Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   8 / 25

21K to 24K   out of 72.9K words

kuma kayan gado da kayan kitchen nake son a sai ma yarinyarnan kina ganin zasu isa ?"
Sai da Malama ?arama tayi murmushi kafin tace.
"Na lefen dai ya isa zata samu kaya da yawa. Ammman kaga na kayan Wakin a gaskiya ba zasu isaba in dai kaya masu kyau za'ayi mata. Sai dai in irin kayannan na bakin kasuwa za'a sai mata"
Kai ya girgiza yace.
"A_a ayi mata komai mai kyau. Kamar yadda kuke ma yaranku. Yanzu to kawo Wari ukun ki gani. In yaso duk abinda ake bu?ata a rubuta komai da kudinshi da jumulla. Yanzu ku gama na lefen tukunna"
Ai kuwa haka akayi a cikin kwana biyu da Malam Baba ya basu suka haWa akwatuna guda biyu da kit sha?e da kaya masha Allah.
Malama Babba tana zaune tana lissafin yadda ta zama bora a gidan mijinta sai ganin Larai da akwati kici_kici tayi.
"WaWannan akwatunan kuma daga ina Larai"?
"Kayan auren Babangida ne Baba malam ne ya bamu kudin muka haWa"
Da mamaki ta kalli Larai ta dubi Wawo dake zaune yana dama ma Baba malam fura.
"Kuma sai baki kai Wakin uwarki ba tunda itace uwar bikin ba?"
" Baba malam ne yace a kawo miki"
Kafin ta kuma cewa wani abun sai ga Malama ?arama ta shigo da sallamarta. Sai da ta nemi waje ta zauna kafin tace.
"Babba ga akwatin Babangida nan na haWo. Toh Malam yace da magriba Wawo da Bashiru su kaimu gidansu Ita Sabuwa mu kai musu akwatin. Sai ki ma Yaya Hanne Magana. Goggo ma tana kan hanya tare zamu je akai."
Sai da Malama Babba ta hadiye yawu mu?ut kafinnan tace.
"Toh shikenan. Allah ya kaimu da rai da lafiya."
"Ameen Babba Allah ya albarkaci auren kawai zamu ce"
Tana gama faWin haka ta fice.
Malama Babba tace.
"Har fishin da Malam yake yi dani yayi irin wannan ?amarin?
Taya zan ?aunaci wannan yarinyar ai har gaba da abada"
MRS BUKHARI
"
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA UKU.
SHAFI NA BAKWAI 7



"Ai muma Malam Baba ya tutsiyemu na harhaWo kan mazan gidan dubu Wari uku muka haWa mishi. Babangida ma saida ya bayar. Bai faWa miki bane?"
Kai ta girgiza tace.
"Bai sanar dani ba. Damuwar dake damunshi yaushe zai bashi damar sanar mun da wani abun. Yau bamma saka shi a idanuna ba. To me Malam zaiyi da kudi?"
"Sai Allah bazai wuce duk akan bikin bane"
Haka dai sukaita tattaunawa ta Waga waya ta sanarma Yaya Hanne duk abinda ake ciki.
Kafin magriba sai ga Goggo ta iso dama dai ?ar Wakin Malama Babba ce anan take sauka.
Ta sauka ko samun damar tattaunawa basui ba. Suna yin sallar isha suka wuce kai kayan lefe.

GIDANSU SABUWA:.
Tun yamma Maigogul ya kafa ya tsare a ?ofar gida domin tarbar masu kawo akwati.
A cikin gidan kuma Rakiya jallof Win shinkafa da kifi tayi ma ?an kawo akwati sai lemun kwalba da aka siyo guda biyu rak sai ruwa guda biyu shima. Da ?yar Maigogul ya bayar da dubu uku wai kuWin salala. Rakiya ta bi kan yaran Wakinta kafin su fita gantalinsu da ?yar ta haWa kudi suka kama dubu biyar.
Suna zaune a tsakar gida takwas daidai suka jiyo sallamar mata daga zaure.
Maigogul ne ya soma shigowa ri?i _ri?i da akwati a ka su Malama ?arama na biye dasu.
Dama tun magriba Rakiya ta shiga gidansu ?ar Shuwa ta sanar ma da mahaifiyarta to ta shigo tananan sai matar ?anin Maigogul itama tananan tazo.
"Ku shiga ga Wakin uwar Lolon nan, kunga ma uwar tata nan.'
Ya faWa yana dariya tare da shigewa da akwatin a kanshi.
"Marabanku ku shiga"
Rakiya ta faWa tare da mi?ewa tabi bayansu. Goggo sai taSe bakinta take yi.
Bayan an gama gaggaisawa a zatonsu Maigogul kuma zai basu waje ne amman sai Goggo taga zama dam. Ita to bata san waye ba kuma irin matannanne ita masu faWa da yawa. Sai cewa tai
"Hala kaine Babban wan Amaryar dai ko?"
Maigogul ya gyara zaman gogul dinshi yace.
"Ni ubanta ne nina haifeta. Baiwar Allah kuyi abinda ya kawo ku ina da wajen zuwa dama isowarku nake jira"
Baki Goggo ta rike tana mamakin wannan abu.
."Toh kayane ai gasu na Sabuwa. Sai a bubbuWa a gargani bisa al'ada ko? Duk da banga jama'a masu tarbar masu kawo kaya ba kamar yadda al'ada ta tanadar."
Babu dai wanda ya kulata Mama ta mi?e ta bubbuWe akwatin ta shiga WaWWaga kayayyakin ana gani harda Maigogul a WadWaga kayayyakin bacci da aka zuba haWe da kayan kwalliya."
"Tabarakallah kaya sunyi an gode. Maigogul sai ka fita ko zasu ci abinci"
Mikewa yayi tare da bibbige malum_malum dinshi a kansu, su dai mamaki ya ishesu.
"To ni kam na tafi. Rakiya bikine damu ni kam sai jibi ma zaku ganni. Ba?i munga kaya Sabuwa tayi goshi ba'a taSa wata yarinya rabin abinda akaima lolo ba, lallai da sa'armu muke tafe kafaWa da kafaWa"
Ya saka kai ya fice yana dariya.
Goggo tace.
"To Malama ?arama inaga ai sai mu tafi ko?"
Umma tace
"Abincin fa?"
"Zamu tafi dashi kar muyi dare"
Cewar Goggo tayi hakanne danta kuresu domin a kallo Waya da taina gidan ta gane suna cikin talauci"
Ai kuwa kwanon da suka gani na abincin ya tabbatar da zarginta.
Har gaban mota Mama da Tani suka rakasu suka dan?a dubu Biyar Winnan a hannun Malama ?arama dan sunga tafi Goggo sau?i."

Gidan Malam:.
Ai fa suna dawowa aka buWe sabon faifayin surutu abinka da mata. Wannan kuWin salala da wannan abinci akaita maganar a tsakar gida har dai yaje kunnen Baba malam sai da ya tsawatar.
Washegari Malama ?arama da Larai suka wuce kasuwa cikin kwana biyu suka gama siyan komai aka jibge a gidan Kawu Manga .
Baba malam da kanshi yasa aka je aka sanarma da su Rakiya ranar da zasu zo a debi kaya aje jere.

SABUWA:.
Gaga gaga abubbuwa sukaita faruwa, ni dai hankalina kwance daga ni har Rahama mun yi ?iba sabida cin daWi, haka ma jajiriyata tayi kiba duk wanda ya ganta sai ta bashi sha'awa.
Saura kwana Waya in yi alba'in wanda yayi daidai da gobe Waurin aurena.
Ni da kaina da safe naje na samu Malam a waje cikin almajirai.
Yana ganina ya girgiza kanshi ya taso ya same ni a zaure.
"Lafiya Sabuwa me kuke da bukata?"
Babu kunya dan a lokacin bamma santa ba nace.
"Kitso da ?unshi nake son ayi mun. To ina da me kitso kar tazo a hanata shigowa"
Hannu yasa ya rufe baki da dukkan halamu maganar ta matu?ar bashi kunya. Da ?yar yace.
"Jeki zan turo ?arama"
Na wucewata ina mamakin dalilin da yasa ya buWe baki.
Na koma ciki Rahama tace.
"Ya ake ciki me yace miki?"
Uhm wai in dawo zai aiko kishiyar babar su Babangida "
Bamma rufe baki ba sai gata ta shigo.
"Ke Sabuwa ?unshi da kitsonne ba zaki iya faWa mana ba sai Malam kika tsallake mata a tsakar gida kika sameshi shi. Dake ku a gidanku babu manya. Uban naki ma bai kama kanshi ba bare ku. To kul a gidannan mu ba'a haka.
Duk abinda kike bu?ata ki sanar mun ni zan isar miki wajen Malam Win dan ba sa'anki bane. ?unshi da lallai kuma zan turo Yahanasu tayi miki maras kunya"
Ahh to naga ai zamanshi nake yi"
Na faWa ina ?unkunni.
"Au zaman Malam Win kike yi?"
"E mana to da zamanki take yi? Ku dai gidannan akwaiku da tsurfa kaiii kuna da zuzuta ?aramar magana ta zama babba. Wai dama haka malaman suke ne?"
Rahama ta faWa tare da juya kai tamkar ba ita tayi maganar ba.
Haka dai Malama ?arama ta fice. Ba'afi awa biyu ba mai kotso tazo.
Mune har bayan isha muna abu Waya. Kitso dai sai da akayi guda Wari da hamsin. ?unshi kuma salateb aka jeramun suffa. Sai takwas na dare aka gama.
Washegari na fito fes dani.
Tun asuba muke ta harhaWa kaya ni da Rahama, muna kan tattare kayan Malama ?arama tayo sallama ta shigo hannunta ri?e da ba?ar leda cike dam da alawa da goro na Waurin aure.
"Gashi ke goron Waurin auren ne. Malam kuma yace ku shirya bayan la'asar za'a kai ki."
Wani sanyi naji a raina jin wannan aure ya Wauru. Murmushi nayi dana tuno rantse_rantsen da Babangida ya dinga mun akan bazai aureni ba. Rashin sani yafi dare duhu ashe daga ranar da zan tare a matsayin mata a gidan Babangida da ranar matsalata ta buWe sabon shafi mai wuyar biyawa.
Yamma nayi akace mu futo ba ai taro ko Wis ba asalima ko yaran gidan basu zo ba. Mardiyya na bayan Rahama ta goyata muka fito tsakar gida da kayayyakinmu.
Malama ?arama, da Goggo, sai Larai sai kuma ni da Rahama aka Wauke mu a mota zuwa gaba can da unguwarmu. Gidan gidane mai cike da jama'a. Da sallama muka shiga sunata hada _hada a tsakar gida, yaran gidan sunata tsalle tsallensu akwai yalwar tsakar gida sosai a gidan.
"Sannunku fa da aiki matan gida. Ga abokiyar zama kun sake samu"
Cewar Larai kenan.
"Ayya sannunku da zuwa. Ai mu da muka ga irin dukiyar da aka zuba da gyaran da akayi mun zaci amaryace munga idanta a bude tangararan"
Cewar wata zabiya uwar rawar kai ta ci wani pink din janbaki baki sai kace babanin akuya. Goggo tayi dariya tace
"Ba Amarya bace ga ?arta a baya ma. Allah dai ya baku zaman lafiya"
Suka amsa da ameen . Ni dai ina tsaye a gefe. Malama ?arama ce tai mana jagora zuwa Wakina.
Lallai Baba Malam ya zuba mun dukiya ko diyarshi ce ni iyakar gatan da zai yi mun kenan.
Goggo dai saida ta lalle?a ko'ina tana girgiza kai.
"?ar???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ama tashi mu tafi kinji."
Tashi suka yi suka fita babu wanda suka kula, muma bamu ce dasu uffan ba.
"Ke Lolo yanzu duka wannan aljannar duniyar wai naki ne? Uhm cikin shege yayi miki rana, mu ne dai muka hadu da jar masifa Adama dai Allah ya yanke mata wahala."
Tashi nayi na cire mayafina harda Wankwalina muka shiga kitchen ga kayayyakinan a jejjere, wasu ma suna kwalinsu, ga gara tubarkallah Baba Malam yayi mun. Muka tafi Wakin gado shima yayi kyau, ko ina kefet ne mai laushi. Zama nayi a bakin gadon nayi shiru haka suddan kuma sai nake jin faWuwar gaba mai tsanani. Har Rahama ta gama jera kayana dana Mardiyya ban ko motsa daga inda nake ba"
"Lolo kinji magriba ake kira bari kiga in yi Sallah sai in kama hanyar gida kuma"
Kallonta nayi tana shimfide Mardiyya a kan gado..
Gidanki zaki koma?"
"Wa? Can gida zanje gobe zamu zo muyi namu bikin ai, kuma a gyara miki wajen da kyau"
Tana bayan gida aka aiko yara biyu ko wanne da kwano a hannunshi na abinci.
Toh kuce musu an gode ko?"
Na amshi kwanukan da fara'a na ajjiye akan teburin tsakiyar falon. Na koma ciki ina ?ara ?arema Wakin kallo. Rahama ta shigo daga banWaki ta sameni a tsaye ina ri?e da labule ina duba kyansu.
"Uhm Lolo anyi Wakin kai. Kinsan Allah ke kam haWuwarki da Babangida alkhairi ne. Jibi waje Lolo komai mai tsada.. kab cikinmu babu ma wacce ta taSa samun arzikin irin gidan hayarnan da aka kama miki. Dan wallahi da gani tsada zaiyi in kika duba yanayin tsarin ginin. Kitchen Winki jibi sha?e da kayan arziki ga su kayan kallo a falo."
Dariya kawai nayi mata na shiga banWakin ita kuma ta tada Sallah.
Na fito na sameta a tsaye ta gama shiryawa tsab.
Rahama nace ko zaki farke katan din taliyar dake kitchen ki tafi muku da ko uku ce kwa karya dashi?"
"Sosai ma muje to in buWe kinga har su maggi da mai na Wiba.
Ai kuwa hakan akayidan mangyaWa ma da muka rasa a ina za'a zuba Rahama ta buWe ruwan gora na swan ta kwankwaWeshi tas muka cika da mangyaWa. Abincin da matan gidan suka kawo ma a leda na juye mata nace ta kaima Rakiya.
Mardiyya na goya na Wauki jakata na kalle Wakin na rakata har bakin titi saida ta samu abun hawa kana na dawo.
A hanyata ta dawowa na tsaya na sai biredi da ?wai a shago da taliyar ?an yara dan ba ?aramar yinwa nake ji ba."
Babu kowa a tsakar gidan sanda na shigo ko wacce tana Wakinta da iyalanta. Nima ina shiga na rufo ?ofata na kwantar da Mardiyya a kujera na shiga kitchen Win na kunna gas na Waura ruwan zafi. Sannan na fito na yi Sallah a falo.
Taliyar ?an yars na dafa da kwai sai tea mai kauri dana haWa dama muna da kayan tea da mika tawo dashi a kaya.
Nayi ?at na shiga da kwanukan kitchen na wankesu na mayar dasu inda na Wauka
?ata na Wauka muka shiga ciki muka hau shirin bacci. Kaya masu sau?i obarol na saka ma Mardiyya ni kuma wata doguwar riga mai sau?i na saka wacce nake bacci da'ita tunda na koma gidansu Babangida.
Na kashe hasken Wakin nayi baccina raina Waya
Wani irin bacci nayi wanda ban taSa yin irinshi ba. Bani na farka ba sai bakwai na safe shima sabida bugun da aketa ma ?ofatane yasa na bude idona a hankali gari tangararan.
"Lolo kizo ki buWe mana ?ofa"
Na jiyo muryar Maigogul ta windon uwarWakin nawa.
Da sauri na duro na zo na buWe musu.
Dukka ?an gidanmu ne suka zo harda ?an Wakin Hauwa. A mazan dai daga Uzairu zuchiyata sai Ma'aru ne suka zo. Daman sune basu fiye yawo ba a gidanmu bar Uzairu zuchiyata dai da yaudarar mata, shi kuma Ma'aru Wan yankan ajjihune ranar cin kasuwannin ?auye yafi fita.
"Kai kai kai Lolo haka Allah ya kashe ya baki, irin wannan kaSakin arziki haka? Masha ALLAH "
Cewar Maigogul dake tsaye yana karema ko'ina kallo su Adama kuma duk sun zazzauna wasu a kujera wasu a kasan kafet.
"Ai kasan itafa Lolo tun tasowarta ta zama daban komanta ya bambamta dana ?an uwanta"
Cewar Rakiya tana yi tana kallon Hauwa. Dariya Hauwa tayi tace.
"Gaskiya mana ta haifi ?ar shege, kuma taje ta haihu a gidansu Baban shegen kinga ai ita kaWaice hakan ya faru a kanta"
Nan cacar baki da habaice_habaice ya soma.
Ni kam suna cikin mayar da zance nayi komawata ciki su Adama suka biyoni dukkansu.
Zuwanku ne ya tasheni ma a bacci. Bari in yi Sallah sai mu shiga kitchen. Adama ashe haka abu ya faru?"
"Ke dai je kiyi Sallar tukunna dai akwai labarai ai"
Cewar ?ar Shuwa kenan wacce ta Wauki Mardiyya tana taSa mata kumatu.
Ina cikin Sallah, su Adama sunyi baje _baje wasu a gado wasu a ?asa Adama babu ko riga a jikinta daga ita sai bireziya da dogon wando hijabi ta ziro kawai. Ina cikin sallah Sai kawai Babangida ya Waga labulen uwar Wakin. Daidai nayi sallama muka haWa idanu dashi.
Wani irin wula?antaccen kallo ya watso mana na raini. Yayi tsaye ri?e da labule shi bai shigo ba, shi bai koma ba.
Su Adama duk suka mi?e tsaye suna neman hanya.
Ina jiyo Maigogul yana gaishe da Babangida amman bai ko yi gezau ba.
Ai saika basu waje su wuce ko?"
Na faWa cike da tsiwa.
Shigowa yayi yana muzurai su kuma suka fice Waya bayan Waya. Mardiyya na kafaWar Sadiya.
Zama yayi yana ?arema Wakin dani kallo.
Mi?ewa nayi na ninke sallayata na cire hijabina ina shirin ficewa a Wakin naji yace.
"Ke Sabuwa"
Juyowa nayi ina kallonshi.
"Me mutanen gidanku suke yi a gidana haka cikin falo? Ohhh nagane"
Sai naga ya mi?e ya iso har inda nake yana wani zazzare idanu.
Daf dani ya tsaya har ina sha?on kamshin jikinshi wanda yake cakuWe da warin haya?in sigari.
"Sun zo ne a cinye garar da ubana ya hadoki dashi ba. Ai kab ?an uwanki babu wacce ta samu gida irin wannan. Shine akazo za'aci banza harda tsohon najadun ubanki"
Maganar ta dira a zuchiyata sosai
Wallahi duk lalacewar iyayena da ?an uwana ina son kayana, kuma ina jin zafin a zagesu.
Murmushi nayi nace.
Ai ko sunci bakai ka siya ba. Da kake kiran ubana tsohon najadu, naka uban ko bai zama tsohon najaduba ya haifi Wan duniya haya?in..."
Marin bakina yayi bub yana zare idanu.
"Ke ni zaki zaga dan iyayenki? Ko da yake babu tarbiyyar bin miji a tattare da sha'anin gidanku. Uwar da uban sa'insa suke yi ko shigowata. Amman ki sani zan koya miki hankali kuma wallahi sai na gigita duniyarki. Na tsanake ke da yarinyar da kuka haifa kike ikirarin tawace. Kuma na lashi takobin sai da kanki kun yi nadamar aurena kin kuma nemi hanyar rabuwa danni kije ki sallamesu kizo ki sauke nauyin da Allah ya Waura miki"
Narantse da Allah sai dai mu gigita duniyar juna. Babangida bari kaji in faWa maka nima fa ba sonka nake yi ba kaddararmu ce kawai a haWe. Kaga ai ko babu komai ka samu ribar bariki kuma ko na fita a rayuwarka har gaba da abada ba zaka manta ni ba"
Tsaki naja nayi ficewata na barshi yana ta kwaWa mun kira da ?arfinshi na gaske.
"Ke Lolo ba kina ji mijinki na kiranki ba?"
Cewar Maigogul daya biyo mu kitchen.
?yaleshi Maigogul rigima yake ji ina daidai dashi ni kuma."
"A_a Lolo yanzu dai duk tsiyar Babangida mijinki ne kije kiji menene"
"Rabu da'ita ai dama ?ar balaja'u ce yaushe zata iya biyayyar Aure ko da yake bata da laifi kai ka koyar da'ita"
Babangida ne fa ya rike labule ya dubu tsabar idan Maigogul yake faWa mishi hakan.
Shi ko wallahi ko gezau sai ma wannan dariyar mai sani ba?in ciki ita yayi. Uzairu zuchiyata ne yace.
"Ai ko mutuwa tana jin kunyar mahaifa ka duba taronmu nan duk ?a?anshi ne amman ji irin furucin da kake furtawa"
Harara Babangida ya zabgama Uzairu zuchiyata yace.
"Kai kuma mai zubin ?an daudu ba dakai nake yi ba. Cin abinci ne dai ya kawo ku da sassafennan sabida dama tun asali mai?on gidanmu da darajar gidan namu kuke bi. In ba haka ba meye naku na zuwa da safe haka kusan ku ashirun wannan rashin kaine fa"
Tsaki yaja ya koma ciki a hakanma bai isheshi ba yaci gaba da maganganu yana ta yaSo musu.
Su dai kowa yayi shiru Hauwa kuwa sai cewa tayi.
"Uhm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta. Dama shi bariki iyakar ribarta kenan"
Rakiya ta dubeta tare da ?an?ance idanu.
"Me kike nufi da iyakar ribar bariki kenan?"
Maigogul dake ?ofar kitchen yace.
"Toh zaku ci gaba da raba hali a gidan yarinya salan mijinta ya sake fitowa yayi mana tijara ko?"
Yana gama faWa haka yace.
"Adama ku ?ara sanwar naga taliya huWu kuka ciro yaushe zata ishemu fisabilillahi?"
"Zamu ?ara da makaroni leda Waya Maigogul. Kaga kaje ka zauna bai kamata fa

8 / 25