Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   24 / 25

69K to 72K   out of 72.9K words

Hauwa mufa arziki ya kiramu dama dai ance kashine to ni dai na tako nawa. Kuma ko babu komai ta sanadiyyata Sabuwa zata keta hazo."
Baki Hauwa ta taSe ba tare da tace uffan ba.
Maigogul bai ce uffan ba sai gyara zaman hularshi yake yi ya caSa adon burgewa.
Gaza da madamcy suka fito muka yi sallama muka kama hanyar zuwa kano bayan mun yi sallama da ?an uwa, dan Adama ma a gida ta kwana sun samu saSani da mijinta. Layuza ma dai auren ya ?are dama igiya Waya ce jol take yawo a kanta to ya tsinke igiyar da yaga ya soma samun faraga. Gata da goyo amman a hakan ya korota Maigogul dai yace yana dawowa daga Lagos zai tusa Layuza a gaba a mayar da goyon Wan nata.
Da misalin ?arfe sha Wayan rana muka shiga Kano. Kai tsaye daga tasha muka yi shatar tasi ta kaimu har Airport na kano dan jirginmu na zuwa Lagos ?arfe biyu cib zai tashi.
A Airport muka yi sallah muka ci abinci.
Maigogul sai waye_waye yake yi da jama'arshi ta Lagos dan baya rasa mutane a ko wanne jaha yanda kuka san wani mai babban mu?ami a hannu."
"To Shikenan mun samu an kama mana babban Hotel a Lagos Win Waki biyu Lolo naki Waya, sai ni da Uzairu Zuchiyata mu ri?e Waya. Amman lolo akwai wani Alhaji da matarshi ta mutu yana ta son ya sake aure shine nake son in tambayeki in Khalid bai shirya ba me zai hana in haWaki dashi?"
Wani irin kallo nayi ma Maigogul wanda shi kanshi saida ya dibibice mamakine ?arara a fuskata da abinda naji yace.
"To Shikenan na fahimci bakya so. Amman ni sonki da arziki nake yi babban hamsha?ine Lolo shi kanshi ma ba lallai fa ya amince da tayin nawa ba dan babbane a mu?ami abokin hulWata ne"
Idanuna na lumshe kaina ya wani sara mun.
Uzairu zuchiyata ne yace.
"Maigogul ai daka bar Lolo ta nutsu ta fitar da wanda ya dace ya kuma yi daidai da rayuwarta. Sannan shi mutumin da kake so ka hadasu ya yanayin ?arfin kuWinshi yake?"
Dariyar da Maigogul da Uzairu Zuchiyata suka saka abun mamaki sai kawai naga sun tafa.
Nan Maigogul ya dinga Sarin zance yana ba Uzairu zuchiyata shi kuma tuni yai na'am da wannan mutumi har hotonshi ya nuna ma Uzairu zuchiyata a waya.
"Wallahi ke Lolo da sa'arki ma dai aka haifoki wallahi irin wannan mai arziki haka a rayuwarnan wa yake son wahala? Jibi Adama fa yadda a lokaci ?an?ani tabi duk ta lalace har ta yo yaji. Ni dama Maigogul ne ya dage saita auri Wan ?auyannan amman wallahi ni nasan dama ba za'ayi abun arziki ba. Shifa Wan ?auye baifa san cima mai daWi ba fa kuWinshi ba bana ci bane na cizo ne"
"Ai in faWa maka wallahi a lokacin da aka haifi Sabuwa mun samu alkhairai da yawa fa. Ai a lokacin ne Alhaji tsalha ya biya mun kujerar umara fa naje, shi yasai ragon sunanta. Wani maigidana Marigayi Alhaji mutta?a shima ya sai rago ti?e?e ya bani. Ya Wakko dubu ashirin ta zamanin baya ya bani. Uzairu zuchiyata a sunan Lolo shinkafa da miya aka ci saida kowa yaci ya ?oshi shi yasa take da sa'a"
Uzairu zuchiyata yace.
"Amman ni lokacin da aka haifeni fa? Gara inji insan wacce iriyace sa'ata ya ?arfin taurarina suke na zahiri?"
Harara na zabgama Uzairu zuchiyata na ba?in ciki da takaicinsu su duka biyun.
A jirgi ya ?arashe mishi labarin yadda sunanshi ya gudana, ya dinga soki buritsun zance Uzairu zuchiyata yana ?ara turashi dama shi haka halinshi yake.
Karfe uku cib muka sauka a Airport dake garin Lagos. Ni dai dana shiga jirgi na sake gane Allah da girma yake. Ashe jirgi haka yake da girma amman a sama a hangoshi ?arami?
Isarmu titi ke da wuya muka tare abun hawa zuwa hotel Win da aka turama Maigogul adireshin a waya da lambar Waki kamar haka uku sifili da uku Waya (30 da 31) Eco Hotel Banana Island. Wannan hotel Win a tsada in akwai wanda ya fishi tsada a Lagos to tsadar da kaWanne amman abinda na sani hotel ne wanda yawanci turawa da hamsha?an ?an kasuwane suka fi iya kamawa sabida bala'in tsadarshi.
"Yauwa Sabuwa ke shiga mai uku sifilin kiyi odar duk abinda kike so akwai abinci kyauta ko sau nawa zaki ci. Kuci ku ?oshi banza ta faWi. Ni dana huta zan shiga garine"
Ni dai Wakin na buWe na shiga na shiga ?arema haWuwar Wakin kallo. Zamana nayi akan gado ina ajjiyar zuchiya. Ni bana ma jin yinwa tunda munci abinci a Airport. Mayafina na zare kawai na haye gado inaso inyi bacci.
Sai nayi shiru kawai ina kallon yadda ac yake buso haya?in sanyi, sanyin na ratsa jikina. Fuskar Alhajin da Maigogul ya nuna ma Uzairu zuchiyata ce ta faWo mun na lumshe idanuna. Ina tunanin da ba dan bansan wanne iri bane shi dana amshi tayin Maigogul. Abu Wayane yake sani tunani da tsoron komawa gidan jiya. Nasan abune mai wuya in ba mazinaci bane tunda har Maigogul ya sanshi. ?ila mata yake kai musu tunda yace abokin cinikaiyarshi ne. To inma nace ba shi Win ba waye zai aureni wai? Bana tunanin akwai nutsattse kamammen da zai iya neman aurena in dai gaskiya zamu faWama kanmu tunda ubanmu ma kawaline. Sannan maza da yawa suna cikin harkar zinace_zinacennan in dai zai ri?eni da mutunci ba gara in aureshi ba me ku kuke gani amma?
In kuma na tuno da kuWurar Allah sai in ji a raina nagartaccen miji kintsattse yananan zuwa lokacine bai ba. Tunda Allah ya sani na tuba nayi nadamar gabaki Waya ma rayuwata ta baya wallahi Allah kenan.
Dan na gaji da irin rayuwar gidanmu Allah ya sani so nake in nesanta dasu sosai ko zam samu nutsuwa a rayuwata. Kuma nafi ?aunar auren gudun sake tsundumawa rayuwar dana tsinci kaina a baya.
Lumshe idanuna nayi a hankali banfi minti goma da rufewa ba bacci ya kwasheni.


Maigogul
Suna shiga ya cire babbar rigarshi ya faWa banWaki yayo wankanshi ya fito daga shi sai wandon shaddarshi da tawul a wuyanshi.
"Uzairu zuchiyata kirasu a waya su kawo mun farfesu mai zafi in sha ni fita zanyi."
Uzairu zuchiyata daya ?yafe a gado yana waya da Felisha ya gyaWa mishi kai tare da Waura yatsanshi a saman labSanshi ma'ana yayi shiru. Shiru Maigogul yayi harda kama bakinshi. Zama yayi a kujera ya ciro manshi ya shafa ga shadda ya zarota ya kintsa tsab wanka iyakar wanka ya feshe jininshi da turaruka masu ?amshin daWi ya ?arama yatsanshi zobe guda Waya mai ba?in dutse kasancewar agogon hannunshi cikinshi ba?ine yana son kwalliyar ta fita da kyau.
Uzairu zuchiyata saida ya sallami Felisha kana ya kira Hotel ya faWa musu sa?on Maigogul cikin minti sha biyar suka kawo farfesun naman akuya lafiyayyen gaske suka dire mishi yana ci yace.
"Uzairu zuchiyata ka shawo kan Lolo ta amince da batun dana kawo mata sabida naga tafi su A'isha wayewa ne kuma turancinma babu laifi tana kwaciSawa shi yasa nayi mata wannan tayin fa. ?arshe in nace su Labbai zan bashi kaga harkar ta lalace kuma Lolo ce zata samu samunta ya zama namu babu kokonto. Wallahi ta aureshi munfa yi bankwana da talauci fa, gaka zaka auri baturiya kaima kaga fa harkar kawalcinma sai in dena Alhaji ya bani jari ko na motocine in dinga zuwa kwatano ina shigo dasu tunda a baya mun Wan taSa harkar"
Uzairu zuchiyata yace.
"Wai Maigogul kai ko wacce sana'a kayi ta ne?"
Dariya yayi mishi kamar bazaai magana ba saida yasha romo sosai kafin yace.
"Hmm har kwasar kashi nayi. Uzairu zuchiyata har angola munje munyi kasuwanci abunne ya?i karSarmu shi yasa muka koma harkar kawalci kuma muka shigeta da ?afar dama shi yasa bana wasa da aikina.
Har a cikin kwata mun kwana. Ni dai dan Allah tunda Lolo ?awarka ce kama zaSeta sama dani ubanka to ka shawo mun kanta ko Allah yasa makkannan mu sake komawarta."
Da haka Maigogul ya gama shan farfesunshi ya saka kanshi ya fice.
Uzairu zuchiyata kuma ya koma dakin Lolo.

SABUWA:.
Ina baccina Uzairu zuchiyata yazo ya tasheni da bugun ?ofa jiki a mace na tashi naje na buWe mishi. Saida muka yi Sallah yayo mana odar lafiyayyen abinci muna ci ne yace dani.
"Lolo in kikayi la'akari da gidanmu da irin mazajen da ?an uwanmu suke aure ni sai inga kamar riba zaki ?irga. Ga shawara kyauta wannan Alhajin ta Sangarenki ki amince dashi ki barma Maigogul sauran. Ni dai shawarar da zan baki kenan a ta?aice. Kinga nima abinda zai fissheni nayi kina ganin shekarun dana kwashe ina neman irin abinda raina yake so da sannu ba gashi kusan nakai ga cimma abinda nake so ba?"
To zanyi nazari akai kafin mu dawo zan yanke hukuncin amincewar ko akasin hakan"
Mardiyya na kira a waya ta haWani da su Malama a waya duk muka gaggaisa suna makarantar islamiyya lokacin suna jiran Babansu ya gama ya Waukesu su koma gida. Nan na faWa musu zamu yi tafiya ni da Uzairu Zuchiyata zuwa ?asar canada su taya mu adda'a. Uzairu zuchiyata yayi carab ya fisge wayar.
"Mardiyya da bakinku na karatu mai albarka ki ro?a mana Allah yasa in samu nasarar abinda zai kaimu. Ita kanta uwar taku ku sakata a adda'a"
Mun Wan jima muna waya tana faWa mun matsalolinsu ni dai a kullum abinda nake cewa dasu suyi ha?uri duk runtsi su dinga tsayama junansu suna gani duk lalacewar gidanmu muna iya tsayama kanmu a kan duk wani abu duk girmanshi.
Gaga_gaga washegari tun ?arfe goma muka fito zuwa Airport sai ?arfe uku jirginmu zai tashi amman ana jiye mana turmutsutsun dake titin Lagos shi yasa aka bamu shawarar mu tafi da wuri mu jira lokacin a Airport.
Mun fita tun goman amman sai karfe Waya muka isa Airport sabida turmutsutsun titin Lagos ( go slow) kai tsaye muka wuce inda ake duba kaya a na'ura domin tantanewa. Sannan muka wuce wajen jira ga kujeru nan sha?e da mutane. A wata kujera muka zauna da wasu mata da miji. Maigogul kuma na kusa da wani Alhaji ya zauna shima ya tsaSa kwalliya. Hannu Maigogul ya mi?a mishi suka gaisa daga haka ya soma yi mishi surutu kai kawai na girgiza.
Muna zaune aka kira fasinjar Dubai duk suka. Mi?e suka hau kan layi in suka mi?a takaddar hannunsu aka duba sai su bi wata ?ofa su fita a haka har suka ?are.
Sallahr azahar muka yi muka dawo
Uzairu zuchiyata nifa yinwa nake ji. Ya kamata mu nemi abinda zamu ci gaskiya. Kai kaga Maigogul ya samu mutum sai surutu kawai yake ta zuba mishi babu kamun kai babu komai"
Baki Uzairu zuchiyata ya taSe kawai.
"Kinga ga wani windo can muje muga me suke dashi ko zamu iya siya kinsan Airport kayansu tsada ko ruwane"
Kafinma mu mi?e Maigogul ya iso inda muke.
"Lolo muje sama akwai gidan cin abinci wannan bawan Allahn da muke tare dashi yayi mun tayi zuwa cin abinci shine nake faWa mishi tare da yarana nake."
Kallonshi nayi na bi bayan Alhajin da kallo da yake kan ?afar bene yana haurawa.
Jikina a sanyaye nabi bayansu har zuwa saman ni da Uzairu Zuchiyata teburinmu daban, Maigogul da Alhajin teburinsu suma daban ga jama'a anan WaiWaiku suna zaune suna cin abinci.
Dafadukan soyayyar shinkafa mai Wauke da kayan lambu wadatacce aka kawo mana da kaza akai muka ci muka ?oshi muka kora da lemun limka na kwalba.
Godiya muka je muka ma wannan Alhajin.
"Wannan sunanta Sabuwa ?ar gaban goshina kenan yarinya ?ar albarka mai tausayi. Ta rabu da mijinta tana da yara huWu. Wannan kuma wanta ne Uzairu zuchiyata"
Da sauri muka katse Maigogul ta hanyar sake yima wannan Alhajin godiya gudun kada Maigogul ya sakar mana Sera a yayi. Ai kuwa sai muka ji an soma sanarwa a amsa kuwa cewar fasinjan Canada su hau layi jirginmu yana jiranmu.
Sakkowa muka yi cikin hanzari zuwa ?asa muka shiga layi.
"Sabuwa Uzairu zuchiyata ni zan koma zamu haWu a Lagos ranar da zaku dawo zan tawo in tarbeku. Duk abinda na baka ka tabbatar kayi amfani dasu kada kayi mana asara"
Alhajinnan yana bayan Uzairu zuchiyata sai ya dube ni yayi mun murmushi ni ina layin mata. Na lura tun muna wajen cin abinci yake ta mun murmushi.
Kaina na sauke kawai.
"Alhaji ni zan nufi jigawa kuma in babu damuwa ka bani lambarka mana"
Cewar Maigogul yana dariya. Katinshi ya zaro a ajjihu tare da littafin rubuta kuWi ( check) ya rubuta ma Maigogul kuWin da mu bamu san nawa bane Maigogul yaita runtuma godiya ya nufi hanyar fita.
Da ido kawai na bishi yadda yake tafe bagajan_bagajan ina juyowa muka haWa ido da Alhajinnan fuskarshi dai Wauke da murmushi da wani irin kallon tsan da yake yi mun.
A haka dai har muka fito aka duramu a bus zuwa bakin jirgi duk muka shiga kowanne ya zauna a inda lambarshi ta fito.
Idanuna a runtse har saida jirgi ya saisaita a sararin samaniya kana na buWe idanuna na sauke ajjiyar zuchiya wai yau mune a jirgi zamu tafi wata ?asar Allah mai yin yadda yaso.
Tafiyar ashe ba tafiya bace mai sau?i ba. Wasane_gaskene saida muka yi tsawon awanni goma sha bakwai a zaune. Muyi bacci mu farka, muci abinci, muje muyi fitsari haka dai haka dai bamu muka iso Canada ba sai wajajen ?arfe takwas na dare. Tafiya yankin azaba wai damma jirgi akwai daWi babu gajiya babu galabaita sam. Hannun Uzairu zuchiyata na ri?e gam dan wallahi Allah ina sauke ?afata a ?asa bayan mun sakko daga ?afar benen jirgin sai naji tsoro ya kamani.
Jakata Uzairu zuchiyata ya ri?e mun sai dariya yake yi mun.
"Lafiya Uzairu zuchiyata wani abunne ya samu shalelen Baba? Naga ka ri?eta ga jakarta ka ri?e?"
Cewar wannan Alhaji da muka shiga jirgi tare.
Kaina kawai na sauke Uzairu zuchiyata yace dashi.
"Babu komai rigimace kawai Alhaji"
Sai ya Wanyi dariya irinta dattijai.
Mu dai muna ta bin mutane a baya a baya har muka shiga wata ?ofa. Ananne akwatunanmu suke suna yawo akan wani ?arfe mai sulu, in jakarka tazo gabanka Sai ka zare, in kayi sanya ta wuce saita sake dawowa zaka Wauka. Uzairu zuchiyata ne ya Wakko mana akwatunanmu wannan Alhaji yana biye damu ?afa da ?afa. Uzairu zuchiyata ya zuge jakata ya ciro tabarau ya saka, ya feshe jikinshi da turare ya saka namijin goro a baki sabida ya Wauke mishi bashin da bakinshi yake yi.
Muna shiga wata ?ofar tangaran sai muka jiyo ihu daga can nesa na wata baturiya da fararen fulawowi sha?e a hannunta har tana kuka. Watsarmun da jakata Uzairu zuchiyata yayi ya kwasa a guje yana ambaton
"My Heart ( zuchiyata_ zuchiyata)
Ni kuma na tsugunna zan kwashe kayana da suka zubo a jaka wannan Alhajinma ya tsugunna zai kwashe mun.
Ganin ya rigani tsugunnawa sai ni na mi?e inata kallonshi hardai ya gama kashewa. A tsanake cikin nutsuwa ta jini ya ke komanshi hatta murmushi Wan gayu yake yi.
"Ga jakar taki shalele. Amman dai tunda hakane ki saka mun lambarki ta najeriya Allah bashi in muka koma gida sai in kiraki in kawo miki ziyara ma har gida. Alhaji Baba ma nasan zaiyi farin ciki da wannan haWin ko? Allah dai yasa ban yi miki tsufa ba kinganni da furfura"
Murmushi kawai nayi mishi gabana na tsananta faWuwa na karSi jakata. Wayarshi ya mi?o mun na amsa na rubuta mishi lambata na mi?a mishi.
Sai ga Uzairu zuchiyata da Felisha sun ?araso hannunsu sar?e dana juna abinka da turawa.
Rungumeni Felisha tayi tana farin ciki tare da yi mun sannu da zuwa ?asarsu mai albarka.
Aka sumbaci gefe da gefen kuncina dai
Ni dai sai murmushi kawai nake yi.
Alhaji ya tambayi Felisha ina zamu je ta faWa mishi har adireshin gidansu naga ta bashi sai ya dubeni yace.
"To shalele abinda zaifi zan zo in sameki a gidansu Felisha sai mu tattauna dukkan abinda ya dace ayi a gama kawai uhm?. Felisha can i have your number? ( Felisha zan iya samun lambarki)"
Ya tambayeta tare da ?are maganar da murmushi.
"Yeah of course " ( E sosai ma)
Nan ta bashi lambarta ni dai ina tsaye Uzairu zuchiyata sai kashe mun idanu yake yi.
Dala ya ciro a ajjihunshi ya zura mun a cikin jakata yana murmushi yana kallon cikin idanuna ya suri akwatinshi ya wuce mu.
Takunshi na bi da kallo har sai da Uzairu Zuchiyata yace.
"Lolo muje kin kafe bawan Allah da idanu. Nifa dama tun a gidan cin abinci naga hakan wallahi. Tabbb wannan ba dai mai?o ba, naga dala ya dunbuzo ya cunkusa miki ke mu dai watanmu ne ya tsaya ?yam ya maman maza. "
Dariya muka yi harda Felisha da bata sam me muke cewa ba sai dai muna tafe inaji tana tambayar Uzairu zuchiyata waye wannan Alhajin. Uhm wai kunji Uzairu zuchiyata yadda yake karya harshe irin na turawa kuwa? Sai ku rantse da Allah yayi digiri da digirgir lallai karanta ?amus yayi rana.
A madadin mu fita a Airport sai muka zagaya Wakin jira ashe jirgi zamu sake shiga daga nan Canada zuwa Alberta. ?arfe goma dot jirginmu ya tashi.
Awanmu huWu a zaune a jirgi dan masifa Felisha sai nan nan take yi damu gata kyakkyawa duk da dai ba yarinya bace, amman dai shekarunta sunyi daidai a matsayin matar Uzairu zuchiyata tunda dai ba na yau bane shi Winma.
Mun sauka a jirgi a cikin Airport Win YYC CALGARY INTANATIONAL AIRPORT. da misalin ?arfe biyun dare kai tsaye muka wuce gidan cin abinci dake cikin Airport Win. Dan Uzairu zuchiyata yace yana jin yinwa sosai dan ta faWa mishi daga nan Alberta kai tsaye birnin CALGARY zamu wuce a mota sai mun yi tafiyar awa huWu da rabi.
Dole muka ci abinci muka rama sallolin da ake binmu ni dai duk na gaji ma wallahi. Anan Airport Win muka samu masu tasi suka Waukemu.
Ananne muka sha kallo muka kashe ?war?watar idanunmu. Kai an tafi anyi mana nisa najeriya sosai. Gari tsab komai akan tsari ga shukoki masu ban ?awa a hanya takota ina simintinnan a lailaye wasu titinan ma da muka wuce su intalock ne ba kwalta ba.
Ga lantarki tako ta ina gari kamar rana
Ba dai mu muka shiga cikin gidan iyayen Felisha ba sai da safe.
Dan?ari ai tun daga bakin ?ofar shiga muke taka jajayen fulawowi da muka shiga cikin

24 / 25