Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   5 / 25

12K to 15K   out of 72.9K words

da cikin shege a jikinta. Tur da wannan tarihi da kuka ajjiye mana mummuna."
Kallonta kawai nayi tana cikin ni?ab idandunanta kaWai nake kalla.
"Ke Sa'a kul kika kuma zuwa kusa ma da Wakinnan doka ce Babanku ya saka. Kuma ya haneku da faWan maganganu marasa kyau akan wannan lamarin. Wuce ki bar nan"
Dole ta wuce. Ita kuma ta shigo ta kawo mun abinci na.
Amman jaraba na cina sai zage_zage nake yi ni kaWai akan maganganun da Sa'a ta yaSa mun ban samu damar ramawa ba."
Wajajen sha biyu na jiyo kamar muryoyinsu Rakiya a tsakar gida kuma da halama hayaniya akeyi.
Zuruf na fice ai kuwa ilai rigimarce akan danme Uzairu zuchiyata zai shigo gidan matan aure. Rakiya kuma tayi ram dashi a hannunta tana rantsuwar dole sai ya shiga tunda nice a cikin gidan. Akan wannan aketa jayayya.
"Kunga malamai wannan yaron dai wallahi saiya shiga gidannan. Ai dalili kesa a zagi malami kuma naji kina wani maganar rashin tarbiyya. Ai rashin tarbiyyar Wanku shine babban maras tarbiyya daya iya yima yarinya ciki sabida ?in gaskiya da ?in ALLAH kuke iya buWe baki kuna cewa wasu basu da tarbiyya Sa'a kuka ci akan Uzairu zuchiyata kuke wannan maganar da Gaza ne ko Magazin ba kwa soma ba."
Sa'a na shirin mayar da martani, ni kuma ina shirin zaro wu?ar ?uguna muka jiyo fitowar Baba malam wanda hayaniyar data fito dashi daga Wakinshi kenan.
Babu shiri Sa'a ta wuce sum_sum kai a ?asa.
Malama ?arama ma wucewa tayi tana yi mishi sannu da fitowa.
Bai kulata ba hankalinshi na kaina.
"Lafiya meke faruwa anan. Bawan Allah daga ina zaka shigo har tsakar gidana ka tsaya.
Ke Sabuwa maza wuce ki sake kayan jikinki kada ki sake fito mun tsakar gida da ?ananun kaya ko babu Wankwali"
A mugun tsawace yayi maganar.
Juyawa nayi Rakiya tayi carab ta ri?oni.
"Zo amshi kayan naki."
Amsar kayan nayi a karamar jakata nayi komawata ciki.
"Malam nice mahaifiyar Sabuwa. Wannan wanta ne laifine dan munzo ganin ?armu? Naga sai wani jijji da kai kuke yi kuna faWa. Wannan al'amarin daya faru daga mu har ku babu wanda zaice abune mai daWi.
Uzairu zuchiyata wuce mu shiga"
Rakiya ta ri?o hannun Uzairu zuchiyata zasu wuce Baba Malam ya ri?e hannunshi carab.
Idan ranshi yayi dubu ya Saci musamman dake bai saba Magana ya maimaita ba.
"Hajiya wannan yaron bazai shigar mun gida ba. Kema dan mahaifiyarta ce amman bazan laminci aita kawo mata ziyara ba bazai yiwu ba in dai ba tozartamu kuke son yi ba."
Ni dai ina daga Waki ina sake kaya nake jiyo su
Rikici ya kai har Baba malam yasa anyi mishi kiran samarin gidan daga waje suka shigo.
Nan suka kori Uzairu zuchiyata shi kuma ya fita yanata zage_zage. Rakiya kuma aka barta ta shigo inda nake.
"Lolo wannan uban miji naki haka yake maras mutunci? Dama Maigogul ya sanar dani yadda suka kwashe. Amman ke kinji kin gani zaki iya zama a cikin wannan gidan, bakya gudun faruwar wani abun?"
Ina girgiza kai nace.
Bana jin taoron uban kowa. Babu fa abinda zai faru. Ni kam nazo kenan Rakiya kinsan Allah daga nan sai gidan Babangida. Ke kina ganin in ba hakan muka yi ba yaushe iyayenshi zasu yadda ya aure ni. Shikenan fa in bai aureni ba an cuceni an barnu da Wan shege"
Rakiya ta jinjina kanta bata dai ce komai ba mu kai shiru na wani lokacin.
"Nan Wakin na yaran gidanne?"
E nasu ne ji Waki mai kyau ba irin na gidanmu ba."
"Hmm ita wannan duma dumar itace uwar Babangidan kinga yadda tayo kaina kamar zata dakeni. Harfa cewa take yi wai bata taSa ganin marasa tarbiyya kamar mu ba. Ke ki ji mun mata da Wiban albarka. Ai kuwa Lolo ko mutuwa zasu yi sai kin zama surukar wannan babban gidan.
Kinga bari in tashi in tafi
Su Adama da tare zamu zo dasu, sai nace su dai bari mu soma zuwa muga kamun ludayin abun.
Ke kina ganin da mun tawo duka ai da anyi Satacciya"
Har ?ofar gida na rakata.
Naso in fito amman gardawan Baba malam suka tare hanya bisa umarnin Baba malam akan kada su sake ko le?e in yo. Dariya kawai nayi na koma ciki.
A zaure na huWu muka ci karo da shi zai fita ko kallo bai isheni ba na Wage kaina sama.
A haka dai na kwana biyu a gidan nan yaran gidan sai zurubtun zuwa suke yi
A kwana na huWu ne aka sallamo Malama Babba daga asibiti.

Babangida:.
Washe garin ranar da Sabuwa ta kwana a gidansu da safe dai asibiti yaje ya duba jikin Malama Babba yai ta bata ha?uri shine harda kuka akan sharrin shaiWanne kuma shi wallahi ba cikin shi bane.
Take Malama Babba da jin haka ta sauke ajjiyar zuchiya taji har ?asan ranta ta gamsu da abinda yace.
"Na yarda da kai Babangida. Amman ta yaya zanyi ma Malam magana ya yarda da kai? Kasan Malam yadda Waya ce a wajenshi. Amman zan yi iyakar yina dan ganin na wanke ka. Ita kuma ba?ar dagar yaya za'ayi ta bar gidannan? Bazan iya zama a gidannan muddin tana ciki ba"
Sa'a tace.
"Babu fa yadda muka iya amman zama dole kinsan tunda Baba malam yace ta zauna Magana ta ?are. Tananan tana zuba rashin kunya, ?an uwanta ma marasa mutunci suna nasu. Wawo dake tsaye duk yana saurarensu yace.
"Malama Babba baifa kamata kima yarda da Babangida ba. Ai ya amsa cewar yayi mu"amala da'ita a gaban Baba malam."
Malama Babba dake fama da jikinta tace.
"Amman kasan yaso yayi Magana bayan ya amsa hakan malam ya ?i bashi dama. Wawo Wana bafa zai aikata irin wannan Sarnar ba"
Murmushi kawai yayi shi yasan dama Babangida bazai taSa zama mai laifi a wajenta ba. Asalima son da take nuna mishi da yawa ?ila shi yasa ya jawo musu wannan abun kunyar da za'aita zancan har abada.
Daga asibiti Babangida majalisar abokanshi ya wuce ya nemi waje ya zauna shiru anata hirar mata Babangida dai sai dai in wannan yayi magana ya kalleshi har dai Mustapha ya ankara Babangida baya magana ga majalisa ta hautsine da musun wasu mata biyu kan waccece tafi kyau kowa na tofa albarkacin bakinshi.
"Babangida kacigari tunda ka shigo majalisarnan baka ce ci kanku ba. Meke faruwa ne. Ko sabida rashin lafiyar Malama Babba ne?"
"Uhmm ku dai ku bari
Wai kunsan Sabuwa a cikin gidanmu Wakin mahaifiyata ta kwana dan bura'ubanci?"
Zare idanu dukkansu suka yi, ai sai kallo ya koma sama.
"Kamar ya a gidanku ta kwana. Kaddai akan cikin da tace tana dashine?"
Nan Babangida ya kwashe labari yake ta basu. Yasan akwai yadda mai ?arfi a tsakankaninsu. Cikinsu babu wanda baima mace ciki an zubar ba abokaine su irin na cin mushennan. Tuni Malam Baba ya daWe da rabashi dasu. Amman halin Wan yau yasa Babangida yayi biris da gargaWin Baba malam malama Babba kuma ta goyi bayanshi.
"Tabb amman Sabuwa ta kuikuya maka akuyanci. Amman zata ga bunsuranci.
Kai wanne mataki kake ganin yafi dacewa ma da'ita ne?"
Cewar Mustapha dake tsaye yana ta hargagi da zage_zage"
"Wallahi ban sani ba. Tun jiya nake tubka da warwarar hukuncin da zan yi mata amman ban tuno ba. Mustapha wallahi saina koya ma Sabuwa hankali. Sai taji a cikin ranta ta tsaneni ta kuma tsani bariki. Cikin da take takama dashi saina zubar dashi dan ubanta ko zan mutu ba zata haihu ba."
Haka dai sukaita tattaunawa tare da jinjina girman matsalar da Sabuwa ta saka abokinsu a ciki.
Babangida ya buWe fitar dare da neman mata a cikin kwana biyunnan sosai. A tunaninshi hakanne kaWai zai wanke mishi damuwar da yake ciki. Dan ba ?aramin matsala yake ciki ba.

Baba malam:.
Dama jira yake yi a sallamo Malama Babba daga asibiti ya tara zama yayi musu aman abubbuwan da suke cin ranshi da irin binciken da ya saka akayi mishi akan Babangida da ita kanta malama Babban lokaci kawai yake jira yasa a zauna yayi musu amai.
Bincikenne bai kammala damuwa kuwa sai cin ranshi take yi a kwana bakwai da zuwan Sabuwa Dattijon saida yayi rama. Kallo Waya zaka mishi ka gane baya cikin nutsuwarshi

Sabuwa
A kwana bakwai da nayi a gidan anyi rikice_rikice masu yawa.
Dan duk waWanda suka zo ganina ba'a barinsu ma su shigo tun daga waje ake taresu a hanasu. Daga haka sai rikici ya tashi.
Nima nayi yin?urin fita kusan sau uku abun yaci tura, a yin?uri na huWunne na samu nasarar ficewa da misalin ?arfe Wayan dare motar su Yar Shuwa na bayan layin suna jirana.
A guje na ja motar muka wuce fuu sai Club.
Ina bayan mota sai sigari nake sha ina jina fayau dani tsabar jin daWi
Kwanana bakwai cib babu sigari babu yawo ?afafuna sun gaji har ?ai?ayi suke yi mun.
Ai kuwa muna shiga club na faWa filin rawa na shiga ti?ar rawa ina aikin shan sigari.
Ban jima da shiga Club Win ba Babangida ya shigo carab idanuna suka sar?e a cikin nashi duk da wuta mai kalar dake kunnuwa ta Wauke kanta bamu kasa gane juna ba.
Kamar mahaukacin zaki haka yayo kaina a lokacin wani namiji na shafa jikina.
Fisgata yayi zuwa waje ina turjewa yana jana cike da mugunta.
Bayan motarsu ya buWe ya jefa ni ya rufe.
Ina hangoshi ta taga dafe da kanshi yayi shiru
Nasan Babangida mutum ne mai mugun kishi akan abinda yake so
Nayi mamaki daya nuna kishinshi a kaina a tunanina ai ya tsananeni shi da na farkema laya..
?ar Shuwa da saurayinta ne suka ?araso wajen motar.
"Lafiya zaka jawo yarinya ka turata a mota. Tare nake dasu fa"
Cewar saurayin ?ar Shuwa.
"Dan abu ta kazanka zaka san tare kake dasu. Ba ni kake cema tare kake dasu ba?
Ina zuwa.
Nan Babangida ya soma nannaWe hannun rigarshi
Ai kuwa ya Wane wuyan saurayin ?ar Shuwa faWa harda fasa kwalba da yankan juna.
Ni dai ina mota inata aikin bubbuga murfin motar ga zafi kamar zai kasheni.
Da ?yar abokan Babangida suka jayeshi suka turashi a mota. Mai motar ne ya cilla mishi keyn mota a cinyarshi.
"Kuje ka mayar da'ita gida ka dawo ka same mu."
MRS BUKHARI

Sai mun haWi ranar litinin in sha Allah
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t
.
18066696785.
Hussaina Bello


HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAU?I DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI?
H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE
MAZA TUNTU?E HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA.
KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ?WAR?WATAR IDANU


IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

LITTAFI NA UKU
SHAFI NA BIYAR 5


*SON SO MASOYAN AL?ALAMINA*
*WANNAN SHAFIN DOMIN SOYAYYARKU NE MASOYAN ASALI INA JIN DA?IN YADDA KUKE NUNA ?AUNA GA AL?ALAMINA. YA ZAME MUN DOLE IN FARANTA MUKU KAMAR YADDA KUKE FARANTA NAWA RAN SON SO=???

Ai kuwa da mugun gudu ya figi motar saida kaina ya gwaru.
Haka yaita watangaririya da rayuwarmu a titi.
Yana yi yana kutuntumo manya zaguna yana Wumamun.
Nima bakina kunsan bazai taSa yin shiru ba yana zagina ina ramawa.
Wallahi sai kawai ya faka a gefen wata unguwa ya fito ya dawo gidan bayaa ya kama wuyana ya sha?eni sosai.
Taimakona Waya akwai wu?a a jikina jin ina kiciniyar zareta a gidanta yasa ya saki wuyana.
Na shiga sauke numfashi. Gashi ya haye kaina yayi kane_ kane.
A cikin motar ya tumurmusheni tas har saida ya samu biyan bu?atarshi.
Yana haki yace.
"Wallahi saina sa da kanki kinyi nadamar zuwanki gidanmu
Kin ga wannan tsinannen cikin da bama nawa bane kika li?a mun?
In sha ALLAH shine ajalinki tare zaku mutu dake da tsinannen Wan dake ciki saina zubar da cikinnan wallahi.
Sabida ke tacacciyar ?ar balaja'u ce shine har zaki fito kuzo Club wani Wan iska na shafa ki. Kuma kike tunanin ni Babangida zan yarda cikin jikinki wai nawa ne?"
Sauka yayi a kaina ya dawo gidan gaba yana gyara zaman wandonshi.
Duk da jikina yayi laushi marata har wani zargewa take yi sabida ba ?aramar mugunta Babangida yayi mun ba. Amman
baisa na ragama Babangida ba.
Ai kuwa sai di mu mutu mu uku dani da cikin da kai ribar ?afa ?ila harda mahaifinka
Wallahi na tsanake bana ?aunar in buWe idanu in ganka a duniya .
Sabida kana ganin kai Wan iska ne. Ni zakaima ciki kayi tunanin kaci biredi ka yaga leda kuma Maigogul ya barka?
Kayi kuskure ?aramin Wan iskan dake Soye shi Wan iskane a gidansu.
Ciki saina haifeshi kuma a cikin gidan da aka haifi ubanshi. Shima shegen sai ya taka doron ?asa yayi adawa da ubanshi.
Wallahi in bakai wasa ba wannan shegen sai ta zama ajalinka"
Haka yaja motar har muka iso bayan layinsu muna farfaWama juna maganganu.
Inya faWi goma zan faWi ashirin dan bana tsoronshi sam.
"Fitarmun daga mota ?ar balaja'u kawai
ke da Club har abada duk inda kika je zan kamaki dan dole zan ganki."


Baba Malam:.
Yana zaune akan sallayarshi yayi raka'a biyu a sallar data zame mishi jiki.
Ya jiyo sallamar Malama ?arama a hankali tare da Wan doka ?ofar shima a hankali.
Mi?ewa Baba malam yayi tare da sake duba agogo.
A hankali ya iso bakin ?ofar
"?arama lafiya a cikin darennan zaki tawo?"
Kafin ta bashi amsa Malama Babba ta ?araso wajen.
"Me zan gani ni da kwanana Karama na son ?wace mun miji?"
Ta faWa ba'a faWa ba, ba da wasa ba amman. Dan tasan halin mijinsu sarai. Kuma tasan a cikin halin da Babangida ya saka gidan.
Kallonta kawai yayi ba tare da yace mata uffan ba.
"Ina jinki ?arama menene?"
"Uhm dama Alawiyya ce tace mun wannan yarinyar da take zaman Babangida bata nan ta gudu.
Na dudduba cikin gidannan kab har banWaki amman malam bata nan"
Kai Baba malam ya shiga jijjigawa yatsanshi Waya saye akan leSenshi ya Wan ciza.
Malama Babba babu shiri tayi ?asa da kanta tana jinjina girman munafurcin ?arama. Da kuma kalar rashin tarbiyyar Sabuwa.
"Ya zame mun dole in san menene mafita. Duk da Yaya Hanne tace in bar komai har zuwa gobe ta iso"
Malama Babba a zuchiyarta take maganar.
Wucewar Baba malam ne ya dawo da'ita hayyacinta. Taji dai sun yi magana amman Allah cikin ikonshi bata ji me yace ba.
A tsaye a wajen ya barsu. Yana ?ulewa Malama Babba ta sha gaban ?arama dake ?o?arin barin wajen.
"Wato sabida dama kina hassada da irin son da Malam yake yima Babangida shine kika tawo sanar dashi halin da ake ciki sabida ya sake tunzura ki kara mishi wutar tsanar Babangida ko?"
Murmushi Malama ?arama tayi tace.
"Wallahi ko Waya a tunanina dukka kuna nan tare tunda nasan kece da miji. Kuma a gabana kika zo kika wuce zuwa turaka.
Babba babu dalilin da zaisa in yi hassada da soyayyar da Malam yake ma Babangida. Babangida Wanane, kuma son da Malam yake yi mishi ai baya nufin su ragowar yaran baya sonsu. Sannan hatta ni dake ko wacce tana da Wa mafi soyuwa a gareta wanda tafi ?auna.
Babu kyau dai nuna fifikone domin ina tunanin yana daga cikin kuskuren da aka aikata har aka samu wannan matsalar ma data afku"
Tana kaiwa iyakar nan tayi tafiyarta.
Malama Babba dake jan numfashi da ?yar sabida ciwo da kuma nauyin kalaman da ?arama ta faWa mata yasa ta kasa ma magana.
Wannan itace rana ta farko a cikin tarihi da ?arama ta mayar ma da Babba martani a iyakar tsawon rayuwar da suka yi tare.
Da ?yar ta daddage ta shiga Wakin Baba malam ta kwanta a kan doguwar kujera tare da shiga dogon tunani da fargaban abinda zai biyo baya. Ta wani Sangaren na zuchiyarta tana ro?on Allah yasa kada Sabuwa ta sake tako gidannan.
Baba malam kuwa yana fita ya le?a Wakin samarin yaranshi su shida da sukai ragowa.
Auwalu, Ramadan da Magajin malam ya taso suka soma zagayen neman Sabuwa cikin tsakiyar dare unguwar babu motsin kowa da komai.
Suna shan kwanar layin dake bayan layinsu daidai lokacin Babangida ya faka motarshi kenan.
Kashe fitilun motar da yayi yasa bai hasko su Baba Malam ba.
Sabuwa ce ta fito tana kun?unni Babangida ya biyota tare da matseta a jikin motar.
"Babu shakka Babangida"
Cewar Malam daya iso inda suke"

SABUWA:.
Da mugun sauri Babangida ya sake ni jikinshi har rawa yake yi. Baba malam kuwa sabida tsabar tashin hankali da ruWu kusan faWuwa yayi daga tsaye. Da sauri magajin malam da Ramadan suka tareshi.
Babangida kuwa kanshi ya sauke ?asa jikinshi na wani irin kakkarwa.
Ni kuwa sai tsilli_tsilli nake yi da idanuna"
Baba Malam ya kafe mu da idanunshi kallon ?yama da tsana yake watso mana.
"Daga ina kuke Sabuwa?"
Ya tambayeni murya a kausashe.
Daga gidan rawar dare muke"
"Shi ya nemi kuje kenan. Dake ke shashashace wacce bata da hankali baki san inda yake miki ciwo ba shine kika bishi? Mutumin da yayi miki ciki ya kafa tarihi mai muni a rayuwarki ya nemi ya tsere miki shine har kika kuma bashi yadda. Kuma a gidana za'ayi wannan iskancin ni Baba Malam?"
Ni dai ban tanka ba.
"Yayi kyau ki wuce mu tafi. Daga yau in kika kuma fita wallahi zan yi mummunan saSa miki zaki yi mamakina sawa zanyi a ban?areki"
Iyakar abinda ya faWa kenan ya juya magajin malam da Ramadan na ri?e dashi
Bayansu na bi muka bar Babangida a tsaye a wajen.
A tsakar gida kuma Alawiyya da Malama ?arama muka tadda
"An ganota kenan Malam?"
Kai kawai yake girgizawa ba tare daya iya furta wata kalma ba.
Malama Babba tana kwance taji shigowar Baba malam ya tsaya a kanta yana kallonta.
"Kin cutar dani sosai Saratu. Amman ki sani abinda kika aikata sai yafi damunki fiye da ni.
Za kuma kiga matakin da zan Wauka wanda daga ke har Baban naki bazai muku daWi ba."
Zama yayi yana huci kawai. Ji yake yi tamkar ya cire zuchiyarshi ko ya huta da irin zugin da take yi mishi. Vidiyon Babangida da Sabuwa sai sake haska kansu da kansu suke yi a ?wa?walwar Baba malam. Tunda yake bai taSa ganin mace dana miji a rungume da juna a cikin gida ma ba a waje ba. Amman sai gashi yau yaga Babangida ido da ido rungume da mace a tsakiyar layi. Idanunshi kawai ya lumshe.
Tsugunnawa tayi a gabanshi tana hawaye. Tayi magana ta kasa sabida ba tasan me zata ce ta kare kanta ba. Tasan bata isa ta iya fahimtar da Malam har ya sake yadda dasu ba, shi sau Waya tak yake yadda da mutum.
"Ai dole Saratu ki kasa furta kalmar da zaki kare kanki da ?anki.
Ki fitarmun a Waki bana ko ?aunar in buWe idanuna nayi tozali dake. Babangida kuma har abada ya fita a

5 / 25