Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   19 / 25

54K to 57K   out of 72.9K words

ma za'ayi a gaba"
Gaza ya buWe baki yace.
"Au haka kake ma kanka fata? Duk irin Akuyancin da yayi maka kana fatan samun wanda ma ya fishi kenan? Gaka ga duniya Dattijo. Maza mujenku ciki duk wanda sukai muku ku saka musu sara wallahi ba wani shege "
?u suka nufi ?ofar gidan bankaWa get Win gidan sukai da mugun ?arfi karnukansu ne suka soma shiga gidan.
Take matan gidan da ?an biki da suka soma taruwa suka dare tsakar gidan ya zama sai fili da kwanukan wanke_wanke da kayan wanki, harda su kayan cefanen biki.
"Adama ku ku shiga, mazaje ku bisu kuje ni da Dattijo zamu tsaya anan kuje a ciro komai da komai. In ga uban da zai hana ku, har ?wayayen wutar lantarki ku ciro kar kubar komai. Kayan abinci ma a kwashe kai komai a kwaso hatta shara muna son abunmu. Ko ba haka ba Maigogul?"
Gaza ya tambaya yana zaro wata shinfiWediyar wu?a mai zarto.
"Hakane a kwaso komai tunda uban Babangida ne yayo mata. Kuma yace ta kwashe abunta ai kaga bama bar musu ba"
Dariya kawai Gaza yayi ma Maigogul.
Haka su Adama sukaita fito da kaya Mardiyya kuma ta haWe ?annenta suka takure a waje Waya tana ta hawaye tana sauke ajjiyar zuchiya. Malama ce kawai bata kuka itama yarinta ke damunta amman dai ganin ?an uwanta suna kuka ga kayan Umminsu anata fitarwa sai jikinta yayi sanyi ta rirri?e ?an uwanta gam.
Har aka gama loda komai da komai a mota babu wanda ya le?o ga Gaza yasa karnuka sai haushi suke yi bisa umarninshi.
?ar Shuwa tana ciki da ?annenta duk ta tsure bata samu kwanciyar hankali ba har saida taji shiru babu haushin karnukan halamun su Gaza sun bar unguwar kenan. Tsoronta Gaza tasan zai iya cewa a fito da'ita yayi mata abinda yaga dama tasan babu abinda zai faru.
Ajjiyar zuchiya ta sauke. Kawai taji an Sallo ?ofarta Rahine na gaba Gaza na baya suka haWa idanu da ?ar Shuwa.
Wallahi sai ga fitsari sharshar yana bin ?afarta.
"Ke Adama da Labbai ku shiga kui mata dukan shan gishiri. Ni eh in nace zan taSata mutuwa zata yi wallahi."
Yana tsaye bakin ?ofar su Adama suka shiga suka rufe ?ar Shuwa da dukan mutuwa Labbai kuwa fuskarta ta samu taita duka ta tara mata jini a idanunta bakinta kuwa leSen ?asa tsagewa yayi tsabar azaba.
Gaza yasa Rahine tayi fitsari a tsakar Wakin suka kama hanya suka fice
Sai lokacin mutane suka samu sukuni. Fuska a kumbure aka wuce da ?ar Shuwa asibiti. Saida akayi mata Winki a leSenta, idanta ya tara jini ta ciki sosai. Cikin ?an?anin lokaci halittarta ta canja fuska da baki suka aune.


SABUWA:.
Ina tsakar gida muna magana da Rakiya muka jiyo tsayuwar motar su Gaza.
Rakiya inaga a siyar da ragowar kayan kawai. Katifa da sib kawai zan bari inaso mu sake Waki wancan dasu Adama suka kama yayi kaWan gaskiya kinga wataran har su Sadiya suna zuwa mu kwana."
"To amman Lolo in kika sake samun wani mijin ayi yaya? Ke kinsan dai bamu yi miki a auren farko ba ba zamu yi miki a aure na biyu ba ko?
Duk da bamu da wajen ajjiye kayannan a dai zube su a tsakar gida muga yadda zata kaya. In kuma kince a siyar to"
A siyar kawai ko Wan kunne na siya in ma?ala a kunnena in auren yazo sai in siyar zaifi mun tunda dama ina da wasu"
Mi?ewa Rakiya tayi ta zare mayafinta a igiyar shanya.
"Bari inje Lolo banci ta zama ba. Dillali zan kira yaima kayan kuWin goro kawai a siyar. In yaso kayan kitchen Win mata sa zo su sissiya inaga hakan zaifi."
Ai kuwa hakan akayi dubu Wari da saba'in aka sai kayan dukka banda katifa da sib amman har firizata babba na siyar da'ita. Ragowar kayan kitchen Wina kusan Layuza ce ta sai rabi da kwatan kayan sai wani fele?e take yi mun gashi kusan kullum tana gidan.
Mun bazama neman Waki ciki da falo cikin sa'a muka samu a farkon layinmu gidan Baban Anya. Sai lokacin muka samu sakewa mu huWu ne da Wakin zamu dinga haWa kuWi mu biya. Ko wacce dubu goma goma.
Haka lamura sukaita tafiya rayuwa tayi ta juyawa. In aka Wauke tunanin Ya?ana da da matsalolin gidanmu da sai ince bani da damuwar komai jina nake tamkar sabuwar mutum.
Sai dai kash matsalolin gidanmu na yau daban na gobe daban. Gaza da matarshi sun sake lalata mana gidan da hayaniya sosai. Bamu muka samu sukuni ba har saida Gaza yaje ya rikito wani jarfan aka sake wucewa dashi gidan yari. Ita kuma Madamsy tace ba zata zauna yinwa da rashin gata ya kasheta a gidanmu ba zata tafi can garinsu ga ?aramin ciki a jikinta. Maigogul yayi juyin duniya akan kada ta tafi ta zauna ta haife abinda ke cikinta amman sai wayar gari akayi babu madamsy babu dalilinta.
Gaga_gaga rayuwa ta tafi sosai.
Wata ranar asabar ina zaune akan katifa ina chart da Dr Kamilu. Su Adama kuma sunata zancan bikinta gobe da yardar Allah za'a Waura aurenta zamu je mu kaita can Malam madori. Har munje mun yi jere babu laifi komai sabo Adama ta siya sabida Alhajinta ya sake mata aljihu babu laifi. Itace ta huWu ga tarin yara a gidan maza da mata gidan dai gaskiya gidan yawane har surukan Adaman suna cikin gidan.
Da ganin irin tarbar da akayi mana ya nuna mana suna adawa sosai da auren babu wanda yake maraba da zuwan Adama, gashi garin ?auye ne duk da dai babu laifi suna da wayewa akwai makarantu kuma akwai ruwa da wuta. Kuma in aka duba baya sai dai muce ya fima Adama sau dubu Wari.
Sai dai fa abincin gidan na gandu ne miyar gidan babu komai a cikinta face daddawa da gishiri. Muma masu jere dashi dai aka taremu da farau_farau. Babu suturun arziki a jikin matan Alhaji da ma su yaran gidan. Amman gaskiya gidan yana da kyau, kuma Wakunan matan tubarkallah, a haka dai gobe za'a rurrufa akai Adama ta zauna a haka ta dage da adda'a shi Winma da yaya akayi har bikin yazo. Sai da Maigogul yaita yawo da'ita wajajen masu magani ana mishi kiranye kafin yazo dan abun yafi ?arfin Maigogul, sai da aka rufe bakin mahaifiyarshi ma kafin itama ta amince.
Wayata ce tayi ruri Khalid ke kirana ikon Allah ko dai yasan aurena ya mutu ne? Na ayyana hakan a raina tare da Waga wayar tashi.
Ajjiyar zuchiya ya sauke wanda saida duk wata tsiga ta jikina ta tashi.
"Sabuwa gani a ?ofar gidanku ki fito in saka ki a idanuna dan ALLAH ko zuchiyata zata samu nutsuwa"
Idanuna na lumshe da muryar jan hankali yake maganar irin ta mayunwacin zakin daya ga akuya"
Wanne gidan namu kake kofar shi Khalid?"
Murmushinsa yayi mun kafin yace.
"Ki gafarceni ?ofar gidan aurenki. Wallahi Sabuwa mafarkinki ne ya dameni dan ALLAH ki fito ni ko hannunki in ri?e"
Hmm Khalid ka karya al?awari amman.."
"E naji amman a soyayya ai akwai afuwa ko Babyn Khalid shi kaWai har abada?"
?an murmushi nayi kawai.
To ai shikenan kazo gidanmu can ka sameni"
Ajjiyar zuchiya ya sauke.
"An gama ranki shi daWe gani nan zuwa. Saima na biya na siyo miki nono mai sanyi nasan kina so. Ko in bari in nazo sai muje mu siyo tare Baby, kinga daga nan ma ehh..."
?an saurayin dariya muka yi dukkanmu ni dai kashe wayata kawai nayi. Ina girgiza kaina. Khalid duk bala'inshi a wannan karon bazai taSa ribatata ba, ko dan in kiyaye martabar yarana.
"Lolo mai lallen har yanzu bata fa zo ba inaga ke da Labbai ku le?ota dan ALLAH "
Cewar Adama da take jin ta matsu kamar ta jawo gobe haka take ji.
Ga dahuwar tattabara ta tusa gaba sai ha?a take yi tana haWawa da wasu irin tsumi da ?awarta ta dafo mata.
To Labbai muje mu dubo ta."
Kafin mu yin?ura ma sai gata ta shigo da sallamarta.
Yauwa kinga yanzu dama zamu je mu Wakkoki kamar Amarya. Amman dan ALLAH Adama a soma yi mun kinga nawa babu yawa ke ko Amaryace sai afi awa nawa ana yarfa miki"
Hararata Adama tayi tace.
"Lallai yama za'ayi kice a soma yi miki. Ku bari ta gama dani ga kitso za'ayi mun kuma zanje gidan Ladidi zamu je karSo Winkinmu a shagon tela, ga ?an ragowar siyayyan ?ananun abubbuwa da ban ?arashe ba."
Baki na taSe nayi kwanciyata.
Uzairu zuchiyata muka jiyo muryarshi kusan tun daga waje yanata rakaWo mun shegen kira.
Da sauri na fito tsakar gidan daidai shigowar Matar Sama da cikinta a gaba.
Ahh Rita kin ?araso kenan, ina shi Sama Win?"
Murmushi tayi da kwaSaSSiyar hausarta tace.
"Baya nan yana Lagos ya tafi neman kuWi. Ko waya ma Bama yi"
Nii tausayi ta bani Allah yasa ba gidoga yayi mata ba. Kai gidogarce ma indai Sama ne.
Ban kai ga bata amsa ba Uzairu Zuchiyata ya shigo ya finciki hannuna muka fice a guje.
Bai saki hannuna ba sai a filin Wakin Rakiya.
Rakiya na tsintar shinkafa Maigogul yana gaban madubi yanata shafa hoda.
"Lafiya zaku shigo da gudu kamar wasu ?awayen Amarya menene hakan, ko wani sabon salon iskancinne zaku faWo mun kai"
Maigogul dake gyara zaman gogul Winshi yace
"Kash Rakiya kin fiye faWa wallahi. Daga shigowarsu kin taresu da balbalin masifa. Kai Zuchiyata menene, Lolo yaya akayi ko dai sabon bazawari kika samu ne?"
Salati Rakiya ta rabka tace.
"Da iddar a kanta kake mata maganar sabon bazawari?'
Baki ya taSe kawai. " Iddar ba saura kwana uku ta ?are ba to kuma menene?
"Maigogul ?wallonane ya shiga raga. Shekara da shekaru sai yanzu Allah ya cika mun burina. Mata na samu a ?asar Canada. Mahaifinta ne ya bu?aci ganina domin su sanni sai a tsayar da maganar aurenmu."
Mi?ewa Rakiya tayi tana murna.
"?asar waje fa kace Uzairu Zuchiyata ko dai ?aryar daka saba ma ?an mata a waya muma ita zaka mana?"
"A_a wallahi Rakiya kinga Felisha ma ta bu?aci in tawo da ?anwata Lolo dake ita kaWai na taSa haWata suka gaisa.
Yanzu bazama zanyi nemo masu dola account za'a turo mun kuWin paspo nawa dana Lolo. Zasu nema mana takaddar yardar shiga ?asan. In suka turo mana zasu biya mana kuWin jirgi sai Canada.
Lolo gobe sassafe zamu je Kano ayi mana paspo na fita ?asar waje da zaran bizarmu ta fito zamu wuce. In muka je ma Kanon ma san yadda za'ayi kuWin a turo. Muna cikin alkhairi dumu dumu"
Nan Maigogul ya shiga murna har yana cewa.
"Kash Uzairu Zuchiyata ni dai da ka bar Lolo mun tafi tare ayi duk wacce za'ayi gemu da gemu inta kama ma sai a Waura auren kawai. Canada fa kabar Lolo kawai gobe muje Kano ayi mana paspo. Su gobe a Malam madori ma zasu kwana."
Rakiya tace ina wuta ta saka Maigogul.
"Maigogul kwantar da hankalinka zaka Canada acan za'a Waura auren dole da kai za'aje. Yanzu shirye_shryen bikin kawai za'ayi kuma ita Felisha ta ganni ido da ido. Sauran batun zai biyo baya."
"To shikenan Amman dole ko kwalli ko turare in sama maka ka shafa sabida soyayyar tayi ?arko Canada ba wasa ba Uzairu Zuchiyata.
Lallai kai ka gajeni a fagen farin jinin mata masu kuWi ?addarace tasa na auri mata fa?arahu alal lalurati ka gansu dai. Dama_ dama ma ita Uwar taku.
Kiran da Khalid yaimun ne yasa na fita a Wakin.
Hauwa nagani a laSe a bakin ?ofarmu ta kasa kunne tana sauraren abinda muke cewa.
Kai kawai na kaWa ina hasaso irin tashin hankalin da zai afku da ace Rakiya ce ta fito ta samu Hauwa a tsaye tana mata laSe.
Baki na taSe nayi ficewata ina fita muka haWa idanu da Khalid wanda ya ?urama cikin gidanmu idanu ko ?ibtawa bayayi.
Shiga gaban motar nayi sanyi da ?amshinshi na asali suka bigeni.


BABANGIDA:.
Basu suka iso jigawa ba sai da daddare sosai sau biyu mota na lalace musu a hanya abinda yasa sukai dare sosai kenan.
?an Rakiyan rabuwa biyu suka yi rabi suka bi Amaryar Mustapha, rabi suka biyo su Sumy gidanta.
Duk da cewar darene bai hana danginta sakin guWa ba. ?ar Shuwa dake manne a jikin taga ta le?o tana ?wafa ga baki da fuska a aune. ?ur tabi takun amarya da idanunta tana share hawayen ba?in kishi dake zubo mata gashi ko ina ciwo yake yi mata a jikinta tafa daku iyaka.
A kujerar falonta ta dawo ta kwanta. Yau Babangida zai shigo gobe ne taji shiru bai shigo ba, tasan ba kwananta bane a tunaninta zai le?o ya sanar mata dawowar tashi.
"Lallai dole saina mi?e zan iya kwasan ?ancina a gidannan. Babangida bansan wanne irin mayen mata bane a rashin kuWinma saida ya ?aro aure kuma fa in yaga dama sai yace zai cike gurbin Sabuwa ko?"
Murmushi tayi tace.
"Duk yadda zanji zafi ba kamar in Sabuwa bace akace yau ta dawo sunci gaba da aure da Babangida ba. Amman wannan Win nasan da wacce tazo tunda naga ko a waya kulawa ta musamman yake bata.
Kuma tana iya kiranshi a duk sanda taso ta kirashi.

MRS BUKHARI

Ina ?an rakiya zuwa Canada suke a soma rubuta sunayen masu zuwa biki
Su Lolo za'aje Canada
[8/23, 2:29 PM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t
Yar uwa ta, kin dade kina neman in da zaki samu nighties da lounge wears masu musulmin kyau, saukin farashi da kuma kyan gani? =?
? To ki daina nema! A thrift bae closet, mun bude exclusive group inda za a dinga kawo thrift nighties, lounge wears da sauran su masu kyau, kamar Sabbi kuma farashinsu abin mamaki ne, very affordable >?)?.

A nan ne za ki kasance cikin na farko da za su ga sababbin kaya kafin su kare. Idan kina son kada ki rasa mafi kyawun kaya kafin a sayar da su gaba Waya, to shiga cikin group Win yanzu kafin ya cika =?G?
https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t


IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA SHA SHIDA

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI



Haka ?ar Shuwa taci gaba da tubkewa tana warwarewa zuchiyarta sam babu daWi. Tasan kamun Allah ne yasa soyayya Babangida tayi mata matu?ar yawa a zuchiyarta har take jin in ya rabu da'ita tamkar bama zata iya rayuwa ba.
Da ba dan hakan ba wallahi da ko ya?i Allah saiya bata takaddarta tuni.


Babangida:.
Tunda dai ya sallami abokanshi, ya sallami Amarya da danginta da su tsire da lemukan kwalba. Sai ya nufi Wakin Sabuwa.yana tura ?ofar ya shiga kanshi ya juya mishi sosai ganin babu ko tsinke a Wakin sai bargo da yaran suke kwance dukkansu kawai.
Duk sunyi bacci yaran banda Mardiyya da idanunta biyu idanuwanta sunyi jawut halamun taci kuka irin na fitar hayyaciinnan.
Tsugunnawa yayi a kusa dasu ya rasa abinda zaice yayi shiru na tsawon lokaci masu yawan gaske. Ga wayarta Sauban yanata kira biyayya irin nata ta?i Waga wayar, da idanu Babangida ya kalli wayar kawai. Sai can yace da Mardiyya.
"Sabuwa da kanta tazo ta Webe kayanta shine ta kasa bar muku katifa?"
Ajjiyar zuchiya na tashin hankali ya sauke ya sake ja ya sauke.
"Ba ita tazo ta kwashe kaya ba su Maigogul ne suka zo dasu Gaza"
?ur yabi Mardiyya da idanunshi tausayinta ya kamashi sabida itace babba yanzu hankalinshi ya dawo kanta ne baki Waya burinshi ya kawar da'ita a gabanshi kawai amman rayuwa mai kyau da inganci yake nema mata ba Auren Sauban da Sa'a zata ta cusguna mata ba.
"Shikenan kuyi ha?uri ku kwana a hakan gobe in Allah ya kaimu zan siyo muku gado da katifa. Mardiyya kece babba ki kula da ?annenki kinji?
Sannan kada ki Waga wayar Sauban na riga dana rabaku, akwai abinda nake so in zaunar dake mu tattauna Wiyata. Akwai abinda kuke so ne?"
Mi?ewa zaune tayi ta gyara zamanta da kyau.
"E Baba mu dai so muke zan dinga mana girkinmu daban ba sai mun jira kowa ba dan Allah Baba"
Wallahi Babangida sai yaji hawaye na zubo mishi tsabaragen rauni.
"Bayan wannan kuma me kike so Mardiyya dan Allah kiyi gaggawar sanar dani zan sama muku shi"
Ya ambata a ?agauce cikin zabarin son jin me take so kuma.
"Shikenan Baba, kuma muna so duk juma'a tunda babu islamiyya mu dinga zuwa wajen Ummi muna dubata. Baba ba daWewa zamu yi ba. Inma kaine zaka dinga kaimu ka jiramu duk babu damuwa"
"To shikenan zan duba in gani. Bawai bana son kuje inda Umminku take bane, gidanne kawai bana son kuna yawan zuwa. Amman zan ?o?arta ko sau Waya a watane zan dinga kaiku."
Da wannan matsayar suka tsaya.
A Wakin Ramatu yaje ya kwanta, amman tunanin Cus da ba?in rashin kunyarta wanda a yanzu yake jin dama zata dawo tazo tai ta yi mishi fitsarar idanu zai zuba yaita kallonta tana ?ara burgeshi ya hanashi bacci
Washegari gida ya kaure da yinin biki, shi kuma ya tsallake gidan ya siyo ma su Mardiyya gado da katifa, sai katifa tasu Adda'u. A wajen Mustapha ya amshi kuWin bashi, duk da Mustapha ya sanar mishi babu bashi tsakaninsu amman shi ya kafe kan saiya dawo mishi dashi.
Yana isowa yaga Sauban da Mardiyya a ?ofar gida Sa'a tana dukan Sauban tana zaginshi daidai isowar Babangida.
Ranshi ya kai iyakar sosuwa murmushi mai ciwo yayi kawai ya sakko a gaban motar kaya. Sa'a na ganinshi ta shige gida Babangida ya ?araso ya dafa kafaWar Sauban. Mardiyya dake kuka ya kalla.
"Ki shiga gida Mardiyya kada ki sake kuka"
"To Baba"
Juyawa tayi ta shige, Babangida yabi takun yarinyar da kallo har saida ta kule ya dubi Sauban.
"Sauban kayi ha?uri Mardiyya ?iyata ce, kai kuma Sa'a ce mahaifiyarka. Tunda dai ta nace bata sonka da Mardiyya kayi ha?uri Allah zai Sullo mata da wanda zai sota a yadda taken wani bare can. Yarinya bai kamata a hukuntata da laifin iyayenta ba.
Shin Sa'a ta taSa faWa maka wani abunne dangane da dalilin da yasa za'a haWa Auren naku?"
"A_a Kawu na sha tambayarta ma dalili amman bata faWa mun. Amman Kawu ni koma menene inason in auri Mardiyya kuma mahaifina ma ya amince. Kawu dan girman Allah kada ka rabamu. Jiya yadda naga rana haka naga dare, yanzu haka zazzaSine a jikina, a duba lamarinnan kawu"
Murmushin gefen baki Babangida yayi.
"Sauban kenan. Kayi ha?uri dai wannan auren bazai yiwu ba. Ina mai baka umarnin kada ka sake zuwa wajen Mardiyya kuma kada ka sake nemanta a waya ka barta zuchiyarta ta warke, ka yarda ta manta dakai, kaima ka daure ka mance da'ita kada akan ku ku biyu zumunci ya ruguje"
Hannunshi

19 / 25