Mis Wasmiti 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   7 / 38

18K to 21K   out of 112.1K words

cikin daga murya yace wlh kar nazo Na sameki a nan Dan wlh sai na lahira ya fiki jikin dadi

Da jin haka Ahmad ya jata sukayi cikin gida

Adam ne ya rinqa yiwa Yusuf din nasiha kan ya tausasa zuciyarsa

Haba biyaye shin a duniyarnan akwai mai wuce qaddararsane ?shin muke tsarawa kanmu rayuwa ne ko mahaliccinmu? haba Yusuf rayuwafa komai asannu mutum zai bishi matuqar kana son cin ribar rayuwar.....

Cikin sauqe ajiyar zuciya ya kalli Adam din cikin rawar murya da hardewar harshe yace Adam ya zanyi ya zanyi da burin Dan uwanmu Ahmad nafi jin makomar rayuwar Ahmad ya kamo hannushi yaci gaba da cewa shin kai baka tunanin yadda Ahmad ke son yarinyar nanne biyaye haqiqa kakanmu ya kasance mai zalumci a kan jikanshi Ahmad da yafi mu dukamu haquri da biyeyya a garesu cikin rawar murya yace Adam wlh so suke su kashe rayuwarmu da bakinciki Adam ya zanyi Plx biyaye ka tayani samawa Dan uwanmu Ahmad farin cikin Sa

Sosai jikin Adam yayi sanyi ya kalleshi cikin sanyi yace insha Allahu yau dinnan zamu samu mafita Yusuf zamuyi tunani daga yanxu xuwa dare gobe da safe sai mu isar da manufarmu a haka ya samu ya Dan lafar da fushin

A cikin gida kuwa Ahmad ne a gaban Nenne bayan ya samu Aysha ta lafa da kukan ya barta tare da Abubakar yana ci gaba da tausarta

zaune yake a gaban nenneshi ya daura kanshi kan cinyarta sai fidda wani nannauyan numfashi yakeyi cikin zuciyarsa sai tafasa takeyi da ka ganshi kaga tashin hankali

Allah sarki uwa da dan ta sai rabbi tuni Nenne ta gano yanayin da gudan jinin nata ke ciki a hankali tasa hannuta cikin sumar kanshi mai tashi da sheqi ta rinqa shafa kan nashi tana Dan shafa kumatunsa da daya hannun nata dai 2 kain kuncinshi taji damshi alamun hawaye😭 da sauri ta dago kanshi ta zuba mai ido shima itan yake kallo ya Sa hannayenshi 2 y daurasu kan nata da ta tallabe mai fuska 😭cikin zubda hawaye da muryar kuka bakinshi har yana rawa kamar maijin sanyi

Yace Nenne Na kingako nikuma kinga yadda rayuwa ta juyamin ya zanyi Nenne inason Aysha kuma Bappa Yaya ya hanani ita Nenne ke kadai zan gayawa naji sanyi ya kuma kamo hannuta yaci gaba da cewa wlh inasonta tana sona kuma an rabamu Nenne duk duniya bayanke da Abba ba Wanda nakeji kamarta

Itama hawayen takeyi cikin salon ni nacuceka ya kai Dana tace Ahmad ba laifinka bane ba laifin kowa bane laifi nane Nina kawo wannan irikitaccan al,amari Amman ka gafarceni D'ana da Sauri ya katseta da cewa ni baki min komai ba ni zan nemi gafararku

a haka baba bello ya shigo ya samesu suka hadu sukayi ta bashi baki da samai albarka

Da slm marsa da shigansa duk kusan a tare yayisu kuma duk batajiba har saida ya zauna gefenta daga dukkan alamu yanxu ta Idar da sallah

A Dan firgice tace kai me hakan wlh dudabe sai nakai qararka gun Aliyu Dan ka isheni ji yadda ka shigomin a fijajam bako slm cikin harzuqa yace ancemiki ni alulkitab ne da zanshiga wuri ba slm toh ai nidai banjiba

Hmm toh nidai nayi slm

bakadai yi da qarfiba kam

toh ni maroqine da Zan kama ihu a gari

oho dai tace masa ai tunda kin ga nine shikenan ga baki ga tsoro harara ta cillamai shi kuma yaci gaba da cemata dama baki ya Dan tabe ya kalleta a cukushe yace ke ni dama zuwa nayi ki...da sauri ta katseshi in baka lbrin ko toh nima bansan komai ba kan batun aurenku da akeson hadawa

Cikin qulewa yace keda Allah fadi ba,tambayaba ai duk surutn siya kin iya Amman da yake kinga INA roqonki shine kiketa wani jirgani toh ni bashixan tabbayeki ba zuwa nayi ki rakani mambila yanxu kafin manqqariba mun dawo baba bellone ya Aiken

aiko dajin haka ta miqe tana yauwa Dama inason zuwa toh mutafi Hajia a yawe

Oho dai sainaje Dan baqin ciki murmushin mugunta yayi aranshi yake cewa kedai komai fada

A hanya kaka sai bala,I take dan ganin hanyar Yola suka kama fada take ase Dama baka da mutunci INA zaka kaini ?

Sama zan kaiki ya bata amsa

fuskarsa Na kan titi yanata tsula gudu mita kam da masifa ya shashi Amman dayake mishkiline kafi mahaukashi ban haushi ko a jikinsa 5:00 pm suna cikin porlon baba Umar

By Garkuwan Fulani

[4/9, 2:25 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

MI,WASMITI...page2⃣1⃣to2⃣5⃣......Na Aysha Ali Garkuwa

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Bayan yan gaishe gaishe da sukayi sai suka Dan tsagaita

Kakace tace kai Dudabe ka bada aike Dan dere yanayi.

toh yace mata gami da Dan kallon baba Umar cikin yanayinshi Na rashin surutu ya Dan sunkiyar da kai gami da Dan sake dagowa ya kalleshi ido cikin ido yace

Baba dama zuwa nayi kamin taimako ka Duba Al,amarinmu ni da yan uwana sai kuma ya danyi shiru Dr Umar ya Dan jinjina kai yace fada min ba komai gayamin menene matsalar

Ya Dan kalleshi gami da cewa baba Dama ni batun Auren nan ne sai kuma ya kurawa kaka ido Dan jin wani uban salati da ta dago haydar ma idon ya zuba mata ta kalleshi a yatsine tace wlh Allah ko Yusufa (a wasmitan ) zakafa yi nadama ka kama bakinka Dan gaba wlh kana dab da jin kunya zakayi nadama gabafa wlh ka iye bakinka.....

Ke da Allah wayasa bakinki cikin zancen nan me hadinki dani bafa cewa nayi kirekoni kimin gatsali a zancena ba kuma wlh ki kama bakinki ni da wadanda suka isadani nake mgn badake karere ba ya qarisa mgnar yana mai watsa mata harara da zazzaro idansa woje Dr Umar yadan murmusa Dan Sani dama haka zata iya faruwa shi mmk mayayi sosai dayaga wai Yusuf ne da kaka a mota daya kuma tafiya mai nisa gashi ba Dan rabiyar fada a tsakaninsu

Yusuf ne ya katsemai tunanin nashi yana mai fadin baba

Wlh tallahi kaji nayi rantsuwar musulmi

ko baba bana son Aysha wlh Na tsaneta ko ganin ta bana son yi Sam banjinta a raina baba wlh Auren da kukeson hadawa wlh masiface baba ni wlh Na yarda ko mahakaciya Ku samo Ku hadani da ita matuqar zan tsira ban Aure Aysha ba

Kaka kam baki ta sake tana ware ido tana fadin wataran zakaji kunya wlh sai kunya ta hanaka ganin abinda ke gaban ka ni kam baza,ayi tijarar nan daniba barima ka gani woje zanyi

Hydar da shima Sam bai farinciki da Auren da suke son hadawan ya harareta yace kifi ruwa tafiya ya koma ya kalli mahaifin nashi yace gsky baba niba banason wannan hadin naku nafison ya Ahmad ne ya auri Aysha

Goggo Aysha dake gefe najin muhawararsu ta bisu da ido tana mai cewa Yusuf ai banan ya kamaceka kazo ka furta qiyeyyar da kake yiwa Aysha ba gun Umminka zakaje ka fada

ido ya Dan zaro yace wlh tace duk randa Na kuma furta mata wani zance akai zata tsinemin cikin kaduwa Dr Umar yace

Subahanallahi

Meyayi zafi haka insha Allahu bazata tsinema ba

Cikin yanayin lallashi ya dafa kafadarsa yace

Yusuf kayi haquri

Qaddara ta rigayi

Fata

Bani da wani zabi bayan Na Bappa Yaya

Yusuf nima cikin qarqashin ikonsa nake

Kayi haquri ka ruggumi qaddara

Kayi biyeyya ga iyayenka zakaga sakayya mai kyau

Wlh bani da ikon watsa Auren ka da Aysha da ina da iko da tuni Na watsashi

Ya kuma dafa kafadanshi yace abinda baka saniba Yusuf ya rigada an Dade da daura aurenku kai da Aysha

Tun Aysha nada shekara 8 aka daura aurenku

Cikin firgici da mmk tsosai haydar kam dake zaune kan hannu kujera bai san lkcin da ya zameba Yusuf kuwa baki ya bude kawai yana binshi da kallo a rensa yake cewa wadannanfa sun Dade da kamu da cutar haukannan bamu kula da wuriba

muryar hydar ce

Ta kuma bashi wani sabon tsoro

Hamma Yusuf toh ai Abu yazo da sauqi yoh ba sai ka saketa ba kawai

Cikin kaduwa ya kalli hydar cikin murmushin takaici yace yoh in banda abinka

Hydar ai Auren da ya halatta ayishi shi ake iya sakarsa toh kai ka yadda Auren ya daurune?

Kai ya jinji yace haka nefa Hamma Yusuf

Dr Umar ne ya kallesu cikin Solon yaro mankaza

Ya kalli hydar yace haba Aliyu ase kaima kna da baqin tinani wannan wacce iriyar shawara kabaiwa Dan uwanka Ali ban sanka da haka ba ya kuma maida dubansa kan Yusuf yace wlh Yusuf ina jiyemaka tsoro fushin iyayenka kaji tsoron Allah kayiwa iyayenka biyeyya shin kai bazaka yi koyi da Ahmad ba ka ganifa shi aka gwara Amman ba Wanda zaice ga qorafin ko furuci mara dadi dayayi kayi koyi da Dan uwanka

Haka dai yaita musu nasiha

Daga bisani suka kama hanyar taraba a motako yasha mita gun kaka

-------------------------------------------------------------------

8:27 pm ya sauqi kaka a qofar gidan ta kai tsaye gidan Anuty Sadiya ya wuce

A Can kuma gidan Anuty sadiyan tun bayan isha Ahmad yazo yana shiga bayan slmar da yayi bai kuma mgn ba

Ikram yarta tai gudu ta shiga bedroom tana mami ga uncle Ahmad yazo

Tare suka fito da ikram tana zuwa kan cinyarshi ta dale tana uncle xamuje gidan zoo ko kai ya Dan gyada mata ba tare da ya bude idoba

A hankali Sadiya ta kalli Dan uwan NATA cikin sanyin murya tace Ahmad ka rinqa mai maita innalillahi ka yawaita hamdala kaji Dan uwana ?

toh yace muryayarsa Na rawa hawayen da yake boyewa suka samu damar zubowa Allah sarki Ahmad duk jarumta irin tashi ga so Na maidashi rego ko yaushe idansa bai bushewa da qollah😭 haqurinshi ya fara gazawa cikin sanyi ya zame daga kan kujerar ya komai gefen Anuty Sadiya ya riqo hannuta ya daura kan qahon zuciyarsa yana mai Jan numfashi da qarfin yace Anuty numfashina tafiya yaketi kiji qahon zuciyata kamar zata stage ina tausayawa rayuwarta INA taushayawa biyaye a INA kuma tausayawa Maryam Dan zan aureta ne kawai Amman ba batun so kam gashi matsalar Aysha ko

tafi komai damuna a duniya wlh Anuty da mutuwa nayi da yafi min da wannan rayuwar gomin ko nasani Nanda Dan wani lkci zan mace Na barku ya daura hannushi kan jinyarta yana mai cigaba da cewa Ayyah

Anutyna zan mutum Na barki nabar Aysha zan barki da Yusuf da Adam Na tabbatar duk abinda zan miki zasu miki toh Amman Anuty duk duniya ba mai yiwa Aysha abinda zan mata biyaye baya Sonta bare ya riqemin amanart Anuty zanbar Amanar Aysha a gunki keda ummina ku kadai ne zaku iya riqemin amanrta bazan ba Yusuf amanar Aysha naba Dan nasan bazai riqemin ba Niko banason abin da zai gasamin Dan uwa

Kuka

Sosai sukayi cikin kuka mai tsuma Sadiya take fadin bazaka mutuba Dan uwana zakarayu zamu rayuwa tare zamu zamewa Nenne mu 3 tamkar da 30 Ahmad banda qawa ko aminiya kune kawayena kai dasu Yusuf

Ahmad ni INA gidan miji in kamutu zakabar Nenne mu da kewa

Rabi,u bazai iya mata kula da biyeyyar da kake matanba

Da Sauri yace Anuty banso Rabi,u ya kasance mai irin halina gashi ni yanxu hiyayyarce ke shirin rabani da duniya

Bazaka mutuba Cewar Abba cikin mmk Sadiya ta kalleshi tana Abba yaushe ka zo ?

Tun dazu nazo Sadiya duk naji hirarku Sadiya Yusuf Na Haifa Amman Ahmad shine jigona insha Allahu Ahmad bazai mutuba Shi daya da nake gani naji sanyi Abba kuka yakeyi harda hawaye Ahmad ya kalleshi cikin dauriya yace Abba dama kana zuwa gidan Anuty Sadiya ne ehh gashi kuma ka gani aini yawanci Abba kanxo muyita hirarmu Amman Sam baba shi baya zuwa ko kadan suka danyi dariya

Abba yace toh ai dama ni ya kamata Nazo bashi ba tunda shi yanaga gidan surkine ni kuwa gidan ma,aikacin asibitinane kuma mijin y'ata

Haka dai sukayi SLM suka tafi suna fita daga layin Yusuf kuma Na shiga Amman basuga junaba da yake akwai cikowar ababen hawa

Cikin tsoro da firgici Yusuf yayi kan Anuty Sadiya jikinshi har bari yake ganin halinda take ciki

Kuyi haquri masoyan wannan littafin insha Allahu zan Duba qorafinku nason Na yawaita Sa fillanci a ciki haka kuma INA Baku haquri da jinkirin da kuka gani

I love all makaranta wannan littafin

Fasaha Writers INA gaidaku Auntys din kamaluuuu

😝

By garkuwan Fulani

[4/9, 2:25 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

MI,WASMITI...page2⃣6⃣to3⃣0⃣ Na Aysha Ali Garkuwa

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Cikin kaduwa yace Anuty meke faruwa? ya Na ganki haka kiga yadda fuskarki ta kumbura ?meya sameki ? Haka ya jero mata tabbayoyin

Cikin qoqarin boye damuwarta tace

Kai Yusuf me haka ka firgice gaba daya kawai ciwon idone ke damuna kuma yanzuma Abba ya kawomin mgni

Hannuta ya kamo suka zauna kan kujera ya kalleta da kyau ya Dan kauda fuskarsa gami da yamutsa fuska

Cikin kula tace Yusuf meke damunka

Lips din shi ya Dan ciza gamida Dan kamo Na kasan yana tsotsa

Yusuf meke faruwa ne ka gayamin mana

Qara matsar lips din yayi yace Aunty Na tsani Aysha Na tsani Auren Anuty

Aysha fa burin Ahmad ce

Eh ita burin Ahmad ce Amman kuma zabin iyayenmu ne da suka zaba maka ita

Cikin takaici yace Anuty hardake bakya tuna makomarmu ba komai Yusuf insha Allahu ba wani Abu

Hmmm

Anuty ba haka naso ji daga garekiba Amman naga kema layinki daya da tsofaffinan

Cikin sanyi ta rinqa mai nasihar da shidai lebenta kawai yake ganin yana motsawa alamar mgn take

Can dai yace ni zan tafi har baking gate ta rakashi yaja mota ya tafi

Allah sarki yau kusan duk ba wanda yayi bacci Abba gaba daya ya karaya Nenne kuma kan sallahya ta kwana tanayiwa gudan jinin nata addu,a Yusuf kam abin ba,a cewa komai a jikin shi yakejin alamun ciwon zuciyarsa ke shirin dawowa Adam shima cikin tunani ya kwana shiko Ahmad ciwon da yakeji a zuciyarsa ne ke qaruwa kullum dare Anuty Sadiya kam kusan kuka ta kwana yiwa Dr Bashir mijinta kenan Dr Umar ma lamarin ya dameshi Ummi kuma tabbas tanaga an cutar da Ahmad haka dai kowa ya kwana zuciya a quntace

*************"*"""****** Yau Monday bayan maqqariba duk suna tare a parlor kowa da abinda yakeyi su Abba ma duk suna nan

lami mai aikice keta kacaniyar ta a kitchen

Abba ne ya kalli Usman yace je ka kiramin Ahmad toh yace gamida miqewa ya fita,,,,,,,,

Tare suka shigo kai tsaye gaban Abba yaje ya zauna baba bello Na cemai Ahmad Yusuf fa ?

Yana wonka ne baba.

toh yayi kyau

Cikin gyaran murya Abba ya kalli duk kan mutanen parlor ya zaro wasu document dinsa daga cikin jakarsa

Ahmad ya miqawa yace ingo duk inda kaga za,asa hannu ka saka cikin mmk ya kalli abban yace toh Abba bari Na jira biyayena

Ido ya Dan qura mai gami da cewa kai nasaka ba shiba

Ahmad bai iya musuba ko da abokaima bare da iyaye

Duk ya shiga budewa yanasa hanu daya bayan daya ya gamasu tas ya dagasu ya hada ya miqawa Abba

Cikin tsantsar qaunar Dan Dan uwan nashi yace toh mutanen parlon nan ku zama shaida bayan shaidawar Allah ☝🏻ni Aliyu Muhammad Aliyu Na baiwa Dana Ahmad company Na dake birnin Abuja Na bashi halak malak Na kuma malla kamai gidana da yake anquwar fada nanan cikin taraba

Gaba dayansu farincikine ya cika fuskokinsu ba abin da suke fadi sai

Masha Allah kai Abu yayi kyau Abba Allah ya qara budi Nenne kam kukan farinciki takeyi sosai baba bello kuma fada ya kama haba Ali kasan abinda kakeyi kuwa ?

Da Saudi Abba ya katseshi da cewa Dan nayiwa danka kyauta shine laifin

Cikin jin kunya baba bello yace a a wlh ba haka bane Ali Ahmad ai dankane Aliyu .

Toh inko kasan da haka barunka kasa albarka kawai haka kuwa akayi

Ahmad kam da ya zama mutum mutumi sai yanxu yaji bakinsa Na furta

Jzkllahu bil jannahπŸ‘πŸ» Abba ubangiji ya jibanci lamuranka gamida yin sujjadah yayiwa rabbi godiya murya Na rawa ya miqa mahaifinshi yace baba ganifa kyautat da Abba yamin Abba Na ya gamamin komai a duniya gaban Abubakar yaje yana kalli Sadip

Na gani ya fada gamida cewa ya Ahmad ka wuce haka a gun abbanka runqumarsa yayi sukayi ta farin ciki kowa yaji dadin wannan kyautar Usman kuma cewa yayi ya Ahmad tukuicina mata nakeso

Ka samu Usman key din motarsa ya cilla mai gamida cewa ga tukui cinka

Wow Rabi,u da Abdul ke fadi usmanko rawar choki ya kama harda juyi

Dai2 lkcin Yusuf ya shigo da Sauri Ahmad ya runqumasa gamida nunamai kyautar da ya samu gsky farin cikin Yusuf tamkar yamafi Na Ahmad Adam kuma cewa yayi dole ayi walima a gongoje

Wunin ranar dai farin ciki ya dawo cikin family din saka makon farin cikin Ahmad din sun shirya kan cewa ran jumma zasuyi waliman shiri sukeyi sosai sun gayato manya manyan mlmanmu Dr Ibrahim jalo jaligo dasu alaramma malam Sulaiman gasu shehk Kabir Gombe su isa Aliyu fantami duk dai anata shiri

Gaba daya shirin walimar yadan kauda damuwarsu kasan su Bappa Yaya tuni anxo Dr Umar ma da iyalansa abokan Abba Dana baba bello da dai dukkan yan uwa musulmai

Qaqa qara qaqa

Taro yayi taro gaba daya duk girma irin

7 / 38