Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   24 / 67

69K to 72K   out of 199.9K words

a sanyaye yake, har ta fara tunanin ko takawa dai yayi mata wani abun ne.

Ammi ta zauna a kusa da ita, ta yi ?asa da muryarta ta ce "Rumaisa, ko akwai wata matsala ne?"

Ruma ta girgiza kai alamar a'a.

"To ki yi ha?uri kin ji, zaki saba ne haka aure yake, ki yi ha?uri, duk abun da yayi miki wanda bai yi miki ba ki gaya mini. Sannan su nusaiba sun gaya mini abun da ya faru washegarin kai ki, shi ma ki yi ha?uri ki kawar da kanki, na san zaki fuskanci ?alubale, amma ki dake. Kar ki yadda da duk wata mata da zata nuna tafi kowa ?aunarki ko ta shiga jikinki, kuma kar ki sake ki gaya wa wani sirrin aurenki, duk abun da zai yi miki, ba zai yi wanda zai cutar da ke ba, na ja masa kunne sosai da sosai, idan yayi miki abun da ba dai-dai ba, ki gaya mini. Kar ki saki jiki da kowa, sai mijinki ko kuma ni da ?annensa zama a masaruta sai ka iya allonka, ki yi ha?uri kin ji rumaisana".

Ruma ta ce "To Ammi, in sha Allah "

Har gaban mota ammin ta rakasu, suka shiga suka tafi.

Tun kan su yi nisa ta fara sana'arta ta barcci, ya taSata ya ce "Idan ki ka yi bacci, sai dai ki kwana a mota, dan ba Waukar ki zan yi ba" da haka suka ?arasa gida ta yi sallar isha'i, ko abincin ba ta ci ba ta kwanta.

Washegari da safe, ta tashi tana Wan goge gogenta, ta fito falo tana ta goge tiles Win.

Adam ya fito cikin suits da jakarsa, da alama aiki zai tafi, ta yi masa ?uri da ido, ba ta yi magana ba.

"Baki iya gaisuwa bane?"

Ta Wauke kanta daga kallonsa ta ce "Ba amsawa ka ke yi ba"

"Yes, ba kya gaisheni yadda ya dace ne, ki bar wannan aikin babu wanda ya saka ki, anjima masu aikin da ammi ta ce za su zo, idan da wani abu su gyara miki.
Ga breakfast can a kan dining, in anjima zasu fara aiki, zan sayo kayan abinci, ko kina bu?atar wani abu?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki zauna wuri Waya, banda taSe-taSen abun da ban saka ki ba".

"To sai yaushe zaka dawo?".

"Lokacin da Allah ya yi".

"Ni dai ka dawo da wuri, tsoro nake ji"

***
Gidansu rumaisa kuwa, mama ce ta hana kowa zuwa gidan, saboda ta san halin rumaisa, ta ce idan suka je kuka za ta yi ta ce zata biyosu. Sai dai ba a cikakken awa guda, ba ayi zancenta ba a gidan.

Kasancewar bayan mai hoton da Sangaren su Adam suka Wauko, Abdallah ma ya Wauko mai hoto, aka turo masa hotunan bikin rumaisa, bai yi ?asa a gwiwa ba, ya tura su group Win su, na ?an gidan.

Mai sunan baba yana kasuwa, da yake bayan makaranta ya kan Wan shiga kasuwa, hotunan suka shigo.
Suna da yawa ya sauke su, ya fara buWewa yana kallo, yana kallo yana murmushi yana jin yadda ya yi kewar ?anwarsa.
Babu tsammani ya ci karo da hotonsa shi da iman, rumaisa kuma a gefensu, ya wuce hoton da sauri, amma ya kuma karo da hoton iman Win, na ranar bridal shower, ta yi wani irin kyau na musamman.
Zuciyarsa ta tsananta bugawa, kuma ya kasa wuce hoton nata, ba shiri ya rufe wayar, ya saka a aljihunsa yana ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi gudu.

***
"Wallahi Adam na yi mamaki da har ka iya Soye mini al'amari mai girma kamar wannan, menene a ciki idan na san wannan yarinyar zaka aura" Jabir yayi maganar cike da ?orafi.

Adam ya ce "Koma menene bai kamata ka ji haushi ba, yanzu ba gashi ka ji ba, ko da yake gara kai a kan Jamil, ni Jamil zai Wauki gaba da ni, ya?i zuwa wurin Waurin aurena, ni na karSi ?addarata dan meyasa shi ba zai Wauka ba".

Jabir ya ce "A'a takawa, so so ne fa, amma son kai ya fi, Samha ?anwarmu ce ga ta gida, amma ace ka auro wata a waje, wadda ba ta kaita komai ba, babu daWi".

"Amma har ya kai ayi gaba da ni saboda hakan? Meye aibun rumaisa idan aka kamanta shi da abun da ta yi mini na sadaukarwa, bai kamata gaba Wayanmu idonmu ya rufe ba, idan akwai rabo a gaba sai ka ga na aureta, amma a yanzu ban zaci haka daga Jamil ba, amma zan shiga wurin aiki, zamu haWu da shi mu yi magana"

Jabir ya ce "To shikenan, har ka gama amarcin kenan ka fito, bai yi wuri ba komawarka aiki ba kuwa?"

Adam ya yi murmushi ya ce "Bai yi ba, ita ma sai a bar ta ta huta. Kai ni har mamaki nake yi yadda kai? ba a saka maka ido ba, ko auren fari ba ka yi ba, amma ba ruwan wani da kai, duk mu aka sanya wa ido"

Jabir ya yi dariya ya ce "Bayan ka ce ba zaka bani iman ba, ai ni na zaci kai zaka aureta"

Adam ya Wan Sata fuska ya ce "Please mu bar wannan zancen"

Jabir ya ce "Shikenan, tun da baka so"

***
Rumaisa ta rasa abun da yake yi mata daWi, zaman shirun nan duk ya isheta.

Ta saman benen take kallon harabar gidan, da gidajen da ke ma?wabtaka da nata, duk manyan gidaje ne, sannan kowane gida a rufe yake, ko gilmawar mutane ba ka gani, sai dai a cikin mota.

Mai gadin ta ga ya tashi ya buWe gate, nan da nan ta fara murna ta yi ba?i.

Ta koma Wakinta da sauri, ta saka hula a kanta, ta fito, sai dai ta yi turus lokacin da ta ga baba uwani, da wasu matasan mata guda biyu.

Jiki a sanyaye ta ce musu "Ina wuni?"

Baba uwani ta yi murmushi ta ce "Ranki ya daWe ai mu zamu gaisheki, barka da wannan lokaci? Mun same ki lafiya?"

"Lafiya ?alau" ta amsa a Wan tsorace.

"To kamar yadda giwa ta yi miki bayani jiya, ga ma'aikatanki nan, sannan kuma ni ce cikon ta ukun, zamu zauna tare da su a nan, na din ga lura da yadda zasu gudanar da aikin".

Rumaisa ta ce "To sannunku".

Baba uwani ta ce "Yauwwa, wani Wakin zamu zauna, da kayanmu muka zo".

"Ku zaSi duk wanda ku ke so" rumaisa ta yi maganar tana kallonsu.

Ta nemi wuri ta zauna a falo, baba uwani ta za?e ta fara dudduba Wakunan da suke saman benen.

Ta shiga Wakin rumaisa, ta ?are masa kallo, ta fito tana faWin "Allah ya taimake ki, ashe an shirya miki kayan, ko takawan ne ya shirya miki su?"

Rumaisa ta ce "A'a ni na yi"

"Masha Allah, to bari Wauki wancan Wakin, tun da na ga Wayan kamar babu kowa a ciki"

Ita dai rumaisa ba ta ce komai ba, ta ?are ta shiga kitchen tana dudduba kayan kitchen Win Rumaisa.

Ganin sun isheta da kallo, sauran mata biyun da ko sunayensu ba ta sani ba, ya sanya ta tashi ta koma Wakinta.

Ta buWe window ta cigaba da kalle-kallenta, ta hango baba uwani a bayan gidan, tana waya. Ba ta jin mai baba uwani take cewa, sai dai da alama kamar wayar ta ta ta sirri ce.

Baba uwani kuwa cikin ladabi take waya da Samha.

"Ki buWe kunnenki da kyau ki saurareni, bana son a samu kowane irin akasi a kan aikin nan, ki zuba mini ido sosai, duk abun da yake faruwa ki din ga sanar da ni, ina fatan kin gane?"

"Na gane ranki ya daWe, duk abun da ki ka ce in Allah ya yarda zan yi, zan zuba ido sosai da sosai"

Samha ta ce "Yayi kyau".


Da la'asar Adam ya dawo, rumaisa ma sam ba ta san ya dawo ba, saboda wunin Waki ta yi, ko haWa hanya ba ta son yi da baba uwani.

Gyaran murya ya yi, hakan ya sa ta waiwaya ta ganshi a tsaye.

Ya shiga Wakin ya ce "Me ki ke yi ke kaWai a Waki?".

"Bakomai"

"Ke ki ka ce wa baba uwani su zauna a Wakin saman nan?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce "To na ce su koma ?asa, ba haka ake yi ba. Ga kayan abinci can na sayo, na zuba a kitchen Win ?asa, zasu din ga girki suna kawo mana, sannan zasu din ga yin duk wani aiki na gidan nan, banda gyaran Wakina, ke zaki din ga wannan ai kin iya ko?" Ta jinjina masa kai.

"Bana son body language, amsa mini zaki yi"

"Eh na iya".

"Good, ki fito zan nuna miki abu".

Ta tashi ta bishi, zuwa kitchen Win saman benen.

Ya nuna mata kayan tea, manyan gwangwanayen madara da na milo, kayan biscuit na ciye-ciye da sauransu.
Sai cartons na lemuka, da kayan marmari ya ce "Gashi nan, wanda zaki kai Waki ki kai, wanda za su saka miki a fridge kuma sai ki nuna musu".

"To an gode" ta faWa a sanyaye.

Gani yake yi kamar an sauya rumaisa, duk wannan tsabar rashin jin da tsaurin ido, duk ta yi sanyi, sai dai a ransa ya ce ba a yabon Wan kuturu.


Kasancewar tun a yau su baba uwani suka fara gudanar da ayyukansu, sun yi abincin dare, suka kai wa su rumaisa sama.

Ruma ko kallon abincin ba ta yi ba, ta din ga cin kayan marmari, sai da ta ji ta ?oshi.
Ta haWa madara da milo, fal a kofi ta tafi da shi Waki, ta din ga sha ta gaji ta ajiye sauran ta yi bacci.

Ba ta san ma Adam ya dawo ba, sai da asuba ta ji yana babbuga mata gefen gado ta tashi ta yi sallar asuba.

Ta buWe ido ta kalleshi ya ce "Ke ba kya iya tashi salla dole sai an tasheki ne? Kuma haka ki ke kwana da fitila a kunne?"

Ba ta ce komai ba shi kuma ya fice. bayan ta yi sallar, ta Wan yi baccin safe ta tashi, ta shiga banWakinta, yanzu duk ta san yadda ake amfani da kayan toilet Win, da idan za ta yi alwala, sai ta kunna hot water ta fara, tana tsaka da yi, ta ji ruwan zafi yana ?ona ta, yanzu kuwa duk ta gane kansu.

Wankanta ta yi a nutse, ta fito tana goge jikinta da ruwa, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta.

Baba uwani ta yi sallama, da kayan mopping a hannunta.

Rumaisa ta razana tana neman hijjabi ta saka, kasancewar daga ita sai towel.

Baba uwani ta ce "Haba ranki ya daWe, ai na haifeki, meye na damuwa kuma, gyara miki Wakin zan yi".

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ki bar shi kawai zan gyara da kaina, kaya zan saka".

"Ki saka kayanki kawai, aikina zan yi".

A Wan hasale rumaisa ta ce "Ki bar shi kaya zan saka".

Ta kalli rumaisa, ba wata uwa a jikin nata sai tsirfa. Ta juya sumi-sumi ta bar Wakin.

Guntun tsaki rumaisa ta ja ta ce "Wannan mata meye damuwarta ne? Bana son shishshigi", rumaisa ta saba yawonta a gidansu, babu suturar kirki ba ta damu ba, amma ba ta yadda wani na waje ya ganta ba. A gaggauce ta saka kayan, tana son ta yi magana da adam Kafin ya fita.

A falo ta tarar da adam yana danna system, babu alamar zai fita yau.

"Ina kwana" ta faWa ba dan ta na tsammanin ya amsa ba, aikuwa bai amsa Win ba.

Ta Wora da cewar "Dama, tambayarka zan yi, yau tun da juma'a zaka Wauko mini Sabir Win, ammi ta ce za a din ga kawo shi, juma'a zuwa ranar lahadi, sannan dan Allah ka kira mini yaya Aliyu a waya, dan Allah su zo".

Ya kalleta ya ce "Da ni ki ke ko da system Wi na, ko akwai wani bayan ni a nan?" kallonsa ta yi da mamakin rainin hankalin da ya yi mata ta ce "Da kai nake mana".

"Bani da suna ne ko yaya?"

Rumaisa ta ce "Ka na da shi".

"Ok, ya sunana?" Yayi maganar yana tsareta da ido.

Har ta buWe baki za ta ce Adam, sai ta ji sunan yayi mata nauyi a bakinta, gashi ya tsareta da ido, yayi mata kwarjini sosai.

"Papa" ta faWa a hankali.

Adam ya ce "Waye hakan?"

"Saboda Sabir, na ji ya fara koyar faWan sunanka"

?an rausayar da kai ya yi, a ransa ya ce "Ashe kina da hankali wasu lokutan '.

A zahiri kuma ya ce "Me ki ka yi wa baba uwani, na ga ta fito daga Wakinki, kamar ranta a Sace?".

Ta Wan tura baki ta ce "Ba abun da na yi mata"

"Bana son ?arya"

"Ba ?arya nake ba, zuwa ta yi wai za ta gyara mini Waki, ni kuma daga wanka na fito ban saka kaya ba, kawai cewa na yi ta bar shi zan gyara da kaina shikenan fa"

"Ba ta haifeki ba, me za ta gani?"

Da sauri ta kalleshi ta ce "TaS, ni wallahi ba zata ganni ba".

"To me za ta gani?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba.

Ya girgiza kai ya ce "Kasancewar ta na yi miki aiki, ba ya na nufin ki rainata bane, ita ce babbar hadimar ammi, muma muna girmamata. Ga abinci can sun girka, ki je ki karya".

"Na ?oshi" ta faWa cikin jin haushi, dan ita ba ta ga abun da ta yi wa baba uwani ba.

"Kin ?oshi saboda me?"

"Ni so nake na din ga girka abincina da kaina, ammi ta ce kar na yarda da kowa, kar na je ayi mini aisiri a cikin abincin"

Tattara hankalinsa ya yi a kan rumaisa sanannan ya ce "Waye zai yi miki asirin?"

Ta ce "An ce a gidan sarauta ana asiri, dan haka ni ba zan ci wannan abincin ba".

"Ai dama me hali baya fasa halinsa, kin huta, sai dai idan ba zaki ci abinci a gidan nan ba, idan ki ka sake na ganki a kitchen da sunan zaki yi girki, sai na saSa miki, ba zaki haWa mini gobara a gida ba, kuma ki cigaba da ina magana ki na yi mini gatsali, zaki ga yadda zamu yi da ke"

Ya mayar da hankali a kan system Win sa.

Jin sa kawai take yi, amma ta yi wa kanta al?awarin ba za ta ci abincin nan ba.

Ya tashi ya shiga Wakin sa, ya fito da mukullin motarsa, ya fice ba tare da ko kulata ya yi ba.

Yana fita ta sauka ?asan benen, ta tarar da su baba uwani suna aikace-aikace.

Tana ganin rumaisa ta saki fuska tana faWin "Uwar Wakina, sannu da fitowa, kina bu?atar wani abun ne?"

Rumaisa a ran ta ta ce, ji matar nan kamar ba yanzu ya ce ta fito ranta a Sace ba.

"Bakomai, Takawa ne ya ce mini, kin fita daga Wakina ranki a Sace, kamar baki ji daWin abun da na yi miki ba, ki yi ha?uri dan Allah. Sannan zan din ga yin aikin saman, zan din ga gyara komai".

Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar Wakina, ai zamanki muke yi, kar ki damu dolenmu mu gyara miki, ai ke hutuwarki kawai zaki din ga yi"

Ruma ta ce "A'a na iya aiki, zan din ga yi da kaina". Baba uwani ta bi rumaisa da kallo, ta shiga cikin kitchen Win, ta Webi indomie, da abubuwan da take bu?ata.

"Indomie zaki ci? Ko in turo barira ta dafa miki".

"A'a na iya girki" ta juya ta nufi stairs.

Mamaki ne ya cika baba uwani, sai a yau ta fuskanci yanayin rumaisa fetsararriya ce.

Ko da rumaisa ta je kitchen Win ta na saman bene, babu gas a cylinder ta, dan haka a kan electric ta dafa indomie da tea ta zauna a kitchen, ta ci kayanta, ta yi wanke-wanke.

"Ke amarya kina ina ne" ta ji muryar Aliyu a bazata.

Da gudu ta fito falon, ta Wane jikin Aliyu tana murna.

Shi da mai sunan baba ta gani, ta saki Aliyu ta nufi mai sunan baba.

Murmushi yayi ya ri?eta da hannu Waya ya ce "Ya kike?"

Take ta fara kuka ta ce "Yaya shi ne ku ka ?i zuwa"

"To yanzu ba gamu ba, idan kuka zaki yi zamu koma".

Ta share hawayen ta ce "na daina"

Zama suka yi Aliyu yana ta kallonta yana "Inyee amarsu ta ango, to yanzu ma mama ba ta san zamu zo ba, wai kar mu saka ki kuka, yaya Umar ya ce mu zo mu ganki"

"Aikuwa kuka na din ga yi, yau ne kawai ban yi kuka ba".

Aliyu ya ce "Ke, na ga wasu mata a ?asa su waye?".

Rumaisa ta ce "Wai hadimai ne, su suke aikin gidan".

"Saboda me, ke baki iya bane?".

"To ya zan yi, ammi ta ce gidan yayi mini girma ba zan iya aikin nikaWai ba".

"Ke, wannan dattijuwar za ta yi saka ido, kamar mara gaskiya kin ga yadda ta din ga binmu da kallo, wai su waye mu daga ina muke?"

Rumaisa ta ce "Ni ina ruwana, tun da ba a kaina suke ba".

Mai sunan baba ya ce "Da ruwanki mana, ki dai kula da kan ki sosai ".

Sallamar iman ce ta kaste musu hirar, rumaisa ta ce "Yeee, yau ba?ina da yawa"

Idonta bai sauka a na kowa ba, sai cikin na mai sunan baba.

Da sauri ta dur?usa ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ?alau " ya amsa yana kawar da kansa.

Ta gaida Aliyu ma, ya amsa mata cikin sakin fuska.

Rumaisa ta karSi Sabir tana murna.

Kamar kullum, tsoro da fargaba ya mamaye iman, kasancewar, mai sunan baba a wurin.

"Anty iman, na zaci ba za a kawo shi ba fa".

"A'a za a kawo shi, amma ba bar miki za ayi ba, sai an haWa masa kayansa tukuna".

Zuwan Iman ya sanya mai sunan baba tashi ya cewa Aliyu su tafi.

Kamar rumaisa ta yi kuka ta ce "Mai sunan baba baku daWe ba fa".

"Eh, ai mun zo dai, tafiya zamu yi sauri muke yi "

Iman ta ce "Idan saboda ni ne, bari in tafi, takawa ya mayar da sabir Win".

Ta yi maganar tana tashi.

"Meyasa zamu tafi dan kin zo? Nemi wuri ki zauna ba zama zamu yi ba dama" ya mayar da idonsa kan rumaisa ya ce "Take care"

Daga haka yayi wa Aliyu alamar su tafi, rumaisa ta ce zata rakasu, amma ya ce ta yi zamanta, ya ajiye mata kuWi, suka fice.

Kuka rumaisa ta yi ta yi, iman tana rarrashinta, ita kan ta tana mamakin irin halina bawan Allah nan.

Kasancewar iman na nan, ga kuma Sabir, ya sanya rumaisa ta ha?ura, suka shiga kitchen ita da iman suka yi girki, iman ta tayata ta Webo wasu daga kayan abinci daga kitchen Win ?asa zuwa na sama.

Iman ta din ga mamakin

24 / 67