Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   19 / 67

54K to 57K   out of 199.9K words

Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*.





Adam bai taSa ta ba, sai bin ta da ya yi da kallo, idanuwanta na neman su kakkafe, sai daddagewa take yi, jikinta yana cigaba da tsuma.

Usman ya ce "Lafiya kuwa?"

Mai sunan baba kuwa wani irin takaici ne ya mamaye shi, ganin rumaisa a jikin Adam gaba Waya.

Takawa ya ce "Ban san meya sameta ba, gani na yi ta haWa kai da gwiwa tana bacci, kawai ta zabura ta faWo jikina".

"Iman! Iman ba ta da lafiya fa, Iman ba ta da lafiya" ta yi maganar cikin surutu da magagi.

"Wace kuma iman?" Mai sunan baba ya tambayeta a ?ule.

Haushi ne ya kama Adam, saboda yadda mai sunan baba ya raina wa kansa hankali, wai wace kuma iman, ya lura da yadda yake a ?ule, dan haka ya ture rumaisa daga jikinsa, ya ja da baya.

Mama tuni ta fito tsakar gida, dan jin abun da ya faru, amma ta kasa ?arasawa soron, saboda jin nauyin adam.

Sosai take kuka tana neman abun ri?ewa, "Iman fa, na gaya muku ba ta da lafiya"

Mai sunan baba ya saka hannu ya Wagata tsaye, amma jikinta ya riga ya saki, tana neman ta faWi.
"Ki buWe idonki menene?" Ta sake rintse idanunta, kamar mai tsoron ganin wani abu.

Cak ya Wagata ya shiga da ita cikin gidan, ya kwantar da ita a tsakar gida, gaba Waya suka rufu a kanta.

Adam har yayi niyyar tafiya, sai ya ga idan yayi haka bai kyauta ba, mussaman da ya ji tana ta ambatar sunan Iman.

Sallama ya yi ya shiga, ya tarar da su a kanta, mama tana girgiza ta, tana tambayarta menene.

Idonta dai a rufe, tana ta zubar da hawaye, ta ce "Iman, ba ta da lafiya sosai da sosai"

Mama ta ce "A'a jikinta da sau?i ai, har an sallameta daga asibiti, tana gida".

Ta Waga hannunta ba tare da ta buWe idon ba, ta Wora shi a saitin zuciyar mai sunan baba, idonta a rufe ta Waga kai in da yake ta ce "Mai sunan baba, ka ji bugun zuciyarka, ai kai ka yadda ba ta da lafiya ko? Ku yi mata Addu'a dan Allah kar ta mutu".

Ya ce "To, kema ki yi addu'a"

Takawa ya Wan yi gyaran murya ya ce "Ni zan tafi, Allah ya bata lafiya"

Mama da sai a yanzu ta lura da shi, ta ce "Yi ha?uri mai babban suna, wallahi tun da aka yi garkuwa da ita na kasa gane kanta, ina ga wani abun ta kwaso a zaman dajin da ta yi".

Adam ya ce "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, abun ya bani mamaki, lafiya take zaune, ta ce idan ban ci abincin da ta kawo ba, an ce za a zaneta, da ban ci ba sai ta ci, ta ce ba za a gane ba, sai ta haWe kai da gwiwa tana bacci, shikenan kuma ta fara ihu" yayi maganar cikin ?o?arin wanke kansa, yadda gaba Waya ?artan nan suka zubo masa ido,sun ga ?anwarsu a jikinsa, ga mai sunan baba sai muzurai yake yi.

Mama ta ce "Bakomai wallahi".

Usman ya ce "Lallai yarinyar nan baki da mutunci, dama zuwa ki ka yi ki ka cinye abincin?"

"Ba cinyewa na yi ba, dama ba na gaya muku ba zai ci ba, na san halin sa fa hmmm" ta yi maganar kamar wadda ta sha ta bugu.
Duk suka tsira mata ido, ta mi?a hannu tana yi wa adam nuni da ya zo.

Ba musu ya taka ya ?arasa, ya sunkuya, ta ri?o rigarsa a hankali ta ce "Iman babu lafiya, kar ku zata da wasa nake yi, kar wani abun ya sameta. Kuma, kuma daga yau ba zan sake baka ko ruwa ba, yau haka aka din ga azabtar da ni, wai sai an yi maka girki kuma ka ?i ci, to daga yau babu ni babu kai, tun da duka zaka janyo mini, sarki mai koriyar alkyabba " ta ?arasa maganar tana murmushi. Sai kuma ta cigaba da zabura.

Ya kalleta ya ce "To, na gode, ba za a dake ki ba, zan tafi da abincin"

Ta kuma cewa "Yauwwa, wannan matar, da ta bamu ruwa ni da Sabir, ka tuna ta?"

Adam ya ce "Eh, na tuna"

"To ka san ta ce wai akwai gwagwarmaya a gaba, hmmm ba ka san fa me nake gani ba ko? To in gaya maka, wani abu na gani rannan a gidanku, kuma ma, wani zai je ya Webi turarenka baka sani ba, yauwwa har da maganin ka ma da ake shafa maka, ana nema".

Gaba Waya surutan da take yi babu ma'ana a wurinsu.

Mai sunan baba ya ce "Ya isa haka ki yi mana shiru"

Takawa kuwa ya ce "To, kin gama na tafi?"

"Eh ka tafi, amma fa kana tafe wannan matar tana binka, saboda tsabar taurin kanta, amma da kaina zan mayar da ita gurguwa"

Adam ya ce "Eh yakamata, yanzu dai ki cigaba da baccin, dama ammi ce ta aikoni, zan kira Aliyu a waya mu yi magana"
Ta ce "To" ta gyara kwanciyarta ta cigaba da barci.

Gaba Waya abun ya Waure musu kai, Adam ya ce "To mama sai anjima, Allah ya ?ara afuwa"

Suka amsa da amin, ban da mai sunan baba.
Usman ya ce "Ka tafi da abincin nan, ka cika mata al?awarin ta".

Adam yayi murmushi, Usman ya bi bayansa.

***
Ko da ya ?arasa gida, sashin Ammi ya wuce, dan gaya mata abun da ya faru, amma ya tarar ba ta nan, ya fito ya tambayi baba uwani, ta ce "Ai suna tare da iman, tana can tana ta fizge-fizge kamar za ta haukace".

What! Ya faWa cikin tashin hankali, da sauri ya nufi Wakin iman, sai dai ya je ya tarar da ita, a kwance tana ta Addu'a, ammi na ta shafa mata ruwa a ka, tana yi mata Addu'a, Nusaiba kuma na ri?e da hannunta.

Da sauri ya ?arasa yana faWin "Iman, me yake faruwa?"

Ta mi?a hannu ta ri?e nasa ta ce "Yaya Adam mutuwa zan yi, dan Allah ku yafe mini, nikaWai na san me nake ji a kaina, baku san me nake ji ba, kaina kamar ana kafa mini ?usoshi.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya din ga maimaitawa, ya saka hannu ya janye piliown da take kai, ya kwantar da ita a kan gadon, ya din ga karanta mata duk addu'a da ta zo bakinsa, cikin ?udirar Allah sai barci ya Wauke ta.

Adam ya ce "Ammi, wai takamaimai me yake damun iman ne?"

"Takawa ina zan sani? Na ga na asibiti sam baya yi mata ma, na rasa in da zan saka kaina ma. To ya aka yi, kun tattauna Win, ya ka baro rumaisa? Ina son a satin nan idan iman ta warware a fara haWa lefe, dan na turawa laila kuWi, ta yi wasu sayayyar a can ?asar"

"Babu lafiya" ya faWa a hankali.

Ammi ta ce "Kamar yaya?" Nan ya kwashe komai ya gaya mata, ammi ta yi shiru ta ce "Ikon Allah, Adam akwai aiki ja a gabanmu, babban fatana yanzu shine in ga an yi auren nan, kuma bana fatan a Waga ko da rana Waya".

Adam ya jinjina kai Sannan ya ce "Bari na je na ga sabir, daga nan na wuce masallac??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i".

Tun da ya fita yake ta jujju
***
Rumaisa sai magariba sannan suka samu kanta, ta tashi daga wannan baccin, ba ta iya tuna komai ba, ta cigaba da sabgoginta.
Mama hankalinta ba ?aramin tashi yayi ba, saboda gani take rumaisa aljanu ne ke son su hanata aure. Babu wanda yayi yin?urin gaya mata abun da ya faru, suka biye mata aka cigaba da harkokin gidan kamar yadda suka saba.

Washegari Ammi ce ta kira mama da kanta a waya, tana tambayarta jikin rumaisa.

Mama ta ce "Jiki da sau?i hajiya, na ce ko Waga bikin nan za ayi, a nema mata magani, alamu sun nuna iskokai suna damunta, kar ayi aure da larura".

"A'a maman rumaisa, Allah zai bata lafiya, wata?ila da an yi auren ta samu lafiya, wallahi kin ganmu nima iman haryanzu jiki ya?i daWi, na rasa abun da yake yi mini daWi, ciwon kai ko sauka ba ya yi".

Shiru mama ta Wan yi, kenan maganar rumaisa gaskiya ce?.

Mama ta ce "Allah ya basu lafiya baki Waya, in anjima zamu zo mu sake duba jikin nata"

Ammi ta ce "Ba sai kun wahalar da kanku ba, ayi mata Addu'a kawai".

Mama ta ce "Haba, ai babu wannan a tsakanin mu, bari ayi sallar magariba, rumaisa ta dawo daga islamiyya sai mu zo"

Ammi ta ce "To shikenan, ta samu ta ga Wanta ma".

Bayan sun gama wayar, mama tayi ta Addu'a Allah ya sa ba aljanu ne suka buWewa rumaisa ido ba, take gane-gane.

Da magaribar, tare da mai sunan baba suka je gidan su takawa, rumaisa na ta murna za ta ga Sabir.

Har Wakin iman, aka yi musu izinin shiga, suka tarar da ita kamar mai shirin zarewa saboda surutai, duk suna kanta ciki har da Jabir.

Rumaisa ta ?arewa Wakin kallo, ta ce "Mama, Wakin nan na yi mafarki fa jiya, ku cirewa iman pillown nan, mafarki na yi wata ?ar tsana tana soka mata allurai a kanta, yauwwa ba na ce muku iman ba ta da lafiya ba jiya?" Ta yi maganar tana ?o?arin tuna abun da ya faru jiyan.

Ammi ta ce "Rumaisa a ina ki ka ga ?ar tsanar?"

"Mafarki fa na yi, ki dafa pillown, ki karanta mata bisimillah da fatiha, amma dai wata ?ar tsana na gani a mafarki"

Abun sai da ya Waurewa kowa kai, Mai sunan baba kuwa tuni ya bar Wakin, saboda yadda iman take, zaka san tana jin jiki ba kaWan ba.

Ammi ta dafa pillown, ta karanto adduoi, Rumaisa ta ri?e hannun iman tana yi mata sannu.

Jabir ya tashi ya ce "Ammi, bari na je gida, Allah ya bata lafiya"

Suka amsa da Amin ya tafi.

Tattaunawa ammi da mama suka cigaba da yi, ammi tayi ta bawa mama ?warin gwiwa, a kan kar a fasa wannan auren.

Bacci iman ta samu, mama ta kalli Adam ta ce "Takawa, kai rumaisa part Wina, ta ga Sabir, sai ka tambayeta abun da take bu?ata na bikin"

Adam bai fiye yin jayayya da ammi ba, balle kuma yanzu da yake a gaban mutane ne, bai ce uffan ba, ya tashi ya fita, rumaisa ta bi bayansa tana murna, jin an ce za ta ga Sabir.

A hanyar sashin ammai, suka haWu da baba uwani, cikin girmamawa ta risuna ta ce "Takarwarka lafiya magajin galadima, ba?uwa muka yi ne?"

"Eh" ya amsa a ta?aice yana fatan kar rumaisa ta yi wani shirmen, amma ga mamakinsa, ko kallon baba uwani ba ta yi ba balle ta gaishe ta.

Sai da suka yi gaba sannan ya kalleta ya ce "Baki iya gaisuwa bane?"

"Wa zan gaisar?"

"Matar da muka wuce, meyasa baki gaisheta ba? Gidan sarauta ba wuri ne da zaki gwada rashin Wa'a ba, akwai girmamawa da karamci, ko da kuwa kai ne kake gaba da mutum"

Ba kunya ba tsoro ta ce "A hakan? Sau nawa na gaisheka a rayuwar nan baka amsawa, gidan sarautar da watarn wanda kake gaisarwa daban masu amsawa daban, ana ce maka an gaisheka Wan talakawa, wannan ba wula?anci bane ba, ban kula kowa ba balle ayi mini wula?anci na ji haushi, ammi da wanda suke amsawa kawai zan din ga gaisarwa"

Wato ya fuskanci ita dai wannan yarinyar, defeating Win ta, ba abu ne mai sau?i ba.

Sai da suka shiga Wakin ammi, in da babu idon mutane, sannan ya dubeta ya ce "Idan ki ka cigaba da wannan taurin kan, ina gaya miki abu kina mayar mini da martani, zaki yi dana sanin aure a gidan sarauta, dan zai zame miki tamkar kurkuku mafi azaba, kowa zai yi ?o?arin yin amfani da ke wurin cimma burinsa, dole ki kiyaye".

Rumaisa ta ce "Na sani, gidan sarauta ba irin normal gida bane, ina gani a film, na indiya da sauransu, daga tsafi sai munafunci, abun ban tsoro, kowa ba abun yadda bane ba, da an ga baka da wayo, sai a cuceka, da ka yadda da wani, sai ya nemi ganin bayanka. Ai ni a duniyar nan kurku mafi azaba ita ce zamana a hannun 'yan bindiga, abu mafi razani kuma ganin mutuwar matar da ta bani kulawa kamar ?ar ta a lokacin da ake yi mini ?amshin mutuwa. Abu mafi tsayawa a rai shi ne tunanin idan har gawarta tana da muhimmancin da za a kasheta a Wau gawarta a mota a bar wurin da ita, saSanin sauran mutanen da ake kashewa wurin, to waye ya saka ayi garkuwa da ita a kasheta, kuma ayi umarnin kashe Wan ta? Abu mafi ban tausayi shi ne haihuwar jaririn da bai san komai ba, na din ga wahalar da shi da sunan kulawa, har koko na bashi, ya shafe kwanaki da ?azantar haihuwa a jikinsa, bayan mun kuSuta a ka yi yin?unrin rabani da shi.
A tunaninka akwai wani abu mai wahalar mantawa kamar wannan? Ko wani irin ?alubale ne, zan jure shi na rayu da sabir, kamar yadda na yi wa anty aisha al?awari, amma ka ?yaleni a yadda nake, ni ba ?ar sarauta bace ba, lokaci Waya ba zan iya zama irin ku ba". Tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta taka a hankali ta ?arasa gaban gadon Sabir, ya ?ara zama ?ato sosai, sai bacci yake yi.

Takawa kuwa kamar an gina shi, wasu gaSoSi ta taSo masu muhimmanci, amma ya san yanzu da yayi yin?urin ya cigaba da yi mata maganar, zata koma masa ainihin rumaisanta, ta fara rashin kunya.

Ta ri?e ?afar sabir, tana kallonsa tana murmushi.

Adam yayi gyaran murya ya ce "Ammi ta ce, na tambayeki idan da abun da ki ke bu?ata na shirin biki"

Maimakon ta amsa kawai sai ta hau dariya ta ce "Ni fa mantawa nake yi aure za ayi mini, ni bana bu?atar komai, su yaya Aliyu suna saya mini kaya, su mama kowa sai mini kaya yake yi".

Ya jinjina kai ya ce "Good, that's their part, a Sangarena nake nufi, wanda ni yakamata na yi"

Ta girgiza kai ta ce "Za a saya mini komai, ni fa bana son ayi mini abu azo daga baya ana yi mini gori, komai za su saya mini, har da turmin ?arfe"

Ya ce "Shikenan, na gaya mata ba kya son komai, tashi mu tafi na san ke suke jira"

Ta sumbaci goshin sabir ta ce "Ka yi mafarkina babyna" sannan ta yi gaba ta bar takawa a baya.

Aikuwa ta tarar da su a falo har sun fito, Ammi ta ce Adam ya mayar da su gida, mama ta ce ba ta yadda ba, ba zata iya hawa motar siriki ba, ?arshe aka saka direba ya mayar da su, mai sunan baba ya ce za shi wani wuri, dan haka bai bi su ba.


A daren sai da baba uwani ta kai wa mummy tsaigumin zuwan su mama, tare da sanar mata ba ta san ko suwaye ba amma suna yawan zuwa gidan.
Mummy ta ce lallai ta sanya ido, ta gane ko suwaye, ta zo ta gaya mata.

Tun da Allah ya sa rumaisa, ta gaya wa ammi abun da ta gani a mafarki a kan iman, suka dage da addu'a, kuma cikin ikon Allah ta samu lafiya.
?angaren su mama shiri suke sosai da sosai, a kan bikin da yake gabato su, sai dai rumaisa ta cigaba da mafarkai barakatai, da razana, har da ganin ta a wurin ?an bindiga.

Mama ta sanarwa da Gwaggo, in za Gwaggo ta yi ta faWa a kan ta sha cewa a nemawa rumaisa maganin tsari, amma maman tana yin burus da ita.

Danginsu rumaisa kowa da abun da yake kawo wa na gudunmawarsa, sai dai ?an unguwa basu san me ake ciki ba.

Kwanci tashi asarar mai rai, ya rage saura kwanaki goma sha uku, auren rumaisa da adam, yayyen rumaisa da dangin mahaifinta, da na mama sai rawar gani suke yi.
Gefe ga masu kawo gudunmawar magunguna na gyaran jiki, da gyara aure, mama ta kasa bawa rumaisa, gani take kamar idan aka bata za a cutar da ita, shekarunta basu kai ba, ba ta da tabbacin ma shi kansa mijin ya saurareta.
Sai dai mussaman babar hauwwaliya, ta biya mai gyaran jiki, take zuwa gida yi wa rumaisa gyaran jiki, shi ma ta din ga tamSele kenan tana guje-guje tana ihu, wai ana azabtar da ita, za'a rina mata fata da azaba.


Tun zuwa Wayan nan da takawa yayi zance, bai kuma zuwa ba sai yau, da dole ce ta kawo shi.

Yau tun da ya zo, ba a kula shi ba, balle a gaishe shi, wasanninta ma kawai take yi, har da duwatsu. Ya lura ta yi wani kyau na musamman, fatarta ta yi haske, sai zuba ?amshi take yi.
Yayi gyaran murya ya ce "Haryanzu kina zuwa makaranta ne?".

"An yi hutu"

Ya numfasa, ya Wauko wayarsa a aljihunsa ya kira iman, ya jira ta Waga sannan ya bawa rumaisa, suka gaisa iman na ta tsokanar ta amarya.

"Yauwwa anty rumaisa, lefenki ya kammala haWuwa,

19 / 67