Author : Maman Teddy Category : Adventure
kyau ba? Aure kuma da Almustapha? Waƴannan tambayoyin sune cike aranta, ganin komai take kamar ba da gaske ba. Dafa shoulder ɗinta Oummu tayi cike da kulawa tace "Karki taɓa cutar da kanki Zieyaderh, idan har kinaga hakan zai sa ki cutu to karki ɓoye ki sanardani, bazan taɓa miki dole ba, nayi hakanne kuma badon na cutar dake ba saidon ina kwaɗayin ganinki cikin zuri'ata, duk da nasan cewa banice na haifi Almustapha ba, amma inayi masa son da nake yiwa ɗana SOORAJ, kuma ina masa kwaɗayin zamowarki mata a garesa!!"
Hawayene suka cika idanun Zieyaderh, har takai ga sun soma sauƙa akan hannunta, wani irin bugawa zuciyarta keyi, ita kanta batasan awani irin hali take ciki ayanzun ba, gaba ɗaya kalaman Oummu sunzama tamkar wani sinadari na bayyanar da raunin zuciyarta.
Ganin hawaye na ɗiga daga idanun Zieyaderh yasa Oummu cewa.
"Ya isa daina kukan, idan kingama cin abincin kije ki kwanta, komai ya wuce nafahimci halin dakike ciki!" tana gama faɗan haka ta miƙe tare da soma ƙoƙarin barin wajen. Da sauri Zieyaderh ta riƙo hannun Oummu, cak Oummu ta tsaya tare da juyowa, ɗago manya manyan idanunta tayi bakinta na rawa tace.
"Kiyi haƙuri Oummu ba ina kukane saboda banason abunda kikazomin dashi ba, nayarda ke uwace agareni, saboda haka NA AMINCE!" taƙare maganar ƙirjinta na mata wani irin suka, yayinda gaba ɗaya gaɓɓan jikinta sukayi weak, so take tafashe da kuka me sauti, so take ta kalli koda ɓangaren da yake ne kozataji sanyi, so take yace wani abu, to amma metakeso yace ɗin, itama kanta batasani ba.
Cike da farinciki Oummu tashafa kanta cikin ƙaunar biyayya irin nata tace.
"Nagode sosai Zieyaderh nakuma ji daɗi da baki watsamin ƙasa a idona ba, haƙiƙa ke yarinyar kirkice, Insha Allahu Kuma zakiyi alfahari da wannan haɗin, kije ɗaki ki huta kinji!" Oummu ta ƙare maganar cike da lallashi. Babu musu kamar wacce ƙwai ya fashewa ajiki haka ta tashi daga zaunen da take, har yanzun bazata iya ɗaga idanunta ta kalli ko wanne daga cikinsu ba, cikin ƙwallan da suka sake cika idanunta ta haura sama daɗan sauri burinta taje tayi kuka kozataji sauƙi aranta.
Tunda suka fara maganar har kawo iyanzu bai koda ɗago kansa ya kallesu ba, sannan baidaina abun daya keyi ba, da kaɗan kaɗan yake sipping tea ɗin da tsabar zafi har tiriri yake, hayaƙin dake fita acikin kofin tea ɗin shine ya sanya gaba ɗaya fuskarsa ta ɗanyi zufa, sam baijin wannan zafin shayin akan harshensa hasalima tamkar wanda yakeshan ruwan randa haka yaji test ɗin shayin ya sauya a bakinsa.
Kallon Oummu dake tsaye tana murmushi Almustapha yayi jikinsa asanyaye yace
"Oummu kinaga kamar ba matsala kuwa?" Still murmushi Oummu tayi tare da dafa shoulder ɗinsa cikin kulawa tace.
"Babu wata matsala Almustapha ka kwantar da hankalinka, kaidai ka shirya bikinka yakusa zuwa Insha Allah" Tana gama faɗan haka ta wuce zuwa ɗakinta.
Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannu ya dafa saitin zuciyarsa, har acikin ransa yaji wani irin farinciki, da sauri yatashi ya nufi ɗakinsa sam yama manta da Sooraj dake zaune agefensa.
Shikaɗai ya rage zaune akan dinning ɗin, ahankali ya aje cup ɗin dake hannunsa, tare da ɗaukan tissue ya goge bakinsa, miƙewa tsaye yayi kai tsaye ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, baijin zai samu relief idan ba shower ya sakarwa kansa ba, bathroom ya shiga tare da kunna shower, tsayawa yayi saitin shower ɗin ruwa na dukan kai da jikinsa, ahankali yake fidda wani numfashi me zafi.
Tana rufe ƙofar ɗakinnata da gudu ta faɗa kan gado, kanta ta cusa acikin pillow tare da sakin kuka me sauti. Sosai tayi kuka wanda ita kanta batasan na menene ba, batasan metakeji acikin zuciyarta ba, saidai tabbas tasan tanajin wani irin yanayi na babu daɗi, ya zatayi idan bata amincewa Oummu ba, ko ba komai su ɗin sunkasance mutane masu tsananin karamci agareta, idan har bata amince da maganan Oummu ba menene sunanta? BUTULU? tabbas Oummu tabata kulawa, sannan duk da batasan wacece itaba ta zauna da ita bata ƙyamaceta ba, shin saɓamata daidai ne? koma badon Oummu ba kodanshi ya cancanci tayiwa mahaifiyarsa biyayya, koba komai shiɗin wani ne na musamman awajenta, idan taƙi aminta da maganan mahaifiyarsa tabbas tasan bazaiji daɗi ba, amma kuma meyasa takejin wani abu dangane dashi? meyasa baice wani abuba alokacin? "Mekikeso yace?" wata zuciar ta tambayeta, shiru tayi da kukan da take tare da soma sauƙe ajiyan zucia akai akai.
Kusan 30 minutes ya ɗauka ruwa na dukan jikinsa, da ƙyar ya iya kashe shower'n tare da ficewa daga cikin bathroom ɗin, sauya shigarsa yayi zuwa wani white yard wanda yaji ɗinkin half jumper da wando, sosai kayan sukayi masa kyau, saidai rashin walwalan dake kan fuskarsa na yau ya zarce na kullum, ɗan makullin motarsa ya ɗauka tare da wayarsa kana yafice daga cikin ɗakin.
Tuƙa motar yake amma batare dayasan ina ya nufa ba, ganin ya soma gajiyawa ne yasanyashi gangarawa gefen titi yayi parking ɗin motar, ahankali ya kifa kansa akan steering motar, shikansa baisan mene dalilinsa na tsayuwa awajen ba, baisan dalilin daya sanya yakejin kansa acikin wani irin bad mood ba, mekenan? me hakan yake nufi? hakanan yaji kansa acikin damuwa, to amma abun tambayar shine damuwar tasa na menene? shikansa baisan akan mene yake damuwan ba, dalilinsa na sanya kansa cikin damuwa yayi ƙaranci, tabbas yanaji ajikinsa cewa idan har ya bari tunanin dake ƙwaƙwalwarsa yasamu mafaka acikin ƙirjinsa to tabbas zuciyarsa zata buga.
*Follow,*
*vote,*
*comment and share*
fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 38*
Ɗago kansa yayi daga jikin steering motar tare da sakin wani murmushi mai ɗauke da tarin ma'anoni, agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba, ƙarfe 11 dae dae, ɗan ƙaramin tsuka yayi tare da tada motar ya cillata kan titi.
Zieyaderh kuwa tana gama koke kokenta baccine ɓarawo ya saceta wanda sai yanzun ta tashi, ji tayi yanayinta ya sauya tamkar wata marar lafiya, bathroom tashiga tayo wanka, tare da dawowa ta zauna akan gado, tv ta ƙurawa ido amma azahirin gaskiya hankali da tunaninta ba ga tv'n yake ba, tunaninsa ya matsanta mata, lallai tana da buƙatar me fayayyace mata halin da take ciki, Shukra, itace wacce ta fara faɗo mata arai, tabbas tasan idan tasamu Shukra to zata fayyace mata komai, to amma idan Shukra ta bata amsar da zai hautsuna tunaninta fa? ajiyar zuciya ta sauke tare da soma ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta, sam yau haka taji zaman gidan ya isheta, komai jinsa take ba daɗi.
Wuse zone 4
SOORAJ, zaune yake akan wata kujera dake kusa da haɗaɗɗen dinning table ɗin dake cikin falon, cup ɗin coffee ne agefensa yayinda yake signing ɗin wasu papers dake gabansa, Mas'oud ne ke zaune akan kujeran dake facing nasa, wayar dake hannunsa ya ajiye tare da kai dubansa ga Sooraj, cikin yanayi na ɗan damuwa yaƙira sunansa.
Batare daya tsaida aikin da yakeyi ba, batare kuma daya ɗago ba yace "Ummm"
Gyara zama Mas'oud yayi tare da cewa "Oummu tayimin magana akan auren Almustapha da Zieyaderh, sannan tace dani gobe Abba zaizo nakuma ce mata zan sameshi muyi magana, gaskiya RAJ nayanke shawaran zan sanar da Abba komai adangane da rashin lafiyanka!"
Aje pen ɗin hannunsa yayi tare da ɗago kansa ya dubi Mas'oud.
"Faɗa masa matsalata bashida wani amfani Mas'oud, kabari kawai badai aure suke so nayi ba, nashirya zanyi" Yafaɗi haka cikin halin ko inkula.
"Yin aurenka bashine mafita ba Sooraj samun lafiyanka shine abunso, ya zakayi da matar idan har baka samu lafiya ba?" Mas'oud ya tambaya cike da tsananin tausayinsa.
Murmushin gefen baki Sooraj yayi tare da ɗan cizan lips ɗinsa, adai dai wannan lokacin shikaɗai yasan me yakeji.
Ɗan numfasawa Mas'oud yayi tare da cewa "Amma RAJ auren Zieyaderh da Amustapha abun na damuna sosae!"
"Why?" Sooraj ya tambaya ataƙaice.
"Sooraj" Mas'oud yaƙira sunansa. Ɗago kai yayi ya kalli Mas'oud ɗin batare daya amsa ba, shima Mas'oud din kallonsa yake, tabbas shikam akwai abun daya jima yana hangowa acikin idanun SOORAJ, amma baitabbatar da abunba sai ayanzu, wani tarin tausayin Sooraj ɗinne yasake kamasa, haƙiƙa Sooraj baisan komaiba agame da so, shi mutum ne wanda yake rayuwarsa shi kaɗai, baya sharing damuwarsa da kowa, saboda haka ba lallai ya fuskanci cewa wani abu na damunshi ba, koda ma yafahimci hakan ba lallaine yasan menene abun ba. Kawar dakae gefe Sooraj yayi tare da miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka tare da cewa "Nagama signing papers ɗinnan, ka kula sai munyi waya!"
Kasa ce dashi wani abu Mas'oud yayi harya fice, shikam Allah Yasani tausayin SOORAJ yake, tabbas yau ya hango damuwa me tarin yawa a cikin idanun SOORAJ.
Monday
Tun kafun 7 yau tagama shiryawanta, bata da wani buri wanda ya wuce taje ta sanar da Shukra damuwanta kozata ji sauƙi acikin zuciyarta, duk yanda Oummu taso ta tsaya tayi break ƙi tayi haka ta tafi makarantar da yunwa acikinta.
Shiru Shukra tayi tare da ɗan nazantar maganganun da suka fito daga bakin Zieyaderh.. "Bansan ya zanyi ba Shukra, bansan me yasa nakejin haka dangane dashi ba" Zieyaderh tafaɗa cikin yanayi na damuwa.
Murmushi Shukra tayi tare da dafa shoulder ɗinta, gyara zama tayi tare da cewa "Zaki iya yarda da cewa kin kamu da son sa?"
Idanu Zieyaderh ta zaro waje tare da dafe ƙirjinta dake bugawa, cikin yanayi na tsoro tace "SO fa kikace Shukra?"
"Eh SO, karki yarda ki ƙaryata zuciyarki akan alamomin so da take gwada miki, tabbas Son shi kike Zieyaderh, don so ne kaɗai ke kawo waƴannan alamomin, idan ba so ba, me zae sanya dan kinganshi gabanki yana faɗuwa? me zaisa tunaninsa ya samu mafaka azuciyarki ba dare ba rana? Idan baso ba me zai sanya tsananin tausayinsa wanzuwa acikin ranki? Wannan duk alamomin SO ne Zieyaderh, hmmm bana faɗa miki SO ya wuce duk wani tunaninki yana zuwa da alamomi masu yawa, haƙiƙa sonda kike masa irin sane wanda yake sanya ciwo azuciya, kiyarda kawai sonshi yana daga cikin ƘADDARA'nki!"
Shiru Zieyaderh tayi tare da rumtse idanunta, tabbas bazata iya ƙaryata Shukra ba, domin itama zuciyarta ta gamsu da hakan... "Menene amfanin wannan son? menene amfanin son wanda baisan kanayi ba, meyasa zuciyata tayi mini haka, tabbas idan nasoshi na so kaina dayawa saboda ba ajina bane!" Zieyaderh ta faɗa murya araunane.
"So baruwanshi da aji ko rashinsa Zieyaderh, kiyi fata wata ƙila shima ya soki!" Shukra tafaɗa cikin son ƙarfafa mata guiwa.
"Soyayyata bata da amfani Shukra, saboda ɗan uwansa zan aura, wani riba zan samu idan naci gaba da sonsa Shukra?" hawaye har sun cika idanunta.
Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da cewa "Kicire sonsa azuciyarki Zieyaderh, haka shine samun sauƙin kai da zuciyarki"
Hawayen dake cikin idanunta ne suka gangaro ahankali tasa hannu tashare, "Nayarda inasonka, amma zan barwa zuciyata ita kaɗai, zan jure duk wani zafi da ƙunci, idan har soyayyarka zata zauna azuciata bazata fice ba, ko ba komai watarana ita zata tausheni" maganan da takeyi acikin zuciyarta kenan... Haka taƙare gaba ɗaya wunin ranan cikin damuwa, sam walwalanta ya ragu babu wani jin daɗi atattare da ita. Koda aka tashi amakaranta data koma gida aɗaki ta zauna, ko abinci bata fito taci ba, damuwar SOYAYYARSA ne kwance aƙasan ranta.
Tun ɗazu yaketa juyi akan makeken gadonsa, shikansa baisan tunanin me yake ba, yasan ƙaddara tana iya sauyawa ako da yaushe amma baya fatan tasa ƙaddaran ta sake sauyawa, saboda zai iya jure komai amma banda sabon baƙon yanayin dayake samun kansa aciki kwana biyun nan, yasani shi mai rauni ne ako da yaushe... Kansa ya cusa acikin pillow tare da sakin wani numfashi me zafi, baitaɓajin ciwon ƙaddaransa ba sai ayanzu, yanaji ajikinsa cewa zuciyarsa nason wani abu, to amma metakeso? shine abun daya kasa sani, sau da dama yakanjinta awani ɓangare ne na zuciyarsa, amma asannu sannu sai yakejin gaba ɗaya ta mamaye zuciyarsa, kowani bugun numfashin da zaiyi da fargaba yake tafiya, ada baisan wani damuwa da zafin zuciya ba, amma asannu yanzu duk ta dalilinta yasansu, yana da buƙatar sanin me hakan yake nufi, baisan mezai kira abun ba, amma wani lokaci yakanji dama ace bai santa ba kwata kwata, yakanji inama da ace baizama silan taimakonta ba wataƙila da bata shigo rayuwarsa ba, akullum ji yake kamar an rubuta wani abu daya shafeta acikin ƙirjinsa, saidai babu wanda zai sanar dashi me hakan ke nufi. Idanunsa da suka kaɗa sukai ja ya ware tare da ɗaukan wayansa ya turawa peter saƙo, akan yayi masa booking flight, kallon agogo yayi yaga ƙarfe 7 na dare, ahankali ya sauƙo daga kan gadon tare da ƙarasawa gaban drawer ɗinsa, wata black trolly ya jawo tare da buɗe sip yashiga ɗebo kayansa yana zubawa acikin trolly'n, yagama sawa aransa cewa acikin waƴannan satuttukan bazaiyi zaman Nigeria ba....
***
Dariya sosai Yasmeen keyi wanda hakan ya matuƙar harzuƙa Aneesa, cikin yanayin fushi tace "Wallahi indai ina da rai bazan taɓa barin SOORAJ ba dole sai na koyardashi yanda zaiyi ya zama namijin gaske!"
Gimtse dariyan da takeyi Yasmeen tayi tare da cewa "Bakida hankali Aneesa, ko kin manta nice wadda nafara son SOORAJ acikin zuciyata? Ke Sha'awar SOORAJ kawai kikeyi Aneesa nikuma ba iya sha'awaba sonsa nakeyi, bandamu ba don kince shiba Namiji bane, ni indai zanna ganinsa akusa dani akullum zan iya jurewa, please Aneesa kibarmin SOORAJ dan Allah Ina burin kasancewa dashi"
Tsuka Aneesa tayi tare da cewa "Duk da cewa shiɗin bashida amfani amma duk da haka inajin sha'awarsa, aranannan naso ace dagaske fyaɗe zaimin, tabbas nasan danaji daɗin da wata mace bata taɓajiba, don hakan ni awajena bazai zamanto fyaɗe ba, hmmm amma haka guy ɗinnan yatafi yabarni da yagaggen riga ko breast ɗina bai iya taɓawa ba!!" Aneesa taƙare maganar cikin yanayi na ƙufula.
Dariya Yasmeen tasakeyi tare da cewa "Bazan hanaki ba Aneesa, amma inaso ki sani bazan janye daga son SOORAJ danake ba saidai mu duka biyun Allah Yabawa me rabo sa'a"
***
Kasancewar Yau Abba zaidawo hakan yasa Oummu tun safe take ta shirye shiryen dawowarsa, tsaye take a kitchine tana ƙoƙarin harhaɗa abincin da tayi akan tray... Almustapha ne yashigo cikin kitchine din fuskarsa ɗauke da ɗan damuwa. Kallonsa Oummu tayi cike da mamakin ganin yanayinsa tace "Almustapha lapia kake kuwa?"
Murmushi yayi tare da cewa.
"Tsoro nakeji Oummu"
Shaye da mamaki Oummu tace "tsoron me?"
Ƙasa yayi da murya tare da cewa "Tsoron abun da muka shirya, nayi wani tunani, yakamata mugayawa RAJ gaskiya Oummu kinsan zuciyarsa, kar azo ayi abunnan kuma yace bayaso, sannan karkuma bayan anyi yazo yace zaiga laifina"
Murmushi Oummu tayi tare da cewa "Karka damu Almustapha, naɓoye hakanne bawai don wani abuba saidon inason wannan auren yafi waƴancan auren nasa ƙarko, jikina yajima da bani cewa awannan karon SOORAJ bazai saki matar da zan aura masa ba, kayi haƙuri Almustapha mucigaba da gudanar da shirinmu ayanda muka tsara!"
Murmushi Almustapha yayi tare da ɗaukan yankakken apple yakai bakinsa cikin yanayi na jin daɗi yace "Amma gaskiya Oummu kada asa lokacin bikinnan da yawa, don kinsan bazan iya jurewa ba watarana kada nayi abun dazai sanyashi gane plan ɗinmu!"
"Karka damu banajin bikinnan zai wuce 3 weeks saboda nima akwai abun danake hangowa, saidai kuma ita yarinyar ce bansan yazataji ba idan taji haƙiƙanin wanda ta aura."
Not editing
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 39*
Amatuƙar gajiye ta dawo daga makaranta, gaba ɗaya ƙafafunta ciwo suke, kasancewar yau ɗin kusan awa guda suka ɗauka tsaye acikin Lab, tana shiga cikin ɗaki tasoma rage kayan jikinta, wani white towel ta ɗaura aƙirjinta wanda ya kawo har kan santala santalan cinyoyinta, bathroom ta wuce kai tsaye, wanka tayi tare da ɗauro alwala. Wata pencil tightly skin gown tasanya wanda bayanta taƙasa yake aɗan tsage, sosai rigan tabi haɗaɗɗiyar surar jikinta ta lafe, wani ɗan madaidaicin hijab ta sanya ajikinta, kai tsaye tanufi ɗakin Oummu, tana knocking door ɗin, Oummu ta bata izinin shigowa, Zaune tasameta akan wata luntsumemiyar kujera dake cikin ɗakin, gabanta wasu takardune yayinda hannunta ke ɗauke da pen. Da murmushi akan fuskarta ta amsawa Zieyaderh gaisuwan da tayi mata, tare da ɗan zare farin glass ɗin dake sanye a idonta tana me cewa "Ya school ɗin?" "Alhamdulillah!" Zieyaderh ta amsa aɗan sanyaye, ƙatuwar leda wanda ke ɗauke da tambarin sunan wani super market Oummu ta miƙo mata tare da cewa. "Ungo amshi Kayan da kuka saya da Almustapha ne, ashe wai ke ya sayawa sai kimasa godiya"
Asanyaye takarɓi ledan dake shaƙe da kaya, cikin sanyin daya sake zama sabo agareta tace "Oummu kitayani godiya, nagode sosai!"
Murmushi Oummu tayi irin tasu ta manya tare da cewa "Ae kinfi kusa dashi ayanzu zai kyautu kiyi masa godiyan da kanki!"
Murmushi kawai tayi cike da kunya ta sadda kanta ƙasa tare da miƙewa tsaye, da ƙyar ta iya jan ledan don tana da nauyi, haka tafita daga cikin ɗakin tanajin wani iri acikin zuciyarta. Tana shiga ɗakinta ta Zazzage ledan akan gado, tabbas sayayyan da sukayi ita dashi ne, sam bata wani ji farinciki ba, juyawa tayi ta fice aɗakin don samawa kanta abun da zata ci, batajin cin wani abu hakan yasa ta tsiyayo fresh milk me sanyi, kanta aƙasa take haura step ɗin da zai sadata da samannasu, sam bata kula da cewa shima yana zuwa ba, haɗuwarsu waje ɗaya ne yasanya gaba ɗaya fresh milk ɗin ya zube masa ajiki, cikin tsautsayi cup ɗin ya faɗi ya tarwatse a wajen. Aɗan razane ta ɗago kanta ta kalleshi, daidai lokacin shima ya ɗago kyawawan idanunsa, idanunsune suka sauƙa acikin na juna, da sauri tayi baya kasancewar sunyi matuƙar kusa da juna, bisa tsautsayi ta aje ƙafanta akan fasassun glass, wani irin ƙara ta sake tare da rumtse idanunta ƙam, beautyful eyes ɗinsa yaɗan zaro waje tare da kallon ƙasa inda ƙafanta tuni har ya soma fidda jini. Ƙaran da tayi shiya janyo