Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   20 / 25

57K to 60K   out of 72.9K words

ya sauke a kafaWar Sauban Win.
Da haka Sauban ya Wauke ?afa a rayuwar Mardiyya sai dai fa ya ?udurce a ranshi shi da aure har abada bazai yi ba in dai ba Mardiyya aka aura mishi ba. Haka yaita jinya a tsaitsaye yaro duk ya zauce ya fita kamanninshi fa.
Ango Babangida dai haka ya kwana a Wakin amarya ga Wansu a falo Amir abun dai babu armashi amman ya riga daya rungumi ?addararshi kawai. Kuma yaji canji akan da sosai. Ko da su Sa'a suka ga Amir tabbas sunce kamarshi sak da mardiyya kamar kwabo da kwabo. Amman tunaninsu bai basu cewar ?an na Babangida bane. Sabida sun san wannan kamar ana iya samunta ko da ba'a ma taSa ganin juna ba. Magungunan mata da Sumy tai ta dibga sunyu aiki sosai a jikinta.
Washegari ya haWa kan matanshi a Wakin ?ar Shuwa tunda itace babba.
Tayi farin cikin girman data samu amman tana kishi da Sumy sosai musamman yadda taga Babangida na wani kallonta. Gata ?ar duma duma da'ita fatarta akwai kyau da gani zata yi laushi sosai.
Baki ta taSe daya faWa musu Wanta zai zauna a hannunta.
Haka dai ya tsara yadda za'a dinga girki da karSa_karSan kwana a tsakaninsu.
Rayuwar dai taita shurawa aiyuka sukaima Babangida yawa sosai dan yana koyarwa a makarantu fin uku. KuWi yake tarawa yana so in Allah ya dafa mishi zai koma sana'ar Baban bola irin na unguwa da ake kawo musu suke siya, in sun tara kamfani tazo ta kwashe. Tsakanin ?ar Shuwa da Sumy kuma ana buga kishi da kirsa na ?in ?arawa sosai Sumy suke zaman gugar jigida da Yar Shuwa abin duniya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yabi ya damu ?ar Shuwa sosai. Ramatu kuwa tana gefe dan wannan faWa yafi ?arfinta nesa ba kusa ba, basa ma ta tata sam.
Duk juma'ar ?arshen wata yana kwasar yara ya kai gidansu Sabuwa. Amman gudun fitina sai dai ya jira su Mardiyya a bakin layin su Sabuwa ya basu awa Waya suje a gaggaisa sai su fito ya maidasu gida
Allah baisa ya taSa ganin Sabuwa ba tunda dai ta bar gidanshi. Adama ko Labbai dai su suke rako yaran wajenshi.
Gaga_gaga haka rayuwa taita garawa har zuwa tsawon wani lokaci.
Yana tsaye a bakin mudubi yana gyara tsayuwar hularshi ?ar Shuwa ta shigo ta sameshi ya buga shadda mai ruwan toka.
Wani ?ududun ba?in kishine ya turni?eta ta tsani juma'ar ?arshen wata kamar yadda ta tsanii mutuwarta sabida tasan Babangida sabida Sabuwa yake son zuwan. Amman in ba haka ba ai yaran sun san hanyar zuwa gidan ya barsu su tafi da kansu mana.
A duk lokacin da zaije kaisu kwalkiya ta musamman yake yi. Duk da ta baza ?annenta suna mata c i d kuma sun tabbatar mata Babangida baya haurowa layin shine ma ta Wan samu sassauci amman fa ba sosai ba tunda tasan gurbin Sabuwa yananan. Kuma wani faWa da suka yi duk kishinta sai da ta ro?eshi ya cikace mata huWu ya kulle ?ofa ita zata fi samun nutsuwa. A wannan faWanne yace da'ita har gaba da abada gurbin Sabuwa zaici gaba da kasancewa dan bai cire ranshi da dawowarta Wakinta ba.
"Lafiya wannan irin kallo kamar zaki hadiyeni. Tunanin me kike yi haka inata magana shiru?"
Cewar Babangida dake magana da yar Shuwa yana fesa turare.
"Hmm naga sai sake gyara zaman hula kake ta faman yi tun tuni sabida zaka je gidansu tsohuwar matarka. Ai na riga dana bugo jirginka duk wannan kwalliyar sabida ita kake yi. Wai ni Babangida zawarcin Sabuwa kake yi ne ko?"
Murmushin cusa haushin daya saba shi Win dai ya kuma yi kafin tace.
"Me kika gani?"
Yayi tambayarne sabida yaji abinda zata ce. Yana mamakin yadda tafi kishin Sabuwa fiye da sauran kishiyoyinta.
"Sabida naga yadda kake Waukar wanka da aro motar abokai in zaka je wajenta abun yayi yawa. Sannan tunda dai Sabuwa taso rabuwa dakai ta makaka a kotu ka dena baccin kirki kullum kana Sallah. Da al?ali ya saketa sai ka sake ?aimi wajen sallarka ta dare ni shine na kasa gane maka. Wai dama Sabuwa kana sonta duk abinda kaita mata a rayuwa har saida ka kaita ma?ura?"
Murmushi yayi kafin yace.
"Ina mamakin yadda kika tsani aminiyarki sabida ni. Da gaske na Wauka ni'imar da ?awarki take ciki kaWai kika biyo. Sai daga baya na fahimci da wata manufar taki ta daban kika shigo ni tsanine kawai. Kina bani mamaki in kina kishi da Sabuwa. Sabuwa da kike gani mun rabu ne bamu rabuba wallahi. Zauna kina nan zaki ji ana guWar shigo da'ita cikin gidannan a karo na biyu. Dan tuni ciniki ya faWa"
Yayi hakanbe danya haWa zuchiyarta da aiki na wuni guda, tunda yasan shi sakine mara kome itace jahila bata sani ba.
Ficewa yayi daga uwarWakin zuwa falo.
A guje ta sha gabanshi a kiWime.
"Wai dan Allah Sabuwa zaka sake kwaso mana duk rashin tarbiyyar dake tattare a gidansu?"
Ranshi ya sosu da abinda tace akan Sabuwa har fara'ar da yake yi saida ta Wauke.
"Da gidansu Sabuwa da gidanki duk Waya nake kallonsu. Ki ?addara gidanku yafi nasu tarbiyya amman ai kema tarbiyya Maigogul ne tunda a cikin gidan kikai rayuwarki.
Ashe ke butulu ce Yar Shuwa har haka. Waime Sabuwa ta tsare miki ne haka? Wallahi Sabuwa ko yanzu tayi miki fintinkau, ta tafi data tashi tafiya saita warce zuchiyata tayi tafiyarta dashi. Aisha babu komai a ?irjina Sabuwa ta tafi da komai, kuma bazan iya karSowa ba. "
Yana isada maganarshi ya ajjiye kuWin cefane akan kujera.
"Sakwara da miyar kifi za'aci yau a gidan.
Sannan kada ki cika ma doyar ruwa sakwara in ba Sabuwa ce tayi ba bana gane kanta duk saita sake. Ko ita zaki kira a waya ta taimaka ta faWa miki yadda take yi ne?"
Ya ?arashe zancan yana dariya ya barta a wajen zuchiyarta kamar zata toye dan ?una.
Su Mardiyya kuma Babansu na fitowa suma suka fito ko wanne cikinsu zuchiyarshi cike da murna.
Mota suka shiga Babangida ya ja motarshi fu.
Wayarshi ce tayi ruri Sumy ke kiranshi amman bai Waga ba dan tun da dai ta fahimci Babangida ta ?are mishi bashi da komai saita buWe faifayin rashin mutuncinta gashi tazo a lokacin da rashin Sabuwa ya ladabtar dashi da kuma al?awarin daya Waukarma kanshi in ba dai da wani ya kama matarshi ba, ko kuma tayi yin?urin kasheshi ba. To babu batun saki haka su ukunnan zasu ci gaba da zama har mai rabawa ta raba su.
Suna isowa bakin layin ya hango motar Khalid a ?ofar gidan. Tabbas ya shaida motar sarai. A madadin ya tsaya saiya kunna kan motarshi zuwa cikin layin. Kafin ya ?araso ya hango Sabuwa ta shige motar Khalid.
Wani yawu mai Waci ya haWiye take jijiyoyin kanshi sukai raWa_raWa. A bayan motar yayi parking. Yana ta ambaton Allah dan har wani duhu_ duhu idanunshi suke yi.
"Mardiyya ku shiga gidan ku gaisa da kowa ku fito mu wuce"
Yadda yayi maganar kaWai yasa kowa ya shiga taitayinshi kawai.
"To Baba"
KaWai
Mardiyya ta iya cewa ta tusa ?annenta a gaba.
Yana yin?urin fitowane ya hango mahaifiyar ?ar Shuwa ta le?o tana waige_waige ga waya a manne a kunnenta.
Jikinshi ne ya bashi ?ar Shuwa ce duk yadda akayi tasa a le?oshi a gani..zuchiyarshi na tafasa Allah _Allah yake yi ya fito yaje ya samu Khalid ya fesar musu da maganganun da suka daWe a zuchiyarshi.
Bai jira komawar Maman ?ar Shuwa ba ya fito ya tunkari motar tasu.


SABUWA:.
?ur mukaima juna ni da Khalid.
Wallahi har ga Allah har kuma a cikin raina inason Khalid. Sai dai matsala guda biyu.
Na farko rayuwar da muka gudanar a baya.
Na biyu rayuwar da muke gudanarwa a yanzu tun da aurena a kaina.
Inna Auri Khalid banyi ma kaina adalci ba. Kuma duk bala'in sona da yake yi bazai hanashi zargina ba. Kuma zai iya fin Babangida rashin ganin darajata da kimata.
Zan iya komawa gidan da yafi na jiya. Ai ina ganin zai fi mun sau?i in Auri mutumin da wani abun bai taSa shiga tsakaninmu ba. Duk da wannan shine abu mai wuya duk wani Wan mutunci bazai zo neman aurenmu yazo Waya biyu ?an unguwarnan su barshi yazo na uku ba.
Ina tunanin irin su Khalid sune daidai da irin rayuwarmu.
Ya Allah ka kawo mun Wauki amman dai irin rayuwar da nayi a baya har abada bazan koma ba, ya Allah kayi ri?o da hannayena.
Hannuna da Khalid ya ri?e gam ne yasa na buWe idanuna muka ?urama juna idanu.
"Sabuwa naga kinyi ?iba kin sake yin haske. Da ganin yanayinki kamar kin samu ?ar nutsuwa.
Na buWe baki zan yi magana tare da yin?urin fisge hannuna kenan saina ga Babangida ya zuro kanshi cikin motar ta Sangaren da Khalid yake.
Da sauri Khalid ya waiga jin hucin mutum a gefenshi.
Idanu suka haWa da Babangida idanunshi sunyi jawur jijiyoyi duk sun tattaso a fuskarshi.
Da sauri Khalid ya saki hannuna ya haWe ranshi shima.
"Kai a tunaninka kaci nasara ka rabani da Sabuwa ko? Hmmm ka sani duk wanda yayi guga da nufin zai Webi duniya ko ya jawo bazai ga komai ba. Ka neme ta da aurena a kanta ma balle yanzu da saura kwana uku ta gama idda. Ke kuma kin kyauta dama halinki ne.
Abu Waya nake son sanar muku wallahi _wallahi wannan mitsiyacin bai isa ya aureki ba. Yadda na rasa shima sai dai ya rasa. Sannan in dai irin hannun wannan ?azamin kike son komawa ai kinyi gwari kuma kinci baya. Mutumin daya nemeki yake kwanciya dake, ya kai ki hotel_hotel shine harda yo miki tsarabar rigar mama da Wan kamfai, da sigari da aure a kanki shine kike tunanin gidanshi zaki koma kuma ki samu nutsuwa, shi kike tunanin ki aura Sabuwa?"
Murmushi yayi mun idanunshi tamkar zasu zubo da ruwan hawayen da suka taru yace.
"Kinyi gwari Cus kinyi gwari Cus. Ajjiyeki zaiyi a gida yaita zarginki, kuma ba zaki taSa burgeshiba neman matanshi zaici gaba dayi ya lalata miki rayuwarki a banza daga ?arshe hawan jinin dana Waura miki ya kasheki a banza.
Dake ke jahila ce ai lissafinki bazai kawo mik..."
Ya isheka nace Babangida ka sani kai ba ubana bane. Kuma na yarda na gamsu zam auri Khalid ko dan in ?unsa maka ba?in cikin da zai yi ajalinka ko yayo maka sanadin kamuwa da cuta marar warkewa kamar dai yadda ka haddasa mun hawan jini.
Yaya kuke so in saka kainane"
"Rufa mun baki ko in bubbuge bakin naki wallahi "
Ya Waga hannu Khalid ya cabke.
"Sanda take gidanka ma..."
Fisge hannunshi Babangida yayi ya sha?e wuyan Khalid da mugun ?arfin da Khalid ya kasa ?watar kanshi.
Fitowar yaran da Maigogul ne yasa ya sake wuyan Khalid.
Da sauri na fito a motar yaran suka nufo ni.
Maigogul kuma ya nufo wajen Khalid har jikinshi na rawa.
Sororo Babangida yayi yana kallon yadda Maigogul yake Sare_Saren son karasawa wajen Khalid har yatsu Maigogul ya take mishi.
"Ummi ashe kina waje. Ina wuni?"
Cewar Mardiyya da take kallona cike da fara'a.
Ina nan ai banga shigowarku bane shi yasa. To ya karatun? Aminu, Yaya AWWa'u yaya rashin ji? Malama yaya rashin son magani."
Babangida yace.
"Ku dallah ku tawo muje ni na gaji"
Jin yadda yayi maganar da zafine yasa yaran sukai saurin juyawa.
Da harara ya bini kawai ya tusasu a gaba suka wuce.
Maigogul yana wajen Khalid yana zubar da mutunci.
"Ke Lolo tawo mana me kike yi a tsaye da yara ki barsu su tafiyarsu"
Yana juyowa yaga ni kaWaice a tsaye.
"Au ashe sunma tafi ai dai yafi.
Kinyi ba?o maimakon kiyi ciki dashi a_a sale_salin ?an unguwa su ganku aje a tareshi ai mishi munafurci. Ki kaishi can gidanku "
Wani ?ududun ba?in cikine yasa nace.
Ai mun gama Maigogul."
Ina faWin haka nayi shigewata ciki na barshi da Khalid Win.
Ya suka ?are oho ya dai shigo ya nemi gefen gado ya zauna yana dandalan yawu yana ?irga kuWi.
Rakiya sai harara take zabga mishi.
"Wai Sabuwa shi wannan Win da dai batun aure yazi dai ko? Naga akwai gari a hannunshi ni dai na shaida mishi nanda kwana huWu ma ya turo magabatanshi"
A_a Maigogul wallahi ni ba aurenshi zanyi ba. Gaskiya karma ka karbi kuWinsu Rakiya ki saka baki fa a wannan karon ba yadda zanyi ba wallahi. Yaushe ma na gama warkewa akan ciwon ba?in cikin Babangida "
Takalmi ya jefo mun nayi maza na rufe fuskata.
"Mara kunyar kawai ni zaki ma ba?in ciki dan abu ta kazan...."
Mi?ewa nayi da sauri zan gudu yako yi nasara ya tare ?ofa.
"Yau ga tsiya da wasali ?asa. Wai meye haka ne Maigogul karyata zaka yi ne ko me?"
Yana huci ga takalmi a hannunshi yace.
"Kinga wata shirgegiyar mota ce fa tazo wajenta Rakiya baki ga wanda yake cikin motar ba yaro matashi mai tsabta. Ga kuWi yanzu wannan kuWin da kika ga ina kirgawa duk shi ya dun?ulo ya bani har jikinshi fa yana rawa.
Dama meye dalilin da yasa muka nace ta zauna a gidan wancan fitsararren tambaWaWWen yaron ba sabida arzikin da take ciki bane? To kuma yanzu Allah ya aiko mata da wani shine zata ce bataso. Ga yayyenta da ?annenta babu ma mai shinshinarsu in banda Adama da gobe za'a Waura aurenta.
Tana gani nine kwana a buzu ina buga ?asa hakan baiyi ba har saida muka bi ?an tsubbu kafin auren ya kusan tabbata zamu ce.
Shine wannan yarinyar zata mun haka?
Rakiya ?yaleni da'ita nace"
Tare suka haWu sukaita zagina Rakiya ta rufeni da duka Hauwa ce tazo ta fincikeni.
"Ke Hauwa babu ruwanki ki bari Rakiya ta ladabtar mana da'ita kaga ?ar ba?in ciki"?
Ficewa nayi a gidan ina haki na koma can gidanmu. Ina shiga Khalid ya kira wayata a zaure na tsaya na amsa wayarshi.
"Sabuwa ashe aurenki ya mutu shine kika kasa sanar dani, ko dai kina sha'awar komawa gidan mijinki ne ni ina can ina haukana a kanki?"
Ajjiyar zuchiya na sauke. Na samu damar saisaita kaina dan na fahimci in banyi ma Khalid dabara ba wallahi sai dai inji labarin an Waura mana aure.
Harga Allah bana fatan sake faWawa matsala. Maganganun Babangida sun sake farkar dani ainun.
Ba haka bane. Dama ni niyyata shine inna kammala iddata sai in neme ka."
Murmushi yayi mun yace.
"Burinmu ashe ya kusan ciki Sabuwa. ?arayinki yananan a rufe madam Wina ma tuni na faWa mata aure zanyi in saka matar a wannan wajen".
Murmushi nima nayi mishi tare da cewa.
Amman ai ina bu?atar lokaci. Maigogul ya shigo yake sanar mana cewar ya faWa maka nan da kwana huWu ka turo. To a zahirin gaskiya ina bu?atar kamar wata biyu masu kyau ko babu komai ai ya kamata in gyara jikina. Kuma yanzu haka gobe za'ayi bikin Yayata, ni kuma goben ma tafiya zamu yi da Uzairu Zuchiyata."
"Uzairu zuchiyarki fa kika ce?"
Dariya nayi nace.
Au kishi ya motsa kenan? Yayanane uwa Waya uba Waya. Kano zamu je gobe dashi akwai abinda zamu yi ne"
Bamu gama wayar ba saida na tabbatar Khalid ya janye da batun turo magabatanshi nan da kwana huWu an Wage sai zuwa wata biyu masu zuwa.
Har a cikin raina bana jin zan iya aurenshi ko da maza sun ?are. Amman ina tsoron yin saki na dafe. Naso batun bikin Adama ayi komai dani ko cikin abokan ango zamu dace duk da ko wacce cikinmu ro?onta shine ta dace wani abokin ango ya ?illota yace yana so.
Da tunanuka ratata na wuni. Dik da dai muna ta hira ana yima Adama tsiya sunje sun siyo kayayyakin bacci harda wanduna shine su Aisha da yaranta da suka zo zamu kwana tare suke ta mata dariya.
Sai naji ina kewar nawa yaran da yanzu suna gefena.
Amman inna tuno Babangida ya tafi da tulin buhunhunan Sacin rai da kishi sai inji wani sanyi a zuchiyata. Tabb yau babu zaman lafiya duk wacce take da girki yau zata gane kurenta in tayi wani wargi."
Washegari sassafe dan masifa muka wuce tasha ni da Uzairu Zuchiyata yaci uban gaye ya ?wama gogul yayi kyau sai kamanninshi ya sake fitowa sak da Maigogul.
Maigogul har tasha ya raka mu bai baro tashar ba ?arewarta har saida motarmu ta tashi.
?arfe taran safiya a Kano tayi mana.
Uzairu zuchiyata ya kira wani abokinshi ko ina suka san juna oho sai gashi anzo har tasha an Waukemu a ?atuwar mota, ni dai ina bayan mota nayi zuru."
Mrs BUKHARI ce taku

Babangida :.
[8/24, 10:16 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ems_copy_c



IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


BABANGIDA:.

Tu?in cikin rashin nutsuwa yake yi. Babu nutsuwa tattare dashi ?wa?walwarshi sai hasko mishi fuskar Sabuwa da Khalid take yi.
"Yanzu kana ji kana gani zai rabaka da matarka ya kuma aureta kai kana kallo?"
Zuchiyarshi ce ta shiga tunzurashi.
Tsaki ya saki kawai ya girgiza kai.
"Ina wallahi bazan taSa bari haka ta faru ba. Sai dai ni dashi mu rungumi juna mu mutu amman ba dai ya auri Sabuwa ba."
Wawan burki yaja a daidai bakin layinsu.
"Ku sauka kuje akwai inda zanje"
Yayi musu maganar a kausashe. Babu shiri suka sakko yaja motarshi fuu sai majalisa dama acan suka yi da Mustapha zasu haWu ya karSi motarshi mashin Winshi ma yana majalisar.
Ko daya ajjiye motar bai zauna ba cewa yayi dasu yana zuwa. Kai tsaye ya nufi gida Baba Malam yana zaune a kujera cikin almajirai yana karSan karatu Babangida ya shiga da sallama.
Ita data zame mishi wajibi ita ya amsa amman dur?uso da gaisubar Babangida basa gaban Baba Malam.
"Baba Malam dan Allah kaimun aikin gafara kaimun izini in dawo da Sabuwa Wakina tunda har yanzu iddarta bata cika ba.
Wallahi tunda muka rabu ban sake samun kwanciyar hankali bane. Kuma a yanzu wallahi na tuba na dena duk abinda nake yi. Nayi maka al?awarin bazan sake sakin ko wacce mace ba ba kuma zan sake jajiSo Aure ba"
?ur Baba Malam yayi yana kallonshi yama rasa me zaice dashi. Domin dashi da shi ai sun san saki ne da babu kome a tsakaninsu. Ha?i?a yaga Wimuwa da gushewar tunani tattare da Babangidan.
Yau ga ranar da yake yawan tunatar da Sabuwa zuwanta tazo. Murmushi yayi yace.
"Bakin al?alami ya riga daya bushe. Hala baka san ?arfi da zafin shari'a bane ko?
To ka sani in ma sabida uwarka kake yi Babba ta bar gidana kenan har abada.
Kasan har saida na rabu da'ita na samu nutsuwa kuwa? Kai yaro tashi ka kama gabanka kada ka sake zuwanmun da irin waWannan yashasshun zantukan. Inma turoka akayi ga amsa ka samar in kayi wasa ?ar gaisuwar taka da nake amsawa sai

20 / 25