Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   8 / 67

21K to 24K   out of 199.9K words

Huzaifa ya saka rumaisa a gaba yana ta mata faWa, ta ?i cin abinci sai mita take a kan abun da aka yi mata a unguwa.
Aikowa aka yi wai ana sallama, ganin ba a faWi da wa ake sallamar ba, ya sanya Usman tashi ya fita ya ga waye yake yin sallamar.
Aikuwa yana fita ya tarar da mijin ma?wabciyarsu, ya kawo ?arar rumaisa a kan abun da ta yi musu, na jifa a cikin gida ta yi musu Sarna, ga uwa uba fashewa matarsa baki ada marmara da rumaisa ta yi.

Usman ya ce "Malam shamsu ai Sarnar da matarka ta yi mana ta fi wadda ruma ta yi mata, shiru kawai muka yi, duk yadda ruma take girmamata bai hanata yi mata ?azafi a cikin unguwa ba, ba dan mama ta hana ba, ga kuma albarkacin aure, sai na yi mata wankin babban bargo a cikin unguwar nan, amma tun da abun ya zo da haka, kawai duk sai mu haWu mu yi ha?uri".

Cikin takaici malam shamsu ya ce "Au haka ma zaka ce? Ta rotse mana ?wan lantarki na tsakar gida, ta fashe mana glass ga zubarwa da matata jini, amma ka gaya mini wannan maganar?".

"To me zance maka, yanzu dai idan baka ha?ura ba, kai ma ka tsinto duwatsu ka yi mana jifa a cikin gidan, ko in kirawo maka rumaisa ka daketa ko? Sai ka huce" aikuwa malam shamsu ya harzu?a ya fara zage-zage, Usman kuwa ya zage shima yana ramawa, suka nemi bawa hammta iska.

Mama har ta manta da Usman ya fita, ta jiyo zage-zagen usman, yana idan baa rufe masa baki ba, sai ya falla masa mari, kuma ya Waga shi ya buga da ?asa.

Cikin tsananin faWuwar gaba mama ta taso, hankali a tashe za ta fita, Huzaifa ya ce "Mama ba zaki fita ba, yaya usman bai fiye faWan rashin gaskiya ba, kuma yaya Abubakar yana kusa, na san zai raba"

Mama ta ce "Kai dan ubanka bani hanya, kar ya janyo mini magana, na ji da malam shamsu suke yi, ba zai wuce a kan abun da rumaisa ta yi bane, usman in dai a kan rumaisa ne, ko ba ta da gaskiya goya mata baya yake yi, shi ba ya bin komai a sannu, wani fannin halinsu Waya da ita, zuciyarsu babu afuwa" mama na cikin maganar yaya Abubakar ya shigo hannunsa ri?e da na usman yana yi masa faWa.

Usman ya ce "Haba yaya, mu bamu suka fi yi wa illa ba, sun yi mana ba?in fenti a unguwa, bamu yi magana ba sai shi, wai shi tattabara wanda ya yankewa ?auna cibiya, shi ga mai mata, banzar matar da fuska kamar ba?ar jaka, wallahi da namiji ce sai na yi mata shegen duka".

Rumaisa ta ce "?azama da ita ba, mai bleaching"

Mama ta dungurewa rumaisa kai, Abubakar kuma ya cigaba da yi wa usman faWa.

Usman ya ce "Da ne nake adawa da aurar da rumaisa, amma wallahi yanzu na zubar da makaman ya?i na bi, wallahi party zamu shirya na tashin hankali a unguwar nan, mu hayo dokuna ayi ta kilisa, zamu kaita gidan manyan mutane, mu ga ?arshen munafurci, mu rufe bakin munafukai" ya kalli rumaisa ya ce "Ke, dan ubanki na daina adawa da auren nan, ki yarda kawai, kuma daga yau daga ita har mijinta kar ki sake gaishe su, ta kuma yi miki maganar banza, zan samo miki duwatsu, daga nan har bamfai ba mai shari'a da ke yarinya ce, na tsaya miki ayi da ni".

Mama ta ce "A'a babu ruwana, kai maimakon ka saita yarinyar nan, ku bi komai a sannu amma kana yi mata huWubar tsiya, Nuraini har da kai fa kake zigata take rashin ji, babu ruwanka da mutumin nan ku fita sabgarsu, ni ba zan iya tashin hankali da mutane ba".

Usman ya mi?e ya ce "Mama irin masu ha?urinki ake cuta, komai ki ce ayi ha?uri a barwa Allah, da ha?urinki muka Wauko, muna zaune za a fille mana wuya ki ce mu yi ha?uri"

Dariya rumaisa ta yi, mama kuwa ta rarumi takalmi, ta jefawa usman, ya goce tare da shigewa Wakinsu.

Ruma ta ce "Allah ya biya yaya usy nawa, Allah ya bar mini kai".

"Ki cigaba rumaisa, yayi ta Woraki a keken Sera ya kai ki ya baro, tun da ke dai ba namiji bace ba".


***
Ko da ammi ta koma gida, Nusaiba da Iman suka tareta suna tambayarta yaya suka yi da turaki?
Nan ta kwashe komai ta gaya musu, iman ta ce "Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya mai girma turaki ya shawo kansu komai ya tafi cikin sau?i, ni dai ina sonta wallahi"

Nusaiba ta ce "Mhmm, ni kam kawai yadda za ayi zaman nan nake hangowa, ba fa sa shiri ammi, kin ga ita tana da tsiwa, shi kuma akwai faWa"

Ammi ta ce "Ke rabu da shi, rayuwar aure ta fi ?arfin wasa, idan suka zauna za su nutsu, sannan a rayuwarsa da ita akwai wani darasi da nake fatan ya koya, kuma kan ayi auren ai dolensa ya dinga zuwa wurinta su saba"

Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai rikici kenan?"

Ammi ta ce "Ta bani tausayi Wazu da muka yi waya, wai an ce ta yi cikin shege, ana yi mata kallon ?ar iska, saboda ta zo da sabir, idan ban saka takawa ya aureta ba, shikenan an yi mata mummunan tambari, mutane Wa idan ba na su bane ba, sun din ga janyo masa jafa'i kenan"

Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya shirya, ya tabbatar da alkhairi" suka amsa da amin.

Baba uwani da take laSe ta ji hirar ta su sama-sama, sannan bakomai ta ji ba, amma a abun da ta jin, ta ?udurce za ta je ta sanar da Mummy.


Rumaisa mita a cikinta, kamar an yi mata gori, yau wuni ta yi tana cigaba da mitar abubuwan da ake yi mata a unguwar nan, mama tun tana yi mata nasiha tana cewa ta bar wa Allah, har ta yi mata banza ta ?yaleta, Abdallah ya sakata a gaba yana cigaba da kunnata, tana mita. Bayan fitar Abdallah rumaisa ta shiga Wakinsu, ta duba wurin da yake ajiye fensiransa na zane kasancewar sa architect.

Ta zauna ta nutsu sosai, ta hau zane-zane.

Mama ta ce "Uban me ki ke yi musu a Waki, ki ka shiga ki ka yi shiru?"

Rumaisa ta ce "Bakomai"

"To fito musu daga Waki, tun basu dawo sun tarar da ke ba"

"Mama zan fito ina zuwa"

Sai da ta gama abun da Allah ya nufeta da yi, sannan ta fito ta fice ba tare da sanin mama ba.

Ma?wabciyarsu ta zana, kuma zanen ya fita sosai, ta yi headline da munafukar unguwa, a ?asa ta rubuta by Rumaisa Mahmud ?anwar maza. Ta je ta li?e a ?ofar gidan matar, ta nausa ta tafi gidansu Habiba, ba tare da mama ta san ta fita ba ma.


Ayshercool.

paid book ne, ? 500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
*PAID BOOK NE, ? 500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*




Jin shirun yayi yawa ya kuma sanyawa mama ta ?walawa rumaisa kira, amma har ta kira kusan sau uku shiru, ba ta amsa ba, mama ta kaste abun da take yi, ta fita domin duba me rumaisa take aikatawa ta ji shiru. Sai dai da ta fito tsakar gida babu rumaisa ba alamarta.
Mama ta le?a Wakin ?an maza, amma babu rumaisa ?arshe ma sai shiga Maman ta yi ta kwaso kwanukan ta, da suka kai Wakin suka bar su, ta fito ta duba banWaki da kitchen duk babu rumaisa, tsayawa ta yi tana tunanin ina rumaisan ta tafi ba ta gaya mata ba?.

Tana cikin jimamin in da rumaisa ta tafi babu izininta, shamsiyya ma?wabciyarsu ta yi sallama, ita da wata mata.
Mama ta amsa musu cikin sakin fuska, ba tare da nuna mata ta san ta yi wa ?arta ?age ba.

"Maman rumaisa ni ba zama zan yi ba, ki shiga tsakanina da yarinyar nan, kalli abun da ta yi mini jiya a fuskata, da Sarnar da ta yi mini a cikin gida, maigidana ya kawo ?ararta, ?arshe ba wani mataki da kuka Wauka, sai ma cin mutumci da ya biyo baya, yau kuma ta je ta yi zane ta li?e mini a ?ofar gidana ya ?i fita, wai munafukar unguwa, me na yi muku haka ne?"

Cikin dattaku mama ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri, yaran zamani ne sai godiyar Allah, wallahi da kaina na yi niyyar shigowa na baki ha?uri, wallahi ban san ta yi ba, kin san dai ni ba zan goyi bayan ta yi wannan rashin kyautawar ba, ban san ta yi miki ba, dan Allah dan annabi ki yi ha?uri, bari ta shigo gidan, zan hukunta ta kuma zan sanya ta je ta cire, dan Allah ki yi ha?uri"

"Wallahi banda ina jin nauyinki, Allah da sai na kama rumaisa na yi mata shegen duka".

Mama ta ce "Ashsha, ba za ayi haka ba, ai ke ma ?arki ce, yanzu kina taSata komai zai Saci, yayyenta ba sa ganin laifinta, amma dai ina baki ha?uri, da kaina zan hukunta ta, kuma zan aikota ta baki ha?uri".

Haka Jamila ta yi ta farfaWar maganganu, mama tana bata ha?uri, da alwashin hukunta rumaisa, bayan tafiyarta mama ta dafe kai, haryanzu rumaisa babu alamar hankali a tare da ita, tuno damben da suka sha da ?ar ajinsu ta yi, abu har wurin ?an sanda saboda wannan shegen zane-zanen da take yi, shi kansa Abdallah dan ba yadda za ta yi da shi ne, abun da yake karanta kenan, ga rumaisa na neman gadarsa, in dai zane-zanen banza da na wofi ne, a litattafan makarantar ta ma yi take.

Mama ta rasa mai ma yakamata ta yi, ba ta san ta ina zata fara neman rumaisa ba.

Rumaisa kuwa gidansu habiba ta tafi, suka shantake suna ta hira, ta bawa habiba labarin abun da ta yi wa ma?wabciyarsu.
Habiba ta ce "Kin mini daidai, da nice ba zan iya ba, tsoro nake ji, kin ji yadda matar nan ta din ga yayata maganar nan a cikin unguwar nan, ummanmu ce ta fara taka mata burki ta ce ?arya take yi, daga nan ta je ta gayawa mamanku"

Rumaisa ta ce "Hmm, ai sai ta gane ba ta da wayo kan ma bar unguwar nan, da ina mutunta ita da mijinta, amma tun da ta taSo ni, za ta gane bata da wayo"

Cikin rashin fahimta habiba ta ce "Ki bar unguwar nan ki koma ina?"

Rumaisa ta Wan yi jimm, sannan ta ce "Ke share kawai, na san zuwa yanzu wata?ila ta je ta kai ?arata gidanmu"

"Me ki ka yi mata?"

Cikin ?warin gwiwa rumaisa ta ce "Zanata na yi, na rubuta munafukar unguwa, na li?e mata a ?ofar gida, na san yau za a azabtar da ni a gida, amma ba zan koma yanzu ba"

Habiba ta ce "Wai ruma ba kya jin tsoro ke? Mama ba ta san kin zo nan ba?"

"Ba ta sani ba, idan aka kai ?arata ina gidan, a gabanta mama zata bani rashin gaskiya, duk da abun da ta yi mini, zuwa yanzu kuwa na san ta tafi, in koma gida a haWani da mai sunan baba, ya bani gwale-gwale"

Dariya habiba ta yi ta ce "Wato ke har ma kin san me za ayi miki, ina yaya Aliyu?"

Rumaisa ta yi mata kallon ?asan ido ta ce "Yana makaranta, in ce kina nemansa ne?"

Habiba ta waro ido ta ce "Ke a'a, kawai dai tambayarsa na yi"

"Meyasa duk cikin yayyena shi ki ka sani?"

Habiba ta ce "Bakomai, ya na da kirki ne"

Rumaisa kawai ta yi dariya, tana lissafa yadda zata wanye da mama idan ta je gida.

Mama kuwa sai kallon agogo take yi, tana lissafa, ina rumaisa ta tafi haka? Ta ?i dawowa, zuciyarta ta bata saboda abun da ta aikata ne ya sanya ta fece.

Kasancewar azahar ta yi, kuma juma'a ce ya sanya ?an samarin mama dawowa gida, domin shirin masallaci, kuma aka yi sa'a ana public holiday, rumaisa ba makaranta ta je ba.

FaWan Abdallah mama ta jiyo, yana faWin "Uban waye ya taSa mini kayan zanena, bana son rashin mutunci, Huzaifa ban hanaku taSa mini kaya ba?"
Huzaifa ya ce "Ni na iya amfani da wannan abubuwan naka ne? Sai dai ko Yasir"

Yasir ya tari numfashin Huzaifa ta hanyar cewa "Saboda ni ka raina ba, yaushe na zauna a gidan balle na taSa masa kaya".

Mama ta fita tsakar gida ta ce "Ba aikin kowa bane, rumaisa ce ta taSa maka, ita ta shiga Wakin ta yi shiru, ita ce ba wani ba".

"Tana ina, sai ta ci ubanta yau sai na zaneta, har da gum Wina ta buWe ta bar mini a buWe"

"Hmm, wannan yarinyar ai sai fatan shiriya, ina fatan Allah ya sanya auren nan ne mafi alkhairi, ko yau aka ce za ayi zance a Waura su tafi da ita"

Abdallah ya ce "Tana ina?"

Mama ta ce "Ina na sani, ta yi wata aika-aikar ta gudu, ban ma san ta fita ba".

Yasir ya ce "Kai wannan yarinya, Allah ya yi mata maganin abun da yake damunta yake sanyata rashin ji".

Rumaisa ba ta tashi tafiya gida ba, sai da unguwa ta yi tsit, duk an tafi masallaci, sannan ta nufo gida, cikin shirin karSar kowane irin hukunci za a yanke mata.

Da sallama ta shiga gidan, ta yi sa'a mama tana salla, ta lallaSa ta shiga Wakin ta zauna, tana jiran mama ta idar, ta shirga mata ?aryar da zata kare kanta.

Mama tana jin motsin rumaisa, amma ta shareta, ko da ta idar da sallar ma ta yi lazumi, ba ta tankawa rumaisa ba.

Cikin tsoro rumaisa ta ce "Mama" banza tayi da ita ta shige uwar Waki ta bar rumaisa.

Tun rumaisa tana War-War har ta Wan saki jikinta, da ta ga mama ba ta da niyyar kulata.
Sai dai ba ta ankara ba, mama ta shammaceta, ta janyota ta din ga Wirka mata dundu.

Ihu rumaisa take yi, tana neman agaji rabon da mama ta daketa har ta manta.

Tun daga waje Yaya Abubakar ya jiyo ihun rumaisa, a soro ya yasar da sallaya, ya shiga da gudu, ya tarar da mama ta samu mafici, tana jibgar rumaisa tana yi tana haWawa da hannunta.

Ai da hanzari ya ?waci rumaisa yana faWin mama lafiya.

"Rabu da ni, yau yarinyar nan ta kaini bango, rumaisa a rayuwarta ba zata bari na huta ba, daga wannan sai wancan, gidan ubanwa ki ka tafi?"

Cikin kuka rumaisa ta ce "Gidansu habiba"

"Gidansu habiba gidan ubanki ne? Wato kin san abun da ki ka aikata ko?, To fita ki je ki bata ha?uri, ki cire takardar da ki ka li?e mata a ?ofar gida, tun kan na murWe miki wuya ki mutu in huta, da Waukar maganar da ki ke yi, kullum nike nan cikin bayar da ha?uri da faWa da mutane saboda ke?
Bari na kira babar adam Win a waya, idan sun shirya ko jibi su zo a Waura auren nan na huta na gaji" Rumaisa ta yi fici-fici da ido tana kuka.

"Ba zaki fice ki je ki bata ha?uri, ki cire abun da ki ka li?a mata ba?" Ruma ta fita da sauri, tana jin haushin sake kai ?ararta da matar ta yi.

Ta je ta yi iya ?o?arin ta, wurin cire cardboard paper da ta yi zanen a jiki, amma gum Win da ta yi amfani da shi ya kama sosai, dan haka ta samo wata ?usa, ta dinga durzawa takardar, ta haWa da sabon fentin da aka yi wa ?ofar duk ta kankare abun ta, sannan ta shiga cikin gidan matar.

Ta tsaya daga soro ta yi sallama, matar ta amsa sannan ta fito, ta sakawa bakinta da goshinta shanshanbale, in da rumaisa ta fasa mata da dutse.

"Kin kai ?arata, mama ta ce sai na zo na baki ha?uri, na cire takardar da na saka miki, na cire takarda, idan ki ka kuma kai ?arata zan yi miki abun da baki zata ba, kuma wallahi ban yafe miki ba sharrin da ki ka yi mini, wuta balbalin bala'i, idan baki nemi yafiyata ba, sai kin ga abun da Allah zai yi miki, kayan da ki ke sayarwa ma sai an daina siya" tana gama maganar ta juya ta tafi.

Da sauri ta biyo bayan rumaisa, sai dai tana zuwa ta tarar da sabuwar ta'asar da rumaisa ta ?yan?yasa mata a ?ofar gida, ta kankare tsakiyar ?ofar da ?usa, duk fentin ya fita ga sauran takardar ba ta gama fita ba, gaba Waya ta sauya fasalin ?ofar.

"Na shiga uku ni Jamila, wace irin masifa ce wannan, fentin ?ofar da bai fi sati da yi ba ki ka dirje?".

Rumaisa ta waiwayo ta kalleta ta ce "Idan baki gaji ba, yanzu ma ki je ki kai ?arata, zaki sha mamakin abun da zan yi miki next"

Ta shige gida tana sunkuyar da kai, mama ta kalleta a fusace ta ce "Kin bata ha?urin ko kuwa?"

"Na bata" ta amsa tana sunkuyar da kai.

Aliyu ya kalli rumaisa ya ce "Allah ya shiryeki ruma, ke ko gajiya da Waukar magana ba kya yi, kullum ayi ta yi miki faWa, daWi yake yi miki ko?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"Zo ki karSi kuWin nan ki sayo mini milo a kantin malam lawan, zan sha shayi bana son cin abinci" kallon yaya Aliyu ta yi, kamar tana hararsa ya ce "Ni ki ke yi wa wannan kallon, ko ba zaki ba?" Ta dur?usa ta Wauki kuWin, ya ce "Ki taho da manja kwalba Waya, na ga wanda muke da shi ya kusa ?arewa".

Ita dai ba ta amsa masa ba, ta fice ko da ta fita a ?ofar gida ta hangi shamsiyya da mijinta, suna duba ?ofarsu da ta dirje, ba ta kula su ba ta tafi shagon.

Malam lawan mai kanti, yana ta yi mata wasa yana tsokanarta, amma ta share shi, ya auna mata manjanta, ta fito. Sai dai tana fitowa ta yi karo da wani tantirin Wan daba da ya addabi unguwarsu, wanda har kisan kai yayi, amma aka sake shi.

Ya kalli rumaisa ya ce "Ke, karSo mini sigari a cikin shagon nan"

Tsaki ta yi, zata wuce, ya sake daka mata tsawa ya ce "Ke, na ce ki karSo mini sigari a cikin shagon nan"

"Na yi maka kama da ?ar iska, ni ce ma zan taSa sigari saboda wula?anci, to ba zan karSo ba"

8 / 67