Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   12 / 25

33K to 36K   out of 72.9K words

hankali a hankali har na gama.
KarSan kwanon yayi ya ajjiye ya haWo mun shayi a nanne nace mishi na ?oshi.
Magunguna ya Sallo ya mi?a mun ya Salle murfin ruwa ya mi?o mun.
Watsa magungunan nayi a bakina na bisu da ruwannan.
"Allah ya ?ara sau?i. Ga kaya nan na tawo miki dashi. Zan turo sista zata zo ta taimaka miki. In kina bu?atar ganina ki mata magana. In kina bu?atar wayarki ma tana hannuna. Ya kamata a kira wani naki ko?"
Da sauri na Wago na kalleshi.
Dan Allah in a kunne wayar take ka kashe. In a kashe take na ro?eka ka sakata a bola bana bu?atarta, kuma bana bu?atar kowa"
Jin na fadi haka saiya lallaSani har saida ya tabbatar hankalina ya kwanta kafin ya tafi.
Da taimakon sista na sake kaya.
Sabuwar doguwar riga yar kanti ce a ledar da mayafinta. Sakawa nayi nawan dana cire na mayar cikin ledar. Saida na Wauro alwala na sake biyo bango na dawo gadona.
A lokacin ne na samu zarafin ?arashe biyan bashin sallolun da ake bina. Sun cika, a_a nayi sun wuce wallahi a lokacin ban sani ba.
Bani na sake gane kaina ba sai washegari.


Babangida:.
Bayan an sallamesu daga ofishin ?an sanda kai tsaye gidan Mustapha suka wuce yaje zai Wauki mashin lifan da Mustapha ya bashi kyauta da ya?i karSa.
Ya?i shiga gidan Babangida yana jingine a bakin get Win gidan har Mustapha ya fito jaye da mashin jin.
"Bari in fito da mesa a wanke kaga tayi ?ira dake ba hawa nake yi ba."
Mashin jin sabone sosai dake siyan jin daWine, haka hawanma na ra'ayine.
Mustapha da kanshi ya wanke mishi lifan din ya dan?a mishi kin.
"Gashi bafa aro na baka ba kyauta ne. Babangida me zai hana ka koma sana'arka ta baban bola.
Shi kanshi Alhaji Abubakar Baban bola ya kamata a sake tuntuSarshi kan kuWaWenka dake wajenshi, inta kama ma sai mu koma kotun kome kake gani?"
Idanu ya lumshe saida ya haye mashin Win kana yace.
"Yanzu batun Sabuwa shine abunda yafi komai mahimmanci a wajena Mustapha. Nagode da kyautar lifan. Sai ka jini."
Mashin Win ya tayar ya bar wajen zuwa gidanshi kai tsaye domin yaga a wanne halin su Mardiyya suke.
A tsakar gidan ya tadda su ?ar Shuwa suna ta hira. Yaji duk munafurcin Sabuwa da ?ar Shuwa take yi da irin watsar mata da daraja da take yi. Ba ?aramin sha?a yayi ba.
Wucewa yayi da mashin dinshi Sangaren Sabuwa ya ajjiye a bakin ?ofar Wakin.
A kitchen yaga Mardiyya a tsaye tana musu girki. Aminu kuma wanke wanke yake yi. AWWa'u da Malama suna zaune su kuma suna Sare Maggi.
Turo ?ofar yayi ya shigo.
"Sannu da dawowa Baba"
Cewar yaran dukka.
"Baba anji labarin inda Ummi take kuwa?"
Mardiyya ta tambayeshi muryarta na rawa.
KafaWarta ya dafa yayi ?asa da muryarshi.
"A_a Mardiyya. Amman ku kwantar da hankalinku umminku tana cikin ?oshin lafiya a duk inda take. Kuma zata dawo Wakinta tayi fishine dani, amman zata sakko ta dawo mu yi rayuwa mai kyau"
Shiru Mardiyya tayi kawai shi kuma Babangida ya dubi tukunyar dake kan gas kayan miya take soyawa. Agogon hannunshi ya kalla azahar tayi.
"Ba'a baku abinci bane naga kina girki, ko ummomin naku basu san kunanan bane?"
Ya tambaya da mamaki.
"Sun san munanan sun shigo ma Wazu suna tambayar ko munji labarin anga Umminmu"
Kai ya girgiza kawai.
"Ku sauke tukunyarnan zansa a kawo muku abinci. Ku shiga ciki. Ku kuma Aminu ku yo alwala mu je masallaci."
Yana tsaye har su Aminu suka fito.
Sake wuce matan gidan suka yi dai a inda ya barsu.
Ganin zai fita da yara yasa ?ar Shuwa ta mi?e ta biyo shi da sauri.
"Baban Fati ina kuma zaka je, kazo ka wuce alhalin kasan a Wakina kake?"
Kallonta yayi kawai tare da girgiza kanshi kawai bai samu zarafin ce mata uffan ba.
Wucewarshi yayi ita kuma tana tsaye har saida taga sun shiga masallaci.
"Allah ya soka wallahi. Ita kuma Sabuwa ta fita a rayuwarka kenan. Ko banza nayi galaba a kanta. Nasan ko aure zata yi a gaba ba dai ta samu irinka ba. Inma ta aurun kenan.
Dariya ta kwashe dashi ta koma cikin gida. Babu Sallah sai sake share wajen zaman gulma da suka yi harsu Babangida suka dawo.
"Ku shiga ciki ina zuwa zan kawo muku abinci"
Wucewa yayi Wakin ?ar Shuwa ya nemi kan kujera ya zauna. Atampopi guda biyu da leshi Waya ya gani a ajjiye a hannun kujera. Tabbas atampar ankon ?anwarta ya gani leshin ma anko ne da yace bazai iya siyan mata ba bashi da kudin.
Bai gama tunanin ba sai gata ta shigo ta nemi waje ta zauna.
"Sannu da shigowa. Yaya na ganka da sabon mashin siya kayi, shine da nace kayi mun ankon gidanmu ka?i kayi ko? Ai babu damuwa gasunan ka gansu Wazu Mama ta aiko amaryar dashi ta karSo mun bashi a wajen dillaliya tace za'ayi mata biya biyu zuwa bayan biki"
Ba?in ciki kamar ya halakashi haka yake ji.
"Baki yi girki bane?"
"Nayi aina Wauka bama zaka iya cin abinci ba sabida Sabuwa data gujeka. Ashe duk yaudararmu kake yi kana son matarka bariki kawai kake yi mana. Hmmmm bari in Wauko maka abincin.
Mikewa tayi tana wata tafiyar iskanci ta Wakko mishi abinci a plate abinda yafi tsana kenan shi a rayuwarshi yana son food flaks ( Wibi da kanka) sosai.
"Ga abincin bari in kawo maka zoSo"
Yawu ya haWiye kawai ya buWe abincin shinkafa da wake da mai da yaji ne, sai maggi star guWa Waya a ciki harda lemun tsami ?arami aka yanka mishi.
Yatsa yasa ya taSa abincin tarara babu ko Wumi. Da kallo ya biya harta kawo mishi zoSon ta ajjiye mishi a gora da kofin roba.
"Nace wai baki san abincin da sanyi bane kika kawo mun a haka?"
Da faWa yayi maganar dan ya zo wuya. Ita kuwa cikin salon sake cunkusa ba?in ciki tace.
",kasan ba kuWin gas ka bani ba, baka bani na kalanzur ba gawayine. To ni wallahi bana iya kunna gawayi kalanzir na siyo gora Waya kuma tas ya ?are."
?ur yake kallonta yana ji kamar ya rufeta da Wan banzan duka.
"To naji kulolinki kuma me ya same su, kinsan bana cin abincin da aka kawo a plate. Kai da gidanka ba za'a kawo ma abinci a kula ka Webi da kanka ba. Sannan ya na bayar da kuWin kayan miya zaki dafa shinkafa da wake har talaucin nawa ya kai wannan matakinne?"
Baki ta zumSure kawai bata ce mishi uffan ba.
Mi?ewa yayi yana tsaki yayi ficewarshi zuwa Sarayin Sabuwa.
Gas ya kunna ya tsayar da sanwar Taliya dama Mardiyya ta riga ta soya jajjage. Firiza ya buWe yaga suna da komai kifi guda Waya ya Wakko ya daddatsa. Murmus???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hi yayi dsya tuno Maigogul sanda yake yanka ma su Sabuwa kifi a Kitchen washegarin aurensu. Jin wannan datsar yasa yaran suka le?o.
"Baba bari in dafa."
Da sauri Mardiyya ta amshi kifin shi kuma ya shiga ciki. Kai tsaye banWakinsu ya shiga. Bayinnan tsab tsab dashi sai ?amshin sabulun wankan Sabuwa na ruwa yake yi.
Idanunshi ya lumshe ya sakarma kanshi ruwan sanyi.
Tunanin Sabuwa na sake bujiro mishi da irin maganganun banzan da Khalid yayi mishi shi da matarshi. Yayi mamakin yadda rashin Sabuwa da gaske ya dakeshi kuma yana mamakin irin yadda yake fata da burin sake ganin Sabuwa. Harma a ranshi ya gama yanke in Sabuwa ta dawo zai yi zama na mutunci da'ita zai sauke duk wani ratayayyen hakkin daya rataya a wuyanshi nasu. Kuma zai mayar da Sabuwa ta daban cikin matanshii, zai nemo daraja ya lulluSeta dashi lib.
?aran wayarshi dake cikin bayan gidan ya dawo dashi kan hankalinshi. Kawu Manga ne
Babu shiri ya kammala wankan ya fito. Maimakon ya fita saiya shige uwarWakin Sabuwa. A nan ya tadda yaran suna cin abinci a faranti.
Yana zaune a bakin gadon yana waya da Kawu Manga Mardiyya ta kawo mishi abinci a kula ta Wauro plate da cokali da abun diba irin yadda Sabuwa ta koyar da'ita.
Gaga_gaga haka abubbuwa sukaita tafiya wasane gaske ne Sabuwa dai babu ko labarin wanda yace ya ganta ma. Duk wani neman daya dace ayi duk anyi amman ba'a samu labarinta ba.
Ta Sangaren Baba Malam bai san da Sacewar Sabuwa ba har saida ta cika kwana uku cib da Sacewa a ranar ma Maigogul ne yazo duba jikin nashi shine ya fasa maganar har Baba Malam yaji.
Yaji damuwa sosai ya kuma yi al?awarin da zaran jikinshi ya warware zai du?ufa ro?on Allah akan ya dawo da tunaninta ta dawo cikin ahalinta.
Hakan ma yasa magajin Malam ya tattaro kan almajirai akaita adda'a har sauka Malam Baba yasa akayi. Malama Babba kuwa labarin Satan Sabuwa kusan shi yasa ta samu lafiya kwananta uku aka sallamota sai tace Wawo ya kaita gidan Yaya Hanne ta gaji da zaman kaWaici da take yi a gidanshi.
Hakan kuwa akayi Malama Babba ta koma gidan yarta da zama tana jiran tsammanin ranar da Baba Malam zai huce ya bata izinin dawowa Wakinta tunda wacce ake ta?addamar a kanta ta tafi yawon duniya a cewarsu.


Ta Sangaren gidansu Sabuwa kab ?an Wakinsu cike suke da damuwar rashin sanin inda Sabuwa take. Amman Rakiya da Maigogul ko gezau basu saduda ba. Gara ma Maigogul wani sa'in in yaran suka mishi ba?ar rowa yakance.
"Allah ya ji?an Lolo ba dan ta mutu ba. Kai Alkhairi Allah ya kai mata a duk inda take"
Ranar data cika kwana huWu da Sata sai fa abun duniya yabi ya ishi Maigogul shine harda zazzaSi, ranar a gida ya wuni a kwance sunata tabka rikici da Rakiya. Ya kuwa zageta ta uwa ta uba akan halin ko in kula data nuna akan lolo.
A lokacin tabbas kab ?an gidan sun yadda matsayin lolo ya bambanta da nasu a zuchiyar Maigogul.
Adama kuma Allah dai ya nufa bazawarinta ya kawo sadakinta amman yace ta jirashi har sai ya kammala gina Sarayin da zai ajjiyeta kafin ayi auren. Ita gudun ma kada ya kuSuce mata gaskiya taso a Waura auren taci gaba da zama a inda suke haya dan ita tsoronta kada ya fasa aurenta. Duk da Maigogul ya baje tabarmar tsubbu ya haWa mata turaren muhibba dan a binciken da Maigogul yayi ya gano ba ?aramin dukiya Allah ya huwace mishi ba. Gabaki Waya hankalinshi ya dawo kan Adama.
Yayin da su Labbai da su Sadiya suka ci gaba da zawarci Qamriyya ma har anci talatar laraba a gidansu tayi mata da ciki ma karami aka fafarota uwar mijin ashe ba'ai bincike ba sai daga baya uwar mijin taji shine fa tasa Wanta gaba saida yayi sakin. Ke Qamriyya jin zafin an sakeki yasa ta zazzage uwar miji tas har tana mata barazanar duka a haka dai tsiya tsiya aka rabu ta dawo taci gaba da yawonta ga ciki a jikinta.
Uzairu zuchiyata kuma kusan abun nema ya samu ya samu wata baturiya da suka hadu a yanar gizo kamar dai wasa suke abota har abun yakai da sun mallaki number juna suna magana ta manhajar WhatsApp. Uzairu sosai ya zage yake bama Felisha kulawa duk da dai ba'a kai ga soma furta love you_love you ba. Amman da dukkan alamu Uzairu zuchiyata yayi kasuwa.
Kuma bashi da wani burin daya wuce Felisha ta Aureshi ya bar najerian ma baki Waya ya huta ma ranshi.
A ko da yaushe bashi da mafarkin daya wuce na barin ?asa.
Wannan kenan.

Mrs Bukhari
[8/16, 9:11 PM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA SHA ?AYA (11)

*AKWAI WATA BAIWAR ALLAH DAKE FAMA DA CUTAR SANKARA WATO KANSA A TURANCE*
*SUNA BU?ATAR TAIMAKONKU KASANCEWARSU MASU ?ARAMIN ?ARFI YANZU HAKA TANA GADON ASIBITI CIKIN MAWUYACIN HALI GASHI ?AN UWANTA BA MASU ?ARFI BANE
GA MAI SON TAIMAKA MUSU A LAMBAR ASUSUN BANKINSU DA LAMBAR WAYARSU
8168309714,HAUWAU ABDULLAHI,OPEY, PHONE NUMBER 08055695830 ALLAH YASAKA DA ALJANNAH






Sabuwa:.

*Bayan wata guda harda Woriya*

Ina zaune a bencin ?ofar Wakin dana gama jinya dan yau aka sallameni kuma alhamdulillah jikin nawa da sau?i.
Kuma na samu sau?in damuwa sosai dan Dr Kamilu ya haWani da terafi Dr mace, da farko dai duk yadda taso dani ta kasa shawo kaina. Sai da muka soma sabawa ne har na saki jiki da'ita dake Allah yayi musu wata iriyar baiwa sosai. Sun iya tarairayan marar lafiyansu kuma suna da hanya da salo_salo sosai na dukan cikin mara lafiya, da bashi misalai wanda har sai mara lafiya ya gamsu Wari bisa Wari dasu ya fasa cikinshi sun san matsalarshi. Duk da akwai abubbuwa da yawa wanda na sakaye ma Dr Fatima ban fayyace mata ba. Iyakar irin rayuwar da nake yi a gidan Babangida da dalilin fitowata kaWai na sanar mata.
Amman ban faWa mata a Club muka haWu da Dr Kamilu ba sabida ya gabatar dani ne a matsayin ?anwa ta jini.
Sai ta fahimta a matsayin auren dole kawai akayi mun. Duk da a cikin zuchiyarta wallahi bata yadda da labarin dana bata Wari bisa Wari ba. Kuma tana yawan tambayata in dai nutsu in faWa mata gaskiya dan a magance matsalar dake damuna. Dolen doliya na fasa mata cikina taji duk sirrina, tayi mun rantsuwar wannan sirrin a ofishinta za'a birneshi babu mai ji.
Uhm bayin Allah makaranta wai ku kunga matan auren da suke zuwa wajen terafis kuwa? ( Allah yasa ina faWan sunansu daidai. Ayi ha?uri ban iya turancin bane amman nasan kun gane=??) Hmm Allah yayi yawa dasu, wasu iyayensu ke kawo su, wasu kuma ?annensu, ko yayyensu ke kawosu. Mata ana cikin damuwa da jarabawa gaskiya.
"Sabuwa kin gama haWa kayan naki har kin fito?"
Cewar Dr Kamilu dake tsaye a kaina.
E Yaya na fito asibitin duk ya isheni wallahi"
Dariya yayi harda tuntsurawa. Ya tsugunna ya debe mun kayana dana haWa nima na Webi wasu muka wuce har zuwa wajen motarshi.
Saida muka kama hanya yake sanar mun wajen mahaifiyarshi zai soma kaini saina murmure kafin su rakani gida. Kuma zasu yi tsayuwar daka kan kes Wina tun ina asibiti yayi mun wannan al?awarin.
Nagode sosai Yaya da irin taimaka mun da kayi. Itama Umma ina godiya sosai a gareta."
Dariya yayi kawai. Bamu tsaya a ko ina ba sai a gidansu Dr Kamilu.
Gidane na mutane tsaka tsaki su ba za'a kirasu talakawa ba, ko za'a kirasu masu kuWi sai dai irin masu ?udin da Winnan. In kayi la'akari da irin ginin gidan na jan bulone tagogi da ?ofofin gidan duk mada'in dane. (made in da)
A rabkeken tsabtataccen falon gidan muka samu Umma a zaune da wata ?ar mata haka dan da gani ba budurwa bace suna Wan hirarsu harda dariya.
"Ahh masha Allah Kamilu marar lafiyanka ta samu kenan?
Sabuwa maraba da zuwa"
A gabanta na zube na kwashi gaisuwa wannan yar mata da suke tare na juyo muka gaisa sai lokacin na gane ashe yawan fara'ar Dr Kamilu gadon gidansu ne.
"Allah ya kara sau?i Sabuwa. Sannan nasihar da zanyi muku ke da Mariya itace ku kama Allah ku kasance masu taurin zuchiya domin ku fuskanci duk wani kalubalen da zai bijiro muku.
Kin ganta itama ta shiga halin da yafi naki ma muni. Da taimakon Allah da kuma ita wannan terafi da nasa Kamilu ya haWa ku har ta samu kanta.
Ku ri?a ha?uri da ?warara xuchiyoyinku ku zama jarumai. Sannan kamar yadda nayi al?awarin kafin ki koma gida inaso ku zanta da lauyanki ku tattauna da kyau. In yaso sai ki koma gida da sammacinki a hannunki na Waukaka ?ara. A matsayina mai rajin kare hakkin Wan adam zan tsaya miki irin tsaiwar da nayi ma Mariya.
Kuma kada ki sake tunanin gudu ki bar danginki ki shiga duniya ko da wannan auren bai mutu ba. Ballantana ikon Allah ne kaWai zaisa ya?i mutuwa, ko kuma ke kice kin janye"
Ni dai sai godiya kawai nake yi nama rasa godiyar wacce iri zanyi musu dukkansu.
?akinmu Waya da Mariya kuma shekarunta ko ya haura nawa zai zama da kaWanne.
Gidansu gidan karamci ko shara sun hanani, duk abinda na tashi zanyi da zummar taya aiki sai Umma da Mariya su hanani fur.
Ana gobe zan koma gida ina kwance shiru, Mariya da Umma sun sun tafi umara, asalin tafiyar ta Mariya ce ta kaita ne domin ta ro?i Allah ya cire mata son tsohon mijinta a zuchiyarta. Sun yi mun al?awarin da sun dawo zasu sa Kamilu Ya kawo su har inda nake. ina tunanin yadda zan koma mu kwashe da su Maigogul.
Ga sammaci har an yanka goben magatakarda zai kaima Babangida sabon sammacinshi. Ni da lauyana kuma duk abinda ya kamata ya sani dole na sanar dashi kuma ya ajjiyeni akan magana Waya babu gargada.
Idanuna na lumshe
Ko yaya su Mardiyya suke, kuma yaya suka ji lokacin da labarin Satan dabo na ya bayyana musu oho.
?ar Shuwa na tuno nayi wani murmushi wanda ni kaina bansan ma'anarshi ba, girgiza kaina kawai nayi ta yi.
Washegari da wuri na shirya Baba Haule mai aiki ta kawo mun abincin karin kumallo.
"Mai sunan Malam yace in kin gama ki fito yana jiranki"
Gabana ya tattake ya kuma yankewa. Tunda dai na tashi nake cikin faduwar gaba.
To Haule nagode sosai.
Sannan na gode da kulawarki gareni. In sha Allah zan dinga kawo muku ziyara lokaci zuwa lokaci."
A sanyaye nayi karinnan na sha magungunana.
?arfe goma dot muka tsaya a daidai gidan da su Adama suke haya.
Tun kafin mu tsaya na hango Adama a tsaye a dokin ?ofar da tsohon mijinta ga ?atuwar leda a hannunshi yana mi?a mata.
"To ki sauka ki soma shiga sai ai mun iso ko? Sai mu tafi gidan naku"
Ajjiyar zuchiya na sauke dan tun muna hanya na sanar dashi wajen yayyena zamu soma zuwa. Tukunnan
Toh bari inje gama ya ta can a tsaye da mijinta"
Idanu ya ?ura ma Adama har yana sauke tangaran Win jikin tagar motar tashi.
Daidai Adama ta dumo wani ashariya ta lailayama mijinta kenan.
Idanuna na runtse shi kanshi na fahimci zagin ya kiWimashi. Abinda nake gudu ?ila fa saiya faru, shi yasa tun farko nake ta neman hanyar zillewa amman dana lura bani da wata hanya dole sai Dr Kamilu ya haWu da su Rakiya yasa dole muka tawo. Tunda ko basu hadu a gida ba zasu haWu a kotu ai.
A hankali na sakko sai kawai Adama ta ganni.
A guje ta shige cikin gidan
Sai gasu tare da su Labbai harda Uzairu Zuchiyata.
Gam muka rungume juna ni da Adama da Uzairu zuchiyata dukkanmu muka saki kuka ni ko da

12 / 25