Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   35 / 47

102K to 105K   out of 140.6K words

da duban fuskarta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da natsuwa, yayinda take ta faman sauƙe ajiyar zuciya akai akai,  saurin ɗauke idanunsa wanda suka sauƙa akan breast ɗinta yayi,  tare da ɗan yunƙurawa ya tashi da ita ajikinsa.
Ahankali ya shumfuɗeta akan gado,  tare da juyawa ya nufi hanyar bathroom.
Zip ɗin wandon jeans ɗin dake jikinsa ya zuge, tare da zame wandon nasa yayi ƙasa,
daidaita tsayuwarsa yayi agaban shower, tare da ɗan murɗa makunnin shower'n,  sassanyar  ruwan dake fitowa acikin shower'n ne ke dukan jikinsa, sannu ahankali yakejin wani irin sanyi na ratsa gaba ɗaya jikinsa, cikin nutsuwa yayi wanka tare da ɗauro alwala,  farar bathrobe ya sanya ajikinsa kana yafito daga cikin toilet ɗin.
Kaitsaye gaban sif ɗin kayansa ya nufa,  wani black jeans tare da white long sleeve shirt yasanya, kana ya fesa turarensa mai daɗin ƙamshi, wani ƙaton darduma ya shumfuɗa aƙasa, inda ya gabatar da sallah  raka' biyu, yana idarwa yaji ana ƙiran sallan Asuba a masallaci, shafa addu'an da yakeyi yayi tare miƙewa tsaye,  har yakai bakin ƙofar fita daga cikin ɗakin, sai kuma yaɗan tsaya tare da juyowa ya kalli inda take, haryanzu baccinta take sha cikin kwanciyar hankali, handle ɗin ƙofar ya murɗa kana ya fice daga cikin ɗakin.  

7:30 am.
Ahankali take buɗe idanunta wanda sukai nauyi kana kuma sukai ja, sake ɗan lumshe idanun nata tayi sakamakon sihirtaccen ƙamshinsa daya samu daman kawowa hancinta ziyara, ahankali tatashi zaune daga kan gadon, ɗakin tasoma bi da kallo, kana ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya, ahankali ta zuro da ƙafafunta ƙasa, wanda suka sha jan lalle gwanin ban sha'awa, direct inda trolly ɗinta yake ta nufa, zuge zip ɗin jakar tayi tare da fito da wata maroon ɗin abaya gown mai kyau wanda aka ƙawata jikinta da adon ƙyalƙyali, cikin sauri ta shige toilet.
Tsayawa tayi tana me ƙarewa haɗaɗɗen toilet ɗin kallo, komai dake cikinsa nead, sosai aka ƙawata toilet ɗin, gaba ɗaya toilet ɗin ƙamshi yake, ahankali ta ƙarasa jikin wani glass wanda aka jere kyawawan bathrobe da kuma towels acikinsu,  rigar dake hannunta ta ajiye tare da zage zip ɗin rigar,  ɗaya daga cikin towel ɗin ta ɗauko  ƙoƙarin ɗaurawa ajikinta take, daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa ne ya daki hancinta, jingina bayanta tayi da jikin bango tare da lumshe idanunta, sosai ƙamshin nasa ke kashe mata jiki, ɗaura towel ɗin tayi ajikinta tare da ƙarasawa gaban bathtube ta haɗawa kanta ruwan wanka, cikin nutsuwa tayi wanka inda ta zura abaya gown ajikinta,  sosai rigar tayi mata kyau ta kuma amshi jikinta, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar bathroom ɗin tafito,  kaitsaye dressing mirror ta nufa, tsadaddun kayan shafansa ne suka cika gaban mirror'n, gwanin ban sha'awa,  hannunta takai ta ɗauki wani kyakkyawan kwalban turarensa dake kan mirror'n,  jujjuya kwalban turaren tayi ahannunta tare da sauƙe ajiyar zuciya,  nannaɗe dogon gashinta tayi tare da sanya ribbom tayi parking gashin atsakiyar kanta, nan tashiga kimtsa kan gadon, duk dama nead yake bai wani ɓaci sosai ba,  saida ta gyara komai dake cikin ɗakin, kana ta wuce toilet ta wankesa  tsab,  zama tayi akan gado haɗe da jingina bayanta da jikin gadon, lumshe kyawawan idanunta tayi sannu ahankali wasu daga cikin abubuwan da suka faru atsakaninsu jiya da dare suka soma dawo mata,  tabbas Ƙaddara tayi mata sauyi, Ƙaddara ta canza duk wani tunaninta, wasu irin sanyayyun hawayene suka samu damar gangarowa daga cikin idanunta, kwanciya tayi akan gadon tare da cusa kanta cikin pillow ta saki wani irin marayan kuka,
tayaya zata fara koyawa kanta zama dashi? wani abu takeji na daban acikin rai da zuciyarta dangane dashi.

Tunda yafita sallan asuba bashi yadawo gidan ba sai 8:30.

Ahankali ya tura ƙofar ɗakin yashiga,   Zieyaderh wacce take fidda sheshsheƙan kuka tana jin motsinsa tayi shiru tare da sake ɓoye fuskarta acikin pillow, hakanan wani ɗan banzan tsoronsa ya shiga zuciyarta, ko ƙaunar haɗa idanu dashi batasonyi ayanzu.

Sam baidamu da cewar waidon tana ɗakin bazaiyi abun da yakeso ba, hasalima ko inda take baikalla ba, tundaga bakin ƙofar ɗakin yashiga ɓalle maɓallan rigarsa, zuge zip ɗin wandonsa yayi tare da cire rigar jikinsa, cikin takunsa dake amsa amo yanufi gaban sif ɗin kayansa,   tamkar ƙirjinta zai fito waje haka takeji saboda tsoro, sake duƙunƙune jikinta tayi tare da ɗauke numfashinta tayi luf akan gadon kamar wacce ke bacci, ƙasa yayi da wandon jeans ɗinnasa, tare da cire wandon gaba ɗaya daga jikinsa, wani white towel ya ɗaura akan waist ɗinsa, kai tsaye ya wuce bathroom, tanajin motsin rufe ƙofarsa, tasaki wata kyakkyawar ajiyar zuciya. 

Ruwan wanka ya haɗawa kansa acikin bathtube inda ya cika turaren wanka aciki,  kwanciya yayi luf acikin bathtube ɗin yana me sauƙe ajiyar zuciya, sosai yakejin wani irin bacci na fusgarsa, wanka yayi kana yafito daga cikin toilet din, ƙamshin sabulunsa ne gaba ɗaya ya cika ɗakin,  wanda hakan ya narkar da zuciyar Zieyaderh dake kwance, cikin nutsuwa ya gama shafa body lotion ɗinsa, men crazy t-shirt black colour tare da pencil crazy jeans shima black colour yasanya, sosai kayan suka fito da natural white skin ɗinsa, suka kuma yi masa kyau matuƙa,   Duk abunda yakeyi tanajin motsinsa, amma saboda tsoro takasa koda kyakkyawan motsine.
 Yana gama kimtsa kansa ya nufi kan lallausan doguwar kujeran da ayanzu ta zame masa gado,  kwanciya yayi akanta yana me fitar da wani irin numfashi,  idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗesu ya sauƙesu akanta, ahankali yake bin jikinta da kallo, harya kawo idanunsa kan fararen ƙafafunta wanda aka ƙawatasu da zanen jan lalle, cikin nutsuwa yake kallon zanen lallen dake ƙafafunnata tamkar mai nazartar wani abu, azahirin gaskiya kuwa idanunsa ne kawai kekallon zanen, dan sam ƙwaƙwalwarsa ba zanen take kallo ba,  ayanzu damuwarsa tafi ta da yawa, yakanji kamar zuciyarsa zata tarwatse, sannan yakanji kamar ana buga masa guduma atsakar kansa, musamman aduk sanda ya tuno da cewa ita din matsayin mata take agaresa, yazaiyi da haƙƙin ta dake rataye a wuyansa? tayaya zai zama cikakken namijin da zai iya maidata cikakkiyar mace?  kwarai ya sani bazata iya ɗaukar rauni da damuwarsa ba.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da lumshe idanunsa, inama da ace Kaddara bata zamo silar haɗuwarsu ba, ya tabbata da duk haka bata faru ba, inama da ace wani namijin daban kaddara ta zaɓa mata ba shiba, tayaya zai fara fuskantarta da matsalarsa? lumshe idanunsa wanda suka soma sanja launi daga fari zuwa ja yayi tare da sakin zazzafar ajiyar zuciya, mintuna goma kacal da kwanciyarsa bacci ɓarawo ya saceshi.

Ahankali taɗan buɗe idanunta, sam babu wani ƙwaƙƙwaran motsi dake tashi acikin ɗakin, sai sautin ƙaran ac da kuma sautin numfashinsa dake fita ahankali, ɗan juyo da fuskarta tayi ta fuskanci inda yake kwance, ajiyar zuciya ta sauƙe ganin cewa yayi bacci, zuro da ƙafafunta ƙasa tayi tare da miƙewa tsaye, cikin takun sanɗa tanufi hanyar fita daga cikin ɗakin, murɗa handle ɗin ƙofar tayi ahankali kana ta fice.

Tana samun kanta acikin ƙawataccen falon nasa, tasaki wata irin narkakkiyar ajiyar zuciya, daidaita nutsuwarta tayi tare da zame ɗan kwalin dake kanta ta yafa bisa jikinta, duk da cewa tana matuƙar jin kunyan Ummi ayanzu, amma tanaga zama da Ummi'n zaifiyi mata daɗi akan tazauna shiru cikin miskilancinsa.  
Bakinta ɗauke da sallama haka ta kutsa kanta cikin falon Oummu'n, zaune Oummu take akan kujera, yayinda Aunty Muhibbat kuwa ke kan dinning area tana haɗa abinci acikin basket.
Ganin Zieyaderh yasa Oummu faɗaɗa fari'arta.
Cikin ladabi haɗi da girmamawa Zieyaderh tayi ƙasa da kanta tare da durƙusawa har ƙasa tagaida Oummu'n,  fuska ɗauke da murmushi haɗe daso da kuma ƙauna Oummu ta jawota, tare da zaunar da ita akan kujeran da take.
Cikin kulawa Oummu ta tambayeta jikinta.
"Dasauƙi."
Tabawa Oummu'n amsa murya asanyaye,  ƙarasowar Aunty Muhibbat wajen yasanyata sauƙowa daga kan kujeran cikin girmamawa tagaida Aunty Muhibbat ɗin.
Fuska asake Aunty Muhibbat ta amsa mata tare da cewa.
"Yanzu nake shirin kai muko break fast, sai kuma gaki kin fito, wa yace miki amarya tana zuwa gaisuwa? ae saidai azo agaisheta." 

Mumushi Zieyaderh tayi cike dajin kunya tayi kasa da kanta, basket din abincin Aunty Muhibbata tamiƙo mata tare da cewa.
"Idan kina buƙatar wani abu waya kawai zakinayi amma kizauna aɓangarenki kinji, nan ɓangaren Oummu ne saboda haka sai angayyaceku kafun kuzo!." Cikin sigar wasa Aunty Muhibbat taƙarishe maganan.
Wani irin kunyane yasake rufe Zieyaderh, Oummu kuwa murmushi kawai tayi, karɓan basket ɗin tayi inda tamiƙe asanyaye ta nufi ƙofar dazai sadata da ɓangaren nasu,
da kallo Aunty Muhibbat ta rakata, aranta tana me ƙissima abubuwa da yawa, hakanan jikinta yafara bata wani abu dangane da SOORAJ, duk da cewa tunanin nata yayi gaggawa, amma dai tabbas zuciyarta nayi mata wani zargin na daban, lumshe idanunta tayi aranta tana cewa.
"Ya Allah Kasa kada tunanina ya zama gaskiya."

Hira suka shiga ɗan taɓawa kaɗan kaɗan ita da Oummu.

Itakuwa Zieyaderh tana shiga falon nasu aje basket ɗin tayi, inda ta zauna akan ɗaya daga cikin royal chairs ɗin da suka ƙawata tsakiyar falon,  kasancewar bata wani jin yunwa sosai hakan yasanya bataci abincin ba, idanunta ne suka sauƙa akan wani haɗaɗɗen hotonsa wanda ke saƙale ajikin bango, sosai hoton yayi kyau yayinda aka sirrantashi cikin wani glass mai tsada, ahankali tashiga takawa harta ƙarasa inda hoton yake,  idanunta ta tsurawa hoton tare da sakin wani murmushi,  ahoton sanye yake da army jeans black and black t shirt, yayinda yasanya wasu kyawawan combat shoe suma kalan baƙaƙe aƙafansa, yanayin tsayuwar da yayi acikin hoton, yasanya shi yin kyau sosai, murmushi taƙarayi tare da kai hannunta daidai saitin bakinsa, sosai murmushin dake ɗauke akan fuskarsa ta ƙara bayyana tsantsar kyawunsa.
"Kafi kyau idan kana murmush!."
Tafaɗi maganar acikin zuciyarta, sai dai abun da bata sani ba shine maganartata tafito fili,  ahankali tasanya hannunta ta shafo kan kyakkyawar fuskarsa,  aranta tace.
"Kai ɗin na dabanne! babu wani ɗa namiji dazai gwada maka komai, koba kyauba kana da abun da sauran maza basu dashi."
Lumshe kyawawan idanunta tayi tare da ɗan matsawa daga jikin hoton, juyowan da zatayi idanunta suka faɗa cikin nasa idanun, ƙirjinta ne taji yaɗan buga, cikin yanayi na ɗanjin kunya tayi ƙasa da kanta, shima ɗauke idanunsa daga kanta yayi tare da  raɓawa ta gefenta ya wuce, ƙasa ƙasa tabi sa da kallo harya fice daga cikin falon, sosai yayi kyau cikin ssbuwar shigar daya kuma sauyawa, lumshe idanunta tayi tare da komawa cikin falon ta zauna, luf tayi akan kujera tana mejin wani irin tsananin shauƙi na ratsa gaba ɗaya jikinta, wani irin abu takeji ajikinta wanda batasan dame zata ƙirasa ba, tanajin gaba ɗaya tsikar jikinta na mimmiƙewa, haka tayita juyi akan kujera daga ƙarshe bacci ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.


Gyara zama Mas'oud yayi tare da duban Sooraj wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa, ɗago idanunsa yayi ya kalli Dr.Waleey, cikin yanayin dake nuna damuwa akan fuskarsa yace.
"Idan har kuma kun gazo gano matsalar RAJ, hakan nanufin kenan sihiri ne ko kuna shafan aljanu."

Murmushi Dr.Waleey yayi tare da girgiza kansa, cikin son kwantar musu da hankali yace.

"Sam ba asiri bane bakuma shafar aljanu bane kamar yanda kayi tunani, sau dayawa Allah kan jarrabi bawansa ta ɓangarori daban daban, wata jarrabawar abayyane take wata kuwa takan zuwa aɓoye, sannan acikin gaba ɗaya mutanen duniya babu wani wanda ya isa ya gujewa ƙaddararsa, me kyu ko akasinta, Ƙarfin ikon Allah ya wuce tunani, tayanda zai iya jarrabanka da komai,  haƙiƙa Allah na jarraban bawansa da jarabawa mafi girma, sau dayawa kuma idan Allah ya jarrabi bawa da jarrabawa mafi muni sai hankalin wasu daga cikin mutane ya gushe, har ta kaisu ga mantawa da ƙarfin ikon Allah, Idanunsu kan rufewa, sukan dage akan cewa asiri akaiwa mutum, bayan kuma babu wani wanda yayi masa asiri jarrabawace kawai daga Allah!."
Ɗan numfasawa yayi tare da shafa sumar kansa, kallon Sooraj yayi da kyau, cikin tsananin tausayin Sooraj ɗin da yakeji yaci gaba da cewa.

"Haƙiƙa kai ɗin maitawakkaline, sannan kuma kana da ƙarfin imanin riƙo da ƙaddara, tabbas jarabawar da Allah ya ɗaura maka mai matuƙar girmace, bakowani Namiji bane zai iya juran rufe sirrinshi tare da fawwalawa Allah Lamuransa kamar yanda kayi ba,  Baka da matsalan komai Sooraj, kuma kaima watarana Insha Allah zaka zama cikakken Namiji mai lafiya, watarana kai da kanka zakayi mamakin kanka, Insha Allahu bazaka taɓa tabbata ahaka ba!." Dr.Waleey yakai ƙarshen zancen cikin tausasa murya.

Ajiyar zuciya Mas'oud yayi cikin sanyi yace da Dr.Waleey
"Tayaya?"

Still murmushi Dr.Waleey yayi, zamansa ya gyara da kyau, tare da gyara zaman glass ɗin dake idonsa.
"Tabbas zai iya zama cikakken namiji kuma lafiyarsa zata iya dawowa ako da yaushe,  zai iya samun sauƙi idan har ya kawar da duk wani tunani tahanyar sarrafa matarsa koda ko bayajin daɗi."
Shiru yayi kana yacigaba da cewa.
"Kusanci da mace zai iya daidaita komai, sannan yawan raɓan mace zai iya rage masa kaso 30 acikin 100 na matsalar dayake tattare da ita."
Sake kallon Sooraj da haryanzu kansa ke ƙasa yayi cikin lallami yace.
"Ka gwada jarrabawa Sooraj, domin lafiyarka abun buƙatace agareka, Namiji baya taɓa zama ingarma kuma jajirtacce, harsai yakasance yana iya biyawa matarsa buƙata, haƙiƙa nasan cewa kaiɗin gwarzone, saidai kuma irin wannan rashin lafiyan taka zata iya haifar da babban matsala arayuwarka, idan ka gwada za a dace insha Allah, matsalace da ka soma jinta ajikinka tun shekatu 8 da suka wuce, bada ita aka haifeka ba saboda haka zaka iya, watarana kuma zakayi mamaki."

Lumshe idanu Mas'oud yayi tare da buɗesu alokaci guda,  kallon Dr.Waleey yayi tare da basa hannu sukayi musabaha, cikin ɗan sukunin da ya samu acikin ransa najin cewa amininsa zai samu lafiya yace.
"Mungode sosai doctor!."

Nan sukayiwa Dr.Waleey sallama, shidai Sooraj ƙala baice daga bakinsa ba har suka bar cikin asibitin, hasalima wani irin abune yaji ya toshe masa maƙoshi. 
Tunda suka shiga mota babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu, agaban tangamemen gate ɗin gidansu Sooraj ɗin, Mas'oud yayi parking motar.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon Sooraj wanda yajingina bayansa da jikin kujeran motar.

Cikin kulawa Mas'oud ya ƙira sunansa.
"RAJ!."
Ɗago idanunsa wanda suka ɗan soma sanja launi Sooraj yayi ya kallesa.

Idanu Mas'oud yaɗan lumshe cikin son samawa Sooraj ɗin nutsuwa yace.
"Tabbas nayarda, kamar yanda Dr.Waleey yace idan ka jarraba zaka iya, please RAJ ka jarraba."

Murmushin dayafi kuka ciwo ne ya bayyana akan fuskar Sooraj, cikin cool voice ɗinsa yace. 

"Ƙaddara itace wacce tarigayi fata Mas'oud, kamar yanda Dr.Waleey ya faɗa hakane, ƙaddarata tana da girma sosai,  banso shigowarta cikin rayuwata ba Mas'oud, saboda nafi kowa sanin menene illata,  bazan amfaneta dakomai ba, sannan aurena yazama laluri agareta, aurena zai kashe mata ƙuruciyarta zai kuma kashe mata lokacinta, anayin aure ne don aji daɗi akuma raya sunna, bazan taɓa iya jiyar da ita wannan daɗin ba Mas'oud, saboda ina ɗauke da Nakasa." Ɗan tsagaitawa yayi da maganan, still murmushi yayi tare da lumshe idanunsa, cikin sanyin murya yace.

"Kasan yanda nakeji akanta kuwa Mas'oud?  Bansan daliliba amma kowani bugun zuciyata da tunaninta yake tafiya, Inajinta awani ɓangare na jikina, tayaya zan cutar da yarinya ƙarama kamarta? duk wata mace indai bata kasance marar lafiya ba tabbas nasan tana buƙatar Namiji akusa da ita, Ni nakasance saɓanin tunanin mutane, bazan amfaneta ba." Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗan cije laɓɓansa, yanzun kam sosai rauni ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, tunda yake bai taɓajin ciwo da ɗacin rashin kasancewarsa lafiyayyen namiji ba sai yau, dama irin wannan ranan yaketa gudu, shiyasa ya keɓe rayuwarsa daga sha'anin mata, irin wannan raunin yake gujewa kansa shiyasa ya nesanta kansa da soyayya, gashi duk iyaka gudunsa ranar ta riskesa,  ɗago idanunsa yayi ya kalli Mas'oud wanda ƙwalla suka cika idanunsa tab, murmushin daya sanya hawayen dake cikin idanunsa gangarowa yayi tare da cewa.

"Zanyi abun daya dace Mas'oud!."

Yana kaiwa nan azancensa ya buɗe murfin motar ya fito, Da kallo Mas'oud ya bisa harya buɗe tangamemen gate ɗin gidannasu ya shige, hawayen dake cikin idanun Mas'oud ne suka samu daman gangarowa waje, wani irin tausayin abokinnasa yakeji, cikin sanyin jiki yaja motarsa yabar ƙofar gidan.

Tsaye take agaban dressing mirror, wani haɗaɗɗen humra wanda Hajiya Arabi ta bata, take shafawa ajikinta, gaba ɗaya ko ina dake cikin ɗakin ya cika da ƙamshin humra'n nata,
gaba ɗaya ta shagala da abun da takeyi, sanye take da bathrobe pink colour ajikinta, wanda ya tsaya iyaka cinyarta,   kunce igiyan bathrobe ɗin tayi tare da ɗan zamesa ya sauƙa zuwa kan ƙugunta,  humra tashiga shafawa akan ƙirjinta har zuwa kan kafaɗunta,  sam ta manta da cewa ma aɗakinsa take, gaba ɗaya ta saki jiki, daga gefe guda na zuciyarta kuwa, mamakin  ɗaukewan period ɗinta take, don yau kwata kwata kwanansa ɗaya amma ya ɗauke, baikuma taɓa yi mata haka ba,     ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ya shiga,  tsaye yayi ajikin ƙofar yana me ƙare mata kallo tundaga sama har ƙasa, santala santalan legs ɗinta dake ta shinning ya kalla, kana ya sauƙe idanunsa akan bayanta wanda ya matuƙar fidda shape ɗin gefe da gefen cikinta, yayinda fatar bayan nata ke shinning tana fidda wani irin ƙyalli, lumshe idanunsa yayi ahankali ya soma takowa zuwa gareta,  sam batasan da shigowarsa cikin ɗakin ba, gaba ɗaya hankalinta yayi nisa wajen rufe kwalban humran dake hannunta, taku ɗaya ne kacal ya rage atsakaninsu, tsayawa yayi, yayinda sosai ƙamshin da jikinta ke fitarwa yayi masa daɗi, ɗan lumshe idanunsa yayi, hannunsa dake rawa yakai kan fresh skin ɗin dake tsakiyar bayanta.


Azabure Pharouk yayi wurgi da laptop ɗin dake hannunsa, wani irin tuƙuƙin baƙinciki da ɓacin rai ne suka cika idanunsa har suke neman rufe ganinsa, jikinsa ne ya ɗauki rawa tamkar mazari, cikin ƙunan zuciya yafara sambatu lokaci guda kuma yasaki wata mahaukaciyar dariya mai cike da ƙeta,  abayyane yace. 
"Aure ko, hmmm lallai kuwa mu dukanmu zamu rasata,  aurenta da kayi bashike nuna cewa ka mallaketa ba SOORAJ! tabbas kashiryawa rashinta daga yau zuwa

35 / 47