ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo, wani irin kallo me matuƙar kashe jiki yakeyi mata, hakan yasa sam bazata iya jure ganin cikin ƙwayar idanunsa ba, domin kuwa wani irin maganaɗisun ƙaunarsane ke fusgarta, ahankali ya ɗago hannunta, kallon yatsunta da suka sha jan lalle yayi, cikin nutsuwa ya tura ƴan yatsun nata abakinsa, lumshe idanunsa yayi yayinda yasa harshe da laɓɓansa duka biu yana tsotsansu ahankali, wani irin matsanancin daɗi ne ke ratsa jikinta, sosai ɗumin bakinsa dake sauƙa akan yatsun nata, suka sanya taji gaba ɗaya jikinta yayi weak,  cikin wani irin yanayi yasake jawota jikinsa, bakinsa ya ɗaura adaidai saitin kunnenta, cikin unique voice dinsa mai sanya bacci yace.
"I MISS YOU!."

(Kuyi haƙuri yau ina azumi shiasa bansamu nayi muku editing ba)

*Vote*
*and*
*comment*

      fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SOORAJ!!!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                   *Wattpad*
           @fatymasardauna
#hearttouching

*(Godiya ta musamman agareku HASSAN ATK and HUSSAINI 80k, nagode sosai da sosai, tabbas bisa ƙoƙarinku nayimana  posting ne yasa SOORAJ yatafi harzuwa inda banyi tunani ba, nagode sosai Allah Yabar zumunci.    Bazan manta dakai ba NAZEEFI N YAREEMA, kaima kataka rawar gani sosai na kuma gode. Dukanku inayi muku fatan alkhairi da farinciki marar yankewa)*
            
         *CHAPTER 56 (END)*

"I MISS YOU!."   yafaɗa yana me duban kyakkyawar fuskarta, murmushin daya bayyana zallan kyawunta tayi tare da ɗan lumshe idanunta, hakanan tasamu kanta da duban cikin idanunsa, wanda suke ɗauke da tsananin mayen soyayyarta, laɓɓanta taɗan ciza, kana ahankali tasoma motsa su, da'alama magana takeson yi.
dubansa yakai kan ƙananan laɓɓan nata inda ya ɗan lumshe idanunsa, hannunsa ya ɗaura akan waist ɗinta, duban fuskarta yayi cikin yanayi irin na kallo mai tsayawa azuciya yace.
"You miss me?"
Kanta ta kaɗa masa alamar "Eh" kana tayi ƙasa da idanunta.
Murmushin daya fitar da kyawun fuskarsa yayi,  inda ya jawota gaba ɗaya jikinsa, kwantar da ita aƙasansa yayi, yayinda ya zamana shi yana samanta,  rumfa yayi mata da faffaɗan chest ɗinsa,  cikin zazzafar ƙaunarta dake ratsa jini da jijiyansa ya sauƙe idanunsa akanta, inda yake binta da wani irin mayataccen kallo,  ahankali taɗan buɗe idanunta, don yanda ƙamshinsa ke ratsa hancinta yasa gaba ɗaya, tasoma rasa nutsuwarta,  langwaɓar da kanta tayi tare da ɗan marairaice fuska, cikin sabon yanayin da ta samu kanta aciki ta jefa idanunta cikin nasa,  karon farko kenan da ta soma jure kallon cikin idanunsa,  hannunsa yakai ahankali ya shafi gefen fuskarta, hakan yasa taɗan lumshe ido,  ƙasa yayi da idanunsa bayan ya gama ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo, inda ya sauƙe ganinsa akan shinning breast ɗinta, wani irin abune yaji yabi ta cikin jikinsa, sosai breast ɗinnata sukayi masa kyau, musamman yanda haskensu ya bayyana acikin ƴar ficikar rigar baccin dake jikinta, wanda babu wani abu nata na sirri da rigar ta ɓoye,  ahankali ya tura kansa cikin wuyanta, cikin wani irin yanayi ya manna mata kiss tare da goga mata laɓɓansa masu masifar taushi haɗi da sanyi akan fatar wuyanta,  wani irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe tare da lumshe idanunta,  daddaɗan ƙamshin daya jiyo acikin jikinta shi ya so haukata tunaninsa, sake tura fuskarsa cikin wuyanta yayi, inda ahankali yake sakin zazzafan numfashi,  wanda hucin numfashin nasa ne ya ƙara mata feeling,  ahankali ta ɗaura hannunta akan naked skin ɗinsa,   ɗago da kansa yayi ya kalleta da idanunsa wanda suka ɗan sanja launi,  murmushine ya bayyana akan laɓɓanta, tare da ɗan juya idanunta,  hakan da tayi sosai ya ƙarawa fuskarta kyau, yatsantsa ya sanya inda ahankali yake zagaye kyawawan laɓɓanta,   idanunsa ya zuba mata, hakan yasa ta lumshe nata idanun, saboda abu biu ne ke yawo acikin idanunnasa, tsantsar soyayya haɗi da sha'awa, wanda kuma sam idanunta bazasu iya juran ganin hakan ba.
Kwantar da kansa yayi adaidai gefen fuskarta, kamar wanda za'a ƙwace masa ita,  haka ya shige cikin jikinta, cikin wata irin murya dake kashe jiki, yace.
"Yaushe kika fara sona?."
Jin tambayar tasa tayi abazata, hakan yasa tayi saurin buɗe idanunta ta kallesa, gani tayi still idanunsa akanta suke, saidai kuma yanayin yanda yayi yasa taji kamar bashine yayi maganan ba,
shiru tayi yayinda taji bugun zuciyarta ya tsananta, ƙoƙarin maida idanunta take, yayi saurin kai hannunsa inda ya ɗago haɓarta,  duban tsab yayi mata tare da karyar da wuyansa gefe, cikin wani irin yanayi daya samu kansa aciki yace.
"Please tell me!."
Baki taɗan buɗe

45 / 47