Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   6 / 25

15K to 18K   out of 72.9K words

raina kenan. Kinsan Allah ba shi kaWai ba hatta da zuriyar da Babangida zai tara bazan taSa jin na ?aunacesu ba abadan.
Tashi ki fita, ki fita nace ko in bar muku gidan baki Waya"
Ya ?arashe maganar cikin Waga murya.
Cikin Sacin zuchiya ta saka kai ta fice tana rausa kuka tamkar yarinya ?arama.
A wannan dare haka wannan iyaye suka sake kwana idanunsu biyu ras.
Asubar fari Baba malam ya sanar da ya dawo da zaman da za'ayi yau. A kira yaran duk a sanar musu takwas na safe za'ayi zaman."

Babangida:.
Su Baba Malam na juyawa ya runtse idandunanshi gabaki Waya babu laka a tattare dashi. Bawai tsoron dan an gansu tare yake yi ba, tsoronshi a yadda aka gansun, dakuma irin tashin hankali da zai ?ara saka Malama Babba a ciki su suka fi komai Waga hankalinshi.
Da ?yar yayi da gaske ya shiga motar ya ja zuwa Club Win. Da ba dan mai motar na can yana jiranshi ba bazai koma ba.
Amman ko da yaje bai wuce uku da rabi na dare ba suka saukeshi a bayan layi ya shige gidan Kawu Manga ta hanyar haure katanga.
Ko da ya shiga Wakin ya tarar da ?asimu yana kan dadduma yana ta tilawa da halama sallah yayi ma.
HaWe girar sama data ?asa Babangida yayi dan ko da ?asimu ya juyo da nufin tuhuma fuskar Babangida saita tsoratashi sosai
Babu shiri ya mayar da hankalinshi kan abinda yake yi.
Babangida ya mi?e ya fita tsakar gida dan bacci ya gagareshi..
Ruwa ya diba a randa a bokiti ya shiga banWaki ya tsarkake jikinshi kana ya dawo ya ta da Sallah.
Da asubar Fari Malama Babba tayi kiranshi akan za'ayi zama yau ba gobe da Malam Baba yace ba. Amman bata san ko za'a bu?aci yazo ayi zaman dashi ba.
A sanyaye Babangida ya sauke wayar a kunnenshi tare da sauke gwauran numfashi.

SABUWA:.
Ni kam ta Sangarena ina komawa ciki nayi baje_baje akan katifa sai bacci.
Sai daf asuba Alawiyya ta tasheni.
Da ruwan sanyi na tsarkake jikina ina idar da Sallah na yi komawata gado.
Abuna, bani na farka ba sai wajen bakwai da minti goma, shima Win Adama ce ta kirani a waya.
Adama da sassafe kira haka kin tashe ni a bacci"
Sai cewa tayi.
"Wallahi kuwa kinga dama dai yau zamu sake zuwane Maigogul ne ma yace zai kawo mu ke harda magazin babu wani shege ko shegiya da zasu hanamu shiga yau.
A shirye sosai zamu tawo"
Dariya na saka.
Kice unguwa yau zata Wauki harami ga Maigogul ga Mazagin kinga ai babu magana. Sai kun zo dan ALLAH Adama in zaku tawo ki kawo mun littattafan hausa zan Wan kakkaranta nifa zaman ya isheni ban saba da haka ba.
Jiya ma na fita ai.
Nan na labarta mata duk yadda fitar da dawowar ya kasance.
Dariya tayi.
"To zan yo miki rentin amman ina kawo miki zaki lale kuWaWen mutane ki basu dan mai rentin Win bata da mutunci ko na mis?ala zarratin dan ko daWewa littafinta yayi saita yi rashin mutunci kuma sai an ?ara mata kuWi.
Baki na taSe ganin shigowar Alawiyya da masa da miya da kunun tsamiya.
To shikenan sai kun karaso baro in karya sai zuwa anjima"
Datse wayata nayi na karSi abincin dake hannun Alawiyya.
Tana bani ta fita. Ni dai ina daga Waki matan gidan masu aure duk wacce tazo sai ta Waga labule ta ganni ta taSe bakinta.
Ko wacce da irin nata salon da take le?owa dashi. Ni dai inata harkokin gabana ko in kula dasu har dai suka gaji suka gama.
Gidan cike da hayaniyar muryoyin maza da mata, harma da yara ?ananu.
?ila wani taron akeyi a gidan yau.
Ina gama faWar haka a zuchiyata na mi?e na fito tsakar gidan na yi zamana a kan turmi ina yanke farce, ina kallon yadda suke ta shigewa Sarayin Baba Malam.
Murmushi nayi ni kaina nasan ba ?aramin saka Babangida da iyayenshi nayi a uku ba.


BABA MALAM:.

Manya manyan taburmaine malale a farfajiyar shayyar Baba Malam.
Yana zaune a kujera wan sita. Yaranshi maza da matan suna ta shigowa kamar dai yadda ya bu?ata. Sai daga can kusa da ?arshe can sosai kafin Malama Babba ta tawo Yaya Hanne na biye da'ita.
Baba malam yayi ?ur ya zuba ma Yaya Hanne idanu, ya mayar da idanunshi tsakiyar idanun Malama Babba.
Sai da suka nemi waje aka zazzauna kana Baba malam yayi gyaran murya ya soma da sallama. Duk suka haWa bakunansu wajen amsa sallamar tashi.
"Kafin in soma magana a kan abinda ya tara mu anan. Hanne inaso ki yi ha?uri ki jira Babba a Wakinta. Wannan taron na cikin gidane"
Yaya Hanne ta dubi Baba malam ta dubi Kawu manga kafin tace.
"Zamu tafi ni da Manga ?aninka kenan?
Dan in ni bare ce a cikin wannan maganar to Manga ma ai bare ne ko?"
Baba malam bai yi mamakin abinda Hanne tayi mishi ba. Dan a baya ma babu irin zigin da bataima Malama Babba ba akan dole saita Sokare mishi. Har anyi lokacin da ya dakatar da ita Malama Babba zuwa duba Hannen sai dai ita tazo ta dubata. Gadararta shine mijinta hamsha?in mai kudine kuma su ?an boko ne sosai. Kuma tana matu?ar son Malama Babba tana taimaka mata. Duk wani kwancen kayanta masu tsada tsada Malama Babba take bama ita ta soma bata kwancen gwal, ita kuma ta soma bata kwancen atampa supa da aura.
"Babba kisa Yarki ta tafi ta jiraki a can falonki"
Bata da yadda zata yi tasan halin mijinta ba daWi gareshi ba yana da bauWaWWen hali.
Da ?yar ta jaye Yaya Hanne ta fita zuwa falonta.
"Ke Saratu haka mijinku yake tsinkaki a gaban kishiya?"
Ta faWa tare da ?an?ance idanunta irin na masifarnan.
"O_o _o_o Wanki ne ya jawo mun. Kinsan tunda ya aikata wannan abun wallahi in faWa miki Malam bai sake sakin fuskarshi dani ba."
"To meye naki ke a ciki halin Wan yau? To ni dai ki cire tsoro ki sanar mishi ciki bana Babangida bane fa?at. Kuma kiyi ?o?arinki cikin ya zube ki tabbatar yarinyarnan taci maganin dana kawo miki.
Ji yarinya a tsakar gida tanaima mutane kallon WaWWaya almura idanta kamar soyayyar gyaWa"
Malama Babba da sauri ta fita ta koma wajen taron.
"Wawo a buWe taro da adda'a"
Wawo yana daga zaune ya buWe taron da adda'a kafin Baba malam yace.
"Dangane da batun wancan shashashan Wan iskan yaronne Babangida. Shine dalilin taruwarmu anan sabida tunda abun ya faru inata aikin nazari da binciken duk daya dace.
Kuma naga saka hannun mahaifiyarshi ta Sangarori manya wanda hakan ba ?aramin mamaki ya sanya ni a ciki ba.
To abu na farko dai shine. Kamar yadda nace Babangida ya bar gidana, to ina nufin ko bayn raina ban yadda yaronnan ya dawo cikin gidannan ba zaici gaba da zama tare da Manga.
Kai Manga"
Baba malam ya dubeshi.
Cike da tsantsar ladabi ya amsa.
"Na'am Yaya"
"Sai kasa idanu sosai akan su ?asimu dan gudun kada ya lalata maka tarbiyyarsu ya rusa maka ginin daka daWe kana ginawa. Ni da a so nane ma yabar gidan naka ya shiga uwa duniya.
Amman dana je Ringim nake labartama Kawu da Goggo Amfana halin da ake ciki. Suma sai suka ce lallai Babangida ya zauna a wajen naka tunda dai kai kaji zaka iya.
Wannan itace maganata ta farko.
Maganata ta biyu kuma itace.
Sabuwa zata ci gaba da zama a gidannan har saita haihu zata bar gidannan.
Sannan na saka doka duk wanda a cikinku ku mata matannan kuka sake takalar yarinyarnan tazo tana mana rashin mutunci a gida zan saSa muku.
Idan ta haihu zata bar gidan izuwa gidan Babangida zan sa a Waura aurensu ta tare a matsayin matarshi suje can su reni abinda suka haifa yafi ace suna yawo gidan rawa_ gidan rawa, dan wani cikinma sai ya sake Wirka mata ba komai bane."
Shiru yayi yana nazarin fuskar kowa.
A cikinsu babu wanda yaji daWin hukuncin daya yanke musamman mata_matan.
Malama Babba kam hawaye ma take ta sharewa.
"Dangane da batun Sata tarbiyyar da nace Babba na da saka hannu ciki shine.
Na daWe da hana Babangida mu'amalar abota da yaronnan Mustapha Wan gidan Baba na shago. Sabida yarone da sunanshi yayi ?auri a unguwa.
Bincike ya tabbatarmun da sahalewar Babba yaci gaba da abotarshi da yarannan ba tare da sanina ba.
Sai abu na biyu tana sane da yawon dare sarai da Babangida yake yi. Da saninta yake yin wannan yawon daren. Sabida bata son Sacin ranshi ita a kullum ta saka Babangida farin ciki. Wanda daga tsakiya ga abinda yaje ya jajiSo mana jibi yanzu ba hawaye take yi ba? To in dai Babangida ne kukanma banyi tunanin in an soma ba.
Sabida a cikin wannan halin da ake ciki har rashin kunyar Babangida ta kai ya kira Sabuwa su fita zuwa gidan rawa har yana iya rungumeta a layi wa'iyazubillah
Tarbiyya, da ilimin addinin dana Waurashi akai bai amfaneshi da komai ba kaico. Magajin malam sunji tsoron sanar dani fitar dare da Babangida yake yi dan gudun su jefani a mawuyacin hali. Wai ashe har ?ananun kaya yake sakawa yaita yawonshi a gari ma. Kuma ita Babba tana sane sarai"
Duk waWanda suke cikin wajen taron hankalinsu ba ?aramin tashi yayi akan lamarin Babangida ba, dama abinda ya aikata jiyan.
Wannan wani sabon lamarine a cikin wannan zuriyar mai Wauke da Wumbun tarbiyya da ladabin yi nayi bari na bari.
Malama Babba taji tsoro da fargaba irin wanda bata taSa ji ba a rayuwarta. Shikenan ashe ma duk abinda suka Tsara da Yaya Hanne babu aikin da zaiyi anan. Bata da kalmar da zata iya dawo da martabarta da kimarta a idanun Baba malam ko Qur'ani zata haWiye tana aman surori bazau kuma yadda da'ita ba. Ita yadda Waya ce a wajenshi, baya kuma bayar da wata dama ta biyu bare har aje ga ta uku."
Kai Baba malam ya girgiza yace
"Ko akwai wanda yake jin yana da magana ko wata shawarar?"
Babu wanda yace shine ba dan basu da abinda suke son faWe ba. Sai dan kawai gudun fishin Baba malam da faWin abinda ka iya tunzurashi yayi fishi da mutum"
"To shikenan tunda babu mai magana na sallameku dukka, banda kai Manga "
Kafin su soma yin?urin tashi suka jiyo hayaniya mai ?arfi a tsakar gidan harda ihun wani almajirin Baba malam da halamar wata muguntar akai mishi.
?uu suka fice matan harda Wan gudunsu dan son ganin menene ke faruwa.
Suna fitowa suka tadda ?an uwan Sabuwa ne a tsakar gidan Almajiran Malam Baba na ?o?arin hanasu shiga shine har aka yanki magajin malam a hannunshi."

SABUWA:.
Ina zaune a tsakar gida na jiyo hayaniya daga nesa tanata tahowa. Murmushi nayi dan nayi imani su Adama ne suke shirin zuwa ganina.
Ai kuwa ban aune ba sai gasu a tsakar gidan almajirai nata faman tattaresu.
Magajin malam magazin ya ri?e yana ja ai kuwa kamar ?ibtawa da bismillah Magazin ya zaro wu?a ya yanki tsintsiyar hannunshi ya sake shi babu shiri, tare da yin wani ihu. Ihun da yayi sanadiyyar fitowar su Sa,a ?uu.
"Meye haka ke faruwa. Me zan gani?"
Cewar Malama Babba wacce dama a cikin ba?in ciki take.
"Abinda kika gani shi kika gani??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????. Ku dai kuna da neman fitina wallahi. Babu damar azo ganin Lolo sai ku hana Malam ya hana Malam ya hana. To ko makawuyane yau dai dole yayyen Lolo su ganta"
Maigogul ke magana cikin Waga muryarshi akan Malama Babba."
Tare da Kawu Manga Baba Malam ya ?araso wajen.
Zuwanshi yasa yaranshi suka soma zamewa, ko wacce na jaye Wanta.
Malama Babba tace.
"Allah ya wadaranku ku dai baku da kunya ban taSa ganin marasa kunyar iyaye kamarku ba. Ace kana uba amman kaine jagora..." Da mugun kallo Baba malam ya kafeta ?irjinshi na sama da ?asa.
"Hattara Dattijuwa bari kul Wallahi. Kin ganni nan na sari mutane sunfi dubu, har kisa nayi an kulleni amman na fito. Wallahi ko a barmu muga Sabuwa ko in tsigema wata kunne a gidannan"
Kafin suce wani abun Babangida da shigowarshi kenan ya ru?un?une Magazin ta baya yana ?o?arin fitar dashi.
Ai kuwa nan kokawa mai haWari ta shiga gudana a tsakankaninsu.
Magazin ya samu Babangida ya dinga naushinshi a duk gaSoSin da yasan zai karya mishi kuzarinshi. Baba malam yana tsaye ya hana su Wawo raba wannan faWan. Sai gwabza dambe akeyi.
Zaro wu?ar da magazin yayi ne Babangida ya danna a guje magazin yabi bayanshi.
"Kuje Wawo ku raba faWan maza"
Yayi maganar cikin ba da umarni.
"Maigogul na fahimci dukkannin take takenka burinka yin fito na fito da nine. Burinka ka kunyatani a idanun duniyane.
Ku matan ku shiga ku ga Sabuwa, amman duk abinda zaku ce mata sai dai kuce mata ayau.
Wallahil azeem babu wacce zata sake shigowa cikin gidannan da zummar ganin Sabuwa In kuma da'ita zaku tafi gata nan. Kuje ku yi duk shelar da zaku yi. In aka sake kawo mata ziyara abinda kuke tunanin yiyuwarshi bazai yiwu ba. Ya kamata ka gane jama'a na ganin ?imata"
Juyawa yayi zai bar wajen. Maigogul yace.
"Ai na faWa na maya muddin muka tafi da Sabuwa to tabbas sai abinda kake son burnewa ya fito"
"Saime ya fito mana. Nima bari kaji duk ranar da wani ko wata daga Sangarenka ya sake zuwa da zummar ganin Sabuwa to tabbas Wana bazai taSa aurenta ba ka sani bana magana biyu. Ka kuma fice mun daga tsakiyar gida babba dakai a shekaru a ido gaka babu laifi sai dai kash hauka da hauragiya su sukai maka ado
Ke kuma ki shige Sarayinku"
Fuu Baba malam ya fice a gidan yana faWan maganganu domin ranshi yayi matu?ar Saci ainun.
Jinshi yake yi kamar ba shi ba. Hatta gidan da mutanen gidan gani yake ba su bane.
Jin wannan furucin sai jikkunanmu dukka suka mutu. Maigogul babu shiri ya fita.
Ni kuma na ja su Adama muka shige ciki.
Yaya aka ?are da magazin da Babangida oho.
Muna daga Waki muka jiyo kukan Malama Babba sai bata ha?uri akeyi.
Fuu ta shigo cikin Wakin da nake ta rufeni da shegen duka.
Banyi niyyar ramawa ba sabida inason sake jefata cikin uku.
?auke numfashina nayi da ?arfin tsiya wanda hakan yasa nayi suman dole.
Su Adama kuma suka fasa ihun Malama Babba ta kasheni.
Da ?yar na yarda na farfaWo harma ana shirin kaini asibiti kafin na yarda na farfaWo.
Baba malam ya dinga faWa a tsakar gidannan tare da gindaya sharruWa masu zafi. Ranar gaskiya an fusata Baba malam sosai.
Gaga_gaga al'amura sukaci gaba da tafiya ranaku suna shuWewa. Abubbuwa marasa daWi sun faffaru ciki harda yin?urin zubarmun da ciki da Malama Babba tayi har sau biyu bata samu nasara ba
Na biyun saida nayi sati biyu a asibiti kafin aka sallamoni.
Malam yayi faWan yayi rikici sosai sai da akaita zuwa bashi ha?uri daga dangin Malama Babba kana ya hakura. Babangida kuma bai ganni ba balle yayi nashi yin?urin. Su Maigogul kuwa an Wauke ?afa gudun kada a fasa aurena. Sai dai su kirani a waya mu gaisa kawai.
Da lokacin daya kamata na soma zuwa awo yayi Baba malam ya haWani da malama ?arama ta rakani muka je. Duk wata hidima Baba malam ke yi mun. Duk abinda nake so zanje in sameshi a makaranta in faWa mishi in sha Allahu kuwa zaisa a aiko mun dashi.
Babangida dai ya samu da ?yar an ro?i malam ya yarda zai dinga shigowa gaishe da mahaifiyarshi amman shi baya bu?atar gaisuwarshi.
?iyayya babu irin wanda ba'a nuna mun a gidansu Babangida ba.
Ni kuma zaman gidan ya dameni nayi yin?urin guduwa har sau biyu Baba malam yana hanawa. Kuma koma dai yayane ina ganin girmanshi kwarjini gareshi bana wasa ba.
Ranar da cikina ya cika wata tara cib na haifi diyata mace a asibiti
Nasha ba?ar wahala dan anyi tunanin ma na mutu
Baba malam duk ya shiga damuwa ainun
MRS BUKHARI
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ac_t



IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA SHIDA 6


Na sha wuya sosai, abun har ya gagara ansa hannu za'ai mun aiki sai kuma na sauka da kaina.
Ana haihuwar kuma duk wahalar sai ta wuce. Sai washegari na samu kaina
Duk da yarinyata ?ar gaba da fatiha ce sai naji duk duniya babu abinda nake so sama da wannan yarinyar.
Gashi babu ta inda ta baro Babangida Kunji wata ?udurar Allah.
Yarinyata tana gadon jarirai a kwance Malama Babba data iso yanzu da malama karama da muka tawo tare duk sun ?i su Wauketa har sai da Baba malam ya ?arasone yasa hannu ya Wauketa. Ya daWe sosai yana kallon yarinyar. Nasan dai bazai wuce tsantsar kamanninta dashi yake mamaki ba.
"Allah mai yin yadda yaso, yarinya ta raba duk wata kaddama. Sabuwa sannu ko. Akwai abinda kike bu?atane?"
A_a so nake dai ?an gidanmu su san halin da nake ciki"
Kai ya gyaWa.
"Nasa a sanar musu zasu zo nan asibiti su sameki. Mahaifiyarki zata zauna ta kwana dake anan zuwa gobe a sallamemu sai mu koma gida"
Malama Babba tace.
"Nayi tunanin ai a gidansu zata yi wanka. Kasan haihuwar fari tana bu?atar kulawa daga ita har jaririyar. Sannan duk wannan kamannin ai yana da kyau a sake tabbatarwa ko? "
Kallo mai Wauke da tuhuma yayi musu du su biyun.
Sai da yayi ma jaririyar adda'a kana ya dubeni yace.
"Akwai wani suna da kike so a saka mata ne. Ko Babanta ya riga da ya zaSa mata sunane?"
Dukkansu su ukun ni suke kallo. Ni kuma sai numfashi nake saukewa.
Babu sunan da muka zaSa mata"
Kai ya gyaWa yayi. Mata huWuba da suna Mardiyya kana ya mi?o mun yarinyar na rungume abata ina jin motsin sonta a zuchiyata.
"Yarinya nayi mata huWuba da sunan kakarta mahaifiyar Babba wato mardiyya. "
Daga malama Babba har malama ?arama sun kaWu sai dai babu halin tankawa.
Ramadanne ya shigo da abinci. Malama ?arama ta zuba mun, farfesun kayan ciki ne sai kunun gyaWa. Nasa hannu na amsa dan dama ba ?aramin yinwa nake ji ba. Ga jikina babu ?arfi kwata_kwata har rawa yake yi nasha wahala fa sosai.
Fita Malam Baba yayi. Ni kuma jinjirata na jikina na cinye wannan farfesun tas na kora da kunun.
Take bacci ya yanko mun.
Na daWe sosai ina baccin wahala ina farkawa naga Rahama da Labbai Sai naji wani sanyi a raina da naga ?an uwana.
"Sannu Lolo kin tashi? Ai kinsha baccin gajiya haihuwa ai ba wasa ba. Allah dai ya raba lafiya saura haramar yin aure kuma. Boyeki ya ?are ai.
Cewar Rahama dake shan tea Labbai kuma na ri?e da Mardiyya.
"Kinga

6 / 25