Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   4 / 25

9K to 12K   out of 72.9K words

malam wannan lamarin n"
Hannu ya Waga mishi dole yayi shiru. Manga ma yaso yin magana amman shima an tsayar dashi. Dubanshi ya mayar wajen Babangida wanda yake ta zare idanu tamkar mazarin tsire.
Ya jima yana ?are mishi kallo kafin ya girgiza kai.
"Kai Babangida. Kasan wannan yarinyar? Ka Wago kai ka kalleta da kyau ka buWe bakinka kowa na ji"
Babangida da ?yar ya iya Wagowa ya dubeni. Idanunshi tab da ruwan ?walla gabaki Waya zufa ta ji?a mishi fuskarshi.
"Ka shaidata?"
Baba Malam ya sake jefo mishi tambayar"
"E nasanta"
Idanu Baba Malam ya runtse tare da jan wawuyar ajjiyar zuchiya ya karanto wasu addu'o'i kafin ya buWe idanunshi kanshi a ?asa yace."
"Kenan duka abinda tace gaskiya ne ko?" Yayi maganar muryarshi na rawa.
Malama Babba tayi carab tace.
"Ai wannan ko a mafarki bazai taSa zama gaskiya ba. WaWannan mutanen kawai sun zo ne domin su ci mutuncinmu su zubar mana da darajar gidanmu, amman in ba haka ba yaushe Babana zai iya aikata wannan aika....."
Idanu Baba Malam ya zuba mata. Kaifin idanunshi da rashin Waukan warginshi yasa tayi shiru. A hakanma daurewa tayi furta abinda ?ila zai zama kariya, ko Waura ma Babangida magana a bakinshi.
"Kar ka bari in sake magana. Kada ka sake kayi mun ?arya. Duk da mazinaci babu abinda bazai iyayi ba, tunda har baiji nauyin Ubangijinshi ba ni kuma waye"
Babangida na share zufa yace.
"Ba cikina bane wallahi "
Wani kallo Baba Malam yayi mishi"
"To cikin waye? Muna jinka bamu labari"
Kawu Manga yace.
"Yaya duk wannan tashin tashinar yafa kamata ace an barta. Batun tone tone baima taso ba. Babangida dai ya riga da ya jajiSo mana abun kunyar da zaita yawo kan haula, abin kunyar da har abada bazai taSa goguwaba, kuma ya rasa yarinyar da zaibi sai ?ar daba tatacciyar maras kunya. Ha?i?a girma da darajar gidannan ta zube"
Kai Baba Malam yaita girgizawa.
"Babangida kayi mu'amala da yarinyarnan ko bakai ba?"
Da mugun sauri ya Wago kanshi hannunshi a saman bakinshi. Da halama tambayar ta matu?ar gigitashi kuma ta matu?ar yi mishi girma.
Amman gudun kada ya hasala Baba Malam dole haka ya runtse idanunshi muryarshi na rawa yace.
"Na na na na yi?
Da gudu Malama Babba ta shige gida.
"Shikenan tashi kaje. Wawo, Bashiru, Manga duk kuje na sallameku zan gana da iyayen Sabuwa "
Ba dan rai yaso ba, sai dan biyayya da rashin yin jajayya da iyaye yasa duk suka bi umarninshi.
Bayan sun shige Baba Malam yace.
"Maigogul yanzu me kuke so ayi? Sabuwa zata koma gida tare da kune zamu Wauki nauyin cinta, shanta, suturarta, kulawa da lafiyarta har Allah yasa ta sauka lafiya kafin mu Waura dana shayarwa?"
"A_a a gabanku Sabuwa zata zauna. Kasan Allah duk barikancin yarana babu wacce ta taSa haihuwar shege a gabana. Ba kuma za'a soma akan Sabuwa ba. Malam Baba ko? Na fahimci kai babban malamine rufin asirinka dole kake nema. Ni daka ganni taceccen kawaline abun kunya gaba na bashi ba baya ba. Tunda kai kake neman rufin asiri da rashin zubewar daraja babban rufin asirinka shine ri?e Sabuwa a gidanka ka haWata aure da Wanka kaga shikenan sai asiri ya rufu. Har abinda za'a haifa shima anyi mishi sutura. Amman fa shawarace kyauta muddin kana son in tafi da'ita to zan tafi da'itamman a cikin ?waryar garinnan sai kab sun san waye uban cikinnan. Ai zancan gaskiya ne saina fallasa maka asirinka uban kowa sai yasan ka haifi baragurbi "
Baba Malam ya ja numfashi yace.
"Shikenan Allah ya rufa mana asiri baki Waya. Sabuwa zata zauna kamar yadda aka bu?ata.
Shikenan ko?"
Cicib yace.
"Ciki lafiya baka lafiya. Maigogul tashi maza muje kasan su Lantana suna Hotel suna jiranmu zamu kaisu Ges house din Mai nasara. Da gayya yayi wannan maganar domin Baba Malam ya san da gaske su kawalaine."
Mi?ewa suka yi sukai ficewarsu ni kuma na bisu da idanu sama da ?asa Allah bai bani ikon nayi musu ko na tanka ba. Nima naji daWin hakan ta wani Sangaren ko dan in cunkusama Babangida ba?in cikin da abadan bazai mance dani ba. Ta wani Sangaren kuma zuchiyata cike take da taraddadin abinda zai je yazo.
"Ke tashi muje ciki"
Mi?ewa nayi ina biye dashi har zuwa cikin gidan.
Ganinmu yasa mazan gidan duk suka daddare kowa ya nemi hanyar waje.
A ?ofar Wakin Malama Babba yayi sallama ya shiga nima nabi bayanshi.
Babangida yana Wakin ya ri?e ?afafuwan mahaifiyarshi yana bata ha?uri ita kuma ta haWe kanta da guiwarta tana sharSar kuka.
Jin shigowar Baba Malam yasa duk suka juyo a firgice. Ganina yafi furgitasu fiye da ganin shi a toh.
"Tashi ka fitar mun a gida yanzunnan, mutumin banza mutumin hofi.
Da mugun sauri Babangida ya fice har yana buga kanshi a ?ofar fita.
"Ke kuma ki zauna tare da Surukarki. Sannan ki buWe kunnanki da kyau ki jini. Ba'a yawo a gidana, ba'a saka ?ananun kaya, ba'a shaye_shaye, ba'a harkar dabanci. Wannan wu?ar dake soke a jikinki ki mi?o mun ita yanzunnan"
A_a nifa gaskiya ba zaka wani tusani a gaba da irin wannan faWan ba gaskiya. Dan wallahi ko a gida ba'a haka dani"
Wata tsawa naji daga kaina.
MRS BUKHARI "

Hmm abun ba'a cewa komai sai dai muce Allah yasa mu dace Ameen
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ac_t



IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA HU?U


INA MI?A SA?ON GAISUWA A GAREKU MASOYANA NA FA?IN DUK DUNIYA.
HA?I?A INA ALFAHARI DAKU SON SO=???

Ina godiya ga Allah daya bani damar rubuta muku wannan littafi mai cike da Wumbun darasi.
Wannan littafin ya haWani da manyan matan da zatona bai zaci ko kusa dasu zan iya zuwa ba. Amman sai gashi sanadin rubutu Allah ya haWamu
Hajiyoyi son so.

LABBAI TACE TANA GAISHE DA ?AN ?AKIN SHARSHI SON SO=???


"Kul kika sake buWe bakin ki kice zaki yima mahaifinmu rashin kunya. Duk fitsararki ki tabbatar kin ajjiyeta zuwa ranar da Allah zaisa ki bar gidannan. Bar ganin Babangida ya zubar da mutuncinshi a idanunku mu masu mutuncine. Kuma ko banza ya fiki da tarbiyya daga ke har uban naki"
Wawo ne yake faWamun waWannan maganganun cikin muryar kuka da hargagi.
Baba Malam ya dubeshi bai iya cewa uffan ba shi dai.
Ni kuwa sai hararar Wawo nake yi ina ?un?unni harda murguWa bakina.
"Sabuwa nace ki kawo wu?ar jikinki ki kuma nutsu nan ba gidanku da kika saba rayuwa babu burki bane"
Ba wai dan tsoro ba wallahi na dai ga damane na zaro wu?ar na mi?a mishi.
"Wawo karSa ka ajjiyeta a wajenka tukunna"
Yana faWan haka ya saka kai ya fice ba tare da ya kalli kowa ba.
Daidai lokacin Malama Babba ta zuba guiwoyinta a ?asa ta fashe da sabon kukan tashin hankali da ba?in ciki.
"Allah ya isa tsakaninmu daku. In sha Allah kamar yadda kuka tona mana asiri sai kunyi wula?antaccen ?arshe mai munin kwatance.
Tana kaiwa haka numfashinta ya Wauke.
Wawo dake kaina a tsaye ba shiri ya yarda wu?ar hannunshi. Ya shiga jijjigata yana ambaton sunanta.
"Wawo Lafiya meke faruwane?"
Malama ?arama wacce ta iso a gigice take tambayarshi tun kafin ta iso.
Tana shigowa taga irin halin da Malama Babba take ciki.
"Ohh wannan lamari ya kwaSe.
Bari in kirawo Ramadan maza a kaita asibiti."
Da sauri ta fita. Ni dai ina tsaye ?erere ina ?are musu kallo ko a kwalar rigata, haka maza biyu suka shigo suka kinkimeta suka fita da'ita. Na saka hannu na Wauki wu?ata na mayar da'ita ?uguna.
Sai a lokacin na nemi kujera na zauna shiru.
Na waiga ina neman soket ai kuwa na hango shi ta bayan ?ofa harda chaja a jiki na ma?ala wayata dan a mace take mus ina son kuma inyi kira.


Malam Baba:.
Da ?yar ya fito daga cikin Wakin har wani duhu yake gani.
Yana zuwa tsakar gida yaga Babangida ya tsugunna a daidai ?ofar Sarayinshi yana dakon fitowarshi.
Malama ?arama tana zaune ita da Alawiyya da Ma'u ?an matan da suka rage a gidan kenan.
Turus Baba Malam yayi ya shiga ?arema Babangida kallo yana haWiWiyar zuchiyarshi. Babangida ya rasa da irin gwalagwalan kalmonin da zai soma ba Baba Malam ha?uri dan yasan mutumme shi mai zafi, gashi da kafiya, da mugun ri?o.
Ganin tsaiwar tayi yawa yasa Malama ?arama ta ?arasa wajen.
"Malam lafiya kake tsaye baka shige ba?"
Sai lokacin yayi ajjiyar zuchiya.
"Kinga Babangida ya fitarmun a cikin gidana ya tarkata duk komatsanshi ya fitarmun a gidana. Wannan gidan ya zama shi da shi sai hange, na cireshi daga yarana na barranta kaina dashi babu ni babu shi har gaba da abada"
Kafin Malama ?arama tace wani abunne ta jiyo Wawo na ambaton sunan Malama Babba a gigice shine taje taga halin da take ciki.
Babangida na ri?e gam da ?afafuwan Baba Malam har aka fito tiri_tiri da Malama Babba.
Da idanu Babangida da Baba Malam suka bisu ko wanne da abinda ke zuchiyarshi.
Malama ?arama ta sake dawowa da sauri wajen hannunta ri?e da hijabi.
"Malam ya kamata in bisu ina neman izinin ka"
"Babu inda zaki je yaranta zasu kula da'ita. Ki aiki Alawiyya ta kirawo mun magajin malam da Jamilu, da ja'afaru suzo yanzu "
A sanyaye ta bar wajen ta aiki Alawiyya kiransu magajin malam bisa umarnin da aka bata.
Har suka zo Babangida na ri?e da ?afar Baba malam sai kuka kawai yake yi amman ya kasa furta kalma.
"Magajin malam ku kinkimi Babangida ku jefar dashi a waje. Ka haWa mishi kayanshi ka jefar mishi"
Baba malam ya faWa a raunace tamkar baya son abinda yace a aikatan. Malama ?arama tana gani tana ji bata da ikon cewa uffan. Sai korar su Alawiyya ciki tayi kawai.
Haka gardawannan suka SamSare Babangida a ?afar Baba malam da ?yar suka fice dashi.
Baba malam har da zai shiga ciki sai yayi waje shima.
To kunsan gardawa babu wanda ya fisu sha?iyanci da ?eta, suna fitowa suka cillar da Babangida kamar Yadda Baba malam ya umarcesu. Malam Baba da kanshi ya shiga shagon kwanan su Babangida su Ashiru da su Abubakar suna kwance Baba malam ya shigo ya ce.
"Waccece jakar Babangida Habu?"
Jikin Habu na rawa ya nuna mishi jakar tashi a gefen katifarshi. Baba malam ya kinkima ya fice da'ita ya cillama Babangida dake wajen da aka jefar dashi Kawu Manga yana ro?onshi akan ya tashi.
Jakar ta sauka a kusa da ?afafuwanshi yana ?o?arin juyawa ya shiga gida kawu Manga ya tareahi.
"Yaya wannan tonan sililin kuma da kanka zaka yi. Yanzu daka koreshi ina kake son yaje. Hannunka baya ruSewa ka yanke ka yar, duk lalacewar Babangida naka ne dole sunanka na ma?ale a sunanshi."
Kallonshi Baba malam yayi tare da dafa kafaWarshi.
"Manga kenan. Har tsohon Wan bariki mai shan sigari da zuwa gidan rawa, da zango ba?i a ce in an koreshi ina zashi? Ga ?an mata nan birjik a bariki irinsu Babangida suke nema. Tonan silili kuma da kake faWe har ya wuce wanda iyayen yarinyar da yaima ciki sukai mana Wazu? Yarinyar fa tana cikin gidana damu da ita mun haWu har abada ko mun?i ko munso tarihi bai isa ya goge wannan lamarin ba"
Hawayene suka zubo a guraben idanun Baba malam lamarin daya gigita ?anin nashi kenan.
Sai rirri?eshi yayi ya shiga dashi ciki. Duk da yana ta cewa.
"Manga zan iya ka rabu dani tuni na amshi ?addarar ai tunda har yarinyar na amsheta zata zauna damu."
"A_a Yaya muje dai in kai ka"
Sai da ya ajjiyeshi a bakin gadonshi kana yace.
"Zan ri?e Babangida ya dawo hannuna ya zauna da su ?asimu."
Malam bai ko kulashi ba, dole ya fice.
A cikin wannan daren a cikin gidansu Babangida babu wanda ya runtsa tun daga kan yaran dake gidan, almajiran malam da akayi komai a gabansu, har zuwa waWanda suke da aure ko wanne yana kwance a gado yana tubkewa da warwarewa. Malama Babba kuma tana gadon asibiti ana mata ?arin ruwa, kukan da take ta faman yi ne yasa akai mata allurar bacci dan ta samu nutsuwa.
Sa'a da Wawo, da Ramadan ne a wajenta
Sai faman waye_waye suke yi a tsakankanin junansu. Hatta jefo Babangida da Malam Baba yasa akayi tuni labarin ya isarma dasu Sa'a.
Baba malam kuwa da ?yar malama ?arama ta dinga rarrashinshi da bashi kalma da tunasar dashi ha?uri da rungumar ?addara duk muninta kana ya sauke nannauyan ajjiyar zuchiya ya amshi abincin yacinye kamar yadda dai ta bu?ata.
Amman dai maganar bacci babu a sallayarshi ya kusan kwana ga zazzaSi mai Wan karen zafi a jikinshi da ?yar yake janyo numfashi daga huhunshi, kanshi ya Wauke akwai tulin tambayoyi daya adanasu yana jiran Babba ta bashi amsarsu.


Babangida:.
Tunda ya shiga Wakin kwanan su ?asimu yaron Kawu Manga yayi shiru akan katifa yana tunanin yadda yayi alalan gero ya kwaSe mishi a bariki. Wai yau duk mutuncin gidansu da kamalar da yake arowa ya yafa amman shine yaima wata macen ciki har asirinshi ya tonu bama a idanun iyayenshi da ?an uwanshi zallah ba. Harda almajiran Malam Baba da WaiWaikun jama'ar unguwa ?ila sun san abinda yake faruwa. Gashi sana???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?diyyar wannan lamarin ga Malama Babba can a kwance a gadon asibiti, shi kuma an koreshi a gidansu.
A tunanunshi irin ?ololuwar son da Baba malam yake yi mishi bazai taSa iya tunanin korarshi ba, duk da shi kanshi yana jin girman abinda ya aikata ya wuce misalin kwatance.
"Hmmm Sabuwa kin taSo tsuliyar dodo. Kin taSo gidan rina zan nuna miki ke ba bariki kike yi ba daga ke har iyayenku. Saina kuikuya miki akuyancin da baki taba cin karo dashi a bariki ba. Yadda kika cire ma iyayena yarda dani suke mun kallon mazinaci. Ni rayuwarki zan tarwatsa wallahi"
Duka waWannan sambatun cikin zuchiyarshi yake yi. A fili dai ajjiyar zuchiya kaWai yake saukewa.
Kawu Manga ne ya buWe ?ofar Wakin ya shigo. Babangida yana daga kwance kawai ba?in ciki da guguwar Waukar fansa na cin ?asan zuchiyarshi.
Zama yayi a bakin katifar, ya dubi ?asimu yace.
"?asimu fita waje ka bamu waje"
Cike da ladabi Ya fita. Kawu Manga yafi minti arba'in yana zazzagowama Babangida nasihu da tunatarwa ya Waura da cewa.
"Zuwa nan da ?ura ta lafa zaka ci gaba da zamanka anan. Babban abinda nake so dakai shine kaji tsoron Allah kada ka sake aikata kuskuren daka aikata. Na tabbatar shaiWanne yayi wasa da imaninka. Kaita istigifari Allah zai yafe maka. Gobe da safe kaje ka duba mahaifiyarka.
Wannan sirrin zamu yi iyakar bakin iyawarmu wajen ganin mun birneshi bai tashi ba.
Kaima saika ri?e bakinka kuma kaci gaba da walwalarka sabida kada mutane su fahimci wani abun"
Haka dai yai tayi mishi nasiha daga ?arshe Babangida yayi godiya tare da sake jaddada cewar sharrin shaiWanne kuma in sha ALLAH haka bazai sake faruwa ba"


SABUWA:.
Bayan wayata ta ?oshi da caji saina kunna ina kwance a doguwar kujera na kira ?ar Shuwa a waya bata Wauka ba. Sai zuwa can sai ga kiranta ya shigo.
"?awata sai kuma muka ji kina gidansu Babangida acan zaki zauna ki haihu. Nayi ta kiran wayarki ma a kashe.
Wai ke kinga irin rikici da tashin hankalin da Rakiya da Maigogul suka yi yau a gidannan duk akan barinki da akayi acan?
Wallahi ?awata kab unguwarmu babu wanda baisan abinda yake faruwa ba.
Rakiya taso ma tazo ta dubaki to wayarki a kashe mu kuma bamu da adireshin gidan. Yau Rakiya saida ta yar da Maigogul har ?asa Uzairu zuchiyata ne ya rungumeshi suka faWi tare duk suka kukkuje"
Ajjiyar zuchiya kawai na sauke.
Ke dai bari nima na yarda na zauna ne saboda Babangida. Sannan iyayenshi basu da kirki kinji yadda suke aibatamu yadda kika san su tun a duniya aka basu tikitin shiga aljanna. Alhalin gasu da ?aton rikakken Wan iska sun haifa a gida. Inanan kane kane a Wakin uwarsa, ita kuma ranga_ranga aka wuce da'ita asibiti."
Dariya muka saka dukkanmu, mun jima muna hira sai daga ?arshene na bata adireshin gidan dan tace gobe zata zo da yamma zamu fita.
Ina ajjiye wayar Alawiyya ta shigo da sallamarta.
"Dama Malama ce tace inzo in kai ki Wakinmu ki kwana acan"
Wani kallo na watsa mata tare da cewa hmm kafin nace.
Ke kuma daga ina? Ai naga Babanku ne ya kawo ni, in dai so ake in koma wani Wakin sai dai yazo ya faWa mun"
"Ke ki kama kanki wallahi. Baba malam ne zai taso da kanshi yazo inda kike? Ke in ma banda ?addara yaushe zaki shigo ko zauren gidanmu balle har ki yi kane_kane a cikin Wakin Sunnah "
Dariyar manna hauka kawai nayi mata.
Dole data gaji da tsayuwarta ta fice fuu nabi banza da harara.
Inata kwance ni ba bacci ba, ni ba abokin hira ba. Sai naji ina kewar gidanmu.
Da ina gida da ana can ana zuba cabta.
Ko kuma muna Club muna jijjigewa, ko kuma muna kwance dai.
Murmushi nayi tare da shafa cikina
Da tunane tunane bacci yayi awon gaba dani
Asubar fari ko kiran sallah ba'aiba naji ana tashina har ana dukan kafaWata.
Ina buWe idanu naga mata a kaina.
"Wai dana turo Alawiyya cewar ki bita kuje Wakinsu ashe baki je ba anan kika kwanta?"
Banza nayi da'ita.
Inaji ta kwaWa kiran Alawiyya tazo da sauri ta shiga tuhumarta. Ita kuma ta mayar mata da yadda nace.
"Uhm Lallai Babangida ya Webo mana abinda yafi ?arfinmu. Ke yarinya kibi duniya a hankali. Ke abinda ke cikinki ma kaWai bai isheki yasa kin rusuna ba?
Taso to muje ki bita kiyi alwala kiyi Sallah a Wakinsu acan zaki ci gaba da zama"
Har zanyi raddi sai kawai na fasa.
Nabi Alawiyya ta nuna mun banWaki dai.
Nayi duk abinda zanyi na shiga Wakin duk su biyun Sallah suke yi.
Bakin karifarsu na hau na zauna ina ?arema Wakin kallo. Harda sib suke da'ita.
Mu kam ina iyayenmu ma suka samu kamar haka balle kuma mu. Ji waje ko ina tas.
"Ga hijabi da goduwar riga kiyi Sallah"
Na jiyo muryar Alawiyya a kaina.
Ta idar har ta tashi ta bani waje.
Hijabin dai na saka banko kalli doguwar rigar ba na tayar da Sallah. Kafin in idar har sun kwashi littattafai sun fice.
Niko ina idarwa na haye katifa na baje harda Wora kai a filo gida babu.
Bani na tashi ba sai tara da rabi na safe.
Wayata na jawo naga na rasa kira kusan sau ashirin ( missed calls)
Kafinma in kai ga dubawa wayar ta sake ruri, sai dai kafin in Wauka aka buWe labulen Wakin Sa'a ce tana tsaye tana ?are mun kallo.
"Allah wadaran wannan abun kunyar. Sai kace wasu tubabbu ace budurwa ta dawo gidan saurayinta da zama

4 / 25