Author : Maman Teddy Category : Adventure
tura kansa cikin motar, ɗaukota yayi kamar wata ƴar baby yayi cikin gidan da ita. Ɗakin dake gefen nasa yashiga da ita, komai na ɗakin neat kamar akwai wani wanda ke rayuwa acikinsa. Yana zuwa daidai gadon ya saketa, ji kake tim tafaɗi akan lallausan katifan dake kan gadon. Tabbas da badon alluran da aika mata mai ƙarfi bace, da ayanda ya wurgatan nan dole saita farka. Juyawa yayi yafice daga cikin ɗakin. Ɗakinsa ya koma, rigar jikinsa ya cire, komawa kan gado yayi ya kwanta. Shi kaɗai yake ƙunƙuni acikin zuciyarsa har bacci yaɗaukesa.....
1:30 am
Tsananin yunwan dake damunta, shiyayi sanadiyar farkawanta daga bacci.. Buɗe gajiyayyun idanunta tayi tana jujjuyasu ahankali. Azabure tatashi tana ƙarewa ɗakin data ganta aciki kallo, tabbas idan zata tuna, wannan bashine ɗakin da ta ganta ɗazu aciki ba, da sauri tashiga waige waige, dirowa tayi ƙasa tana ƙarewa royal bed ɗin data ganta kwance akansa kallo, jingina tayi da bangon ɗakin zuciyarta cike da tarin tsoro da kuma tambayoyi, hanu tasa ta dafe cikinta, da takejinsa kamar babu ƴaƴan hanji acikinsa, tsabar yunwan dake nuƙurƙusanta, wani irin juwa ne ke ibanta, durƙusawa tayi aƙasa haɗe da fashewa da kuka, da duka hannayenta ta kama cikinta, tunda take adunia bata taɓa jin yunwa irin wanda takeji ayanzu ba, jitake kamar wani abu na tsakalan cikinta. Miƙewa tayi ta buɗe wata ƙofa dake cikin ɗakin, atunaninta ko wani ɗakine da zata iya samun abinci taci, gani tayi ɗakin ba komai sai fanfo da kuma wasu fararen abubuwa, saikuma wani abu da tagani asama kamar famfo, duk da cewa bata taɓa zuwa birni ba, amma jikinta yabata cewa nan ɗin banɗaki ne, jan ƙofar tayi ta rufe haɗe da nufar wata ƙofar, tana jan ƙofan kuwa ya buɗe, ahankali ta buɗe ƙofar ta fita, ganinta tayi acikin wani katafaren falo wanda yagaji da haɗuwa, duk da cewa babu yalwataccen haske acikin falon, amma hakan baihanata ganin kyawun falon ba, wurga idanunta dake ɗigar da ruwan hawaye tasomayi tako ta ina, tsorone yasake kamata, kawai saita sulale awajen tashiga rera kuka.
Bayida nauyin bacci ko kaɗan, sama sama yakejiyo gunjin kuka acikin kunnuwansa, ɗan ya mutsa fuskarsa yayi, haɗe da buɗe idanunsa. Shiru yayi yana maijin sautin kukan naƙara ratsa kunnuwansa, Ahankali yace "Najidowa kaina masifa!"
Gyara kwanciyarsa yayi cike da takaicin tashinsa daga daddaɗan baccinsa da tayi, hanu yasanya ya toshe kunnuwansa, sosai yatsani jin kukan mace arayuwarsa, so yayi ya shareta amma kukan da takeyi masa yakasa barinsa yayi hakan. Sauƙowa yayi daga kan gadon, batare daya sanya riga ajikinsa ba ya fice zuwa falo.
Hanunsa ya ɗaura akan makunnin wutan dake falon haɗe da ɗan matsawa, take haske ya gauraye cikin falon, saurin ɗago kanta da ta cusa acikin cinyoyinta tayi, idanunsu ya sauƙa acikin na juna, wani irin bugawa kirjinta yayi kamar zai faɗo waje, take jikinta yaɗauki rawa, da sauri ta rumtse idanunta, ganinsa a haka babu riga da tayi, ya mafi yunwar da takeji ɗaga mata hankali.
"Wai Uban me kikewa kuka?" ya tambayeta a tsawace.
Bakinta ne ya ɗauki rawa, ƙanƙame jikinta tayi guri guda, ahankali ta shiga jijjiga masa kanta alaman "Babu"
"Mcheeww" yaja tsuka cike da takaicinta.
Kallonta yayi a ƙufule sakamakon yanda yaga gaba ɗaya jikinta na rawa. Harara ya wurgamata haɗe da nufar inda zai sadashi da kitchine ɗin dake cikin falon.
Tana ganin tafiyarsa, ta saki wani irin marayan kuka, aranta tana cewa, inane takawo kanta, wataƙila ma saida ita zaiyi, shikenan itakam ga abun da guduwa yajawo mata.
Mintuna kaɗan yadawo cikin falon, hanunsa ɗauke da wani cup, ƙarasowa gabanta yayi haɗe da miƙa mata cup ɗin. Jikinta na rawa haka tasanya hanu ta karɓi kofin, ruwan tea ne aciki, hanunta har ɓari yake alokacin da takai kofin bakinta, abun da batasani ba shine Tea ɗin da zafi sosai, da sauri ta furzar da wanda ta kurɓa, sakamakon ƙona mata harshe da yayi, ta gefen ido yakalleta, haɗe da yin wata muguwar murmushi, yana sane ya haɗa mata tea ɗin da tafasheshshen ruwa.
Hawayene suka gangaro daga cikin idanunta, harshenta ya ƙone sosai, amma Allah yasani bazata iya haƙura da shan tea ɗin ba, saboda yunwa takeji sosai. Haka ta daure ta cigaba da shan tea ɗin tun tanajin zafinsa har ta daina ji, tas ta shanye tea ɗin ta aje kofin, lokaci guda jikinta ya soma tsatstsafo da gumi, sake jin gina bayanta tayi da jikin bango tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai.
Fitowa yayi daga kitchine ɗin haɗe da sanya key ya rufe ƙofar, plate ne ahanunsa, wanda ke ɗauke da yankakkun kayan fruit, miƙa mata plate ɗin yayi cike da haushinta yace
"Gargaɗi na ƙarshe kada ki sake tashina idan ina bacci!"
Itadai kanta na ƙasa bata sake ɗagowa ta kallesaba tun ganin farko da tayi masa, jin ƙaran rufe ƙofarsa ne, yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, da bibbiyu take tura yankakkun kayan fruit ɗin abakinta, fruit ɗin nada yawa, amma saida taci fiye da rabinsa sannan taji ta dawo cikin hayyacinta, hamma tayi haɗe da tashi tsaye tanufi wajen da fridge ke aje, bata iya buɗe fridge ɗin ba, hakan yasa tasoma kiciniyar ɓalle murfin, da ƙyar dai tasamu ta buɗe dayake murfin na glass ne, kana iya hango komai dake cikin fridge ɗin, goran ruwa ta ɗauka tasha, mayarda sauran ruwan tayi cikin fridge ɗin, saɗaf saɗaf haka ta koma ɗakin da ta ganta aciki tun farko, jingina tayi da jikin ƙofar tana mai ƙarewa ɗakin kallo, tsananin tausayin kantane ya kamata, yau gata a wata duniya wacce batasan ina bane, gata acikin gida tare da wani, wanda batasan ko shiɗin waye bane, ahalin yanzu batasan menene makomarta ba, zamewa tayi akan yalwataccen carpet ɗin dake malale a tsakar ɗakin, kuka tashiga rerawa marar sauti, sosai tayi kuka harsaida taji kanta yayi mata nauyi, sannan ta tsagaita ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, tana jingine ajikin bango, wani wahalallen bacci ya ɗauketa.....
Tunda kukanta ya tashesa yakasa komawa bacci, toilet yashiga ya ɗauro alwala, dardumansa ya shumfiɗa yatada sallah.... Yajima yana salla kafun ya idar, laptop ɗinsa yajawo ya soma gudanar da wasu ayyuka, yananan har aka ƙira sallan asuba, rufe laptop ɗin yayi yafita zuwa masallaci...
Sauri Sauri yake shirya kansa kasancewar angayyacesa meeting ɗin gaggawa anan branch ɗinsu dake cikin Kaduna.
Sanye yake da riga da wando na suit masu mugun tsada da kyau, navy blue colour, takalmin ƙafarsa kuwa toms ne mai kyau shima navy blue colour, sosai yayi kyau acikin kayan, nikaina bansan haɗuwarsa takai hakaba, sai yau dana gansa acikin shigar suit. Lol.
Agogon Rolex yake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turarensa mai sauƙar da nutsuwa, gashin kansa kuwa sai ƙyalli yake fitarwa, sosai yasha gyara da mayuka kala kala, wayarsa mai tambarin Apple abaya ya ɗauka, tare da key ɗin motarsa, kana yafice daga cikin ɗakin..
Haɗaɗɗiyar sabuwar motarsa BMW ya hau, mai gadi na buɗe masa ƙofa ya cillata kan titi ahankali yake murza steering motar cike da nutsuwa..
Tun ƙarfe 7 tatashi zama tayi jigum acikin ɗakin, kallon kayan jikinta tashigayi gaba ɗaya sunɓaci da jini, gashi sunyi bala'in yin dotti, banda ɓarkewan da saman rigarta yayi.
Tun tana zaune tana nazari harta kwanta, juyi kawai take tayi, amma gaba ɗaya bata da nutsuwa, jin ana knocking ƙofar ɗakinnata yasa taji ƴaƴan cikinta sun sake hautsinawa saboda tsoro, cigaba akayi da knocking ƙofar, yayinda itakuma ta matse jikinta waje ɗaya, mugun tsoronsa takeji.
"Good Morning Madam" taji muryan mai knocking ƙofar na faɗan haka.
Tsorone yasake kamata, raba idanu tashiga yi tana neman wajen ɓuya don batasan meyake cewa ba, tasan dai wani yare kawai yake yi.
Peter dake tsaye jikin ƙofa hanunsa riƙe da leda ɗin abinci, yaji yasoma gajiya saboda haka, yaciro wayarsa yaƙira ogansa, bansan mai SOORAJ yafaɗa masa ba, sai gani nayi ya aje ledan abakin ƙofa yajuya yayi tafiyarsa.
Jin shiru andaina ƙwanƙwasa ƙofarne bakuma alamar motsin mutum, yasata sauƙo daga kan gadon ahankali. Saɗaf saɗaf take tafiya harta buɗe ƙofar ɗakin, bugewa tayi da ledan da Peter ya ajiye. ko kallon ledan batayi ba tashiga takawa harzuwa tsakiyan katafaren falon. Gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta sai waige waige take, ƙirjintane keta bugawa da sauri sauri fatanta ɗaya Allah yasa kada wani yakamata. Wata ƙofa dake cikin falon tanufa, tana buɗe ƙofar kuwa ta buɗu, wani irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya tasauƙe sakamakon ganinta a waje da tayi. Da sauri sauri ta nufi inda ta hango wani ƙaton gate, burinta ɗaya shine ta ganta awaje, sam batajin zata iya zama agidan ƙattin maza, wataƙilama da wata manufa suka ajiyeta. Taci sa'a kuwa babu kowa abakin gate ɗin saboda haka gadan gadan tanufi ƴar ƙaramar ƙofan dake jikin gate ɗin ɗaura hanunta tayi ajikin ƙofan tare da buɗewa....
*(Niba cikakkiyar bahaushiya bace dole sai kunyi haƙuri da hausana, nasan wasunku bakomai suke ganewa acikin rubutuna ba😥)*
*21/March/2020*
*✅OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna
#hearttouching
#truelove
[4/7, 12:02 PM] fatymasardauna: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*🎂HBD Yaya Hayat wishing you long life and more money in to your bank account*
*Chapter 8*
Tana buɗe ƙofan idanunsu ya sarƙe acikin na juna, wani irin tsorone taji ya kamata, take jikinta ya ɗauki rawa.
Kallo ɗaya yayi mata ya watsar agadarance yace.
"Wuce mukoma ciki"
Samun kanta tayi da kasa musa masa, tana gaba yana biye da ita abaya, suna shiga cikin falon ya murzawa ƙofar key, direct ya wuce ɗakinsa ko kallonta baiyiba, tana ganin wucewarsa cikin ɗaki ta saki wani irin marayan kuka. Yana shiga cikin ɗakin yasoma rage kayan jikinsa. Toilet yashiga yayi wanka, fitowa yayi dagashi sai towel dake ɗaure a ƙugunsa. Sama sama yashafa mai, farin riga da blue ɗin wando yasanya, ba abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshi, buɗe ƙofar ɗakinnasa yayi yafita zuwa falo, ko kallon inda take durƙushe tana kuka baiyi ba, kitchine ya nufa, mintuna ƙalilan yadawo hanunsa ɗauke da wani faranti wanda samansa ke ɗauke da kayan fruit.
Zama yayi akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon, haɗe da ɗaura ƙafansa akan rug, apple ya ɗauka yana gutsura ahankali, jingina bayansa yayi da jikin kujera haɗe da lumshe idanunsa, ahankali yake tauna apple ɗin dake cikin bakinsa, a rayuwarsa idan yaji kukan mace sosai hankalinsa ke tashi, amma a yau ko ajikinsa, daɗima kukannata keyi masa, gani yake ita damuwarta ma mai sauƙice tunda hartana iyayin kuka, shi kuwa shi kaɗai yasan abun da ya keji, idan da zai samu daman yin kuka to tabbas da yayi, idan da za'ace dashi idan yayi kuka matsalarsa zata yaye to tabbas da shikam yayi kuka irin kukan da ya amsa sunanshi kuka, ba irin nata kukan na shagwaɓa da sakalci ba. Ahankali sautin kukanta ke tashi acikin falon, ware idanunsa da suka somayin ja yayi haɗe da watsa mata su. "Keee!!" yafaɗa murya akausashe.
Ɗago fuskarta da yayi caɓa caɓa da hawaye tayi ta kallesa. Yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur ne yasa taji gabanta ya faɗi, miƙewa tsaye yayi, haɗe da takowa harzuwa inda take, hanunsa yasanya ya finciko nata hanun, yana janta haka suka fita daga cikin falon, yana zuwa bakin motarsa ya buɗe murfin motar haɗe da cillata ciki da ƙarfi, har saida ta buge goshinta, shiga cikin motar yayi haɗe da kunnata, baijira mai gadi yagama wangale masa gate ɗin bama, ya figi motar da wani irin gudu haɗe da cillata kan titi. Gudu yaketa shararawa akan titi, bai tsayaba harsai da ya kusan fita daga cikin Kaduna, parking yayi agefen titi.
"Fita!"
yace da ita cikin wata irin murya.
Tsaida kukanta tayi cak, haɗe da ƙura masa ido.
"Kifitarmin amota nace!!" yanzu kam atsawace yayi maganar.
Jikinta na rawa tasoma kiciniyar buɗe murfin motar. Yanajin fitanta yayi reverse haɗe da cilla motarsa kan titi, bayan ya buleta da ƙura yabar wajen.
Tana ganin ɓacewar motarsa ta saki wani irin kuka haɗe da durƙushewa a wajen, kuka take mai cike da tsananin tausayin kanta, kuka take nakasancewarta marar gata, kuka take nakasancewarta ƴa mace marar galihu... Sama da mintuna 14 ta kwashe tana durƙushe a wajen, jifa jifa motoci ke wuceta.
Wata haɗaɗɗiyar motace ta tsaya adai dai gabanta, da sauri taɗago atunaninta shine yakuma dawowa, wani saurayi tagani ya sauƙe glass ɗin motar sa, haɗe da sakar mata murmushi.
"Ƴan mata mai yasameki haka kike kuka?" yatambayeta yana mai ƙarewa ƙirjinta kallo.
Sunkuyar dakanta ƙasa tayi batare da ta tanka masa ba.
Ganin bata kulasa bane yasashi fitowa daga cikin motar, batasan cewa yafito daga motarba sai ganinshi kawai tayi agabanta, har numfashinsu na dukan na juna. Da sauri ta matsa baya tana mai rau rau da idanunta. Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake matsota, kallonta yake kamar tsohon maye.
"Wai tsorona kikeji ne? haba karki bani kunya mana, zo muje nakaiki masauƙina kiyi wanka kinji!" yanayin yanda yayi maganar saida yasa tsikar jikinta ya zuba. Da sauri tashiga girgiza masa kai tana mai sake ja da baya, shikuwa sai ƙara matsota yake, hanunta ya cafke haɗe da yunƙurin jawota jikinsa, tureshi tasomayi yayinda ruwan hawaye keta ambaliya akan fuskarta.
"Ka...ƙyale..ni" tafaɗi haka cikin rarrabewar murya cike kuma da tsoro. Idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da sanya harshensa ya lashi laɓɓansa, cike da iskanci yace.
"Haba Babe karkimin haka mana, nafa kamu, please ko 30 minute ne kiban, muje mota please!" yanzukam kuka mai sauti tasanya haɗe da soma turjewa, hanunsa yakai zai taɓa kafaɗanta, yaji anyiwa hanunnasa wani irin riƙo, da sauri yajuya don ganin wanda yayi masa katsalandan. Ido huɗu sukayi, take saurayinnan yaji gabansa yayi wani irin faɗuwa, bakomai ya tsoratashi ba kamar ganin ƙwayar idanun SOORAJ. da gudu Ziyada tayi bayan SOORAJ ta ɓuya haɗe da sakin wani marayan kuka. Irin kallon da SOORAJ keyiwa matashin saurayinne yasashi sulalewa yashige motarsa da gudun gaske yabar wajen.
Aƙalla sun kusan mintuna 9 ahaka yana tsaye ya rumtse jajayen idanuwansa, yayinda ita kuma ke tsaye abayansa ta saƙala hannayenta akan cikinsa, fuskarta ta ɗaura akan bayansa tana kuka.
Hanunsa yasa ya zare hanunta daga kan cikinsa, baice ƙalaba, yakama hanunta suka nufi wajen da motarsa ke fake. gidan baya ya buɗe ya sanyata aciki, kana yaja motar suka ɗauki hanyar komawa cikin gari.
Tunda suka shiga cikin motar ta kifa kanta acikin cinyoyinta taketa faman rera kukan maraici. Shikuwa ko ƙala baice mata ba har ya iso gaban wani tafkeken mall. Fita yayi daga cikin motar yashiga cikin mall ɗin. Aƙalla ya ɗauki kusan sama da 20 minute acikin mall ɗin, fitowa yayi, yayinda wani yaro ke binsa abaya hannayensa riƙe da ledodi, inda Ziyada ke zaune SOORAJ ya buɗe masa yaron ya zuba ledodin aciki. Shiga motar yayi suka sake ɗaukan hanya.
Horn biyu kacal yayi maigadi ya wangale masa gate, a parking space yayi parking motar.
"Biyoni"
yace da ita ataƙaice batare da ko kallonta yayi ba, babu musu tafito daga cikin motar, dai dai lokacin Tanimu maigadi ya iso wajen.
"A kwai kaya acikin mota kashigomin dasu ciki!" SOORAJ yafaɗi haka ga maigadi, kana yasa kai ya wuce ɓangarensa Ziyada na biye dashi.
Harsuka ɓace Tanimu maigadi baidaina kallonsuba, tsantsar gulmane ke cinsa, a iya tsawon rayuwar da sukayi da SOORAJ baitaɓa ganin SOORAJ yashigo da wata mace cikin gidanba, ko auren da yakeyi ma kawo masa matan ake, amma yau abun mamaki gashi da wata ƴar ƙaramar yarinya, ganin cewar gulma bazata kai mishi bane yasashi kwashe kayan ya bi bayansu SOORAJ ɗin.
Suna shiga cikin falon SOORAJ ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa, ɓalle murfin goran yayi, haɗe da kai bakin goran kan nasa bakin, baicire bakin goran daga kan nasa bakinba har sai da yashanye ruwan cikin goran tas, a durstbin ya jefa roban ruwan haɗe da dawowa tsakiyar falon ya zauna akan kujera. Dai dai lokacin Tanimu maigadi yashigo, aje ledodin dake hanunsa yayi kana yafice daga cikin falon sumu sumu.
"Zo!" yace da Ziyada dake tsaye tana ta aikin murza ƴan yatsun hanunta.
Kanta aƙasa tatako harzuwa inda yake, durƙusawa tayi agabansa haɗe da cewa "Gani"
"Kinci abinci?" yatambayeta ataƙaice.
Kanta ta girgiza masa alaman "A'a"
"Tashi ki ɗaukomin ledan da aka kawo miki ɗazu" yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ya kalleta ba.
Babu musu taje ta ɗauko masa ledan, dama ledan tananan abakin ƙofa kamar yanda peter ya ajiye tun farko.
Har ƙasa ta durƙusa haɗe da miƙa masa ledan.
"Zauna kici !" yafaɗa ataƙaice tare da tashi yanufi hanyar ɗakinsa.
Zama tayi akan carpet tare da buɗe ledan take away ɗaya ta ciro haɗe da buɗewa. Soyayyen chips ne da ketchup sai kifi, ahankali take tsakuran abincin tanaci.
Koda yashiga cikin ɗakin zama yayi abakin gado haɗe da sanya duka hannayensa ya dafa kansa. Maganganun mahaifinsa da yayi masa ɗazune ke dawowa cikin kansa filla filla, Damuwa da rashin gamsashshiyar nutsuwa sune abun dake damunsa ako da yaushe, haƙiƙa Allah bai tauye masa komaiba nadaga arziki da abubuwan jin daɗi, saidai kuma atawani ɓangaren yana da babban rauni, akullum da tunanin ciwon dake damunsa yake kwana yake kuma tashi, tunanin zuwa gida wajen Ummu ne yaji ya ɗarsu acikin ransa, tashi yayi yashige bathroom, yana tsaye agaban shower ruwa na dukansa amma tunanin yanda zaiyi da rayuwar Ziyada ne yacika zuciyarsa, a yanda ya fahimta shine bata da wani gata, kuma tabbas akwai tawaya acikin rayuwarta, ya fahimci cewa kamar yanda yake cikin ƙunci haka itama take cikin ƙunci, saidai kuma damuwarsu sun banbanta, duk da baisan menene damuwarta ba, amma tabbas yasani matsalarta mai sauƙine akan nasa.
SOORAJ sarkin ado yanzuma sanye yake da riga da wando farare ƙal ƙal sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake.
Aƙalla yaɗauki sama da 10 minute yana tsaye abakin ƙofar ɗakin, duka idanuwansa ya kafa mata, komai nata acikin sanyi take yinshi tundaga kan yanda take tsakalan chips ɗin harzuwa yanda take taunasa acikin bakinta. Murmushin gefen baki yayi haɗe da girgiza kansa. Ahankali yashiga takawa harzuwa tsakiyan