Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   14 / 25

39K to 42K   out of 72.9K words

zata koma. Ai ko shine autan maza ehh gara ta zo ta zauna tunda ba dole bane sai tayi auren ba. Dattijo a wannan karon fa Babangida zai iya rasa ranshi in baiyi sakinnan ba, wai anya kuwa ba'a caca aka ciyomu ba kuwa? ?iyayyar da kuke ehh mana tun muna yara ai ta isa. Ke Lolo ki shiga ki zauna ki bararraje."
Maigogul yace.
"Inta bararraje kai zaka Wauki nauyinta ashe ko?"
"To saime tunda kai ba iyawa zaka yi ba saita rataya ai a wuyana. Su kuma waWannan yaran su bar gidannan tun kafin in yankasu Wallahi kar su sake zuwan mana gida. Ku kuzo ku fice kafin in yanke ku ehh"
Da sauri ya nufo kanmu.
Matar dana gani a gefen Gaza da bansan wacece ba itace tayo carab ta ri?e wu?ar tana magana da muryan dabanci.
"Ahh huce Gaza ai su yarane kuma basu da lefi a kan komai. Zasu koma shima ubansu bazai bari su dawo nan ba. Eh su Maigogul a dinga sassauta musu iyayene koma yayane eh ba zaka so mu haifi Maigogul ?arami yazo yana sa'insa damu ba"
Kaina a Waure cikin rashin kuzari nace.
Gaza wacece wannan Win?"
Ihu yayi da wu?a a hannunshi yana jujjuyawa kafin yace.
"Wallahi aure nayi fa Lolo da aurena na baro gidan yari ma kinji rabo. Kin ganta nan ?ar amana ake faWa miki mace mai ha?uri da kulawa. Kayanta nake wankewa ma kuka shigo. Wallahi baki ga kulawa ba lokacin ina kotu harda nama take kawo mun. Allah kin ganta da aikinta gandiroba ce mai tsaron ?an balaja'u.
Idanu na zare kawai ina mamaki.
Rakiya tace.
"Ai sai ku koma tunda Gaza ya Waure miki baya zaki bijire mana."
"A_a kada ki ja magana Rakiya a bijire take fa dama. Wai yau aka saba wannan rikicinne. Ku dan abu ta kazan... Kuzo ku bar gidannan nan ai ba gidan ubanku bane"
A gigice Mardiyya ta ri?e hannun ?annenta suka fita. Juyawa nayi na bisu a baya na jasu zuwa gidansu Adama. Ina jiyo ihun Gaza yadda kuka san mahaukaci wallahi. Yaushe ma dan Allah ?wa?walwata zata huta a gidanma. Maigogul sai donna zagi yake yi shi kuma, girki ma yake yi yau a gidan.
Ku zauna anan nima yanzu zan dawo"
Nan na barsu na koma ciki na tadda matar Gaza a cikin su Adama a Wakin Rakiya harda Gazan sai labari suke ana dariya.
"Lolo kinga gini inayi ko? Madamsy nake ma gini kinsan bata tare ba har yanzu tana kwana dasu Rakiya ne."
Allah sarki Allah ya baku zaman lafiya"
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ameen ai Lolo tun a gidan yari Gaza yaita bani labarinku
Sai bayan da mukai aure ya fito sai muka zo muka tarar ba'asanma inda kike ba. Amman yanzu me ake ciki dangane da makomar auren naki?"
Adama ce ta basu labarin na sake shigar da wata ?arar harma an kaima Babangida sammaci. Gaza yace.
"Bana wallahi in dai Babangida bai bini a hankali ba saiya rasa rayuwarshi. Nifa Lolo da zaku yarda sawa zanyi a kamosho in saka mishi wu?a a wiyanshi wallahi sai ya sake ki. Ko in kasheshi kya yi idda ne ko takaba oho dai. Uban kowa ya huta.
Su su Maigogul babu abinda suka saka a gabansu sai son kudi.
Ku duba yadda duk muka zama ?a?a duk babu na gari"
Rahama ce tayi carab tace
"Gara ka bari abi matakin Shari'a tukunna. Yaci albarkacin ubanshi da ?a?anshi Gaza.
Na ro?eka kada ka aikata abinda zaka sake komawa gidan yari ga madamsy nan ka barta da wa?"
"Ahh in barta da Allah mana. Wai ke Rahama an faWa miki tsoron gidan yari nake yi? Naci dubu wallahi sai ceto. Wallahi ke wuya a Lagos wuya a kwatano, wuya a tafa wuya a mararraba, wuya a shagamu fa."
Madamsy ce ta shiga yi mishi kirari yana ?ara botsarewa da ?yar suka harhaWu aka bashi ha?uri daya tsaya abi matakin kotu tukunna in hagu ta ?iya a wannan karon dole ayi dama.
Ni dai da ba daWin jikina nake ji ba na mi?e na fito ni dasu Labbai zamu koma can Wakinsu.
"Lolo zan samu dubu uku a hannunki zanyi kuWin motane wallahi kun ganni ba?i zanje tasha in taro zan kaisu ges house ?an kuWaWen jikina dasu nayi girki."
Maigogul ke magana yana gaban murhu yau dai shi yake girki a gidan duk da ba wani sabon abu bane. Yayi gwafe_gwafe a gaban wuta jallof sai ?amshi take zubawa wallahi saida yawuna ya tsinke"
To zan aiko maka dashi"
"Allahu Akbar kaga ?ar albarka wacce aka haifa tsiya na bacci. Lolo ta Maigogul Allah yayi miki albarka. Ba zaku tsaya kuci abincin nawa bane? Duk da ba?i na dafama. Bari in zubo miki ke kaWai zaki samu arzikin cin abincinnan Lolona uhm bana so kina damuwa Lolo kin ganni nan Hamsha?in garna?a?in mai kuWi nake miki fatan ki aura. Lolo kika auri mai kuWi dani zaki tafi ai bazan iya zama ba"
Ya tashi harda Wan gudunshi ya zari kwano a kwando ya zuba mun da dama kuwa ga nama an yayyanka ?anana abinci sai ?amshin kori yake yi.
Hawayene masu zafi suka zubo mun daya tawo da sauri ya bani kwanon.
Madadin in amsa sai na faWa kafaWarshi na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuchiya.
Shiru Maigogul yayi yana ri?e dani da hannu Waya ga abinci a Wayan hannun nashi.
"Aikin banza da wofi yanzu nan har Ma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????igogul ya kai irin wannan uban a wajenki Lolo? "
Cewar Rakiya.
?agoni yayi yana share mun hawaye da gefen malum malum Winshi yana wani irin murmushi.
"Lolo kiyi ha?uri ki dena yawan kuka ni Maigogul ina tare dake har abada. Zaki yi albarka zaki samu rayuwa mai kyau a gaba. Amshi abincinki kije kici ki ?oshi"
Amsa nayi na kalleshi muka yi murmushi.
Sai kawai ya amshi kwanon ya sake zuba mun abincin na karSa na fita Rakiya sai shewa take yi.
Da muka isa Wakin su Labbai saina buWe kayana na zaro dubu shida naba Sadiya ta kaima Maigogul dubu huWu Rakiya dubu biyu.
Abincin daya bani kuma nasa su Mardiyya a gaba suka ci. Saida suka gama na aiketa ta siyo biredi suka kara da shayi. Ganin lokacin shan maganina yayi ne yasa nima na sha shayin na warwatsa magungunana na jingina da bango ana Wan hira ina saka baki sabida in ?warara kaina.
Hmmm wajajen huWun yamma muka jiyo sallamar yaro wai ana sallama da Sabuwa inji wani mutum a ?ofar gida.
Ina kyautata zaton Yaya Kamilu ne. Wanka na fito da sauri na soma saka kayana.
"Mardiyya kije ki ce ma mai kirana ganinan fitowa likitane shi ya taimakeni a asibiti kuma shi yaita biyan komai na maganina"
Na faWa mata ne tun kafin su zargi wani abun su soma tuhumata ko in bar ?wa?walensu da hasashen da bansan wanne iri bane.
Fita tayi a nutse nima na samu zarafin shiryawa na zura hijabina na ja hannun Malama muka fito.
Ai kuwa shi Winne yana jingine a bakin motarshi Mardiyya na gabanshi yana mata tambayoyi tana amsawa na isa da sallama.
"A_a Sabuwa har kin warware an shiga cikin ?an uwa ko?"
Dariya nayi mishi kawai.
Ya yafito Malama halamun taje. Sakinta nayi taje suka gaisa yake tambayarta ita izufinta nawa tunda yaji Mardiyya tayi sauka"
"Sabuwa ashe yaran namu malamai ne dan ko ni babu sittin a kaina akwai dai arba'in."
Murmushi kawai nayi Mardiyya ta kama hannun Malama zasu koma ciki yaa kirayi sunanta.
"Mardiyya tsaya ku shigarma da Ummi kaya"
Both ya buWe ya zaro manyan fararen ledoji ya mi?a mata. Tana kan karSa na hango Babangida yana daidai ?ofar gidanmu yana tawowa idanunshi a kaina ?em.
Har su Mardiyya suka shige bai ?arasoba.
Isowarshi ke da wuya sai cewa yayi
"Sabon farka kika samu shine kika yi ?aryar kurumcewa kika gudu kika bar gidan aurenki da yaranki, kika tafi kika barni da kewarki da tunaninki ashe?
Malam dan abu ta kazan ubanka... Bata faWa maka tana da aure bane? Ko da yake son zuchiya bazai barka ka tuno wannan ba.
Nine mijinta wanda zamu ?are rayuwarmu tare"
Kawai saiya cukume Kamilu.
"Ki shige gida Sabuwa wallahi ko in miki dukan tsiya na rantse tunda baki da mutunci matar ?addara maras kamun kai ko ki koma ciki ko ni dashi muyi mutuwar kasko wallahi"
Kamilu yace.
"Sabuwa shige gida abunki zanyi mishi bayani"
Ina Babangida da dambe ya kama Kamilu Ni Ko nasa hannu aka na kwarmata ihu dan na fahimci Babangida ranshi yayi mugun Saci sosai yafi ?arfin Kamilu.
Ai kuwa jama' a kamar jira suke yi suka fiffito ciki harda su Adama.
"Tabb Lallai Babangida abun naka yakai
Labbai maza kirawo Gaza yazo ya raba wannan faWan.
Ina gefe ina kallo kukanma ya?i zuwa mun dan nasan bama a soma komai ba.
Ina buWe idanuna na hango ?ar Shuwa na tawowa wajenmu. Gaza kuwa a guje ya tawo matarshi na biye dashi. Su Rakiya ma sai gasu afujajan babu ko mayafi.
Yana isowa yasa hannu ya SanSare Babangida a jikin Kamilu faWa ya koma a tsakaninsu.
Babangida ya naushi Gaza 'Gaza ya rama.
"E lallau yau sau nayi ajalinka wallahi wai ni ka fasama baki Tabb yau zaka gane waye Gaza"
Wu?a ya zaro kamar ?ibtawar idanu ya yanki Babangida, Babangida idanunshi sun rufe da kishi sai tijara yake yi. Madamsy ce tayi saurin shiga tsakaninsu.
?ar Shuwa ganin jini na fita a jikin Babangida yasa ta dinga danna ihu kowa da kowa ya fito. Da ?yar faWan ya lafa da taimakon mutane, da taimakon su Rakiya da suke ta cakume Gaza. Maigogul dai baya nan. Sun sha naushi in nausa da Babangida sosai shi kuma Gaza ya yayyankeshi a waje kusan huWu ga jininshi nan kaca kaca. Kamilu yana ri?e da hannun Gaza ga dattijai anata bashi ha?uri.
"To naji amman ya bar unguwarnan kuma kada ya sake zuwa layinnan da sunan zuwa wajen ?anwata wallahi ko yaranshi na gani sun zo gidanmu saina illatasu. Ai kai ?aramin dan abu ta kazan ubane mu iyayenka ne yaro a iskanci."
Babangida na Waure hannunshi da Wan kwalina daya faWi yace.
"A fito mun da yarana to. Kuma wallahi ko mutuwa kuke yi kuna dawowa Sabuwa tawace ina son matata sonta a jinin jikina da jijiyoyina suke yawo bazan saki Sabuwa ba sai dai duk abinda za'ayi ayi
Kai kuma wallahi bazan taSa yafe maka hakkina a kanka ba."
Gaza sai ihu yake yi ganin matarshi shi ya hana ya kai Babangida ?asa.
Labbai ce ta tarkato yaran ta turasu gabanshi. Shine ya ja hannayensu suka bar layin. Gaza ya ja hannun matarshi suka tafi. Su Rakiya suka bishi Rakiya sai Webo zagi take tana dura ma Gaza. Shi kuma yana faWa yana sake rantsuwar faWanma yanzu aka soma.
"Kinga ?anwata kiyi ha?uri zuwanane duk yaja wannan abun. Ki shiga gida ki tabbatar baki Wauki damuwa kin Waura ma kan ki ba. Kinsan ba lafiya gareki ba.
Ashe Babangidan naki mahaukacin zaki ne. Duk da naga halamun makauniyar soyayyar da shi kanshi bai gane soyayya bace a tattare da amonshi ba, amman tabbas yana mutuwar sonki. Ki je zamu yi waya kinji ko?"
Kai kawai na Waga Adama ta ja hannuna muka shige ciki.
Naci kuka kamar raina zai fita har saida ciwo ya bigeni sai Dr Kamilu Adama ta kira bai jima ba ya dawo yaita rarrashina yana bani kalma har dai raina ya Wanyi sanyi amma fa ba sosai ba gaskiya.




Babangida:.
Yana tafe su Mardiyya na binshi a baya ya ri?e hannunshi da Wankwalin Sabuwa wanda ya ji?e da jini sharkab.
A guje ?ar Shuwa ta biyosu lokacin har sun hau abun hawa.
"Baban faty ashe dama zaka iya zuwa wajen Sabuwa matar da tabi tsohon saurayinta. Bayan data dawo kuma ta wuto gida kai tsaye. Inaga dai bokancin Sabuwa da mahaifinta yayi tasiri a kanka dan bokace ita da ubanta nasan baka san wannan ba"
Kallonta a matsayin mahaukaciya Babangida yake yi. Idanunshi a mugun rine ga yaranshi jikinsu duk yayi sanyi .
"Malam ja abun hawannan mu tafi kaji ba hankali bane da'ita"
?ar Shuwa tace.
"Tafiya zaka yi ka barni wai?"
"Ke in kinga dama kema kiyi zamanki a gidanku. Ba Sabuwa ba ko wacce macen ma ta fice mun a raina gayyar tsiya"
Da faWa yake maganar dan a mugun hasale yake.
Fuu abun hawan ya wuce ya bar ?ar Shuwa tana she?a dariya a titi.
"Ai wallahi Babangida ko tsirara zanyi yawo dolen dole saika rabu da Sabuwa har shegiyar ?arta sai ta bar gidanka domun ba Yarka bace.
Ai tunda Sabuwa ta kwace mun Khalid to dole ta rabu da Babangida. Kuma saina saka mata ba?in jinin da ko kallonta wani Wa namiji bazai kuma yi ba wallahi sai dai ta dawwama a gaban shegun iyayenta Khalid kuma saina rabasu ya dawo hannuna domin tun kallon farko ni Khalid naso ba abokinshi ba."
A titi Babangida yasa aka sauke su Mardiyya shi kuma ya wuce kemis aka wanke mishi wajen yankan a can layinsu. Kai tsaye gidam Kawu Manga ya nufa.
Yana shawo kwana ya hango Kawu Manga tare da Baba Malam a ?ofar gida harda Sa'a tana gurfane a gabansu.
Baiso Baba Malam ya ganshi a wannan halin da yake ciki ba amman babu yadda ya'iya haka ya nufesu.
",ina wuni Baba Malam yaya kufan jikin naka?"
Baba Malam sai ya yin?ura da ?yar ya mi?e.
"Manga zan shiga daga ciki in kwanta. Ke kuma Sa'a duk bijirewar da zaki yi daidai ne. Sauban ai Wanki ne kina da ikon zaSa mish mace ta gari kam ai naki da sau?i akan abinda ?aninki ya aikata ai duk wata Saraka daga wajen mahaifiyarku ne"
Yana kaiwa nan ya shige. Ai kuwa yana shigewa Sa'a tace.
"Duk Babangida ne ya ja mana bala'innan. Ni kuma taya ina kallo Wana zai auri yarinyar da aka sameta bata hanyar aure ba. Da uwar ?ar da uban ?ar duk gasu ga kamarsu. Inace ita uwar wajen saurayinta ma ta gudu da aurenta..."
"Yafa isheki Sa'a. Ki sani nima daga yau na soke maganar auren Sauban da Mardiyya. ?ata ko zata rasa miji ni ni kaWai ubanta na isa in sanyata a farin ciki. Kawu zan koma dama nazo in sanar muku Sabuwa ta dawo, amman gidansu ta wuce kuma ta sake mayar dani kotu"
Yana gama faWin haka ya wuce yana jin tsabar jiri tamkar ya faWi. Da ?yar ya iya kai kanshi gida. ?akin Sabuwa kai tsaye ya shiga bai zarce ko inaba sai kan gado ya kwanta yana sha?ar ?amshinta wani al'amari na bijiro mishi a zuchiyarshi game da sabuwa shi ba ?iyayya ba kuma ba jin haushi ba.
Kiran wayar Sumy ce ta dawo dashi hayyacinshi wanda yayi daidai da kiran sallah azahar da aka soma a masallacin unguwar.
?aga wayar yayi a sanyaye. Yana Wauka yace.
"Sumayya bari inje masallaci inna fito zan kiraki"
"To shikenan ina fa jiran kiranka ato dan ina da magana fa ato."
Kai kawai ya gyaWa ya kashe wayar ya mayar aljihunshi ya fito falo.
"Aminu kuyi alwala bari in sake kaya sai mu je masallaci ko?"
Sai da ya sake taSa jikin Malama kafin ya fita har zuwa lokacin da zazzaSi kau a jikinta. Shi sai yake jinma kamar zazzaSin ?aruwa yayi.
Dole ma ya ?aru ai irin wannan jafa'in daya faru a gabansu ai dole ya sake assasa hauhawar zazzaSi.
?akin Ramatu ya shiga ya ko tadda Wakin ma?il da mata.
Sabida haushi kawai sai ya fita ya nufi Wakin ?ar Shuwa ya saka ki ya buWe ya shiga.
Yana tsaye a cikin uwar Wakinta zai cire kaya Ramatu ta shigo.
"Haba ranka ya daWe ya zaka shigo nan kuma alhalin kasan nice nake dakai har sai anyi la'asar girkina zai fita.?"
?ur yayi kawai yana kallonta yama rasa mai zaice mata. Sai a lokacin ne taga yankan dake tafin hannunshi dana wuyanshi mammanne da filasta.
"Subhanallahi wannan ciwon kuma fa daga ina haka?"
Wucewarshi banWaki yayi ya sakar ma kanshi ruwan sanyi kawai idanuwanshi a lumshe yana hango Sabuwa a gaban Dr Kamilu harma da yaranshi.
Kanshi a mugun Waure yake ga tambayoyi cike a bakinshi ko ya fesar babu mai bashi amsarsu.
"Wato Sabuwa dai na lura ajalina take so tayi ta huta. Ko wanne Wan iskan ta kuma samowa oho. Kuma iyayenta da ?an uwanta suka mara mata baya. Ni Sabuwa zata ci ma amanar Aure?"
Lafiyayyen hannun ya doka a bango yana jin wani irin ?aikayi a zuchiyarshi.
A gaggauce ya dauro alwala ya fito.
A zaune fa a bakin gadon ?ar Shuwa ya fito ya tadda Ramatu.
"Ki tashi ki fice mata a Waki. Ai da tana nan ko labulen Wakin baki isa kin ri?e ba balle har kima kanki masauki a kan gadonta ko?
Bana son neman jarfa ki barni da damuwar dake damuna dan ALLAH"
Jikinshi ya goge harya sauya kaya Ramatu bata fita ba tana kallonshi baki a taSe.
"Wai shin har sai zuwa yaushe zuchiyarka zata dena wahalaka akan Sabuwa ne. Oho wato wannan ciwon ma ?an gidansu ne suka sake ji maka amman ka saketa ka?i sakinta. To ma dame tafi ragowar matan daka dinga saki in banda farar fata.
Tsinka mata mari yayi mai zafi
A Wakin ya barta a tsaye yayi ficewarshi. Shine dai ta biyoshi ta fito tana ri?e da kunci
Masallaci suka wuce da yaran ana idar da Sallah ya dauki Mardiyya da Malama a mashin sai asibiti. Ai kuwa suna zuwa akace ciwonta ne ya tashi babu shiri aka basu gado da gaggawa.
Daga shi sai Mardiyya a asibitin har zuwa bayan la'asar kuma ya kira Malama Babba ya sanar mata a tunaninshi zata turo a zo a zauna dasu a asibitin shi kuma ya tafi neman kuWi sai yaji shiru.
"Mardiyya ki zauna da Malama ina zuwa yanzu Waya daga cikin Ummanku zata zo ta zauna da Malama su kwana ke kuma inna dawo sai in mayar dake gida"
"Toh Baba sai ka dawo Allah ya tsare"
Har wani tashi kan Babangida yayi sabida tsantsar daWi.
Yana tafe yana lissafi har ya karasa gida. Bai shiga gidan ba sai da akayi magriba tukunna.
?akin ?ar Shuwa ya nufa kai tsaye ya taddata a kitchen tana tu?a tuwo.
Bai kulata ba ya shige ciki, itama babu abinda tace mishi har saida ta gama tu?a tuwonta kana ta shiga ta sameshi yana waya da Mustapha yana labarta mishi an ba Malama gado. Sai da ya gama wayar tas ya sauke kana ya dubi Yar Shuwa da tayi ?uri tana kallonshi.
"Ki haWa abinci a kula zan kaima su Mardiyya a asibiti Malama aka ba gado. Sannan inason ki zuba ruwa a filas"
"Kash gashi abincin daidai cikinmu da yarana na girka sai kuma naka. Ruwan zafin dai tunda da wuta bari in Waura

14 / 25