Author : Maman Teddy Category : Adventure
hanunta ɗauke da tray. Shigowansa yayi daidai da juyowa yafuskanci bakin ƙofan, idanunsune yasarƙe acikin na juna amatuƙar tsorace tasaki tray ɗin dake hanunta tare da sulalewa awajen tana kallon cikin idanunsa da suka zama tamkar garwashin wuta.
*Vote!*
*Vote!!
*Vote and Comment please my lovely fans!!!*
*/26/May/2020*
Fallow me on Wattpad @fatymasardauna.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*Wattpad*
fatymasardauna
#romance
*This Page Is Dedicated To You My Habibtie Niesher Jay. Love yhu Habibtie💘🔐*
*Chapter 25*
Cikin sauri tasoma tattara glass bowl ɗin daya tarwatse akan tiles ɗin, gaba ɗaya jikinta ɓari yake. Baiko kalli inda take ba ya juya ya koma toilet. Jiki asanyaye haka ta tattare wajen. Moper taɗauko tazo tasoma ƙoƙarin goge wajen da fruit salad ɗin ya ɓata, gashi gaba ɗaya glass bowl ɗin da fruit salad ɗin ke ciki ya tarwatse awajen.
Wanke hanunsa yayi acikin sink tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel ya goge gumin dake fesowa ta goshinsa, atunaninsa zuwa yanzu bata cikin ɗakin don haka ya murɗa handle ɗin ƙofar toilet ɗin ya fito, ganinta a durƙushe tana tattare fasassun glasses yasan yashi saurin ɗauke kansa daga gareta, direct gaban closet ɗinsa ya nufa, wani Pencil Combat jeans black ya ciro sai kuma wata white button shirt, kallon agogo yayi yaga har lokacin sallan Magriba yaɗan gota, tsuka yaja ahankali tare da ɗan cizan laɓɓansa.
Gaba ɗaya jikinta ɓari yake, tsoro takeji kada yayi mata faɗa ko yace zaiyi mata wani abun. Jin takunsa na isowa gareta yasanya batare data kulaba ta sauƙe hanunta akan wani fashasshen kwalba, yana cakanta kuwa saiga jini, wani ƙara ta sake cike da ɗan tsoro, dubanta takai ga hanunta wanda har yaɗan fara fitarda jini, take tasoma jin wani irin raɗaɗi. Sooraj dake tsaye agaban dressing mirror yana dressing hanunsa daya yanke, baiko waiwayo ya kalleta ba, yi yayima tamkar baiji ƙaran nata ba, yana kammala dressing ɗin, ya ɗauki kayansa ya wuce toilet.
Haka tacigaba da gyara wajen, duk da cewa hanunta nayi mata zogi amma haka ta daure.
Yana fitowa daga cikin toilet ɗin sassanyan ƙamshin turaren dake fita ajikin kayansa ya daki hancinta, cikin takunsa na isa yaƙaraso ta bayanta ya raɓa yafice daga cikin ɗakin batare da ko kallonta yayi ba. Tanajin rufewar ƙofarsa, tasaki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, sai alokacin ruwan hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa. Cikin mintuna ƙalilan ta gama gyara wajen, tattara fasassun glasses ɗin tayi tazubar a durstbin, daganan ta wuce ɗakinta duk raɗaɗi ya isheta.
Yana fita kaitsaye babban masallacin dake gefe da gidannasu kaɗan ya nufa, anan yayi sallan Magriba, haka ya zauna har aka ƙira sallan Isha. Koda ya idar da sallan bai ko motsaba, istigfari yashiga yi acikin zuciyarsa, duk ƙoƙarinsa nason kawar da tunanin dake neman addabar zuciyarsa abun yaci tura, kansa ya jingina ajikin bango tare da lumshe idanunsa, numfashi yake fitarwa ahankali yayinda yake furta kalman "Astagfirullah!" daga bakinsa ahankali. Ahankali nutsuwa ke sauƙa ajikinsa, yayinda yaji damuwarsa na gushewa, sosai yaɗanji sanyi acikin zuciyarsa. Ƙarfe 9 daidai yabaro cikin masallacin ya nufo gida.
Ziyada
Gaba ɗaya ɗan yankewan da tayi ya ɗaga mata hankali, sosai yake mata zafi da zogi, fitowarta daga toilet kenan tana ta faman hura iskan bakinta adaidai saitin wajen data yanke, zama tayi akan gado, tare da jawo school bag ɗinta, gaba ɗaya zaman kaɗaici ya isheta sam batajin daɗin zaman da take yanzu burinta shine akoma makaranta. Tajima tana dudduba littatafanta kafun daga bisani bacci ɓarawo yayi awun gaba da ita.
_SOORAJ_
Yana dawowa daga masallaci direct ɗakinsa ya wuce, gaban Computer ɗinsa ya ƙarasa tare da soma lallatsata, koda ya kunna wayarsa kuwa saƙon gaisuwane da kuma na jaje waƴanda abokai da ƴan uwa suka tara masa suka dinga shigowa, bai tsaya wani duba saƙon ba yamaida wayar ya ajiye, har ƙarfe 11 yana kan computer. Aɗan gajiye yaƙarasa gaban fridge, bottle water ya ɗauko tare da ɓalle murfin, magungunan dake hanunsa ya watsa abakinsa tare da bin kansu da ruwa, long jeans ɗin jikinsa ya cire yasanya wani 3 guater, hanunsa yakai kan makunnin wutan ɗakin ya kashe take duhu ya mamaye gaba ɗaya ɗakin. Kan lafiyayyen gadonsa ya hau tare da danna makunnin bedside lamp, take wani ɗan haske dark blue yabayyana acikin ɗakin. Lumshe idanunsa yayi tare dajawo pillow yaɗaura kansa akai, wata ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya hanu ya shafi ƙasan maranshi, wanda yakejinsa aɗan kumbure, duk yanda zuciyarsa taso sanyashi dogon nazari yaƙi aminta da hakan, haka kuma yaƙi bawa brain ɗinsa daman yin tunani kamar yanda yasaba akoda yaushe, dayake acikin magungunan dayasha akwai maganin dayakesa bacci sosai, hakan yasa acikin mintuna kaɗan bacci ya ɗaukesa.
Washe Gari.
Tuni tatashi tayi sallan asuba, ɗan madaidaicin ƙur'aninta ta ɗauka tashiga tilawan aƙur'ani, dayake ana koya musu amakaranta shiyasa tamai da hankalinta sosai, tana kammalawa ta wuce toilet donyin wanka.
Ahankali ta buɗe ƙofar bathroom ɗin tare da sako kanta, duk dacewa tasan ita kaɗaice acikin ɗakin, amma hakanan take jin kunyan fitowa da towel ajikinta, kamar wata marar gaskia haka ta rakuɓo ta fito, zama tayi akan stull ɗin mirror tare da ɗaukan body lotion ɗinta tashiga shafawa, tana gamawa ta murza powder akan fuskarta, wani peach colour oil lipstick ta goga akan lips ɗinta wanda yaƙara bayyana asalin kalan lips ɗinnata, wata simple maroon colour Straight gown ta sanya ajikinta, duk da kasancewar rigan tana da ɗan faɗi amma hakan baihana hips ɗinta bayyana ba, ɗan kwalin rigan da yakasance tamkar gyale shita ɗauka ta yafa ajikinta, daidai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, da sauri ta waiga zuwa bakin ƙofan, idanunta ne ya sauƙa acikin na Ummu da sauri tayi ƙasa da kanta, tare daɗan durƙusawa, cike da ladabi tace da Ummu. "Ina kwana!" Fuska asake Ummu ta amsa mata da "Lafiya lau kin tashi kenan?"
Kanta ta kaɗa alamar "Eh"
"To biyoni mushiga kitchine saboda yau mu zamuyi aiki kafun masu aiki su ƙaraso"
Babu musu tabi bayan Ummu suka fito daga cikin ɗakin, direct tamfatsetsen kitchine ɗin dake cikin babban falon suka nufa, kitchine ne da aka ƙawatashi sosai tamkar wani haɗaɗɗen falo haka kitchine ɗin yake, komai na cikinsa light green and milk colour ne. gyaran su carrots da green beans Ummu ta bata, cikin mintuna ƙalilan ta kammala, haka ta ɗebo irish patatoes tashiga ferewa tana musu yankan chips, yayinda Ummu kuma ke kula da miyan egusin da zatayiwa Abba wanda zaici tuwo dashi, da taimakon Ummu Ziyada ta haɗa liver and garlic sauce, sannan ta soya chips, kasancewar Ummu tasan Sooraj daga fruits sai tea sune abincinsa yasanya dakanta ta haɗa masa fruit salad, Ziyada kuwa Ummu ne ta nuna mata yanda zata haɗa milk shake, haka kuma da taimakon Ummu ta samu tayi pepper soup ɗin cow meat, tuwon semo miyan egusi wanda yaji kifi Ummu tayiwa Abba tare da Coconut juice domin Abba baicika shan drinks ɗin company ba. Ziyada ce keta kai kawo tsakanin dinning area dakuma kitchine, tsab tagama jere duk abincin da sukayi akan dinning table, komawa kitchine ɗin tayi ta haɗa gaba ɗaya kwanukan da suka ɓata tasoma wankewa. Ummu naganinta taɗanyi murmushi tare da ƙarasowa gareta "Wannan ba aikin ki bane kibarshi idan masu aiki sunzo zasu ƙarasa" Ummu tafaɗa cike da kulawa.
Ɗan murmushi Ziyada tayi cike da jin nauyin Ummun tace "Ummu kibari nima zan iya!"
Murmushi Ummu tayi haɗe da cewa "To Naji, amma dai yanzu lokacin cin abincine muje maza" Babu yanda ta iya haka ta tsame hanunta acikin wanke wanken tabi bayan Ummu. Tanasanya ƙafarta acikin falon ƙamshin da ke matuƙar tafiya da imaninta wanda tasan mutum ɗaya ne tak me amfani dashi ya daki hancinta, lumshe idanunta tayi alokaci guda tare da buɗewa, ƙoƙarin gyara mayafinta take har suka iso dinning arean, idanunta ne suka sauƙa akanshi sanye yake da riga da wando farare, sosai yayi wani irin kyau, gashin dake kwance akan fuskarsa sai sheƙi yake, idanunsa nakan iphone 11 pro max ɗinsa da alama gaba ɗaya hankalinsa na kan wayan. Hakanan taji wani irin abu yashiga dukan ƙirjinta amma saita daure tayi ƙasa da kanta. Kujera Ummu taja ta zauna tare da cewa "Ziyada yi serving ɗinmu"
Jiki asanyaye haka Ziyada tashiga serving ɗinsu, ɗaukan glass bowl ɗin fruit salad ɗin da Ummu tace mata nashine tayi ta ajiye agabanshi, cikin sanyinta ta juya zata bar wajen.
"Ina kuma zaki?" muryan Ummu ya katseta.
"Uhumm dama ɗaki zankoma!" tafaɗa tana mai wasa da yatsun hanunta.
"Zauna idan kinci abinci saiki tafi ɗakin!" Ummu tafaɗi haka tana me jawo mata kujeran zama wacce take facing na Sooraj.
Sam musu ba al'adanta bane don haka kamar wacce aka cirewa laka ajiki haka ta zauna akan kujeran aɗaɗare, hanunta har rawa yake alokacin data soma serving kanta, chips ta ɗiba ɗan kalan acikin plate sai liver sauce shima kaɗan. Milk shake dinne dai tasanya har rabin cup. Abba da Ummu tuni sunfara cin abincinsu amma banda ita da Sooraj, ita kam wani iri haka takeji domin bata saba zama da manya ba, sam ita batasan wannan soyayyan ba, shikuwa Sooraj tunda yazauna ma bai ɗago kanshi ba screen ɗin wayarsa kawai yaketa shafawa, kamar wacce aka razana haka taɗauki fork tashiga tsakalan chips ɗin da ɗaya ɗaya tana kaiwa bakinta. Aƙalla yaɗauki sama da 10 minute yana latsa phone dinsa kafun ya ɗago, bowl din fruit salad ɗinsa yajawo ahankali yasanya spoon aciki, 2 spoon kawai yayi ya sake mayar dakansa ga wayarsa, Ummu gaba ɗaya tana lura dashi, duk da tasan cewa bayida yawan cin abinci, amma yanda yanzun yaƙi maida hankali yasha fruid salad ɗin yasanya taji ba dadi acikin ranta, cike da kulawa ta ƙira sunanshi "SOORAJ!"
Ahankali yaɗago kanshi ya kalleta batare dayace wani abuba.
Ɗan ɓata fuska Ummu tayi tare da cewa. "Kasan dai me Dr. yace akanka ko? saboda haka yanzu lokacine da zakaci abinci sosai, rashin cin abincin shine zaisa kadingajin kanka kamar baka da lafiya"
Ɗan yamutsa fuska yayi tare da kaɗa mata kansa alamar "Yaji"
Kansa yamaida ga bowl ɗin ya ɗeɓo fruid salad ɗin yakai bakinsa. Abba daya kammala cin tuwonsa ya ɗago yana goge hanunsa da tissue. Sam babu wanda yayi zato saijin muryarsa sukayi yace.
"Sooraj Ina magananmu ta tsaya?"
Dummmm haka Sooraj yaji gabansa yafaɗi, har acikin ransa yama manta da maganan da sukayi da Abban.
Shirun da yayi yasa Abba ci gaba da cewa. "Ayanzune zan matsamaka fiye da da akan maganan aurenka Sooraj, kaduba kai bakajin kunya ne ace har yanzu mahaifiyarka itace zata nunamaka abun daya dace? kula dakai ayanzu ba haƙƙin mahaifiyarka bane, yakamata ne ace kana da mata domin kulawa da irin waƴannan abubuwan, saboda haka ina mai tabbatar maka da tunkan nama abun dazaisa kaji babu daɗi ka nemo mata kakawomin ko acikin satinnan ne ni zan aura maka ita!" Cikin maganganun Abba gaba ɗaya babu wasa, yana gama faɗan haka ya miƙe tsaye yabar wajen. Gaba ɗaya tunanin Raj ne ya tsaya cak, sam baiyi tunanin Abbansa zai sake tada wannan maganan ba, musamman ma da yanzu bawai wani lafiyane ya isheshi ba, inama da Abba yasani dabaiyi maganan nan ba, domin kuwa gaba ɗaya ya sukurkutamasa tunani, duk wani ɗan annushuwan dayake ciki ya kau.
"Ina fata dai kaji abun da mahaifinka ya faɗa ma? kasan shi kakumasan abun da zai iya aikatawa saboda haka tunkan yazaɓama da kanshi kai kazaɓarwa kanka, don na tabbata wannan karon bazai maka da sauƙi ba!" Ummu tafaɗi haka itama tana me miƙewa tsaye, bata wani tsayaba tabi bayan mijinta, akabarsu su biyu akan dinning table ɗin.
Hakanan Ziyada taji murfin ƙirjinta na ƙoƙarin faɗawa.
"Aure akeso yayi?" ta tambayi kanta, sam bata wani fahimci inda kalaman Iyayen Sooraj ɗin suka dosa ba, amma kuma da dukkan alama aure sukeso yayi, tsintar kanta tayi da kasa cigaba da tauna chips ɗin dake bakinta sai kawai ta haɗiyeshi.
Shikuwa Sooraj hannayensa yasanya ya rufe fuskarsa da tafukan hanunsa, wani numfashi me ɗumi ya fesar ta bakinsa, wani irin dokawa ƙirjinsa keyi, sam bayason yaji anyi masa maganan da zata alaƙantasa da mace, bayajin zaiyi aure a irin wannan lokacin, bayamajin akwai wata wacce zata soshi ayanda yake, koda ma wata ta soshi shibabu soyayya atsarinsa, baisan menene so ba, baitaɓayi ba baisan yazai fara ba.
Sam bazata iya jure zaman wajenba, don haka saɗaf saɗaf tamiƙe tsaye tare da juyawa zata bar wajen.
"Waye sa'anki dazakibar masa ragowan dattinki anan?"
Husky voice ɗinsa yadaki dodon kunnenta wanda ya tilasta mata tsayawa, jikinta naɗan rawan tsoronsa ta juyo, plate ɗin data ci abinci tasoma ɗaukewa sannan ta haɗa dana su Ummu ta nufi kitchine, har yanzu bai sauƙe hannuwansa daga kan fuskarsa ba amma kuma komai take yana kallonta. Baitashi akan dinning arean ba harsaida ta tsabtace wajen ta goge, duk abun da takeyi atsorace takeyinsa, fatanta ɗaya kar tayi kuskure yayi mata masifa, tana tsaka da goge kan haɗaɗɗen royal table ɗin yatashi cikin tafiyarsa ta isa yanufi ɗakinsa. Tana ganin shigewarsa ɗaki, ta saki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, tare da share hawayen dasuka silalo daga cikin idanunta.
28/May/2020
*Vote......and comment....*
fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
fatymasardauna
#romance
*Chapter 26*
Hanunta tasa da sauri ta goge hawayen daya sauƙo mata akan ƙuncinta, kitchine ta koma ta tare da cigaba da wanke wankenta......
RAJ
Tsaye yake agaban shower ruwa na dukan jikinsa, hannayensa duka biyu ya sanya ya dafe jikin bango, idanuwansa wanda suka sha ruwa sukayi jajur ya buɗe tare da furzar da ruwan dake bakinsa. Maganganun Abba gaba ɗaya sun gama dagula masa lissafi, ko tantama bayayi koda sun nemo zaɓinsu sun aura masa awannan karonma bazai iya jure zama da mace ba, dole zai saketa, sannan kuma dole ne zasuyi fushi dashi, ayanzu kam baya tunanin zai sake yarda alaƙa ba masa nauyin wata ƴa mace akansa, koda sau ɗayane yanason iyayenshi su fahimcesa amma kuma hakan ya gagara, kashe shower'n yayi tare da jawo towel ya ɗaura akan weast ɗinsa, baidamu da yanda jikinsa ke ɗigan ruwa ba ya buɗe ƙofar bathroom ɗin ya fito, idan yace zai iya baje damuwowin dake ranshi to tabbas ƙwaƙwalwa da zuciyarsa bazasu iya ɗauka ba, kaya ya sanya ajikinsa tare da ɗaukan car key ɗinsa yafice daga cikin ɗakin, direct compound ɗin gidan ya nufa, wata baƙar 4matic ya buɗe yashiga tare dayi mata key, tun mai gadi baigama wangale gate ɗin da kyauba ya cilla hancin motarsa waje.
Tafiya yake amma gaba ɗaya hankali da tunaninsa suna wani waje daban, ababban ƙofar asibitin yayi parking, yau bakamar ko yaushe ba, don bai shigar da motar tasa ciki ba kamar yanda ya saba.
Direct office ɗin Dr.Yunus ya nufa, yana knocking aka bashi izinin shigowa, kujera yaja ya zauna tare da miƙawa Dr.Yunus hannu sukayi musabaha, cike da fari'a Dr.Yunus yace. "Yajikinnaka ina fata dai ankama waƴanda suka aikata laifin?"
"Dasauƙi!" Sooraj yafaɗa aɗan gajarce kasancewar bayason zancen yayi tsawo.
Murmushi Dr.Yunus yayi domin sarai yasan halin Sooraj sai mutum ya shekara yana masa magana baitanka ba.
Gyara zama Dr. Yunus ya sakeyi tare da cewa "Result ɗinka yana ajiye tun after 1 week" Wata ƴar drawer dake jikin table Dr.Yunus ya jawo tare da zaro wata farar envelope.
Miƙawa Sooraj yayi tare da cewa "Komai yananan daidai, nayi duk wani bincikena dazanyi Sooraj amma gaskia bangano wata sabuwar matsala ba, magungunan dana baka acan baya sune kawai zakana sha har abubuwa su daidaita!" Dr.Yunus yafaɗi haka cike dason kwantar da hankalin Sooraj.
Wani murmushin gefen baki wanda yafi kuka ciwo Sooraj yayi, shikaɗai yasan wani irin zafi zuciyarsa keyi masa awannan lokacin, karɓan takardan kawai yayi tare da sake bawa Dr. Yunus hanu sukayi musabaha, daganan yafice daga cikin office ɗin, wani irin kallon tausayi Dr.Yunus keyiwa Sooraj, sosai matsalan Sooraj ɗin ke ɗaure masa kai, iya binciken duniya sunyi shida abokan aikinsa amma sam su basu iya gano matsalan Sooraj ba, hasalima komai nasa lafiya lau yake bashi da wata tawaya a halittar jikinsa. .
Tunda yafito daga cikin office ɗin Dr.Yunus yake ganin duhu a idanuwansa, cikin cijewa ya ƙarasa wajen da motarsa take, yana shiga ya kifa kansa ajikin steering motar tare da fesar da wani breath me ɗumi, aƙalla yaɗauki kusan mintuna 9 ahaka batare dako motsi yayi ba, gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya cak.
Da ƙyar ya iya ɗago kansa, idanuwansa tamkar jan garwashin wuta haka suka koma, Envelope ɗin da Dr.Yunus ya basa ya buɗe, tare da zaro wata ƴar farar takarda dake ciki, ahankali ya warwareta tare da sauƙe idanunsa akan rubutun dake cikin takardan . Yana gama karanta abun dake cikinta ya duƙunƙuneta tare da rumtse idanunsa da ƙarfi. Laɓɓan bakinsa yaɗan ciza tare da ɗauko wata lighter ya kunna, takardan yakawo jikin lighter'n take ta kama da wuta, sauƙe glass ɗin motar yayi ƙasa tare da cilla takardan waje, take takardan ta ƙone ƙurmus, key yayiwa motarshi tare da cillata kan titi yabar wajen....
Ziyada kuwa tana kammala wanke wankenta, ta shige ɗaki bata kuma sake fitowa ba, duk da cewa zaman ɗakin bawani daɗi yakeyi mata ba amma kasancewar bata da abunyi yasanya ta gwammacewa kanta zama waje ɗaya.
***
After 3 days.
Tunda Abba yayiwa Sooraj maganan aure sai ya zamana Sooraj baya zaman gida kwata kwata, idan yafita tun safe bazai dawoba sai after Sallan Isha, kafunnan Abba yajima da dawowa suna tare da Ummu, sam bayason Abba yasake ɗago masa da wannan maganan domin magana ta gaskiya aure