Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   7 / 25

18K to 21K   out of 72.9K words

Lolo yarinya kyakkyawa sak ubanta babu inda ta baro shi.
Sai dai mun zo muka tarar babu kowa a wajenki ga jaririya a kwance kunata she?ar bacci."
Hmm ai basa zauna ba. Gara da Allah ya kawo ku dan ni kam daga nan sai gidanmu. Na gaji da wannan kullen da suke yi mun."
"A_a kada ma ki soma Lolo. Gara ki koma can Win dai kinga kar maganar Auren naku ya rushe kuma. Za dai ayi magana zan zauna dake acan Win sabida a kula dake yadda ya kamata. Ki Wan haWa da shan magungunan mata dana gyaran jiki tunda yanzu batun aurenku ne abu na gaba.
Adama ce taso tazo ta zauna dake to bata jin daWine a kwance take babu yadda take, ga babu kuWin zuwa asibiti. Lusarin mijin nasu kuma baya ma garin yabi babbar mota wai zuwa Inugu. Shi Babangidan yazo yaga yarinyar?"
Bai zo ba. Kuma nasan bazai zo ba. Ai hatta kayan jaririya, da duk wani kayan haihuwa Baba Malam ne yayi. Babangidan da har yanzu ba'a amsa gaisuwarshi"
?ar Shuwa ce ta katse mana hirarmu.
Ina ganinta nayi murmushin farin ciki nayi kewarta sosai duk da dai a rana ma mukan yi waya takai sau uku inma ta kama har fi.
Haka muka kwana mu uku ma a asibitin daga mu sai mu, an dai kawo mana abincin dare lafiyayyen tuwon shinkafa da miyar shuwaka har da man shanu.
Washegari sassafe su Rakiya da su Maigogul da ?an Wakinmu dukka suka zo ganin yarinya.
Anan Baba Malam ya tarar dasu aka dai gaisa babu yabo babu fallasa
A hakan Maigogul ya nemi Rahama zata zauna dani ta kula dani acan.
Allah cikin ikonshi sai tace .
"Dama ko baku bu?aci hakan ba ni zan bu?ata. Sabida Sabuwa na yin arba'in a ranar za'a Waura aurenta a ranar kuma zata tare a gidanta in sha ALLAH"
Murmushi Maigogul yayi yace.
"To hakan yayi kyan al?awari cikawa. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Ni ina zanga kuWin kayan gado nan da kwana arba'in? Ka gansu nan dukkansu lokacin aurensu su suke yima kansu kayan Waki. ?arya da ciwo bani da kuWin da zanma Lolo komai. Sai dai a Wan ?ara mana lokaci"
Rakiya tace.
"Gaskiya kam muna bu?atar ?arin lokaci. Dan inta wannan za'a daka ma auren bazai yiwu ba in dai da kudinshi za'ayi bikin."
Ai da faWin haka Maigogul ya hau nuna ma Rakiya hannu tana faWa yana faWa har sai da ma'aikatan jinya suka zo suka musu magana akan su fita.
Baba Malam yana tsaye motsin kirki ya kasa yi sai zuwa can yace
"Ya yara ba zasu lalace ba ace yarinya ita zata ma kanta kayan Waki ita ba aiki ba ba sana'a ba. Shin waWannan waWanne irin mutanene Babangida ya kwaso mana wai? Hmm babu damuwa. Sabuwa ku shirya ga mota a waje an riga an baku sallama"
Yana gama fadin haka ya fice.
Su Labbai ne suka haWa mana kayayyakinmu. Suka kawo mu har bakin mota.
"To Rahama duk yadda ake ciki mayi magana ko ta wayane"
"To Rakiya. Amman fa ni ina ganin babu bukatar a Waga aurennan. Bari dai in muka isa can Win zamu yi waya"
Da wannan muka rabu.
Muna shiga gidansu Babangida Malama Babba dake tsaye a tsakar gida rike da bokiti ganinmu yasa ta sau bikitin.
"Ohh ni Saratu yanzu Malam ashe da gaske yake yi wannan yarinyar a nan Win zata yi jego? Babu komai ai zata gama jegonne"
Rahama tace.
"To da a ina kike son tayi? Akayi renon cikin da haihuwarshi ma sai wankan jegone ba za'ayi ba.
Ke Lolo inane Wakin da zamu zaunan yake?"
Nuna mata nayi da hannu muka wuce muka bar Malama Babba na sababi a tsakar gida.
Ina kwance Rahama tace.
"Kinga Lolo tashi ki ba yarinyarnan mama tasha sai mutsu mutsu take yi. Ko ruwan nonon bai zo ba ki bata in tana Wan zu?a zai zo da kanshi."
Mi?ewa nayi nasa hannu zan karSeta Malama ?arama tayi sallama ta shigo da gaushi ta dire ta fita, bata daWe ba sai gata da ruwan wankan jinjira a sabon bawon na cikin seti da Baba malam ya bayar aka siyo.
"Gama bata Maman sai ki mi?ota ayi wanka. Rahama ko? Sai kuje kiyi mata wankan yamma. Ni na dunga mata na safe"
Baki Rahama ta taSe tare da mi?ewa.
"Lolo kafin ta gama sha bari in wanke kayan jinin da muka dawo dashi. Baiwar Allah sabulu da omo fa"
Malama ?arama tace
"Zan je in tambayo Malam duk yadda akayi ya manta ne bai siyo a siyayyar haihuwar ba. Bari a gama ma Mardiyya wanka tukunna"
Tayi maganar babu annuri kamar a yadda Rahaman tayi mata kenan.
Mi?a mata jinjirar nayi na fita Rahama ta bi bayana zuwa banWakin tayi mun wankan tawul ta gargasa mun jikina, in tasa tawul dinnan a ?asan marata ta danna sai jini yaita zuba.
Naji daWin jikina sosai ana kiran sallar muka fito daga wankan.
Mun shiga mun samu Malama ?arama harta gama yima Mardiyya wanka tayi mata gashin cibi tana wanke kayan da aka cirema yarinyar ne a cikin ruwan wankan. Muna shigowa ta suri bawon ta fice tana faWin.
"Allah ya sauwa?e wallahi ko a cikin labaran hikayoyi ban taSa jin labarin da yayi kama da wannan ba. Wannan abun kunyar da yawa yake"
Tsaki muka ja ni da Rahama. Ni dai tsabar daWin wanka har wani bacci_ bacci nake ji.
Ina gyangyaWi Rahama na gyaran Wakin Alawiyya ta shigo da ?aton filas na ruwan zafi sabo fil. Bayan ta ajjiye ta kuma shigowa da ?atuwar leda sha?e da kayan tea komai na gongoni sai sikari ne kaWai na kwali mai zaki ce, wasu na kiranta mai iyali.
Data sake shigowa sai ta dure ?atuwar kular abinci da wata babbar farar leda.
"Ga sabulun da omo Baba malam yace a kawo muku. Allah ya raya Mardiyya "
"Ameen in da gaske kike yi. Shi zakaran da Allah yaso sai yayi cara ko ana shawo ana muzuru sai yayi caranshi."
Rahama na gama faWin haka ta buWe ledar ta suri ?aton omo ta fice zuwa tsakar gidan.
Ni kuma tea kakkauta na haWa cikin ?aton kofi, na saka lokaci a cikin kular da aka sha?o mun da lafiyayyar jallof mai nama da kifi.
Sosai na zage ina cin abincin.
Na jiyo Rahama tana ta dura ashariya a tsakar gida.
Ban dai ji muryar kowa ba halamu ya nuna wani abun ta gani shi yasa.
Muryar Baba malam naji yana gargaWinta akan ba'a mishi hayaniya bare ashariya a gida, ta kiyaye in ba haka ba zata koma inda ta fito.
Daga nan na jiyo takun tafiyarshi zuwa Wakin da nake. A bakin ?ofa ya tsaya.
"Sabuwa an kawo miki kayan shayi da sabulai?"
E an kawo gasu nan"
"Akwai wani abu ne da ake bu?ata wanda ban siyo ba?"
Shiru nayi ina nazari gaskiya yayi ?o?ari ya sai komai da komai ko Wan halak albarka.
A_a babu a yanzu dai"
"To shikenan gobe za'a soma miki naman gashi. Ki zauna da shirinki kina yin arba'in zaki tare a gidanki. Allah zai rufa asiri ko babu yawa ni zanyi miki kayan Wakin sai ki sanar ma iyayenki"
Nan ya tafi ya barni da mamaki baki a hangame jin wai zai mun kayan Waki.
A idanunshi kaWai inna kallla ina hango ?iyayyar da yake yi mun, amman duk da haka yana ?o?arin lallai sai Babangida ya aureni.
Murmushi kawai nayi naci gaba da kora tea.


Malam Baba:.
Daga wajen Sabuwa kai tsaye Wakin Malama Babba ya wuce.
Suna zaune ita da Yaya Hanne suna tattaunawa dangane da batun haihuwar Sabuwa suka jiyo muryarshi da ma abinda suke sa?awa mummuna.
Basarwa yayi tamkar bai ji ba dan ko a fuska bai nuna ba, Malama Babba kuma sai tasha jinin jikinta. Ganin babu damuwa a fuskar Malam yasa ta fito da fara'arta shi kuma ya riga da yaji komai murmushi kawai yayi.
"Yauwa Babba batun auren Babangida da Sabuwa ne. Ki faWa ma Wanki ina neman dubu Wari biyu a hannunshi kafinnan kafin sati uku.
Kafinnan kuma ya kawo kuWin ragon da za'aima ?arshi hakika nera dubu talatin cib.
Ku kuma mata ta Sangarenku sai ku soma shirye_shiryen biki"
Mamaki yasa Malama Babba ta kasa rufe bakinta data hangameshi hangangan.
Har Malam ya kusan barin Sarayin sai taga ya juyo.
"Af Babba na mance. Zai soma iya fara neman gidan haya tun yanzu kinsan gidajen haya tsada suke yi"
Dole ta haWiye malolon daya tokare ma?oshinta murya a dashe tace.
"To Malam zan faWa mishi sa?onka."
?aki ta shiga ta zauna daSas a kusa da Yaya Hanne. Sai salati kawai suke yi a cikin wannan yanayin Babangida ya shigo da sallama ya samesu.
Yasan baya raba Wayan biyu shi yasa ma bai tambayesu meke faruwa ba.
"Babangida kaga dai abinda ka jawo mana yanzu muna ji muna gani zaka auri wannan yarinyar maras tarbiyya ta zamema uwar ?a?anka. Wannan wanne tarihi Malam yake son kafa mana mai zafi haka. Yaya Hanne duk wani shirinmu ya rushe ki duba sunan uwarmu ya saka ma yarinyarnan sabida ya nuna ma ?arama iyakata"
Babangida ya razana sosai da wannan labari daya riskeshi. Har ?asan zuchiyarshi baya jin ko Wigon son Sabuwa face zallar sha,awarta. Manufarshi shine cin moriryar ganga kawai kamar yadda akema duk wata karuwa.
Sai gashi yaci biredi yana tunanin ya yaga leda ashe ledar bata yagu ba.
Yafi kowa sanin rashin tarbiyyar gidansu Sabuwa shi a iyakar saninshi ma bai taSa ganin gida maras tarbiyya da kowa Wan iskan kanshi bane kamar gidansu Sabuwa ba, wai ashe Malam Baba zai yarda a auro Sabuwa a matsayin surukar gidan malamai gaba da baya? Tunaninsu duk barazanace duk da sun san malam kaifi Wayane amman duba da tarbiyyar gidansu Sabuwa yasa suke tunanin ba za'ayi auren ba"
Iska ya busar yana jin wani zazzaSi_zazzaSi na buso mishi.
"Saratu ku kwantar da hankalinku. Gobe ki tambayi Malam zuwa ?auyensu in ya barki zamu je a motata. Inma hagu ta?i yi zamu koma dama. Kinsan Allah Babangida bazai Auri wannan yarinyar ba. Kuma dena damun kanku"
"To Yaya Hanne ai bazai taSa barina zuwa ?auyansu ba sabida yasan abinda zai kaini. Kuma kinsan kafiyar Malam kuwa? Balle wannan abun yadda ya Waukeshi da zafi. Kuma duk ya fimu tsanar Sabuwa da danginta ma."
Yaya Hanne ta dafa Malama Babba tace
."zanzo gobe zaki ji zuwa da dawowan Saratu. Kai kuma saika kiyaye gaba kana ganin halin da kasa mahaifiyarka a ciki. Gata da kishiya sun samu abun goranta mana marar goguwa."
Shi dai Babangida yama kasa cewa komai, zuchiyarshi sai tu?a mishi take yi. Duk duniya babu wanda yake so sama da sabuwar budurwarshi wadda a lokacin ita ce a gaba. Duk da baya jin aurenta, amman tana da dukkan abinda yake bu?ata a jikin mace.
"Ka fasa bankinka ka ciro dubu talatin zan kaima Malam kuWin sayen rago kamar yadda ya bu?ata"
Cewar Malama Babba.
Haka dole Babangida yayi abinda Malam yace musu. Malama Babba taje ta sameshi ta bashi kuWin.
Ta Sangaren Babangida yamma nayi ya isa majalisarsu nan akaita kacancana zancan masu zugashi ya aureta ya koya mata darasi sunfi masu cewa kada ya aureta yawa.
Ya gamsu da ya aureta yai mata wula?anci na fitar hayyaci yai mata sakin wula?anci.
Murmushi mugunta yayi da ya hango irin rashin mutuncin da zaiyi mata.
Sai yaji hankalinshi ya kwanta a sauwa?e zai koyar da'ita darasin rayuwa.
Washegari."
Malama Babba tai ta jiran Yaya Hanne ba ita tazo ba sai wajajen sha biyun rana.
Abunda tazo mata dashhi yafi ?arfin tunaninta bata taSa zatin haka ba.
"Kinga wannan maganin ? Kina zuba ma Malam a abincinshi wallahi zancan wani aure ya ?are. A ta?aice duk taurin kanshi sai yadda kika yi dashi Allah"
Jikinta da hannunta har rawa suke yi ta amshi maganin. A ranta ta gamsu kota wanne irin haline da dai a auro Sabuwa gara ta kauce hanya.
"Amman Yaya Hanne babu abinda zai sameshi ko?"
"Babu abinda zai sameshi. Ke dai ki saka mishi maganarnan a kasheta kowa ya huta"
Haka ta amsa akan nan da kwana biyu in girkinta ta zago zata zuba mishi."

SABUWA:.
Sassafe Malama ?arama tamun wankan jego, tayi ma jinjira wanka, Rahama kuma ta wanke kayan da muka cire har da nata.
Ina daga gado ina cin tuwo Rahama kuma tana waya dasu Rakiya tana sanar dasu halin da ake ciki biki saura kwana talatin da bakwai kenan.
"Rakiya inaso kije ki samu Zahira ta gidansu Malam Bala ta haWo mana magunguna zamu biyata daga baya sabida a tari abun da wuri kunga bamu da lokaci"
"To ba zuwan bane matsalar ba. Kuma nasan Zahira zata baku bashi. Waye zai kawo muku gida babu kowa sai Uzairu zuchiyata kuma kun dai san halin wannan kafaffen tsohon."
Rahama tace.
"Aba Uzairu zuchiyata ya kawo in yazo ?ofar gidan ya ba almajiran gidan zasu kawo nana."
"Rakiya tace.
"To shikenan zanje yanzu, dan dama gyalena na hannuna inaso zanje dubo Adama ne jikin dai ya?i ance kishiyoyinta sun rarrafa sun kaita ?aramin asibiti kuma ga ba kuWi. Da ?yar na haWa dubu biyu su Sadiya suka harhaWa mun shine zanje. Zan soma zuwa wajen Zahiran tukunna"
Da haka sukai sallama.
"Lolo kinji jikin Adama yayi tsanani kishiyoyinta nema suka kaita asibiti.
Ni dama gida Rakiya ta dawo da'ita duk da gidanma babu daWi. Inma ta dakkota abinda zata ci shine aiki. Amman wallahi da kashe auren akayi da sai yafi.
Kwananta nawa dama a gida tayo yaji da kanta yinwar gidan da rigimar gidan yasa ta kwashi jiki Aisha ta rakata ta koma Wakinta."
Ai da tana jin magana da tuni ta kashe wannan ?addararren auren. Allah dai ya bata lafiya. Amman Rahama ni da an bar wani maganin matan. Ni ba auren soyayya ba ba komai ba ina ni ina wani shan magunguna azo a barni da biyan bashi."
Rahama tace.
"Ai ko ba aure zaki yi ba yadda kika haihunnan yana da kyau kiyi gyara sosai. Ki bar ganin irin auren da zaku yi kenan. Sanda zai lallaSo ya biyo dare mu muna ina? Su Labbai su Adama da Layuza duk ba irin auren da suka yi ba kenan?"
Haka dai mukaita hirarmu muna daga Waki.
Da yamma sai ga kunun kanwa da naman gashi sha?e da kwano naci naci har saida na ture.
Ina samun kulawa a gaskiya fiye da tunani. Kullum sai naci naman gashi, ga magunguna Rahama sai durkamun take yi harda nasu tsugunno a gaushi duk inayi.
Ranar suna aka yanka mun katuwar tinkiyata a soye marau aka kawo mun halamu sun nuna ko tsoka Waya basu Wauka ba. Ni dai nasa Rahama ta raba nama gida biyu aka kira Uzairu zuchiyata yazo ?ofar gida Rahama ta bashi ya kaima Rakiya harda dubu biyar na bashi dan Adama tana gida auren nata ya mutu ga jinya har yanzu bata warke ba."

Malama Babba:.
Ta Sangaren Malama Babba tayi iyakar yinta Malam yaci wannan maganin a ranar da yaci sai batai mishi maganar ba sai washegari ta tareshi da maganar suna kwance.
"Malam yanzu wai da gaske kake yi yaronnan Babangida shi zai auri wannan yarinyar ?ar marasa tarbiyya? Ka duba watan yarinyarnan ta shiga na gomaa kenan a gabanmu mahaifinta kawaline kuma maras mutunci yanzu duk girma da darajar wannan gidan namu mai daraja da surukan da yaranmu suka auro daga gidan malumta a rasa wacce za'a gaiyato cikin haular sai Sabuwa?"
Tsam yayi yana kallonta. Tunda ta iya tunkararshi da wannan maganar tabbas yasan akwai abinda take sa?awa abinda yaji suna faWa ta aikata kenan. Sai yayi ?o?arin gwadata ta hanyar cewa.
"To yaya za'ayi Wanki ne ai ya jajiSo mana ita. Sai nake ganin kamar dashi da ita ?waryar sama ke dukan ta ?asa. Ko wacce ?warya da abokin burminta, in banda abinki mugu ai shi yasan makwancin mugu, ba'a abota sai hali yazo Waya"
Yayi shiru tare da kafeta da idanu yana karantarta
"Malam bambamcinsu a fili yake. Kai mai mutuncine, malami mai koyar da al'umma. Ka duba makarantarka Walibai nawa garemu muna ba mutane karatu harda tarbiiya. Nima Malama ce da taimakonka na zama hakan. ?arama ?ar gidan malamai ce. Kaf surukanka daga gidan malumta suka fito. Taya zamu haWa iri da Sabuwa"
Dariya yayo sosai wanda ya daWe bai yi irinta ba.
A baWini kuma zuchiyarshi ji yake tamkar zata faWo dan raWaWi. Yafi kowa ?in Sabuwa yafi kowa ?unsan ba?in ciki da takaici in yaganta, ko yaji muryarta da duk danginta da abinda ma ya shafeta baki Waya. Shi ta Sangarenshi zai aurama Babangida Sabuwa ne sabida ita yarinyar da aka haifa, an riga da an haWu ko ba'a soba. Dalili na biyu zai aura mishi itane a matsayin horarwa dan yayi imanin Babangida zaifi son ya auro ?ar mutunci, ?ar manyan mutane, ?ila ma ?ar malamai kamar yadda sauran ?an uwanshi suka yi hakan. Na uku, zaiyi hakanne a matsayin hannunka mai sanda ga sauran yaran gidan. Duk da baya fatan a sake samun Babangida kashi na biyu, amman kashi na farkon ma ai baisan za'a samu ba. Hausawa suka ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
Dalilinshi na huWu shine ita kanta Sabuwan ai mata adalci a taimaki rayuwarta a tsamota daga cikin duhun da take. ?ila ta sanadinta ?an uwanta su shiryu. Domin har ga Allah duk yadda yake ?in Sabuwa yafi ?in Babangida fiye da'ita. Ita gaskiya gaskiya ce baya bayan kowa sai bayan adalci. WaWannan sune manyan dalilinshi.
"Yanzu dai mu kwanta da safe ma ?arashe maganar na gaji, gashi ina da raWin suna da asuba"
Yana faWin haka ya juya mata baya.
Zuchiyarta fes ta kwana amman da asuba kafin ta bar turaka Malam ya kankare mata hadda ta hanyar wasu kalmomi marasa yawa sai firgitarwa da sare guiwa.
"Babba ki sake sanar da Babangida batun kuWaWennan lokaci nata gabatowa, sannan ya tabbatar a satinnan ya nemi inda zai zauna sabida ayi fenti da komai. Za'aje ayi mata jere ranar talata mai zuwa rana ita yau kenan."
Yana gama faWin haka ya nufi hanyar waje saida ya fita ya girgiza kai yace.
"Mata kenan mai ilimi ma kenan ina ga jahila kuma?"
Haka dole ?anwar na?i Malama Babba ta saduda, ita ta sai da sar?arta ta dan?ama Malam Baba dubu Wari biyu daya bu?ata a wajen Babangida. Shi kuma Babangida ta barshi da neman haya.
Harma an samu ciki da falo da bayan gida da kitchen sai dai gidan gidan yawane sosai. A haka aka kama akayi duk gyare_gyaren daya dace kamar yadda Baba malam ya bu?ata dai.
Ta nashi Sangaren kuma Malama ?arama ya kira ya bata dubu Wari biyu da hamsin. Da wasu dubu Wari uku daban.
"?ari biyu da hamsin Win kayan lefe zaki haWo mun ke da Larai. Wannan Wari ukun

7 / 25