Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   32 / 67

93K to 96K   out of 199.9K words

ta yi, ta ce "Na shiga uku" har da haWawa da gudu, ta bar masa falon.

Shi a zahiri ma ba film Win yake kallo ba, yanzun ma fitowa ya yi, domin ragewa kansa damuwa, da kaWaici, atleast ya Wan ji releif kaWan, ya saka a ransa zai yi mai yiwu wa, wurin bin shawarar Bashir, ya saki jiki da rumaisa su samu kusanci sosai da sosai.

Har dare, ba ta sake yadda sun haWu ba, dan ya gama ba ta kunya gaba Waya.

Har Waki Asiya, ta kawo mata uniform Win ta, an wanke wanda ta cire an goge mata su.

Ta karSa ta yi wa Asiya godiya, ta cewa Asiya dan Allah ta dafa mata indomie, dan ba za ta fita ta haWu da adam ba.

A Wakin ta bar kwanun, ta yi sallar isha'i, ta hau aikin nata na bacci.

A cikin mafarke-mafarkenta, da ta saba yi, yau ta ga Mummy ri?e da sar?ar da take yawan ganin an WaWWaure adam da ita, yau ta ga mummy ri?e da sar?ar, ta hankaWa adam cikin wani rami.

Ba ta san ya aka ?are ba a mafarkin, ta tsinci kanta a tsaye, tana ta haki zuciyarta na bugawa da sauri.

Da sauri ta fita daga Wakin, ta tafi na takawa, ta tarar da shi ya na bacci.

Kuka take yi sosai, tana dukan pillown sa, "Ka tashi"

Kasancewar baccin na sa ba nisa ya yi ba, ya farka, dan bai daWe da yin baccin ba.

Da fari ya zata ko ciwon marar ne, ya tamabaye ta lafiya?.

"Ni tsoro nake ji".

"Tsoron me kuma?"

"Ni dai tsoro nake ji" ta yi maganar tana kuka.

Ya tashi zaune ya ce "To zo ki kwanta a nan" ba musu ta haye gadon nasa, ta kwanta, ?arshe dai har asuba bai samu ya yi bacci ba, ita ma kawai bakan ta yi, amma idonta biyu..

Sai dai tun lokacin da ya tashin, yake jin kamar an zare masa lakar jikinsa, ya fita masallaci, ta sauka daga kan gadon ta koma Wakinta, tana ta addu'a a zuciyarta.

Sai dai kamar jiya da safe, walwalarsa ta sake Waukewa, bai ko karya ba, ya tafi kaita makaranta, sai dai a tu?insa kawai, ya isa ka fuskanci lallai akwai matsala. Ta yi masa a dawo lafiya ya jinjina mata kai ya tafi.

Sai dai ita ma ta shiga cikin tunani, tun da Allah ya sa ta ga Mummy, take yawan mafarkinsu tare da takawa.

Ikon Allah ne kawai ya kai shi wurin aiki, dan ko gani ba ya yi sosai.

Tun da ya shiga office, jiki yake nema ya rikice, ya rufe kansa a ciki, yake ta fama da matsanancin ciwon kai.

Bai iya aikata komai ba, ya kunna karatun Alkur'ani a wayarsa, ya ajiye dan idan ya shiga wannan yanayin ba ya iya karanta komai.

Ya daWe a haka, kan a hankali ya fara samun nutsuwa, ya Wau wayar, ya kira Jamil a waya, ya ce dan Allah ya zo office Win sa.

Ko mintuna biyar ba ayu ba sai ga Jamil, ya na ganin adam ya ruWe ya ce "Lafiya kuwa? Ba ka da lafiya ne?".

"Bana jin daWi ne, dan Allah so nake ka kaini gida wurin ammi, ba na son kowa ya san halin da nake ciki, bana son ayi ta mun sannu, ko azo a zagayeni ban san me zai iya faruwa ba".

Jamil ya jinjina kai, ya Waukar masa wayoyinsa, ya rungume shi suka fita.

Ko da suka je can gida, adam ya yi garajen buWe ?ofa ya fita, ya faWi a wurin. Dai-dai da shigowar motar hajiya jamila da Hajiya Lubabatu.

Saukkowa suka yi, suka nufi adam tare da ma'aikatan, suna tambayar ko lafiya.

Jamil ya ce "Bashi da lafiya, ya ce na dawo da shi gida, kuma ya faWi".

Haka aka kama adam, zuwa cikin gida sashin Ammi.

Ammi ba ?aramin tsorata ta yi ba, rabon da haka ta faru an kwana biyu, dan an samu kyakkyawan cigaba a lamarin lafiyar Adam.

Kamar gawa haka aka kwantar da shi, a bedroom Win ammi, su Mummy suka je suka tsaya a kan sa suna yi masa sannu.

Tamkar wanda aka mintsuna, ya fara daddagewa jikinsa ya na rawa, yana dan?ar bedsheet Win kan gadon, yana girgiza kai.

"Ammi, Ammi! Jikina ki danne ni" ya din ga maganar cikin Waga murya.

Tuni hawaye ya cika idon ammi, ta ce "Sannu Allah ya baka lafiya".

Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kai wannnan lamari, ni abun nan na rasa gane kansa, Wannan wace irin larura ce?".

"Ammi! Ana kakkarya ni fa, Ki zuba mini ruwan sanyi a jikina" yayi maganar yana neman abun da zai ri?e.

Jamil ya ce "Takawa, ka yi addu'a Allah ya baka lafiya".

Hajiya Lubabatu ta ce "Jamil yo baya fa, kar ya yi maka illa, ko ka manta abun da yake yi, idan ciwon ya tashi haka?"

Gaba Waya suka tsaya daga baya, sai ammi ce ta zauna a kusa da shi, tana cigaba da yi masa sannu, su iman duk suna makaranta, da ma daga ita sai sabir.

Kan ka ce kwabo, sai ga samha ta shigo tare da Fauziyya, suna sashin Mummy, Mahmud ya gaya musu.

Samha na zuwa ta ganshi jikinta ya yi sanyi, ta na jin labarin rashin lafiyar sa, tun suna yara, wasu lokutan abun ya kan tayar masa, amma ba ta taSa tunanin abun ya kai haka ba.

Ya na cikin wannan halin, ya koma cewa "Rumaisa! Ammi a Waukkota daga makaranta, kar wani abu ya sameta. Rumaisa! Ammi Rumaisa".

Jamil ya ce "Ka kwnatar da hankalinka, wace makarantar ce, in je in Waukkota".

Mummy ta ce "Takawa ka na ta kanka, kana ta wata daban, ka yi addu'a, fatanmu ka samu lafiya"

"Ammi rumaisa" ya sake nanatawa.

Haushi ne ya ?ule Samha, kamar ta buWi baki, ta ce Allah ya tsinewa rumaisan.

Ammi ta gaya wa Jamil makarantar, ya fita da sauri ya Wau mota.

Mahmud kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, atleast ya na son jin ya jikin Adam, a wani situation yake, abun da bai taSa ji ba sai yau.

Rumaisa kuwa tuni aka tashi, har ta fara ?uluwa, ta ce "Lallai papa, zaton sa ba zan iya tafiya ba kamar yadda na ce masa ko? To wallahi tafiyata zan yi, in bi hanyar da ba ta gida ba, in Sata sai ya nemo ni". Ta na cikin mitar, ta ga motar adam, sai dai ta ga jamil a ciki, dan haka ta tsaya ta na kallonsa.

Ya sauke glashin ya ce "Zo mu tafi"

"Mu je ina?".

"Can gida, takawa ba lafiya, ya ce na Waukkoki, ya na cikin gari wurin ammi".

"Sai ka ce ba ni da hankali zan hau motar da ka ke tu?awa, in je ka kasheni a banza, tun da na san ka tsaneni, saboda papa bai auri ?anwarka ba, to ba zan hau ba".

Ya kwantar da muryarsa ya ce "Da gaske nake yi miki, ni ba kasheki zan yi ba, ba dan shi ya ce na Waukko ki ba, ba abun da zai kawo ni".

"TaS, ka isa ka gaya mini magana in yadda, ai ni yadda mutum yayi mini a haWuwarmu ta farko da shi nake amfani. Ba Wazu papan? ya kawoni ba ka ce shi ya ce ya zo ya Wauke ni, bayan a gabana ranar ka ke yi masa rashin mutunci, ka ce wai bai gaya maka anty aisha an sace ta ba, to ba zan hau ka kasheni ba, ba kai ne yayan anty aisha ba, duk na san komai, da ku ka din ga cin zalinta, tun tana ?arama, sai da ta mutu za ku nuna kuna son ta. To wallahi ba zan hau ba, gara na tafi da ?afata".

Baki buWe yake kallon rumaisa, ita ba ta manta abu, waye ma ya gaya mata wannan zancen, ita aishan ce ko adam Win ne ya gaya mata? Kuma ai ba shi ne ya nuna wa aisha ?iyayya ba.

Ya dai-daita nutsuwarsa ya ce "?anwata ki na ji, shigo mota mu tafi, sai mu yi magana, duk wanda ya gaya miki zantukan nan ?arya yake yi, na san dai aisha ba zata gaya miki ba".

"Kai ni fa ba a lallaSani, kuma ba a hantarata ko ayi mini dole, ka tambayi mijina ka ji" ta juya tayi tafiyarta, kan ya kunna motar, ya bita, ta haye a dai-daita sahu, ta ce a kaita gidan tsohon galadima.

Ana zuwa ta sauka abun ta, sai masu gadi ne suka biya kuWin napep Win, ta nufi sashin Ammi, a ranta ta na raya idan ?arya Jamil yake, sai ya gane ba shi da wayo.

Sai dai ga mamakinta ta ga baba uwani a falon ammi, bayan a gida suka bar ta.

Ta na ganin rumaisa ta hau kuka, ta ce "Tun Wazu aka ce a zo a Waukko ki daga makaranta, yanzu aka kirani a waya, takawa babu lafiya".

Ruma ba ta amsa mata ba, ta fara laluben a ina adam ya ke.

Ta na kaiwa bedroom Win ammi, ta ji tsigar jikin ta ta tashi, kanta ya wani sara.
Kamar ?wai ya fashe mata a ciki, ta shiga Wakin.

Duk ga su Mummy a gefe, har da Samha da su Fauziyya su na kuka.

Rumaisa ta ?arasa kansa ta tsaya, sai fizge-fizge yake yi, kamar zai fita hayyacin sa.

Rumaisa ta waiwaya, ta ?urawa mummy ido, a take jikin Mummy ya hau rawa, ta fara kame-kame "Rumaisa ko?, kin ga takawa ba lafiya ko?? Dama yanzu yake ta kiran sunanki ya ce a Waukko ki".

Ammi ta ce "Rumaisa, ashe jamil Win ya Waukko ki?".

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ni ba shi na biyo ba, saboda ya tsaneni, haka kawai in je ya kashe ni, ai haushina yake ji saboda takawa bai auri ?anwarsa ba, na zata ma ?arya yake yi, lafiyar papan ?alau, yaudarata zai yi na hau adaidaita sahu na taho".

"Yaya jamil Win ne yake yi miki ?arya?" Samha ta yi maganar a ?ufule.

"Waye shi da ba zai yi ?arya ba? Na faWa na zata ?arya yake yi, tun da a gabana yake yi wa papa rashin mutunci, wai bai gaya masa anty aisha ta Sata ba. Sai kuma ya zo ya ce mini papa bashi da lafiya na yarda? Ai ni a ganin farko nake gane mutum".

Ammi ta ce "Ruma ya isa haka, ki yi masa addu'a"

"Ammi ni fa rashin adalci ne da fuska biyu ba na so".

Kallonta duk suke yi, ba tare da gane in da zamcenta ya dosa ba.

"Ammi ki danne ni, ?asusuwana karyewa suke yi" maganar takawa ta sa suka mayar da hankalinsu kan shi".

Iman ce ta yi sallama a bedroom Win, jikinta a sanyaye ita ma.

Rumaisa ba tare da jin kunyar wani ba, ta zauna a gefensa, ta ri?o hannunsa da yake cikin na ammi, ta ce "Papa meye yake maka ciwo?"

Ya ri?e hannunta sosai, cikin tsananin ciwo ya ce, "komai ma, Allah idan mutuwa za ta zama hutu a gareni, Allah ka sanya na mutu, da wannan azabar da nake ji" yayi maganar yana sake ri?eta tare da yin ?ara.

Duk ta na jin azabar ri?on da ya yi mata, ta sunkuya dai-dai kunnensa ta ce "Papa ba kyau fatan mutuwa fa, idan ka mutu sabir fa, ammi fa? Dan Allah ka daina, ka bari in cikawa anty aisha al?awarin da na yi mata, zaka warke gaba Waya har abada" ta yi maganar tana zubar da hawaye.

Samha wani uban tsaki ta doka, ta tashi ta fita, abun da babu wani take gaya mata game da zamansu daban, abun da take gani yanzu daban.

Mummy ma tashi ta yi ta ce "Giwa, Allah ya bashi lafiya, amma akawai bu?atar ki din ga kwaSar sirikar ki, ta iya bakinta".

Ammi ta ce "To na gode".

Baba uwani ta kawo kai, suka haWu da Mummy, Mummy ta yi mata sigina da ido, sannan ta tafi.

"Ki yi mini Addu'a" ya faWa ya na sassauta ri?on da ya yi mata.

Baba uwani sai jera masa sannu take yi, iman ta kawo maganinsa, a shafa masa, ya ce ba ya so.

Iya abun da Allah ya sa rumaisa ta iya, ta din ga karanta masa, sai dai ta fi nanata la'iila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin. Saboda tana da ya?inin duk wahalar da ta shiga, idan ta karanta ta na samun mafita.

Lumshe idanunsa ya yi, ya daina hargowar da yake yi, ta kalli ammi ta ce "Wallahi ammi asiri aka yi masa, wai ku ba kwa ganin abun da nake gani?".

Ammi ta ce "A'a rumaisa, Allah ne ya Wora masa, muna fatan Allah ya yaye masa".

"Ammi, wai baku ga matar da take zaune tare da su Mummy ba, tana kallonsa, wata ba?a, idonta ya na ci da wuta, haka fa wataran idonsa yake yi, idan ransa ya Saci, kuma wallahi ni ban yadda da babar mahmud Win nan ba...... Kamar daWi take ji abun da ya samu baban sabir, sai murmushi fa take yi ku.........

Hannun sa ya saka ya toshe mata baki, duk da idonsa ya na rufe.

Rumaisa baba uwani take kallo, idan har abun da Mahmud da kuma Asiya suka gaya mata a kan baba uwani gaske ne, to za ta yi amfani da shawarar yaya usman, dan ranar da suka je gida, ba abun da ba ta gaya masa ba, kuma shi ya bata shawarar ta faWi wata maganar a gaban baba uwani, wadda ta san za ta iya zuwa kunnen Mummy.

A zahiri rumaisa ta ga matar da take faWa, a tare da Mummy, sai dai a wannan karon ma, ta gane ita kaWai take ganin ta.

Bacci ne ya Wauke Adam, rumaisa ta tashi ta ce za ta yi salla.

Ammi sai sannu take yi mata, saboda ta san idan har ciwon adam ya tashi, duk wanda ya yi wa wannan ri?on sai ya ji jiki, amma ta ga rumaisa ras da ita.

Maimakon ta je ta yi sallar, sai ta fice harabar gidan.
Lelle?awa take yi, ko za ta gano Mahmud, dan ta na da labarin gaya masa.

Bisa sa'a, ta ga yana tahowa daga waje, da alama masallaci ya je.

"Daddy" ta ?wala masa kira.

Yana hangota ya yi murmushi, ya ce "Daughter, ina takwarana?".

"Ya na wurin ammi, dama kai nake nema, Allah ya sa na ganka".

"To gani ya aka yi? Amma ba kya tsoron kar mijinki ya ganki, ya kuma hantararki?".

Ruma ta tura baki ta ce "Bashi da lafiya fa, kuma kowa ya zo duba shi, har da mamanka amma kai ba ka zo ba"

"To ai kin san ba shiri muke yi ba"

"Daddy meyasa?".

Mahmud ya numfasa ya ce "Manta kawai, ya aka yi?".

"Ka san maganar da muka yi ai ranar ko?, kuma ka ce zaka taimaka mini".

Mahmud ya ce "Ko zan yi wa kowa ?arya, ban da ?a ta".

Rumaisa ta ce "To ni fa na ce mamanka ce ta ke yi wa mijina asiri a gaban baba uwani".

Ya Wan yi shiru ya ce "Ke waye ya gaya miki haka?"

"Haka nake tunani, kuma nake son tabattarwa, amma so nake na kama baba Uwani, yaya usman ne ya bani shawara. Ni fa ban yadda matar nan mamanka ba ce, jiya mafarki na yi tana tura papa rami, yau kuma na ganta da wata mata, ba wanda yake iya ganinta sai ni, ba?a mummuna, idonta sai wuta yake yi, abar tsoro kawai dai ni ba ta tsorata ni ba. Papa sai ihu yake yi, abun tausayi"

Yayi zuru da ido yana kallon rumaisa, sai kuma ya ce "Da gaske ki ke ko da wasa?".

"Ni ba kullum nake yin ?arya ba" ta bashi amsa.

"So, you want expose my mother daughter?".

Ta yi shiru, tare da zuba masa ido.

Ya ce "Shikenan, ni na yi al?awari ai kuma zan cika in sha Allah, duk wani support da ki ke nema, i will assist in sha Allah, zan taimaka miki, ki cika al?awarin da ki ka yi wa fulani, amma yaushe zaki bashi bayani a kan abun da yake nema na binciken? Ya na son aisha sosai, a yanzu ba shi da burin da ya wuce, ya gano wanda suka saceta".

Rumaisa ta ce "Kamar ka na son takawa? Tun da har ka san abubuwa a kan sa, amma meyasa ba kwa shiri?"

Jiki a sanyaye ya ce "Kar ki damu, lambar wayata na nan, na rubuta miki, a bayan sashin su mijinki, duk lokacin da ki ke bu?ata ki kirani, idan har ina Nigeria" yana gama faWa ya juya zai tafi ta ce "Idan kuma na gane ka zaSi uwar ri?on ka, ka yaudareni, zan yi maka abun da ba ka zata ba, zan iya yin komai a kan uban Wa na"

Cak ya tsaya, ya waiwaya ya kalleta, kawai ta kwashe da dariya, ta ce "Kamar a film ko? Zan iya acting ashe, ai na san ba zaka yi mini haka ba"

Tun da ya dawo ?asar nan, suka haWu da rumaisa, suka yi magana, yake jin kamar wani abu ya sauya a tare da shi, sosai yake jin tausayin Adam, kuma a jikinsa yake jin, lokaci ya yi, da yakamata Mummy ta tuba, shekaru sun fara ja, ko ba komai ta mutu ta samu rahamar Allah, sarautar da take yi masa ?uzu kuma, shi ba a gabansa take ba ma.

A Wakin Iman rumaisa ta yi salla, iman ta baya doguwar rigarta ta saka, suka zauna su na Wan taSa hira, iman ta Wan bata labarin, irin wahalar da yake sha, idan yana ciwon nan, da kuma wahalar neman magani da ammi take yi, ba yau ba gobe".

Iman ta Wora da cewa? "Anty rumaisa, da kin sani ba ki faWi maganar nan ta Wazu a gaban mutane ba, ba zan musa miki mummy ba ta asiri ba, amma idan maganar ta koma kunnenta fa? Zai iya haddasa wata rigimar".

"Ai na ga duk wanda yake wurin, amintacce ne. Waye zai je ya faWa? Ammi ce za ta gaya mata, ko kuma ke? Ko kuma baba uwani, da dama dan ita na faWa"

Iman ta kalli rumaisa da mamaki, rumaisa ta yi dariya, ta ce "Iman, ina da wayo fa, kawai dai ba na ji ne, amma dan Allah Meyasa papa suke gaba da daddyna? Ko da ba ammi ce ta haifesu duka ba, amma ai ?an uwa ne"

Iman ta ce "Duk ?a?an ammi ne"

Rumaisa ta ce "Ai na zata kema zaki raina mini hankali ne, ai na sani, na san duk ammi ce ta haifesu, amma daddy ya dage wai waccan matar ce babarsa, amma dan Allah meyasa gaba Waya gidan nan naku, a hargitse yake? Kowa ba shi da gaskiya".

Iman ta rausayar da kai ta ce

32 / 67