Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   64 / 67

189K to 192K   out of 199.9K words

magiya ita ma a kan a taimaka a sanya baki, a saki Jabir.

Mummy ta ce "Wallahi ba ta isa ba, ba zai lalata mata ?a ya ci bulus ba" jin abubuwa babu Allah a ciki, dagulewar lamuran yayi yawa, ya sanya wambai cewa su tafi su je su ?arata a wurin ?an sanda.

Sai da ya rage daga shi sai turaki, sannan turaki ya samu zubar da hawaye, ya daWe matar nan tana citar da shi da Aisha, amma ba ya iya Waukar mataki, dama tun a farko rumaisa ta gaya masa komai, sai dai bai tabattar ba sai a yanzu.
Wambai ya dafa kafaWarsa ya ce "Ina neman afuwarka Wan uwana, na rashin tsayawa in fuskance ka a abubuwa da dama. Dama na san biyayya ce ta sanya ka auri Sa'adatu, sai dai wannan abu ba kai kaWai ya shafa ba, zan yi iya ?o?arin ganin cewa maganar nan ba ta fita ba"

"Kar ka yi haka, ko kayi hakan, ko ba kayi hakan ba, dole sai maganar ta fita, Allah ya ji?an fulani da mahaifiyarta, rumaisa kuma Allah ya yi mata kyakykyawan tukuici da ita da iyayenta.


Mahmud kai tsaye har gida ya kai Adam da rumaisa.

Adam na kwance a jikin rumaisa kamar uwa da Wa, sai aikin rarrashin sa take yi, tana bashi ha?uri.

"Rumaisa, ni wakili yake gayawa sai in dai in yi ha?uri, ran matata ya salwanta a banza, saboda wautata da rashin hankali, kuma wai ba wani abu da zan iya yi a kai"

"Ban gaya maka ba? Na ce zaka iya bincike ne kawai, amma in dai a ?asar nan ne, kar ka yi tsammanin samun adalci, mu bar wa Allah papa, you try your best, Allah shaida ne"

Mahmud ya ce "Takawa dan Allah ka daina kukan nan haka, kar ka tayar mata da hankali, ga ciki tana fama da shi".

"Mahmud baka san me nake a zuciyata ba, ba zaka gane ba"

"Na sani mana, saboda sau?a?a maka raWaWin da ni da rumaisa muka yi aiki tare dan sau?a?a maka aiki. Ina mai baku ha?urin rashin exposing Mummy, amma ita ma very soon in sha Allah, ka yi ha?uri dan Allah"

Cikin kuka ya sake cewa "Jamil fa mahmud, a Wakin Ammi muka yi wasa tare muka faWi muka tashi, amma ni Jamil zai din ga yi wa wannan cin dunduniyar? Me nayi masa? An kashe mini mata kuma ya cigaba da bibiyata da ?o?arin Wora mini sharri? Me nayi masa ne?"

"Baka yi masa komai ba Papa, hassadar ka fi shi komai ne kawai da kwaWayin abun duniya ya sanya shi haWa kai da ma?iyanka, gashi wanda ka ke yi wa kallon ma?iyin, shi ne ya taimake ka, duk lalacewar Wan uwa naka ne papa".

"Na gode mimi na gode sosai"

"Dan Allah ka daina yi mini wannan godiyar, ni ba abun da na yi "

Mahmud ya mi?e ya ce "Daughter, ki kula mini da shi sosai dan Allah, zan je gida wurin ammi, na san tana cikin damuwa ita ma"

Ruma ta ce "Wait, wai ba daga gadon asibiti ka taso ba?"

"Rabu da ni na warware "

"Amma ka yadda maman jabir tayi maka wani abu?"

Ya ce "Na yarda, Kamar yadda muka saka Yasir bibiyar wayar Mummy, ya kunna mini wayar da Mummy tayi da Hajiya Lubabatu. Na karSi duk wata shaida ta hannunsa, jibi in Allah ya kaimu zai tafi wurin Anty laila, kar ma a samu wata matsala saboda aikin da ya yi mana"

Ruma ta ce "When are you exposing her?"

"Soon in sha Allah"

"Idan ba zaka yi ba, allow me to do it"

"I will in sha Allah" ya juya ya fita.

Haka ruma tayi ta aikin rarrashin Adam, dan abun ya dake shi sosai da sosai, duk iya tunaninsa bai ga ta ina zai iya jayayya da SMOKE ba.

Kuma dolensa ya ha?ura da cigaba da duk wani yin?uri a kan garkuwa da aisha, saboda rayuwar rumaisa.

***
Kwanaki uku kenan, gidajen sarautar suka shiga Wimbin tashin hankali, komai ya damalmale, ba kama hannun yaro, aka gaza samo bakin zaren abubuwan da suka riga suka dagule, Kodayake ba komai ne zai gyaru ba, kasancewar wata Sarakar ta samo asali ne tun shekarun da suka gabata, ba tare da an mayar da hankali an gyara su ba.
Kodaye rumaisa ta kawo gagarumin cigaba da kuma gyara wasu abubuwan.

Ba tare da wani cikakken shiri ba, Mahmud ya ce lallai sai Yasir ya tafi canada, Yasir ya so ayi bikin yaya Abubakar yana nan, amma ba dama, aikuwa sai da yayi kuka saboda rabuwa da mama da ?an uwansa. Mahmud kuma ya ?arfafa yin hakan ne, kar wani abu ya samu Yasir, saboda aikin da yayi musu, dan a wata fuskar laifi ne abun da ya aikata Win, kutse da satar bayanan mutane ba tare da izinin su ba.
Haka ya tsallaka ya tafi ya bar Nigeria.

Abdallah kuwa Bashir ya ce sai sun tafi da shi Abuja, mama ta tashi hankalinta ganin kamar ana yi wa yaranta Wauki Waya-Waya, amma ya bata tabbacin babu wata damuwa, a kan Jamil ne ita ma rumaisa Adam ne zai wakilce ta, saboda tsohon cikinta.

Ranar da zasu tafi Abuja, takawa yayi ta rarrashin ruma, tare da bata tabbacin, Abdallah zai dawo lafiya, tun da har da shi zasu tafi.

Rumaisa suna ta shirin fara Waec, sai dai fa nauyin ciki ya hanata sukuni sosai, tun da ta dawo daga makaranta, mararta take yi mata ciwo da ?afafuwanta, kuma takawa ya riga ya tafi, dama ya ce mata idan ba zata iya zaman gidan ba, ta tafi gida wurin mama ko ammi.

Jin ciwo ya?i ?arewa, ta kira Usman a waya, ta ce ya zo zata mutu.

Ya je ya tarar da ita duk a firgice, ta bashi mukullin Waya daga motocin takawa, ta ce ya kaita asibiti.

Suna tafe a hanya ya ce "Ko dai haihuwa zaki yi?"

"Edd Win bai cika ba fa"

Ya ce "Ikon Allah, muna zaune yarinyar da muka goya, muka yi wa wanka za ta haihu, haryanzu muna gararamba, bakomai akwai lokaci"

Bakin rumaisa bai mutu ba, sai da aka ce mata haihuwa ce a asibiti, ita dai ta san lokacin haihuwa da saura, aka ce usman ya je ya kwaso kayanta.
Maimakon ya kira mama a waya, ko ammi, kawai sai ya kira Aliyu da Huzaifa, sannan ya ?arasa gidanta, ya Waukko akwatin da ta kwatanta masa, dan tuni takawa ya gama sayen komai na jariri.

Mamaki ya kama nurses Win, suka ce babu wata mace wadda za ta zauna da ita duk sai maza.
Huzaifa ya ce "Hajiya gidanmu ita kaWai ce mace, babarmu kuma tsohuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, duk abun da mata zasu yi, mu ma zamu yi"

Nurse Win ta ce "A dai duba dangi a samo wata"

Usman ya ce "Hajjaju, wallahi zamu iya komai, ki ?yalemu kawai".

"To ina mijinta?"

Aliyu ya ce "Tafiya ce ta kama shi Wazu"

Ta jinjina kai ta ce "Lallai ?ANWAR MAZA"

Rumaisa ta sare da al'amarin, saboda tun da mama ta haifeta ba ta taSa jin masifaffen ciwo kamar wannan ba.

Mai sunan baba kuwa, ganin hankalin Adam yayi wani wurin, mahmud kuma ya warware, ya sanya ya yi wa mahmud zancen, mahmud ya din ga murna, ya ce dole su je Lagos tare, dan tabattar da wannan lamari, dan haka ya ce zai yi musu booking Flight su je, su yi abun da za su yi, saboda su koma bakin aiki.

Mai sunan baba ya kira Huzaifa a waya, yana masa faWan duk suna ina, gida ba kowa sai mama itakaWai a gidan.

Mama ta ce "To yarinya ce ni, da lallai sai sun zauna a gida?".

Huzaifa ya gaya masa in suka tafi, ba tare da ya gaya wa mama abun da ake ciki ba, ya tafi asibitin.

?arshe sai da suka cika asibitin, Abdallah da Yasir ne kawai babu.

Gaba Waya suka zama abun kallo a asibitin, wai sun kawo ?anwarsu haihuwa a asibiti.

Ruma ba ta haihu ba sai bayan magariba, babyn pre term ne, watanni bakwai da sati biyu.

Nurse ta fito ta ce "Kun ga ga mahaifa, ga kayan jini, dan girman Allah ku nemo mace"

"Sai kuma ki yi, karSar haihuwar ma da kin matsa sai mu karSa, ko abun da ya fi kayan jini ne zamu gyara, babarmu tsohuwa ce, bamu da ?ar uwa mace, dangi ba kowa ke son ka katse masa hidimomin sa ba, dan haka ba jini ba, ko menene zamu iya"

Mai sunan baba ya ce "Ina jaririn?".

"Nursery zamu kai shi, sa an saka shi a kwalba"

Sai da suka jira aka basu damar shiga su ga ruma, tana kwance kai da ganin idonta ka san an sha gwagwarmaya.

Nurses suka ce a kawo mata abinci, sai a lokacin mai sunan baba ya tafi gida, ya gaya wa Iman, ruma ce ta haihu.

Mamaki ne ya kamata, dan washegarin taron nan sun haWu a gidan ammi, ta ce mata haihuwarta da saura.

Nan da nan ta yi girki, jiki na rawa tare da mamakin haihuwar ruma, ta kira ammi ta sanar mata.

Ammi ta ce "Ba dai rumaisa ba, takawa ya ce da saura ai"

"Wallahi ammi da gaske nake, yanzu yaya umar ya shigo ya gaya mini".

Nan da nan aka cika asibitin, ?an barka, sai dai ba ganin jariri, rumaisa kuma ba baki, duk wanda yayi mata sannu, sai dai ta jinjina kai kawai, amma ta san halin tashin hankalin da ta shiga a haihuwar.

Mama ta kalli rumaisa ta ce "In ce dai ta bakin ki ka haifo Wan naki, yau mata sun ga ta in da ake haihuwa" ruma tayi murmushi kawai.

Da ?yar ta iya cin abincin ma, ta fara cewa ita a kawo mata Wan ta fa, saboda lokacin da ta haife shi, tana gani ana ta fama, ya ?i yin kuka yadda yakamata.


Abdallah ya sha tambaya a babbar headquarter Dss ta Abuja, dan sai da aka karSi zanen aka sa shi sake yin wani, suka yi iya binciken da zasu yi, babu ko shakka Jamil ne, Wanda dama already yana hannunsu, takawa yayi kamar ya gaya musu da sanya hannun wakili, amma tayaya meye hujjarsa? Rumaisa ce kawai ta ji sun ambaci wakili, idan da wanda zai faWi da sanya hannun wakili, to Jamil ne yakamata ya faWa.
Duk wani report na bincike lokacin Satan aisha da suka yi, sai da suka gabatar da shi a wurin hukumar, laifin Jamil ya zama biyu, da na tuhumar fitar da sirrin hukumar, da kuma haWa baki tare da yin garkuwa da ?anwarsa, ga kuma Satawa Adam suna da yayi.

Ko da ana nunawa Jamil zanen nan, da Abdallah yayi, sai da ya zabura, saboda tabbas ya san shi ne.

Adam ya ce "Jamil ka tabattar wannan kai ne? Jamil me muka yi maka ni da Aisha? Idan ma wani abun na yi maka, meyasa zai shafi aisha? Ka haWa kai da wakili ka cutar da ni?"

"Adam jin dalilin hakan ba shi da wani amfani a gareka, tun an riga an kama ni, sai ka je ka cigaba da rayuwarka, ka ?yaleni. A kan me mahaifinmu zai fifita aisha a kanmu? Kuma duk wani abu na cigaba, ko na masarauta sai dai ya sanya ka a ciki alhalin gani. Wallahi da na san yarinyar nan ta gane ni, da ban barta ta rayu ba"

Adam yayi murmushi mai ciwo ya ce "Na gode sosai Jamil, sai dai ka sani, duk da ciwon hauka da nake fama, na tsaya ga Allah, shiyasa nake cigaba, kuma na barka da Allah Jamil, Jabir ma har shi da duk wanda ku ka cutar da ni, kamar yadda rumaisa ta faWa, ta ce in bar ku da Allah, zan ga yadda zai yi da ku, na bar ku da Allah"


Takawa suka koma masauki shi da Abdallah, tare da Bashir.
Sosai suke bawa Adam baki, tare da bashi ?warin gwiwa.
A lokacin yake sanar da su abubuwan da wakili ya kira shi ya sanar da shi.
Sun girgiza sosai da sosai, Bashir ya ce "A gaskiya na girgiza, dama biri yayi kama da mutum, yadda aka kasa magance wannan Smoke Win. Amma ina ga kamar yadda madam ta faWa, ka yi ?o?arin gano wanda suka yi maka ma?ar?ashiya, amma hukunta su sai Allah".

Ammi ce ta kira Adam a waya, ta sanar da shi rumaisa ta haihu, sai dai yaron an saka shi a kwalba.

Adam kansa abun ya Waure masa kai, wace irin haihuwa ana zaune ?alau, ba tare da cikakken lokaci yayi ba.

Gashi bai bai gama?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? da abuja ba, amma ya ce dole ya koma kano. Zai bar Abdallah da Bashir ko za a bu?aci wani abun, idan komai ya lafa sai su taho, shi kansa Abdallah abun ya bashi mamaki, a kan ya aka yi rumaisa ta haihu a wannan lokacin.


Sai dai cikin ?udura ta Ubangiji mai kyauta da ?ari, yaron da mimi ta haifa ya koma ga mahaliccinsa cikin dare, dama ana ta fama, ya?i kuka amma d girmansa ba ka ce bai kai lokacin haihuwa ba.

Aka yi shiru ba a gayawa mimin ba sai washegari da safe, aikuwa rumaisa ta dira rigima, ta din ga kuka, tun mama na rarrashinta, sai da ta ?ular da ita, ta fara zaginta.

Mama ta ce "Ba zaki rufe mini baki ba?"

"Mama baki san me nake ji ba ne"

Mama ta ce "Dan ubanki ?a?a biyu na binne, da zaki ce ban san me ki ke ji ba".

Ammi ta ce "Maman rumaisa ki yi ha?uri, yarinya ce kuma dole za ta ji babu daWi"

Aka naWo jaririn, aka kawo wa rumaisa, kamarsa Waya sak da Adam.

Sabir da yake zaune a kusa da rumaisa ya kalleta ya ce "Mimi, baby ya buWe ido" yayi maganar cikin yarinta.

"Boy babynmu ya mutu"

Ammi ce ta karSi jaririn, ana jiran shigowar adam, ayi masa sutura.


?arfe tara na dare Adam ya dira, ko gida bai je ba, kai tsaye asibiti ya taho, ammi tuni ta sanar masa da rasuwar yaran, dan haka hankali a tashe ya ?arasa asibitin jikinsa duk a sanyaye.

Ya tarar tuni Ammi na can ita da nusaiba, mama tana wurin rumaisa.

Ya dur?usa suka gaisa, ammi ta tambaye shi ya ake ciki, ina Abdallah?.

Ya ce mata yana lafiya, yana tare da Bashir, akwai abun da zasu ?arasa.

Ammi ta mi?a masa jaririn, ya karSe shi ya buWe zanin, kamar mai bacci, kamar sa Waya sak da shi duk da jikinsa yayi fari, amma da gani ka san yaron fari ne.

Ya mi?awa ammi shi, ya ce "Allah ya sa mai ceto ne" suka amsa da amin.

Mama tuni ta tashi ta bar Wakin, ya ?arasa gaban gadon mimi, ya zauna a kusa da ita ya ri?o hannunta.

Kawai ta fashe da kuka ta ce "Papa babyna ya mutu, kuma ina son shi"

Ya rungumota jikinsa ya ce "Am sorry mimi, ni kaina na ji ba daWi, amma Allah ya fi mu sanin me ya dace da mu, kiyi ha?uri ki daina kuka"

Yayi maganar yana shafa bayanta, shi kansa ya ji mutuwar yaron, sun sanya rai da yaron sosai da sosai.

"Ko dai abubuwan da suka faru ne, ya sanya ki ka tashi hankalinki ki ka fara labor?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To shikenan, Allah ya bamu mai amfani, ya sanya wannan mai ceto ne, na sanya masa sunan mahaifina Muhammad, Allah ya bamu wani" rarrashinta ya din ga yi tana jinjina masa kai.

Iman ta shigo ita da Usman, Usman sai da ya sunkuyar da kai, kunya ce ta kama shi, ganin yadda takawa ke zaune ya rungume mimi yana rarrashinta, ga ammi a zaune.

Abun da bai sani ba shi ne, har abun da ya fi haka yi suke, ita ba abun da ya dameta bane ba, domin ita kanta bata manta lokacin da aka yi mata aure, ba shirmen da ba sa yi ita da marigayi galadima, dan haka duk taSrar da ruma take ba ta damunta.

Usman suka gaisa da Ammi, ammi ta ce wa Iman "Ina mai sunan baban?"

"?arfe takwas suka tafi Lagos shi da yaya mahmud, wai wani abu za su je su yi"

Ammi ta ce "To, ni yanzu Mahmud tsoro nake ji, kar ya sake Sallo mana ruwa, ba a gama da wannan tarzomar ba, kodayake tare suke da mai sunan baba, ba zai bari yayi wani rashin jin ba.

Aka sallami ruma daga asibiti, tare da jaddada mata yadda za ta kula da kanta, saboda Winkin da aka yi mata.

Mutane suka din ga zuwa barka, Adam yayi mursisi ya ce ruma ba zata tafi gida ba, gidanta za ta koma, a Waukko mai kula da ita.
Ya kafa hujja da mama ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Gashi ya samu labarin su Huzaifa ne suka kawota asibiti.



Mai sunan baba kuwa lokacin da suka isa lagos, suka je gidan Alhaji Aminu, suka tarar yayi tafiya, Ade kuma ta koma Gombe!.


Ayshercool.
08081012143.

*WANDA KU KA KARANTA MINI LITTAFI BA TARE DA KUN BIYA NI HAKKINA BA, BA KUMA DAN BAKU DA SHI BA, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA GA ACCOUNT NUMBER NA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK*



Mahmud ya ce wa mai sunan baba, bai kamata su yi sanya ba, idan da dama kamata yayi kawai su tafi Gomben su bita can.

Mai sunan baba ya ce "Tayaya ni ban san a ina take a gomben ba"

"Tambayar mutanen gidan zamu yi, ba zamu yi sanya ba"

Ba tare da wani Sata lokaci ba, mutanen gidan suka basu kwatancen in da Ade take, kasancewar sun san mai sunan baba.

***
Rumaisa kuwa gwaggo ce ta je zauna mata, saboda bi?i, mutane suna ta zuwa duba ruma tare da jajanta mata abun da ya faru.
Tana zaune a Wakinta, suna video call da laila, sai kuka take yi mata, wai babyn ta ya mutu.

Laila sai rarrashin ta take yi, tana kwantar mata da hankali, tare da jaddada mata, idan komai ya dai-daita, lallai ta nemi maman Khadija, da maman ilham ta gyara, duk da yaron ya rasu, akwai bu?atar ta gyara jikinta sosai.

Rumaisa ta ce "To anty laila, in sha Allah ai ina da numbern su, ina Yasir".

Laila ta ce "Yaya bacci yake yi bai tashi ba"

Ruma ta ce "Inyee su yaya manya, ina fatan dai ba ya miki rashin ji?"

"Ba wani rashin ji, rashin ji ai sai ke, wallahi na ji daWin zuwan Yasir gidan nan rumaisa, very kind and brilliant guy, darling ya yi masa registration ma, very soon zasu fara lectures, baki ga daWin da babansu ya ji ba zuwansa, su anam ma suna ta murna"

Ruma ta ce "Sai wani yabon sa ki ke yi"

"Dole in

64 / 67