Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   60 / 67

177K to 180K   out of 199.9K words

yayyen ruma har da Mahmud, suka gaisa ya tafi Wakinsa.

Ruma ta bishi, ta bashi abincinsa, tare da yi masa ?orafin rashin kula Mahmud, sai dai bai tanka mata ba, ya nemi wuri ma ya kwanta.

Bikin Nusaiba ma ya fara ?aratowa, ammi tana ta shiri, wanda ranar yayi dai-dai da saura kwana Waya Mahmud ya tafi shi ma.
Sashin Ammi ya shiga, kasancewar ya Wan kwana biyu bai shiga ba, saboda zuwa lagos da suka yi, Ammi ta ji daWin ganinsa.

Kansa ya risunar ya ce "Barka da wannan lokaci"

Ammi ta amsa masa da "Barkanka dai, kana lafiya?"

"Alhamdilillah, na ce gobe in Allah ya kaimu ne tafiyarmu zan fara zuwa aiki"

Ammi ta ce "Haka Iman take gaya mini, Ubangiji Allah ya sa a fara a sa'a"

Ya ce "Amin" ya kalli Nusaiba ya ce "Kira mini baba uwani" Nusaiba ta tashi, ta je ta kira baba uwani.

Tana ganinsa ta washe baki za ta hau kirari ya ce "Bana bu?ata, kayanki zaki kwaso ki bar gidan nan a yanzu"

Gaba Waya suka kalleshi da mamaki, ya ce "Ke kin san me nake nufi, ni na ro?i rumaisa ta rufa miki asiri, tare da tunanin ko zaki shiryu, tun da ba zaki daina ba, sai kin bar gidan nan yanzu"

Ammi ta ce "Mahmud ban gane me kake nufi ba? Me ta yi ne? Tsawon shekaru ina tare da ita rana tsaka ka ce ta tafi?"

"Ke kin Wauketa mutum, kin kula da ita da iyalinta, ita kuma tsawon shekaru tana cin dunduniyarki, duk abubuwan da suke faruwa a sashin ki, Mummy na da masaniya a kai"

Gaban Ammi ya faWi ta kalli baba uwani ta ce "Uwani, da gaske yake yi?"

"Wuce ki kwaso kayanki ki bar gidan nan, ki je dan kanki, ko ba a Wauki wani mataki a kanki ba, hakkin mutanen da ki ka Wauka ba zai barki ba"

Mahmud ya ?i yi wa ammi cikakken bayani, ya kori baba uwani a gaban sauran hadimai, wanda ya san tilas maganar za ta watsu, ace ya yi mata korar kare ba tare da cikakken dalili ba".

Baba uwani na kuka, ta kwashi tsummokaranta, ta fita.

Gaba Waya ammi ta zama confused, Barira ta ce "Ai ni na san baba uwani ba zata sauya hali ba, nayi mamakin rashin tona mata asiri, da maman sabir ba ta yi ba".

Jin abun da ta faWa, ya sanya ammi ritsa Barira, barira kuwa ta kwashe komai ta gaya mata.

Ammi sai da ?afafuwanta suka nemi gaza Waukarta, saboda tashin hankali da zullumi, hadimar da ta amincewa tsayin shekaru, ita ce ta ci amanar ta.

Kasa jurewa tayi, a daren ta je gidan takawa, hankali a tashe, dan kuka take suka je gidan. Wanda hakan ba ?aramin Wagawa ruma da takawa hankali yayi ba.

Rumaisa ta tabbatar mata da ta san baba uwani muguwa ce, tun a lokacin da ta din ga gaya mata takawa mahaukaci ne, da lokacin da ta ce Mummy tana yi wa takawa asiri maganar ta koma kunnen Mummy.

Rumaisa ta tabbatar mata da cewa, Mahmud ya gaya mata ya sha ganinta cikin dare a sashin Mummy, amma ya ce kar su tona mata asiri a lokacin, saboda basu da cikakkiyar hujja, yanzun ma tun da ya ce ta tafi, yana da dalilin yin hakan, kuma ko daga baya an tayar da magana, suna da cikakkiyar hujja a kan ta yanzu.

Sai a lokacin ammi ta din ga tuna wasu daga cikin abubuwan da suka gabata, tabbas idan da babu munafuki a sashin ta, babu yadda za ayi wasu maganganun su din ga fita.

Sai dai a hakan ma, ruma ta Soyewa ammi binne-binnen da baba uwanin ke yi mata a cikin gidan.

Takawa ya din ga rarrashin ammi yana bata ha?uri, tare da yin faWa dalilin da ya sanya Mahmud ya kori baba uwani kai tsaye, ba tare da girbar abun da ta shuka ba.

Ammi ta daWe abun nan yana ci mata zuciya, ta daWe tana jinjina tsawon lokacin da baba Uwani ta yi, tana zaluntar ta, ta hanyar kwasar sirrinta tana kaiwa wajen Mummy.

Baba uwani bayan ta fita cikin kuka, ta kira Mummy ta sanar da ita halin da ake ciki, wanda hakan ya faru a dalilin ritsa Mummy da yayi suna waya da baba uwani, dan sai da suka samu saSani ma.
Babu kunya Mummy ta ce "Ba abun da za ta iya yi mata, sakacinta ne ya janyo mata"

Baba uwani ta sha mamaki, ba ta taSa tunanin abun da Mummy zata gaya mata kenan ba.

Sannu a hankali rumaisa ciki ke tasawa, tayi ta Soye-Soye, gashi yau da lafiya gobe babu, haka nan take zuwa makaranta.
Ga koke-koken ba gaira ba dalili, wai ita rasa abun da yake yi mata daWi.
Sai dai takawa yayi ta rarrashin ta, ya san ?uruciya ce da rashin sabo.

Iman kuwa kusan awanni kaWan sai sun yi waya da mai sunan baba, idan ta ma?ale a kan waya, har mantawa Ammi take yi da ita.

Ammi ta ce "Iman dan Allah ki ?yale yaron nan yayi aikinsa mana, ma?al-ma?al a kan waya ko gajiya ba kwa yi ne?"

Rufe fuska tayi tana murmushi, dan kuwa ba ta yi zaton ammi ta Wagota da yawan wayar nan ba.

?angaren mai sunan baba, yanayin aikinsa yayi masa daWi, sai dai kewar gida da yake yi sosai, sannan ya fuskanci akwai tarin kitimurmura da rashawa a aikin.
Sai dai yadda yake umar Win sa bai canza ba, ba ruwansa da kowa aikinsa ne kawai ya dame shi.

Sallama aka yi a office Win sa, ya amsa tare da kallon ?ofar.

Wani babban mutum ne ya shigo, fari sol da shi, cikin manyan kayansa.

Mai sunan baba ya yi masa ?uri da ido, ya ?araso ya zauna suka yi musabuha da mai sunan baba.

Ya ce "Namu ne ka na jin hausa ko da turanci zan yi" yayi maganar cikin guSatacciyar hausarsa ta cikakken bafulatani"

Mai sunan baba yayi murmushi ya ce "Ina kama da bayerabe ne?"

"To ai abun naku ne, wasu lokutan ba a banbance ku hausawa".

"Eh amma irin naku da kun ga junanku ku ke ganewa"

Mutumin yayi dariya, duk da yau ya fara ganin mai sunan baba, kamalarsa ta burge shi.

Ya ce "Masha Allah ya aiki?"

"Aiki Alhamdilillah"

"To da dai ba kai nake tararwa a office Win nan ba".

"Eh, sabon ma'aikaci ne ni"

Ya ce "Yauwwa ni fa in ce. Kayana ne nake ta sintiri ayi mini clearance, amma bayan gama biyan duk wani haraji sai wani hanya-hanya ake yi mini, ana dai nuna mini sai na bayar da cin hanci, sai dai ba dan babu kuWin ba, bayarwa ne ba zan yi ba. Tun da na san kayana ba na laifi bane"

Ikon Allah mai sunan baba yake gani, hatta yadda mutumin yake kallonsa, tamkar iman ce a zaune a gabansa.

Ya ce "Wasu irin kaya ne? Fanta ne, buredi da ?osai ne ko kuma shanu"

Mutumin ya sake yin dariya ya ce "Ka fa dame ni fa, ko dai babarbare ne?"

Cikin murmushin sa na ?asaita ya ce "Ba Waya, mai Wakina ce bafulatana, ai ni akwai amana a tsakaninmu"

"Ahhh ashe ma sirikinmu ne, ina fatan ka bayar da nagge 100, kafin a baka" yayi maganar yana ciro wayarsa daga aljihu da take ringing.

Ya cewa mai sunan baba "Afuwan dan Allah"

Ya kara wayar a kunnensa, yana magana da fulatanci, mai sunan baba yana fahimtar wani abun, sai dai ya ji yana cewa Ade a cikin maganarsa.

Ya gama wayar ya girgiza kai ya ce "Ade na da damuwa. Wai mahaifiyata na Waukko daga garinmu, na dawo da ita nan Lagos gabana, na din ga ganinta. Ni da matata fa ?an uwa ne, kuma akwai wasu ?an uwana da na Waukko duk muke zaune tare. Amma ta saka an kirani a waya, wai na rabota da danginta na zo na ajiyeta a nan, ita tunanin shanunta da awakinta ma take yi. Ace Allah ya yi mini rufin asiri, amma uwata na ?auye ai lamari ya Saci"

Mai sunan baba ba wai dan halayyarsa ce sakin jiki hira da mutane ba, sai dan son cigaba da kallon ?UDURAR ALLAH (Kar ku manta da sabon littafin NAZEEFA SABO NASHE, da tuni ya fara zuwar muku, kar ku yi ?asa a gwiwa wurin bin wannan ?ayattacen littafin)
Mutum mai matukar kama da matarsa, ya fara tambayar kansa anya mutumin ba shi da ala?a da Iman Win sa.

Hira suka Wan yi da mutumin, yana bashi labarin rigimar Ade, kuma ya ke gaya masa akwai mataimakin shugaban ?ungiyar fulani ta ?asa a familynsu, Ade Allah ya yi wa iyalanta rufin asiri, amma ita ta dage sai zaman ?auye.
Mai sunan baba ya bashi labarin, shi nasu gidan, da ?an uwansa, tare da tattaunawa a kan jajircewar iyaye mata idan aka mutu aka bar su da yara.

Haka suka din ga hira, daga baya suka yi exchange Win numbern waya, mai sunan baba ya ce zai sake duba maganar kayan na sa.

***
?an kwanakin nan, Mummy tana ta fama da ciwon kai, ta je asibiti an yi mata teses amma bai daina ba, ko san haske ba ta yi sosai.

A hankali kuma Allah ya taimaketa ya fara sauka, shiryawa tayi zata fita, tana son yin waya, amma tata ba network, dan haka ta karSi wayar ru?ayya ta saka lambar wayar da zata kira, ta yi wayarta.

Sai dai bayan kammala wayar, ta ga sa?o ya shigo wayar ru?ayya daga Jabir.

"Wallahi ru?ayya idan ba ki zo kin same ni ba, mun cigaba daga in da muka tsaya ba, zan watsa videos Winki, duniya kowa ya gani, and i mean it"

Bakin Mummy ne ya fara rawa, ?afafuwan ta suka nemi gaza Waukar gangar jikinta, cikin tsananin tashin hankali da mamki, ta dawo falo in da ru?ayya ke kallo. Fauziyya na chatting.

Tana zuwa ta jefa nata mata wayar, ta ce "Me wannan sa?on yake nufi?"

Gaban ru?ayya ya faWi, ta Wauki wayar, ta karanta, a take ta fara kuka tana girgiza wa Mummy kai.

"Ki gaya mini me sa?on nan yake nufi?"

"Mummy zan yi miki bayani dan Allah"

Danneta mummy ta yi tana hargagi ta ce "Ni zaki tonawa asiri ru?ayya, wace irin ala?a ce a tsakanin ki da Jabir? Wallahi gara na kashe ki, na kashe banza, akuya ce ke? Da ke za a haWa kai a janyo mini abun faWa? Ni Lubabatu da Jabir za su haWa kai su cuta? Ni?" Da ?yar Fauziyya ta janye Mummy daga kan ru?ayya da tuni numfashinta ya fara sama-sama.

Ruma ce zaune daga ita sai mini skirt da brezia, domin kuwa kayan ma ita yanzu damunta suke yi.

Ta ?urawa Adam ido, "Ya dai babyna, jikin ne?"

"To jiki ai sai Alhamdilillah, papa baka gano smoke Win ba haryanzu?"

"Mimi da na gano, ai da na gaya miki, bashir suna nan suna bincike a kan al'amarin, kuma an gano wurin da ki ka ce ana Wibar ma'adanai, mun yi magana da hukumar mu ta katsina ana targeting wurin, kama su ake son y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i red handed kamar yadda na gaya miki"

"Papa, na san na yi maka laifi, tun haWuwarmu yakamata ka san komai, amma na din ga yi maka wasa da hankali. Ka san dalili?"

Ya ce "A'a"

"A wannan lokacin da ka san komai, zaka yi aiki da zuciya ne, zaka iya Sata aikin, saboda kana kan jin raWaWin abun da ya faru.
Anty Aisha ta bani labarin komai, wanene kai, abubuwan da suka faru a rayuwarta da taka, rashin jituwaku tsakaninka da Mahmud, sannan a ?arshe ta ro?i da na auri mijinta, saboda tana ji a jikinta zan iya taimakonka, idan har zan rayu a tsakanin ?an bindigar daji marasa imani da tausayi, in zauna a cikinsu da ba?in taurin kai, har na din ga abun da nake so wasu lokutan, su ?yaleni, to lallai zan iya tan?wara zuciyarka da koya maka ha?uri da sassauta fushinka.
Na tubure na ce ni fa ba zan aureka ba, dan ba ka yi mini ba, mussaman da ba ma jituwa, amma ta cigaba da yi miki magiya, tare da ro?on in taimaki rayuwar mijinta, ita tayi iya nata ?o?arin ta kasa".

Rumaisa ta Wan yi shiru sannan ta ce masa "Lokacin da anty aisha za ta mutu, ta cigaba da nanata mini, ta bar mini jaririn ta, kuma ta bar mini mijinta, dan Allah kar in bari ?ar uwatta ta aureka, kuma in tabattar an samu daidaito tsakanin ka da Wan uwanka, domin samun farincikin ammi.

Papa, wakili na da saka hannu a yin garkuwa da anty aisha, dan ?an bindiga sun ambaci sunansa, cikin dare suna zaton duk mun yi bacci".

?irjinsa ya buga da saurin gaske ya kalleta.

"Amanarka na karSo papa, shiyasa nake iya ?o?arina da zuciyata da jikina domin baka kariya, da tabattar da cika al?awarin da na yi wa anty aisha. Ina neman afuwarka bisa wahalar da kai da na din ga yi, but Alhamdilillah atleast na cika wasu daga cikin alwashin da na yi"

Shiru yayi ya sunkuyar da kai, ya kasa cewa komai.

Rumaisa ta Wago kansa ta ce "Papa fushi ka yi?"

Cikin tsananin ?arfin hali, da hawayen idonsa ya kasa Soye damuwar, ya ce "Mimi ba ki yi mini komai ba, ni ya cancanci na yi miki godiya mimi, ban san da wasu kalaman zan yi amfani ba ma" yayi maganar yana kwanciya a jikin ta.

Ta kalli hannunta da hawayen sa yake Wiga a kan hannunta, ta saka hannu tana share masa hawayen, tare da shafa sumar kansa.

"Mimi ba kya so na? Saboda al?awarin aisha kawai ki ke tare da ni?"

"To ai ban san me zan ji idan ina son ka ba"

Yayi murmushi ya ce "Shikenan, but i already fall for you, ni ina son ki sosai rumaisa i love you, and i will surely keep loving you, to my last breath. Ina son ki rumaisa".
Ji ta yi tsigar jikinta na tashi, kalamansa na ratsa ko ina na jikinta, har wani lumshe ido take yi saboda daWin kalamansa.

Ta yi ajiyar zuciya ta sake cewa "Papa, jaridar da suke wallafa ci maka mutunci, lokacin da anty aisha ta rasu, Yasir ya bi diddigin gidan jaridar, daddyna ya gano wakili ne suke Waukar nauyinsa, dan ya ce mini sun taSa kiransa har aka nemi ya bayar da haWin kan cutar da kai, ya ce ba ruwansa. Kaga dole a cikin family ba za a rasa wanda suka haWa kai da shi ba, ake cutar da kai"

Ya lumshe idanunsa ya ce "Mimi kaina ya daina Waukar wannan abubuwan ma, bari na samu nutsuwa"

"Idan ka samu nutsuwar, ka yi bincike sosai a cikin gida. Sannan ka sani tun a yanzu ka sanya wa ranka cewar, zaka iya gano su waye, amma samun hukunci da adalci sai a wurin Allah, amma ba a wannan ?asar ba"

Ya numfasa ya ce "Ina sauraren Bashir ne, na ji me za su ce mini, nayi magana da su barrister ma, waWan da ki ka ce mini kin yarda da su, muna kan faWaWa bincike"

"Nima ni da ?an team Wina muna ta ?o?ari, Allah ya yi mana jagora" ya jinjina kai ba tare da iya yin magana ba.

Abu kamar wasa mai sunan baba yake ta ?o?ari akan kayan Alhaji Aminu Wan fulani, kuma kasancewar an samu sauye-sauye a wurin, cikin ikon Allah komai ya zo masa da sau?i, dan ana daf da releasing Win kayan.

Alhaji Aminu yana yawan kiran sa, su gaisa, shi kuma mai sunan baba, sai ya tambaye shi ina Ade, ya ce masa tana nan tana rigima.

Alhaji Aminu ya matsawa mai sunan baba, a kan lallai ya zo gidansa su gaisa, dan yana bawa Ade labarin sa, ita kuma ta ce tana son ganin sa.

Mai sunan baba ya ji a ransa yana son sanin ahalin Alhaji Aminu, ko zai samu abun da yake son tabattarwa, ko Alhaji Aminu yana da ala?a da Iman.

***
Tamkar za su kacame da dambe, haka suke musayar yawu, tamkar ba aminan da suka kwashi shekaru suna cin mushe ba, tamkar ba tare suke ?ullawa da kitsa duk wani hatsabibanci ba.

Mummy tamkar za ta ari baki, saboda ha?ilo da bala'i.

Hajiya Lubabatu a fusace ta kira Jabir a waya, a kan lallai ya zo tana son ganinsa, ta ajiye wayar ta kalli hajiya jamila ta ce "Kar ki sake kiran Wa na da mazinaci Wan iska, idan ma hakan ne, sai ki ce mazinata ?an iska".

"Na faWa Win, koda yake barewa ba ta gudu Wan ta yayi rarrafe ba, tun da sai da ki ka yi yawon tazubar ki ka gama ki ka tuba aka yi auren. Kin yi wa mijinki asiri, kin ya da shi a Germany, kin cigaba da watsewa a gefe, ke ki yi Wan ki yayi".

"Jamila kina nufin ni ce nake biye? ni zaki yi wa sharri? Ko kin manta kema irin abubuwan da ki ka shuka, yayan giwa da ki ka din ga sadaukarwa, da ?a?an Adam, ai ni ban kai ga aikata kisan kai kamar ke ba"

Jabir ne yayi sallama, suka yi shiru suka waiwaya.

"Sannu munafukin Allah ta'ala"

Jabir ya ce "Mummy lafiya kuwa?"

Mummy ta ce "Saboda kai watsatstse ne, mara mutunci, na amince maka na amincewa uwarka, amma ku ka zalince ni, wace irin ala?a ce tsakanin da ru?ayya har ka ke i?irarin yaWa hotunanta?"

Yayi shiru yana kallon Mummy.

"Wallahi lubabatu sai kun yi dana sanin abun da ku ka aikata mini, kai ba da ni ka ke zancen, dabba Wan akuya".

"Kar ki sake kiransa Wan akuya, ru?ayya ce babbar akuyar da ba ta san ciwon kanta ba"

Mummy kawai ta fice, zuciyarta na wani irin zafi, kuka take son yi amma ba ta son bayyana karayarta a fili.

***
Mai sunan baba ya amsawa Alhaji Aminu cewar zai kai masa ziyara ya gaida Ade, sai dai yana fargabar kar ya ga abun da bai yi tsammanni ba, zai fi kowa farin ciki, idan aka ce a sanadinsa Iman ta samu ko wani ne a danginta, duk da rashin hakan ba ya nufin zai juya mata baya ne.

Kiran Iman yake yi yana zancen zuci, ta Waga video call Win ta ce "Hi dear"

"My yellow, how are you?"

"Fine Alhamdilillah, ya aiki?"

"Ai akwai shi, yanzu salary ya shigo, na ce let me call the person close to my heart"

Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, mun godewa Allah" kallonta yake sake yi, hatta yanayin gashin girar iman, irin na Alhaji Aminu ne.

"Ya naga kana kallona ne, na canza ne?"

"Bakomai, yanzu ya za ayi da salaryn nan ne?"

Iman ta ce "Ai zaka shigo kano ko? Ka ce fa ?arshen wata zaka

60 / 67