Mis Wasmiti 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   6 / 38

15K to 18K   out of 112.1K words

yake fidda numfashi taci gaba da cewa zance fuskarka ba zahiri bane kai kace

Aysha bugun zuciyarkace πŸ’—

A.yanxu kuma sai ka shimfida ja rumtanka kan fuskarka Dan kawai kayiwa

Kakanmu biyeyya kan abinda bashi da iko a kai

Da qarfi ta riqe kafafunshi tana jijjigawa tana kuka

Ya Ahmad haqurinka zai cutar da rayuwarmu

Tuni jikinshi yayi sanyi sonta da yake dannewa qasan qoqon ransa da ruhinsa suka rinqa tsirgowa rauni sosai ya ziyarci zahirinsa

Hannunshi yasa ya runqumota tako manna kanta cikin qirjinshi tana sakin ajiyar zuciya hannunshi yasa yana share mata qwallar idanta sosai suke sauqe ajiyar zuciya Nenne kam tuni tabar porlon

Can kuma zuciyarsa ta darso zancen gskyar da aka rigada aka fada mai bashi ba ita kamar cikin razana ya balleta a jikinshi ya Dan tureta zai fita ta sake kamo hannunshi

Juyowa yayi cikin sanyin murya yace Auta Abba Na kirana ya janye hannunshi ya fita ranshi Na soyuwa

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

A hankali ya shiga parlon ya kwanta kan tattausan kujerar kaka ya harda qafafunshi ya daura laptop enshi kan ruwan cikinshi phone enshi kuma ya ajiye kan hannun kushin din ya lumshe idansa

Maganganun kakansu ke masa yawo a kai a ranshi yake gskanta jibewar Bappa Yaya numfashi ya furzar a hankali yaci gaba da cire abin a ransa

Kaka dake kitchen tana girke girkenta Na tsofoffi duk ta cika gidan da qamshin man shanu girki take tana ta zirga zirga kuma sai mita take ita kadai

Missxx ya Dan ja gajeren tsaki ita dai wannan tsohurwa bakinta bai iya shiru

Tazo parlon kusan sau 3 Amman bata ganshiba sai yazu da ta shigo riqe da akoshi sai qamshi yake

Tana ni bana son iyayi in zaki fito kici abinci ki fito irinku nawa akayi daga baya a dawo kamar za a hadiye juna...

Tsaiwa tayi da sauri ta kalleshi cikin da tsorita tace kai Dudabe yaushe kazo ban saniba ? Ai saikasa nai ihu mutum ko slm bazaiyiba

Shiru bai kulata ba ta sake ta kalleshi tana kai hannuta kan qafarshi da yake ta kadawa tace kai da Allah banson isa ehe Dan kai kazo ka sameni har gidana kuma inama mgn kamin banza

Duk dai bai kulataba ta juya ta ajiye akoshin kan santer table ta Dan matso tana ai nasani ba bacci kakeyi ba mutum sai baqin hali ni yau har ina murna bazaka zoba jarabatu kawai😏ta ja dogon tsaki ta juya zata tafi da Dan sauri ya kamo hannunta ba tare da ya bude idonshiba cikin rashin son surutun

Yace

Dan Allah ki nitsu mana shin ke bakya iya Abu a hankaline

Ya tashi ya zauna ya jawota gefenshi yana gsky ni

Yau ba fada zamuyiba mgnar gsky nakeson muyi dake kaka ta Dan harareshi tace kar kawani min zaqin baki ban da masaniya kan tabbayoyin da kakemin kullum batun aurene dai ba fashi kuma dolenka ita zaka aura

Ya Dan kauda kanshi daga gareta Dan yasan zai harareta kuma yana son ta Dan bashi wani qarin hske kan batun birkiceccen auren da suke ta tunanin zai yiwu

Hakan yasa ya kalleta a daqile yace wai ke gani kike zakumin dolene ni zancen yayanki kamar tatsuniya nake ganinshi wlh kin San bashi ya haifeniba bare ya wani haqiqance a kainaba

Tace aiko tunda ya haifi ubanka zance ya qare

Da sauri yace (hey oyani handebo hala mai habe kudina) ke hajia yau kuma abin naki harda zagine

Edin ai naga kaima zagemin Yaya kake da niyar yi

A a Na isa Na zageshi gaban qanwarsa

Da yafima kam ta bashi amsa

Kaka ya kirata cikin tausarta yaci gaba da cewa mgnar gsky ni dai yayanki bai isa ya Sani abinda bana soba Dan bashine ubanaba

Amman matsalata Dan uwana sun cusa tarin damuwa a rayuwar Dan uwana klonta yake cikin neman mafita yace ni shawara nake nema a gunki Dan ni kam kwanannan zan Koma gun karatuna Amman nafison sai Na tabbata Na bawa Dan uwana farin cikinsa cikin raunin murya yace wlh kaka komai zai iya faruwa da Ahmad Ku tausaya mai tunda shi mai biyeyyene a gareku

Duk yanayinshi ya sauya azahiri ake gane tausayin Dan uwanshi dake cikin ransa

Kai ta Dan jinjina tace Dudabe ( no mi watta be alkawal be wadi daga dubi cabfande tati e tati ) ya zanyi da alqawarin da akayi 33 years da suka gaba ta bazan iya hana komai ba

Kallonta yayi cikin jin haushi yace ke kullum abi daya kike gayamin bakya tuna haramcin auren da kuke cewa za,ayishi

Yarinyar da muka fito ciki daya da ita insha nono in barmata da yake duk kun jibe shine kuke ta babatu a kai toh wlh zan shiriya zanje Yola gun baba Umar da iyayen Ummi Na tunda kunfi son sai wasu sunji barnar da kuku tutiyar aika tawa zanje nace baba Umar ni banaso kar a kuma hada koda sunana da wannar mayyar yarinyar ni Na tsani koda ganintane ban ko qaunar tunata ya qarisa mgnar yana tattara phone enshi cikin klon yarinta da take mai tace Dudabe kar kaje zafa kaji kunya wata ran harara ya watsa mata yace dudabo

Wlh in baki daina kirana hakaba bazan sake zuwa gidankiba ai dama bani Na kiraka ba tabashi amsa

Aysha dake jin duk hirar da sukeyi tana tsaye qofar shigowa dama tunda safe tazo kafin ya shigone taje gun matar mai gadin gidan kakartasu itama kanta kaka bata San bata nanba tsaye tayi idanta tab hawaye bata lura dashiba sai jin da tayi ya yarfa mata mari yasa loptop enshi ya hanka deta ta fada qasa shiko yayi wucewarsa

By Garkuwa Fulani 09097853276πŸ“±

[4/9, 2:24 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

MI,WASMITI...page1⃣5⃣ Na Aysha Ali Garkuwa

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Tunda ya fita taje ta kwanta kan cinyar kaka tanata kuka mai shiga rai da gyar taita lallashinta

Cikin kuka tace ba gashiba ai kuna gani da idonku kaka wlh kun Sani sarai mugune 😑bai qaunata kuma shine kuke wani cewa zaku qullamai ni kaka gajiya dani kukayi shine kuke Neman Mae kasheni ko ???

a,a Aysha insha Allah bazai kashekiba da yardar Allah zaki zama Zahra ⭐a gareshi

Tashi tayi ta gyara mayafin jikinta ta tura Dan bakinta tace Sam kaka buku duba haram ko halal kan batun aurenan shiyasa ba amfanin sauraronku

Cikin kunar zuciya tace

Ni ya riqada zuciyata ta bushe zan daina tsoron Hamma Yusuf koda ko kasheni zaiyi ta juya tai tfyarta kaka Na kizo Aysha tace anqi zuwan

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Yau jumma,a kuma yaune baba bello da ya Abubakar suka dawo daga qasa mai tsari daga aikin umrah da sukaje gaba daya suna cike a babba parlon suna ta Dan hira Adam ma dayaje Yola jiya ya dawo Shiyasa suke cike a parlon sunata hira sai Aysha ne da take dakin su tayi shiru cikin tunanin. Ko meyasa ya Ahmad ke gudunta

Idanta a lumshe hawaye Na bin gefen fuskarta a hankali

Abubakar ya Sa hannunshi ya share mata qollar cikin lallashi ya dagota yana gyara mata gashin kanta daya Dan baje cikin tausarta yace ayyah autan Ummi meyasa kike kebe kanki daga cikin mu banajin dadi Sam nafison ganinki kina raha da walwalah Aysha ki yarda da qaddara ki jure zafin da kikeji duk abinda kikeji baikai abinda ya Ahmad ke jiba baki ga yadda ya dawoba Amman

A hakan yake bawa iyayenmu qarfin quiwar yiwa nasu iyayen biyeyyeh

Kanta ta manna a jikinshi taci gaba da sheshsheqar kuka tana ya Abbukar kafasan waye Hamma Yusuf kasan baida wani buri a duniya daya wuce yasani baqinciki ya Abubakar ko ka manta uwa daya uba daya muke a ina aka taba irin aurenan

Kai ya jinjina ya jawo hannuta suka nufi palon yana Aysha kada ki tsananta bincike

Ni zuciyata tsinkewa take sabida bansan meye a qasaba banson jin wani mugun qulli shiyasa banason binciken haka ya jata suka tfi

******* suna shiga tana maqale da hannuta cikin hannu Abubakar suka zauna ta daura kanta kan damtsen hannunshi

Ahmad dake sunkuye da kanshi sai yanxu ya dago ido cikin ido sukayi da qarfi yaji zuciyarsa Na duka Tara Tara

Cikin qarfin hali ya miqe ya Dan kalli Yusuf dake murtuqe da fuska yace (biyaye in dulliko) mu tafiko kai ya Dan girgiza mai bazaka tafi ba eh yace yaci gaba da latsa phone enshi shi kuma cikin hikima ya zame ya bar gun

Dakin shi ya tafi

Duk abinda yake binshi da kallo kawai take bayan fitarsa kadan ta Dan saki hannun Abubakar ta miqe tayi woje

A hankali ta murda qofar dakin ta shiga can ta hangoshi kwance kan gadonshi yayi ruf da ciki matsowa tayi ciken sanda tasa hannuta ta zare picture enta daya kifu a kai idansa ya rumtse gamida cije lips enshi cikin Dan dakewar murya tace bude idonka budesu ka kalleni ka gayamin meye a zuciyarka shin xaka gskanta zancenka Na baya ko zaka qaryata kanka da kanka

Kai ya rinqa juyawa cikin disashewar murya yake ta maimaita a,a

Hannu tasa ta dafa kafa dunshi tace ya Ahmad wlh kashemu kake son yi kallifa yadda ka dawo da rayuwarmu

A hankali yace Aysha nine da laifi meyasa kike qara azabtar da zuciyata?

Ehh kaine da laifi Ashe dama yaudara gsky ce maza nayi sannan kai sai ka rasa wacce zaka yaudara saini qanwarka kasan dama ba aurena zakayiba meyasa ka cutar da zuciyataπŸ’”

Ya Ahmad ka cucemu ta fada cikin kuka kan qirjinshi ta fada tana kuka 😭

Sosai tana Dan bugaga girjinshi tana dama baka sona ashe zancenka qaryane dakace Aysha ce bugun zuciyarka πŸ’—

A hankali zaciyarsa keta cushewa zancenta ke ratsashi idanshi ya fara budewa bakinshi ya fara motsawa zafi da yakeji ya fara bunqasa cikin rauni ya kamo hannuta ya daura kan qirjinshi

Yace kinjin har Abadan bazan miki qaryaba haqiqa ke Aysha kece buguzucitaπŸ’— Na gayamiki duk numfashin da zan zuqa da sonki nake zuqarsa wlh ina mai sheidamiki rayuwar Ahmad sauran kadan tunda aka tirsasawa zuyata fidda qaunarki Ayshaaa ki sani wlh duk randa Na gama cireki a raina toh tabbas a ranar zan barduniya🌍

Cikin sanantar kukan tace OK zaka ciren a ranka kenan ?

Eh Aysha ya zama dole naiwa iyayenmu biyeyyah da qarfi ya danna hannuta kan qahon zuciyarsa yace kiji har abada zan mutu da qaunarki hannushi 2 ya hada yace plxx Aysha( burtinam ha sudu am usenifu ta loru waru ha am)

Fitamin a dakina ina riqonki karki qara zuwa guna

Klonchi tai sosai cikin zubda qollah tace fitar numfashinka shi zai yanke nawa numfashin yayinda muka mutun zuciyar Dan uwanka dakafiso zata buga Dan rashinka ta sake kallonci tai murmushin takaici tace Allah sarki duniya su Abba zasuga tarin qawarwaki wataqil rashinka yasa Abba na barin duniya ayyah baba bello zai qunci takaici da dacin rayuwa

A hankali ta matsoshi tace yau zanyi ban kwana da kai kiss taimai kan kumatunshi yayinda shi kuma ya lumshe ido a hankali ya manna kanta kan qirjinshi can kuma ya Dan daqota ya manna mata kiss a goshinta ta kalleshi cikin yin murmushi takaici ta sake shi tafi tana suyar zuciya

By Garkuwan Fulani

[4/9, 2:25 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

MI,WASMITI...page 1⃣6⃣ Na Aysha Ali Garkuwa

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

----------------------------------

Haka dai rayuwa taci gaba da juyawa cikin quncin rayuwa

Yau jumma,a

Bayan an sauqo daga sallan jummaa

Duk sukayi gida

Cike suke a parlon

Sai Yusuf da Ahmad da basa gun

Baba bello ne ya dan kalli Usma dasu Rabi,u ya danyi gyaran murya yace kai Abdul tashi kuje parlona ku fitomin da kayayyakin dake ciki

To suka amsa gami da miqewa sukayi part inshi din

Aysha ya kalla a dan fizge gamida dan yafi tota da hannu a hankali ta dan saki hannun ya Abbakar ta miqe taje gabanshi ta dan duqa

Wani dan leda mai sheqin gaske ya miqa mata yana gashi ki kaiwa Yusuf kuma kice ina kiranshi dum zuciyarta ta Nada wani sauti

😳😳😳ido ta zaro cikin firgici tace baba ni kuma ?

Eh ya bata amsa gami da gyada mata kai

Cikin firgici da razana da bugun zuciyarta da ya tsananta πŸ’“ da gyar ta miqe dakin Ummi ta nufa riqe da laidar

Kaka da tazo bikonsu su duk sun daina zuwa gunta

Ta kalleta cikin wasa tace ke figi ruga yau ba mgn ne

Baki ta dan zunbura ta zauna gefen

Umminta tana rau rau da idanta tace ayyah Ummi dan Allah ki ajiye wannan in Hamma Yusuf yazo ki bashi wai inji baba

Kai ta dan girgiza mata

A a ni ban isaba ko ni ya aika dole nakai aiken ba wani nawa den ke kiwani ce sai ni zan bayar

Kaka tayi caraf ta karbe da cewa ai wannan ma rashin kunya ce

Kallonta tayi a lkcin da tamiqe tasa bayan hannunta tana goge qollah tana wlh Na Sani sai ya zageni kun sanshi sarai mugune 😑 banje inda yake bama Yaya ke kaka badai burinki ke da dan uwanki ku naqasamin rayuwa ba kusani kunci da takaici

Da sauri Ummi ta dan yimata don qolo

Kaka tai dry tace

Barta Fatima ai randa zatayi alfahari da hadinmu nanan tafe

Ita dai fita tayi tana dan qunquni

Zaune yake a dakinshi a qasa kan carpet jikinshi sanye da 3 qtr sai dan riga mai hade da hula ya Daga dukkan alamu woya yake

Ita kuma a tsakiyar parlon ta dan tsaya tana tunanin ya zatayi tayi slm shiru toh ko bayananne ta tabbayi kanta sabida tayi SLM yafi a qirga shirun da taji yasa

Ta danyi tinanin shiga dakinshi ta ajiye mai kawai

Cikin nitsuwa kanta a sunkuye tayi cikin dakin ba tare da tunanin ko yana cikiba sai xuciyarta dake bugawa

Bugun zuciyar ya tsananta a lkcin da ta shiga dakin kanta a qasa tana nufin ajiye mai kan gadonshi sai ji tayi tayi tuntube da qafarsa aiko tai taga taga ta fada kan kirjinshi

Da sauri cikin mmk da jin ta kaici ya hanka data duk da bai gama gano wayeba sabida duhun dake dakin

Itako tuni hancinta ya sheida mata shine qamshin turarensa yasa ta ganoshi shiyasa cikin sauri ta miqe gami da miqa mai aiken jikinta har bari yake cikin tsoro da rawar murya ta miqa mai ledar tace (da Hamma baba on vi mi waddine ) gashi Yaya baba ne yace in kawo ma

Fuska a murtuqe ya zaro ido ya buga mata tsawa yana ( salu vurti nam hado ) wuce ki ficemin daga nan

Tsoron sawar da masifarsa yasa ta dan saki laidar

Wasu yan takardu masu kyan gani suka watse a gun har kan qafarsa

Iskar pankar dake kadawa ya rinqa watsa su

Mmk sosai ya bayyana a fuskarsu su dukka cikin al ajabi da dimuwa yasa hannu ya dauko daya yana dubawa da fargaba sosai cikin minti 2 kamanninsa suka qara sauyawa bugun zuciyarsa ya tsananta numfashinsa ya fara dabur cewa idansa ya sauya daga yan qanana farare suka koma manya jajaye hatta jijiyoyin kanshi dana hannushi suka taso sama da wani irin yanayi ya tako ya nufi inda take

Cikin tsoron da take ta Sa hannu ta toshe bakinta da hancintaπŸ™Š da nufin hana kukanta fita sai hawayen daketa kwaranya a hakali ta rinqa takawa tana baya baya shi kuma yana binta har suka pito parlon

Ganin zatayi waje yayi saurin fizgota har saida ta fada jikinsa

By garkuwan Fulani

[4/9, 2:25 PM] β€ͺ+234 909 785 3276‬: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Mi,WASMITI..page 1⃣7⃣to2⃣0⃣ Na Aysha Ali Garkuwa

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Cikin takaici ya rinqa sakar mata maruka

Zuwa yanxu tsoro ko gudun dukan ya fita a ranta firgicin ganin i,v din Auren sun da suka gani yafi komai bada tsoro a gareta jikinta da zuciyarta duk sun qageshe

Zafi sosai Yusuf keji a ransa ya gama makancewa da bacin rai shiyasa baiji bai gani yaketa bugarta kallonta yake ido cikin ido a fili yake cewa badai ke kince taurin kaiba ba tsayuwa kikayi kina tsuramin shegun idanunki πŸ‘€ kamar Na matsafaba toh wlh kanki zakici mayya fitinenniya ya kuma hambararta tai baya 2 ta fadi bakin qofa a dai 2 lkcin Ahmad da Adam suka shigo parlon

Da sauri Ahmad ya sunkuyo ya dagota yayinda Adam ya nufi gun Yusuf din yana fadin

Haba biyaye me hakan anya kana cikin hankalinka kuwa ko dai ka fara shaye 2 ne

A harzuqe yayi kan Adam yana zazzaro ido woje yana eh giya nasha Adam ko kana da maganin buguwarnan tawane cikin mmk Adam yake klonsa kamar dai a bigen yake kam da sauri ya dakatar dashi hannushi ya jawo ya ajiyeshi kan kujera Goran Faro mai sanyi ya ballo ya miqamai karban Goran yayi ya cillata kan Aysha da sauri Ahmad yasa hannushi zai tare Goran cikin qeqashewar zuciya ta ture hannun ta kalleshi ido a bushe cikin yana yin dacin rayuwa tace barshi barshi ya Ahmad wlh ni a yanxu nafi buqatar azabar Hamma Yusuf ina dai sau daya ake mutuwa toh kubarshi ya kasheni ko duk ma huta wlh nafi buqatar zalumcin Hamma Yusuf din Don gwara nashi ai Ku naku boyeyyen zalumci kukemin wanda zai iya fasa zuciyata ta qareshi mgnar tana mai zubda qollah😭

Cikin sanyin jiki Ahmad ya kamota ya rugumota ya mannata a girjinshi yana Dan shafa kanta yana bubbuga bayan ta

A hankali ta rinqa sheshsheqan kuka mai tsuma rai

Yusuf da yake ta numfashi kamar zaki Dan zabar bala,i da zuciya

6 / 38