Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   11 / 25

30K to 33K   out of 72.9K words

barsu anan na Wan wani lokaci ai?"
Rakiya tace.
"Su tafi maza. In aka barsu Hala ke zaki Wauki nauyin basu abinci ko? Komu da Allah ya kawo mu wayewar garin yau munyi farin ciki da muka ga yau da rayuwarmu ruwane kaWai amman a gidannan muma shi zamu kamfata kowa ya kama gabanshi. Gidansu da gidan kakaninsu akwai abinci suje can su ?arata. Ita kanta uwarsu dadine yayi mata yawa dan banga haka a gidan ubanta ba. Kinsan in daWi yaima mutum yawa sai yace Allah ya kasheshi ya huta."
Kai Mustapha ya girgiza ya tarkata kan yaran suka fice.
Babangida fa jiki yayi tsanani dauriya ce kawai da addu'o'in da yake ta jerowa yasa ya kai war haka.
"Kaini asibiti Mustapha yaran sai a mayar dasu gida wajen Aisha ko Ramatu. Mardiyya mamanku bata faWa miki inda zata je ba, ko kinji tana waya haka?"
"A_a Baba bata faWa mun komai ba. Abinda na sani shine jiya bata ko magana har muka dawo daga islamiyya "
Ido ya lumshe kawai yana dafe da kanshi har suka ?arasa asibiti. A ?ofar asibitin suka ga Kawu manga da matan su wawo isowarsu kenan.
"Mustapha ya zamu yi da naso ka rakani asibitin inaso inga Khalid ne?"
Shiru Mustapha yayi yana tunani can kuma sai yace.
"To yanzu abinda za'ayi muje mu duba Malama Babba sai mu futo mu sauke yaran in yaso sai mu wuce."
Fitowa kuwa suka yi dukkansu.
"Ai ga Babangidan ma ya iso"
Cewar Safiya matar Bashiru.
A tsanake ya isa wajensu aka gaggaisa duka. Kawu manga yace.
"Ina ka shiga Sa'a ta kirani a waya ta kawo ?arar baka kwana a asibiti ba?"
Kafin yace wani Abu su Safiya suka wuce tare da yaran zuwa ciki. Wajen ya rage daga Kawu manga sai Mustapha sai shi mai gayyar.
"E ban kwana a asibiti ba gaskiya "
Kura mishi idanu yayi kafin yace.
"To me yasa?"
"Sabuwa ce akai mun waya jiya da daddaren wai ta gudu. Wannan dalilinne yasa na bar asibitin. Tun jiya muke nemanta cikin dare har izuwa safiyar yau babu labarinta.
Yanzu ma nazo in duba jikin Malama ne inaso Mustapha ya rakani mu kai report ofishin ?an sanda, mu ba da cigiyarta a gidan TV "
Kawu manga shiru yayi baice komai ba. Bai kai ga cewa uffan ba su Wawo suma suka iso asibitin tare da dukka mazan gidan baki Waya.
Nan aka shiga gaggaisawa nan kuma suka dunguma zuwa ciki. Bibbiyu bibbiyu ake shiga sabida bazai yiwu su shiga fin haka ba. Kuma da sun fito sai su nufi hanyar waje, dan tsaiwar ba zata yiwu ba sabida yawansu.
Babangida sai kallon su Mardiyya yake yi da suke zaune a takure a kan benci.
Mardiyya itama uban nata take kallo ta saka fuskar tausayi.
Sai da ya rage saura Babangida da Mustapha ne kaWai a tsaye suna jiran Kawu Manga ga Wawo su futo su su shiga shine ya dubi Malama Babba ya mi?o mata hannunshi. Allah sarki yarinyar ta taso ta ri?e hannun Baban tana mishi murmushi. Sai yaji tamkar hawaye zasu sakko mishi.
"Mardiyya ku kun shiga kun duba jikin Malama ne?"
A sanyaye yayi maganar linkib da rauni. Itama a sanyayen tace.
"Bamu kai ga Shiga ba Goggo Sa'a tace kar mu shigo bata son ganinmu shine nace musu mu zauna anan"
Wani irin abune ya soki ?irjinshi jin abinda Sa'a ta faWama yaran.
A zuchiyarshi sai yafi ganin lefinshi da bai tabbatarma da ?an uwanshi cewar su Mardiyya sunfi mishi ko wanne yara soyuwa a zuchiyarshi ba. Sai yasa ?afa ya shure yaran yake nuna musu ?iyayya duka hantara, kyara duk shi kaWai. Baima kamata yaga laifin Sa'a ba sam. Sai dai yayi tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya siyo musu martaba da kima a idanun duniya baki Waya.
Isowar su ?ar Shuwa da Ramatu, da Sauban ne ya dawo da Babangida daga cikin hayyacinshi.
Wawo na fitowa Babangida ya ja hannun Mustapha suka shiga ciki. Malama na kwance amman idanunta biyu.
"Sannu Malama ya ?arfin jikin naki?"
Kai ta Waga da hannunta halamar da sau?i. Babangida tsoro ya shigeshi yace.
"Yaya Sa'a Malama bata magana ne?"
"Da tana yi ai da tayi. Kai da kake son ma ta mutu ka huta? Saboda fasi?ar matarka ta gudu tabi namiji shine dalilin da zaka fice a asibitinnan babu ko sallama ga mahaifiyarka kwance babu lafiya silarka. Ita dai wannan soyayya da Malama take nuna maka bata da wani amfani ma tunda ka kasa tsaya mata a lokacin da bata da lafiya "
Kallonta Babangida yayi. Ya dubi Malama Babba da take Waga ma Sa'a hannu akan tayi shiru.
"Lafiyanki ?alau kuwa Sa'a da irin waWannan maganganun da kike fesarwa a gabana. In a gaban Yayane kin isa Wago kaima bare har ki dinga wannan kalami haka? Dame kuke so mutum yaji ne. Babangida inya tsaya a kanku shine samun lafiyarne koka sai akayi Yaya?
Duk lalacewar Sabuwa ai matarshi ce Uwar manyan yaranshi dole. Sannan kufa sani Sauban ne zai auri Mardiyya fa"
Shiru Babangida yayi yana nazari. A yanzu ne yake jin in sama da ?asa haWewa zata yi bazai bari Sauban ya auri Mardiyya ba. A yaune ya gano zata rayune cikin ?unci da tsangwama ?ila har a wajen Sauban Win. Yafi taje waje ta auri bare ba Sauban ba.
"Kayi ha?uri Kawu Manga bazan sake ba."
Ya jiyo muryar Sa'a tana ba da ha?uri.
Kawu manga yace.
"Babangida muje daga waje in ganku tukunna"
A baya suka bishi zuwa waje.
Sauban na zaune a kusa da Mardiyya suna hirarsu cike da girmama juna. Kuka ma take yi shi kuwa ya rage murya sai aikin rarrashinta yake yi. Ganin futowar Babangida ne yasa su ?ar Shuwa da Ramatu suka tashi.
Gaishe da Kawu manga suka yi tare da tambayar mai jiki. ?ar Shuwa ta Waura da cewa.
"Ashe da abubuwan da muka tashi kenan. Naji labarin Mamansu Mardiyya ta tafi wajen khalid tunda Baban Mardiyya ya?i sakinta"
"Ke baki da hankali ne kinsan abunda kike faWa kuwa?'
Matsowa yayi gabanta cikin zafin nama kamar zai kifa mata mari. Take fa har hawaye ya taru akan fuskarshi. Kawu Manga ne yayi saurin ri?eshi ya dawo baya. ?ar Shuwa ba ?aramin mamakin yadda Babangida ya birkice tayi ba. Duk da zuchiyarta a cike take da farin cikin tayi nasara akan Sabuwa, sai da taji kishin yadda Babangida kishin Sabuwa ya baiyana ?arara a abinda ya aikata mata kuma taji ciwon hakan.
"Assha Babangida ashe dai baka dena halinka na dukan mata ba wai? Ke kuma Aisha menene wannan wacce iriyar magana kike furtawa haka ke haka ta faWa miki wajenshi zata je?"
A zuchiyarta tayi murmushin mugunta ta kuma samun wata dama. A zahiri sai ta sau fuskar tausayi tare da cewa.
"Ayi ha?uri Kawu manga amman yadda Sabuwa take da Khalid ba zata taSa iya rayuwa babu shi ba. Shima Baban Mardiyya baisan tsakanin su bane nice nasan komai shi yasa nace haka amman ayi ha?uri tunda maganar tayi zafi"
Idanu Babangida ya rufe yana jin juwa tare da wani yaji a idanunshi. Allah yasa ma su Mardiyya tuni sunyi gaba da a gabansu za'ayi wannan abun. Mustapha da yasan ha?i?anin irin kishin Babangida babu shiri ya ri?eshi dan ya fuskanci yana cikin mawuyacin hali.
Kawu manga yayi kasa?e yana kallonta kafin yace.
"Allah ya kyauta ku shige kuje kuyi abinda ya kawo ku. Kai kuma kuzo mu tafi"
Har suka shiga mota babu wanda yayi magana.
Wawo da yaga tahowarsu Kawu manga ya buWe mishi mota sai yaga ya shige motar Mustapha. Karasowa bakin motar yayi.
"Wawo ku ku tafi wajen nema. Zamu je wani wajennne da su Babangida."
"To shikenan yaran ma dasu za'a tafi ko su fito in ajjiyesu a can gida?"
Kawu manga yace.
"A_a barsu tare da ubansu kai dai jeka Allah yayi albarka"
Saida suka hau titi kafin Kawu Manga yace.
"Mu je can wajen nashi a asibitin Dan ba ace an barku ku kaWai kunje za'a iya yin Satacciya."
Har aka iso babban asibiti Babangida bai buWe idanunshi ba saida Mustapha ya dafa kafaWarshi kana ya buWe idanunshi da suka zama tamkar garwashi ko kuma tasshi dan ja.
Sakkowa yayi ya yafuto Malama ta futo.
"Mardiyya ku jiramu muna zuwa ko?"
Ya faWa yana gyara ri?on da yaima Malama.
Da tambaya aka kawosu har bakin ofishin Khalid. An kuma ci sa'a ma yananan. Izinin shiga aka basu suna shiga Malama ta saki hannun Babanta ta isa wajen Dr Khalid tana dariya halamun ta sanshi tayi sabo dashi.
Tsawar da Babangida ya dako mata ne yasa ta dawo da sauri ta ri?e hannunshi da suke ta rawa. Illahirin jikin Babangida rawa yake yi.
Kenan yaranshi ma sun sam Khalid kenan. To Sabuwa ko dai tana shigo da Khalid gidanshi ne ya kwana ma shi bai sani ba. Shima yana can yana lalata yaran mutane, ko yana tare da daduronshi?'
"Yaro kaine Khalid tsohon saurayin Sabuwa ko?"
Kawu Manga ya tambayeshi.
"Baba nine ku zauna ga kujeru"
Yayi maganar ko a jikinshi. Mustapha da Kawu Manga ne suka zauna. Babangida na tsaye jikinshi na rawa. Wai yau shine suka tawo wajen saurayin matarshi nemanta. Wannan tashin hankali da yawa yake.
Kawu Manga ya yi ma Khalid bayanin zuwansu kab. Babu shiri ya cire gilashin dake idanunshi cikin nuna damuwa yace.
"Guduwa Sabuwan tayi? Wallahi Allah bansan inda take ba kuma bama waya da'ita Baba ka yarda dani da Sabuwa na hannuna ko bazan bayar da'ita ba zan sanar muku tana hannuna ko dan ku samu nutsuwa"
Ai sai ji suka yi Babangida yayi kukan kura ya Wale jikin Khalid ya hau naushin bakinshi dan ba?in ciki.
Khalid shima ingarma ne kuma ba baya ba wajen karfi sannan a kule yake da Babangida da kuma faWan da sukayi kwanaki har Babangida ya samu galaba a kanshi.
Dambe da zagine ya kaure a ofishin.
Babu shiri Kawu Manga ya ja hannun Malama ya fita da'ita ya zaunar da'ita a benci inda mata ke jira dan shiga ganin likita.
Shigar da yayi ne ya samu Babangida ya caka ma Khalid almakashi a tafin hannu Allah yaso bai shiga da yawa ba sai dai wajen ya fashe.
Tsakiyansu ya shiga gashi Babangida ya kawo naushi ganin Kawu Manga a tsakiyansu yasa ya sauke hannun nashi idanshi Waya na zubar da hawayen kishi mai zafi.
"Ku barni dashi bakwa jin abinda yake faWa da gadara wai da tana hannunshi ko bazai bamu itaba. Dan uwar ubanka kai an faWa maka ni kanwar lasa ne.
Wallahi sai nayi shari'a da kai akan keta mun haddin aurena daka yi"
Babangida ke magana maganar cikin rufewar idanu yake yi.
KHALID dake ri?e da tafin hannunshi ya danne inda Babangida ya caka mishi almakashin da babban yatanshi yace.
"Sabuwan da kake son kaga ta mutu ka huta. Matar da ka Waura ma cutar hawan jini da ciwon damuwa a kanta kake haka?
Ai babu namijin da zai so Sabuwa sama dani. Ka zauna kananan zamu yi aure ni da ita"
Ai ashe ba'ai komai ba Wazu. Babangida baisan sanda ya janye Kawu Manga ba shi da Mustapha suka shiga aikama da Dr sa?on naushi. Kafin kace me aka soma cika har saida aka kira ?an sanda suka wuce dasu dukkansu. An dai ci sa'a dpo yasan Kawu Manga yasan Malam Baba shi yasa ?urar cikin awa uku ta lafa akai musu tsakani tare da tuhumar Khalid inda Sabuwa take .
Zancan Waya ne baisan inda take ba.
Yara kuma tun sanda za'a tafi dasu Babangida ofishin ?an sanda Kawu Manga ya kirawo Wawo a waya yace ya zo ya Waukesu a asibiti ya kaisu gidansu
Hakan kuwa akayi aka maidasu gida, sukaita kuka a Wakin Mamansu. Ma?ota sai shigowa suke yi suna musu jajen Satan Mamansu. Ga Babansu a ofishin ?an sanda, ga kakanninsu a kwance babu Lafiya "


SABUWA:.
Sannu kan hankali idanuna suka buWe tarwai. Wani irin sarawa da kaina yayi ne yasa babu shiri na Wan runtse idanuna. Jijiyoyin gefen kaina sai aiki suke yi tamkar an kunnasu.
Abubuwan da suka faru a kotu da baro gida dana yi izuwa Wakin hotel kaWai na iya tunawa.
Da sauri na sake buWe idanuna sai na ganni a asibiti harma hannuna a sa?ale da robar ?arin ruwa.
Gefe da gefena na waiga matane da ko sun Warani a shekaru kaWanne ko wacce tana kan gadonta. Macen dake hannun dama na idanta ita biyu.
"Baiwar Allah yau kin farka kenan masha Allah. Sannu kinji Allah ya bamu lafiya baki Waya."
Na buWe baki zanyi magana sai naji na kasa Waga harshena. Ko dana yinkura zan mi?e izuwa zaune shima sai naji na kasa jan jikin nawa. Ga kuma jiri dana soma gani Wakin ma a wani hargitse nake ganinshi.
Wasu hawayen ba?in cikine suka soma zubowa daga kwarmin idanuna suna gangarewa ta gefe da gefen fuskata.
"Yauwa Baban Adam ko zaka yima ma'aikatan jinya magana. Kaga matarnan da aka kawota kwana uku da suka shige itace ta farka."
Na jiyo amon muryar matar dake hannun damana.
Kwana uku, kenan har kwana uku nayi a kwance bansan inda nake ba. To wama ya kawo ni nan. Kaddai Babangida dasu Adama sunsan inda nake su suka kawo ni nan?"
Duk waWannan tambayoyin da nake ma kaina a zuchiyata nake yi. Take naji Wan ?arfi ya shigeni harna yin?ura zan tashi zaune kuma jikin ya motsa jirine dai yasa na koma.
Wanda aka kira da Baban Adam bai jima da fita ba sai ga wata ma'aikaciyar jinya biye dashi turyan_turyan har izuwa bakin gadona.
"Sannu baiwar Allah kin farka yaya jikin naki?"
Kafin in bata amsa ta shiga dubani tare da aunani da wannan abun awon nasu da suke ma?ewa a wuya da kunne. Da jima sosai a kaina tana duba lafiyata
MRS Bukhari

Sai kuma Allah ya kaimu Ranar Asabar.
Son so=??? [8/16, 5:47 AM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA




Ta jima a kaina kafin daga bisani ta tambayeni.
"Yanzu da me dame kike ji a jikinki"
Jiri da ciwon kai. Sai kuma ina ji kamar in kashe kaina" Na faWa harshe da nauyi.
"Subhanallah. Kiyi ta adda'a in sha ALLAH komai yayi tsanani sau?i na nan zuwa."
Amman waye ya kawo ni asibitinnan dan Allah?"
Na tambayeta muryata ta sake yin sanyi.
"Dr Kamilu ne ya bani ke dai. Amman sanda aka kawo ki bani ce da duti ba ranar. Shi kuma yanzu baya nan sai zuwa dare yake da duti. Sai dai yace in kika tashi duk abinda kike bu?ata a kawo miki.
Me zaki iya ci ko sha a kawo miki?"
Idanuna na lumshe ina hamdala a zuchiyata da akace wani ne daban ya kawo ni asibiti ba Babangida ko ?an gidanmu ba.
A kawo mun ruwan zafi kawai"
Na faWa ba tare dana buWe idanuna ba.
Tunanin ko a wanne hali ?a?ana suke shi ya jani har wannan ma'aikaciyar jinya ta dawo ba tare dana sani ba.
"Tashi ki sha shayin ko saina taimaka miki ne"
Ajjiye shayin tayi a durowar gefen gadon ta cire mun ruwan daya ?are a hannuna.
Taimaka mun tayi na zauna tare da jingina a fuskar gadon.
Shayinnan kakkaura zafinshi daidai da sha.
Dana kafa kaina ban sauke ba saida na shanye tas. Ba dan yinwa ba ba kuma dan daWi ba. Sai dan Allah Allah nake yi in gama bakina babu komai face Waci. Sai nake ji kamar in doka kofin da ?asa, ko in jijjige gadon da nake kai.
Bayan kamar minti goma ma'aikaciyar jinyarnan ta dawo da bokitin ruwan dumi a hannunta zuwa banWakin dake cikin Wakin jinyar. Sai da ta kai ta dawo inda nake.
"Ga ruwan wanka can na kai miki ko zaki daure kiyi wankan kafin Dr Kamilu ya kawo miki kayan sawarki?"
Dan gudun kada in gwasale bajintarta yasa na amince da taimakonta na isa banWakin tsabtatacce tamkar ba asalibiti ba sai dai warin izal da yake yi kamar ko wanne asibiti.
Ina kwara ruwan duminnan a jikina hawaye na wanke mun fuskata tunanuka cunkushe fal kaina. Gurina shine gina sabuwar rayuwa a duniya Sabuwa.
Da haka na gama wankan na Wauro alwala na goge jikina da farin tawul Win dana ga ta rataye mun a bakin ?ofar banWain. Saina maida kayana da wari ma suke yi.
Da bin bango na fito majinyatan dake kwance sai sannu suke yi mun da jiki.
Kai kawai nake Waga Musu ji nake dama in mutu in huta, ko kuma in Waura hannu aka in kwarmata ihu, ko kuma in kashe kaina zanfi samun farin ciki.
Wani irin ?ai?ayi ?wa?walwata take yi mun kwatanta muku ne bazan iya ba, zuchiyata tayi duhu kuma a cunkushe nake jinta.
Duniyar ganinta nake yi kamar mitsitsiyace kuma kamar ni kaWai nake rayuwa a cikinta.
Iyakar kwatancen da zai kwatantu ya Wauki hankalin mai karatu kenan. Amman sanin ha?i?atan Win yadda nake ji sai macen da ta taSa kamuwa da ciwon damuwa, ko kuma likitocin da wannan fannin suka karanta ne kaWai zasu gane mai nake ji.
A haka nayi Sallah daga zaune inayi ina kuka.
Na dai yi ne ko zan samu nutsuwa amman abinda nake karantawa a cikin sallar ban sani ba.
Banma gama ramawa ba na hakura kawai.
Wannan ma'aikaciyar jinyar ce ta kawo mun maganguna na hadiya na sha ruwa.
Ban jima ba bacci ya Waubeni. Bani na farka ba sai wajajen taran dare.
Abokan jinyata duk bacci suke yi, sai masu kula dasu da suke zaune wasu a kujerar roba wasu a ?asa kan dadduma.
Durowar gefen gadona na kalla sai naga kular abinci, da filas din shayi da kayan shayi da wasu ruwa. Kawar da kaina nayi, wanda yayi daidai da buWe ?ofar Wakin namu.
Wani irin razana nayi da jin ?aran ?ofar har ?an?ame jikina nayi idanuna na runtse su da ?arfi inata adda,a a fili.
Na daWe sosai a haka da dabara na buWe idona Waya sai naga mutum da fararen kaya a zaune a gaban gadona yayi tagumi yana kallona.
Da sauri na buWe Wayan idon na gyara jikina tare da sauke kai ?asa.
Baice komai ba, nima ko tari na?i yi, sai can ya sauke ajjiyar zuchiya tare da cewa .
"Yaya jikin naki?"
Da sau?i lafiyata ?alau"
"Zan iya sanin sunanki? Ni dai sunana Dr Kamilu nine mutumin daya kawo ki asibitinnan. Mun haWu dake ne a zangon ba?i. Muka ganki a cikin wani hali shine muka Waukoki zuwa asibiti, yau kwananki huWu za'ace a kwance"
Hawaye na soma zubarwa can saina soma shesshe?ar kuka.
"Kiyi ha?uri in tambayar ita ta saki wannan kukan. Bari. In zuba miki abinci kici zaki sha maganine"
Bance komai ba amman na tsagaita kukan.
Mi?i mun kwano yayi da farfesun kayan cikin saniya.
"Amshi ki daure ko bakya jin daWinshi ki cinye. Magungunanki suna da ?arfi kuma sister ta faWa mun shayi kawai kika sha."
Kwanon na karSa na soma ci a

11 / 25