Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   22 / 25

63K to 66K   out of 72.9K words

huWu harda ?ar budurwa" id??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????anu ta zare tace.
"Yanzu a hakan da wannan jikin naki me kyau har budurwa gareki? Masha Allah gaskiya kin more jiki. Nima bazawarace mai yara uku amman ?ananune. Butulci da tozarcin Wa namiji ne ya fito dani daga gidan aurena na tsallake na bar yarana. Duk da iyayena sun tsaya mun amman al'ummar gari ban tsira daga maganganunsu ba. Cewa suke yi wai aikina na zaSa akan auren kuma wallahi ba haka bane Sabuwa. Toh duk da dai hakan gashi wani dai auren dole zan sake yi. Inata adda'ar Allah yasa a karo na biyu a dace."
Hmm to ameen Sakina ai mu dai mata muna ganin rayuwa. Ni kin ganni sai jibi zan gama iddar ma. Saina nutsu kafin na soma tunanin wani auren duk da ni mazan duk sun fice mun a kaina. Kuma sai in dinga ganinsu a cikin riga iri Waya"
Dariya tayi tace.
"Wallahi nima hakan nake gani. Amman fa hakan na da nasaba ne da wahalar da muka sha. Ni dai nayi istikara zuchiyata kuma ta samu nutsuwa wallahi Sabuwa ko bacci bana yi sosai ina kai kukana wajen Allah akan wannan auren da zanyi na biyu in babu alkhairi duk yadda nakai da son inyi Allah kar ya bani damar yi"
Mun jima muna ta surutu kafin dai na gabatar da Sallah itama tayi tata sallar.
Da yamma list Uzairu zuchiyata da Sagagi suka Waukemu suka zagaya garin Kano damu sosai gaskiya kano tana da kyau sosai gasu da wuraren buWe idanu da sha?atawa sosai har siyayya muka yi naga Uzairu zuchiyata sai facaka da kuWi yake yi. Har kantin ?an gayun maza muka rakashi ya sassai suturu masu kyau da tsada sosai abun yaita bani mamaki dai.
Nima ya sai mun dogayen riguna biyu masu kyau da takalmi.
Washegari bayan mun karSi paspo Winmu Sasagi da Sakina suka kaimu tasha har saida motarmu ta cika kafin suka tafi. Mun tsayar da al?awarin in sha ALLAH zan zo bikin Sakina dani za'ayi komai daya dace munyi musayar lamba ma. Hajiyarsu ta bayar da dan?areriyar atampa tace a kaima Rakiya turare kuma a bawa Maigogul.
Wai ni Uzairu zuchiyata a ina kasan su Sasagi haka ni naga ba zuwa Kano kake yi ba?"
Hararata yayi yace.
"Kaji mun yarinya fa. Au in zan zo Kano. Zaunar dake zanyi in baki labari kenan. Tunda ni gantalinku in zaku je kuna bani labarine. Ina da abokai a kab garuwan arewa a kudu ne kawai bani da aboki. Adam a zango ma abokinane"
Dariya kawai nayi mishi.
Wai Uzairu zuchiyata kaima kirista kenan zaka aura kamar yadda Sama ya auri matarshi? Kuma da gaske ita wannan Felisha Win take sonka bata da wata manufa a kanka?"
"Wallahi bata da wata manufa yo Lolo inma tana da wata manufar zadai muyi aure. Ta ri?e manufarta nima in ri?e nawa. Da kike ganina ni kaina ina da manufar auren nata. In kin lura ai ba budurwa bace ta taSa yin aure a baya suka rabu da mijin a shekaru zata yi Rahama kinga kuwa ai ba sa'ar aurena bace. Wallahi lolo rayuwar cikin gidanmu abun dubawace shin mu haka zamu ?are ne? Kinsan Allah shi yasa kawai nayi amfani da damata kawai. Kuma Felisha tace zata mayar dani makaranta ko da iya karatun na tsira ai na gode. Balle inna tafi na tafi kenan"
Haka dai mukaita tattaunawa har muka iso Dutse. A bakin tasha ina tsaye zan sai lemo da Ayaba sai muka ga Sama yana tu?a wulbaro.
Uzairu zuchiyata kaga can Sama"
Ai kafinma in rufe baki Uzairu zuchiyata ya shiga kiran sunanshi. ?arasowa yayi.
"Ku kuma me kukeyi anan na ganku da jaka tafiya zaku yi ne?"
Hmmm Sama kenan. Baka ko le?owa gida kama mance damu sai dai matarka da'ita aketa komai. Gaza shima matarshi ta gudu ga ciki a jikinta. Matarka shekaran jiyannan da tazo bikin Adama take faWa mana kana kudu wai neman kuWi ashe a wannan kudun kake"
Uzairu zuchiyata yace..
"Dama duk guje_gujennan ka dena kayi dakonka ka koma gida kayi kwanciyarka a gado ai yafi maka kwanan tashar. Duk da dai a tashar kai kam ka girma dole kafi gane hakan. Bijeka wallahi baka da wata maraba da majinuni. Lolo muje kinji"
Sama ya dubemu yace.
"Kada ku sake ku faWa mata kun ganni. Inna tara abinda zan tara kafin haihuwarta zan koma. Duk da wallahi ban tara ko sisi ba kuWin ana abinci da haya?i kawai yake ?arewa"
Nan mu dai muka barshi yanata surutai harda ashariya fa kamar haukacewa ma yayi wallahi ni ko saina Wauki damuwar duniya na Waurama kaina Uzairu zuchiyata kuwa ko a gyalenshi sai harkokin gabanshi yake yi. Niko muna shiga gida da zancan naso in tari Rakiya sai muka ga Gaza a zaune a tsakar gida yana cin abinci a roba ya rame duk ta tara suma.
"Kaga Sabuwa da Uzairu Zuchiyata. Eh ai naji kuna cikin alkhairi dumu_dumu kai Uzairu zuchiyata ka samu mata eh a Canada. To in Allah yayi tafiyar taku muma ?ila eh silar mu auri turawan canne yasa. Kema Lolo ina miki fatan eh wani baturen yace zai aureki Allah kuwa. Gashi na dawo na tarar eh Adama anyi aure. Allah ni mamakina ma eh ya akayi su Sadiya wai basu shiga ba eh sai Adama guzuma. Gashi wai Madamcy ta tafi nazo na tarar tabar Wakin sunnah. Zata eh dawo Amman munyi waya da maWaurin auren eh namu"
Wallahi tun muna gane me yake cewa mu dai har muka dena fahimtarshi a fahimtata shima kamar matsala ya samu fa. Ya shiga mana labarin firsina. Ni dai zama nayi ina wuce gajiyata. Uzairu zuchiyata yana zaune a turmi yana cin ayaba yace.
"Ai gara ta dawo tunda kaima ka dawo tazo ta haihu. Nima dai na kusa shiga daga cikinnan Wan Babannan da muke ji ana cema abokanmu muma ace mana"
Uzairu zuchiyata Wayarka fa aketa kira"
Dariya yayi yace.
"Ke rabu da ?an wahala. Ni wallahi Felisha tana aurena sim zan sake. Kinsan turawa da kishi yanzu saita yanki jiki ta faWi ta mutu. Ko tayi kukan kura ta kasheni.
Ko ta rataye kanta Dama itace zata mutum da sau?i kinga na gaji dukiyarta"
Dariya muka yi harda Gaza shima.
"Bari in eh yi wanka inje inyi aski kafin Madamcy ta dawo. Rakiya ta tafi kayi nayi Hauwa kuma wai Layuza ta haihu jiya ma a gidanta ta kwana."
Baki na taSe kawai mukai zamanmu a tsakar gida.
Da faWa Rakiya ta shigo da tarkace cikin ?aton Buhu a kanta. Tanata zage zage har ta dire.
"Au kun dawo ne?"
Mun dawo Rakiya. ?an biki basu dawo bane?"
Zama tayi a kusa dani tace.
"Hmmm basu dawo ba Lolo sai anjima nake ga ko yamma. Ke Lolo jiya dai da daddare Adama sai da ta lakaWama uwargidanta duka"
Salati muka saka ni da Uzairu Zuchiyata Rakiya kuma ta zuba tagumi tana girgiza kai kawai.
"Dama an shirya hakanne dan a gano wace irice Adaman ita kuma maimakon ta kwantar da kanta ta tura musu aniyarsu saita kasa daurewa ta biyema su Labbai har abinda zai faru ya faru. Allah dai ya ta?aita kowa laifin uwargidan yake gani"
Kai kawai na girgiza na shura mata tsarabar kayan marmari dana yo musu na mi?e.
Ni kam zanje in watsa ruwa in kwanta in huta. Ashe Layuza ta haihu kuma?"
Na faWa ina taSe bakina.
"Ta haihu ranar da kuka tafi Wanta namiji. Hauwa ma tana can ta tare. Sai kuka ga Gaza shima ranar da kuka tafi kwatsam su Adama sun kama hanya sai gashi uwa an jefoshi. Masu Waure musu ?un?uru sunsa an sakoshi ba ana shirin doka gangar siyasa ba. Hmm itama matar tashi tana hanya yau zata dawo"
Tana cikin wannan labarin Gaza ya fito daga Wakinshi ya nufo Rakiya.
"Ga Wan madubi in Madamcy tazo ki bata. Wannan dubu biyun ki bata na cefane dan ba dawowa zan yi da wuri ba ki faWa mata zanyi dare"
Rakiya tasa hannu ta karba yana fita nabi bayanshi nayi shigewata gidanmu. BuWe ?ofar nayi na jefa jakata na zari bokiti na ja ruwa a rijiya nayi wanka fes kafin na shiga Waki.
Ai banci ta bacci ba, ko ina kaca kaca saida na share awa guda ina gyare gyare kafin na samu dama na kwanta bacci yayi awon gaba dani. Cikin baccin wayar Khalid ta tasheni. Idanuna a lumshe na Waga wayar
Hello ranka shi daWe.
"Mitsiyaciyya la'ananniya tambaWaWWiya kawai.
Ai babu shiri na wattsake nice harda mi?ewa zaune zumbur.
Matar Khalid ta zageni ta zageni yadda take so.
"Kece Sabuwa wacce ta hana mijina sukuni kika hana ya dinga kwanciyar aure dani ko? Mitsiyaciya la'aninniya ai an bani labarin har gidana ya taSa kawoki. Sabuwa duk ranar da mukai ido huWu dake to wallahi ki kuka da kanki dan sai nayi miki abinda baki zata ba. Shegiya karuwa mai bin mazan mutane"
Shiru nayi naita tunanuka masu yawa. Jikina yayi wani irin sanyi. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke ina shirin zan sakko akan gadon in yi alwala akaci gaba da kiran wayata da lambar Khalid ni dai ban Wauka ba alwala nayi nayi sallar la'asar na kulle Wakin na nufi gidansu Rakiya.
Ina shiga na tarar da madamcy ta dawo tana girki a gaban Wakinta. Dariya tayi data ganni, nima nayi mata dariya.
Wato kinji masoyin naki na hannun ?arfen ya dawo shine har kin dawo. Wannan soyayya dame tayi kama"
Dariya muka saka duka harda Rakiya da take shanya. Su Labbai ne suka yo sallama suka shigo kwararam kwararam.
"Ya na ganku haka babu komai a hannun kowa?"
"Ai Rakiya ke dai bamu waje kawai. Madamcy kin dawo kenan?"
Cewar Labbai data zube a tabarma. Nan duk muka baje akaita hira ana mayar da zance. Suna bamu labarin faWan da akayi. Muma muka basu labarin abinda ya faru da basanan. Mune har magriba muna gidan. Matar sama ta mi?e tace.
"Ni kam zan tafi gida Rakiya sai wani lokacin kuma"
Binta muka yi ni da Labbai zamu rakata anan na labarta mata inda zata je taga mijinta yana gari babu inda yaje."
Washegari saiga Khalid yazo mun a kiWime fur na?i saurarenshi na faWa mishi ya fita a rayuwata bazan taSa aurenshi ba. Tun yana magiyar harya hakura tun yana kiran wayata yana samu harma na kulle layin nashi ta yadda koya kirani baya samuna, tun yana zuwa ?ofar gidanmu ya turo yaro, wallahi har ya soma shigowa kai tsaye. Sau biyu yana dur?usawa akan guiwowinshi akan yin yi mishi rai, na biyun har hawaye yayi mun yaita mun rantsuwar zai zauna dani duk rintsi ni kuma na?i fur Allah.
Gaga_gaga haka lamura sukaita tafiya kwanaki nata tafiya har kamar wasa yau saura kwana biyu tafiyarmu canada mun gama shirya komai tsab akwatunanmu sababbi mun zuba duk abinda muke bu?ata lokaci kawai muke jira gobe zamu wuce Kano. Daga kano zamu shiga jirgi zuwa Lagos ta can jirginnu zai tashi da izinin Allah

?AR SHUWA:.
"Mama wannan mutane haka dan?am anya kuwa zamu tsaya? Suna fa nace zanje kinsan halin dangin miji yanzu sai su iya faWama Babangida banzo da wuri ba"
Hararata Mama tayi tace.
"To saime su faWa mishin mana. Ke da kike neman yadda zaki kafu da kyau a gidan kuma. Ai ba'a bori da sanyin jiki ni naso ma in kaiki Maiduguri ne Wungurungum ayi a gama. To mijinki baya barin tafiya ke kuma kina tsoron kada ya sakoki. Ina mamakin irin son da kike yima mijinnan naki shi ba kuWine dashi irin na da ba balle kice
Saifa kin tashi tsaye zaki iya karSan ?ancinki"
?ar Shuwa tace.
"Wallahi hakane Mama kinsan amaryar da ya kawo itama tazo da nata salon iskancin duk tabi ta tsaneni kofa abincina bata ci shi kuma ya Waure mata ?un?uru baya cewa uffan sai dai duk ranar girkina tayi nata"
Mama tayi tsaki tace.
"Ai saiki samu hujjar da zaki saka borin cewar tunda abun hakane a raba girki ko wacce ta dinga yin nata. Dama yanzu wa yake wani yayin girki da kishiya ai kowa yaci nashi gudun kada a barbaWa maka abinda zai zo ya halaka rayuwarka"
Zaman wata matashiya da ba zata haure shekarun ?ar Shuwan bane yasa suka tsayar da hirar tasu.
"Akwai mai waje fa baiwar Allah "
?ar Shuwa ta faWa ma wannan matar. Sai tayi murmushi tace.
"Nice mai wajen Yar aikinace nasa tazo ta kama mun layi saida na tashi daga bacci shine nazo"
Kallonta dukka suka shiga yi. Da gani matar mai kuWin gaske ne dan komai na jikinta na kuWine gata da fara'a. Haka kurum ?ar Shuwa taji wannan matar tayi mata wani bala'in kwarjinan da bata ko son dena kallonta.
Ita kuma idan suka haWa idanu sai tayi mata murmushi.
Tunda dai suka zauna har azahar basu samu shiga ba saura mutum biyu a gabansu damma sau?inta bibbiyu ake shiga.
Wannan matar ce ta dafa kafaWar ?ar Shuwa tace.
"Ko zamu je mota muci abinci kafin layi yazo kanmu Mama ta jire mana layin?"
Tayi maganar tamkar tana magana da saurayinta. Mama tace.
"Kuje mana in layi yazo na kiraku"
?ar Shuwa ta mi?e tana murmushi tabi bayanta sukaita ratsa taron mata har suka zo wajen da manyan matan da suke zuwa wajen bokan suke ajjiye motocinsu. Wannan mata ta buWe bayan ?atuwar motarta fara.
"Bismillah ki shiga ta waccan ?ofar ko?"
?ar Shuwa ta zagaya ta shiga suka zauna tare a gidan baya. Basket Win abincin yana kujerar tsakiya. Wannan mata ta buWe lafiyayyar miyar ganyen da ?amshinta ya mamaye cikin motar. Da tuwon shinkafan daya tu?u.
"Guda nawa zaki ci?"
Ta faWa tana rausaya idanu"
"Biyu zaki saka mun ya isheni"
Murmushi kawai tayi ta saka mata ta sa mata colali itama ta saka nata. Motar tayi tsit baka jin komai sai ?aran cokali kawai, gashi ta kunna musu motar ac sai ratsasu take yi.
Irin rayuwar da ?ar Shuwa ta daWe tana burin kasancewa kenan. Kamar tana karantar zuchiyarta sai ji tayi tace.
"Macce tana iya zama duk abinda take son ta zama sai dai in taso ta damkwafe a waje Waya. Kin saba zuwa nanne dama?"
Ta ?arashe maganar da tambaya ga idanunta masu kwarjini ta zuba ma ?ar Shuwa.
"Yaune zuwana nan wajen na farko. Mijina nake son mallaka sai kishiyoyina da nake son a saisaitama zama, da kuma tsohuwar matar mijina da yake son dawo da'ita. Kefa kishiyar ko mijin kika kawo?"
Dariya suka yi duka.
"Ni abinda ya kawo ni ma duk ba wannan bane. Kinsan duniya cike take da abubbuwan ban mamaki. Aini namiji bana mishi kallon ishasshe balle har in kawo shi wajen malami balle kuma kishiya"
?ar Shuwa tace.
"To hala akan kasuwanci ne ko?"
"Ashe kin gane in banda abunki ana ta kuWi wa yake ta Wa namijin da yanzu zaka iya sakinshi ka auro duk wanda kake so in kana ganin da takura" ?ar Shuwa sai taji matar ta kuma burgeta. ?wan?wasa ?ofar motar da aka shiga yine yasa suka juya.
"Kinga Mama ta biyo mu ?ila layinne yazo kanmu"
?ar Shuwa ta Salle murfin motar ta fita dama ta gama cin abincin. Wannan baiwar Allah kuma ta fito da kula ?arama a hannunta ta mi?a ma Mama.
"Ga naki Mama dama nace in muka gama kema sai a kawo miki naki"
Mama ta ?arba tana godiya.
"Ga ?ata ko zaku yi ?awance tunda naga kamar kin fita wayewa. Kin ganta mijine yake yadda yaso da'ita kishiyoyinma ba ?yaleta suka yi ba. Ni auren ma naso in kashe to mijin nata irin almajirannanne ya kafeta a gidan bata ko son ayi batun rabuwa. Kyau iya kyau kin ganta dai tubarkallah mijin nata karayar arzikice ta sameshi yanzu ticha ne fa."
Baki ta taSe.
"Ticha fa Mama. Yanzu kamarki mijinki ticha ne? No nasan yadda zanyi Mama. Mu dai jenku"
Nan suka rankaya suka koma waWanda suke gabansu su biyunnan suna ciki sai sun fito zasu shiga Suna fitowa suka shiga dama bibbiyu ake shiga. Ita wannan matar godiya kawai taje yima bokan ta ?ara bashi kuWi masu yawa duk na godiya.
"Ku kuma meke tafe daku. Ke ki dena wannan kalle kallen kar kije ki makance. Mijinki kuma ba zaki iya mallakarshi ba. Sai dai kishiyoyin naki. Sabuwa kuma babu kome a tsakaninta da mijinki. Yaran mijin dai zaki samu nasara a kansu amman sai kin zuba musu magani a abinci sunci da kansu zasu ro?i uban nasu suce zasu dawo wajenku sai yadda kika yi dasu"
?ar Shuwa tayi mamaki Amman ba sosai ba kasancewar ba wai yau ta saba zuwa wajen bokaye ba."
"To amman boka"
"Ke iyakar abinda zai yiwu na faWa miki yarinya duk ma inda kika je sai dai suci kuWinki Babangida ba zaki iya mallakarshi ba. Kuma bazai taSa dena son uwar Ya?anshi ba. Sai dai fa ba zasu sake zaman aure ba."
?ullin maganine ya faWo daga sama guda biyu Waya a ?unshe a jar fata Waya a ?unshe a ba?ar fata.
"Wannan jan maganin shi zaki barbaWama kishiyoyinki a ?ofar Wakinsu su taka Muddin suka taka zasu biki zasu miki biyayya tamkar ke kika haliccesu. Wannan kuma yaran mijin naki zaki sama a abinci suma in suka ci zaki samu duk abinda kike so daga garesu. Sai dai akwai wani haske mai gauraye da duhu da yake tunkaroki sai kinyi a hankali. Na hangi tashin hankali, da ruWani, na hangi nadama, da dana sani. Amman akwai dukiya, Waukaka, farin jini duk a cikin lamarin"
Kan su ?ar Shuwa ya Waure sosai.
Mama taso jin ?arin bayani amman ya Waga mata hannu dole taja bakinta tayi shiru.
KuWinshi ya faWa Mama ta kunce bakin zaninta zata ?irgo.
"A_a Mama bari in bayar ai mun zama Waya"
KuWin ta ?irgo ha da ?ari ta bashi suka fito tare. Ta nemi ta rage musu hanya ai kuwa babu musu suka shiga.
Ai suna kama hanya aka Salle da wani irin ruwa mai cike da iska, ga garin yayi shegen duhu sosai. Sai samun gefen titi suka yi suka tsayar da motar dan ko gabansu basa iya gani tsabar yadda ruwan yayi ?arfi.
"Baiwar Allah kinga wata ?udurar Ubangiji ko. Da ba dan ke ba da ruwannan haka zai taremu a hanya. Nace wai me sunanki ne kuma a wacce unguwar kike ne a Dutse?"
Mama ta ?arashe maganar tana mai dariya. Itama dariyar tayi.
"Sunana Samirah amman Mama ba'a Dutse nake ba ina cikin jigawa ne cikin garin Bamaina anan nake"
?ar Shuwa kuwa hankalinta ba ?aramin tashi yayi ba tana dai zaunene tana tunanin wacce ?aryar zata yi in taje gidan sunan da tun safe ta fita zata je. Ga kishiyoyinta suna can dole ma su sanar ma Babangida lokacin da taje gidan sunan ko dan gulma.

22 / 25