Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   9 / 25

24K to 27K   out of 72.9K words

kana cikin kitchen Winnan ba gaskiya. Kana jin wancan maras mutuncin abinda yake cewa."
Labbai bata gama Magana ba muka jiyo Hauwa na cewa.
"Abinda nake nufi ai kin sanshi. Ke da kikai aure a barikin baga mijin naki ba har gobe kuna cukume_cukume ba? To ga kuma ?arki mijinta ya leko yana gargasa mana Magana."
Kafin Adama ta fito Maigogul ya tsallako kitchen Win ya kama taliya yana bude mana.
"Hauwa dan ALLAH bama son neman fitina ku daure in kuka koma gida sai ku Waura daga inda kuka tsaya."
"A_a fa ya za'ai ta faWa mata magana irin haka?"
Cewar Labiban Hauwa. Adama tace.
"Na ci ubanki wallahi in haWaki da bango in sha?eki. Ji yarinya figigiya da'ita wai ni zataina rashin mutunci."
Da ?yar dai fitina a falon ta lafa sakamakon kallo da na fito na saka musu. Uwar Waki na koma inaso zan dakko kuWi in ba su labbai a samo kayan miya ko da da kifin gongonine muyi girkin dashi
Babangida yana banWaki dan ina jin saukar ruwa daga cikin banWakin. Jakata na dauka na fita.
Dubu biyu na ba Labbai da Sadiya. Basu daWe ba sai gasu da kayan miya harda kifi Wanye.
"Lolo ai a gidannan naku ana saida kifi ashe kala kala kin gansu manya. Kayan miyanma gida biyu ne tsakaninku mai kifin ce ta kwatanta mana muka siyo.
Maigogul yasa hannu ya karSi ledar kifin yana dubawa.
"Babu laifi yayi kyau. Kinga kin huta gya dinga siye. Uhm Aisha matsa kiga in yanka muku kifin sai in soya muku."
Matsa mishi Aisha tayi ya karasa inda wajen wanke_wanken yake ya soma yanka mana kifin. Mu kuma muna ta hira. Duk da zuchiyata a cunkushe da maganganun da Babangida ya zubo ma su Rakiya take. Hakan bai hana mu wasa da dariya ba.
Babangida ne ya le?o kitchen Win ko me zaiyi oho.
Ganun Maigogul a bakin famfo yana wanke kifi yasa ya buWe bakinshi galala yana kallonshi
Shi kuwa Maigogul sai ya hau dariya.
"Uhm kifine nake yanka musu ba iyawa zasu yi ba baka jiba da ?an?ara sosai wai nace inna soya musu ai na taimaka musu. Kasan lokacin suna yara wallahi ni nake yin girkin gidana safe rana dare, sai dai ranar da bananan sai iyayensu suyi. Kasan nayi girki a hotel gashi na iya haka siddan akaimun ma?ar?ashiya aka koreni ina kan ganiyata"
Tsaki Babangida yayi yace.
"Ni Babangida na shiga ukuna wannan wacce iriyar ?addarace ke bibiyata haka?"
Aikin banza aikin wofi"
Na faWa da tsiwa tare da hararar Babangida na ja dogon tsaki.
Ta gefenshi Maigogul yake so ya raSe ya fita. Ni ko dan in ?ara ba?anta ma Babangida sai cewa nayi.
Dama kayi mana miyar kifin Maigogul yaushe rabon muci girkin da kayi mai daWinnan"
Yana jin haka ya washe bakinshi yana farin ciki. Sai naji tausayinshi ya kamani.
Babangida na tsaye na kunna ma Maigogul Wayan gas Win.
"Mi?o abun tuya da mangyaWa. Lallai yau zaku ci miya ?ar kwatano takumbo kenan"
Babu shiri Babangida ya koma ciki fu.
Da harara na bishi, su Adama kuwa sai ?unshe dariyarsu suke yi.
Haka muka gama dafa farar taliya da makanoni sai miyar jajjage wacce ta wadatu da kifi.
Maigogul da kanshi ya rarraba mana shima ya zuba nashi, Uzairu zuchiyata ya dinga rarraba musu.
"Lolo wannan ki kaima mijinki"
Ya mi?o mun abincin a plate.
A_a yadda yake ciki da rashin mutuncinnan nasan ko na bashi ba ci zai ba. Ku dai kuci ku ?oshi kawai"
"A_a Lolo ke dai kai mishi koma baici ba kin bashi. Kinga irin wannan daular da Allah ya huwace miki samunta? Kada ki sake Babangida ya sake ki duk wuya duk rintsi. Kai mishi dai ki zo kuci abinci da ?an uwanki"
KarSa nayi na shiga uwar Wakin.
Yana kwance yana waya da mace dan naji ya ambaci baby.
Baki na taSe tare da ajjiye mai abincin a durowar gefen gado ina ?o?arin wucewa ya ri?o hannuna.
Da sauri na juyo ya wani kashe mun idanu.
"A_a Baby zamu haWu da yamma. Yanzu ina gidane inaso nayi bacci. Amman baccin ma ya gagara jama'a ce cike da gidan nawa ma"
Tsaki nayi tare da fusge hannuna ina shirin fita yayi saurin kashe wayar ya cabkeni ya jefa a gado yana nunani.
"Wai dame kike ta?ama ne. Ni kike ma tsaki dan uwarki?"
Ba dai uwata ba kasan uwar da kake zagi dai"
Ina faWan haka ya duro a kaina. Muka shiga dambe da gaske. Da ?yar na kwace kaina na fito.
Muna gama cin abinci ba'a daWe ba su Maigogul da su Rakiya, da su Ma'aru sukai mana sallama. Kafin su tafi saida maigogul yayi mun miyar sutu mai daWin gaske taji soyayyen kifi.
su Adama kuma muna gama hutawa. Adama taima Mardiyya wanka na shiga na Wakko mata kaya lokacin Babangida yana bacci. Wankan nima nayi na saka atampata daga cikin kayana da suka kawo mun daga gida. Duk da ?ar Shuwa ta kwashe rabi da kwatan kayanma.
wanke_wanke da gyaran kitchen da bubbuWe wasu kayayyakin da ba'a buWe ba muka soma. Muna ajjiye komai a muhallinshi bamu muka kammal ba sai azahar.
Lokacin Sallah nayi Babangida ya fice.
Allah ya taimakeni bai dawo gidan ba.
Abincin dana kai mishi kuwa ko taSawa bai yi ba.
?wafa nayi na Wauki plate Win nakai na rufe abincin a kitchen.
Labbai na kitchen Win tana mana jallof mai kifi ?amshi duk ya kaure ko'ina kunsan kifi da ?amshi.
A ta?aice dai sai magriba su Labbai suka bar gidana.
Na Wibar musu abinci mai yawa musamman ma Rahama.
Babangida bai tashi dawowa ba sai wajen biyun dare yazo yana buga mun ?ofa.
Cikin bacci na jiyoshi haka nazo na buWe mishi. Nayi komawata gado na kwanta.
Shi kuma yana tsaye yana jera kayan sawarshi daya tawo dasu cikin jaka.
Gaga_gaga haka rayuwar taci gaba da garawa.
Babu daWi sam zaman gidan Babangida. Dan bamu da aiki sai faWa, har dukana yake yi duk da nima bawai barinshi nake yi ba.
Matan gida bamu daWe ba suka gane Babangida maras kirki ne ta Sangaren iyalinshi.
Mu'amalarshi mai kyau da mutanene da kuma sakin fuskarshi, ga yawan larabci da kawo hujjoji da hadisai yasa ake ganin kamar nice marar kirki ba shi Win bane.
MRS BUKHARI
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA TAKWAS 8
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI.



To kunsan sha'anin gidan haya musamman gidan yawa. Sai ya zamana ko a hira sai kuji suna faWa mun magana.
Ni kuma a lokacin ba kanwar lasa bace ya zamana bana shiri da kowa a cikin gidan sai mace Waya Maman Hidaya itama tsohuwar ?auriyace shi yasa tamu ma tazo guda.
Haka dai al'amura suka ci gaba da tafiya. Watana huWu a gidan Babangida babu abinda ya taSa shiga tsakaninmu na mu'amular aure.
Kuma ya dena kwana a waje sai dai fa sai dare ya raba yake shigowa cikin gidan yaita buga mun ?ofa matan gida na jinmu kullum.
Wani sa'inma daya shigo zamu kaure da rikicin da zai iya kaimu har asuba muna abu Waya.
Dan wallahi in rikicina ya tashi da kaina nake rarumarshi da damben, ko in fasa mishi wayarshi da zaran wata ?ar bajala'u ta kirashi.
Daya ga haka washe garin dana fasa wayar da mace ya kwanta a gadona ya jefoni falo a ?asa na kwana ina kukan ba?in ciki.
Mardiyya kuwa bai taSa Waukar yarinyarnan ba kwata_kwata ko kuka take yi a kusa dashi baya Waukarta baya kuma rarrashinta sai dai yaita kallonta kawai.
A wata biyar Winnan sau biyu naje gida, shima da ?yar Babangida ya barni. Saida na sauka a ?ofar layinmu na gane ashe Babangida na biye dani a machine. Bai gushe ba har saida yaga na shige gidanmu tukunna.
Yau dai tun sassafe nake ta aikace_aikace sabida gobe akwai biki a gida na Adama da ?ar Shuwa kuma duk a gida za'ayi anko ma iri Waya muka yi .Ankon da sai da Baba malam ya saka baki kafin Babangida ya yarda yayi mun. Kuma ya saka shi ya bani kudin gudunmawa.
Ina zaune Malama Babba ta korani a waya ta zage ni tas ta inda ta tsikara ba tanan take jawowa ba duk akan kuWin ankon da akasa Babangida ya bani ne kuma.
Tana tsaka da maganarta ma na kashe wayata a hakanma nayi mata da ?auna tunda dai ban faWa mata magana ba.
Da daddare ina kwance a kan kujera ina kallo. Mardiyya kuma tana Wan wasanta a ?asa ta rarrafa can in kamota ta sake komawa.
Tunda dai ta soma rarrafe da mikewa tsaye kullum bata da aiki sai rigima da fasa mun abubuwa.
Na tashi zan kamota a gaban tv Babangida yayo sallama ya shigo.
Juyowar da zanyi naga ni yaketa kallo idanunshi cike da ruwan sha'awa.
Dogon ba?in wandone a jikina sai farar top da na saka matsattsiya kaina babu Wankwali sai sabon kitson da wata mai kitso tazo ta yarfamun shuku da na gaba.
Ga ?unshi nayi dai haka.
HaWe rai nayi na dawo na zauna.
Kujera ya samu ya zauna
"Sabuwa babu ko sannu da zuwa""
Rijalu kenan in suna son abu sun iya kwantar da kansu.
Ai Rakiya bata koya mun ba ka tuna?"
Nayi maganar idona na kan tv.
Murmushi yayi wanda in ba dan yana bu?ata ba sai dai mu hau sama mu duro.
"Toh a kawo mun abincina ko shima Rakiyan bata koyar dake yadda ake ba miji abinci ba?"
Banza nayi mishi na nuna mai abincin akan tebur na ajjiye mishi komai da komai.
Hatta akan abinci saida Baba Malam ya kirani yayi mun faWa kafin na soma yin girki dashi.
Ko da gara ta ?are babu laifi ya siyo abinci ya jibge har nama da kifi da kayan miya masu yawa ya siyo na adanasu a gidan ?an?ara.
Sai dai fa baya bani ko asi komai dai ya siyo ya ajjiye, ko kitso nake son na sabumta dole saina tambayeshi. A nanne yake yin yadda yaso kafin ya bani. Ko zai bani kai da kai yake bani, koma ya bani bai isa ba.
?aukar ?ata nayi a ?asa harta soma bacci muka shiga ciki. Dan sa?on da Babangida yake mi?o mun ya soma tasiri a jikina. Nima dauriya kawai nake yi.
Ina shiga ciki na shinfiWe Mardiyya da baccinta yayi nisa a gefe. Ina da burin siyan gadon yara amman ina bani da kuWin haka dole na ha?ura.
Shirin bacci nayi na yi kwanciyata na ba ?ofa baya.
Can Babangida ya shigo shima ya gama abinda zaiyi ya kwanta.
Sai da dare ya kusan rabawa naji yana lalubena.
Hannunshi na ture tare da juyowa cikin tsiwa nace.
Meye wannan kuma kake yi.?"
"Halalina nake nema wasu ?an iska ma aka basu balle ni da aka ?a?abamun ke ?addara mai munin gaske"
Ai ku ake rabama ?a?an iska sai ?an iska irinku"
Ina faWan haka ya ru?unkumeni dambe sosai ya kaure a tsakaninmu duk na yakusheshi, shi kuma yai mun wulakancin da wallahi da safe da ?yar na shiga cikin ruwan zafi. Kafin na samu salama. Ina zargin maganin ?arfin maza ya afa duk da dai dama a wannan fagen bashi da tamka a cikin mazajen da nayi mu'amala dasu.
Haka raina a jagule na isa gidanmu aka shiga hidimar biki.
Kwanana hudu a jere ina sunturin zuwa gida dan Babangida ya?i fur in je gida in an gama bikin in dawo. ?ar Shuwa dai Allah yasa nan Dutse suka soma zama mijin nata ya samu aiki a jigawa sai ya tattago matarshi ya siya musu ?aramin gida can muka kaita dai.
Muna gama bikinsu ?ar Shuwa kuma aka shiga bikin gidansu Babangida za'ayi bikin mutum biyar Alawiyya da Sauwama sai maza uku biyu ?an dakin Malama ?arama Waya Wan Wakin su Babangida.
Daga lokacin na soma sanin ashe ma gidan babu wani haWin kai na azo a gani. Dan dai suna da ilimine shi yasa suke yin abun na hankali.
Biki dai rana Waya akeyi amman ko wanne Sangare da ankonsu, abinci ma bambamcewa akayi.
Surukan gidan kuwa sai lokacinne nasan adadinsu da kalarsu.
Sai dai fa ko wacce wani irin kallon gani_ gani take yi mun. Duk inda na gilma ni da Sadiya dake ri?e da Mardiyya sai inga ana zunWena.
?anne da yayyen Malama Babba kuwa sai da suka ci mun mutuncin da duk taurin raina saida na zubar da hawaye. Nima na farfaWi maganganun da ya jawo rikicin da Malam Baba yace in koma gidana washegari buWar kai bama sai nazo ba.
Gaga gaga
Wata na takwas da aure Babangida yayo aure wata ranar juma'a.
Ina kwance naga ya shigo da magriba abunda bai taSa yi ba kenan. Saye ya shigo da farar malum_malum sai ?amshi yake zubawa.
Ban isheshi kallo ba naga ya Webi kayanshi a jaka ya jejjera ya kwashe turarukanshi daya jera a gaban mudubi.
"Kizo ki kulle Wakinki ni yau aka Waura mun aure da budurwa tiya leda ba irinki tokumbo ba. Gangariya ba irinki oshele ba.
Yarinya ?ar gidan malamai ba irinki ?ar gidan kawalai ba. Dan haka ni na tafi saina gama dandalar romo tas."
Ficewa yayi.
Sabida tsabar zafin kalmominshi, da kishin da banyi tunanin zanyi akanshi ba yasa idanuna suka rufe.
Ganin zai fita ya barni da cizon yatsan ban mayar mishi da martaniba yasa na duro a guje naje na sha gabanshi.
Ai wallahi baka isa ka faWa bam mayar maka ba"
Dariya yayi tare da buWe baki zai yi magana nayi wuf na rigashi.
"Da kake kirana tokumbo. Ai ire irenku suna numfashi a doron ?asa ba za'a taSa dena samun mata tokumbo ba.
In kuma juninka neman matan banza ne da sannu zaka tadda wacce zata zama ajalinka.
Aure da kayi ko a jikina.
In sha ALLAH ba zaka taSa samunta yadda kake tsammani ba. Murhu sai tukunya Wan banza sai ?ar banza.
Ina gama faWin haka na koma ciki da sauri na kulle ?ofar uwarWakin na shiga aikin zurga zurga.
Wallahi kishi masifa ne mata. Kar kuyi mamaki dan nayi kishin Babangida.
Har ga Allah ai ina sonshi sosai kuma dai kun sani
Kuma ko auren dole aka ma mace da mijinta ranar da zai kawo mata batun ?arin aure dole sai taji babu daWi a ranta. Nasan masu kishiyane zasu biya wannan karatun. Marasa kishiya sai dai suce Sabuwa tayi asara ko menene na kishin Babangida oho.
A wannan daren sabida tsabaragen masifa ji nayi kamar in ?ona kaina in huta. A ranar na gane dare da tsawo yake.
Washegari sassafe ina gama aiyukana na wuce gidan ?ar Shuwa takwas a ?ofar gidanta tayi mun. Dama munyi waya da'ita a daren jiya ta sanar dani miji ba'a Wakinta yake ba. Kuma itama tana cikin matsala babba.
Ina ?wan?wasa ?ofarta kishiyarta ta wani le?o tana cewa.
"Waye haka sassafe dan rashin hankali. Mai gidanma ba za'a barshi yayi bacci ba"
Tana le?owa muka haWa idanu irin kallon dana watso mata ya tsoratata sosai.
Tana dai tsaye har ?ar Shuwa ta buWe mun ?ofa.
"Aisha ba?uwa da sassafe haka kika yi. Kamar Sabuwa ?awarki ko?"
Kuji gulma wato dai kishiyoyi akwai gulma wallahi WaiWaikune masu iya Wauke kansu ga sha'anin kishiya.
"E wallahi ai Sabuwa zata iya kawo mun ziyara a duk sanda naga dama sabida ?ar uwatace"
Hannuna ta figa muka shige ciki.
A kujerarta na zauna.
Ita kuma ta shiga Wan kitchen dinta da kamar karin kumallo take haWawa.
Jinta shiru yasa na shiga kitchen Win na sameta a gaban doyar da take soyawa a zaune ta gasa tagumi tayi shiru.
Bata san na shigo ba har saida na dafata tukunna ta juyo da sauri. ?urama juna idanu muka yi dukkanmu muna cike da damuwa.
Doyar zata ?one ki kwashe tukunna sai mu nutsu muma juna bayanin matsalalolinmu.
Doyar tayi maza ta kwashe ta toya mana ?wai guda biyu da ruwan tea.
Muna kan karyawa take zayyyanu mun irin matsalolin da ta soma fuskanta daga kishiyarta na makirci da haWata faWa da miji duk ran kwananta.
"Kinga jiya a Wakina yake wallahi har tsirara nayi a gabanshi amman ko gezau da kika sani. Duk wata hanyar maWe da hilatar Wa namiji kinsan na iya Sabuwa ni gangarance a wannan babin. Amman ace kayi aure miji kuma ya Waukeka da kai da banza baku da maraba. Shikenan duk soyayyar dana iya a bariki zata ?are kenan. Duk yadda nake tafiya da imanin maza ace nawa mijin na kasa tafiyar dashi. Shikenan tarairaya da nuna kulawa an barma mazan bariki kenan?
Kai na jinjina ina taSe bakina.
Ni duk wani iskancin Babangida wallahi baima taSa damuna ba wallahi. Nifa jiyane kaWai Babangida ma SirSishin sonshi da kishinshi suka tashi mun da yace yayi aurennan.
Tunda haka yake miki ki share shi kawai kiyi harkokin gabanki. Tunda naga matar tashi in jeraku za'ayi ko sisi babu mai siyanta."
Dafa mun cinya tayi tace.
"Sassauta murya dan kamar tana laSe wallahi. To ai inna barta ta samu galaba a kaina kenan. Ni haihuwa nake son nayi tunda ita kanta albarkacin yaran take ci. Kuma dasu take yi mun gadara.
Akan ?arta ta goye fa sai ya sauka a kaina muna mu'amalar aure ya tafi sabida kawai yaji kukanta mafiya yawan lokuta shiryawa kawai take ta saka yarinyar kuka dan ya baro Wakin nawa.
Wani sa'inma baya dawowa sai in yayo sallar asuba.
Sabuwa babbar matsalata fa shine matar tashi wallahi duk bala'ina kamar tsoronta nake ji. Kinsan Allah ko haWuwa muka yi gabana yata faWuwa kenan. In naji muryarta a tsakar gida bana fitowa sai dai in ta kama dole. Gashi yana cewa zai mayar damu maiduguri kawai can kuma a gidan gandu suke kinga in muka koma yaya zanyi? "
Mun jima sosai muna tattaunawa da Yar Shuwa nice har la'asar kafin na baro gidanta.
Sai naji na Wan samu sau?i babu laifi dai
Haka naita zuba ido yau Babangida zai dawo a_a gobe ne shiru har saida ya kwana ashirin cib da magriba sai gashi lokacin ina kaWa miyata ta yau?i nayi tuwona na alkama.
?urama juna idanu muka yii kowanne cikinmu da abinda dai yake sa?awa a zuchiyarshi.
Nice na soma kawar da kaina.
Dana gama girkina bayan ya dawo sallahr isha na zuba mishi yaci.
Haka zaman yaci gaba da tafiya babu daWi cin mutuncin iyayena da cin zarafina babu wanda Babangida ya fasa saima abinda ya ?aru.
Ya tsani yaga su Adama a gidana, ya kuma tsani ince zanje gida ganin gida.
So da yawan lokuta yana korar su Adama haka dole suke fita zukatansu a jagule kuma suna ?yaleshine dan gudun kada su turguWe mun auren nawa. Har Maigogul Babangida ya taSa kora wallahi a nanne Maigogul ya zazzare mishi idanu ya nuna baifa isaba. Inaji sun daWe suna faWi in faWa. Cin fa mutunci da cin kashi babu wanda Babangida bai mun ba, babu

9 / 25