Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   2 / 25

3K to 6K   out of 72.9K words

sabo. Bana neman wata magana ki duba mun Lolo cikinne da gaske ko kuwa?"
Rakiya zata yi magana Maigogul ya dan?aro ashariya ya dan?ara mata tare da doka ?afarshi yana kumfar baki.
Allah dai ya taimaka Rakiya bata yi yin?urin ramawa ba ta nufo ni ni dai jikina har rawa yake yi dan kaWuwa. Latsa cikina tayi ta dubeni muka haWa idanu, ta sake latsawa.
Maigogul da Hauwa, da su Sadiya kowa yayi shiru yana jiran abinda Rakiya zata ce.
Jikinta a mugun mace tace.
MRS BUKHARI
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI....
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA BIYU 2
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t
.
18066696785.
Hussaina Bello


HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAU?I DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI?
H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE
MAZA TUNTU?E HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA.
KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ?WAR?WATAR IDANU



"shikenan Lolo yanzu duk jan hankalinki da nake yi saida kika sake yadda wani shegen ya durka miki wani cikin. Kin mance da jar wahalar da kika sha, da gargaWin da likita ya bayar akan ki, ke da kamar ba ma zaki rayu ba.
Ai shikenan, ke kuma Hauwa hankalinki ya kwanta, kai kuma me son ji Lolo to cikine da'ita sai kayi abinda zaka yi akai."
Tana faWan haka tayi shigewarta Waki. Tana kutuntuma zagi. Maigogul ya daWe a tsaye yana nazari kamar ma bazai ce komai ba. Hauwa kuwa sai shewa take yi tana faWin.
"Bana dai ?ar so za'a wuce gidan miji tunda ita ba sai tayi ciki sau uku da namiji Waya yanzu duk cikin daya shiga dole a haifeshi. Uhm lallai nagode Allah da yasa a Wakin Rakiya za'a soma kafa tarihin Wan kuka, Maigogul da Rakiya za'a sha raino. Mai arzikin dai da ake nema ake fata ba'a samu ba Alhamdulillah. Yadda yaranmu aka cusa su kema dole a cusa ki."
Da ido maigogul yake ta bin Hauwa abun al'ajabi baice uffan ba.
Waya Maigogul ya zaro a ajjihunshi ya danna kira, jim kaWan aka Wauki wayar.
"Cicib kazo ka same ni a asibiti zaka raka ni wani wajen daga asibitin"
Iyakar abinda ya faWa kenan ya kashe wayarshi.
"Ke Lolo ki shirya dan ubanki zamu je asibiti daga asibiti kema kinsan sauran zancan. Ke kuma Hauwa ki kaimun ruwan wanka yanzunnan in watsa mitsiyaciya mai neman maganar tsiya yau dai in baki bi Rakiya a sannu ba tana iya danda?aki"
?akin Rakiya fuu ya shige. Hauwa kuma ta juye mishi ruwan wankan tana ta wa?en baka.
"Lolo kije ki shirya kafin ya fito. Ki dena Waga ma kanki hankali cikin shege ba kan ki barau ba kuma ba zaki zama ?arau ba.
Wanne irin cikin shege ne ba'ai a gidannan ba?"
Cewar Adama. Labbai tace.
"Kuma ba'a Wakko shirin denawa ba. Shima Maigogul faWan gan_gan kawai yake yi. Kuna zuwa aka bashi kuWi shikenan fa zancan ya ?are duk da naki lamarin ya dakeshi ya sha bambam da namu"
Ni dai zama nayi a cikin ?an uwana nayi shiru babu uhm banu uhm_uhm.
A wannan ranar Rakiya da Maigogul ba karamin rikici suka yi ba. Tun suna yi a daki har suka fito tsakar gida Rakiya na cukume da wuyan Maigogul. Da dai yaga Rakiya na neman ta kwashe mai ?afafu ta zuba shi da ?asa ai sai dambe ya kaure Rakiya na Kururuwa. Abun kunya matan ma?otane da Malam Habu ma?ocinmu mutumin Labbai suka raba wannan rikicin. Kuma akaimun terere akan nayi cikin shege ne. Ni kam a lokacin ko a jikina dam bamu san wata kunya ba.
Har Maigogul ya fito wanka ya shirya su Labbai nata godona akan in shirya nima na?i fur.
"Taso muje Lolo asibiti a tabbatar mun cikin ne in shine kuma wata nawa"
Carab Hauwa tace.
"Wannan cikin zai iya kaiwa wata biyar ko huWu"
BuWar bakin Maigogul yace.
"To da shike ke kika yi mata ko? Hauwa ki kiyayi Rakiya a gidannan yau."
Rakiya ce ta fito mayafinta a kafaWa.
"O_o batta tayi ai duniya ce. ?a?a gasu nan jibge a Wakinta. Lolo kuma ita ta siyo mun abinda Hauwa ta samu nasara a kaina. Sana'ar kayi nayi na ta fiye mun wannan kaddararren gida, da ?addararren miji, da ?addararriyar jar makirar kishiya wallahi dukkanku bakwa gabana"
Tana kaiwa nan ta wuce.
"Ke Adama tawo muje ki raka mu ayi komai a gabanki."
Tasowa Adama tayi muka rankaya asibiti. Muna kan bin layi Cicib ya ?araso yana rausaya mu uku muka shiga Wakin Adama aka barta a waje.
"Ku kuje daga waje Baba inna gama dubata zan kiraku"
Wannan likita ta faWa ranta a Waure.
Haka su Maigogul suka fita.
Likita ta gama aune aunenta ta tabbatarma da su Maigogul cikine na wata huWu babu sati Waya a jikina.
"Lolo ina fatan kinsan wanda yayi miki cikinnan, sannan kinsan gidanshi ina nufin gidan da matarshi da yaranshi suke ko?"
Maigogul ne yayi mun wannan tambayar cikin dakewa da kakkafeni da idanu.
Saurayine bashi da aure. E nasan gidan amman"..
Dakatar dani yayi da hannunshi.
"Wuce ki kaimu gidansu tunda dai kinssn gidan. Saurayine, magidancine, talaka ne, ko mai kuWi wannan kuma ke ta shafa"
"A_a Maigogul me zai hana shi yaron a kirashi tukunna ya sameka in yaso in yayi musu sai a dangana da gidan iyayen nashi. Kaduba abubbuwan da suka faffaru a baya. Sannan Lolo kes Winta ya bambamta ita dai babu halin zubar da ciki ya kamata a nemeshi ayi magana ta nutsuwa dashi, in aurenta zaiyi sai ya aureta su rufama juna asiri"
Maigogul ya dubi Adama data gama magana ya dubi Cicib dake tsaye yana gyara mayafinshi. Nima ya kalleni tsab.
Cicib yace.
"Yarinya tazo da hanzari. Yanzu Maigogul abi a hankali din. Ita Lolo ta kirashi ta sanar dashi mu muna nemanshi zuwa da daddare ?arfe takwas. Barsu su yi tafiyarsu kasan na baro ba?i ."
Sai da naga su Maigogul sun Sace kafin na sauke ajjiyar zuchiya mai ?arfi.
Muna cikin abun hawa Adama taga nayi shiru ina tubkewa ina warwarewa.
"Ke Lolo da mun koma gida sai ki kira shi saurayin naki ki sanar mishi halin da ake ciki. Amman ina ganin zaifi kyau ki sanar mishi cewar ana nemanshi a gidanku. Duk da dai nasan babu al?awarin aure a tsakaninku. To yaya zamu yi a haka muka tsinci rayuwarmu.
Maigogul da kanshi yaita ingizamu zuwa shiga duniya sabida kyan da Allah ya huwace mana. Gashi duk kyanmu ya zama kyan Wan maciji.
Ajjiyar zuchiya na sauke duk abinda ta faWa babu gyara a cikinshi
Amman Adama kai tsaye sai inga kamar in nace mishi ana nemanshi ba tare dana sanar dashi dalilin neman ba. Ba lallai bane yazo, amman in yaji akwai ajjiyarshi a jikina zai iya zuwa ko dan tsoron tonuwar asirinshi tunda gidansu gidan malamai ne."
"Toh hakane kam kince wani abun kuma. Shikenan ki sanar mishi yayi ?o?ari yazo in ba haka ba sai yayi dana sanin saninki a rayuwar baki Waya dan wallahi Maigogul suka je gidansu za'ayi Wauki babu daWine."
Haka mukaita tattauna matsalolin kanmu da kanmu har abun hawa ya saukemu a kofar layinmu.
Gidan ko da muka shiga Hauwa ce kaWai a gidan sai ?ar Shuwa dake ta shafa hoda halamun fita zata yi ita mahaifiyarta ta sama mata miji wani Wan uwanta zata aura harma magana tayi zurfi yazo ya ganta sau biyu kuma ya yaba, itama ?ar Shuwa tayi na,am dashi. Yanzunma shine yace zai zo daga Maiduguri bai wuci kwalliyar tarbarshi akeyi ba dan a Wakin Rakiya suke zancan.
A tsakar gida Adama tayi zamanta mu biyu ne a Wakin.
"Sabuwa anya kuwa cikin dake jikinki kuwa na Babangida ne? Ni sai nake ganin kamar na wannan Alhajin da yazo Jamus ya haWaki dashi ne. Ko dai kin mance ne? Gashi shi ba'asan ma a ina yake ba. Ko dai a hakan kike so ki ?a?abama Babangida? Kinsan dai mitsiyacine baida wani kuWi ke rayuwarsu Layuza bata zame miki abun duba ba, yama kika yi sake ciki ya shiga ne? "
Ras gabana ya faWi nama rasa ni kam mai zance dan shab na mance da batun Alhajin da Jamus ya haWani dashi, kuma cikin yayi daidai da lokacin da muka haWu. To amman Yaya zanyi? Tunda dai wannan Alhajin ni bansan inda zanma sameshi ba. Shi kanshi Jamus in wu?a za'a saka mishi baisan inda yake ba kuma baida lambarshi, duk da dai babu tabbacin cikin nashi ne gaskiya.
To ?ar Shuwa yaya zanyi ni dake kaWai muka san wannan ?ullin inaso mu haWu mu binneshi a tsakankaninmu. Dole Babangida zan li?ama cikinnan. Tunda bamu da tabbacin ba nashi bane tunda shima ai muna tare dashi a lokacin."
Shigowar Adama tare da Rahama da tazo yanzu tana tafe raSe_raSe da yara yasa dole muka rufe shafin nan aka buWe sabon shafi.
"Lolo kiyi ?o?arin kiran saurayinki tun yanzu ni dai na faWa miki"
Kafinma ta haWiye yawo kiran Babangida ya shigo wayata. ?anewa nayi ?uryar katifar Rakiya.
Allah ya taimaki mai martaba sarki a cikin zuchiyata. Koda yaushe zuchiyata da gangar jikina cike suke da kewarka. Dama ko baka kirani ba daman ni zan kira akwai abinda ya taso ne"
"To bari in gama sauraren sarauniyar dake da babbar fada a zuchiyata. Lokacina naki ne ke nake saurare"
Kai tsaye nace dashi.
Cikine dani, kuma kasan cikinka ne tunda bana kula kowa. Shine Maigogul yace kazo yana so ya ganka zaku yi maga.."
?it Babangida ya kashe wayarshi. Da mamaki na zare wayar a kunnena da gaske katsewa yayi?
Sake kira nayi sai ga wayarshi a kashe abun almara. A karon farko dana taSa jin wayar Babangida a kashe kenan.
Hmm bariki kenan alalan gero kunun wake, ni Babangida yake so yaima akuyanci? Ashe baisan wacece Sabuwa ba labarin Sabuwa yake ji? Ni da na zauna a kango na kwana na tashi a cikin ru?a??un shegu. Na taka duk ubanda naso. Naba Babangida kwana biyu matsawar bai neme ni ba kuma bai zo ba zan nuna mishi nawa kalan barikin"
?ar Shuwa ce ta duro gadon, na kalleta kawai ina harare_harare, gasu Adama sai mayar da zancan cikin suke yi."
Labartama yar Shuwa nayi tare sa Waurawa da cewa.
Wallahi saina kuikuyama Babangida rashin dajarar da sai yayi dana sanin shiga bariki. Waini Lolo yau ni namijin bariki zai nuna ma bariki ni da tsabar yagewan idanuna dayan ya haWe da Wayan."
Dariya muka saka harda tafiwa.
"Tabb ustaz ya taro mach Win da bazai iya bugawa ba. Da yasan waye Sabuwa da Maigogul wallahi bazai kashe wayar ba, kuma bazai ?i amsa wannan gayyatar girman da babuma wanda ya taSa samu ba."
Da daddare sai ?aryar Babangida yayi tafiya zuwa jibi zai dawo nayi musu.
"To naji jibin kaWai kike dashi wallahi. Ko ya dawo ko kar ya dawo zamu je gidansu dan asan da ajjiyarshi a jikinki tunda haihuwar cikin za'ayo dole ?anwar na?i."
Da haka muka rabu dasu ina cike ni kuma da mamakin Akuyancin Babangida.
Duk sanda zan kira wayarshi a kashe take har Allah ya kawo mu kwana biyun wa'adin sharaWin da Maigogul ya gindaya.
"To Lolo taso muje rana bata ?arya. Cicib yana waje yana jiranmu"
Riga da wandone a jikina a haka na mi?e na warware gyalen dake Waure a kaina na yafa, wu?a na soke a ?un?uruna muka fito. Har munzo bakin ?ofar gida Rakiya ta tawo da sauri.
"Maigogul wai yanzu in kunje me zaka cema mahaifan yarannan?*
KafaWa ya Waga tare da cewa.
"Me kuwa zan faWa musu daya wuce abinda ya faru. Ke kinga mu sai mun dawo"
Haka suka sakani a gaba abun hawanmu har kofar gidansu Babangida. Ai kuwa almajirai cike da makaranta anata karatu. Ga wani farin dattijo mai cike da kamala da haiba. Yanayinshi kaWai ya tabbatar da yana da managartan halaye Albasa ce kawai batai halin ruwa ba.
Wallahi ko ku kuka ga mahaifin Babangida sai kunji inama wani Wan uwanku ne.
Ga gidannan. Inaga wannan shine mahaifin nashi."
Na faWa ina kallon Maigogul.
A cikin abun hawan muka fito ga Cicib harda Wankwali a kanshi duk da ma ba'a rabashi dashi.
"Abinda za'ayi Maigogul bari inje in karawoshi gefe muyi abinda ya kawo mu. Ikon Allah ko meye kuma haWin kifi da gaska? Uhm yau za'a yita ashe da dukkan halamu"
Yana rausaya. Ya isa gaban Dattijon yana tsaye babu wargi ko wasa sam a tattare dashi.
Bama jin abinda suke faWi amman dai munga Cicib ya nuno mu Dattijon ya juyo ya kallemu.
Yaro ya tayar daga cikin gardawa ya shiga zauren gidan, shi kuma Cicib ya tawo wajenmu da rausaya.
"Maigogul muje an mana iso zuwa cikin zaure. Naga tsohon babu wasa daidai da fara'a ya?i yayi."
"Ai sai ki shige muje. Ki rasa wanda zaki bi kema sai talaka duk samarinku masu kuWi yanzu jibi gidan malumta kika kawo mu, yaushe za'a wanye lafiya ke da gani"
Cewar Maigogul. Ni dai bakina shiru inata binsu a baya har muka shiga zauren muka samu Dattijonnan a zaune a tabarma yana tsumayarmu.
?agowa yayi ya kalleni tare da saurin sauke kanshi.
Zama muka yi dukkanmu muna fuskantarshi. Sai daya sauke gauron numfashi kana yace.
"Toh Assalamu alaikum tunda ku bakui sallama ba"
Maigogul yace.
"Adana sallamarka domin ba ita muka zo ansaba"
Murmushi yayi irinna takaici tare da raina wayon Maigogul.
"Malam ai wajibine amsa sallama ga duk musulmin da akaima. A ?a'ida ku da zaku shigo ai ku yafi dacewa da kuyi sallamar. Amman nayi muku ma kun kasa maidomun da'ita? To meke tafe daku haka?"
Ya ?arashe maganar yana nazartarmu.
"Kaine mahaifin Babangida kacigari?"
Cikin alfahari yayi murmushi yace.
"Uban masu gida kenan. Nine mahaifinshi meke tafe daku?"
Zama Maigogul ya gyara shima cikin alfaharin yace
"Wannan ?a tace ta cikina. Wannan kuma amininane wanda baida tamka.
Kar in cika ka da surutu a ta?aice Babangida ?anka yaima Wiyata cikin shege. Kaga cikin ai a jikinta harma ya bayyana ko? Wata huWu ne gashinan. Ga takaddar shaidar tana Wauke ma da cikin ke lolo buWe cikin ya gani"
Salati Baba Malam ya shiga yi a hankali. Ha?i?a kaWuwa da damuwa sosai sun bayyana a fuskarshi ainun. Cike da mamaki yace.
"Babangida kace fa? Bana jin ko cikin mafarki Babangida zai iya neman mace da fasi?anci balle har ace tana Wauke da cikinshi. Kamar yadda kuka gani nan gidan gidan malamai ne. Shi kanshi Babangidan Malami ne. Sabida haka ba Babangidan wannan gidan kuke magana a kai ba. Nawa Babangidan ya ?oshi da tarbiyya. Jibi ?ar da kake ikrarin taka ce, ji da irin shigar data biyo ka ta tsuke jikinta tamkar ba yarinyar musulmai ba. Kai da kake a matsayin mahaifinta baka ji kunyar Wakko Wiyarka a tsirara ba, wai ashe har lalacewar al'ummarmu ta kai haka?"
Ai kuwa daga haka Maigogul da Cicib suka mi?e nan suka shiga Waga murya da zagin Malam akan shine marar tarbiyya dashi da mazinacin Wanshi. Yana ta basu ha?uri kan in maganar tayi zafine. Hankalinshi ya tashi yadda yaga su Maigogul suna Waga murya Cicib sai tattafa hannaye yake yi.
Lamarin daya tunzura almajiran Malam suka zo sukayi waje damu. Dan ba ?aramin Waukar zafi su Maigogul suke yi ba.
Abunda su Maigogul suke nema kenan suka hau ihu da tafe tafen hannaye jama'a suka taru aka shiga basu ha?uri Maigogul nata ?o?arin sai yayi ma mutane bayanin dalilin?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? zuwanmu. Amman dai baici nasaraba sabida yadda suka ?i saurarenshi suke ta bama Malam ha?uri. Yaran Malam daga cikin makaranta mata_matan duk suka fito. Harma dasu Malama Babba.
Malam ko a fuska yayi mamakin abinda su Maigogul suka yi. A tunaninshi duk abinda ya faWa mana si gaskiya ce sai dai mu?i karSa.
"Kuyi ha?uri ni ban zaci ranku zai Saci ba. Amman a inda babu ?asa anan ake gaddamar kokawa. Kuzo muje zan aika a kirawo Babangida a duk inda yake, kada ku zubar mun da mutunci a unguwa na rokeku ana mugun ganin darajata.."
Jin an ambaci Babangida Malama Babba tace.
"Wai to su Win su waye Malam da zasu zo da irin wannan hayaniyar. Ko da yake ko a shigarsu banga wata kamala ba ballantana tarbiyya ba ina namiji ina kallabi"
Ina jin haka nace.
A_a fa Dattijuwa ki kiyaye harshanki, dan bazan tsaya ina gani ku dinga aibata mun iyayena ba. Dan haka wallahi ku kiyaye"
Nayi maganar ina ciccijewa irinna mata ?an daba."
Sa'a ce ta matso kusa dani ta daki kafaWata. Nayi mata wani mugun kallo tace.
"To in bata kiyaye harshenta ba me zaki yi mata?"
Dariya nayi mata tare da Waga rigata suka ga SharSeSiyar wu?a a cikin gidanta a soke a ?uguna. Baki Malam ya buWe su Malama Babba duk suka bude baki. Itama maras kunyar babu shiri ta matsa baya.
"To duk dai mu jira wanda ya haWa wannan fitinar. Ku mu koma daga zaure. Ku kuma ku koma makaranta kuci gaba da koyarwarku.
Ke Sa'a ki kirawo mun wayar Babangida kice ina nemanshi maza, duk a inda yake yazo. Kome yake yi ya bari yazo zasu tabbatar da Satan kai suka yi"
Haka muka sake Wungumowa muka shigo zauren.
Tunda aka zauna Maigogul yake ta mita da farfaWan maganganu. Sama da ?asa Baba Malam ko Wago kanshi baiyi ba bare har ya kalli Maigogul. Shigowar Sa'a zauren da sallamane yasa Dattijon ya Wago kanshi.
"Yaya akayi Sa'a ince an sameshi dai?"
"A_a Baba Malam wayarshi a kashe take. Mun kira kiran duniya tana rufe"
Jim yayi yana nazari, can ya dubu Maigogul yace.
"Ko zaku dawo da daddare dan ALLAH sai ayi komai a gaban shi Babangidan. Tunda yanzu baya nan. Shine kaWai zai tabbatar mun da gaskiyar lamarin?"
Maigogul yace.
"Zamu tafi mu biyu. Amman ita wannan tazo kenan ba zamu koma da'ita ba ehe wannan furucin cewar babu tarbiyya tattare damu naka Wan shine mai tarbiyya wallahi zan nuna maka ni bansan ma me ake nufi da tarbiyya ba"
Malam Baba ya dubi Sa'a yace.
"Kiyi tafiyarki Sa'a. Amman in kin fita ki kirawo mun manga lallai inason ganinshi"
Sai da Sa'a ta fita kafin Malam Baba yace.
"Bawan Allah ban gane me kake nufi da cewar ?arka tazo kenan ba. Ko za kai mun bayani?"
Cicib ya karSe yana tafi yace.
"Nufinshi shine Sabuwa zata zauna a wajenku har Allah yasa ta haife abinda ke cikinta. Inta ajjiye muku Wanku sai ta dawo gida. Ko ba hakan kake nufi ba Maigogul Aminina ?"
Gabanane naji ya take ya faWi a raina na furta.
A nan gidan za'a barni har saina haihu fa? TabWi jan hakanma ba mai yiwuwa bace nasan sun faWane dan kawai su tsurar da iyayen Babangida aure ayishi dole.
Murmushi

2 / 25