Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   21 / 47

60K to 63K   out of 140.6K words

iya jurewa ba, sosai mararta ke murɗawa, gawani sabon ciwon ciki me tsananin azaba da takeji,  ganin irin yanda take kuka yasa Nasma da Shukra kamata suka fice daga cikin masallacin, aƙasan wata bishiya suka zauna su dukansu, cike da kulawa haɗi da damuwa Nasmah ta dubi Shukhra wacce idanunta sukayi raurau alaman itama kuka takesonyi. "Ki kula da ita Shukhra banaje na faɗawa discipline master, nasan zai faɗawa principal!"   kae kawai Shukhra ta iya kaɗa mata alamar taji, saboda itama zuciyarta cike take da rauni haɗi da tausayin halin da Zieyaderh ke ciki, don zuwa yanzu numfashinta har seizing yake kamar zai ɗauke,

Sauri Nasmah keyi don taga ta isa office ɗin discipline master, kamar daga sama taji anƙira sunanta.

Tana juyawa tayi tozali da Pharouk, da sauri taƙaraso gareshi, kallonta yayi daga sama har ƙasa, ganinta aɗan hargitse yasanyashi cewa.
"Lafiya kuwa naganki ahaka? Sannan kuma ina kuka shige tun ɗazun naketa nemanku?"

"Zieyaderh ce batada lafiya sosai, yanzuma office ɗin discipline master zanje!"

Sexy eyes ɗinsa yaɗan waro tare da cewa. "Tana ina? Meke damunta? Muje kinunamin inda take!"

Babu musu Nasmah ta juya shikuwa yabi bayanta..  Lokacin dayaga Zieyaderh na kuka baƙaramin tashi hankalinsa yayi ba.  Shida kansa ya je office ɗin principal yasanar dashi cewa zai wuce da Zieyaderh asibiti,  su Nasmah ne suka sata acikin motarsa sannan suma suka shiga, zuwa lokacin gaba ɗaya hankalinta yasoma gushewa.  Da wani irin speed Pharouk kejan motar.   A babban haraban asibitin yayi parking, zuwa lokacin bata da ƙarfin da zata iya ko da taka ƙafarta ne,  batare da tunanin komai ba Pharouk ya sanya hannayensa duka biyu ya ɗagota zuwa jikinsa, tamkar ƴar baby haka ya ɗauketa yayi cikin asibitin da ita, duk dacewa baya cikin ishashshiyar nutsuwa amma duk da haka daya ɗagata saida yaji wani shock ajikinsa.   Emergency aka wuce da ita, take aka shiga bata kulawa.

Nasma da Shukhra gaba ɗaya basa cikin nutsuwarsu,   ganin haka yasanyashi lallaɓasu tare dace musu su koma makaranta shi zai kula da ita, babu yanda suka iya dole haka suka hau taxi suka koma makaranta, saidai kuma gaba ɗaya hankalinsu naga Zieyaderh har acikin ransu basason wani abu na cutarwa ya sameta.

Zama yayi akan wasu kujeru tare da sanya tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa, numfashi yake fitarwa ahankali, wani irin feeling yakeji ajikinsa, daga wata ɓangare na zuciyarsa kuwa tunanin halin da take ciki yake,   yana awannan yanayinne aka fito da ita daga emergency room ɗin, kwance take flat akan wani gado me ƙafafun taya,  kaitsaye ɗakin hutu aka wuce da ita.    Likitan da case ɗin ke hanunsa ne yace da Pharouk ya biyosa office.

Zama Pharouk yayi akan kujeran dake fuskantar na Doctor, cikin damuwa yace. "Yajikinnata?"

"Kada ka damu jikinta da sauƙi dama bawani babban ciwo bane, nace dama tana irin wannan ciwonne aduk sanda zatayi period ko kuma yanzune abun ya soma?" Doctor ya tambaya yana me ɗan rubuce rubuce ajikin wata fafar takarda.

Shiru Pharouk yayi cike da ɗaurewan kai, kwata kwata shi bai fahimci me Doctor'n yake nufi ba.

Ganin haka yasa Doctor ɗin gyara zama tare da duban Pharouk. 

"Munyi mata alluran bacci, tana buƙatar hutu sosai, menstrual pain ne insha Allah idan tafarka zataji sauƙi,  saidai irin wannan ciwon baicika warkewa ba harsai mace tayi aure, wasu kuma yakan daina idan sun haihu, wasu kuma ko basuyi aure ba idan suka dace da magani yana iya dainawa, so amma nata yanada tsanani sosai gaskiya, yakamata akula, sannan tarage yawan shan zaƙi, saboda shima yana ƙara ciwon sosai,  ga wannan magunguna ne da zaka nemo saboda idan tafarka tasha" Dr Ya faɗi haka yana me miƙawa Pharouk wata ƴar farar takarda.
Karɓan takardan Pharouk yayi tare da yiwa Doctor'n godiya.

Koda yafito daga office ɗin Dr direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa,   ahankali yaƙarasa gaban gadon da take kwance, gaba ɗaya gashin kanta ya watse akan pillow, yayinda kyakkyawar fuskarta tayi fayau, bakinta kuwa har ɗan bushewa yayi saboda wahalan da tasha,  numfashi take fitarwa ahankali, kallon kyakkyawar fuskarta yayi tare da sanya hanu yashafi lallausan gashin kanta,   wani irin tausayi da soyayyarta ne suka sake dirarwa zuciyarsa,   kallonta ya shigayi sosai, yaune karo na farko daya fara ganinta babu hijab,  ashe duk iya tunaninsa da yanda yake fasalta kyawunta azuciarsa tama wuce haka, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta, wanda har ana iya hango saman breast dinta, domin wuyan rigan yaɗanyi mata yawa kaɗan. Lumshe idanunsa yayi tare da jan numfashi mai tsawo, hanunsa ya zare daga cikin hair ɗinta tare da ɗan matsawa baya, wani irin abu yakeji ajikinsa na musamman agame da ita, kawar da kallonsa yayi daga gareta, domin kuwa idan ya yarjewa zuciyarsa yaci gaba da kallonta, to tabbas zai iya losing control ɗinsa. Jiki asanyaye yajuya yafita daga cikin ɗakin, azuciyarsa kuwa tattauna maganganun da Dr ya faɗa masa yakeyi. Aƙaton pharmacy'n dake gefen asibitin ya saya magungunan, motarsa ya shiga tare dayi mata key, inda ake saida fruits yanufa, duk wani kayan fruit saida ya saya sannan kai tsaye yadawo asibitin.

Har zuwa wannan lokacin bata farka ba, zama yayi akusa da ita tare da zaro wayarsa daga cikin aljihunsa ya soma dannawa.

Jin kamar tana ƙoƙarin motsawa yasashi tashi da sauri yaƙaraso inda take, hanunsa yakai ya taɓa goshinta. Daidai lokacin aka turo ƙofar ɗakin, waiwayawa yayi don atunaninsa likitane sai kuma yaga saɓanin tunaninsa, wani kyakkyawan farin gaye idanunsa suka gane masa, wanda yake sanye da maroon suit me tsananin kyau da tsada, kallo ɗaya kayi masa zakasan ko wanene shi, matashin saurayi, maiji da kuɗi, ilimi, wayewa,ƙasaita, jinkai, da kuma miskilanci, domin ko alaman annuri babu akan kyakkyawar fuskarsa, hannaye Pharouk yasanya acikin aljihun wandonsa tare da kafe wanda ke shigowa cikin ɗakin da ido. Yanayin takunsa kaɗai ya isa sanar dakai cewa shiɗin wanine, baigama shigowa cikin ɗakin ba, Doctor ya biyo bayansa.

"Tafarka ne?"
Dr Ya tambayi Pharouk yana me ƙoƙarin ƙarasawa gaban gadon.

"A'a" Pharouk yabasa amsa ataƙaice yana me kallon mutumin da shigowarsa ya tsaya masa amaƙoshi.

Babu wanda ya saurara acikinsu ya ƙarasa gaban gadon, kallon fuskarta yayi tare da dawo da kallonsa ga ƙirjinta, rumtse idanunsa yayi tare da cije lips ɗinsa, lokaci guda yaji wani irin ɗaci amaƙoshinsa, hijab ɗinta dake gefe da ita ya ɗauka, hannayensa ya sanya ya tallafota tare da sanya mata hijabin, ransa na ƙuna haka yajawo hijab ɗin ya rufe mata ƙirjinta dake buɗe, lokaci guda idanunsa suka sauya kala daga farare zuwa jajaye. Juyowa yayi ya kalli Dr cikin lion voice ɗinsa yace "Inason kayi discharge ɗinta yanzu"

"Babu damuwa ae dama ba wani babban ciwo bane" Cewar Dr

Cikin rashin fahimta Pharouk yace.
"Saboda me za a sallameta bayan bataji sauƙi ba?" yanayin yanda yayi maganan daɗan zafi yasanya, Dr sakin murmushi nuna masa SOORAJ dake tsaye ya haɗe fuska, yayi tare da cewa "Yayanta ne inaga yafiso subata kulawa agida ne"

Dummmm haka Pharouk yaji ƙirjinsa ya buga, atare suka kalli juna shida Sooraj, wani irin kallo sukawa junansu mai ɗauke da tarin ma'anoni. Wani killer smile Pharouk yayi tare da miƙawa Sooraj hanunsa cikin wata murya me amo yace "Am Pharouk" Wani kallo Sooraj yayiwa Pharouk, daga ƙasa har samansa sannan yaɗan taɓe baki shima ya miƙa masa hannu suka gaisa, saidai da sauri Sooraj ya zare hanunsa daga cikin na Pharouk tare da kawar da kansa gefe, Murmushi Pharouk yayi tare da ƙarasawa gaban gadon, hannunsa yakai daniyar taɓa fuskarta, kafun hannunsa ya gama sauƙa akan fuskarta tuni Sooraj yayi masa wani irin riƙo wanda ya sanya Pharouk ɗagowa da sauri ya kallesa, ido cikin ido haka suke kallon juna, kai Sooraj ya girgiza masa, sannan ya ɗauke idanunsa daga kansa, kallo Dr da yazama kamar wani statue agarin kallonsu yayi yace.

"Thank you Doctor"

Hannayensa duka biyu ya sanya ya ɗago Zieyaderh dake bacci, akafaɗansa ya ɗaurata tamkar ƙaraman yarinya ƴar shekara 3, ko kallon inda Pharouk yake baiyiba yafice daga cikin ɗakin.

Bin bayansa Pharouk yayi da kallo tare da sakin murmushi. Azuciyarsa yace.
"SOORAJ!!! Yanzu aka soma wasan."


*Da Vote ɗinku kaɗai nake gane kunason labarinnan, ina godiya sosai masumin vote da comment Son So nake muku❤*

*Vote*
*Comment and share*


*fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
      @fatymasardauna

https://my.w.tt/7FVfmex8a7


*Chapter 31*

Yana fita daga cikin ɗakin direct hanyar dazai sadashi da compound ɗin asibitin ya nufa, baidamu da kallon da jama'a keyi masa ba.  Yana isowa jikin motarsa ya buɗe gidan baya tare da kwantar da ita akan kujera, yana shiga yaja motar da wani irin speed yabar cikin asibitin, ransa amatuƙar ɓace yake wanda baisan dalili ba, hakanan yakejin wani ɗaci amaƙoshinsa.  Yanayin yanda yake sharara gudu akan titi yasanyasa isowa gida cikin ɗan ƙanƙanin lokaci,  ko jira agama buɗe masa gate ɗin gidan  baiyiba ya tura hancin motar ciki.

Yana gama daidaita parking ya fito tare da buɗe gidan baya ya ɗauko ta,  still akan shoulder ɗinsa yasake ɗaurata, wata hanya daban naga ya nufa ba wacce zata satadashi da babban falon dake cikin gidan ba,    ajikin wata ƙofa naga ya tsaya tare da sanya key ya buɗe, ahankali yatura kofar ya shiga,  wani ɗan corridor ne wanda gefe dashi wani haɗaɗɗen swimming pool ne wanda aka ƙawatasa, ruwan ciki gwanin ban sha'awa, sai kuma wasu ƴan tsirarun shukokin flowers da suka ƙara ƙawata kyawun wajen,   wata ƙofar yasake buɗewa, wanda ya sadashi da ɗakin baccinsa, kasancewar bayan ƙofar shiga ɗakinsa wanda ke cikin babban falon gidan, akwai wata ƙofa ma wacce take ta bayan compound ɗin gidan.   Ƙofar ya mayar ya rufe tare da murza mata key, ƙarasawa gaban makeken gadonsa yayi tare da birkito da ita ta dawo kan hannuwansa,  cike da tsananin muguntan dake ransa yasaketa tafaɗa kan gadon da ƙarfi, atake ta saki wani ƙara tare da sakin wani marayan kuka, hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa, tare da  tsayawa ƙyam yana kallonta, sam fuskarsa ko alaman wasa babu.
Agalabaice ta sanya hannayenta ta riƙe weast ɗinta dake ciwo kaman zai ɓalle, sam batama gama sanin awacce duniya take ba, kasancewar  alluran baccin da akayi mata baigama saketa ba, azaban sakinta da ƙarfi da yayi akan gado ne  yasanyata farkawa,    ahankali idanunta suka ɗan soma washewa saidai duk da haka bata gani sosai, idanuntane suka sauƙa akan fuskarsa, adaburce taja jikinta baya, duk da cewa bata gama dawowa hayyacinta ba, amma hakan bai hanata tsorata data gansa ba,  kukan da takeyi ta tsayar, tare da sanya white teeth ɗinta ta datse lips ɗinta, alaman wani waje nata nayi mata zafi.

Sooraj dake tsaye ya harɗe hannuwa ganin yanda take ciccije baki, yasanya cikin husky voice ɗinsa yace da ita "Tashi!"  

Da sauri tasoma yunƙurin sauƙa daga kan gadon, tana aje ƙafafunta aƙasa, wani irin jiri ya ɗebeta tare da ƙoƙarin kada ita, da sauri tasanya hannayenta duka biyu ta dafe bango, siririn kuka tasaki marar sauti, don masifar tsoronsa takeji,   kallon jikinta yayi sannan ya kalli white bedsheet ɗin dake shimfuɗe kan bed ɗinsa, idanunsa yaɗan zaro tare dasanya hannu ya dafe goshinsa, aɗan harzuƙe yace.
"Bakida hankali ko? Ɗauka maza kije toilet kiwanke minshi yanzunnan, sannan kuma ki tabbatar da cewa yafita!!" yafaɗi maganar agadarance yana meyi mata nuni da bedsheet ɗin. Dubanta takai kan gadon, nan taga jini yaɗan ɓata tsakiyan bedsheet ɗin, wani irin faɗuwa gabanta yayi take taji wani masifaffen kunya ya rufeta. Kanta aƙasa ta sanya hannu tashiga jan bedsheet ɗin, duk da cewa dishi dishi idanunta suke gani sannan kuma babu wani ƙarfi ajikinta, hakan yasa komai takeyinshi cikin sanyi, ɗaukan bedsheet ɗin tayi tare da nufar wata ƙofa ta daban atunaninta nanne toilet, daga yanayin tafiyarta kaɗai ya isa sanar dakai cewa bata cikin hayyacinta, don har yanzu pain ɗin bai saketa ba.

Hannunsa yasanya ya damƙo ta, yanayin irin riƙon daya mata ba na wasaba ne, don har saida wani ƙashi dake cikin hannunta yayi ƙara, ƙafarsa yasanya ya daki ƙofar toilet ɗin, take ƙofar ta wangale, hankaɗata cikin toilet ɗin yayi tare da jawo ƙofar ya rufe.   Zama yayi akan wata kujera tare da ɗaukan laptop ɗinsa yashiga dannawa, gaba ɗaya wani irin takaicinta yakeji.

Itakuwa Zieyaderh rasa inda zata sanya bedsheet ɗin tayi, wani irin bacci tare da jiri ne ke fusganta har bata iya ganin gabanta sosai, wani bucket ta ɗauka tare da sanya bedsheet ɗin aciki, ruwa ta zuba acikin bucket ɗin sannan tajefa sabulu,  tsugunnawa tayi ta zubawa bucket ɗin ido, tama rasa ta ina zata fara, ganin tsayuwan ya isheta yasanya ta zauna daɓas aƙasan tiles tare da jingina bayanta da jikin bango, 5 minute kacal bacci ya ɗauketa awajen.

30 minute ya ɗauka azaune yana daddana laptop ɗinsa, kwata kwata shi yama manta da ita,  ƙiran sallan magriba da akasomayi ne yasanyashi rufe laptop ɗin tare da miƙewa tsaye.  Ahankali ya tura ƙofar toilet ɗin yashiga bakinsa ɗauke da addu'a.   Hannayen rigarsa yasoma naɗewa tare da ƙarasawa gaban sink. Alwala yayi yana cikin wanke ƙafarsa na hagu idanunsa suka sauƙa akanta, saida yaji wani irin faɗuwar gaba domin shi sam yama manta da ita,  cike da mamakin yanda tabaje tana sharar baccinta yashiga ƙare mata kallo, ga bucket agabanta sannan kuma ga bedsheet da sabulun wankansa nan acikin bucket ɗin, sabulun ya narke saboda yasha ruwa,  itakuwa baccinta take tana sauƙe ajiyar zuciya. hankalinta akwance.  

Ƙafansa yaɗan sanya ya zungureta, ko motsi batayi ba,  wani murmushin da iyakansa leɓen baki yayi,  gaban babban bathtube ɗin wankansa ya ƙarasa, ruwan sanyi ya tara har saida yacika bathtube ɗin,  ƙarasowa gabanta yayi tare da ɗan durƙusawa ya ɗauketa,   kamar wata ƴar tsana haka ya jefata acikin bathtube ɗin,  aruɗe ta buɗe idanunta da sukayi luhu luhu sannan sukayi ja,  wani irin sanyine ke ratsata.  Juyawa yayi cikin halin ko inkula yafice daga cikin toilet ɗin, cikin daurayi ta fito daga cikin bathtube ɗin, gaba ɗaya kayan jikinta sun jiƙe jaƙab,   ahankali take taka ƙafafunta da takejinsu kamar bazasu iya ɗaukanta ba.   Bazata iya jurewa azabobin dayake gana mata ba, ganin bakowa acikin ɗakin yasanya tanufi hanyar fita, saɗaf saɗaf take tafiya kamar munafuka,   ƙofar corridor ɗin ta buɗe ahankali, kanta tasako taɗan leƙa babban falon, kamar dai koda yaushe babu kowa acikin falon, da sauri ta fito ko tsaya rufe masa ƙofar batayi ba, daɗan sassarfa ta soma haura step ɗin dazai sadata da ɗakinta,   tana tafiya tana waigen ƙofar ɗakin Ummu, kamar ɓarauniya haka ta buɗe ƙofar ɗakinnata ahankali tana shiga ta kulleshi gam,  jiƙaƙƙun kayannata tasoma cirewa, sannan ta wuce bathroom. Adaddafe ta haɗawa kanta ruwan ɗumi, tayi wanka, har yanzu pain ɗin bai gama saketa ba, saima wani sabon fever daya sauƙa ajikinta,  pad ta ɗauka ta kimtsa kanta sannan ta sanya wata doguwar riga me ɗan nauyi, domin kuwa sosai takejin sanyi, duk da cewa akwai yunwa sosai acikinta amma bata damu da  neman abinciba, kan gado ta hau tare da jan blanket ta rufe gaba ɗaya jikinta, jikinta sai rawan sanyi yake, haka ta lumshe gajiyayyun idanunta da suketa ambaliya wajen fitar da hawaye.

Ganin har ƙarfe 7 Ummu bataji motsinta ba gashi yau bataga dawowanta ba yasanya hankalinta yaɗan tashi,  saboda haka tafito don dubata.

Ahankali Ummu tatura kofar ɗakin tashigo bakinta ɗauke da sallama,  ganin Zieyaderh nannaɗe acikin bargo yasanya Ummu ƙarasawa wajenta da sauri cike da kulawa tace.

"Zieyaderh lafiya kike kuwa?"

Zieyaderh da duk jikinta ke rawan sanyi, ta girgiza kanta cikin ciwo tace.
"Ummu zazzaɓine ke damuna!"

"Subahanallah shine kuma bakizo kin faɗamin ba? ba'a zama da ciwo ae, sam hakan ba kyau,  kin maci abinci kuwa?" Ummu ta tambaya.

Kai Zieyaderh ta girgiza alaman.       
  "A'a"

Juyawa Ummu tayi tafice daga cikin ɗakin. 

Mintuna kaɗan saiga  Ummu ta dawo hannunta ɗauke da plate da kuma cup ɗin tea, kan bedside drawer ta aje plate da cup ɗin, bargon da zieyaderh ke lulluɓe dashi Ummu taɗan yaye tare da miƙar da ita zaune, cup ɗin  tea ɗin Ummu ta bata, babu musu ta amsa,  ahankali takeshan tea ɗin,  sai da tasha kusan rabin cup ɗin, kafun Ummu ta amshi cup ɗin, plate ɗin soyayyen dankali da ƙwai wanda yaji sauce Ummu ta miƙo mata, nanma bata musaba ta amsa, ahankali takecin abincin duk batajin wani daɗin bakinta.   Pain reliever Ummu ta bata tasha,  sannan tace da ita ta kwanta tayi bacci,  luf tayi akan gado tana maida numfashi ahankali, cikin wasu mintuna ƙalilan bacci ɓarawo yayi gaba da'ita.  

Tunda Yafita sallan Magriba bashi yadawo gidanba sai 9 pm,  direct toilet ɗinsa ya wuce, wanka yayi yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi, sama sama yashafa body lotion,  white trouser yasanya, tare da feshe jikinsa da turare me daɗin ƙamshi,  Luf yayi akan gadonsa tare da cusa kansa cikin pillow, sanyin AC ne ke ratsa naked skin ɗinsa, ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya, ƙoƙarin faɗa da tunaninsa yake, sam bayason wani abu yasake damunsa,  a ƴan kwanakinnan yana yawan jin zuciyarsa nayi masa zafi, sam bayason ciwonsa yayi ƙarfin da harsai kowa ya gane yana ɗauke da ciwon zuciya, akullum yanaji ajikinsa bashi da wani sauran farinciki daya ragemai,   numfashi ya fitar ta bakinsa tare da lumshe idanunsa,  duk yanda zuciyarsa taso da yayi tunani yaƙi bata daman hakan, yajima sosai kafun yasamu bacci ya ɗaukesa.

Washegari.

7:00 am daidai yagama shirya kansa cikin navy blue suit,  Sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake,   waya da key ɗin motarsa ne riƙe ahanunsa,  cikin nutsuwa yake takunsa har yakai bakin ƙofar da zai fitar dashi daga cikin falon. Muryar Ummu da yaji abayansa yasanyashi tsayawa, juyowa yayi cikin ɗan rusunawa yace.
"Good morning Maaa" 

Murmushin daya bayyana tsananin kamanninsu dashi Ummu tayi tare da cewa
    

21 / 47