Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   47 / 67

138K to 141K   out of 199.9K words

ba ko?" Jabir yayi shiru.

Mai sunan baba yayi tsaki, ya nufi hanyar fita, a daidai lokacin laila suka shigo ita da Nusaiba, bai kula su ba ya fice.

Laila ta ce "Waye wannan?"

Nusaiba ta ce "Yayan rumaisa ne ya zo duba iman, shi ya korani waje ma".

"Au ya koraki waje ma, wane irin abu ne zaku din ga barin ?arti suna kaiwa suna komowa a wurin matar da zan aura, wannan ai cin amana ne"

Laila ta ce "Nawa ka biyamu kuWin gadin da zamu hana wasu zuwa wurin iman jabir? Kai ka isa kyakywar yarinya kamar iman, ka ce zaka hana masoya zuwa wurinta"

Jabir ya ce "Ba haka bane ba anty laila, amma ai kun san bai kamata ba".

Laila ta ce "Haba jabir, kalli fa kuka take yi, da wanne za ta ji? Kuma dai naga ai baka kai kuWin auren ba tukuna. Kai baka san ka lallaSata ba"

Ya ce "Haka ne, Allah ya bata lafiya, kishi ne ya sanya ni yin hakan, zan dawo da safe" ya ajiye ledar hannunsa ya fita.

Laila ta ?arasa gaban gadon, ta zauna ta rungumo iman tana rarrashinta.

Ta samu ta Wan yi shiru sannan ta ce "Ashe rumaisa tana da wa babba kamar haka"

Nusaiba ta ce "Ba ki ji ana ce mata ?ANWAR MAZA ba? Yayyenta bakwai maza, ita ta takwas"

"Masha Allah"

Nusaiba ta ce "Amma wanda ya fitan nan, shi da Hassan Win sa ne manya, masifaffe ne, ba shi da fara'a ko kaWan, daga zuwansa fa wai na tashi na fita".

Halin da take ciki, bai hanata sake lafewa a jikin laila ta ce "Ba masifaffe bane ba, yana da kirki"

Laila ta shafa kanta ta ce "Ko dai ko dai? Ko akwai wata a ?asa ne" iman tayi shiru ba ta ce komai ba.

Laila ma tayi shirun, tana cigaba da shafa kan Iman.

Mai sunan baba kuwa, yana kan babur Win sa ?irar lifan, babu abun da yake tunani sai kukan iman, kuka mai taSa rai, ga wannan mara hankalin a yanayin da take ciki, ya je yana yi mata masifa.

Laila kuwa sai da ta ga iman ta samu bacci, sannan ta kwantar da ita.

Mai sunan baba sai da ya koma gida, sannan ya samu ya ci abinci, sai dai condition Win iman, da kukanta ya gaza barin zuciyarsa.
Tuni laila ta yi bacci, ita da Nusaiba, iman kuwa jin wayarta tayi vibrating a ?asan fulo, ya sanya ta buWe ido.

"Ya jikin?" Da sauri ta sake mutstsuke idanunta, ba mafarki bane ba, mai sunan baba ne.

What's app Win ta ta buWe, ta tura masa sa?o "Yaya umar ya ka je gida, Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi, bacci ne ya Waukeni, shiyasa ban tambayi ya ka je gida ba".

"I don't mean you should reply now, bacci yakamata ace kina yi yanzu"

Wani irin murmushi iman ta yi, a ranta ta ce 'Gane in da ka saka gaba sai Allah yaya umar'

Tayi masa reply da emojin murmushi ta ce "You are a good counsellor, na ji daWin nasiharka, but please include me in your prayers, Allah ya bani mafita" ta haWa da emojin kuka da na magiya a ?arshe =?-?=?O?.

Ya sauke numfashi a hankali ya tura mata emojin kuka da cancel =?-?L'.

"To na daina in sha Allah"

Ya tura mata alamar jinjina, sannan ya tura voice message, abun da ba ya yi, shi chatting Win ma ba damunsa yayi ba, amma yayi mata message "Na ga saura few weeks bikin saukar al?ur'aninki karo na uku, kamar yadda ki ka Wora a status, wannan kawai ya isheki godiya ga Allah, babbar ni'im ce da baiwa, da ba kowa yake yi wa ba. Dan haka kar ki daina addu'a khadija, kuka baya maganin matsala kamar yadda na gaya miki Wazu"

Subhanallah, iman taji voice Win babu adadi, musamman jin sunanta na asali a bakinsa, yana da very deep voice irin na cikakken namiji jarumi, wanda muryarsa kawai ta isa sanya mutum shiga hankalinsa.

"Alhamdilillah, yaya umar ashe kana ganin status Wina, haka ne na kusa sauka a karo na uku, na gode sosai yaya umar, na yadda you are very simple, unlike before da kake bani tsoro" ai shi ma a nasa Sangaren, ya saurari voice Win ta bai san iyaka ba, sassanyar muryarta wadda yake gauraye da sigar shagwaSa, haWi da iyayi mai matu?ar daWin sauraro".

Tunawa yayi da Jabir ne zai aureta, gaba Waya ya ji wani irin haushi ya kama shi, ba tare da yayi reply ba, ya rufe datar sa ya kwanta.

Yayi shiru yana tunanin, duk wanda ya auri mace kamar iman, idan bai tausaya mata ba, sai yaushe, mai zai sanya mutum ya din ga Waga mata murya haka, yarinyar da gaba Wayanta kalar tausayi ce.

***
Sai da ta kwana biyu, sannan aka sallami iman suka koma gida, sai dai ammi ta shiga sa?e-sa?e a kan batun auren nan.
Rumaisa ta zauna ta zana takawa a plane sheet, tare da calendar a ?asa, wadda kullum take cancel Win kwanan wata, na lokacin dawowar takawa.
Laila ta ce "Rumaisa meye haka? Ya zaki li?e mini hoton gunki a Waki"

"Papan ne gunki, wallahi ba gunki bane"

"To ni a wurina gunki ne mana, kawai ki zana Wan alajani ki kafe mini, baga hotonsa nan a waya ba"

Ruma ta ce "Ni bana son na waya, na fi son wanda na zana shi da kaina, ba kin hanamu yin video call ba, kuma ke kullum sai kin ga mijinki ba, ki bar mini zanena"

Lailaa kawai tayi murmushi, wasu lokutan rigimar rumaisa dariya take bata.

"Kin sha kununki na yamma, da maganin maman ilham?"

"Na sha mana, ai anty laila bana wasa

Ta ce "Good, yanzu dai je ki Waukko jakarki ta islamiyya, da ta makarantar boko muyi karatu, kin ga exams za ku fara"

Ruma ta tashi ta ce "Bari in Waukko, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi"

Tana fita falo tayi kiciSis da Jabir, ya Wago a yastune ya kalleta ya ce "Yauwwa dan Allah yi mini magana da iman mana"

Cikin tsiwa ta ce "Kai ka isa? Wallahi baka isa ka aikeni na je ba, ka nemi ?ar aiken ka"

Jabir ya ce "Wai ke meye haka, ka kowa ma sai ki ci masa mutunci baki da kunya?"

"Ina dai yi wa mutane marasa kirki, kuma wallahi ba zan bari ka auri iman ba in sha Allah, yayana zata aura yaya Umar ba, kuma zaka gani, idan kana da zuciya ka canza hali, ka fara zuwa ka kula da mahaifinka, kan ka yi tunanin auren iman"

Ba ?aramin zafi maganganunta, suka yi

Ya risuna ya gaida ammi, suka gaisa yace mata wurin iman ya zo, ammi ta ce masa iman tana bacci, likita ya ce a bari ta samu hutu.

Ko da jabir ya tafi, rumaisa ta din ga ziga ammi, tare da nanata mata idan har jabir bai tausayawa mahaifinsa yayi jinyarsa ba, tayaya zai tsaya ya kula da iman da ciwonta?.
DaWin daWawa ga masifa da tijarar mahaifiyarsa, da take i?irarin cewa ba za a auro mata wadda ba ta da asali ba.
Kasancewar rumaisa tayi sara a kan gaSa, domin zuciiyar ammi ta fara kaiwa da komowa a kan batun, ya sanya ta ji ita ma ta gamsu da maganar rumaisa.

Abu kamar wasa a hankali mai sunan baba ya fara Wan sakewa da iman, da Allahn da yayi shi ba shi da yarda ko kaWan.
Duk safiya za ta yi message ta gaishe shi, daga nan kuma sai ya tamabayeta ya jiki, sai dai tana shan fama kan ta Wan ja shi da hira.
Sai dai ta fuskanci yana son tayi zancen karatu, mussaman na addini, hakan ya kan ri?e mata shi, gaba Waya mai sunan baba mu'amala da shi sai mai ha?urin gaske, miskili ne na bugawa a jarida.

Mai sunan baba yana lura da yadda Aliyu yake gudanar da tasa soyayyar, ba kunya yake soyewa da ?ar mitsitsiyar yarinyar da a baya yake zage gwanji ya kwaWe Saboda rumaisa.

Komai ya siyo sai ya ce tun da ba ruma wannan na sweet hibba ne.
Mai sunan baba ya fara tunanin yi wa iman kyauta, amma sai ya rasa ita da ke wannan gidan mai zai bata ma? Wani irin kallo ma za ta yi masa idan ya bata abu.

Unexpected ya ga Mahmud a online, suka gaisa mai sunan baba yake tambayarsa ya mai jiki?

Mahmud ya ce "Wace mai jikin?"

"?anwarka mana, khadija" sai da Mahmud ya Wan yi shiru sannan ya tuna sunan iman ne.

Ya ce "Ohh tana lafiya, ban ma san ba ta da lafiya ba ai".

Cikin mamaki yake tambayar sa ya aka yi bai san ba ta da lafiya ba.

Mahmud ya ce "Labarin dogo ne, amma ina da tabbacin jikinta da sau?i, dan na ganta Wazu tare da daughter na a garden".

Mai sunan baba ya ce "Ina so mu yi magana ne, ban taSa shiga abun da ba ruwana ba a rayuwata, amma a wannan karon, ko sau Waya na ji ina son shiga, kuma ban ji zan iya maganar da kowa ba sai kai"

Mahmud ya ce "Ba damuwa, lallai na ciri tuta, bari mu yi maganar ta waya".

Mai sunan baba ya kira Mahmud da kansa, Mahmud ya ce "Ina shirin kiranka"

Ya ce "Bakomai, ni yakamata na kira dama. A kan Khadija ne, na je asibiti na duba ta, kamar yadda ta gaya mini tana da ciwon zuciya ne, amma kun san da wanda zaku aura mata ba ta son shi? And he is even mad gayen, ba shi da hankali gaba Waya, tayaya zai je yana mata shouting a ka a condition Win da take, ba tare da ya tausayawa halin da take ciki ba?. Yakamata ku ?ara bincikarta, kar zurfin cikinta ya sa ayi abun da zata cutu"

Ajiyar zuciya Mahmud yayi, shi kansa yana tausayin iman, kuma yayi dana sanin abun da ya yi wa ammi lokacin da ta ro?i ya auri iman.
Yarinya ce nutsatsiya da ba ruwanta da hayaniya, ita ma ta tashi cikin tsantsar ?alubalen rayuwa, a wannan gaSar kan shi ma ya san za ta cutu idan ta auri jabir, dan ya fita baki, kuma ba kirki ya cika ba, ya ji ina ma zai iya yin wani abu a kan lamarin, dan jin kunnensa ya ji jabir Win na gayawa mummy, wambai ya san maganar, turaki zaa kaiwa kuWin auren.

Bai gama tunanin ba ya ji muryar mai sunan baba ya ce "Ban taSa neman alfarma ayi wa wani abu ba, a karon farko na ro?e ka, ko dan lafiyarta"

Mahmud ya ce "Kar ka damu, zan san abun da zan yi a kan lamarin in sha Allah".

"Masha Allah na gode sosai"

Mahmud yayi shiru yana kallon wayarsa, ya nunfasa ya ce "Allah ya sa rabonka ce Malam Umar, ni na yaba da dattakunka"

***
Laila ce suke waya da takawa, tana gaya masa ruma ta ishe ta da rashin ji, ita da Wan ta, yana ta dariya mussaman da ta ce wai ruma ta zana mata aljani ta ajiye a Waki, wai hoton takawa.

"Anty laila bani shi mu yi magana" ruma tayi maganar tana ?o?arin karSar wayar.

Laila ta ce "Ungo ku ?arata, ban da video call dai, bari na shiga wanka".

Ya ce "Budurwar"

"Mmm saurayin, ya garin? Ya karatu?".

"Alhamdilillah, ya naki karatun, na ji anty laila ta ce tana yi miki lesson, kun kusa fara exams, dan Allah a dage a mayar da hankali"

"To in sha Allah, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi"

"Meyasa kuma?"

"Ba karatu kawai ake koya mana ba, sai a din ga faWar wasu maganganu"

Tun da ta faWi haka ya san akwai ?ura, ya ce "Wasu maganganun kenan?"

"Wai se malamar ta din ga tsayar da mu, wai za ayi lecture, ka ji abun da take cewa kuwa?, wai a din ga saka ?anan kaya ana karairaya sai ka ce wasu karuwai, yanzu dan Allah ya dace a zaunar da mutane ana gaya musu haka?"

Da ?yar ya iya gimtse dariyarsa ya ce "Ke ya aka yi ki ka san karuwan ne suke haka?"

"Ai in gaya maka, da akwai wani gida a unguwarmu, sai matan su dinga saka riga da wando, ko mini skirt, suna yawo, aka koresu, na ji ana cewa gidan karuwai ne, har da vest fa suke fitowa waje ana kallonsu, na zo ina bada labari a gida, mai sunan baba ya sakani kama kunne, aka ce mini kar in kuskura abun da suke yi ya burgeni, idan mutum yayi irin wannan ba ga muharraminsa ba Wan wuta ne. Ni fa wani abun ba zan iya faWa ba ne, wallahi ni duk mutuncin malamr ya zube a idona ma, ni kuwa da ta fara nake tashi na tafi.
Da fa sun rainani ba su zata ina da miji ba, sai da malama ta ce musu ni matar aure ce, wai wata ta ce mini, wai zan sai maganin mata? Na ce mata ni ban san shi ba, dan Allah a chemist ana ware maganin maza da na mata?"

Ya ce "A'a"

"To a in gaya maka, na ce mata ni idan bani da lafiya asibiti ake kaini, kawai ta? nuna mini Wasu ?ulle-?ulle da robobi mai hoton ?an iska a jiki, Wai in saya, na rufe idona na ce a'uzubil'ahi, gaskiya ni dai a cireni daga makarantar nan"

Maimakon ta ji ransa ya Saci kawai sai ya din ga tuntsura dariya, har da tari, laila ta ?arasa ta ?wace wayar, ta ce "Ke dai ban taSa ganin yarinya mara kan gado kamar ki ba? Wai ke baki da ?awaye ne?"

"Nifa ?awata Waya habiba, ko nayi ?awaye mama korarsu take yi, kuma ko ba ta kore su ba, idan muka yi faWa duka nake yi musu sai mu Sata"

"Aikuwa wannan karatun, dole na zauna na Wora miki shi, idan kin ?i ganewa kuma shi idan ya dawo ya karanta miki yadda zaki fuskanta. Haba ke gaba Waya abaibai ce ba kya gane komai kenan".

"Anty laila ki daina hantarata, zamu yi faWa"

"To muyi faWan mana, ke zaki yi wa kanki ai".

Rumaisa ta kalleta ta ce "Saboda zaki daina sai mini garin kunun sabayar maman Khadija ko? Ba ita ce a zariya ba lambarta 0703777 7442. Sai maman Ilham mai magani ba da ke cikin garin kaduna kawo road ba, lambarta 08135613021, na ri?e komai tsaf a kaina saboda irin haka".

Laila ta ce "Iko sai Allah, ke yanzu zaman hadda ki ka yi kenan?"

"Ai Anty laila ba komai ake faWa mini ba, in dai an yi abu a gabana, tsaf nake haddace komai tas a kan nan nawa".

"To kin kyauta, tashi ki je kitchen ki haWa mana kayan aiki, yanzu zan zo ki gwada mini girkin da na koya miki, in gani idan da gaske kina haddace komai Win"

Rumaisa ta tashi ta ce "Yanzu kuwa".

***

Iman duk ta kuma zama so silent, ba babban abun da yake sanyata farinciki, irin ?o?arin jan mai sunan baba da hira, da safe ta gaishe shi, daga nan yayi mata ya jiki. Mutum ne miskilin gaske, tana shan fama, amma wasu lokutan ya kan saki jiki, mussman idan tana yi masa hirar karatun addini.
Wani irin matsanancin tausayinta yake ji, da ya tuna Jabir, sai gabansa ya faWi, ya san duk wani kauce-kaucensa son iman yake yi, gashi shi bai san ta ina yakamata ya fara ba, bai san meya kamata yayi mata ta din ga farinciki ba, saboda shi ya saba da bosy life, ba wasa.

Rumaisa ce a tsaye a banWaki za ta yi wanka, tana ?arewa kanta kallo a mudubin banWaki, har da tsalle tana Wan juyi, ganin abun arziki ya fara fitowa, yana cika.
"Wayyo daWi kasheni, zan wuce gori da wula?anci, na ga me sake ce mini ?waila, kai za a ga jan aji idan suka ?ara girma, wayyo ni maman Khadija da maman ilham sun kankaro ni yasin"
Ta gama wankanta, ta fito ta shafa mayukan gyaran fata, ta saka kaya, ta kuma tsayawa tana kallon mudubi, ta ce "Hmmm, na ga wanda zai sake ce mini ?waila, mu haurata da shi, har shi papan, yanzu dai sun fi ?arfin murfin jarkar faro"

Ta Waga kai ta kalli zanenta, da take kansile date kullum, na kwanakin da ya rage ya dawo.

A hankali ta furta "Lokaci baya sauri".

Ammi fa gaba Waya ta ji batun auren nan na iman da jabir ya fita daga ranta, kuma ta bi maganar rumaisa cikin tsanaki, taga lallai gaskiya take faWa, ta sanyawa ranta aure lokaci ne, bai kamata ta jefa rayuwar iman cikin hatsari ba.
A wannan zullumin turaki ya kirata, ya sanar da ita, wambai ya ce masa zai kawo wa jabir kuWin aure.
Takanas ammi taje gida, ta iske turaki, ta nemi ya taimaka a janye maganar nan.
Turaki ya ce "Giwa saboda ne, kin fi kowa sanin halin wambai, daga ni har ke ba zai saurara mana ba".

Nan ammi ta yi masa bayanin komai, tuntuni ta so ta yiwa wambai maganar, amma ta san ba zai saurareta ba, turaki ya gamsu da maganganunta, dan ya san halin hajiya Lubabatu sarai, za ta aikata fiye da haka, ga yarinya na fama larura.
Dan haka ya ce shi da ita yakamata su je wurin wamban, su yi magana da shi.

Ammi kamar ta ce ba sai sun je tare ba, saboda tana fargaba wambai ba ya yinta ko kaWan. Amma yadda ta iya, tun da suggestion Win turaki ne.

Aikuwa kamar yadda ta tsammata, wambai ya balbalesu da faWa ta in da ta shiga ba ta nan yake fita ba, ya din ga masifa.

"Kana bani mamaki turaki, da ka ke biyewa matar nan, dan kawai tana sirikarka, ke ba abun farincikin ki bane ba, kamar jabir zai auri yarinyar da ba wanda ya san iyayenta sai ke da mijinki a da'awarku.
Nagartaccen yaro mai daraja daga gidan sarauta, sau nawa ana shirin aurenta ana fasawa, saboda wannan abun kunyar?".

Turaki ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba jabir Win ake gudu ba, ita mahaifiyarsa da ta je har gida, ta nuna bata son abun, ta ci musu mutunci har yarinyar, wanda sai da ciwonta ya tashi, ita ma fa ?a ce Allah ya baka yawan rai"

"Ita lubabatun ce ta ce ba ta son auren, bayan mun gama magana da ita?"

Da mamaki ammi ta kalleshi, sannan ta ce "eh, har gida taje ta ce mini ba ta so"

Wambai ya kira wayar hajiya Lubabatu, amma cike da ?warewa a mugunta, ta hau salati ta ce ?arya ne, kawai dai giwa ta ce ba zata bawa

47 / 67