Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   13 / 25

36K to 39K   out of 72.9K words

gaske nake rerashi kamar wata ?aramar yarinyar goye.
"Iko sai Allah Lolo kece kika dawo ashe zaki dawo garemu mu har mun cire ?auna da sake sanyaki a idanunmu. Duk rintsi kada ki sake tunanin guduwa mu tsaya ma kanmu da kanmu"
Cewar Uzairu zuchiyata dake tsaye kusa daf da mijin Adama.
"Ya isa haka Adama ido ya soma yawa."
Labbai tayi maganar tare da SanSareni a jikin Adama
Tare muke da ba?o Adama. Yana so yaga su Rakiya"
Kafin ma in rufe baki har ya ?araso inda muke da sallamarshi.
"Allah sarki bawan Allah kaine ka tsinceta kenan? Tawo mu shiga daga ciki. Su Maigogul basa nan Hauwa ce kaWai a gidan."
Kallonshi nayi nace.
Yaya mu shiga kaji basa nan. In ka sake dawowa ka gansu"
Muna gaba yana biye damu har cikin Wakin su Adama wanda naga sun samu arzikin gyarawa har da gas ?arami, ga Wan kayan abincinsu a gefe.
Waje muka bashi akan kujerar ya zauna shi da Uzairu zuchiyata wanda hankalinshi yana kan wayarshi ma.
Mu kuma muna kan katifa.
Gaggaisawa akayi Dr Kamilu ya kwashe kab halin daya same ni ya basu kabari da dai irin jinyar dana sha duka komai dai.
Ajjiyar zuchiya Adama ta sauke.
"Tabb ashe daman akwai bayin Allah irinka? Bawan Allah mun gode maka da iyayenka baki daya Allah ya saka da alkhairi.
Ni na tashi daga bacci na tarar bata gidan cikin dare ta fice. Kuma ta fita ne a cikin wani irin mawuyacin hali mai muni. Alhamdulillah data faWa hannu nagari. Jiya jiyannan naje na dubo su Mardiyya inata dai basu ha?uri kan rashin uwarsu da irin zaman da suke yi a hannun matan uba.
To iyayenmu har yanzu suna kan bakarsu akan ba'a isa an kashe wannan auren ba. Ita kuma Lolo dama tauri gareta inta botsare kamar gandar kai haka take.
Amman dai zamu kuma tuntuSarsu Allah bashi in suka ji irin halin data shiga fitar data yi ko zasu sassauto"
Dr Kamilu ya gyara zama yana kallon agogonshi.
"To a dai fahimtar dasu ba'a zaman aure da zalunci. Haka zalika ba'a aure dole balle irin nata auren mai cike da zalunci. A irin kondishon Win da take ciki ba'a bu?atar ko tunani ta yawaita balle shiga wata damuwa.
Inaga Sabuwa ni zan tafi ko zuwa dare sai in dawo inaso shi Baba mu gana dashi ko zai fahimceni"
Da sauri na Wago Labbai tayi carab tace.
"Ai shi tafiya yayi Allah kaWai yasan yaushe zai dawo ma. Sai dai in ya dawo ko a waya ne saita sanar maka"
Muka haWu muka rakashi har bakin motarshi muna mishi godiya marar iyaka.
Kayana ya sauke mun
Muna shiga Wakin sai ga Maigogul ya faWo Wakin afujajan babu ko sallama.
Tsaye yayi hannunshi ri?e da ?ugu yana kallona tar.
"Lolo kece ashe da gaske ashe zaki dawo garemu?"
Nice Maigogul "
Sai kuma naga ya zauna yana ?are ma Wakinsu Adama kallo
Labbai na gaban tukunya tana zuba abinci, Uzairu zuchiyata ko hankalinshi na kan waya sai murmushi yake yi.
"Lolo sabida mun hana mijinki ya sakeki sabida ke ?ar abu ta kazan ubace shine kika tafi wajen shi Khalid mai hure miki kunnen gabaki Waya ayi duk abinda za'ayi ko?
Ai kin bamu mamaki kuma baki cika ?ar duniya ba da kika dawo. Sannan da kika tawo wajensu Adama kin kaso auren ne hankalinki ya kwanta ko?"
"Haba Maigogul wai me yasa baku damu da rayuwarmu bane, ku dai kan ku kawai kuka sani?"
FaWin Adama kenan. Da?uwa yayo mata.
"Ohh sabida kuna zawarci shi Dakacin da yake zuwa wajenki yana baza ?aryar kaya ya kasa turo iyayenshi. Mijinki yanzu haka yana gida amman kin ?i bashi haWin kai shine ita kike so ta kaso auren nata. In ta kaso kika san waye zai zo ta aureta? Sannan in hakane baga can mijinki yana ta godonki ki koma kin ?i ba sabida kina neman mai?o ba. Shine ita kike son rabata da nata mai?on da yake hannunta ko? Kuma ai ko dan Mardiyya ai ta daure tayi ha?uri. Lolo mufa dukka wannan akan sonki muke yi wallahi Allah"
Adama tace
"Shikenan tunda haka kace a mayar da auren shi Alhaji in yazo zan faWa mishi na koma gidan mijina shikenan ai. Inata faWa muku saki ukune aure ya ?are a tsakaninmu ?aryace kawai yake yi muku"
"Ni dai bance miki haka ba Adama. Ba haka nake nufi ba ehe"
Sai naji yayi ?asa da muryarshi. Harma da bagarar da zancan ta hanyar cewa.
"Labbai mi?o mun inci in tafi. Hiye harda kifin gongoni kuke girki ni ubanku kun barni cikin wahala"
Kai kawai na girgiza ina jin ba?in ciki tamkar yayi ajalina.
Saida ya zuba loma a bakinshi kafin yace.
"Kici yanzu in mayar dake Wakin ki tun kafin kayi nayi ta dawo."
A_a Maigogul wallahi Allah na gama auren Babangida bazan sake zaman aure dashi ba. Na gwammaci in kashe kaina kowa ya huta tunda ba ?aunata kuke yi ba"
Na ?arashe maganar cikin tartsatsin kukan ba?in ciki.
Adama ta shiga labarta mishi halin da na shiga da duk labarin da Dr Kamilu ya basu. Uzairu zuchiyata ya Waura da cewa.
"Yarinyarnan tana fa da ?ancinta a wannan karon mu ?an uwanta wallahi sai inda ?arfinmu ya ?are daga nan har kotun Allah ya'isa. Wannan karon har ku in bakui wasa ba wallahi a kotu zamu maka ku a cire mana hakkunmu. Yanzu fa da a ?asar wajene hukuncin ma kisa za'ayi muku"
Labbai tace.
"Tabbas kuwa a wannan karon dole sai Lolo ta rabu da mijinta tunda dai tace bata yi. Bari ma in kira su Rahama in sanar musu da dawowarta. Mardiyya ma akwai waya a hannunta bari in kira su ro?i Babansu suzo"
Nan da nan ta kira su Rahama. Tana kashewa ta kira Lambar Mardiyya ihun yaran naji suna karanto adda,ar godiya ga Ubangiji
Ai sai kukana ya tsananta."
"To ai shikenan. Na tsame hannuna a kan sha'anin Lolo. Ai kowa rai yaima daWi ba kamar maishi ba. Kuma duk daWin inuwar gemu taba kai ga ma?oro ba. Allah ya baku sa'a mu ?an kallo ne. Nauyin ki ba a kaina zai ?are ba inma kin fito yawon tazubas kike sha'awar komawa gaki ga duniya. Har ku koma ga Allah ba ku isa kunyi abinda ni ko uwarku tayi ba. Kai kuma da kake cewa a yanke mana hukuncin kisa Bismillah. Lolo kiyi ha?uri ki dena kukan haka kukanki na dafani kinsan sonki"
Kwanon daya ci abincin ya jefo ma Adama a fuska ya fice.
Hmm kaWai na iya cewa.
Idona kawai na runtse na kwanta na juya bayana kawai.
Ina jinsu sunata hirarsu har Rahama ta ?araso, su Sadiya ma duk suka shigo da suka dawo. Harda Hauwa saida ta rarrafo tazo ganin ?wab. Rakiya ma tun kafin ta dawo gida labarin dawowata ya isheta.
Itama ansha tababa da'ita su Adama ke Magana ni ko bana ko buWe idona ma.
Ma?ota sukaita shigowa munafurcinsu ni dai sai dai ace musu bacci nake yi.
Idanuna biyu ras.



Mardiyya:.
Suna zaune tana ba Malama maganin da Babansu ya kawo mata na mura tana sha. ?ar Shuwa tayo sallama ta shigo tare da tsayawa a kansu.."
"Ba wanki kike mun ba ubanme yasa kika barmun wanki kika dawo wajen wannan makirar yarinyar. Ke ga mai ?anne ko?"
AWWa'u yace.
"Ita ba makira bace wallahi. Kuma in ummin mu ta dawo saina faWa mata duk dukanmu da kike yi"
Ai kafin Mardiyya tayi magana tuni Yar Shuwa ta makanta ganin AWWa,u da wani zazzafan gigitaccen marin da sai da ya shiWe.
"Kaji mun ?aramin marars kunya. Ko da yake barewa ba zata yi gudu Wanta yayi rarrafe ba. Tunda ka Tsotsi nonon Sabuwa kuma jinin Maigogul da kayi nayi yana yawo a jikinku dole kayi.
Ke kuma dan abu ta kazanki zaki wuce ne ko saina Sallaki?".
Da sauri Mardiyya ta dure Malama ta fita ta koma kan tulin wankin da ?ar Shuwa ta tula mata dana Fati dana Babangida ma.
Zuwa tayi ta dasa kujera tana kallon Mardiyya tana zage_zage.
Wayar da Babangida ya mallakama Mardiyya dan ya dinga jin ya suke in baya nan. Da kum su ri?a magana da Sauban itace ta shiga ruri. Ganin number Labbai yasa ta Waga da sauri. Ai tana jin abinda Labbai tace sai ta mi?e.
"Kika ce Umminmu ta dawo? Alhamdulillah"
Iyakar abinda tace kenan ta kwashi gudu sai Waki.
Su Aminu suna kan Malama da take ta faman kukan ciwo. Mardiyya ta shigo sa gudu ta Wauki hijabinta ta saka.
"Ku taso muje wajen Babanmu ya bamu kuWin mota Umminmu ta dawo.
Ai nan suka shiga murna a gaggauce suka fito ?ar Shuwa sai kwaWama Mardiyya kira take yi amman ko waige.
Da wani bawan Allah suka ci karo yana neman Wan aike. Ganinsu yasa ya tsaidasu.
"Ku shiga cikin gidannan kuce ana sallama da Babangida kacigari "
"Ai Babanmu ne. Baya nan yana makaranta"
AWWa'u ne yayo maganar.
"A ina makarantar take dan Allah?"
Mardiyya tace.
"Babu nisa can ?asan layinnan ne yanzu ma wajenshi zamu je"
Ai kuwa wannan ma'aikacin kotu yabi su Mardiyya har makaranta wajen Babangida.
Mai gadin makarantar ne ya shiga ya kirawo musu shi.
Tun daga nesa daya hango su Mardiyya tsaye da wani mutum sai yaji faWuwar gaba.
Hakan yasa ya Wago ?afa ya ?araso.
"Baba Ummi ta dawo zamu je wajenta"
?uruci dangin hauka. Malama ce ta tari Babanta da wannan maganar.
Sai kan shi ya Waure ya shiga rarraba idanu tsakanin yaran da wannan mutumin.
"Assalamu alaikum bawan Allah kaine Babangida kacigari ko?"
Hannun daya mi?o mishi dan suyi musabaha shima ya mi?a mishi tare da amsa sallamar.
"Nine Babangida Allah yasa lafiya?"
"Sai alkhairi dama naje gidanka nemanka ne to sai yaranka suka ce dama wajenka zasu zo suma shine na biyo su. In babu damuwa mu Wan keSe mana"
Yaranshi ya kalla yayi jim daga bisani yace.
"Mardiyya ku shiga ku zauna a waccan barandar ku jirani"
"To Baba"
Ta ja yaran zuwa ciki. Wannan mutumi ya mi?o ma Babangida sammaci.
"Wannan sammacine daga kotun musulunci matarka Sabuwa ce ta shigar da ?aran
Akan abinda take ?aran, da kuma ranar halartar kotun yana jikin takaddar zaka gani.
Dama Abinda ya kawo ni kenan na barka lafiya "
Musabaha suka kuma yi har wannan mutumin ya wuce Babangida na tsaye kanshi na jujjuyawa ya shiga zurfin tunani. Duk da ta ?asan ranshi yayi matu?ar farin ciki da jin kalmar Sabuwa ta dawo, sai dai wannan sammacin ya danne mishi murnar tashi.
"Sabuwa uwar rigima da taurin kai. Mu zuba muga waye zaiyi nasara a tsakaninmu. Babangida shine mijinki tilo a duniya, babu Wan abu ta kazan daya isa yasa in sake ki"
Muryar su Aminu ce tasa ya juyo da sauri ya kallesu.
"Mardiyya Ummanku wai ta dawo da gaske tana gida yanzu haka?"
"E Baba ta dawo Labbai ce ta kirani take sanar mun. Acan ta sauka shine muka zo ka bamu kuWin mota muje wajenta"
Tashin hankalin da yake ciki ai sai ya kuma nunkuwa duk da yana da ya?inin su Rakiya zasu iya dawo da'ita ko Baba Malam ya kirata yace ta koma Wakinta. Da wannan dalilin ya sauke ajjiyar zuchiya. Ya shafi kan Malama zafi rau.
"Mamana jikin har yanzu da zafi. Inaga zansa zuwa yamma a kai ki asibiti"
KuWi ya zaro a aljihunshi dubu Waya ya basu suka kama hanya suka tafi.
Shi kuma ya koma class amman ina ya kasa koyarwar sam dole ya nemi izinin cewar baya jin daWi zai koma gida.
Yana tafe yana juwa.
Su Ramatu ana tsakar gida an barbaje magungunan mata matan unguwar sun cika tsakar gidan anata batsa Babangida ya shigo.
Karab a kunnenshi yana jin sanda Ramatu take ba da labarin jiya data yi amfani da wani magani waishi kurman namiji wai saida Babangida yaita ihu tana rufe mishi baki."Kai kawai ya girgiza dan ?arya take yi shi salab ma ya jita musamman jiyan.
Kanshi a ?asa yazo ya wuce su ya shiga Wakin Ramatu kwananta ne.
Zubewa yayi a kujera ba?in ciki goma da ashirin ya haWe mishi.
Sai da Ramatu ta ?araci surutunta kafin ta shigo Wakin.
"Lafiya ka dawo alhalin lokacin dawowarka cin abincin rana bai yi ba? Kaga ni ko cefanen banyi ba ma wanda zan aika ya siyo mun kayan miya na rasa kuma yaran waccan matar naga basa gidan.
"Wacce matar kike magana akai Ramatu?"
Yayi tambayar cikin tuhuma jin kamar muryarshi a Sace yasa ta haWiye maganarta.
?urum ?ar Shuwa ta shigo Wakin da shirinta tsab na fita uunguwa.
Zama tayi a kujera.
"Sannu da dawowa?"
"Hmm yauwa sannu"
Sai ta Wanyi murmushin dole kafin tace.
"Dama yanzu na fito zan le?a makaranta in sanar maka Mama ce ta kirani wai tana son ganina da gaggawa shine dama"
?ur yayi mata da idanunshi kamar yana karantar wani abu daga motsinta.
"Amman bana hana a dinga biyo ni makaranta ba. Shin wayar hannunki meye amfaninta da ba zaki kirani ba?"
"Allah ya huci zuchiyar mijina da girman kujerarka. Wayarce babu kati shi yasa wallahi. Aimun afuwa"
Sassautowa yayi kaWan. Hannu yasa a aljihu ya ciro dubu guda ya mi?a mata.
"Kar kiyi dare kinsan ke zaki karSi girkin dai yau ko?"
Murmushi tayi harda wani kallon gefen da Ramatu take tako tsume. Sai ta saki murmushin kissa.
"Ni ko nasan ni zan karSi girki Jannati. Ai kamar yadda kake zumuWin zagayowar kwanana nima inayi. Ko zaka bani kuWin cefanen nayo a gida dana dawo girki kawai zan Waura"?
Hannu yasa a ajjihu ya ciro dubu biyu ya bata.
"Me kake so to a girka?"
Saida ya Wan yatutse fuska kafin yace.
"Tuwo zaki yi miyar kuSewa Wanya kisa nama kona Warri biyar ne na gaji da cin shinkafa shinkafa "
Mi?ewa tayi tana dariya.
"An gama harda kifi ma zan haWa in saka maka. Ni saina dawo. Ramatu na fita"
Ciki ciki Ramatu tayi mata saita dawo.
Ledarta data ajjiye a ?ofar Wakin ta Wauka yara na biye da'ita taima matan gida sallama.
Gidan dillaliya ta shiga. Tako yi katari babu kowa a gidan dillaliya kamar ma fita zata yi.
"?ar Shuwa kece da hantsi haka ta samu kenan?"
"Uhm dillaliya duk wanda kika gani a gidanki ai siya ko siyarwa yazo yi. Tukunna ma dan Allah an samu kulolin kuwa?"
Dillaliya tace.
"Bana kuloli sunyi wuyar samu waWanda na samu gaskiya masu tsada ne irin na ?arfennan dubu har Wari da goma. Jiyannan kishiyarki ta siye su wallahi.
Idanu ?ar Shuwa ta zare harda dafe ?irji ta furta.
"Na shiga uku. Kikace fa dubu Wari da goma kuma Ramatu ta siye dama Ramatu na da kuWi haka?"
Dillaliya ta fashe da dariya tace.
"Ki dai zauna ta fiki fada. Kinga tun lokacin da kika haWo kan kulolinki duk kika siyar Wayar mai shegen tsadan saida nace miki kada ki siyar amman kika ?i ji. To ga kishiyarki tasai waWanda suka fi naki tsada kuma babu mamaki dan tasan kina da sune. WaWannan fa in sababbine zasu iya yin Wari huWu ma"
?ar Shuwa duk saita ruWe abubbuwa suka caSe mata goma da ashirin.
Atampopi biyu ta zaro ta mi?a ma dillaliya tana haWiyar yawu.
Bayan dillaliya ta gama jujjuyasu saita buWe jakarta ta zaro dubu sha uku ta ba ?ar Shuwa.
"Haba dillaliya bafa kayan sata bane. Ya atampopina masu tsada zaki mun haka?"
KuWin ta mi?a ma Dillaliya ita kuma ganin haka yasa tace.
"Kai daWina dake gajen ha?uri yanzu iyakar abinda ke wajena kenan. In kika dawo ki biyo
Allah bashi na sama miki wasu kulolin kinga sai mu wanye.
Dariya ?ar Shuwa tayi tace.
"Dillaliya kin yarda dai ina binki bashi ko?"
Dariya suka saka duka.
A tare suka fito har titi daga wajenne kowacce ta kama gabanta.
Rai babu daWi ?ar Shuwa ta shiga gidansu da sallama an je munafurci.



MRS BUKHARI

Gobe bazan samu zarafin turowa ba haka jibi ma sai zuwa talata in Allah ya kaimu cikin masu rai
Aimun afuwa bani da lafiya ne yanzu haka ma daga asibiti muka dawo.
Nagode sosai son so=??? [8/18, 7:50 AM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA SHA BIYU

*KUYI HA?URI BA KULLUM ZAKU DINGA SAMU BA HAR SAINA SAMU LAFIYA NAGODE SOSAI*




SABUWA:.


Idanuna ban buWesu ba har saida na jiyo amon muryarsu Mardiyya. Malama ta faWo jikina tana kiran sunana. Naji jikinta kau da zafi.
Da sauri na mi?e zaune kaina ya wani mugun sara mun har saida na dafe.
Mardiyya bata da lafiya ne Malama?"
Dawowa suka yi kusa dani dukkansu sai tattaSani suke yi.
"E Ummi bata da lafiya mura da zazzaSi take yi amman Baba ya siyo mata magani. Yace ma da yamma zai kaita asibiti. Ummi ina kikaje dan ALLAH kada ki sake tafiya ki barmu"
Murmushi kawai nayi musu. AWWa'u yace.
"Maman Fatima kullum saita dake mu kuma taita tsine miki Ummi."
Adama tace.
"Zata rina. ?ar abu ta kazan... Zan rakaku gidan in zaku koma wallahi sai munyi kare jini biri jini da'ita dan Yar Shuwa zuma ce sai da wuta."
Nan wannan yace wannan wannan yace wancan. Ni dai ina ma?ale da yarana.
"Ummi baki da lafiya ne kin rame sosai?"
Mardiyya bani da lafiya tun ranar dana barku ina kwance ne a asibiti ko gane wanda yake kaina bana yi."
Nan yaran suka shiga aikin yi mun sannu da jikina.
Rakiya ce ta aiko ai kiranmu dukkanmu.
Mi?ewa mu ka yi muka Wiba yuu zuwa gida.
Gaza na tsakar gida ya gwafe sai wanke kaya yake yi. Ga wasu lesuka ya dauraye harya shanya. Naga ga wata mata mai kama da ?an daba taci riga da wando ta Wame a zaune a gefenshi tana ta shafa kan Rahine.
Ga magina a cikin gidan sun tayar da ginin Waki harma an gama zance dan baifi bulo Waya za'a Waura ba a kashe ginin.
"Allahu Akbar kaga Lolo Sabuwa mai sabon aiki ba ehh ashe kin samu kanki yarinya kin waiwayo gida? Bafa zan Soye miki ba gara da kika dawo duk tsiya ku mata ne kar ku sake ku shiga bariki gara ku zauna ehh a gabansu Rakiya kuyi duk wacce zaku yi. Duk da ehh na sani da gabansu da Bariki duk Waya amman ko yayane zasu yi muku garkuwa dai"
Maigogul dake zaune akan turmi yana yanka nama yace.
"Loko kizo ki shirya su Adama sui miki rakiya gidanki dalilin kiran da Rakiya tayi miki kenan tun kafin uban mijinki yazo kinsan zaice miki ki koma Wakinki dai kafin a gama shari'ar da kika nace"
Na buWe baki zanyi magana Gaza ya daga mun hannu tare da tsame hannunshi a wankin. Wu?a ya zaro a kugunshi ya shiga kartawa a wani ?aton dutse da muke zama.
"Inaaa wallahi Allah daya ne Lolo ba zata koma gidan wancan Wan akuyar ba. Ko abinda ya faru a kotu wallahi Ni Gaza dan bana gidannane da bazai faru ba.
Nifa zan kashe Babangida uban kowa ma ya huta wallahi. Ehh jibi yarinya yadda ta fita hayyacinta har ta gudu ta bar gida yanzu ta dawo ace

13 / 25