Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   23 / 67

66K to 69K   out of 199.9K words

ba?i sun fara zuwa na ce bacci ki ke yi, na dakatar da su a ?asa, kin tashi kuma baki san ki yi wanka ki canza wasu kayan ba".

Muryarsa ta ji a bayanta, dan haka ta juya da sauri, ta sha kunu ta ce "To ina ruwanka da ni, ai ni yarinya ce, a gidanmu wanka ake yi mini, ban fara yi da kaina ba".

Mamaki ne ya kama shi, ba?ar magana rumaisa ta gaya masa.

Wata irin fincikowa yayi mata gabansa, ya tsuke fuska sosai ya nuna ta da yatsansa ya ce "Nan gidana ne, kuma fadata, kuma dole ki bi umarnina, da duk abun da nace, ko na yi umarni, idan ina magana, kina mayar mini da abun da ki ka ga dama, zan yi miki abun da ba kya tunani, wuce mu je"
"To, zan yi wanka ba soso da sabulu ne?"

"Wuce mu je na ce" ya faWa a kausashe sumi-sumi ya sakata a gaba zuwa Wakinsa.

Ya nuna mata banWaki ya ce "Ki wuce ki shiga ki yi wanka, ki yi brush, ki fito ki karya, mutane na ?asa suna jiranki".

Sai da ta gama kalle-kallenta a banWaki, sannan ta kalli kayan wankan, ta ga soson a ji?e, alamar yayi amfani da shi.

"Wallahi ba zan yi wanka da soson da yayi amfani da shi ba"

Ta murza sabulu, ta yi wankanta, ta mayar da kayan da ta cire, ta fito.

Yana zaune a gefen gado yana jiranta, ya nuna mata mai a kan mudubi ya ce ta shafa, ya buWe wardrobe ya Wauko, kaya ya tsaya ta gama shafa man.

Ya kalleta ya ce "Ga kaya nan ki canza".

Ta karSa ta ce "To a gabanka zan canza kayan?".

"Ai yarinya ce ke, ba yanzu ki ka gama cewa yi miki wanka ake a gida ba, da ban yi miki wankan ba, ai sai na saka miki kaya ko?"

Zare masa ido ta yi, ya ce "Ki wuce toilet ki canza ni ba in da zani"

Har mamaki rumaisa take, yadda yake ta hantararta.

Riga da skirt ne na lace, har da undeas, ta canza kayan ta fito.

Tana ta kakkare jikinta, kar ya kalleta.

Fita ya yi yana waya, ta tsaya a gaban mudubi, tana kallon kanta, lace Win yayi mata kyau sosai. Ba wani iya Wauri ta yi ba, dan haka kawai ta Wora Wankwalin a kanta.

Dawowa yayi tare da iman, tana ganin iman ta fara murmushi.

Iman ta ce "Amaryar takawa, ina kwana"

Haka kurum sai ta ji kunya ta kamata, ta sunkuyar da kanta.

Ya kalli iman ya ce "Ta yi a haka?"

"Yes, ka san komai na ta mai kyau ne, bari ta karya, a Wan yi kwalliya sama-sama".

Rumaisa ta ce "Ni fa bana son wannan kwalliyar, haryanzu ta bikin nan jin fuskata nake a WaWWaure kamar ba ta wa ba".

Iman ta ce "Ai ba da yawa za ayi ba, bari na kawo miki abinci nan ki karya".

Abinci ne na alfarma, ammi ta saka aka kawo musu.

Rumaisa ba ta iya ci da yawa ba, dan babu abun da yake yi mata daWi, Adam kuwa cin abincin sa yayi, bayan sun gama, iman ta shafa mata powder, ta saka mata jambaki, ta Waura mata Wankwali.

Adam ya ce "Ki je ki ce musu su hawo, ta tashi" Iman ta jinjina kai ta fita.

Ya kalli rumaisa ya ce "Akwai familynmu, da naku duk sun zo, idan ki ka kuskura ki ka yi making any rubbish scene, sai na rufeki a gidan nan, ba mai sake zuwa wurinki, kuma ba zaki sake fita ba".

"Kidnapping Wina zaka yi kenan?" Ta yi maganar tana kallon sa.

"Eh" ya bata amsa, yana mamakin ita duk abun da aka faWa tana da amsar bayarwa..

Ta yi shiru, tana kallon awarwaron hannunta.

Mintuna kusan biyar, ta suka fara jiyo hayaniya sama-sama a falon saman benen.

Iman ta shigo ta ce "Yaya ku fito".

Ya ce "To, muna zuwa"

Ya sake kallon rumaisa ya ce "Ina sake gaya miki, kar ki sake ki yi wani abu a gaban mutane, da zai sa kin janyo mana magana, you should behave yourself"

Ta yi ?uri da ido tana kallonsa. "Am talking to you" yayi maganar a Wan kausashe.

"To" ta amsa a hankali.

Mi?a hannu yayi zai ri?o nata, ta janye a Wan razane.

Ta girgiza kai ta ce "Ka daina taSani, ni bana son a din ga kallona, kuma kar in je su Yaya sun zo, su ga ka ri?e mini hannu".

Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ikon Allah, to mu je" da ?yar ta yadda suka jera, suka fita.

Suna fita aka din ga rafsa guWa, ana yi masa kirari, haka nan rumaisa ta ji ta takura.

Suka ?arasa suka zauna, ya zauna a kusa da rumaisa, masu addu'a na yi, masu shewa na yi, ita dai ta yi ?uri, ji take kamar ta tashi, ga adam ya wani matseta a kan kujerar.

Wata mata da rumaisa ba ta san ko wacece ba ta mi?awa adam hannu ta ce "Ban ga ka fito da ?yalle ba, dan mu tabattar da me ka aura".

Ya ce "Haba jakadiya, wannan al'adar ai an daina ta, ko lokacin da na auri Aisha, ai ba ayi haka ba, kuma wannan sirrinmu ne kawai ko Mimi?" Yayi maganar yana kallon rumaisa.

Sororo rumaisa ta bishi da kallo, tana tunanin wacece mimi kuma a wurin, ko ba da ita yake ba?.

"To ai ita aisha tamu ce, kuma ka san ji muka yi an ce, ta shafe watanni shida a hannun masu garkuwa da mutane, kuma mun san ba a bawa kura ajiyar nama, shiyasa muka bu?aci gani, kar mu je saura aka kawo mana".

Duk da rumaisa ba ta gane kan zancen ba, amma jikinta ya bata ci mata mutunci ake yi.

Sai da ?irjin Adam yayi wani damm, amma ya basar ya kalli rumaisa, ya ce "Kamar kowacce mace, za ta yi alfahari da daren jiya, za ta yi proud sosai da hakan"

Ji ta yi kamar ta ce da ka koreni daga Wakin, na kwana a ?asa, meye wani abun alfahari.

?an uwansu rumaisa kuwa, jin zancen suka yi ba arziki, suka din ga sunkuyar da kai, Gwaggo ta ce "Dama Waki muka dawo mu gani, mu anjima zamu koma gida".

Da sauri rumaisa ta ce "Haba dai Gwaggo, to wai ya baku taho da mama ba, ban ga su yaya bama".

Adam ya ce "Bai kamata ku tafi yanzu ba, Yakamata a Wan tayata zama"

Gwaggo ta ce "A'a, ai gaka nan, mu mun tafi, ga sa?onki nan babarki tana gaishe ki"

Tashi rumaisa ke ?o?arin yi, amma ya ri?eta, ya hanata tashi.

"Gwaggo dan Allah karku tafi ku barni, dan Allah ku dawo, lawisa kema ba zaki zauna ba?" Ta yi maganar tana kuka.

Adam ya zura hannu a aljihunsa, ya bawa iman, ya ce ta bawa su gwaggo.

Ya ce Gwaggo mun gode sosai da sosai, sai mun zo gida yin bangajiya"

Ta ce "Babu komai, Allah ya sanya alkhairi"

Ya ji daWin tafiyar su gwaggo, ko ba komai, ba za a cigaba da cin mutuncin rumaisa a gabansu ba.


?ago fuskarta yayi, yana goge mata hawayen fuskarta, yana faWin "Is ok, yi ha?uri kukan ya isa haka"

?o?arin ture hannunsa take yi, amma yayi mata kallon kashedi, a dolenta ta ?yaleshi.


Baba uwani sai shiga take tana fita, tana koWa yadda gida yayi kyau.

Hajiya Lubabatu wato maman Jabir ta ce "Abun dai ya bawa kowa mamaki takawa, bamu taSa zaton zaka auri ?aramar yarinya kamar wannan ba, kuma ma dai abun da mamaki, ace wannan ?aramar yarinyar ce ta kuSuta da Sabir, daga hannun 'yan bindiga"

"Ai babu mamaki a ikon Allah, ?an?antarta kuma ba zai hana a aureta ba, tun da bai saSawa shari'a ba".

Ta kalli rumaisa ta ce "Sannu ?ar nan, sannu da shigowa familyn gidan sarauta, kin zo babban gida, Allah ya baki wuyan Wauka"

Rumaisa dai ba ta kulata ba, sai kuka da take yi, na tafiyar Gwaggo da kuma rashin ganin mama.

Haka Adam ya zauna tare da ita a wurin, dan kar ya tashi su ci zarafinta, ita kuma ya san ba kunya ce ta wadaceta ba, tsaf zata iya yi musu fitsara.

Sai wajen azahar suka ragu, bayan sun gama faWe-faWen maganganun su, da yada habaici.

Da azahar Win kuma, Nusaiba ce ta zo da kayan abincin rana.

Sai dai rumaisa ta?i cin abinci, duk surutun nata kuma ta yi shiru, ta?i kula kowa, Iman sai rarrashinta take yi.


Takawa baba uwani ya saka, ta kwashi akwatunan rumaisa, ta kai mata Wakinta, da sauran kayanta, ya ce ta shirya mata wasu kayan a cikin wardrobe Win ta, ga su iman nan, su tayata a haWa mata Wakin.

Sai dai Iman ta din ga bin baba uwani da kallo, har sai da ta tsargu, tana ta yi wa rumaisa surutu tana tsokanarta, amma rumaisa ba ta ce komai ba, sai kallonta kawai da take yi.


Tana ?o?arin fara shirya mata kayan, rumaisa ta ce "Bar shi, zan yi da kaina"

Kallonta suka yi gaba Waya,Nusaiba ta ce "Ki bari ya shirya miki, ke ga gajiyar biki, idan ya so sai ki gaya mata yadda ki ke so"

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a, idan ma ta yi sai na sake, kawai ta bar shi".


Nusaiba ta ce "To shikenan, baba uwani ?yale mata".


Adam ya shigo Wakin, yana tambayarta ko an shirya mata kayan.

Nusaiba ta ce "A'a ta ce a ?yale mata, za ta yi abun ta da kanta".

"Shikenan, ku ?yale mata abun ta, tun da ba ta san gwaninta ba, idan an yi sallar la'asar sai ku tafi gida, ba sai an kawo abincin dare ba".

"A'a dan Allah kar su tafi, shikenan sai kowa ya tafi ya barni?".

Tausayinta ya kama iman, amma takawa ya tsare gida ya ce "Do as i said"


Baba uwani ta yi mamakin yadda ?iri-?iri rumaisa ta ce ba zata shirya mata kaya ba, ta so ta saki jiki da ita ta shigeta, saboda ta din ga samun wasu bayanan, da za ta din ga kai rahoto, amma mursisi rumaisa ta?i. Sai ta bar shi a rashin sabo ne, amma tayi alwashin shiga jikin rumaisa, tun da a ganinta yarinya ce ba ta da wayo.


Sannan ta yi mamakin yadda suka haWu da rumaisa, amma ba ta san ita ce wadda Adam zai aura ba, ta fara tunanin ko dai ammi ta ganota ne, ya sanya ta fara Soye mata wasu abubuwan.

Kan su ?arasa gida, ta ce a ajiyeta a hanya, za ta je wani gida, suka ajiyeta su kuma suka ?arasa gida.


Tun da suka koma, ammi ke tambayarsu, ya suka baro rumaisa, iman ta ce "Wallahi tana ta kuka ammi, gwanin ban tausayi".

"Allah sarki rumaisa, za ta saba ne in sha Allah, na san dama za a sha daru".

Iman ta ce "Ammi kin san me?"

"A'a sai kin faWa".

"Wai jakadiya, da maman su jabir, suka saka takawa a gaba, wai ya basu ?yalle su san me ya aura, sun samu labarin watanta shida a hannun 'yan bindiga, wai ba a bawa kura ajiyar nama"

Ammi ta yi shiru ta ce "Daga kawo yarinyar jiya, shi ne za su fara wannan abun? Bakomai Allah ya fi su, kuma auren Adam?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? da rumaisa, sai ya bawa mara Wa kunya in sha Allah".

Nusaiba ta ce "Suna da matsala, daga zuwanta jiya za su fara nuna hali, kuma wallahi wata?ila Mummy ce zata saka su, ai daWinta maman Sabir Win ma ba kanwar lasa ba ce".




Baba uwani kuwa, gulma na cinta kasa jurewa ta yi, but ta faWa sashin Mummy, Aikuwa aka yi sa'a Samha tana nan, suna ta kitsa tsiya.

Mummy ta kalleta ta ce "Ya aka yi?".

"Daga gidan muke, aikin da aka bani dama na yi shi, ba wata matsala, amma jakadiya sun tambaye shi ?yalle, ya ce wannan tsohuwar al'ada ce, kuma kamar kowace mace, za ta yi alfahari da daren jiya, nake tunanin ko dai ya....

Samha ta ce "Dakata, ?arya yake yi wallahi, ai shi da ita sai kallon kallo, ?arya yake babu abun da ya faru"
Mummy ta ce "Haka ne, ke dai ki yi duk mai yiwuwa ki saka ido sosai, ki din ga kawo mana rahoton duk wani abu da yake faruwa, kuma idan muka baki aiki, ki tabattar kin yi shi yadda ya dace".

Ta risuna ta ce "In sha Allah uwar Wakina".


Tun da su iman suka tafi, ya rage daga ita sai Adam a gidan ta cigaba da kukanta, ta window Wakinta ya hangota, tana shirya kaya tana kuka, bai kulata ba ya koma falo, yana gwada kayan kallo.


A haka rumaisa ta shafe kwanaki uku a gidan Adam, ko ?asan bene bata taSa sauka ba, sai dai ba ta gajiya da kuka, mussaman yadda ?an gidansu babu wanda ya nemeta, gashi ko an zo mata ta Wan rage damuwa, da yin la'asar kowa zai watse, shi kuma Adam ba abun da ya iya banda bayar da umarni, ko ya hantareta.


A kwana na huWu ya lura, tana gujewa haWuwarsu, idan ta ji motsinsa ko falo ba za ta fito ba, ya lura abincin ma ba ci take yi ba, ta takura kanta sosai da sosai.

Bayan sallar magariba ya shiga Wakinta, ya tarar ta yi salla tana zaune a kan sallaya ta yi shiru.

?aga kai ta yi ta kalleshi, yayi mata alamar ta zo. Ba musu ta taso yana gaba tana bin sa a baya.

?asan bene ya sauka, ta bi bayansa, tun da aka kawota, yau ta fara sauka ?asan benen.

Harabar gidan suka fita, ya nufi motarsa, ya buWe gaban motar ya ce ta shiga.

Ta shiga ta zauna, tana kallon cikin motar sabuwa da ita fil, ga tsofaffin nasa da ta san shi da su a harabar.

Sai a yanzu ta lura, har da burgar dawakai a gidan, da dokuna manya guda huWu, ga wani murgujejen kare, da shi ma ba ta san da shi ba a gidan.

Security light duk ta haske ko ina a gidan.

Ba ta san in da zasu tafi ba, ita dai ta ga suna tafiya.

Sai da suka je gidan, ta gane gidansu Adam suka je.

Ammi na ganin rumaisa ta rungumeta tana murna, ta ce "Takawa, baka bari ta gama hutawa ba ka fito da ita"

"Ta isheni da koke-koke, shiyasa na kawo ta"

Ammi ta ce "Haba rumaisa, kukan bai isa haka ba, ai yakamta ki kwantar da hankalinki haka" Rumaisa ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba.

Nusaiba na ganin rumaisa ta fara murmushi "Amarya ba kya laifi, yau da kanki"

Rumaisa ta ce "Shi ne baku kuma zuwa ba da ke da Iman".

"Yaya ne ya ce kar mu sake zuwa ai"

"To ni kaWai nake zama a gidan fa, kuma shi ba kulani yake yi ba, sai dai in wuni ina kuka"

Ammi ta kalli Adam, ya sunkuyar da kai, ta kalli rumaisa ta ce "Haba Yarinyar kirki, zai din ga kulaki kukan da ki ke yi ne baya so, gobe in Allah ya kaimu za'a baki hadimai mutum biyu, da zasu din ga yi miki aiki, sa din ga Webe miki kewa, abun da ma kin kusa komawa makaranta, wani satin za a koma makaranta".

Ammi ta yi maganar baba uwani ta fito, Wauke da Sabir a hannunta.

Murmushi rumaisa ta yi ganin sabir, Adam ya karSe shi, Baba uwani ta ce "Amaryarmu, sannu da zuwa ya gida, bamu san da zuwanku ba ai da an she?a girki na mussaman"

Rumaisa ta ce "Mata ina wuni"

Baba uwani ta ce "Tuba nake, ai ni yakamata na kwashi gaisuwa"

Sabir kuwa rumaisa ya din ga mi?awa hannu.
Adam ya ce "Kai, kwana huWu baka ganni ba, amma baka ta tawa, Mimi zo ki Wauke shi"

Waiwayawa ta kuma yi, taga da wa yake, sai kuma ta tuna abun da ya ce washegarin kai ta.

Ta tashi ta je Waukar Sabir, yayi ?asa da muryarsa ya ce "For the second time, idan na ce mimi da ke nake, ba zan so Sabir ya tashi ya ji ina faWar sunanki ba" ta jinjina masa kai, ta karSi Sabir.

Ta kalli Ammi ta ce "Ammi, sai a haWo mini kayansa, na tafi da shi ko?"

Ammi ta ce "A'a, ke da zaki koma school, za'a din ga kawo shi, juma'a da yamma, sai a Wauko shi ranar lahadi, saboda ki samu ki yi karatunki a nutse, sannan bayan hadimai biyun nan, baba uwani za ta zauna da ku, saboda ta saka ido a kan yadda zasu din ga gudanar da aiki a gidan, idan komai ya daidaita sai ta dawo, saboda ita ce amintacciyar hadimata".

Babu tsammani rumaisa ta ji gabanta ya faWi, ba ta son baba uwani, kamar ma tsoronta take ji!.




Ayshercool
08081012143
*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*


Rumaisa kasa cewa komai ta yi sai jinjinawa ammi kai, baba uwani kuwa har da shewa tana juyi, tana yi wa ammi godiya da karamcin da ta yi mata, a matsayin wadda za ta je ta yi guiding Win ma'aikatan gidan takawa.

Ammi ta yi wa Adam alamar ya bi ta, ya tashi ya bi bayanta Wakinta, ta kalleshi ta ce "Takawa, na san auren nan ba son ka bane, zaSina ne amma dan Allah ina sake ro?on alfarmarka, ka yi ha?uri da yarinyar nan, komai zai wuce zaka yi alfahari da auren nan, ka ga yarinya ce ?arama, dole za ta yi ta koke-koke na rabata da gida da ka yi, dan Allah ka yi ha?uri da ita. Ko dai wani abun ka yi mata?"

Ware ido ya yi ya ce "Ba abun da na yi mata wallahi".

"A'a takawa, dan Allah ayi ha?uri a bata lokaci, yarinya ce sosai sai ka yi ha?uri"

Adam wata irin kunya ce ta kama shi, ya ji tamkar ?asa ta tsage ya nutse don kunya, ya girgiza kai ya ce "Ban yi mata komai ba"

"Na ji ba wai ina son jin sirrin aurenku ba ne, amma dan Allah ka kula da ita, next week idan Allah ya kai mu za a koma makaranta ko?"

Ya ce "Eh, na biya komai ma, ana komawa zan kaita sai kuma na samo direban da zai din ga Waukota idan bana nan"

Ammi ta ce "To shikenan, Allah ya ?ara buWi"

Suka fito, Ammi ta ce a zubawa su takawa abinci su tafi da shi.

Ammi dai ta lura gaba Waya jikin rumaisa

23 / 67