Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Love

Chapter   15 / 25

42K to 45K   out of 72.9K words

a hita yanzu."
Ficewa tayi ta jona ruwan a ?aramar robar fenti tana tsaye tana jiran ruwan tana magana a zuchiyarta ko kuma ince sa?a mugun sa?a.
Biyota yayi ya dubeta suka haWa idanu tayi kwalliya da ?ananun kaya tayi kyau sai ?amshin humra take yi.
"Ki haWa nawa abincin a kula bari in samu Ramatu dan ita zata kwana dasu."
Nanma bai jira abinda zata ce ba ya shiga Wakin Ramatu ya taddata suna cin abinci ga TV suna kallo ko ina kaca_kaca ga kayan Waki har kaya amman Ramatu irin matannanne da ba ko yaushe suke gyaran daki ba. Duk randa taso gyara wa dai zata gyara komai ta ajjiye komai a muhallinshi.
Jallof Win shinkafar manja da alaiyawo suke ci da ruwansu Wan kamface a gabanta.
"Lafiya naga ka shigo Sangarena kaga kar kasa jarababbiyar matarka ta biyoka"
Murmushin takaici kawai yayi.
"Ki gama cin abincin zan kai ki asibiti zaki zauna da Malama bata da lafiya an bata gado."
Idanu ta ware amman da suka haWa idanu taga ya murtuke fuskarshi tamau bata ga fuska ba dole ta hadiye maganarta ta kora da ruwan sanyi "
Sallar isha da aka soma kirane yasa ya tashi tsaye.
"Ki tsimtsa kafin in dawo sallah sai mu wuce. Su kuma yaran ki mi?a su wajen Aisha ko ki mi?a su Wakinsu Mardiyya"
Yana faWin haka ya saka kai ya fita.
Tare suka je masallaci da su Aminu.
A cikin masallacinne yake sanar musu Mardiyya na asibiti tare da Malama.
"Amman kunci abinci.?"
Aminu yace.
"E na dafa mana farar shinkafa dama muna da miya"
"To akwai ragowar abincinne ka zuba sai a kaima ita Mardiyyan?
Kafin Aminu yayi magana ma yace ya barshi kawai tunda a gida Mardiyyan zata kwana.
Suna shigowa ya karSi abinci da filas Win ruwan zafin a cikin basket ?arami.
Tun daga tsakar gidan Ramatu ta hau mashin Win tana ri?e da basket Win abincin aminu ya buWe musu get suka fita.
Mardiyya na zaune ?walam ta hango Babansu da yadikkonsu ajjiyar zuchiya ta sauke.
"Mardiyya yaya jikin na Malama ta farka kuwa?"
"Ta farka Baba tana ta kuka tana kiran Ummi ni kuma wayata babu kati ban kira mata Ummin ba. Likita ma yace in ka dawo yana son ganinka."
"To shikenan bari naje. Ramatu bata abincin taci sai in zo mu tafi."
Ficewa yayi. Mardiyya kuma ta tusa wannan tuwo a gaba malmala Waya ?arami da nama tsoka Waya ta cinye. Ramatu kuma ta hakimce a bakin gadon jinyar sai hararar Mardiyya take yi. Sauban ne ya shigo da kaya kici_kici harda su lemu da ayaba da abinci kula guda, da ruwa katon guda.
"Baba Ramatu ina wuni ya mai jiki?"
Sauban cikin girmamawa yake gaishe da Ramatu. A gatsine ta amsa tana ?arema ledojin daya jibge a gaban Mardiyya ido. Ledar da kular take ciki ya buWe mata.
"Kici abincin kince mun yinwa kike ji ko?
Kai ta Waga mishi kafin daga bisani tace.
"Baba ma ya kawo mun tuwo naci. Sai dai tunda wannan kai ka kawo bari inci kafin mu tafi"
Abincin ta zuba a plate lafiyayyar jalof ce wacce taji Wanyen kifi. Ramatu kanta saida ta haWiye yawunta. Mardiyya na cikin ci Babangida ya shigo da sallamarshi. Sauban ya kalla ya dubi ledojin daya kawo ya kalli abincin da Mardiyya take ci. Idanunshi ya lumshe yaji wani abu na tafasa mishi ranshi.
"Baba ina wuni yaya jikin Malama?"
"Lafiya Sauban. Jikinta da sau?i za'ace. Kaine da wannan hidimar?"
Kai Sauban ya sosa tare da cewa.
"Ah ai wannan ba komai bane"
Zama Babangida yayi a farar kujera.
"Mardiyya zubo mun in Wanci kafin mu tafi"
Mrs Bukhari

#Team Babangida
#Team Sabuwa
#Team Gaza
#Team Maigogul
[8/19, 7:41 PM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA SHA UKU


Harta ciro kwano zata zuba mishi sai yace ta zuba mishi a cikin kwano da taci.
Ko data zuba mishi bai wani ci sosai ba. Ta mi?a mishi ruwa yasha sai yace.
"To Sauban mu fa tafiya zamu yi Ummansu ce zata zauna a wajenta. In kaje gidan ka gaishe da Sa'a"
Tare suka fita dashi Mardiyya ta hau mashin Win Babangida Sauban ya shiga motarshi kowanne ya nufi gida.
Saida Babangida ya jima tare da su Mardiyya a Wakinsu kafin yayi musu sai da safe ya nufi Wakin ?ar Shuwa yana murWawa yaji ta kulle Wakinta saida yaita bugu kafin tazo ta buWe mishi ya shiga.
Yana zaune a bakin gado tunani yayi mugun yi mishi yawa sai ya jiyo muryar ?ar Shuwa a kanshi.
"Aina Wauka acan dukka zaku kwana a wajen ita yarinyar shi yasa ma na kulle dakina.
"Zauna muyi magana Wake"
Fuskarshi a mugun murtuke take babu ko wasa dis a fuskarshi, sai jikinta ya mutu. Zama tayi a kusa dashi tana saurarenshi.
"Da farko inaso in tambayeki ki tabbatar kin faWa mun gaskiya in kikai mun ?arya ranki zai Saci kuma zan saSa miki"
A sanyaye tace.
"Ina saurarenka"
"Kulolinki ina suke danna lura kin dena saka mun abinci a kula. Sai yau naga wata koWaWdiyar kula a ciki kenan kika zuba mun abinci, sannan ina kika samota dan ni ban sanki da wannan kular ba naga kuma ba sabuwa bace."
Gabanta ya faWi ras da jin abinda yake tuhumarta akai. Dama tasan za'a rina shi yasa tun kafin azo hakan taso ta samu kula ta siya ko sakan ko sabuwa mai Wan rangwamen kuWi.
Ita kanta jin Ramatu ta sai kula mai tsada ya matu?ar Waga mata hankali. Gashi shima ya tare ta da maganar.
"Kulolin suna gidanmu ne da ragowar kayan wutana sabida kaga kitchen Wina babu kanta ga ?an?anta kulolina manyane ba zasu zauna a kitchen Win bane."
?ur yake kallonta.
"Sai kuma kika kasa cire mun kular da zaki dinga zuba mun abinci a ciki? Sannan har sai kin kai kuloli gidanki ga ?ar?ashin gado ga store naga tarkace ne a ciki me yasa baki ajjiye a ciki ba"
Tsuru_tsuru tayi mishi. Shi kuma bai yadda da abinda ta faWa mishi ba. Shi zarginshi siyarwa tayi tayi hidimar bikin ?anwarta dasu dan yaga ta dinka kayayyaki manya harda su takalmi da jaka. Kuma hakanne a dalilin bikinne ta harhaWa ta kaWar dasu sabida ta fita kunya dangi suna ganin tana auren mai kuWi ace an tashi bikin ?anwarta ba'aga tayi bajinta ba har ?aramin zobenta na gold saida ta siyar duk a bikin dan kawai tayi bajinta.
"Hmmm ki kira waya gobe a dawo miki da wasu kulolin na faWa miki kenan. In kin fahimta ni namijine mai son kula Webi da kanka wannan tsarinane kuma kin sani ba tun yau ba.
Magana ta biyu itace me yasa inna bada kuWin gawayi sai in dawo in same ki kina girki da risho."
"Ai Ramatu ma a rishon naga take yi"
A tsawace yace.
"Yanzu dake nake yi ba Ramatu ba. Ko so kike mu kafa teburinta a Wakinki?
Wato na fahimci rayuwar ?arya daga ke har ita kuke son yi. Bazai yiwu kuje ku jawo mun jarfa ba. Ni na rungumi ?addarata ace ku matana kun kasa Waukar ?addararku kullum ?orafinku kifi nama, ko ban bada kudin kifi ko nama ba sai in dawo in gani a girkinku alhalin nasan ba sana'a kuke yi ba. To wallahi in kuna son zamanku lafiya ya zame muku dole ku dawo cikin taitayinku.
Duk da a cikinku duk sabida kuWi kuka aureni Sabuwa ce kaWai a lokacin dana aureta ?arma ?arma kawai nake yi.
Kuma daga yau dole a haWe girki duk wacce take da miji zata yi girki na dukka gidan har da su Mardiyya"
Baki zata buWe tayi magana a zafafe ya nuna mata yatsa.
"Kimun shiru maras kunya fitsararriya kawai sai in fasa bakin ki Allah. Bar ganin nayi sanyi ki zaci zan Wauki take_ taken iskanci wallahi ?aryane. wallahi baku isa ku juya ni yadda kuke so ba wannan doka ce na kafa daga gobe ki Waura girkinki da kowa."
Yana gama wannan maganar ya haye gado yayi kwanciyarshi.
ShinfiWa ta fita falo tayi ma yara ta dawo ta juya mishi baya a gado. Cikinsu babu wanda yayi bacci sai tubkewa da warwarewa suke yi. Ita ta ?uduri niyyar gobe sassafe zata je ta kai ?aranshi wajen Malama Babba dan tayi rantsuwar ba zata taSa haWa girki da kishiya ba har taci abincin kishiya ba
Shi kuma Babangida da tunani biyu ya kwana tunani na farko na sabuwane da wannan namiji daya gansu tare. Sai kuma Malama dake gadon asibiti.
Har mafarki yayi Sabuwa ta dawo cikin rayuwarshi suna ta zuba soyayya harma sun sake samun karuwar Wiya mace mai kama da Mardiyya sak.
Farkawa yayi da asuba sai yaji zuchiyarshi ta sake yin nauyi sosai.
Yana dawowa sallar asuba sai yayi wanka ya kintsa ?ar Shuwa tana gado tana baccin asara.
"Aisha ki tashi ki dafa shayi zan siyo kayan tea"
Cikin magagi ta amsa mishi amman harya dawo bata tashi ba. Ga yara a falo sai kawai ya juna ruwa a hita ya tafasa ruwan tea ya soya musu ?wai. Ya zuba nasu Mardiyya ya cika musu jug da tea ?wansu ya zuba a kwano ya kira Aminu yazo. Daidai futowar ?ar shuwa daga Waki tana mu?a.
Da kallo tabi Babangida da Aminu da aka mi?a mishi jug. Yawu ta haWiye mu?ut bata ce uffan ba ta koma ciki. Da kanshi ya sallami yara tsab, ?an asibiti kuma ya ware musu nasu harya zuba a basket. Yana gama karyawa ya mi?e ya ajjiye mata kuWi nera dubu biyar.
"Ga kuWin cefanen rana dana dare dukka ayi da ?an asibiti"
Ficewarshi yayi baibi ta kanta ba. Itama ko a dawo lafiya bata ce mishi ba. Ta zauna tana ta tunanin ?ila lokacin rabuwarta da Babangida ne yazo dan ita bata tsara rayuwar gidan aurenta a haka ba"



SABUWA:.

Washegari

Sassafe Mardiyya tayi kiran wayar Adama take sanar mana Malama a asibiti ta kwana ba lafiya. Abunka da sha'anin ?a da uwa sai hankalina ya tashi ba shiri su Labbai suka soma girkin asibiti. Taliya da kifin gongoni suka dafa sai shayi mai kayan ?amshi ko basket bamu dashi a leda muka zuba komai.
Jikina babu ?arfi nayo wanka tas na zura doguwar rigar kanti daga cikin rigunan da Dr Kamilu ya sai munne. Labbai sai ta saka Waya doguwar rigar tawa, Adama kuma ta saka lace muka fito sai ga motar Dr Kamilu a ?ofar gidan isowarshi kenan.
Gilashin motar ya zuge yana mun murmushi nima murmushin nayi mishi. Ya ?urama Adama idanu yana Wan murmushi.
Yaya kaine sassafe haka?'
Na tambayeshi"
"Kin ganni dai dake na kwana cikin raina. Yaya Adama ina kwananku yaya Lolo da jiki?"
Nan dai suka gaggaisa.
"Dama nazo in duba jikin nata ne sannan in gaishe da su Mama'"
Gabana ya yanke ya faWi Adama tace.
"To sakko mu ?arasa gidan. Dama asibiti zamu je dubiyar ?ar gidan Lolo karamar jiya a asibiti ta kwana.
Ai kuwa ya ajjiye motarshi muka Wunguma zuwa cikin gidanmu
Shigarmu da sallama wallahi sai ji mukai an jefo bokitin roba tabb ya sauka a?irjin Dr Kamilu.
Gaza ne suke damben Allah tsine a tsakar gida shi da madamcy. Ga su Rakiya a tsakar gidan kowanne harkan gabanshi yake yi. Babu wanda ya damu da abinda su Gaza suke yi.
Hauwa na gaban murhu tana dumame, gasu Qamriyya a tsakar gidan duka. Rakiya kuma wasu jemammun kayan gado aka kawo mata tana siye. Ga Maigogul a kan turmi yana brosh. Uzairu zuchiyata yana zaune akan kujerar tsugunno yana ta aikin goge ?afarshi. Su Sadiya kowa na zazzaune babu wanda ya shiga faWan su Gaza.
Illahirin kunya ta kamani da mugun gudu Gaza ya biyo madamsy ita kuma ta nufo kanmu ai kuwa ta bangajeni sai gani a ?asa jiki dama duk ciwo ya cinyeshi. Gaza sai Wuma zagi yake tayi.
"Ke Rakiya ga ba?o munyi fa"
Cewar Maigogul daya nufo mu da sauri. Ni kuma a sanyaye Sadiya ta Waga ni na mi?e ina kaWe jikina.
"Bawan Allah kayi ha?uri ka shigo gidan ka tarar anata hatsaniya. Shaye shaye kasan babu abinda baya sawa shi yasa. Wannan rikicin tun dare ake yi da sassafe suka ci gaba da faWansu duk kamar a bige suke sun ci kai shi yasa. Yanzu da zaka goyi bayan Waya sai cibi ya zama ?ari, ?ari ya zama ?ababa shi yasa kaji munyi kurum. Labbai surikinne aka kawo shi Allah yayi kenan?
To madallah"
Da sauri ya koma da kanshi ya Wauko tabarma ya shinfiWa ya ri?o hannun Dr Kamilu suka zauna. Gaza kuwa ya kama madamcy sai dukanta yake yi sai da ya daketa son ranshi kana ya rabu da'ita yayi ficewarshi ma a gidan.
A sanyaye Dr Kamilu ya gaishe da su Rakiya da Maigogul kafin Adama ta gabatar musu dashi.
Baki Maigogul ya washe.
"Allah sarki munfa gode da Wawainiya wallahi Allah ya saka maka. Itama muna ta lallaSata ta daure ta koma Wakinta wallahi kaga ta?i shi wannan mahaukacin wan nasu daya fita ya Waure mata baya akan ba zata koma ba. ?an uwanta mata duk sun goyi da bayanta.
Kafa gansu cike da gidan duk zawarawane zaman auren ya gagaresu dama itace ta samu...
Carab Adama tace.
"Sauri muke yi Maigogul ?ar wajen Lolo ce babu lafiya zamu je asibiti mu dubota dama gaisheku yazo yayi.
"Assha to ai sai mu tafi tare. Kai Uzairu zuchiyata maza sako kaya muje asibiti. Malam Kamilu da mota kake ne?"
"E Baba da mota ai sai in sauke ku"
"To to shikenan Allahu Akbar bari in shirya ai sai mu tafi baki Waya."
Ya ?arashe yana wannan dariyar da in yayi sai inji kamar in haWiyi zuchiya in mutu.
Da sauri ya shiga Waki ya bugo kwalliya ya fito yana ta baza ?amshi yayi kyau tabbas tamkar wani minista ko Wan majalisar jaha fa haka yake ado komai nashi mai daraja ga kyau Allah ya huwace mishi idanunshi farare tar_tar gashi da suma mai laushi da furfura jefi_jefi.
Uzairu zuchiyata shima ya bugo nashi wankan dama dai jirgi Waya ne ya kwaso su yasa wani ?aton takalmi sai she?i yake yi hmmm.
"Dama nace akwai kayan abinci Yaya Adama a mota ko yara zasu shigo dashi?"
Dr Kamilu ya yi maganar yana kallon Adama.
Maigogul yayi carab yace.
"Muje kaji in kwaso in dire musu sai mu tafi"
"A_a Maigogul su Sadiya kuzo muje ku shigo da kayan. Anfa gode sosai"
Nan su Rakiya da Hauwa suka shiga godiya. Dubu goma_ goma yaba Rakiya da Hauwa. Ga ?aton buhun shinkafa da katan na taliya da mangyaWa an dire a kofar Rakiya. Mu kuma muka shige mota Maigogul yana gaba sai labarai yake ba Dr Kamilu marasa ma'ana, daga yace ?awarshi ta gari kaza, sai labarin sunje bikin ?ar gwamnan gari kaza haka dai dama salon hirarshi suke. idanuna na lumshe wasu siraran hawaye suka gangaro mun. Gashi Maigogul sai ?o?arin saka su Labbai a hirar tasu yake yi. Suma suka biye mishi sukaita hira har muka karasa asibiti.
Muna sakkowa a motar muka haWa idanu da Babangida. Dr Kamilu kuwa dama bai fito ba yace bazai shiga ba dan gudun fitinar Babangida.
Gaba muka yi ni kunya tasa na kasa tsaiwa muyi sallama ma. A guje Maigogul ya biyo bayanmu yana cusa kuWi a ajjihu bakinshi kuwa har kunne.
A cikin Wakin da Malama take muka tadda Babangida fuskarshi a mugun murtuke gashi ya shigo ya tadda Malama sai kuka take tana kiran umminta. Muna shigowa nayi saurin isa bakin gadon na zauna na rungumi diyata ina shafa bayanta. Sai tayi tsit tana ta sauke ajjiyar zuchiya ta ?an?ameni sosai yarinyar tamkar tana tsoron kada in gudu.
Ana kan gaggaisawa muka jiyo sallamar Baba Malam da Malama ?arama da Wawo sun shigo suma da abincinsu ni?i _ni?i.
Har ga Allah banso muka haWu da Dattijon ba domin bana so ya bani wani umarni in saSa mishi.
Yako nuna farin cikinshi da ganina duk da yayi mun faWa sosai akan kada in kuma tafiya ko'ina duk abinda ya dameni in garzayo in faWa mishi.
"Babangida kaida waccan ku fice ku bamu waje"
Babangida dama a takure yake da sauri ya fice. Ramatu tabi bayanshi sum_ sum_ sum.
"Maigogul gaka ga Sabuwa dama nayi niyyar zuwa gidan daga asibitinnan sai gashi mun haWu. A gaskiya ro?o dama zanyi Sabuwa ta dawo Wakinta tunda labarin ?arar data kuma shigarwa ya iso mun. Tayi ha?uri in Allah ya cika mata burinta sai ta tafi gabaki Waya. Amman yanzu ai ba daidai bane ace tana zaune a gida ba ko ba gaskiya ba?"
Maigogul yace.
"Wannan gaskiya ne ni da Rakiya munyi munyi da'ita amman ta?i komawa. Kuma tun ranar data bar gidan nata tana asibiti babu Lafiya"
Nan ya kwashe labari ya ba Malam Baba harda Worawa da cewa.
"Yaronne ma ya kawo mu asibiti yanzu yaje gida dan mu gaisa sai dai fa Babangida yazo har ?ofar gidan anyi Wauki babu daWi daga zuwa ya runtuma a wuyan wannan bawan Allah ya kamashi da kokawa akaita turzawa. Yaita rantsuwar dai bazai yadda ya saketa ba. In sha ALLAH daga nan in aka sallami yarinyar zata koma gidanta kai tsaye in yaso sai a tafi da Adama da ita Labbai Win zuwa yadda shari'ar ta kaya. Har cikin raina bana goyon bayan mutuwar auren Lolo wallahi "
Ni dai bance komai ba kuma bana jin a wannan karon zanyi ma Malam Baba biyayya nifa na baro gidan kenan.
KuWi ya Wakko masu yawa yace in ri?e a hannuna ya ba Maigogul ma harda su Adama.
A ta?aice dai kwanan malama biyar a asibiti muna jinya. Kullum Babangida yana zuwa amman ko ga miciji bama yi ma juna yayi yin?urin samun damar magana dani nice ban bashi damar ba nace mu haWu a kotu kawai. Tunda matarshi ta fice a asibitin ranar da muka je babu wacce ta sake tako ?afarta. Daga dangin Babangida matan babu wanda yazo mazan dai sun zo Sauban ma yanata hidimar kawo abinci dasu lemo da ayaba. Dr Kamilu kuma kullum sai munyi waya ya tambayi jikina.
Rana na shida aka sallamemu kuma a ranar ne zamu yi zaman kotu na farko.
Ni dai kai tsaye gida muka wuto da Malama dasu Adama duka. Sunyi juyin duniya akan in koma Wakina na?i fur. Su Sadiya ma nasa suka je suka tattaromun suturuna da duk wani abu muhimmi suka kawo mun ai kuwa Wakin dama ba girma ba duk saiya cike.
Sha Wayan rana a kotu tayi mana ni da su Adama da Rakiya Maigogul yace ba zashi wani kotu ba.
Sai gani gasu Malama Babba da Sa'a a harabar kotu sun zo suma.
Kafin mu shiga cikin kotun Dr Kamilu shi da lauyana suka ?araso. Sha Waya dot muka shiga Wakin shari'a.
Nan aka gabatar da dalilin ?arana lauyana ya zayyano

15 / 25