Author : Maman Teddy Category : Adventure
yanzun ma murmushine ɗauke akan fuskarta, miƙowa Zieyaderh wata haɗaɗɗiyar ƴar jaka me kyau tayi, amsan jakan Zieyaderh tayi tana me kallon Oummu cike dason ƙarin bayani, "Kyautane daga surakanki, inafata zakiyi murna zakuma ki yaba da kyautar!" Oummu tafaɗa tana me ƙoƙarin manna farin glass akan idanunta.
Jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi sunkuyar dakanta ƙasa tayi asanyaye tace "Nagode sosai Oummu amma sai nake ga kamar kyautan sunyi yawa, duk dama banga menene aciki ba!"
Murmushi Oummu tayi tare da cewa "Bana tunanin kyautar tayi yawa kedai ki amsa kawai, gaba kuma idan kunsake haɗuwa sai ki musu godiya"
Cike da jin nauyin Oummu'n tasake yi mata godiya sannan tatashi ta wuce ɗakinta. Koda taje zama tayi akan gado tare da buɗe jakar, wani ɗan box me kyau da burgewa taciro daga cikin jakan, tare da buɗewa, wani danƙareren agogon hannu na gwal ne ya bayyana acikin kyakkyawan box ɗin. agogone na mata me matuƙar ɗaukar hankali, kyawawan duwatsunsa sai ɗauke ido suke, sake fito da wani box ɗin tayi wanda har yamafi wancan ɗin girma, shi kuwa wani irin danƙareren sarƙa da ɗankunnen gwal ne acikinsa me kyaun gaske, sosai design ɗin sarƙan ya mata kyau, har batasan sanda ta saki lallausan murmushi akan fuskarta ba, ganin kyaututtukan nada yawane yasanyata zazzage jakan gaba ɗaya akan gado, nan tayi arba da wasu arebian gown masu kyaun gaske, tare da wasu kwalaben humra masu ƙamshi irin masu kama jiki ɗinnan, cike da jin daɗi ta tattara kayan ta maida cikin jaka, sosai kayan suka mata kyau saidai kuma tasan matsayinta baikai nanba, bai kamata ace amatsayinta na ƴar wanda ba kowa ba ayi mata irin wannan hidiman, shigowar Nabila cikin ɗakinne yasanya ta tsaida duk wani abu da take tana kallonta.
"Hajiya tace ashaida miki kina da baƙo awaje"
Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi yayinda taji gabanta ya ɗan faɗi cikin yanayi naɗan mamaki tace "Baƙo?"
Kai kawai Nabila ta iya kaɗa mata alamar "Eh" kasa cewa komae tayi har Nabila ta juya ta fice daga cikin ɗakin, Vail ɗinta me kyau da walwali ta sanya tarufe jikinta, cikin fargaban sanin ko waye haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita, bata samu kowa afalon ba hakan yasa kaitsaye tanufi ƙofar da zai sadata da compound ɗin gidan.
Tsaye yake ajikin motarsa ƙirar jeep yasha kyau cikin shigarsa ta half jumper White and blue colour, yayinda ya kafa hular Zanna bukar mai adon blue akansa, haɗaɗɗen sajen dake kwance akan fuskarsa ne ya kwanta luf akan ƙuncinsa, yana ganinta yasaki murmushinsa mai kyau wanda har saida gefe da gefen kumatunsa suka loɓa, ganinsa baƙaramin faɗar mata da gaba yayi ba,take mood ɗinta ya sauya daga ƙwarin guiwa zuwa raunin zuciya, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da kasa ƙarasowa inda yake, murmushi yayi ganin ta tsaya batare da ta ƙaraso garesa ba, ahankali yashiga takawa har zuwa inda take, daddaɗan ƙamshin turarensa ne yasanar mata da zuwansa, ahankali ta ɗan lumshe idanunta tare da buɗesu, kanta taɗan ɗago ta kallesa, idanunsune suka sarƙe acikin na juna kasancewar shiɗinma kallonta yake, kasa ɗauke idanunta daga kansa tayi saima wani irin marairaicewa da idanun nata suka yi, shiɗinma kallonta yakeyi da sexy eyes ɗinsa wanda suke wani irin lumshewa kaɗan kaɗan, cikin wata irin murya me sanyi yace "Anan zaki barni bazaki bani wajen zama ba?"
Kanta ta sunkuwar ƙasa tare da ɗanyin murmushi, kallonta tamayar ga wajen ɗan shaƙatawan dake cikin gidan wanda aka ƙawatashi da wasu kujeru guda huɗu masu kyau gaba ɗaya flowers sun zagaye wajen yayinda sukayiwa rumfar dake wajen ƙawanya, kallonsa tayi sannan tanufi wajen shima ya rufa mata baya. Akan ɗaya daga cikin kujerun ta zauna yayinda shima ya zauna akan kujeran dake facing nata. Ƙasa tayi da kanta tare da soma wasa da ƴan yatsun hannunta murya asanyaye tace. "Ina wuni!" murmushin daya bayyana dimples dinsa yayi batare daya amsa taba sai idanu daya zuba mata, sosai yau ɗin tayi masa kyau, don kokaɗan meckup ɗin dake kan beauty face ɗinta bai goge ba, jin shiru bai amsata bane yasanyata turo bakinta gaba aɗan shagwaɓe tace "To ba gaisheka nake ba kuma kaƙi amsawa!" Murmushi yayi harsai da haƙwaransa suka bayyana. "To ae banji bane, please kiɗan ƙara ɗaya sainaji!" Yafaɗa cikin salon kwaikwayon maganarta. Idanunta ta ɗago kana taɗan watsa masa hararan wasa tare da ɗan murguɗa masa ƙaramin bakinta dayasha baby pink colour lipstick, lumshe idanunsa yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran, wani irin shauƙi ne ke shigansa, sosai yanda tayi da bakinta yayi masa kyau, cikin wani irin yanayi yace. "Kullum ƙara kyau kike, idan kina fushi kyau kike ƙarawa, idan kina murmushi kyau kike ƙarawa, haka ma idan kina gabana kyau kike ƙarawa, inajin kamar sonki acikin jinina yake Zieyaderh, ko sau ɗaya ne please ki amsa min cewa kina sona!" yaƙare maganar yana me kafeta da mayun idanunsa wanda suka ɗan sauya kala, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da ɗan ciza laɓɓanta, ƙirjinta ne yake bugu da sauri, maganan aurenta da Almustapha ne yazo yayi tsaye aranta, tabbas tanajin wani abu na daban dangane da Pharouk, to amma bata da tabbacin cewa wannan abun soyayyace, koda ma acd sonsa take mecece amfanin soyayyar? yanzu burinta shine ta koyawa zuciyarta soyayyar Almustspha, dan sai da soyayya ne kaɗai zata iya kyautata masa azaman aurensu. Ɗago idanunta da sukayi raurau da hawaye tayi daniyar yiwa Pharouk magana, saidai tuni maganan nata ta maƙale sakamakon Ido biyu da sukayi da Almustapha dake tunkaro inda suke, ganin ta tsaida idanunta abayansa yasanyashi ɗan waigawa don ganin abunda take kallo, idanunsa ne suka sauƙa akan kyakkyawan saurayin dake zuwa garesu, kwata kwata bai wuce saura taku shida ya ƙaraso inda suke ba, tashi tsaye yayi yana me fuskantar saurayin, daidai lokacin Almustapha ya ƙaraso, dayake shi jan ajin nasa baya hanasa fari'a, hakan yasa bawani ɓata lokaci ya miƙawa Pharouk hannu don su gaisa, ganin haka yasa Pharouk ma bashi hannu suka gaisa, cike da kulawa Almustapha ya kalli Zieyaderh wanda kanta ke ƙasa, hakanan gabanta keta faɗuwa, cikin muryarsa me ɗauke da nutsuwa yace "Inason aron baƙon naki naɗan wasu mintuna, inafatan bazan takuraki ba?"
Wani iri taji yayinda wani irin nauyi da kunyarsa suka lulluɓeta alokaci guda, jikinta asanyaye ta miƙe tsaye tare da kaɗa kanta alaman "Babu komai" cikin nutsuwa haka tajuya tanufi cikin gida, ita kanta bazata iya tantance awani hali take ciki ba awannan lokacin. Kamar wanda ƙwai ya fashewa haka ta haura sama ko lura da Oummu dake tsaye a bakin kitchine batayi ba, Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da duban hanyar da Zieyaderh'n tabi, wani irin fargabane taji ya kamata, sai yanzu takejin tsoron haɗin da tayi, musamman ma da taga yanayin da Zieyaderh'n tashiga ayanzu, shiru tayi tare da faɗawa wani sabon duniyar tunani.
Ita kuwa Zieyaderh tana shiga ɗaki ta rufo ƙofarta, samun kanta tayi da sulalewa ta zauna daɓas aƙasa, batare da ta ankara ba taji wasu hawaye masu ɗumi suna sauƙa akan ƙuncinta, tabbas wannan sabuwar ƙaddaran da ta tsinci kanta aciki tayi mata girma, ƘADDARA tana neman haɗa aurenta da Almustapha, sannan kuma agefe guda ga Pharouk da yake neman ta amsa masa soyayyarsa, ƘADDARA mafi girma awajenta kuwa itace soyayyar Mr.Helper, hannayenta tasanya ta share hawayenta, wata zuciya ce me bata ƙwarin guiwa akan ta yarda da duk wata ƙaddara da tazo mata me kyau ko akasin haka, samun kanta tayi da kwanciya luf akan gado, mintuna ƙalilan bacci ɓarawo ya saceta.
Pharouk. Gudu sosai yake sharawa akan babban titin gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya jikinsa, maganganun da Almustapha ya faɗa masa suketa yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa, da ƙarfi ya daki steering motar ransa amatuƙar ɓace yace
"Bazan taɓa zama looser akaro na biyu ba SOORAJ, awannan karon tabbas bazan bari kasake nasara akaina kamar lokutan baya ba, bazan taɓa bari ka auri Zieyaderh ba SOORAJ!!" wani irin murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, ahankali yashiga rage gudun da yakeyi tare da ƙoƙarin samarwa kansa nutsuwa tahanyar aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa.
***
Oummu ce ta shigo cikin haɗaɗɗen ɗakin wanda yake mallakin Mijinta ne, Abba dake tsaye yana sanya garen kayansa ya ɗan juyo tare da kallonta murmushi yayi mata tare da cewa "Saboda kawai ɗanki zaiyi aure shiyasa kika kasa zaune kika kasa tsaye ko Sulaimiyya!" yaƙare maganar cikin yanayi na ɗan tsokana.
Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarta tare da cewa "Yanzuma ai nashigo ne nasanar dakai abokan tafiyanka sun iso"
Murmushi ya kumayi tare da cewa "Bake kaɗai kikejin farinciki aranki ba Sulaimiyya nima inaji, saidai kuma ata wani ɓangare na zuciyata ina ɗauke da fargaban abun da zaije ya zo"
"Insha Allah Alhajina babu wani abu da zaizo sai alkhairin Allah!" Tafaɗa cikin son ƙarfafa masa guiwa.
Yaji daɗin maganan nata sosai hakan yasa yayi murmushi, har wajen motarsa Oummu ta rakasa inda ya haɗu da manyan aminansa su Uku suka kama hanyar airport, kai tsaye suka wuce Kaduna, daga nan kuma zasu shige cikin motocinsu su wuce ƙauyen saminaka.
Itakuwa Zieyaderh gaba ɗaya wunin yau batajin daɗin jikinta, hakanan takejin kanta cikin ƙunci, wani irin kewa me taɓa zuciya takeji yana ratsa duk ilahirin jikinta, gaba ɗaya su Shukra sun lura da rashin walwalan da takeyi kwana biyu, yanzuma zaune suke su duka ukun akan wani ɗan dakali suna me shan iskan dake kaɗawa asararin samaniya. Cikin yanayi naɗan zolaya Nasmah tace "Amarya badai wai cin amarcin aka fara tun yanzu ba? naga gaba ɗaya duk kin rame, sometimes kuma kina cikin damuwa"
Hararanta Zieyaderh tayi tare daɗan murguɗa mata baki cikin yanayin ɓata fuska tace
"Ni ba amarya bace"
Dariya Nasma da Shukra suka sanya, wanda hakan yaƙara ƙular da ita. "Uhumm kigama zille zillenki yarinya wallahi sai mun fidda ankon bikin ki ehe, sannan kuma sai mun sha rawa koya kikace Besty" Shukra tafaɗa tana kallon Nasmah. "Ƙwarai kuwa" Nasmah tafaɗa tana me gimtse dariyanta. Cikin turo baki gaba Zieyaderh ta miƙe daga zaunen da take tare da nufar hanyar da zai sadata da class ɗinsu. Kallo su Nasmah suka bita dashi harta ɓacewa ganinsu, sannan suka sa dariya, har acikin ransu su mamakinta suke na yanda gaba ɗaya tabi ta takura kanta.
Acan Ƙauyen Saminaka kuwa Tuni Abba sun gana da Malam Garba baban Zieyaderh, inda yayi musu karɓa ta mutumci, babu laifi kuma sun yaba da halin karamcin daya nuna musu, nan suka zauna suna me sake fahimtan juna, sam su Abba bada wasa suka ɗauko maganan auren ba hakan yasa lokaci guda suka gama magana inda Malam Garba ya shaida musu cewa ya basu auren ƴarsa Zieyaderh, Alhaji Maham ɗaya daga cikin aminan Abba shi ya ciro wasu kuɗi dake cikin aljihunsa inda ya miƙa amatsayin sadakin auren Zieyaderh, naira dubu ɗari ne cas, cewar da sukayi basason bikin ya ɗauki lokaci ne yasanya Malam Garba cewa suyi haƙuri suɗan bashi lokaci zuwa nan da kwana huɗu zai sanar dasu kowani lokaci ya yanke, shikuwa yayi hakanne don yanason tattaunawa da Zieyaderh akan batun auren, domin tun da aka fara batun auren baiji ta bakinta ba kuma itama tana da haƙƙi, cikin mutumta juna su Abba sukaiwa Malam Garba sallama inda suka kama hanyar dawowa cikin garin Kaduna.
..........
15 minute da tashinsu a school kenan amma har zuwa yanzu Kamalu driver baizo ɗaukarta ba kamar yanda ya saba, waige waige taɗan somayi wai kozata hangosa amma babu ko me kama dashi, gashi gaba ɗaya ƴan makarantar sun soma watsewa don tuni su Shukra ma sun tafi, ahankali take takawa harta isa bakin gate ɗin fita daga makarantar, tsayawa tayi daga ɗan gefe kaɗan tana me ƙarewa motocin da keta hada hada awajen kallo, wata haɗaɗɗiyar blue car wanda taji black tinteck ne ta tsaya adaidai gabanta, kallon motar Zieyaderh tayi amma ganin bata iya ganin wanda ke cikin motar ya sanya ta ɗauke kanta gefe,tare da cigaba da kallon hanya, ahankali ya shiga zuge glass ɗin motar, fuskarsa ɗauke da murmushi yace "My ƴar kyakkyawan budurwata!" jin muryarsa acikin kunnuwanta yasanya tayi saurin ɗagowa ta kalleshi, hakanan taji gabanta ya faɗi amma sai tasaki murmushi, da hannu yayi mata alaman da ta taho, samun kanta tayi da kasa musa masa sai kawai taɗan ƙarasa jikin motar, daga ciki yasanya hannu ya buɗe mata murfin motar, duk da cewa ƙirjinta na dukan uku uku haka ta daure tashiga cikin motar saidai bata rufe murfin motar ba, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da kama ƴan yatsunta tana wasa dasu, shikuwa Pharouk ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ƙiran sunanta murya asanyaye. Jin yanda yaƙira sunannata yasanyata ɗago da kanta ta kalleshi, gani tayi gaba ɗaya murmushin dake kan fuskarsa ya kau, zuwa yanzu damuwane shumfuɗe akan fuskarta sa, kasa ɗauke idanunta daga kansa tayi saidai kuma ba cikin idanunsa take kallo ba, tunowa da tayi cewa jiya tabarsu da Almustpha batare da tasan me Almustaphan ya faɗa masa ba yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, jitayi idanunta naneman kawo ruwa, ahankali yasanya hannunsa ya ɗago haɓarta, hakan yasa suka jefa idanunsu cikin na juna, cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa yace "Kinason aure'n?" gabantane ya faɗi dajin tambayar tasa amma kuma saita samu kanta da kasa amsa masa, fuskarsa yasake mareraicewa tare da cewa "Da gaske kenan aure za'a miki? me yasa kika amince da hakan? kinyarda arabani dake kenan ko?" yaƙare maganar yana me matuƙar nuna rauninsa akan fuskarsa.
Hawayen dake kwance acikin idanunta ne suka samu daman gangarowa batare da ta shiryawa hakan ba. Ganin hawaye akan fuskarta ya sanyashi lumshe idanunsa tare da matso da fuskarsa gaf da tata har suna iya jiyo hucin numfashin juna, jin sauƙan numfashinsa akan fuskarta yasanya azabure tayi saurin buɗe idanunta , shima buɗe nasa idanun yayi wanda suka kaɗa sukai ja, wani irin kallo daya mata ne yasanya tayi saurin jan jikinta baya tare da ture hannunsa dake kan haɓan ta, kuka ne yake neman cin ƙarfinta hakan yasa ta juya da sauri ta fita daga cikin motar, dai dai lokacin kuma motar da aka saba zuwa ɗaukanta dashi wanda kamalu driver ke ciki ya tsaya adai dai ƙofar shiga gate ɗin makarantar, da ɗan sassarfa taje ta buɗe murfin motar tare da faɗawa ciki kana ta jawo murfin ta rufe, kanta ta cusa acikin cinyoyinta tare da sakin kuka me sauti, Ko bi takan Kamalu driver dake bata haƙurin rashin zuwansa da wuri da yayi bata biba, kuka take sosai tana me kakkame jikinta, wani irin zafi zuciyarta ke mata, Me yasa har izuwa yau baice komai ba? me yasa ya hanata ganinsa har na tsawon kwana uku? tanajin zafi acikin rai da zuciyarta, safe, rana, dare, duk shine acikin rayuwarta me yasa takejin hakan? Kukanta taci gaba dayi wanda babu me rarrashi, zuwa yanzu harta soma jin haushin kanta, musamman yanda tamaida kanta wata wawiya akansa.
Ganin tashin motarsu yasanya Pharouk sakin wani murmushi wanda shikaɗai yasan ma'anarsa, key ɗin dake jikin motar yaɗan murza, tare da cilla motar tasa kan titi, yayiwa kansa alƙawarin matuƙar shine Pharouk to SOORAJ bazai taɓa samun Zieyaderh amatsayin mata ba.
SOORAJ
Ahankali yake matsowa jikinta yayinda takeja baya shi kuma yana me ƙara matsota, wani irin numfashi yake fitarwa me zafi, kasancewar takawo jikin bango hakan yasa ta tsaya cak, hakan kuma yayi daidai da ƙarasowarsa gareta, ganinsa adaf da ita yasanyata lumshe kyawawan idanunta tare da sakin wani sassanyar ajiyar zuciya, kyakkyawan fuskarta yake kallo yayinda idanunsa ke lumshewa ahankali hankali, numfashinsu ne ya cakuɗa dana juna, yayinda ƙamshin turarensu ya haɗe waje guda, hakan yasa wani irin ƙamshi mai daɗi ke fita ajikin kowannen su, fuskarsa ya manna da tata fuskar yayinda ya sauƙe hannayensa akan faffaɗan waist ɗinta, cikin wani irin yanayi ya ɗaura lips ɗinsa akan nata tare ɗan kama lip ɗinta na ƙasa ya ɗan tsotsa, wani irin abune yaji ya zirga masa har cikin tafin ƙafansa, sake kama lips ɗinnata yayi yashiga tsotsa ahankali yayinda yake fitar da wani irin numfashi, ahankali cikin rufewar ido yake ƙara tsotsan laɓɓanta, wanda hakan yasanya taɗan buɗe bakinta, ahankali ya tura bakinsa cikin nata yayinda harshenta ya faɗa cikin bakinsa, wani irin abu yaji yatsarga ajikinsa yayinda yaja wani irin numfashi tamkar wanda zai shiɗe, azabure ya farka daga baccin da yakeyi, tare da buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, wani irin zufane ke ketowa ta jikinsa yayinda gaba ɗaya gashin jikinsa suka mimmiƙe, jijiyoyin jikinsa ne suka fito raɗa raɗa, tashi zaune yayi yana ne ƙoƙarin jawo numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwacewa, yayinda yakejin tamkar ana buga masa guduma acikin kansa, wani irin ƙara yayi tare da dafe kansa wanda yakejin wani irin azababben ciwo acikinsa, hannayensa yasanya ya dafe kunnuwansa tare da rumtse idanunsa, duniyarce gaba ɗaya take juya masa.
*17:40 pm*
fatymasardauna.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 41*
Ahankali ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, tare da rumtse idanunsa wanda suka kaɗa sukai ja tamkar waƴanda aka watsawa garin barkono, hannayensa ya sanya ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa, wani iri yakeji acikin kansa tamkar ana doka masa gudu ma, cikin ƙarfin halin daya aro ya dasawa kansa ya miƙe tsaye tare da soma binbango yana neman hanyar da zai sadasa da toilet, zuwa yanzu ko gani sosai baya iyawa, wani irin duhu ne ke neman mamaye ganinsa, sunan Allah Yashiga ambata acikin ransa yana me tafiya ahankali, ƙafafunsa ne sukayi masa nauyi, haka yakeji tamkar an ɗaure masa su da kaca, aninayen dake jere reras agaban rigarsa ya soma cirewa, tare da sanya hannunsa ya kunna shower take ruwa yasoma zuba ajikinsa, duka hannayensa ya sanya ya dafe bango tare da rumtse kyawawan idanunsa, yayinda ruwa ke dukan naked skin ɗinsa, still ambaton Allah Yaketayi acikin ransa, ahankali yakejin nutsuwar