Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   45 / 67

132K to 135K   out of 199.9K words

mijinki yake ajiye miki komai, ki zo ki saka mini rani".

Ruma ta ce "Allah sarki mijina, ya tafi ya barni, papa saurayina"

Aliyu ya ce "Ke fa baki da kunya ko?"

Flashing aka yi wa Aliyu, ta le?a wayar ta ga an rubuta "Baby Hibba".

"Ohhh ni ?a su, yaya Aliyu soyayya?"

Ya harareta, ya kira wayar "Hello my haidar".

"KuWin wayar sun ?are ne ake mini flashing?"

"A'a ba su ?are ba, bana son ka Waga su ?are ne, kuma ka sake saka wasu, shiyasa na yi maka flashing"

Yayi murmushi ya ce "An taso daga tahfiz Win ne?".

"Eh, yanzu na shigo gida ma"

"To shikenan, in ajima zan zo in sake jin haddar. Bari yanzu abinci zan ci"

"To my haidar, ka gaida mama, ka ci ka ?oshi da yawa".

Rumaisa ta ce "A gaban maman ka ke waya da ?an mata?"

Da?uwa ya yi wa rumaisa, ta hau tafa hannaye.

"Yaya Aliyu, habiba ce ta koma sweet hibba?".

"Uban wa ye ya ce miki ita ce"

Rumaisa ta ce "Na rantse da Allah muryar habiba ce, munafuka, habiba take soyayya da yayana, ba tare da tana biyan subcidy ba, dole na je gidansu habiba, mama a gabanki ake soyayya?".

Mama ta ce "Ya ce zuwa za ayi ma ayi masa tambaya, nan da shekara biyu"

Ruma ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Su mai sunan baba ba su yi aure ba sai kai"

"Uban wa ye zai bari kansa ya kulle kamar su? Yaya Abubakar ma kuWin aure za a kai masa, yana gama service. "

"Innalillahi, yaya Aliyu habiban da ka ke zanewa saboda ni"

Aliyu ya doke mata ?eya ya ce "?ar rainin hankali ba, duk ke ki ka ja, na daki mata ta".

Mama ta ce "Too har an yi auren kenan" da sauri Aliyu ya Wau plate ya fice daga Wakin yana dariya.

Wani irin zullumi mai sunan baba ya shiga, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa gane tausayin iman yake ji, ko tashin hankali ya shiga jin wani na neman aurenta, wani irin kishi ne ya taso masa, tabbas ya fi jabir komai, sai dai jabir ya fishi kuWi, sannan kuma wa iman take so

Yaya usy ne yayi sallama, rumaisa ta tashi da gudu ta tare shi, ta ce "Mussaman saboda kai na zo gidan nan yaya usy".

Ya ce "?arya ki ke yi".

"Wallahi da gaske, zo mu zauna daga nan"

Ba tara da ta bari ya shiga ko wurin mama ba, ta ja shi kitchen ta rufe ?ofa, sannan ta ce "Yaya usy wani abu ne yake damuna, na ga kaine abokin shawarata, na ce bari na gaya maka".

Ya ce "To ina jin ki"

"Yaya usy, dama...dam..mm"

"Wai meye haka ne?"

"Kunya nake ji ne, amma shawara nake nema. Ka ga dama takawa ne kan ya tafi, yake yi mini abun da bai dace ba, kuma"

"Kuma me? Wane irin abu ne da bai dace ba".

"Yaya usy kiss yayi mini kuma, ba zan iya faWar sauran ba dai, kuma kaga bai dace ba, bana son mama ta gane, ya ce mini wai ai ba komai, in tambaya in ji, wai tun da ihu nake idan ya taSa ni, zai ?ara aure, kuma ni bana son ya yi mini kishiya. Dan Allah yaya usy ya zan yi, bana son Sata tarbiyya ta, idan mama ta sani za ta yi fushi da ni, kuma bana son yayi mini kishiya"

Ayshercool.

08081012143
Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels


Usman ya yi ?uri da ido yana kallonta.

"Yaya usy ba ka ce komai ba?"

"Ji nake kamar in kama ki in ma?ure mini wuya ne".

Cikin damuwa ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri, ka rufa mini asiri"

"Ke dalla ware malama, ke yanzu duk zaman da ki ke yi, yake baki ci da sha, ya Wauki nauyin karatunki, shirme kawai ki ke tafaka masa, zuwa ki ke kiyi masa ?iri-?iri da ido, kamar gardi a cikin gida, ke kanki ba zaki taSa waye ba, abun da aka koya miki baki san idan kin yi aure ki waye ba, sai kayan hauka da rashin hankali"

"Ni fa yaya usy ban gane me ka ke nufi ba"

Usman ya ce "Idan bai yi miki kiss ba, wata zai je ya yi wa a waje?"

"Yaya usy, ku fa ku ka ce mini haramun ne, Allah zai ?ona ni idan na yi"

"Kuma sai aka ce miki har da mijinki? Ai gara ya ?ara auren, kuma ba abun da zai hanamu ra?ashewa da bikin, ki je ki yi ta shirmenki" Usman ya tashi ya bar kitchen Win.

Ta yi shiru tana tunani, ta yaya haka zai yiwu? Sun ce mata abu babu kyau, yanzu kuma an dawo an ce mata ya halatta ba tare da wani cikakken bayani ba. Ta basar da zancen ta cigaba da harkokinta.

Mai sunan baba kuwa rumaisa ta haWa shi da assignment mai wahalar gaske, domin kuwa kasa sukuni yayi, maganar ta din ga damun zuciyar sa, ya din ga jin tamkar yayi tsuntuswa ya je ya ga Iman.

Da wayar mama, rumaisa ta kira Mahmud a waya, ta ce ya zo ya Wauke ta, ta bashi adress Win gidan.

Yayyen ruma sun sha mamakin ganin Mahmud, basu san shi, ba sai dai wasu lokutan ta kan yi maganar sa.

Ya fi takawa sakewa da mutane wasu lokutan, dan haka nan da nan ya shiga cikin su Aliyu kamar sun saba.

Rumaisa ta ce "Daddy, ga Yasir, shi ne hacker shi ne ku ka yi waya da shi"

"Ki ka kuma ce mini hacker, ba zan sake yi miki wani abu ba"

Mahmud ya ce 'Rabu da ita, ai ni da kai muke aikinmu" ta nuna masa Abdallah ta ce "Ga masterna a wurin zane-zane, da shi nake koyi, duk da idan na taSa masa kayan zane, wataran ran?washina yake, amma a hakan Alhamdilillah na koya, dan haka shi zai yi mana zane, sonake kan papa ya dawo, mun gama komai"

Ya ce "Lallai team Win nan an haWa manyan ?wari a cikin sa, Allah ya dafa mana". Mama sam ba ta san a kan me suke magana ba, bayan la'asar sosai, sannan ya Wau ruma suka tafi gida.

Aikuwa ta sha faWa a wurin laila, wai ta tafi gida, ba a kira takawa an tambayi izninsa ba, ruma tayi mata banza, irin kan ki ake ji Win nan.

Kusan sati guda, laila ta saka ruma a gaba, ta hanata sukuni, gashi ta yi ta mata magana da turanci, komai ruma ta yi sai ta ci gyaranta.
Ta hanata kwana tare da iman, tare suke kwana a Waki tare da ita, gashi ta kasa ta tsare ta hanata video call da takawa.
Abu Waya ne yake yi mata daWi, kunun maman Khadija na sabaya da take sha safe da yamma, wannan kam tun da batu ake na ci, ruma tana jin daWin haka.
Ban da wannan, duk wani wanke-wanke da gyaran fata rumaisa ba so take yi ba.

Rumaisa na zaune tana shan kununta, ita da sabir, dan idan suna sha, kamar ya shiga cikin kofin, ko zama ba ya yi, yana tsaye ayi ta bashi yana lashe baki.

Laila sai video call take da mijinta, ga mijin ya fara manyanta, amma ta shagwaggwaSe, sai taSara take, tana ce masa baby, suna wani abu mai kama da iskanci a wurin rumaisa.

Rumaisa har le?awa take, ta sake kallon fuskar mijin, wai wannan gundumemen mutumin ne baby, 'TaS sukumbiya, wai baby taS' laila tana jin ta, ta?i kulata, su suke wayar amma ita take jin kunya.

Babu babban abun da yake bata mamaki, kullum da daddare sai sun yi video call, laila ta Wau kwalliya kamar zata biki, ta sha ?anan kaya, ta zauna a gaban waya ko system.

Yau kam da abun ya ishi kunnuwan rumaisa, ta saka hannu ta toshe kunnenta. Sai da laila ta gama wayar, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ba zaki iya ba ko, ni ?ar iska ce ni da mijina, shi ne ki ka toshe kunne?"

Ruma ta yi shiru. "Ban ce dole sai kin yi irin nawa ba, ni na yi shekaru a gidan aure, na saba da mijina sosai da sosai, ke nake fatan ki daina wannan shirmen, ki san me ki ke yi" ruma ba ta ji za ta iya abun da laila ke yi ba, a ganinta fitsara ce muraran, ga takura mata da take yi.

Da safe kan ta tafi makaranta, ta karSi wayar iman, ta kira Adam voice call.

"Budurwata"

"Papa" ta kira sunansa a shagwaSe.

"Ya aka yi?"

"Ni gaskiya wannan anty lailan ta takura mini, ta yi ta mini masifa, da na motsa ta yi mini faWa, duk ta bi ta saka mini ido".

Adam ya ce "Haba mimi, baki kira ni kin ji lafiayata ba, sai kawo mini ?ara, ke ma ta ce mini ba kya ji, taurin kai ki ke yi mata".

"Yi ha?uri ya kake?".

"Ban sani ba, tun da baki damu da ni ba"

"In ji wa? To yau saura kwana Wari da saba'in da biyu ka dawo, calendar ce da ni, kullim sai na yi marking kwanakin da suka rage ka dawo"

Adam ya ce "Wow, lallai kin damu da ni sosai, take care, kar ki makara"

"Ni kar ka kashe"

"So ki ke ki makara a school ko?"

"Hmm ka san me?" "A'a sai kin faWa"

Ji tayi kamar ta gaya masa zancen kunun da take sha sai kuma ta fasa.

Jin tayi shiru ya sanya ya ce "Akwai matsala ne?".

"A'a"

"To ki shirya a kai ki school kin ji budurwata, sai mu yi waya anjima"

Ruma ta ce "Video call nake so mu yi in ganka, amma wannan anty lailan ta hana, duk abun da zai sani farinciki ba ta so".

Ya ce "nima dokar nan ta isheni gaskiya, mutum da budurwasa a hanasu sakewa"

Ruma ta yi dariya ta ce "To saurayina, sai na dawo, kun gama taron yaushe zaka wuce karatun"

Ya bata amsa da "sai Allah ya kaimu jibi".

Da ?yar suka yi sallama, ta ajiye wayar ta tashi.

Wata irin kewar adam ce ke sake bijirowa rumaisa, ji take kamar sun shekara ba sa tare, tayi shiru tana tuna abubuwan da suka faru a tsakanin su, daga aurensu zuwa yanzu, a hankali ta yi ajiyar zuciya, ta tashi tana shirin makaranta.

Mai sunan baba kuwa tsayin lokacin nan, kullum sai ya Wau wayarsa ya ji kamar ya turawa iman message, amma sai ya kasa, ya duba chats Win su, ko zai ganta online, amma ya ga sam ba ta fiye hawa online Win ba ma, gashi sai yana tsaka da jimami, da tunanin ya zai yi, Aliyu ya zo yana kashe murya yana waya da habiba, wanda ba ?aramin ?ular da shi yake yi ba.

Mummy ba ta sake nunawa Mahmud fushi ko damuwa a kan abun da yayi ba, hasali ma ta?i yarda su sake Waukko zacen, kamar babu abun da ya faru, ta ?ar?ashin ?asa kuwa, tana cigaba da shirin, sake rusa giwa, saboda ta yi alwashin sai ba?in ciki ya kashe giwa, in dai da ranta babu wani abun alkhairi da zai sameta, babban birinta yanzu bai wuce kassara rayuwar rumaisa ba, kasancewar ita ce babbar barazanar ta.

?angaren Jamil ma, yana ta neman hanyar da zai yi magana da rumaisa, dan ya sha zuwa makarantar su, ya tarar da sidi yana tsaye yana jira, kuma alamu sun nuna babu wanda ya san adam yana zarginsa, dan haka so yake ya tutsiye rumaisa, ya ji me da me ta sani.

Baba uwani ma kullum zaman War-War take yi, a kan kar rumaisa ta tona mata asiri, dan tuni mummy tayi mata fata-fata ta sallameta.

Ammi na ta yi wa iman bayanin cewa Jabir ya ce mata, yana jira mai girma turaki ya dawo, wambai ne zai nema masa auren iman, kuma ya bata tabbacin cewa ya shawo kan hajiya Lubabatu ta amince masa ya nemi aure iman, kuma yayi mata zancen haWa lefe ta ce masa wannan maganar su ce, su yakamata su tattauna.

Iman da ke shan kunun sabayar maman Khadija, dan ba a bar ta a baya ba, har ita ake sha, dan kuwa kogi bai ?i daWi ba, ta sunkuyar da kai tana sauraren ammi, ruma kuwa tana ta game a wayar ammi, kamar ba ta san me ake faWa ba.

Ammi sai ta yi zaton kunya ce kawai irin ta iman, ya sanya ta?i magana, Nusaiba kuwa sai za?al?alewa take yi, tana tsara yadda biki zai kasance.

Sallamar hajiya Lubabatu ce, ta katse musu hirar, Ammi ta amsa su kuma duk suka bita da kallo.

Ammi ta faWaWa murmushin ta, ta saka duk abubuwan da suka faru a baya, mussaman da Jabir ya ce mata ai ta amince da aurensa da iman, dan haka cikin murna ammi ta karSeta.

Sai dai ta turSune fuska ta ce "Giwa ba zama na zo yi ba, magana zamu yi dan Allah"

Ammi ta ce "To shikenan, ko zamu shiga daga ciki ne?"

"A'a ba wani daga ciki, magana zamu yi a buWe a fai-fai. Wallahi giwa ki ji tsoron Allah, idan har kina son gamawa da duniya lafiya, mace sai tsabar son kanki a zuciyarki. Kawai kin juya mini tunanin Wa, ki rasa da wanda zaki haWa shi, sai auren ?ar tsintuwar ki, yarinyar da ki ka ce kin san iyayenta, ki ka gaza nuna su har rana mai kamar irin ta yau, kawai dan ki cuceni, wato sarauta ta bar gidanku, idan Allah ya yi jabir ya samu sarautar galadima, kin dai aura masa ita, dan ku mallake shi sai yadda ki ka yi da shi, wato kowa ya rasa, wanccan ba lafiya ce da shi ba, kin san ba sarautar zai yi ba, Mahmud kuma tun da Jamila ce ta ri?e shi, ba zaki bari abun arziki ya same shi ba, tun da ba ke yake yi wa kallon uwa ba, sai ki ka lallaSa zaki aura mata Wa na, to ba zai yiwu ba wallahi"

Ammi ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri Lubabatu, ki fuskance ni, Jabir fa shi ya kawo kansa, ya ce yana son iman, ba ni na takura masa sai ya auri iman ba, kuma shi ne ya bani tabbacin lallai kin amince wa auren nan"

"Ni ina na san ana yi, ana ?ulla mini kitimurmura, ina Wan sarauta ina auren shegiya da aka tsinto, wallahi ?ar tsintuwa ba zata samar mini da zuriya ba, idan ba haka ba a nemo iyayenta a nuna mini"

Tuni jikin iman ya fara rawa tana kuka, rumaisa kuwa ji tayi kamar ta mari iman, ba ta da kataSus, da an yi mata abu sai kuka saboda tsabar shagwaSa.

"Lubabatu shi Wa na kowa ne, iman kuma ?ar ku ce, meyasa lallai sun kun nuna mini, iyakata ne?".

"Ba wani Wa na kowa ne, idan na kowa ne ki aurawa adam mana, ko dai sarautar ki ka ?allafawa rai, sai kin mamaye komai, wallahi Wa na yafi ?arfin auren ?ar tsintuwa, ba?in halinki ne yake bibiyar ki da yaranki".

Tuni rumaisa ta hasala ta ce "Wai jabir Win banza Jabir Win wofi, me aka yi aka yi wani Jabir munafiki da shi, ban da ?addara ta Allah, ki kalli iman ki kalli jabir Win mana, wani sololo kamar an mari Wan akuya. Wai ku baku da wani buri sai ku zo kuna zagin ammi, me tayi muku?".

"Ke rufe mini baki, ko na zo na talitseki, ?ar matsiyata ban saka da ke ba, sa'arki ce ni?"

Ruma ta ce "Wallahi talitseni, dai-dai yake da taka kan Wan maciji, baku da magana sai ta sarauta, fir'auna ma ya mutu ya bar mulki, dan abun kunya, mijinki na can na jinya, ke da Wan ki kuna nan kuna fafutuka a kan wata sarauta, wannan ne abun alfahari dan za a aure shi? Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, wallahi jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ai ni idan mutum babban banza ne, bana ganin girmansa, tun ranar da muka je gidanki, ki ka ci mini mutunci nake ?ullace da ke"

Ammi jikinta har rawa yake, ta ce "Rumaisa ya isa haka, ku tashi ku shiga ciki" dan ammi ba ta taSa ganin ruma tana asalin tijara ba sai yau.

Laila ta ?araso falo ta ce "Ammi su shiga ciki su je ina? Rumaisa kin yi mini dai-dai, ai asara na ga matar da ta wofantar da mijin da ya gatantata lokacin yana da lafiya, yana ?asar waje yana jinya, tana nan tana shirme a gari, ita da Wan ta mara tarbiyya.
?ar wahala, tun da na sanki Lubabatu baki da al?ibla daga ke har Mummy, shiyasa rayuwa ta ?i yi muku yadda ku ke so, kuma albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da al?ur'ani, cigaba yanzu muka fara"

Ruma ta ce "Kuma in sha Allah, sai na dawowa da ammi Mahmud"

Laila ta ce "Dan Allah malama kwashi banzayen ?afafuwan ki, da aka saba bin bokaye, a bar mana part, kar a zuba mana masifa".

Hajiya Lubabatu ta nuna kanta ta ce "Laila har da su kaza a cin dan?o, ni ?ar ri?o za ta gayawa magana haka".

"?warai ?ar ri?o ba, ko nima zaki ce mini shegiyar ne? Ke sa'a fa ki ka ci, Jabir yana girmamani, da wallahi ashar zan WuWWura miki, zaki iya fita"

Su biyun duk suka ?ureta da ido, ba wanda ya fi Sata mata rai, irin cin mutuncin da rumaisa ta yi mata.

"Giwa a gabanki sirikarki suka ci mini tuwo ko, duk saboda wannan yarinyar, na faWa ba zan bari Wa na ya auri wannan yarinyar ba, da ban san asalinta ba, wanda ba na raba Waya biyu, ?ar gaba da fatiha ce, kuma zaku ga abun da zai biyo baya" ta fice tana huci.

Bayan fitarta, Ammi ta kalli laila ta ce "Laila mey....."

"A'a Ammi, daga ni har rumaisa ba wanda yayi laifi, nima fa ba son aurenta da jabir Win nan nake yi ba, saboda duk wani abu da ya shafi mummy, bana ?aunarsa na tsani matar nan kamar yadda na tsani mutuwata, ke kuma iman, idan aka kuma zuwa ana gaya miki magana, ki ka Sare baki kina kuka, ubanki zan ci, sokuwa kawai komai kuka, bayan kin san larurar da ki ke Wauke da ita".

Jikin Nusaiba duk yayi sanyi, ita dai tana yi wa iman

45 / 67