Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   10 / 25

27K to 30K   out of 72.9K words

wanda danginshi basu yi mun ba.
Wata haihuwa da Sa'a tayi ne da naje suna ananne farkon haWuwata da matar Babangida mai suna Zahiya fara kyakkyawar gaske mai hijabi da ni?abi.
Abinka da dangin miji an gama faWama kishiya sirrinka ko gaisawa yarinyarnan ta?i muyi sai fele?e take ta faman yi tayi nan tayi can.
Ni da Adama data rakani sai ido muka Wauka muka zuba mata har habaici take zubarwa. To ananne da naji ta ambaci sana'ar kawalci na dira a bakin mitsiyaciya nai mata kafirin duka na tarwatsa taronnan tsab.
Aurenma bai daWe ba suka rabu da ciki a jikinta daga baya cikin ya zube.
Kwatsam Babangida yace in shirya gobe gobe zamu tashi a wannan unguwar zuwa wata unguwar.
Cikin dare yasa naita haWa kaya ina Waurewa a buhu. Sassafe su Labbai suka zo suka taya ni harhaWa kaya mota na waje anata loda kaya.
Muna gamawa naima matan gida sallama babu wacce tace zata rakani face maman Zahira kawata. To Babangida ya gama shafeni da ba?in fenti.
Hmm muna zuwa ?ofar gidan da aka tsaya sai muka ga motar kayan Amaryar a ?ofar gidan akata aikin saukewa gasu Sa'a da su Gudidi da sauran maza ?annen Babangida.
Ga Waki ga Waki ni da sabuwar Amaryar Babangida wacce za'a Waura auren a ranar.
Mu da su muka cakuWa akaita jera kayan Waki matan gida kuma suna ta kallon ikon Allah dai.
Su Adama sai rarrashina suke yi sabida yadda suka ga na damu ainun.
Da daddare muna zaune ni da Rahama da naita ro?onta ta tayani kwana sai ga Babangida ya le?i.
Ganin Rahama ne yasa ya koma. Ni dai a wannan dare da ?yar nayi bacci.
Masu karatu na barku da hasashe ku hasaso duk wani wula?anci da za'aima mace ta muzanta wallahi babu irin wanda Babangida bai mun ba.
Cikin ?an?anin lokaci na lalace na fige na fice a hayyacina. Abinci fa akwai a gidana babu wannan yinwar hakama sutura.
Amman ba?in cikin ba Babangida suke cusa mun yana da yawa sosai.
Gaga gaga haka rayuwa taita garawa matsaloli ta ko wanne Sangare gana Babangida gana matarshi, gana danginshi, ga mai dungurungum na ?an gidanmu.
Ko da yaushe a cikin zuwa beli muke. Wannan ya yi sara, a_a wancan yayi sata, wancan yayi ma mace ciki muke nan a haka zamu ?are.
Ga ?ar Shuwa sabida tsabar damuwar da take ciki ko gidanta bana zuwa daga baya ma suka koma maiduguri can dangin mijin duk da danginsu Waya.
Gaga_gaga
Ina zaune da tsohon cikin Aminu a kan gadon Rakiya anata taWin bikin Sadiya ni dai bana cewa uffan sabida tun jiya nake jina wani iri dai.
Toh ni kam Rakiya zan tafi gida. Jikinne nake jinshi babu daWi inaga haihuwarnan tana hanya dab take da isowa"
Adama ta mi?e tace.
"Ni kaina tafiya zanyi Lolo. Allah ya kaimu asabar Win duk abinda ake ciki kafin masu kawo kayan su zo zamu haWa abinda ya dace.
Ina mota a zaune zani gidane na tuno mai zai hana in dinga duba tunda babu wahala Maigogul a gabana yake yin abubbuwa da yawa.
Murmushi nayi dana tuno ba ?aramin kuWi zan samu ba kuwa.
Ina isa gida na?uda ta kamani matan gidanmu ne suka tsaya mun hardai na haifo Wana namiji naci azaba har sau biyu na suma bayan yaron ya duro duniya.
Ko da aka kira aka sanar ma Baba Malam batun haihuwar shiru har washegari babu wanda yazo barka.
Babangida ma yana Wakin sabuwar Amaryarshi da bata fi wata biyu da tarewa ba.
Jiya dai ya le?o ina kwance bayan mun dawo asibiti.
Amman fa baice mun sannu ba. Ya dai le?a fuskar yaron a gaban Adama yace.
"Wannan dai nawa ne. Amman ita waccan a nuna mata ubanta tun wuri"
Mardiyya na kalla sai ta bala'in bani tausayi sai kallon uban take yi. ?ar Shuwa ma sai sake tabbatarmun take yi Mardiyya ba ?ar Babangida bace duk da kamanninsu, ni dai ce mata nake yi ta bar wannan zancan yarinya dai tashi ce. To shima bai yadda tashin bace.
To yau da muka wayi gari babu wanda ya le?o mu tsakanin Babangida da matarshi. Ga jariri bashi da sutura sai kayan Mardiyya na jinjirantaka ake saka mishi a hakan
A cikin kwana na uku da daddare Baba malam yazo yayi mun barka ya Wakko dubu ashirin ya bani.
A cikin kudinne na samu na bayar da Winki, su ?unshi da kitso duk a ciki nayi.
Ranar suna da safe sai ga Amarya ?ebe_?ebe ta shigo da atamparta a leda ta tarar dasu Labbai harda Uzairu zuchiyata sunata ?ulla zoSo da kunun aya.
Ta yi mun barka ta bani wannan Atampa ta fita.
Haka akaita zuwa suna ?awayenmu na makaranta, ma?ota da ?an gidanmu.
Da rana can wajen azahar tawagar gidansu Babangida suka iso.
Daga lokacin taron suna ya watse aka rabu tsiya_tsiya dambe har ma?ota Adama ta kwaSe ma Sa'a hijabi a ?ofar gida akaita karawa.
Zagi ta uwa ta uba sabida Aminu yaci sunan mahaifin malama Babba bisa umarnin Baba malam, shine fa wannan rikicin.
Ni kuwa sabida tsabaragen ba?in ciki Waki na shiga na kulle sai kuka. Da la'asar gidan suna babu kowa duk kowa ya watse. Ga ubn tulin aiki da ragowar abinci da ba'aci ba.
Sabida tsabar haushi haka na goya Aminu a baya Mardiyya na biye dani na fito naita aiki. Abinci kuwa matan gidanmu babu wacce tayi girki abinci faca faca har ma?ota. Maman Abdul ce tai ta tayani aiyukannan zuchiyata kamar zata fashe dan ba?in ciki.
Malama Babba har gida tazo washegari ta tusa ni a gaba da ?anta akan sai dole dole ya sake ni tana yi tana kuka.
Ana cikin haka Babangida da biro da takadda a hannunshi sai muka ji shigowar Baba malam yazo akan faWan da aka gwabza jiya dan Sa'a ma tana asibiti sabida mahangurSan data dinga sha.
"Yayi kyau Babba ashe da kika ce asibiti zaki je nan kika tawo kin tusashi gaba yayi saki ko?
To kai kaji matsawar hannunka ya saki yarinyarnan to tamkar ka saki gyatumarka ne wallahi, kuma bazan yafe maka ba. ZaSi ya rage gareku. Ramadan wuce ka mayar dani. Ke Sabuwa Allah ya raya Baba Aminu. "
Jiki a sanyaye malama ta fita, Babangida ya dinga dukana gani da Wanyen jego babu ?arfi a jikina
Take jini ya Salle mun, kusan wata guda nayi a asibiti dan na daku sosai.
Haka aka kuma kwatantawa a sunan AWWa'u sabida shi kuma sunan mari?in Malama Babba ne yaci ?anin mahaifinta wanda a hannunshi malam ya auri Malama Babba. Sai dai shi wannan ba'a watse ba dangin dai Babangidanne suka watse. Amman fa rikici harda zubar da jini dattijan unguwane suka yayyafama ?urar ruwa a lokacin Babangida yayi kuWi yana da mota kuma naji labarin yana gini ma, ya saki mace ta biyar yana shirin zai ?aro ta shida zuwa bayan ?aramar sallah nima a bakin Alawiyya naji da bazan sani ba sai dai inga ana shigo da Amarya.
Ni kuma a lokacin na zama mai duba mata na zuwa cikin sirri ina musu duba kuma suna samun biyan bu?atarsu, ni kuma ina amfana da kuWaWen hannunsu harda ma kaji da turamen zannuwa.
Yadda harkar take duk bige ce gaskiya. Babu komai a cikin duba face ?arya da suddanaru.
Bugun ?asa dai anayi ne dan a duba tauraron mutum a cikin waWannan taurarinne ake duba abinda zai iya faruwa, misali kaga mutum a gidan bakwai ko huWu, ko gidan tara. Ko kaga wata guguwa, ko wani duhu, ko wani irin haske mai tsanani. Siddabarune mara wahala sai dai in baka koya ba.
Iyakar abinda kaWai na iya kenan tunda ni nasan la?anin da ake amfani dashi wajen duba.
Magunguna kuma duk bige ne, kuka, munjirya, rawaya, sabara, itacen kuka, sassa?en mangoro babu abinda bana bayarwa ince mace tayi amfani dashi. Kuma sai kuga an dace dake shi dama tsafi gaskiyar mai shine na yarda da wannan hausar.
Amman bana aiki da aljanu, damfara ce kawai. Yanzu dai kun gane ina fata? (Bana son fito da ha?i?anin sahihin bayaninne dan gudun matsala)
Gaga_gaga
Haka abubbuwa suka ci gaba da faruwa bayan Sallah kuwa sai ga Amarya Hamida an kawota. Kafin a kawota nayi muku tsallake kusankwana Babangida yakke yi waya da Hamida akan gadona ina ji ina kuma gani. A lokacin na soma sanyi na saduda da duk wani rashin kunya hankalina ya dawo kan tarbiyyan ya??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????rana musamman da Mardiyya ta soma zuwa makarantar boko da islamiyya.
Babangida sai ya sake samun damar ci mun mutuncina yadda ranshi yaso.
Abubbuwa da suka ci gaba da faruwa suna da yawa, tunda kuWi ya zauna ma Babangida sai ya sake buWe faifayin neman matan baza, da yawan yin Winkuna, da yawan zage_zage da gore_gore dai.
A cikin wannan wahalar Allah ya ?addara na haifi Malama haihuwar da tafi ko wacce haihuwa bani wuya kenan.
Haihuwar da bazan mance rikice_rikicem dake cikinta ba. Haihuwar da ko awo ban taSa zuwa ba.
Allah ya ?addara aka sama yarinya suna Saratu. Sunan da har gobe mai sunan na nadamar da Wiyata aka saka ma wannan sunan take yi.
Cikin yarannan guWu dana haifa in aka cire mardiyya basu taSa saka daidai da wando ace na ubansu bane har saida suka girma da abun duniya ya isheni shine nayi tattaki na sanarma Baba Malam duk halin da nake ciki tun daga farkon auren har zuwa lokacin da nakai ?arar. Shine Baba Malam yaci mutuncin Babangida sosai da sosai kuma ya zamana yana yawan tuntuSata halin da nake ciki da yaran.
Bayan Hamida Babangida ya auri mata biyar sune Zainabu, ita tana da Wa dashi yana hannun Kawu manga. Farida itama ta haifi Wiya mace dashi, sai Abida basu da rabo, ?ar shuwa, Ramatu.
A ta?aice iyakar abinda zaku samu kenan a cikin haiwayen da akayi.
Ragowar na barku da hasashe. Amman kuimun adalci wajen nazari mai kyau kafin ku yanke hukunci.
Inci gaba da zaman ?as?anci da auren Babangida.
Ko in matsa in gina sabuwar rayuwa?

Mrs Bukhari
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA TARA



DAWOWA DAGA LABARI

Babangida:.


Yana zaune a benci shi kaWai. Maza masu majinyata a asibitin wasu suna kwance a tabarma, yayin da wasu suke zaune a tabarmar.
Babangida dai sai aukin kiran lambar Sabuwa yake yi, abinda yafi komai Waga mishi hankali jin wayar tata a kashe yanzu_yanzu.
"To mutuwa wayar tayi, ko kuwa kashe wayar Sabuwa tayi ne?"
Shiru yayi yana tunanin yadda ya damu akan son jin jikin Sabuwa. Kwatsam yaji wayarshi tana ruri ?ur ya ?urama ba?uwar lambar idanu. Tabbas yasan kiran na dole ne in aka duba lokacin da akayi kiran lokacine da mafiya yawan al'umma baccinsu tuni ya jima da yin nisa.
A kasalance ya Waga wayar kirjinshi na dokawa
"Babangida Adama yar Lolo ke Magana"
Babu shiri ya bude baki har yana harWe harshe wajen furta.
"Adama kaddai jikin na Lolo ne ya?i?"
Zaka iya fuskantar tashin hankali sosai a muryarshi
"Uhm Babangida dama jikinne da sau?i. Lolo fa ta gudu bata gidanka. Kuma bata gidanmu ma dan yanzu muka gama waya da ?an gida"
Baisan sanda ya mi?e tsaye ba sai jirine ya dawo dashi ya zaunar da karfi.
Cikin rarrabe kalma yace.
"Adama kika ce Sabuwa ta gudu fa ba'a san inda take ba? Hasbunallahi wa ni'imal wakil. Gani nan zuwa gidan yanzu"
?it ya kashe wayar tare da dafe gefen zuchiyarshi da yake jin tamkar zuchiyar tsaga ?irjin zata yi ta faWo.
Ashe Sabuwa haka ta tasirantu a rayuwarshi shi yananan yana haukarshi baisan itace cikon numfashinshi ba?
Mi?ewa yayi cikin dauriya duk da dai jiri na dibarshi amman dole yaje gida yanzu abi duk inda za'abi dan ganin matarshi ta dawo gida cikin ?oshin lafiya "
?akin jinyar ya shiga ya tarar Sa'a bacci take yi a zaune. Malama Babba kuma yana da tabbacin sai zuwa gobe allurar baccin da akai mata zata saketa juyawa kawai yayi ya futo bakin asibitin zuchiyarshi cike da ciwo da tunanuka. Duk shi kaWai sai bama mutane wahala yake yi duk sabida shi kaWai iyayenshi na kwance basa iya gane kansu shi ko wanne irin son kaine dashi haka ne?
Kai ya girgiza yanata aikin istigifari a fili da zuchiya ga kukan zuchi da yake yi wanda yafi na zahiri ciwo da duka.
Titi tamkar an share shiru babu gilmawar ko mota Waya. Babangida ganin wankin hula na shirin kaishi dare yasa dole ?anwar na?i ya kira Mustapha a waya dan ya kawo mishi Wauki. Wayar dai ta shiga sai ruri take yi, Babangida na adda'ar Allah yasa Mustapha ya Waga.
Ai kuwa Mustapha ya Wauki wayar muryarshi tarwai ga sautin kiWa na tashi a inda yake da dukkan halamu baya ma gida yabi dare yana shuka tsiya tare da ?a?an iska.
"Ustaz kaine a cikin darennan ko dai ruwa ka koma ne?"
Girgiza kai Babangida yayi irinna wanda yayi nadamar gaske yace.
"Allah yaimun tsari da komawa wannan ruwa mai cike da ?azanta. Kaima bazan gushe ba ina maka nasiha akan kaji tsoron Allah ka tausayama iyayenmu, matanmu, da ?a?anmu. Mustapha ko a ina kake kazo bakin asibiti ka kaini gida. Sabuwa ce akace mun bata gida ana zargin guduwa tayi"
Mustapha yace.
"Guduwa kuma? Wani abun ya sake faruwane banda wanda ya faru a kotu?"
Sai da ya lumshe idanunshi da suke mishi yaji kana yace.
"Shidinne kasan dole abun ya jijjigata. Kai dai tawo dan ALLAH "
Murmushi Mustapha yayi yace.
"Kaci sa'a ina kusa bani minti goma in sallami Ruda"
?it ya kashe wayarshi. Kafin ya kashe Babangida yana jiyo ?aran summatar Ruda da Mustapha yake yi.
Shi kuwa dake a cikin damuyoyi yake masu girma tare da lissafin rayuwa da kusakuren daya yai ta tabkawa Sai yaga Mustapha ya iso da wuri alhalin saida yaci mintuna ashirin masu kyau.
Zama yayi a gaban motar ya rufe idanunshi zuchiyarshi na dokawa da ?arfi.
Mustapha yayi juyin duniya su Wan tattauna Babangida ya?i fur.
"Allah ya kyauta. Ka kwantar da hankalinka babu inda zata je fa. Inma zata gudu taje wani wajen bafa zai wuce wajen Khalid ba. Kum....
"Ya'isheka Mustapha kada ka sake jifan Sabuwa da wannan kalmar. Bana jin Sabuwa zata hugu taje wajen wani Wan balaja'u da aurena a kanta. Yaya kake son nayi ne in haWiye zuchiya in mutu kaima ka huta ko? "..
Ya ?arashe maganar cikn haki. Haki?a Mustapha ya sake jefa rayuwar Babangida a cikin garari ya kunna mishi wutar kishi bisa wutar da take ta tafasa jini da tsokar jikinshi.
Suna isowa ?ofar gidan Babangida bai jira Mustapha ya gama gyara tsaiwa ba ya dire kawai.
A baya Mustapha ya bishi da sauri sai a falon Sabuwa suka haWu.
Su Adama suna zazzaune a falo sunyi shiru ciki harda Mardiyya.
"Adama kika ce Sabuwa bata nan. Kuma bata gida?"
Babangida ya tambaya a kidime"
"Wallahi kuwa Babangida. Ni ko dana farka nayi tunanin tana banWaki ne. Ashe Sabuwa ta hau dokin zuchiyar abinda su Rakiya sukai mata, da irin tashin hankalin da ka jima kana jefata a ciki. Ta yanke hukuncin tunda ba zaka saketa ba ta shiga duniya. Mu faWa ma kanmu gaskiya Babangida kayi ma Sabuwa cin zarafin da ba duk mace ba. Ko mu ?an uwanta ka wula?antamu. To Sabuwa dai ta tafi"
Da mugun sauri ya wucesu zuwa uwarWakin Sabuwa. Yayi tsaye kawai dan baisan abunda ya shigo dashi ba.
Idanunshi suka sauka akan akwatin data haWa kayanta ta barsu. Babu shiri ya isa ya buWe akwatin yana kallon kayan data gwamutsa a ciki. A haka ya bar akwatin a buWe ya isa gaban sib duk ya bubbuWe ji yake tamkar zaiga Sabuwa a ciki. Rigar baccinta ya zaro ya ?an?ame a hannunshi tare da rufe idanunshi yana tuno ranar da yayi mata wani fyaWe a lokacin tana sanye da rigar a jikinta.
A duk yawon biye biyenshi da duk samfurin matan daya aura ha?i?a Sabuwa tayi fice WanWanonta daban yake dana sauran matan daya sani. Wannan yana daga cikin dalilan da yasa duk yadda yake nuna ma Sabuwa ?iyayya a fili a can ?asan zuchiyarshi akwai sha'awarta wadda ashe cakuWe take da wata iriyar soyayya mai haWe da kishinta wanda shi baisan wannan motsin soyayya bane sai a cikin kwanakinnan. A tunaninshi motsin sha'awarta ne.
BuWe idanunshi da suka rine yayi ya ajjiye rigar ya fito jikinshi a mace.
"Babangida inaga tunda da mota a darennan mu garzaya gidajen ?anne ko Allah zaisa Sabuwa taje can Win sabida zukata su samu nutsuwa."
Cewar Labbai
Kamar wasa suka soma zagaye cikin dare tare da buga gidajen mutane.
Abu kamar haWin baki dai har suka gama karaWewa ko wanne gidan ?awayen Sabuwa har gidan Layuza suka je zancen Waya ne Sabuwa bata zo ba.
Zuwa lokacin yaci in asibiti aka kai Babangida a bashi gado tare da bashi kulawar gaggawa. Amman Mustapha ke ri?e dashi a masallacin layin gidansu Sabuwama sukai sallar asuba. Su kuma su Labbai suka shiga gida.
Saida suka idar da sallar sannan sukai sallama a ?ofar gida aka basu izini, sai ga Babangida a tsakar gidan su Sabuwa.
Yana shiga kiran wayar Sa'a na shigowa wayarshi sai lokacin ya tuno da batun Malama Babba ma.
"Assalamu alaikum Yaya Sa'a?"
"Babangida kana inane na futo Sallah ban ganka ba. Kaddai kace mun baka kwana a asibitinnan ba. Ko kuma Club Win ka zame jikinka ka tafi tunda ka saba jawo mana maganar da zata hanamu bacci?"
Idanu ya lumshe yana jin wani abu mai tauri a ma?oshinshi yana tokare mishi harshe. Yana ji tana ta Hello Hello amman ya kasa buWe baki ma yayi magana. Ita a nata tunanin network ne yasa bata ji maganar Babangida ba. Sai ta kashe wayar. A hankali ya sauke wayar a kunnenshi cike da girma Babangida ya gaishe da Rakiya da Hauwa. Nan aka shiga kiran ?an uwa na ?auye ko Lolo taje wajensu.
Babu labarinta sam.
"Babangida kaje ka nutsu Lolo ba Sata tayi ba ba kuma saceta akayi ba. Babu mamaki Khalid ne ya hure mata kunne shi yasa ta gudu taje wajenshi. A babban asibiti yake ko zaku je mishi da yan sanda a kamashi zai fito da Lolo nayi imani tana can."
Cewar Rakiya kenan.
Wata ?atuwar ajjiyar zuchiya ya sauke yana jin duniya na juyawa dashi kamar gajimare zai sakko mishi a ka.
Matarshi wani ?ato ya Wauketa ta koma wajenshi bacin da aurenshi a kanta uwar ?a?anshi. Wai dama haka bariki ?azantarta take ne?"
Kai ya ri?e kawai Mustapha ya ri?eshi suka fita.
"Mardiyya ja ?annenki ku shiga ciki"
Cewar Adama kenan. Amman kafin ta rufe baki Mustapha ya dawo.."Mardiyya ku tattaro mu tafi a kaiku gida"
Labbai tace
"Na zaci za'a

10 / 25