Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   9 / 67

24K to 27K   out of 199.9K words

ware jajayen idanunsa ya yi a kan rumaisa, a hargitse malam lawan ya ce "Yi ha?uri bari na mi?o maka".

Cikin muryar mashaya, Wan daban da ake cewa Wan kada ya ce "Ni ki ke gayawa haka?".

Fitowa ta yi zata wuce shi, ta tafi, amma ya sanya ?afarsa ya kwashe na rumaisa, a take kuwa ta faWi ?asa, manjan hannunta ya fashe, ta datse goshi.

Idan da abun da rumaisa ta tsana, bai wuce ganin jini a jikinta ba, jiki na rawa ta tashi ta kalleshi, ya kalleta ya ce "Sai na tsarge hanjinki da wu?a, na kashe banza ni zaki nemi ki zaga wata jagwal da ke"

Cikin hanzari malam lawan da sauran mutane suka fara lallaSa Wan kada suna bashi ha?uri, rumaisa ta shiga cikin shagon, ta dumbuzo ?wan da ke kan teburi, ta fito ta shiga jifan Wan kada da shi.

Rikicewa malam lawan yayi, dan yanzu aka sauke ?wan ko lissafawa ba ayi ba, ji ta yi zuciyarta na tafasa, ta juya da gudu ta tafi gida.

Aliyu na ganinta ya ?are mata kallo ya ce "Meye haka?" Cikin kuka ta kwashe komai ta gaya masa, nan da nan ransa ya Saci ya ce "Mu je" mama na banWaki tana gyaran murya, amma Aliyu ya ja rumaisa suka yi waje.

A ?ofar shagon suka tarar da Wan kada, har ya karSi sigarinsa ya fara sha, malam lawan kuma yana ta masifa, yana sai ya je gidansu rumaisa an biya shi, shi kansa Wan kada yayi alwashin sai ya kashe rumaisa, saboda wula?ancin da ta yi masa,ta din ga jifansa da ?wai.

Idan da abun da samarin gidan maman suka tsana, bai wuce taSa Wannan tilon yarinyar ba, dan haka a zafafe Aliyu ya ?arasa, yana zuwa ba tambayar ba'asi ya ci kwalar Wan kada, ya shiga kifa masa mari.

Kokawa ta kacame, ga Wan kada a buge, dan haka ya kasa wani abun arziki, Aliyu ya din ga haWa masa naushi.

Da ?yar mutane suka shiga tsakani, ana rirri?e Wan kada yana rantsuwa sai ya kashe Aliyu.

Mama kuwa a gigice ta fito daga banWaki, jin wanda rumaisa ta tsokano, dan babu wanda bai san yadda ya addabi unguwarsu ba.
Mama ta kira mai sunan baba a waya, ta ce masa duk abun da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yake ya bari ya tafi shagon malam lawan, Aliyu ya fita ba ta san mai zai aikata ba.

Aliyu kuwa ya kalli Wan kada ya ce "Jinina da na zuriyar gidanmu ya fi ?arfin mutum irinka,? duk wani hauka da iskanci da kake ji da shi a unguwar nan ?yaleka aka yi, ?anwata ta fi ?arfin wawan mutum irinka su cutar da ita"

Malam lawan ya ce "Wai Meye haka ne Aliyu, ina nan aka sace ?anwar ta ku me ku ka yi, sai yanzu zaku haddasa mana masifa a cikin unguwa"

"Wallahi malam lawan, duk shekarun da muka yi tare a unguwar nan, idan ka taSa rumaisa sai na tuSe na yi maka bugun sakwara, saceta kuma da aka yi wannan ?addararta ce, ba yadda muka iya"

Rumaisa ta ri?e hannun Aliyu ta ce "Yaya mu tafi gida"

Da ?yar rumaisa ta ri?e hannunsa, suka juya suka fara tafiya, sai dai ana sakin mai kada, ya zare wu?a ya nufi Aliyu da ita gadan-gadan yana ihu.

Ihu rumaisa ta saka ganin wu?a tsirarata, wu?a ba ta wasa ba an nufo yaya Aliyunta da ita, wanda ba da tabbacin ita aka nufo ko shi. Aliyu ya hankaWeta, ya kuma ri?e mai kada suka hau kokawa ga wu?a tsirarta.

Aliyu ya danne mai kada a ?asa, ya Wau wu?ar ya ce sai ya yankashi da ita a wurin.

Nan aka din ga kokowa da Aliyu, aka kasa ?wace wu?a.

Rumaisa ta ce "Yaya Aliyu kar ka yi kisan kai, amma dai ka yi masa dukan tsiya".

Cikin takunsa na isa da ta?ama, ya din ga ture dandazon mutane, ya ?arasa in da Aliyu yake kan mai kada ana fama da shi, ya ri?e hannun Aliyu mai wu?ar ya murWa, ya jefar da wu?ar, sannan ya Wago shi daga kan mai kada ya tsayar da shi a kan ?afafuwan sa ya Kalleshi ya ce "Meya haka? Shaye-shayen kai ma ka fara ne?" Ya kalli rumaisa ya ce "Duk saboda ke ko? Sai ku wuce mu tafi ai".

Daga kwance mai kada ya ce "Na rantse da girman Allah, idan har ina yawo kana yawo a unguwar nan, sai na kasheka na kashe matsiyaciyar yarinyar nan, na ga uban waye gatanku"

Aliyu ya sake tunzura, jijiyoyin kansa suka kumbura, mai sunan baba ya kalli mai kada ya ce "Idan kana zubar da jini a unguwar nan kai da yaranka, ana tsoronku, kar ka ratso ta gidanmu, wallahi duk wanda ka zubarwa da jini in dai Wan gidanmu ne, kaima sai na zubar da naka, ka kiyaye"
Ya ri?e rigar Aliyu, hannu Waya ya tankaWa ?eyar rumaisa zuwa gida.

Mutane wasu har da shewa, abun ya burgesu, kaf unguwar nan babu gidan da suke da haWin kai da nunawa juna soyayya kamar gidansu rumaisa.

A gigice mama ta tashi da suka shigo, ta ga jikin Aliyu duk ?asa, rumaisa kuma da fasashshen goshi, duk da ba ta zubar da jini da yawa ba.

"Mai sunan baba, maiyafaru?"

"Kar ki damu, ba abun da ya faru"

Mama ta ri?e Aliyu da yake huci ta ce "Ina fatan dai ba abun da ya sameka ko?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

Mama ta ce "Duk saboda wannan jairar yarinyar ne, da ba zata bari a zauna lafiya ba? Ina ke ina faWa da gagararren Wan daba saboda Worawa kai bala'i" Mama ta yi maganar tana ?o?arin kai mata duka, amma mai sunan baba ya tare ya ce "Ki ?yaleta please, baki ga ta ji rauni a goshi ba, ki yi ha?uri"

Mai sunan baba ya sakata a gaba, ya kai ta chemist, aka duba goshin, Allah ya taimaketa babu Winki, suka dawo gida.

Mama ta kai ?arshen ?ulewa da rumaisa yau, ta din ga yi wa ?an mazan faWa a kan biye mata wurin tare mata faWa.

Kasancewar ma?wabcin su rumaisa malam shamsu, yana cikin ?an kwamitin unguwa, shi ne mataimakin ?an ?ato da gora, yana dawowa aka sanar masa da abun da ya faru a unguwar, nan da ya ji ya samu damar rama wula?ancin da rumaisa da yayyenta suka yi masa, kai tsaye ya je ya sanar da ?an sanda abun da ya faru.

Mama har ta bar sallahun a rufe gida, ?an sanda suka yi sallama, suka ce sun zo tafiya da Aliyu.

Duk yadda aka so sasanta lamarin, abu ya gagara, ga Abubakar ya koma makaranta, Mai sunan baba da Usman suka bi bayansu, amma har wurin sha Wayan dare, ?an sanda suka ?i bayar da Aliyu, ?arshe ma suka sanar da su cewa sashin kula da manyan laifuka na bamfai zasu turasu, tun da Aliyu ya yi i?rarin kisan kai.

Haka mai sunan baba suka koma gida, jiki a sanyaye, mama ta rasa in da zata saka kanta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, tare da Wora zargin komai a kan rumaisa.

Adam kuwa bayan ya kammala cin abinci, ya tashi ya yi wa ammi sallama, ammi ta ce "Yauwwa, na ce ba" Adam ya Wan tsaya yana kallon ammi.

"Dan Allah gobe in Allah ya kaimu, tun da da wuri zaka fita, kuma ka ce zaka je gidan gona, dama unguwar su matarka ne, zan baka sa?o ka kai wa rumaisa"

Adam ya kalli Ammi ya ce "Matata kuma? Kuma ni zan kai ss?on?"

"Ban isa ba kenan?"

Ya ce "A'a tare da sunkuyar da kai"

"A yanzu kana da wata matar da ta wuce rumaisa ne? Zaka kai mata sa?o, kallonka kawai nake yi, har na je wurin turaki na dawo ba ka tambayi yaya muka yi ba, kuma ya zama dole ka din ga zuwa wurinta, saboda ta saki jiki da kai, kuma ka daina yi mata wannan muzuran"

Adam ya jinjina kai yana wasa da yastun hannunsa.

"Je ka, da safe in Allah ya kaimu kan ka wuce, ka biyo"

Bai ce komai ba ya fice.

Ayshercool.

Chat me on what's app, to subscribes yours
08081012143
*PAID BOOK NE, ? 500 NE VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA, 08081012143*



Gaba Waya ji yake duk wani girma da mutuncinsa sun zube, kamar shi ace wai zai je wurin wata ?ar yayyiyar yarinya yayi zance da ita, wai zai aureta, ko aurensa na fari aisha ta kammala deegree ya aureta, wannan shi ba ya tunanin ko primary ma ta gama.

Mama kuwa kwana ta yi ba barci, sai addu'a kawai da take yi, ji take tamkar ta rufe rumaisan da duka, dan bayan gama ?an koke-kokenta tuntsirewa ta yi ta hau bacci.
Mama ta kalleta ta girgiza kai ta ce "Allah ya shiryeki, ya ganar da ke"

Da asubar fari, bayan rumaisa ta idar salla, ta tafi Wakin su mai sunan baba ta yi sallama, suka amsa mata.
Ta le?a ta ce "Yaya usy jiya kun dawo da yaya aliyun?"

Abdallah ya ce "Wuce ki bawa mutane wuri, duk ba ke ki ka janyo ba, karfa kawai"

Mai sunan baba ya kalli Abdallah ya ce "Kar ka kuma gaya mata haka, bai dawo ba a can ya kwana, duk saboda ke, gaba idan ki ka sake, ke zan kai musu in karSo shi, dan mun fi son sa a kan ki, mara kai kawai"

Sumi-sumi ta juyo za ta fito, ta fuskanci kowa haushinta yake ji yau.

Usman ya ce "Wallahi yau da na ga malam shamsun nan a masallacin asuba, ji na yi kamar na Waga shi na wurga shi cikin kwalbati, shi ne babban munafukin da ya je ya kai wa ?an sanda"

Mai sunan baba ya ce "Ba ruwanka da shi, ku bari mu kashe wannan case Win tukuna".

Abdallah ya ce "Ni malam lawan mai shago na kusa kifawa mari, ya biyo ni wai rumaisa ta yi masa asarar ?wai cret huWu, wai in zo in biya, na ce masa sai dai mu yi kokowa ya Wiba, gaba Waya mutane fuska biyu ce da su".

Rumaisa da take tsaye tana jin su da sauri ta ce "Wallahi ko kret Waya bai yi ba, bai fi guda shida ba fa"

"Au laSe ki ke yi mana ko?" Abdallah ya faWa yana nemo abun duka.

Da gudu ta shige Wakin mama, sai dai irin kallon da maman ta yi mata, ya sanya ta rasa in da zata saka ranta.

Haka ta tsuguna ta takure, da duku-dukun mama ta shiga kitchen, ta girka abinci, gari na yin haske, ta ce lallai mai sunan baba ya taso su tafi station Win.

Mai sunan baba ya ce "Mama, idan kin je wurin nan babu abun da zaki iya a kai, ki bari zan je ni da Usman"

Mama ta ce "Ni dai ka ?yaleni na je na ga a yaya ya kwana?"

"Lafiya ?alau ya kwana, kuma in sha Allah zamu dawo miki da shi, ki yi ha?uri" da ?yar mama ta yadda, ta basu abincin suka tafi.

Rumaisa ta ce ita ba zata tafi makaranta ba, sai yaya Aliyu ya dawo.

Mama ta ce "Aikuwa ba ki isa ba, sai kin shirya kin tafi, wata?ila kan ki dawo na huce, dan da na kalleki haushi nake ji, haka kurum saboda ke kin saka an kulle mini Wa, mara jin magana" shiru rumaisa ta yi tana kallon mama, kenan yanzu mama ta daina son ta?.

Jiki a sanyaye ta shirya, mama ta hanata kuWin makaranta, ba babban abun da ya sake ?ular da mama, irin yadda rumaisan ta zauna ta naWi abincinta, kamar abun bai dameta ba sosai.

Haka ta tafi makaranta, tana tunani kala-kala, amma har ga Allah abun ya dameta.

Kamar yadda ammi ta bu?ata, da safe Adam ya je gidan, a lokacin su iman duk sun tafi makaranta.

Ya Wau sabir yana yi masa wasa, sai dai ?ememe yaron nan ya?i dariya, sai bin sa da yake da kallo.

Ammi ta fito suka gaisa, ta ce "Yanzu wurin aikin zaka tafi?"

"Eh, na biyo na karSi sa?on ne".

Ammi ta ce "To, tun da baka tambayeni ba, ni bari na gaya maka yadda muka yi da turaki".

Ya sunkuyar da kai yana wasa da hannun sabir.

"Mun tattauna da shi, ya ce mini in bari ya dawo daga umara, zai yi magana da su wambai, dan na san akwai ?alubale, tun da rumaisa ba jinin sarauta ba ce, ko ?ar wani sananne ba, dan haka zai yi muku Addu'a a can, da ya dawo aka daidaita kuWin aure za'a kai, bayan salla idan Allah ya kaimu za ayi"

"To, Allah ya wuce mana gaba".

"Amin, wai da ce mini yayi, Jamil ya ce ko za'a maye gurbin Fulani da samha, ni dai ban ce komai ba na shigar da maganar rumaisa, dan ita ta fi kwanta mini"

Adam har mamakin ?aunar da Ammi take yi wa rumaisa yake yi, tabbas da so samu ne, Samha ta maye gurbin aisha, dan ita ta isa mace da hankalinta da iliminta, kuma Samha ta daWe tana son shi, ya san hakan, amma ammi ta dage a kan wannan ?ar yayyiyar Yarinyar.

Ya numfasa ya ce "Allah ya kyauta"

Ammi ta mi?a masa leda ta ce "Gashi nan, sabuwar jakar makaranta ce, da litattafai da turare, ka kai mata ka ce ina gaisheta"

Adam ba yadda ya iya, ya karSa ya amsa da to.

Ya fita ri?e da ledar kayan a hannunsa, ya san zuwansa wurin Yarinyar nan, ba abun da zai ?ara masa sai raini.

A harabar gidan ya tarar da Mahmud, tun da ya dawo yana ganin shige da ficen motocinsa, amma basu ta Sa haWuwa ba sai yau, yana tsaye a wurin parking space Win Adam, kusa da in da zai Wau motarsa.

Adam bai kula shi ba, shi ma bai kula shi ba, ya je ya buWe motarsa ya kunna, ya Wan jima a ciki, amma ya ga Mahmud ba shi da niyyar matsawa, ya din ga danna horn, amma Mahmud ya yi burus, ba tare da wani Sata lokaci ba Adam ya bawa motar wuta, yayi reverse, ai kuwa ya buge Mahmud, ko kaWan Mahmud bai kawo Adam zai yi masa haka ba, kan ya ankara ya ga Adam yana ?o?arin bi ta kansa, ba shiri ya mirgina, Adam ya ja motar da gudu ya bar gidan.

Ma'aikatan gidan suka yo kan Mahmud suna yi masa sannu, suna ?o?arin Waga shi, sai dai ciki gwasalewa ya nuna musu shi zai iya tashi, sai dai abu kamar wasa, da ya mi?e Win ?afa ta?i takuwa.

***
Rumaisa tana hanya tana addu'a, Allah ya sanya yaya Aliyu ya dawo, Allah ya sa komai ya wuce, sai dai ko da ta iso gida, ta tarar da Usman da mai sunan baba amma babu Aliyu. Cikin damuwa ta ce "Yaya usy ina yaya Aliyun yake?"

"Ke, case Win nan fa ma?abcinmu malam shamsu, ya yi uwa yayi makarSiya yana ta kambama abun, gaba Waya ma sun ?i saurarmu a station Win, wai sai DPO ya zo, DPO na zaci wanda ku ka yi case Win nan ne kwanaki, ashe an canza wani, sun kafi wai sai an je state cid tun da aka yi i?rarin kisan kai".

Rumaisa ta ce "Na shiga uku, ba fa yaya Aliyu ne ya ce zai kashe shi ba, shi ne ya ce zai kashe shi".

"Koma menene ba ke ki ka janyo ba rumaisa, duk abun da mutum zai gaya miki sai dai ya shiga ta kunnen dama ya fita ta hagu, saboda wautarki kin jefa Wan uwanki a wahala"

Usman ya ce "Dan Allah mama ki daina faWar haka, ?addara ce"

A fisace mama ta ce "Rufe mini baki, ko na make ka, ai duk gidan nan babu mai koya mata rashin ji irin ka"

"Allah ya baki ha?uri, ba ri mu yi salla mu koma".

Adam kuwa ko kaWan bai ji babu daWi ba abun da ya yi wa Mahmud, dan a lokacin nan yadda ya hasala, da ya samu dama sai ya taka shi da mota uban kowa ya huta, ya sauke masa wannan girman kan da rashin mutuncin da yake ji da shi.
A haka yake wurin aiki, ya gama abun da yake yi ya fito, yana da niyyar zuwa gidan gona, sai dai dole ya je ya kai wannan sa?on kan mama ta Sata ranta.

Mahmud kuwa ?arshe, sai ka shi sashin Mummy aka yi, a rikice take tambayarsu maiya same shi, suka gaya mata Adam ne ya buge shi da mota.
Nan da nan ta hau ta fara bala'i "Wannan wane irin wula?anci ne, anya Adam bai fara shaye-shaye ba? Ko dai haryanzu haukar ce a kansa, tayaya zai taka ka da mota? Wallahi ba zan lamunta ba sai na Wau mataki"

Mahmud ya Wan cije lips Win sa ya ce "Ki rabu da shi zan rama ne, yanzu ni dai ?afata zafi take yi ki yi wani abu a kai"

"Wallahi ba zan ?yale ba, Fauziyya Wauko key mu tafi asibiti kawai, Allah ya sa ba wani abun ne ya samu ?afar ba"

"Mummy, dan Allah ki rabu da shi, am just testing his anger, ashe yana nan a yadda yake bai canza ba" yayi maganar cikin zolayar Mummy.

Cikin fushi ta ce "Ka rufe mini baki, this is an serious issue, ba zan bari ba" ganin yadda ta Wau zafi ya sanya shi yin shiru yana kallon ?afarsa.

A ?ofar gidan su rumaisa, Adam ne a tsaye, yake kiran wayar Aliyu, amma shiru bai Wauka ba, wayarma a rufe take, ya kira har ya gaji, ya aika yaro ya ce ace ana sallama.

Usman ne ya fito, domin duba waye, ya tarar da Adam a tsaye, ya ?arasa yana wani basarwa, suka gaisa sama-sama.

Adam ya ce "Aliyu nake nema, na kira wayarsa ba ta shiga"

Usman ya kalleshi, ya lura ta su ta zo Waya da Aliyu sosai.

Ya ce "Ya Wan haWu da tsautsayi ne" ya bashi amsa a ta?aice.

"Wane irin tsautsayi kuma?"

"Eh waccan yarinyar ce ta tsokano Wan daba, ya je tare mata, kuma dama ta yi rigima da ma?wabta, shi ne mai gidan ya saka aka kama su, tun jiya muke zuwa police station, an ?i sakinsa, yanzu ma komawa zamu yi"

Mamaki ne ya sha kan Adam, duk rumaisan ita kaWai ta janyo wannan tarzomar.

Cikin mamaki ya ce "Wai duk ita wannan Yarinyar ce ta yi faWa da Wan daban?"

Usman yayi wani irin murmushi ya ce "Wannan ta wuce tunaninka, ka san ?anwar maza ce, bamu raineta da tsoro ba"

Adam har cikin ransa ya ji babu daWi kama Aliyu da aka yi, ya ji da rumaisan aka kama

9 / 67