Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   12 / 67

33K to 36K   out of 199.9K words

faWi, ta dafe ?irjinta ta ce "What, again ta sama mata? Iman ko? Iman ce na sani, wai dan Allah me na yi wa matar nan ta tsaneni haka? A wancan karon ma ita ta yi uwa da makarSiya ban auri Adam ba, a wannan karon ma ta kuma yi mini, na san ba wadda za ta zaSa masa sai Iman"

Mama ta ce "To, ai a wannan karon sai ki kwantar da hankalinki, tun da an kuma kwatawa, sun nuna muraran ba sa ?aunarki, sai ki ?yale mata Wanta ko?"

Samha ba ta iya cewa komai ba kawai ta tafi Wakint, tamkar wadda take shirin zarewa, kaiwa ta din ga yi tana komowa a Wakin, cikin zafin rai ta furta "Giwa me na yi miki, ki ke ?yamar haWa zuriya da ni ne? To wallahi a wannan karon ba zan yadda ba, ko ni ko ke ko mu rasa Adam daga ni har ke, har wadda zaki aura masan" ta yi maganar tana zubewa a kan gadonta cikin ?unar rai.

***
Dukan teburin gabansa yayi, tare da tura kujerar da yake kai baya, ya ce "Aikin banza kawai, wai shi adam Win wanene da ganin ?arshensa ya gagara, duk wannan abubuwan da aka yi a kansa, na gidajen jaridu da social media, yayi burus ya ?i cewa uffan, sai ma wasu da yake turowa suna kare shi, wannan wane irin abu ne haka, ta ina kuma ya rage a Sullo masa?"

Usman wakili yayi murmushi ya ce "Yaro man kaza, kai fa ka ce da na sakar maka ragamar komai, zaka iya komai ka san ta yadda zaka Sullowa lamarin"

Khalifa ya ce "Haka ne Daddy, na yi duk iya yi na, ka sani na zaci yadda maganganun nan suka yamutsa hazo za su gigita shi, amma ya mayar da mutane mahaukata wato mu je ma mu yi ta yi kenan"

Senator ya yi murmushi ya ce "Na jinjinawa ?o?arin ka Khalifa, ban taSa zaton zaka iya wannan ?o?arin ba ma, ka bani mamaki sosai kuma na yabawa ?o?arin ka, labarin da yake zuwar mini, hankalin yaron nan ba ya kanmu yanzu, kuma waWanda suke jagorantar aikin tare da su, na saye wasu daga cikinsu, sannan kuma dama shi yake jagorantar aikin, kuma hamkalinsa ba ya kan aikin yanzu, na yi magana da shugaban kwamitin da shugaban ?asa ya kafa, mun gama magana ba wani abu zasu wanke ni"

"Amma daddy kana ganin hakan ya wadatar, kar fa ya kuma Sallo mana ruwa".

"Ai ba haka zan bar shi ba, ba ka da wata damuwa, na san abun da nake yi"

Khalifa yayi murmushi ya ce "To shikenan daddy"

***
Adam yana zaune yana aikinsa a office Win sa, ya Wau wayarsa ya kira Bashir.
Suka gaisa Adam ya ce "Ka je ka ma?ale ka ?i dawowa, akwai update ne?"

Bashir ya ce "Babu wani update, sai dai na haWu da barrister Sa'ad, ya ce akwai yiwuwar kwamitin da shugaban ?asa ya kafa a kan senator Usman wakili ba zai yi wani tasiri ba"

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na sani, dama ban ji a raina za su yi wani abun kirki ba, amma babu damuwa, zuwa next week ko upper in sha Allah zan shiga Abuja, ina son zuwa EFCC".

Bashir ya ce "Meyasa ba zaka shigo next week ba?"

"Wallahi ammi ce ta sakoni a gaba da wani batu, yanzu da na ce zan yi tafiyar nan, za ta ce ban Wau abun da muhimmanci ba"

"Eh kuma haka ne, to shikenan Allah ya kaimu upper week Win, ni ranar sunda in sha Allah zan shigo kano, dama da zaka zo next week Win ne sai na jiraka, duk yadda ake ciki dai za mu yi waya"

"To shikenan Bashir, Allah ya yi mana jagora "

"Amin ya rabb, a tashi lafiya".

Ya ajiye wayar kenan, Jabir yayi sallama a office Win Adam, Adam ya kalleshi ya ce "Me ka ke yi a nan lokacin aiki?"

Jabir ya harare shi ya ce "Ban sani ba, sai avoiding Wina kake, ba na samunka a gida, gidanka ma baka nan, na ce bari na zo na ritsaka a nan"

"Amma dai ka san lokacin aiki ne yanzu ko?"

Jabir ya ce "Ai lokacin salla ne kawai ba zan datseka ba, kuma sai ka saurareni, ai ka san abun da ka yi ba ka kyauta ba, dole ka yi ta gudun haWuwarmu"

Adam yayi masa shiru, ya cigaba da aikinsa.

"Adam, ka san yanzu kaf idon duniya a kan kan ka yake, amma na lura kai ba ka damuwa da hakan, baka gudun janyo wa kan ka magana, yanzu dan Allah da wani mummunan abu ya faru da Mahmud saboda zuciyarka me zaka ce? Yakamata ka sassauta wa zuciyarka wannan ?iyayyar da ka ke yi masa, ko kana so ko ba ka so Wan uwanka ne shi"

Adam ya yi masa shiru, wanda wannan shirun shine halayarsa da ta fi Satawa makusantansa rai.

"Ko ka kulani, ko kar ka kulani, na san dai kai ba kurma bane ba, kuma ka na jina, jibi in Allah ya kaimu zan je duba galadima" sai a yanzu Adam ya Wago ya kalli Jabir ya ce "Ubangiji Allah ya tsare hanya, ka ce ina gaishe shi" Jabir ya girgiza kai ya tashi ya fice, dan halin Adam sai shi wasu lokutan.

***
Tun da rumaisa suka yi waya da ammi, take ta zuba ido ta ga ta ina za a kawo mata Sabir ta ganshi, danne zuciyarta kawai take yi, mussaman idan ta tuna da alwashin dabta yi wa Adam, a akan ba zata sake zuwa gidansu ba.
Ammi kuwa ta kasa ta tsare, ta ce lallai Adam ya Wauki Sabir, da shi da Iman su je a kaiwa rumaisa shi, ko awanni su yi tare ta ganshi, tun da dai an yi mata al?awarin yin hakan, a duk lokacin da ta bu?ata.
Tun da Iman ta ji za su je gidansu rumaisa, gabanta ya faWi, saboda tana matu?ar fargabar haWuwa da yayan rumaisa mai sunan baba, dan ita gaba Wayansa tsoro yake bata.

Adam dan dai babu yadda zai yi da ammi ne, ba zai iya bujerewa maganarta ba, amma a ganinsa tun da ya yadda da auren, wannan aika shin da ammin take, ba abun da zai janyo masa sai raini.

Da la'asar suka shirya, aka shirya Sabir suka fito domin tafiya gidansu rumaisa, Adam na gaba iman na bin sa a baya da Sabir. kasancewar Mahmud ?afarsa ta fara sau?i, ya fara yawonsa a cikin gidan, hango Iman yayi da yaron a hannunta, wanda ko ba a gaya masa ba ya san shi ne jaririn, haka nan ya ji ya kwaWaitu da son ganin fuskar yaron, tun da a yanzu, kansa kawai ya hango, mai Wauke da tulin suma ba?a wuluk.

Suna tafe a hanya Iman na yi wa sabir wasa, yana ta mi?a hannu yana son kamo sitiyarin motar.

"Iman" Adam ya kira sunanta.

"Na'am yaya".

"Abubuwa sun fara yi mini zafi, na san magana zata fara yawo a kan auren nan nawa, dan Jamil ya zo ya tutsiyeni na gaya masa idan maganar gaske ne, kuma na tabattar masa da gaske ne, abun da nake so da ke, dan Allah ku yi shiru da bakinku, kar wanda ya san wa zan aura, idan an yi auren sa ganta"

"Yaya kunya ka ke ji ace rumaisa ce matarka?"

"Ke rabu da ni kawai, banda rigimar ammi, ina ni ina wannan Yarinyar da a rayuwarta babu wanda ta raina kamar ni, kuma bana son a cutar da ita, Samha haryanzu tana son aurena, a wannan karon ma ba zai yiwu ba, shiyasa bana son kowa ya san wacece".

"In sha Allah yaya ba zan faWawa kowa ba, ammi ma ta gargaWemu a kan hakan"

Ya ce "Good, ku shiga ki kai mata shi, ni zan je gidan gona, wancan karon ban samu na je ba, saboda wani dalili " yayi maganar lokacin da ya yi parking.

Ta ce "To shikenan, sai ka dawo" ta sauka ta Wauki kayan rumaisa da ammi ta sake bayarwa a bata, ta shiga gidansu rumaisa da sallama.

Sai dai gidan shiru, babu alamar aksai mutane a gidan.

Iman ta yi sallama, sai dai muryar da ta amsa mata sallamar ce ta razanata. Kasa shiga ta yi, ta kuma kasa komawa baya.

Shi kuma bai kuma tankawa ba, sallama ta kuma yi, ya ce "An amsa a shigo mana" daga Wakin mama take jiyo muryarsa, kamar mai shirin arangama da horo, ta shiga Wakin.

Mai sunan baba ne a zaune yana cin abinci, mama kuma tana salla.

Cikin War-War, ta shiga ta zauna hannunta rungume da Sabir, kanta a ?asa ta ce masa "Ina wuni?"

Bai kalleta ba ya ce "Lafiya lau" Sabir ya ?urawa mai sunan baba ido, "Mi?o mini shi" yayi mata maganar cikin umarni.

Kai a ?asa ta mi?a masa Sabir, ya rungume shi yana cewa "My boy, ka ?ara girma Masha Allah" bai yi masa ?yuya ba, ya cigaba da cin abincin sa, iman ?o?arin satar kallon mai sunan baba take tana tsoro, shi kuma da ya lura da hakan, sai ya tsareta da idonsa tana Waga ido suka yi ido huWu, aikuwa ta razana ta sunkuyar da kanta.

'Yarinyar nan tana da hankali kuwa?' mai sunan baba ya tambayi kansa.

Mama ta idar da salla da addu'a, ta juyo tana yi wa iman sannj da zuwa.

Iman ta gaisheta mama ta amsa mata cikin sakin fuska, Iman ta ce "Ammi ce ta ce a kawo wa Anty rumaisa Sabir"

Mama ta ce "Allah sarki, yanzu za ta shigo daga islamiyya, ya babansa?"

"Yana lafiya shi ya kawomu, zai dawo ya Waukemu ma"

Mama ta kalli Sabir ta ce "Mutumin, zo mu gaisa mana" ya sake kwanciya a jikin mai sunan baba, yana cin hannunsa.

"Allah ka aika munafukinmu ?arshen nesa, mamarmamar, igiyar ?asa ko da lafiya ko babu mamarmamar" Rumaisa ta shigo tana wa?e-wa?enta, da ?an ciye-ciye.

Tana shiga falon mama sabir ta fara gani, ta buga tsalle zata Wauke shi, mai sunan baba ya ce "Fita ki yi sallama" sumi-sumi, ta koma ta yi sallama, sannan ta Wau sabir tana murna.

Ta kalli Iman ta ce "Anty iman sannu da zuwa, ya ammi?"

"Tana lafiya tana gaishe ki"

Babban abun da ya bawa mama mamaki, bai wuce yadda Sabir ya saki fuskarsa ba da ya ga rumaisa.

Rumaisa ta shimfiWa tabarma a tsakar gida ta ce "Anty Iman, dawo daga nan mu yi hirarmu, ya fi iska"

Haka yayi wa iman daWi, dan mai sunan baba ya takurata.

Rumaisa ta cire wandon uniform Win ta, daga? ita sai rigar uniform, ba hijjabi ba Wankwali, sai murna take yi.

"Anty Iman, bari na zubo mana abinci"

Iman ta ce "Wallahi a ?oshe nake"

"Ba kya cin abincin gidan talakawa dai"

Da sauri Iman ta ce "A'a wallahi"

Rumaisa ta ce "To kawai zan zubo ki ci".

Rumaia ta zubo wa Iman jallof rice, mai kyau har da nama, ta kawo mata ruwa, ita kuma ta Wauko tukunyar da aka yi girkin da cokali da yaji ta zo ta zauna.

"Anty rumaisa me zaki yi da tukunya kuma?"

"?anzon shinkafa zan ci ya fi daWi"

Iman ta zuba mata ido tana dariya, rumaisa ta din ga kankarar ?anzo ta na ci, Sabir ya din ga zura hannu yana nema ya ci shi ma.

Iman ta na cin abincin tana yi wa rumaisa santin abinci yayi daWi.

"Garadan mama ne suka girka, kuma ba wani daWi yayi ba kar su ji ki ziga su" hira suke yi sosai da iman.

Suna tsaka da hirar suka ji sallamar Adam a ?ofar shigowa gidan, suka amsa masa, mama ta ce ace ya shigo, mai sunan baba ya tashi ya baro Wakin mama, dan ya san nan zai shiga.

Adam na shigowa da rumaisa ya fara tozali, ta ta?ar?are tana kankarar ?anzon tukunya tana ci, kamar mayuwanciya, ga kuma abinci mai kyau a gaban iman, Sabir kamar zai shiga cikin tukunyar, yana son ya duntsi ?anzon ya kai bakinsa.

Ayshercool.
08081012143
PAID BOOK NE, ? 500 VIA 0009450228,AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143.




Sallamar Adam bai hana rumaisa cigaba da ta?ar?arewa tana ?wa?walar ?anzo da cokali tana cin kayanta ba, ba ta da niyyar tashi ma ta saya jikinta, abun da ya dameta kawai take yi.
Usman da tun zuwan iman yana cikin Wakinsu, ya le?a ta window, ji yayi kamar ya fito ya kifawa rumaisa mari.

Adam ya wuce su, ya shiga wurin mama, Iman ta kalli rumaisa ta ce "Anty rumaisa baki gaida takawa ba?"

Ruma ta kwaSe baki ta ce "Kin ga ya kulani ne?"

"Amma da kin yi masa magana zai kula ki"

Rumaisa ta ce "Wallahi ba zai amsa ba"

Cikin mamaki iman ta ce "Meyasa ki ka rantse"

Ruma ta ce "Mufa gidan nan babu mai kalar halin da babu, dan haka ko sau Waya na haWu da mutum zan gane halinsa, ni ba dan Sabir ba kuma a daina ce mini ?ar iska ba, ba abun da zai saka na aure shi, kuma dai ina son ammi ita ma ina jin maganarta, amma wannan mak faWan da zuciyar taS"

Iman ta ce "Wai ni, meyasa ba kwa shiri ne, wallahi takawa mutumin kirki ne sosai Anty rumaisa, ko wani abun yayi miki?"

"Hmm ba ruwanki a wannan faWan"

Iman ta ce "Haka ne, faWan masoya ne" aikuwa rumaisa ta ?ware da ?anzo jin abun da iman ta ce, "TaS lallai kin tafka saSo"

Iman ta kuma cewa "Allah Anty rumaisa, yaya Adam yana da kirki sosai, ki din ga yi masa uzuri, abubuwa sun saka shi a gaba, kawai kina ganinsa a haka ne, idan ki ka ji abubuwan da yake ciki sai kin tausaya masa".

Ruma ta taSe baki ta ce "Da zai gane da ya daina Waukar damuwowinsa a zuciyarsa, babu abun da zasu ?ara masa sai nauyin zuciya, ya din ga Waukar damuwowinsa a ?wa?walwarsa, ita ke da ma'aunin samar da mafita"

Mamaki ne ya kama Iman, jin rumaisa na wani lissafi, da ba ta gane ba.

"Ban gane me ki ke nufi ba".

"Kar ki damu, manta da ni kawai, bari na Wauko takarda da biro ki rubuta mini lambar wayarki, zan din ga kiranki muna hira".

Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai jotter a jakata, bari na rubuta miki" Aikuwa ta rubutawa rumaisa lambarta, a lokacin rumaisa ta shagala da wasa da sabir, sai dariya yake yi.

A daidai lokacin Adam ya fito, mama ganin a yadda rumaisa ke zaune ba ?aramin ?ular da ita ya yi ba.

Iman ta ce "Anty rumaisa kawo shi mu tafi" a take jikin rumaisa yayi sanyi, ta sake rungume Sabir.

Mama ta ce "Ke bana son shirme, ki ba ta shi su tafi"

Kawai ta fara kuka, hawaye wani na bin wani, wanda a ganin adam kawai shagwaSa ce da wula?anci.

"Mama dan Allah a bar mini shi a nan, mu kwana tare" mama ba ta saurari rumaisa ba, ta karSi sabir ta bawa iman.

Wadda jikinta yayi sanyi, tausayin rumaisa ya mamaye mata zuciya.

Kallon ruma da take kuka Sabir yake yi, Iman ta ce "Ka yi wa maminka bye-bye"

KwaSe baki ya shiga yi, zai yi kuka, Adam ya karSe shi ya yi waje da shi, saboda haka nan ya ji tausayin su ya kama shi, wata irin Soyayya mai ban mamaki tsakanin yaro da zuciyar da ba ta uwassa ba.

Iman ta dafa kafaWar rumaisa ta ce "Anty ruma ki yi ha?uri kin ji, da kun yi auren nan, za a dawo miki da sabir Winki, ki daina kuka" ruma ta jinjina mata kai ta ce "Ki gaida Ammi, da wannan Win nan mai kamar da baban sabir"

"Tom za su ji in sha Allah"

Suna tafiya mama ta dirarwa da rumaisa faWa, mussaman a kan rashin hankalin da ta tafka, a gaban wanda zata aura ta ta?ar?are tana kankarar ?anzo tana ci, babu ko kunya balle kawaici, ga wannan koke-koken na babu dalili da take yi, a duk lokacin da aka kawo sabir.

Ita dai rumaisa a wurinta, ba ta Wau adam wani na mussaman ba, balle idonsa ya hanata abun da take yi, tun da duk gidansu maza ne, ita ba ta Wau abun da ta yi wani laifi ba.
Maganar Sabir kuwa, ta barwa ranta cewa babu wanda ya san halin da take ciki sai Allah a kan yaron nan, dan haka ta daina damuwa a kan mitar da ake yi mata.

Usman ya fito yana faWin "Bagidajiya kawai, wannan ai yawa ne ki ka yi, to wallahi nan gaba rainaki zai yi, sai la ce wata budurwar ?auye, ke ba wani class bakomai"

Abdalla da bai daWe da shigowa ba, ya tambayi mai ta yi, Usman ya gaya masa, ya ce "Kai yanzu har wani aji kake nema a wurin rumaisa, ai tun da suka ce za su aureta a haka, sai fatan Allah ya sanya su gama lafiya"

Ko a jikinta, an mintsini tattaura, abun da ya dameta kawai shi ne a gabanta.

***
Su Iman da suka koma gida kuwa, Ammi ba ta nan, Iman ba ta son ta fita ta koma gida ta tarar Ammi ba ta nan, gashi tare suka fita da Nusaiba, Kasancewar Sabir yayi bacci, da shi Adam ya tafi sashinsa ya kwantar da shi, Iman kuma ta wuce Wakinta.

Sai dai tana zuwa Wakin, ta yi tozali da Samha a tsaye, sai da ta razana ta ce "Anty Samha lafiya kuwa?".

"Ban sani ba, munafuka tsintacciyar mage da ba ta mage" cikin rashin fahimta iman take kallonta, dan ba ta san me ya kawo wannan maganar ba.

"Saboda tsohuwar munafuka ce, shi ne ki ka je ki ka cewa giwa kina son Adam, za a haWa aurensa da ke a maimakon ni, duk da irin kashedin da na yi miki ko?"

Kamar zata yi kuka ta ce "Ni kuma?"

"Ke Win fa, algunguma ni zaki yi wa pretending, to ki rubuta ki ajiye, gidan Adam kabarinki ne, yadda aisha ta shige shi ta bar duniya, duk wadda ta shiga bani ba sai ta bita, idan ba haka ba kuwa ayi babu, kowa ya rasa daga ni har ke, da ni ki ke zancen, zan yi maganinki ba?ar annamimiya"

Gaban Iman ya faWi da jin furucin da Samha ta yi, tana gama zazzage mata ta yi waje.

Jikin iman har rawa yake yi, saboda tsananin tashin hankali, da yadda hankalinta ya dugunzuma, a take rumaisa ta faWo mata, wato a zaton Samha Takawa ita zai aura, tausayin rumaisa ya kamata ya ruma za ta yi da wannan manyan al'amura ta ko ina, ga ma?iyan mijinta, ga tarin ?alubalen gidan, ga kuma masifar Samha, a kaf dangin nan babu wanda bai sarawa

12 / 67