Author : Maman Teddy Category : Adventure
"Morning how are you?"
"Am fine!" ya amsa ataƙaice yana me gyara wrist watch ɗinsa.
"Kasanar da Mas'oud Zieyaderh batajin daɗi, sannan yau bazata samu zuwa school ba ya kamata asanar" Ummu tayi maganar tana me ƙoƙarin zama akan kujera.
Kansa kawai ya jinjina alamar yaji kana yafice daga cikin falon.
Sosai tasha bacci sai 10 tafarka, Alhamdulillah ta ɗanji sauƙin jikinta, saidai kuma duk da haka bakinta babu daɗi, fitowarta daga wanka kenan, wani riga da sket ƴan kanti tasanya, sket ɗin irin rubber pencil ɗinnan ne yayinda rigan takasance me buɗaɗɗen kafaɗa, sosai kayan sukayi mata kyau ajiki, rubber hijab tasanya ajikinta, sannan tanufi ƙasa, ahankali take saƙƙowa daga kan steps ɗin, Ummu ce zaune afalon tasha ado cikin wani tsadadden lace maroon colour wanda yayi matuƙar amsar jikinta, gefe da ita wata matace wacce bazata wuce shekarun Ummun ba itama zaune ta caɓa ado, dagani basai anfaɗa ba kasan naira yazauna musu su dukansu. Cikin ladabi taƙaraso tare da durƙusawa ta gaidasu, fuska ɗauke da murmushi Ummu ta shafa kan Zieyaderh'n tare da cewa
"Kintashi? har baccin ya isa kenan, to ga can break fast akan dinning"
Murmushi Zieyaderh tayi tare da miƙewa tsaye tanufi dinning area. Hajiya Munah dake zaune tabi Zieyaderh da kallo, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da duban Ummu cikin yanayi naɗan mamaki tace.
"Hajiya Sulaimiyya ina kikasamo wannan kyakkyawar yarinyar kodai daga ƙasarku take ne?"
Murmushi Ummu tayi tare da cewa. "Ƙanwar Mas'oud ne abokin Sooraj, ai kindai san Mas'oud?"
Murmushi Hajiya Munah tayi tare da cewa "Ayya gaskiya balaifi yarinyar akwai hankali, uwa uba gata da kyau masha Allah!"
"Wannan halayyan nata shiyasa nakeson haɗata aure da Almustapha, nasan bazaiyi takaicin samunta amatsayin mata ba" Cewar Ummu wacce ke sipping pineapple juice ahankali.
Murmushi Hajiya Munah tayi tare dacewa "Gaskiya kinyi tunani me kyau, amma ae zai fi kyau ki haɗata da Sooraj, don aganina yafi Almustapha buƙatar mace akusa dashi"
Aje glass cup ɗin hanunta Ummu tayi tare da duban Hajiya Munah, wani murmushi me ciwo Ummu tayi cikin wani irin yanayi tace "Saikace bakisan waye Sooraj ba Hajiya Munah? hmmm Sooraj ɗin da baibzauna da matan da suka amsa sunansu mata ba ma, mene zaiyi da ƴar wannan ta tsitsiyar yarinyar da duka duka shekarunta basu wuce 18 to 19 ba"
Ajiyar zuciya Hajiya Munah ta sauƙe tare da cewa "Allah ya kyauta"
Da "Ameen" Ummu ta amsa daganan suka ci gaba da hiransu.
Zieyaderh kuwa zama tayi akan dinning tare da zubawa kanta pepper chicken soup, and chips, ahankali take tsakalan abincin don gaba ɗaya bawani daɗinsa takeji ba. Koda ta kammala ɗakinta takoma magungunanta tasha kana ta kwanta, tashar Mbc Action take kalla da haka har bacci ya ɗauketa.
Dayake magungunan da tasha suna da ƙarfi sosai hakan yasa ba ita ta tashiba sai wajen 5 na yamma, wanka tayi tare da sanya wata blue gown marar nauyi, yunwa takeji sosai hakan yasa tashiga ƙoƙarin zura hijab ɗinta don sauƙa ƙasa, jin anturo ƙofar ɗakinne yasanyata waigawa da sauri, ido biyu sukayi da Ummu wacce fuskarta ke ɗauke da murmushi.
"Barka da yammaci Ummu" tafaɗa murya asanyaye.
"Yauwa, dama wai me gadine yanzun yashigo yace wai wani yana sallama dake awaje, shine nace ko kunyi da wani zaizo wajenki ne?"
Idanu Zieyaderh ta zaro, lokaci guda ƙirjinta yashiga wani irin bugu, bakinta narawa tace "Ni....ni...kuma?"
"Eh haka dai yace, yanaga kin tsorata? Maza kije kiga ko wayene bakyau kabar mutum yana jira!" Ummu nagama faɗan haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin.
Tsorone ya kama Zieyaderh adaburce ta sanya hijab dinta,kana ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice. Bataga Ummu afaloba kai tsaye saita nufi hanyar waje.
Koda tafito compound ɗin gidan idanunta tashiga warewa ko zata hango wanda akace na nemanta.
Tun fitowarta daga cikin falon yake kallonta, sosai tayi masa kyau acikin hijab ɗin dake jikinta, ashe sosai uniform ke ɓoye kyawunta. Kamar wanda akace tawaiga bayanta, hangosa tayi tsaye ajikin black car ɗinsa mercedes benz, sanye yake da riga da wando na bugaggiyar shadda Blue colour wanda tayi matuƙar yi masa kyau, mamakin ganinsane kwance acikin ranta amma saita sunkuyar da kanta ƙasa tare da nufar inda yake, murmushine kwance akan fuskarsa yana me kallonta harta ƙaraso. Cikin siririyar muryarta tayi masa sallama. Bai amsa sallamannata ba saima tsayawa kallonta da yayi, jin shiru bai amsa mata ba yasanya ta ɗago kanta ta dubeshi, idanunsune suka sarƙe cikin na juna, yanayin kallon daya mata yasanya ta sauƙar da idanunta ƙasa da sauri tana murmushi. Kansa yaɗan sunkuyo yana leƙa fuskarta, ganin haka yasa tasanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta da sauri.
"Jiya nakasa bacci saboda bansan wani hali kike ciki ba, amma ganinki danayi yanzu yasa naji sanyi araina, basai ma kin faɗa ba nagane kinji sauƙi" Yafaɗi haka cike da tsantsar nuna kulawarsa gareta.
Har acikin ranta taji daɗin maganganunsa, domin tanada buƙatar kulawa sosae.
Ɗan matsowa kusa da ita yayi hartana iya jiyo sassanyan ƙamshin dake fita ajikinsa. Hannayensa yakai ya zame hannunta dake kan fuskarta.
Cikin wata irin sweetness voice yace "Kullum ƙara kyau kike, komai naki me kyaune, zanso kasancewa dake akoda yaushe sannan akowacce rana, please faɗamin kina sona?" yaƙare maganar yana me juya idanunsa akan kyakkyawar fuskarta.
Lumshe kyawawan idanunta tayi sosae zuciyarta ke bugawa, batasan me zatace masa ba, sannan kalamansa sunyi mata nauyi sosai, shikaɗai ya lura da mota ƙiran black range rover dake shigowa cikin gidan, kasancewar ita tabawa ƙofar gate baya, sannan gaba ɗaya tunaninta yatafi izuwa wani wajen daban. Ahankali taɗan buɗe idanunta tasaci kallonsa, abun da bata saniba shima kallonta yake sai kawai idanunsu ya sauƙa acikin na juna. Da sauri ta kawar da kanka gefe tare da sanya hijab ɗinta ta kare gefen fuskarta, idanunta ne suka sauƙa akan motar da ta shigo cikin gidan, wani irin masifaffen tsorone ya kamata take jikinta ya soma ɓari, lokaci guda jikinta yashiga fidda gumi, yana gama daidaita parking ɗin motar yafito, sanye yake da white t-shirt and combat army jeans, baƙaramin kyau yayi ba sosai kayan suka fitar da kwarjininsa. Cikin isa yake takunsa yana me dosowa cikin gida, saidai abun mamaki bai ɗago kai ya kallesu ba, bawai kuma don baigansuba tun shigowansa idanunsa sukayi masa tozali dasu, baya baya Zieyaderh keyi tana me ƙoƙarin ɓoyewa abayan Pharouk, tuni hawayen tsoronsa sun cika idanunta. Yayinda shikuma yake daɗa kusanto inda suke, fuskarsa sam babu alaman wasa ko murmushi akanta.
*Vote*
*Comment and share......*
9/June/2020
Fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 32*
Cikin nutsuwa yake takunsa, tuni Zieyaderh ta koma bayan Pharouk ta ɓoye, rumtse idanunta tayi ƙam cike da fargaba. Ƙamshin turarensa da yacika hancinta ne yasanya jikinta ya soma rawa, saboda tasan zuwa yanzu yana gab dasu. Sam bai kallesuba balle yasa aransa cewa da gaske mutanene awajen, kansa tsaye ya wuce.
Aƙalla taɗauki kusan 5 minute ahaka, idanunta a rufe suke, jin shiru bataji motsin kowa ba yasanya tasoma buɗe idanunta ahankali, da beuty face ɗinsa tasomayin arba yayinda ya kafeta da sexy eyes ɗinsa, waro idanunta waje tayi tare da ɗanja da baya tashiga waige waige.
Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi, tare da ɗan kashe mata idanunsa ɗaya.
"Tsoron me kikeyi haka? ba Brother ɗinki bane?"
Kanta ta sunkuyar ƙasa tare da sauƙe ajiyar zuciya, duk da bata ganshi awajenba amma amatuƙar tsorace take domin batasan wani hukunci bane zai biyo baya.
"Meyasa kikejin tsoronsa? Ya hanaki kula kowa ne? Waye shi awajenki? Please tell me karkimin ƙarya!" yafaɗi haka yana me gyara tsayuwarsa tare da kafeta da idanunsa....
Sallama ɗauke aƙasan maƙoshinsa yashiga cikin falon, kai tsaye ɗakinsa ya nufa.
"SOORAJ!" Ummu dake zaune acikin falon taƙira sunanshi.
Cak ya tsaya da tafiyan, ahankali ya ɗan juyo ya kalleta.
Fuskarta babu alaman wasa batare da ta kalleshi ba tace "Badai ka ɗauki maganganun da Abbanka yayi maka amatsayin wasa ba?"
Shiru yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, baijin zai iya furta wata kalma awannan lokacin.
Sanin halinsa yasanya Ummu cigaba da cewa. "Kashiga hankalinka Sooraj, yakamata ace kasan mekakeyi, sai yaushene zaka fuskanci cewa ka girma? sai yaushe ne zaka nemawa kanka mutumci da daraja tahanyar yin aure? Ashe kafiso koda yaushe muta faɗa muna nanatawa duk akanka kai kaɗai? Idan kasake mahaifinka yayi mummunan fushi dakai to wallahi ba zakaga da kyau ba, sannan kuma gobe Almustapha zai dawo ka tura mota a ɗaukosa!" Ummu tafaɗi maganganun fuskarta babu alaman wasa.
Kansa kawai ya jinjina alaman yaji, ko 1 second baiƙara ba ya juya ya shige ɗakinsa.
Da kallo Ummu tabisa, tarasa hali irin na sooraj wani kalan alfano gareshi, ita tahaifesa amma batasan a ina yasamo wannan miskilancin nasa ba, sam itakam ba haka take ba.
Yana shiga cikin ɗakin ya murzawa ƙofarsa key, kayan jikinsa ya shiga ragewa, towel ya ɗaura ya shige bathroom, ruwa ya sakarwa kansa tare da sanya hannunsa na dama ya dafe bango, lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗaga sama ruwa ya shiga dukan fuskarsa, saida numfashinsa yasoma barazanan ɗaukewa sannan ya sauƙar da kansa ƙasa, numfashi yashiga fitarwa akai akai, yana mejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.
Ƙanƙance idanunsa yayi tare da lumshesu alokaci guda. "Zieyaderh!!" yaƙira sunanta in a cool voice ɗinsa.
Kanta ta ɗago tare da ɗan satan kallonsa, cikin muryarta me sanyi tace. "Na'am!"
"Inasonki!" Yafaɗa asanyaye yana me karyar da kansa gefe.
Kanta tajinjina tare da ɗan sakin murmushi, ƴan siraran laɓɓanta dake motsawa ahankali ya kalla.
Da alama maganace abakinta amma tanajin nauyin furtawa.
"Bakiji daɗin zuwana ba ko?"
Kanta ta girgiza alaman "A'a"
"To meyasa ba kya farinciki? Natafi ko kin gaji da ganina?" Ya tambaya yana me zura hannayensa acikin aljihun wandonsa.
Kanta ta girgiza cikin wani irin yanayi na shagwaɓa tace
"A'a nifa bance haka ba!"
Idanunsa ya lumshe har cikin ransa yaji salon shagwaɓan nata ya taɓasa, cikin ƙasa da murya yace "to faɗamin"
Tafukan hannayenta tasanya ta rufe fuskarta tana dariya.
"Pleaseeee mana baby faɗamin kina sona?"
Kasa jurewa tayi da sauri tajuya cikin yanayi na ɗan gudu gudu sauri sauri ta nufi cikin gida, murmushi Pharouk yayi tare da binta da kallo, wani irin sanyi yakeji acikin ransa, duk da cewa bata furta masa da bakinta ba, amma tabbas yasan bataƙinsa, don baiga ƙiyayyarsa acikin ƙwayan idanunta ba, motarsa ya buɗe ya shiga tare dayi mata key, mai gadi ne ya wangale masa gate, haka yabar cikin gidan zuciyarsa da tunani kala kala, gaba ɗaya ayar tambayarsa ya ɗigata ne akan SOORAJ.
Da ɗan gudunta tashigo cikin falon, tana rufe ƙofar ta saki wata ajiyar zuciya tare da sanya hannu ta dafe ƙirjinta, ƙoƙarin daidaita nutsuwarta tayi sannan takalli ɓangaren Sooraj, jin gabanta ya faɗi yasanya ta haura sama tana shiga cikin ɗakinta tafaɗa kan gado tare da lumshe idanunta, wani iri takeji azuciyarta, batasan dalilin da yasa takejin Pharouk awani ɓangare na zuciyarta ba, saidai kuma ako da yaushe kalamansa daɗi suke mata.
Luf yayi akan gadon tare da sake cusa kansa cikin pillow, gaba ɗaya ya rasa inda zai tsoma kansa yaji daɗi, ba yason yakai gayin abun dazai dameshi daga baya hakan yasa ya jure duk wata damuwarsa, sosai yakejin rauni azuciyarsa, musamman dangane da matsalarsa,,, yajima yana saƙawa da kuncewa acikin zuciyarsa kafun daga bisani bacci ɓarawo ya sace sa.
Washegari.
Alhamdulillah yau taji daɗin jikinta sosai hakan yasa ta shirya kanta tsab cikin shigar uniform ɗinta, hakanan takejin sanyi azuciyarta, ahankali take saƙƙowa daga kan step ɗin. Ƙaran takun takalmanta yasanya shi ɗago da kansa, dai dai lokacin itama ta ɗago kanta, idanunsune ya sauƙa cikin na juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, shima kansa ya kawar tare da ci gaba da sipping coffee ɗinsa.
Sumu sumu haka taƙarasa sauƙowa daga kan steps ɗin, ahankali take tafiya harta ƙaraso inda yake, cikin wata irin murya me sanyi tace "Ina kwana!"
Bai amsata ba hakan yasa taɗan ɗago kanta ta kalleshi, ganin kamar baisan tana wajenba yasanya ta soma wasa da yatsun hannunta tana me murzasu, cikin yanayi naɗan shagwaɓa tace "Ina kwana Ya...yah?"
A yanzu kam ɗago kansa yayi ya kalleta saidai haryanzu bai amsa mata ba, jiki asanyaye ta gyara zaman school bag ɗinta sannan tanufi hanyar fita daga cikin falon.
Kamalu driver tasamu tsaye ajikin mota, da sauri ta ƙarasa tare da buɗe gidan baya ta zauna, tana ƙoƙarin aje school bag ɗinta, ya buɗe ƙofar motar ya shigo, ƙamshinsa take yacika ko ina dake cikin motar, mamakin shigowarsa cikin motar ne ɗauke akan fuskarta. School bag ɗinta ta rungume aƙirjinta tare da duƙunƙune jikinta waje ɗaya, tunda suka ɗauki titi yake ta faan latsa wayarsa, gaba ɗaya kwarjininsa ya cika mata ido, musamman yau da yasha ado cikin white and black suit, sai ya zamana yaƙara kyau. Aƙofar makarantar tasu Kamalu driver yayi parking motar, kamar marar gaskiya haka ta buɗe ƙofar motar tafice, ko taku uku batayiba taji ƙaran tashin motar, tana waiwayawa taga sunbar wajen, tana shiga cikin school ta haɗu dasu Nasmah, gaba ɗayansu hankalinsu atashe suke tambayarta yaya jikinta, sosai taji daɗin kulawarsu agareta da haka suka wuce class.
Ƙarfe Biyu daidai jirginsu ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin Abuja, wani kyakkyawan saurayi wanda aƙalla bazai haura 29 years ba, shike sauƙowa daga kan matattakalan jirgin Sanye yake da riga da wando na jeans masu kyaun gaske, kai tsaye baza'a ƙirasa da fari sol ba, sannan kuma shi ba baƙi bane, yana daɗan tsayi daidai misali sannan yana da faffaɗan jiki, daga yanayin shigarsa kaɗai zai sanar maka da ɗan gaye ne, fuskarsa ɗauke take da murmushi, Kamalu driver yana hangosa ya ƙarasa garesa da sauri cikin yanayi naɗan girmamawa yace "Ranka ya daɗe barka da zuwa"
Murmushi Alhmustapha yayi tare da bawa Kamalu driver hannu suka gaisa, cikin muryarsa yace "Yauwa Kamalu barka da aiki!"
Tunda suka baro airport ɗin Kamalu driver ke ta masa zuba, yayinda shikuma yawan maganartasa ba sosaiba saidai murmushi kawai da yakeyi.
Gyara zama Shukra tayi cikin kulawa tace "Me yasa zaki tauyewa kanki haƙƙi Zieyaderh? indai kina sonsa kawai ki amsa masa, mene aibun Pharouk? Sam bashida wani aibu komai nasa mai kyau ne, inta ƙaicemiki babu wata ƴa mace da zataga Pharouk kuma ta ƙishi coz ba Namijin wasa bane"
Sunkuyar dakai Zieyaderh tayi tare daɗan ciza lips ɗinta, "Bansan ya zanyiba Shukhra amma karki manta nafaɗa miki matsayina bai kai ace naso Pharouk ba, duk da bansan wanene shiba amma nasan ko sama zata haɗe da ƙasa yafini tsatso me kyau, da kuma gata, banason na tozarta rayuwata Shukhra!" taƙare maganar idanunta cike tab da ƙwalla.
Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da sakin murmushi "Wannan ba hujja bane Zieyaderh, ana iya auren shegiyama wacce bata da uba, balle keda kike da uba, balallaine don bakisamu kulawan mahaifanki yazamana kin tauyewa kanki haƙƙi ba, ke macece idan baki zaɓi mijin da zaizame miki garkuwa ba me kenan kikayi? Ki farka daga baccin da kike Zieyaderh akowacce ƙwanan duniya ƙara girma muke, ayanzune yakama musan dacewa muma matane sannan ayanzune yakamata mukau da wani shashanci da yarinya wanda ke cikin sense ɗinmu, yes nasani bamu da wasu shekaru masu yawa amma kuma babu wani abu na ƴan matanci ayanzu daya ɓoye kansa ajikinmu, zamu mori damarmu ne kaɗai idan mukayi amfani dashi tun muna ƙanana, alokacin da muka girma kuwa bazamu taɓa morarta da kyauba, saboda alokacin bakowa ne zaizo ya kallemu yace yana sonmu ba, ayanzu kuwa kowa so da sha'awarmu yake" Ɗan tsagaitawa da maganar tayi tare da sanya hannunta ta dafa kafaɗan Zieyaderh.
"Ki amincewa Pharouk Zieyaderh, inada tabbacin Pharouk bazai taɓa nuna miki tsana tsangwama da kuma kyara ba!"
Wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi Zieyaderh ta sauƙe, tabbas tasan abunda Shukhra ta faɗa gaskiya ne, saidai kuma tayaya zata furtawa Pharouk cewa tana sonshi? Idan har taso Pharouk menene matsayin tunanin Mr.helper dake kwance acikin zuciyarta? Da sauri takawar da wannan tunanin acikin zuciyarta. Murmushi tayi cike da son samawa kanta ƙarfin guiwa tace "Zan faɗa masa komai game dani Shukra, idan har zai soni ahaka to nima zan amasa masa, saɓanin haka kuwa shikenan zanjira wata ƙaddaran"
"Bazai taɓa gudunki ba Insha Allah!" cewar Shukra. Dariya suka sanya su dukansu.
5:10 pm zaune take acikin motar gaba ɗaya tunaninta yayi nisa izuwa maganganun da sukayi da Shukhra, sanyin AC'n dake tashi acikin motarne ya cakuɗa da daddaɗan ƙamshin turaren sa, duk da cewa baya cikin motar amma zaman dayayi acikin motar da safe yasanya har yanzu ƙamshinsa bai bar cikin motarba, hakan yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi wani iri, jingina bayanta tayi da jikin kujeran motar tare da lumshe idanunta, sosai ƙamshin yake jefata cikin wani irin yanayi. Sam batasan da cewa sun iso gidan ba saida taji Kamalu driver ya tsaida motar. Jiki asanyaye take tafiya harta kawo ƙofar falon, tura ƙofar falon tayi ta shiga, da ƴar siririyar muryarta tayi sallama, Amustapha dake tsaye acikin falon ya juyo ahankali yana me amsa mata sallaman, idanunsune ya sarƙe acikin na juna, da mamaki akan fuskarsa ya shiga kallonta, Itama kallonsa take, "Almustapha" Muryar Ummu da suka ji yasa suka ɗauke idanunsu akan juna.
Ummu ce taƙaraso cikin falon fuskarta ɗauke da murmushi.
Kallon Zieyaderh tayi tare da cewa "Zieyaderh ga ɗana Almustapha"
Mamakine ya bayyana akan fuskar Zieyaderh amma saita share,cikin sakin fuska tare da murmushi taɗan rusuna tagaidashi, shima murmushinne akan fuskarsa ya amsa mata, har yanzu yana me dubanta don baigaji da kallonta ba. Harta haura steps bai ɗauke idanunsa akanta ba, Murmushi Ummu tayi sannan ta juya tafice daga cikin falon don dama fita zatayi.
Da ƙarfi ya buga table ɗin dake gabansa ransa amatuƙar ɓace yace "Get out Aneesa!!"
Murmushi Aneesa tayi tare da juya idanunta dake cike da ruwan hawaye, laɓɓanta ta ciza, "Bazan tafi ba RAJ Why kake kyarata? menene bani dashi? Kyau,Ilimi, dukiya, ko kuma me?" Ta tambayeshi hawaye suna mai sauƙa daga cikin idanunta.