Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   17 / 25

48K to 51K   out of 72.9K words

ya falla mata.
"Wai Sa'a baki da hankaline ina kike barin iliminki da tarbiyyar da aka baki ne? Ya Wan uwanki ido da ido ki dinga nuna ?in kininshi. A tunaninki dan bata hanyar aure ya samu Mardiyya ba zai ?ita ne? Ki bar ganin yana zafafa ?iyayyarshi ga uwarsu dasu kansu. Nayi imanin a yanzu da Sabuwa zata dawo cikin rayuwarshi zai fi kowa farin ciki da samun nutsuwa kuma in faWa muku soyayya zai nuna ma matarshi sosai.
Ai abinda ya faru tuni ya riga daya faru harma ya wuce tunda yau ina Sabuwan take? . In Sauban bazai aureta ba ai shikenan sai a haWa auren da Mahadi yaron Wawo ko kuma Surajon Kudidi ba shikenan bane? Mardiyya ai ba zata rasa mijin aure ba a haularmu ba. Ki guji Sacin ran Yaya a kanki ina gargaWinki"
Malama Babba tace.
"Shikenan wallahi Mango. Abinda Sa'a take yi sale_salin Sata zumunci ne tunda shi Sauban ai yana son Mardiyya so mai tsanani sosai. Sannan ai ba wannan maganar ake yi ba"
Wawo ne yayi gyaran murya kana ya Waura da cewa.
"Ni kam wannan maganar a barta tukunna ayi batun inda Malama Babba zata zauna tukunna. Dan Mahadi yana da wacce yake so Wiyar ?anwar mahaifiyarshi zai aura shekararsu guda suna nema"
Wani yawun ba?in ciki da takaicine ya taru a bakin Babangida da ?yar ya haWiye yawun dan ba?in cikin yadda Ahalinshi suke zu?ewa kan Auren Mardiyya. A zuchiyarshi ya ?udurce Mardiyya zata auri bare a waje can inda za'afi gane darajarta kuma kome za'ace sai dai ace amman bazai taSa cusa yarinyar a inda zata sha wahala ba zumuncine zai lalace a banza.
"Ke Babba ki daure ki koma Wakinki kiyi zamanki Malam yayi miki wannan alfarmar. Yarannan zaki duba ko ba gaskiya ba Wawo?"
"A_a Kawu ni ina ganin kawai mu haWu mu siya ma Malama Babba gidan da zata zauna a cikin layinnan, su Nusaiba sai su koma hannunta islamiyyarta da take koyar da mata sai ya koma cikin gidan kawai. Amman zaman ba daWi zaiyi mata ba. ?a?a kam ai Auta ne kaWai a gabanta shima kuma mata zai fito dashi yayi aurenshi a huta"
Kudidi tace.
"So samu a sai gidan da shi Auta zai iya zama tare da matar tashi in yaso sai su dinga Webe mata kewa tunda su Nusaiba Wakin miji zasu tafi suma."
Nan suka tsayar da matsaya akan hakan.
Babangida kuma Malama Babba da Kawu Manga da Wawo sukai tayi mishi nasiha kanshi na ?asa hankalinshi gabaki Waya baya ma wajensu yana dai jin abinda suke cewa fahimtace dai baya wani yi Sabuwarshi kawai yana tunowa a inda tayi sujjada a harabar kotu na godiya ga Allah bisa rabuwarsu. Idanunshi ya lumshe kawai.
Da wannan taron ya watse akan Malama Babba zata zauna a gidan Wawo kafin a samu gidan da za'a siya mata ta koma.
Bayan Babangida sunyi Sallah a masallaci sai ya wuce kai tsaye majalisarsu data soma taruwa da abokanshi.
Nan daga masu tsine ma Sabuwa albarka sai masu ganin gara da aka saketa uban kowa ya huta.
Daga haka suka shiga tsara yadda tafiya Waurin auren gobe zai kasance.
?asimu yace.
"Ohh Allah dai yayi cewar dole_dole sai Sumy ta zama matarka. Wane karsashi ko zumuWi angon da yasan amaryarshi ciki da bai zaiyi?
Ai nasan babu wani marmari ko mis?ala zarratin tattare da kai dubi sauran aurarrakin da kayi a baya irin zumuWi da abubbuwan da kake yi."
Musbahu yace.
"To wannan auren ai auren dole ne za dai a yishi ne sabida rufin asiri. Bawai dan ana so ba"
Babangida dai sai ido duk wanda yake magana idanunshi a kanshi. Shi kaWai yasan irin zafaffakin da yake ji a zuchiyarshi dukane kawai tako ta ina bashi da ma hannun karewa.
Bashi ya nufi gida ba sai sha Wayan dare sabida gidanma baya ?aunar ya koma. Da ba dan ya tuba ba tabbas da yau a Club zai kwana ko dan ya samu sau?in zuchiya.
Amman dake ya tuba yana tafe a lifan dinshi yana rera karatun Qur'ani hakanne ma ya haifar mishi da ?ar nutsuwa kaWan.



SABUWA:.
Har ?ofar gida motar Dr Kamilu ta kawo mu duk da saurin da yake yi hakan bai hana bayan dasu Adama suka sauka ya tsaya ya rarrasheni ba.
"?anwata kiyi ha?uri nasan dai hankalinki ya kwanta amman fa ba duka ba sabida rayuwar yaranki zaki duba. Amman zan baki shawarar ki nutsu sosai ki kama kan ki, sannan kada kice wai ba zaki yi Aure ba da zaran miji ya fito miki kuma anyi bincike an tabbatar da nagartarshi kiyi aurenki kije ki huta hakan shine mutuncinki. Sannan ki sani ba duka maza bane suka taru suka zama Waya ba. Wani in kika aureshi sabida tsabar dadi ji zakiyi tamkar ba a wannan duniyar ta mutane kike ba.
Kar ki mance gobe kina da ganin likitarki kar kice ba zaki je ba. Sannan ki dage da shan magungunanki da sun Wakko ?arewa ki sanar dani.
Kuma duk abinda kike bukata kada kiji nauyi ki bugo ki faWa mun.
Ga kayan abinci a both na kuma kawowa ki nemi yara su shigar miki dashi."
Godiya nayi mishi sosai sai washe baki nake yi wai yau nice nayi firi babu igiyar kowa a kaina ni Sabuwa.
Sakkowa yayi ya sauke mun kayan abincin mu kai sallama ya ja motarshi ya tafi. Sadiya ce ta shigo layin a mota, tsayawa nayi har dai ta gama sallamar ba?onta kafin ta taya ni muka kwashe kayan abincin muka adana a Wakinsu Adama wanda anan nima zan zauna, muka koma cikin gida da sallama a bakina.
Rakiya sai zage _zage take yi ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Ina shigowa tace.
"Ga filin tsakar gidannan Lolo ba dai zawarci ke baki sha'awa ba? To gaki ga zawarci wallahi kun Waura ai. Duk waWannan riWa riWan banzan da suka cika gidannan ko wacce mafaka take nema ko wanda yafi mazajensu na baya talaucine yazo aurensu za suyi ko babu komai ai Aure yana da daraja."
Gaza ne ya le?o daga Wakinshi labule a hannunshi yace.
"Rakiya yafa isa haka Lolo ba lafiya bace da'ita.
Shi kuma Babangida Allah ne ya so shi shi yasa ma al?ali ya raba auren. Rakiya baki san me muka shirya mishi bane wallahi shi yasa. Kuma babu wanda ya isa yasa Lolo ta koma mishi ta fito kenan. Zawarci ai ba mutuwa bane. Da yawan yaran gidannan sau nawa eh su ka yi aure eh suka fito kuma me ya cinyesu. Wani auren dashi bama gara babu ba. Ko ni nan da nasan ma haka aure yake da me zai aikeni in wani faWa. Ni naga abokaina sai rubibi suke yi ashe babu daWi auren"
Adama tace.
"Nima dai shi na gani. Gaza ya batun Webo kayan nata anjima zamu je tunda Baba Malam yace taje ta Webe kayanta shi ya siya kuma aure ya bata?"
"A_a da yamma akwai inda zani an bani wani aiki. Mu barma gobe ba sai in tattaro eh yarana muje a Webo mata kayan ba? Duk wanda yayi mana warki in sa yara su farWe shi eh wallahi Allah Rakiya naga eh kina haratata ne ai"
A haka suka barshi. Ni dai Wakin Rakiya na shiga na kwanta. A Wakin na tarar da Uzairu Zuchiyata da Salaha.
Salaha yaushe kika zo garin?"
Na faWa muryata da sanyi duk da zuchiyata fal farin ciki.
"Ban jima da shigowa ba Lolo ashe dai auren ya mutu to barkan ki na taya ki murna. Nima yaji nayo ke ni auren wallahi ya isheni haka. Zagi da cin mutuncin ya isheni.
Su Adama ne suka shigo duk aka bararraje gidanmu gidan daWi duk da ko wacce da matsalarta ba'a zama ayi jigum sai dai ayi ta hira ana musu ana nishaWi. Jin tashin muryoyinmu ne yasa Gaza shima ya shigo aka ci gaba da hira dashi.
"Adama kunji labarin Aisha tayi Sari ko? Tana asibiti bata ma wai gane wanda yake kanta. ?axunnan ?anwar mijin ta kira waya"
"Wayyo cikinne ya zube? Zaki je ne Rakiya ki zauna da'ita ko ni gobe sai in shirya in tafi?"
Rakiya tace.
"Gara ke kije Win dai gaskiya ni kam bazan iya wata doguwar tafiya ba.
Kafinma ta rufe baki sai ga kiran waya ya kuma shigowa wayar Rakiya Aishan ce wai suna hanya ita da mijin zai kawota gida tayi jinya anan.
"To ai shikenan tunda saida kuka kamo hanya zaki sanar. Da zamanki kikayi a Wakin ki ai yafi dama yanzu muke maganar Adama gobe zata tawo"
Tsaki Rakiya tayi ta kashe wayarta ta shiga mita.
"Kai wato a gidannan dai dole mutum ya dage ya zama mai kuWi ko dan ya huce takaici wallahi. Kai da naka amman sai ya ba da kai jibi Rakiya yadda eh kike tsaki fa dan kawai Aisha zata zo jinya, eh ba gara tazo ba"
Cewar Gaza kenan.
Ni dai sai ido kawai nake binsu dashi har wani murmushi nake yi wanda sai dai kawai naji yazo mun sabida a cikin farin ciki nake duk da yarana suna tsaye a raina.
Abu Waya nake tunawa inji hankali na ya kwanta na watsar da batun yaranma.
Yafi mun alkhairi in fuskanci abu na gaba.
Khalid ne naji ya faWo mun a raina. Amman sai take zuchiyata ta gargaWeni da faWin.
"Kada ki sake ki koma ?ar gidan jiya. ?ila matsalar da zaki samu tare da Khalid ta danne ta gidan Babangida. Auren Khalid tamkar an rabu da bukar ne aka haifi Habu.
Ajjiyar zuchiya na sauke na gamsu da zuchiyata Wari bisa Wari tuni nayi fatali da tunanin Khalid.
Yanzu burina shine sake gina sabuwar rayuwa ina fatan ta kasance mai inganci.
Da yamma lis sai ga Aisha sun iso ita da mijinta da Wiyarta muna can Wakinmu ana tattaunawa akan batun inda in an Webo kayana za'a ro?a a ajjiye Aisha ta shigo duk ta rame ta lalace ta saje ta zama ?ar ?auye sai dai idanunta har gobe yananan a buWe tar kallo guda zaka yi mata ka gane hakan.
"Kun iso kenan. Ina shi mijin naki ko yana gidansu Rakiya ne?"
Cewar Adama dake zaune tana ma Laraba kitso. A wahale tace.
"Yaje ya siyo magungunan da aka rubuta mun a asibiti ne.
Wallahi tunda na fito daga wannan ?auyan na fito kenan tunda ashe shima yafi son in zauna anan tare dashi dangin mahaifinshi ne suka zigashi. Ni kuma nace wallahi bazan koma ba"
Tashi zaune nayi nace mata.
Shi to me yace dake ina kuma yarinyar taki kika barota?"
"Cewa dai yayi na Wan zauna a gida ko na wata shida ne ya gani tukunna zai san yadda zai shawo kansu su ha?ura mu zauna anan. Sai ya kwaso mun kayana mu kama haya a nan yarinyar tana wajenshi, tare amman zasu koma tunda ni jinya nazo yi."
To hakan yafi zaman ?auye tsakani da Allah su ya kama. Amman Rakiya ta san komai?"
Idanu ta zare tace.
"Ina fa a hakanma sai zagina take yi wai na tawo. Nifa nakai sati a asibiti cikin yakai kwana goma da Sarewa kuma maganar gaskiya zubarwa nayi kawai sabida zaman garin bai yi mun ba. Shi kanshi ya fice mun akaina bazan sake jiki inta sumSulo ?a?aba wallahi kazo duk ka tsofe."
Bakina na taSe kawai. Adama kuma bazawarinta dakaci ne ya iso dama da shirinta tsab mayafi kawai ta saka ta fice.
Labbai kuma ta dubeni.
"Lolo ku haWo kuWin cefane ayo sai a Wora sanwa. Kema Aisha ki kawo.
?ari biyar na mi?a Aisha ta bada Wari uku anfa soma kenan.
Da daddare mu huWu akan katifa Waya kuma bawai shida da shida (6 by 6) ba ?aramar katifa ta gadon bono fa.
Wallahi baccinma kasawa sam nayi saida na dawo ?asa na kwanta a leda shine na Wan samu sassauci, zafi da sauro suka gallabeni naita juyi ina tsaki. Labbai kuwa kusan raba dare tayi tana waya tana kashe murya. Adama ma tayi nata ta gamane ta kwanta.
A ranar na sake tabbatar da tsayin dare.
Washegari muka tashi da sabon lamari faWa tsakanin Maigogul da Rakiya wallahi har waje.
A guje muka fita muka samu Rakiya ta cukume Maigogul ta shakeshi fa sosai har idanunshi sun yi ja. An cika layin ma?il kullum a cikin abun kunya mu dai muke a gidanmu.
Da ?yar Gaza ya raba faWan ya ja hannun Rakiya ya jefata zaure.
Wu?a ya zaro a ?ugunshi yana ta Webo ashariya yana Wumawa jama'ar da suka fito gulma. Daya karta wu?ar a ?asa kuzo kuga gudu.
Ni wallahi dan takaici da ba?in ciki ma ko magana na kasa yi su Adama suka biye ma Gaza akaita duma zagi na borin kunya.
Maigogul ya shiga gida suka Waura rikici daga inda ya taya.
"Tur wallahi da wannan gidan. Ni wallahi ba dan Madamcy ta matsa sai mun zauna a gida ba wallahi Wa ba zaku sake ganina ba ma har abada nima fa ji nayi kamar in sha?e Maigogul Win dan ba?in ciki.
Ya wanna zubar da mutunci a layi haka. Dan Allah ya ba za'a dinga kore muku samari nagari ba? Ku fa duba eh duk fa masu zuwa neman naku duk ?an balaja'u irinkune suke zuwa har ita Lolon mijinta Wan kunamane fa."
Adama tace.
"Gaza bar wannan sokiburutsun dan ALLAH ya batun Webo kayan Lolo nace?"
Wukarshi ya mayar ?ugunshi.
"Ku jirani zan tawo da ?an iska cikin bus tare da motar kaya. Zan kiraki ku fito titi mu haWu mu wuce. Eh duk wanda yayi mun wani wata wata bazai ji daWi ba wallahi in na dama sai an shanye."
Ya wuce fuu zuwa ?asan layi.
Mu kuma muka shige cikin gida.
Ashe_ashe wai Rakiya kama Maigogul tayi yana gulmarta a Wakin Hauwa shine fa akayi ta dambarwa daga ?arshe faWa ya koma kan Hauwa da shi dai muka karya mu kam.
Ana haka Gaza yayo kiran Adama akan su fito su wuce Webo kaya.
Adama da Labbai, da Sadiya, harda Aisha mara lafiya aka fice. Labbai har da soke wu?a itama
Maigogul yace.
"Gara in bi yarannan kada suje suyi Satacciya nasan ba'a haWa hanyar arziki da Gaza"
Aikuwa rigarshi ya bige ya fita da sauri na bishi na tsayar dashi.
Maigogul yanzu dakai za'aje Webo kayan? Nikam dan ALLAH "
Daga haka hawaye ya soma zubo mun. Taya in banda gida irin namu ace a saki ?arka kuma a matsayinka na mahaifi ace dakai za'a tafi kwaso kayanta. Wannan abun kunyar har ina"
Tsaki yaja daya dubeni yaga bil ha??i kuka nake yi wiwi yace.
"Aikin banza da wofi ai baki yi kuka ba Lolo badai zaman wannan gidan kika zaSa ba?"
Ya nuna gidan da bakinshi tare da Worawa da cewa. Abinda nake guje miki fa suna da yawa. Yanzu dubi da bala'in kayi nayi muka tashi a gidannan dashi muka karya fa. Lolo wa yasan sanda zaki kuma wani auren.
Zamu je a Webo kayan naga inda ma zaki ajjiye kayan naki a gidan uban naki da kike gadarar a sake ki ki dawo"
Ana ga ya?i Maigogul yana ga ?ura. Bai ko sake bi ta kaina ba yabi bayan su Adama suka gangara, ni kuma jikina a mace mus na shiga gidan. A Waki na samu Uzairu zuchiyata da Rakiya.
"Zo lolo Felisha ta ganki"
Ya kirawoni na matso kusa dashi. Wata baturiya na gani a kwance sai murmushi take yi. Tana ganina ta faWaWa murmushinta tana Waga mun hannunta.
Nima murmushin dole na ?a?aro nayi mata na Waga mata hannu.
Turancin nawa bazai wuce gaisuwa ba sai yes da no su biyo baya a haka dai muka gama gaisawa.
Shi ko Uzairu zuchiyata yaji turanci da figi da yagi sabida aji daWin yin ?arya har yanzu yana karanta ?amus tare da wasu littattafan koyon turanci irinsu tech your self ( koyi da kan ka).
Kaina na girgiza kawai na zauna kusa da Rakiya ina sauke numfashi.
Uzairu zuchiyata sai zuba turanci bil ha??i yake yi.
"Nace wai in aka Webo kayan naki ina za'a jibge miki su Lolo. Ga kaya masu tsada kada a jibgesu a tsakar gidannan su lalace. Gu Gaza da Sama su biyo dare su sace miki. Shine nace ko gidansu Bala zan shiga in ro?i alfarma ko zasu ara mana Waki a ajjiye kayan kafin Allah ya Sullo miki da wani sha ?undum Win?"
Uzairu zuchiyata da ya gama bidiyo da baturiyarshi sai yace.
"Kema kinsan ba zasu wani karSi ajjiyar gidannan ba. Ko sanda Auren Labbai na biyu ya mutu ba anje an ro?i za'a ajjiye kayan ba suka ?i fur ba. Amman lokacin da auren Halimar gidan Malam Habu tsohon mijin Labbai daya mutu su suka ajjiye musu kayan har tayi wani auren. Ni Rakiya wallahi baturiyarnan in fa na aureta kinsan Allah Waukeki zanyi daga wannan gidan in sake miki gida. Ranar girkinki Dad ya dinga zuwa yana dubaki, ban kuma yadda ya koma ba ke kaWai zaki zauna ehe"
Dariya muka yi ta yi dukkanmu na dubeshi nace.
Amma a mafarki ko? Wacce baturiyar ce zata aureka Uzairu zuchiyata? Yaro bari kada kyanka ya ruWeka. Kuma ina laifin a madadin ka Wauke Rakiya ka kyara musu gidan? Maigogul yau kuma shine Dad Win. To nima in ka Wauke Rakiya sai nima in gyara ma maigogul gidanshi in mishi aure ba shikenan ba tunda Ummin Mama ta kafe tana ciki.
Wallahi Allah har mamaki take bani. Shima maigogul Win murmushi yayi da Labbai ta kawo mishi taWin."
Da?uwa Rakiya tayi mun.
Mi?ewa tsaye yayi ya shiga jujjuyawa yana wata mayaudariyar dariya gashi a tsaye a kanta.
"Tabb na rantse da Allah ba duk turawaba wannan kyau nawa. Motsa jikima zan soma tace ?irjina tana Wanso yafi haka faWi kinga banci ta zama ba wallahi lolo ke bafa wasa bil ha??i Auruwa zanyi a turai tsab"
Rakiya ta kwaWo mishi takalmi duk muka kwashe da dariya.
"?an baWo ji abinda yake yi sak ubanshi. Ina tuno sanda Maigogul yake kamarshi. Ai har Uzairu zuchiyata ya mutu bai isa ya kamo ?afar gayen Maigogul ba. Tunda a yanzun ma shiga yake jerin gwanon manyan masu kuWi in dai a sutura ne ya saje harma ya fisu kwarjini. Ai lokacin da yake zuwa zance wajena wallahi da yamma ?an matan layin sa'annina da wanda suka girme mun firfitowa suke yi ko wacce ta zauna a ?ofar gidansu. In maigogul ya tunkaro layinmu zo kuga kallo a lokacin farinshi har kashe idanu yake yi halin rayuwane kawai ya mayar dashi haka. Amman maigogul yana halin a so shi"
Tafi Uzairu zuchiyata yayi yace.
"Yau dai Waya bayan an ci dambe Rakiya ta yabi Dad.
Uhm ai Maigogul na baza capacity.
Jiya naje gidan cin

17 / 25