Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   58 / 67

171K to 174K   out of 199.9K words

zata nemi wuri ta nutsu ta zauna ba, wannan kyan da take yi da she?i, da ?yar idan ba ciki ne da ita ba, a garin wannan rawar kan sai ta zubar da shi tukuna, nayi magana ta ce ita ba ta da ciki, manya ne suke haihuwa, wai ita kunun gaya take sha ko na sabulu? Ita dai ta sani"

Hauwwaliya ta ce "Gwaggo kunun sabaya ta ce miki bana sabulu ba, ta ce ni ma zata bani na din ga sha. Ni yanzu jira nake ta ce za ta saka azo a Wauke mu a tafi da mu gidan amarya".
"Oho muku dai, daga ke har ita".

Abubakar ne ya zo ya janye mai sunan baba suka fito, a mota ya kalli yadda umar Win yayi jugumm ya ce "Wai kuka zaka yi ne?" Yayi maganar yana dariya.

Mai sunan baba yayi masa shiru.

"Ango mai kuka, duk na gulma ne, da an ga Khadija za a ware, inyeee ango na mama". Ya din ga tsokanarsa, yayi shiru ya ?i kula shi.

Takawa da kansa ya saka Iman a mota laila da ?awayen ammi a motar suka je suka kai iman.

Hatta su Fauziyya sai da suka je gidan iman, domin ganin ?wal uwar daka, sun kukkushe abubuwan da dama, sai dai duk yadda suka so gano makusa a jikin angon basu gano ba.

Gidan Iman Wan madaidaici, dai-dai zaman amarya, sai dai an zuba mata dakakkun kaya, na gani na faWa.

Zuwansu babu daWewa, su mai sunan baba suka ?araso, har da Mahmud a tawagar angwaye.

Aka yi adduoi, ?awayen ammi suka yi musu nasiha sosai da sosai suka tafi.

Takawa ya kalli mai sunan baba ya ce "Kamar yadda ka kawo mini taka ?anwar ka ce amana, nima ga tawa nan, amanar marainiya ce a hannunka"

Ya kalli in da ruma take zaune kusa da iman, suke ta kuka, ya kalleta ya ce "Mimi tashi mu tafi" yayi maganar yana jan hannunta, da ?yar ta tashi, iman sai kuka take suka tafi.

Takawa sai da ya zazzarewa Nusaiba ido, sannan ta tashi, saboda tare suke faWuwa suke tashi da Iman a gida.

Kowa ya watse, daga shi sai iman, sai dai sun shafe lokaci, ba tare da wani ya ce uffan ba, mai sunan baba ya tashi, ya je ya rufe gidan.

Ya dawo falon, ya tarar da ita a in da ya bar ta a zaune, ya ?arasa gabanta ya mi?a mata hannu ya ce "Ranki ya daWe bisimillah"

A hankali ta kalli hannun nasa, amma ta kasa motsi, ya ?ara mi?a mata hannu.

A hankali ta mi?a masa nata hannun, ya ri?e ta, ta tashi tsaye ya ja ta zuwa Waya daga cikin bedroom ukun da yake falon.

Ya taimaka mata ta cire Alkyabbar jikinta, ya saka hannu ya Wago fuskarta, fuskar tayi pink saboda kuka, sai jan mayafin take, tana rufe ba?in gashinta wuluk, da ya sha gyara.

Kallonta yake yi, wai wannan zu?e?iyar yarinyar ta sa ce, Alhamdilillah ala kulli halin.

Ya Wan lumshe idonsa sannan ya buWe su ya ce "Kukan me ki ke yi ne?".

Tayi shiru ba ta ce komai ba.

"Mu je mu yi alwala" ta jinjina masa kai, toilet Win cikin Wakin suka shiga, ya kunna mata famfo ya ce "Bismillah" tare suke alwalar, sai dai da ya kai hannu idan hannunsu zai haWu, sai ta janye nata.

Ya shammaceta ya Wan watsa mata ruwan hannunsa, ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Salla suka yi raka'a biyu, yadda mai sunan baba ya din ga kwararo addu'a ba ?aramin burge Iman yayi ba, dan a rayuwarta tana ?aunar namiji mai addini.

Bayan sun idar sun shafa, ya koma falo, ya shiga kitchen in da Mahmud ya ajiye kaji, da lemuka ya Waukko ya dawo Wakin.

Gaba Waya a takure take, sai sunkuyar da kai take kamar mara gaskiya.

"Yaluwa, me zaki iya ci a nan?"

Murmushi ta yi ta ce "Yaya umar yaluwa kuma?".

Shima Murmushin yayi mata ya ce "Yeluwa mana, balarabiya a Nigeria".

"Idan Larabawa sauka ji ka babu ruwana".

Yayi murmushi ya tura plate Win gabanta ya ce "Bismillah"

"Na ?oshi" ta faWa a hankali.

Wata hamma ta kamata, tayi a hankali tana lumshe ido.

Ya Wan ?are mata kallo ya ce "Bacci ki ke ji zaki kwanta ne?" Da sauri ta ce"A'a".

Ya sake cewa "Bacci ko yunwa, wanne ne dalilin hammar?"

"Yunwa"

"Oya ci abinci" tamkar za ta nutse, haka take Wan mintsunar naman tana kaiwa bakinta tana sunkuyar da kai.

Tashi yayi ya bata wuri, ya tafi gaban wardrobe ya buWe, an shirya mata kayan sawarta, kuma duk ciki ba wanda aka Wauka na lefenta aka Win ka.

Ya sauya kaya zuwa wata jallabiya, ya cire agogon hannunsa ya ajiye.

Ta nannaWe sauran da ba ta ci ba, ta ajiye, ta tashi zata fita, ya ce "Ina zaki?"

"Can Wakin zan je na kwanta"

"Mhmm, Ashe da bayan Waurin aure, sai ki yi zamanki a wurin ammi, nima na zauna a wurin mama. Dan na kusa yin kuka nima Wazu kamar ke, bana son yaran nan su raina ni ne" tayi gajeriyar dariya.

Ya ce "wanko hannun ki zo"

Ta ce "To" ta shiga ta wanko hannunta, ta fito.

"Ki kwantar da hankalinki, ba abun da zan yi miki nima tsoro nake ji kamar ke, a gajiye ma nake kaina ciwo yake, i know what you are scared of, am scared too, ki shirya ki kwanta" wata irin Muguwar kunya ce ta kamata.

Har ?o?arin tuntuSe take yi, ta nufi gadon ta kwanta.

"In baki bargo ne?"

"A'a yaya umar ai zafi ake yi "

"Shi hijjabin da kayan jikinki iska suke baki?"

"A'a"

"Trust me, ba abun da zan yi miki yanzu, nima tsoronki nake ji, ki sassauta kayan mana"

Da ?yar ta canza kaya, zuwa wata doguwar rigar bacci, mai balance, ta raSa da ?yar da kwanta a bayansa.

Ba tare da ya waiwaiya ba ya ce "Kiyi Addu'a"

Ta amsa da "To"

Sai da ta tabbatar da gaske ba abun da zai yi mata, sannan ta yi bacci.

***
Rumaisa a gidan ammi ta so kwana, amma takawa ya ce bai yadda ba, tun da suka koma gida tayi wanka, take mitar ta gaji sosai.

"Papa ka yi mini sannu na gaji fa"

"Lokacin da nake cewa ki nemi wuri Waya ki zauna, ai baki ji ba"

"Mhmm, dan Allah kayi mini tausa to, ?afata ciwo bayana duka jikina ma"

Takawa ya ce "Maganinki kenan"

"Wayyo mama na gaji, ka ce mini sannu"

"Ke ni tausayin ?anwata ne ya dameni yanzu, ta shiga sabuwar Rayuwa Allah ya bata ikon jure ibada"

"Wai Iman, ai mai sunan baba ba irinka bane, na san ba zai mata abun da ka ke yi mini ba"

"Allah ko, saboda ga shugaban waliyyan ?arshen zamani ko?"

Ruma har cikin zuciyarta ta ce "Allah da gaske nake, shi fa mai sunan baba babu ruwansa".

Ba ?aramar dariya ta bawa Adam ba, kuma ita har ga Allah take gaya masa iya gaskiyarta.

"To ai shi idan ba ruwansa ke da ruwanki" da sauri ta Sata fuska ta ce "Dan Allah wallahi bani da lafiya, gashi kuma na gaji".

"Lokacin da nake hanaki ai ba kya ji, maganin mara ji kenan" ba yadda ta iya da papa, haka ta ?yale shi.

Bayan komawa bacci bayan sallar asuba, ringing Win wayarta ya sanya ta farka, murya ?asa-?asa tayi sallama.

Nusaiba ta ce "Amarsu ta ango, baccin gajiyar ne haryanzu baki tashi ba?"

Iman ta ce "Bari Anty Nusaiba, gajiya fa akwaita"

"Ko a taho da ruwan zafi"

Kallon in da mai sunan baba yake kwance tayi, sai dai ya juya baya ta ce "Anty Nusaiba sai ka ce wata mai jego".

"To idan ba mai jego ba ce yanzu, nan da 9months dai an zama"

"Ina ammi?"

"Tana can tare da sauran ba?i, ita ta ce na kira ki ma, zaki yi ba?i wanda ba su samu zuwa jiya ba, za a taho miki da abinci"

Iman ta ce "To, Allah ya kawo su lafiya, ke ba zaki zo ba?"

Nusaiba ta yi dariya ta ce "Ai ruwan zafi na ce zan kawo miki, tun da kuma ba kya so shikenan"

Tayi dariya ta katse wayar ta ce "Allah ya shiryeki Anty Nusy"

"Ai da kin gaya mata ba ayi komai ba, tun da shi take son ji"

Gabanta ne ya faWi, ba ta san idonsa biyu ba, ya juyo gaba Waya ya zuba mata ido, ta saka hannu ta rufe fuskarta.

Yayi murmushi ya janye hannun ya ce "Da kin gaya mata, duk a tsaroce ki ke, nima haka, duk tsoron juna muke ji, amma zamu iya nemanta da ruwan zafinta nan kusa ko nesa kaWan".

Wato ba ?aramin mamaki abun da mai sunan baban yake faWa yake bata ba, bata taSa zaton Wannan maganganun daga bakinsa ba.

Hular kanta da ta zame, ta bawa gashinta damar bayyana, ya shafa gashin ya ce "My pretty yellow. Tashi mu kintsa kan ba?in naki su ?araso".

Ta tashi zaune ta ce "In haWa maka ruwan wanka ne?"

"Kar ki damu da ni, yi wankan ki"

Kafin Iman ta fito, cif ya Wame gadon, gidan babu wani datti dama.

Kasancewar baya Wakin, ya sanya ta saki jikinta, ta shirya ta fito ta same shi a falo, yana ta ?an dube-dube.

"Yauwwa ?araso ki ga gidan naki, Wan abun da talakan mijin naki yayi miki"

Ta ?arasa ta ce "Ni wannan gidan ya fi mini kowanne kyau da tsari".

"Really?"

"Yeah"

"Jazakillah khair for appreciating it, Allah ya yassare mini in yi miki wanda ya fi wannan"

"Amin ya Allah" tare suka zazzagaya, ta din ga yabon gidan, da yabawa ?o?arin sa.

Aka ?wan?wasa gate Win gidan, Umar ya je ya buWe, ya ga Usman da Abdallah, da ledar viva a hannunsu.

"Mai sunan baba ko mu koma ne na ga kana kallonmu, mama ce ta bayar da abinci mu kawo" buWe musu yayi, ya juya ya koma falon.

A kujerar da iman take ya je ya zauna, cikin murna Iman ta ce "Yaya usy sannunku da zuwa"

Usman ya ce "A'a ai mu yakamata mu gaishe ki, ina kwana antynmu"

Iman ta ce "Kai dan Allah har ka bani kunya"

Ya ce "Ai girmanki ne, dole a baki"

Ta shiga yi musu bangajiya, tare da tambayarsu ya mama.

Abdallah yayi ?asa da murya ya cewa Usman "Ka tashi mu tafi, gulma ce a bakina, kar na yi misbehaving a samu akasi"

Usman ya ce "To mu tafi, nima ita nake son yi"

Suka tashi Abdallah ya ce "Bari mu tafi".

"Haba yaya Usman, daga zuwanku, ko ruwa ban baku ba"

"Bakomai ma sha a waje, tun da mai gida ya haWe rai, baya bu?atar mu ne sai anjima"

Bayan sun fita ta ce "Yaya umar ka din ga dariya mana, ko smiling ne"

"Ban iya ba, tun da ke kina yi ai shikenan deejangala, bari mu karya ko, dan ni na fara jin yunwa".

Tare suka karya, duk ita duk a Warare take, tun da suka fara ba?i ya fice ya bar gidan.

Usman kuwa gulmar mai sunan baba suke yi, wai yadda ya wani zauna a kusa da Iman, wai shi mai gida.

Suna tafe rumaisa ta kira Usman, ya Waga ya ce "K???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e kuma meye zaki dame ni?".

Ta ce "Daga kira me nayi maka to?"

"Ke rabu da ni, nima aure nake so rumaisa, ke kin yi aure, mai sunan baba yayi, Aliyu da yaya Habu suna hanya, jiya dan abun takaici, rige-rigen katifar mai sunan baba muka din ga yi, da tsofaffin kayansa. Kin ga yadda yake wani basarwa yau da muka je, wai shi maigida. Ke ma kina ta ?arshe a gidanmu, amma ?iri-?iri daga sunanki rumaisa an mayar da ke mimi, saboda aure, kallemu ni da Abdallah aka bawa kwanukan abinci muka kai musu. Allah ka aurar da ni, ko babyn nan a din ga ce mini"

Rumaisa dariya har da tuntsurawa, "Zaki yi dariya ne, wato ke kin tsallake, mijinki na ta lallaSa ki, zuwa zan yi mu dai-daita da Hauwwaliya, daga baya mu yi kuWi a tare, dama mutuniya ta ce, tun da yanzu mata sun fi son mai kuWi muyi tuwona maina, kar na je na lalace"

Shi har ga Allah yake maganar, takawa da yake jin su ya ce "Usman idan ka lalace ina muka kama? ka samo mata, in dai aure ne zan yi maka na baka jari"

Usman ya ce "Subhanallah, Allah ya taimake ka dan Allah ka ce ba ka ji abun da na ke cewa ba, har kunya ta kama ni".

Suka yi tayi masa dariya.

***
Ba?i suka fara watsewa, saboda an kammala biki.

Gidan Iman ma mutane suka yi ta sintirin zuwa gidan ta, mai sunan baba yayi burus da ita, har ta Wan sake daga tsoronsa da take ji.

Yau kiran sallar farko na asuba, ya tashi yayi nafilfilinsa da karatun Alkur'ani, ana daf da fara kiran sallar asuba, ya tashi da niyyar tashin Iman ta yi alwala.

Sai dai zancen ya canza, maimakon first night shi first asuba yayi, ?arshe sai da hasken rana ya hudo, sannan sallar asubar nan ta yiwu.

Mai sunan baba kenan, komai nasa daban ne, sai dai kamar wanda ya yi laifi, duk ya diririce, mussaman ganin tana kuka.

Bayan ta idar da sallar asuba, ta kifa kanta a kan sallaya, a hankali ya kira sunanta "Khadija"

"Na'am"

"Ki tashi ki kwanta mana".

"A'a bakomai, ai gari ya waye ma"

"A'a ki kwanta dai ki huta, kina bu?atar wani abun ne?".

Ta ce "A'a"

"To tashi ki kwanta"

Ya Wagata ya rakata kan gadon ta kwanta.

Har zai tafi ya ce "A cewa Nusaiba ta zo tayi aikin nata, ta kawo ruwan zafin duk da ma dai na yi da kaina".

Rufe fuska kawai ta yi ta, lumshe idonta tana murmushi.

?iri-?iri mama ta kira mai sunan baba, ta ce masa ma?wabta za su zo, amma ya ce kar su zo, ba ta jin daWi.

Abun da Iman tayi tsammanni, da kuma wanda mutane suke jiye mata, ba shi ta tarar a gidan mai sunan baba ba, mutum ne matu?ar kulawa.

Aikace-aikacen gidan kuwa ba ruwansa, tashi yake yayi abun sa, da ta motsa sai ya ce ta zauna ta huta, shi tausayin ta yake ji.

Ranar da zai koma kasuwa kuwa, shagwaSa iri-iri a wurin Iman, kamar kar su rabu.

***

Ihun da rumaisa take yi ne tana salati, ya sanya takawa fitowa daga toilet a hargitse, ya nufota.

"Menene lafiya?"

Ya tarar da ita bacci take yi, tana ta fizge-fizge tana son ta tashi, ta Waga murya tana "La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin".

Da sauri ya Wagata ya din ga karanta mata adduoi, yana tofa mata, ko da ta buWe ido ta ganshi, ta saka ihu ta ?wace tana haki.

"Mimi lafiya kuwa? Menene?"

"Ba kaine ka zo idonka na haya?i ba, zaka huda mini cikina da faratanka ba".

Gabansa ne ya faWi ya ce "Ni kuma mimi?".

Eh mana tayi maganar hawaye sharkaf fuskarta.

Jiki a sanyaye ya ce "Mafarki fa ki ka yi, ni ina banWaki".

"Da gaske mafarki ne, ba ka fasa mink cikin ba?"

"Duba ki gani".

Ta shafa cikin ta ta ce "Ni fa tun ina gida nake mafarkin idonka na ci da wuta, zaka soka mini farce a wuy, har a gaske fa watarn idonka yana yin haya?i"

Ya Wan yi jimm sannan ya ce "Ki yi addu'a ki cigaba da baccinki mafarki ne"

Ta ce "Ba zan iya ba tsoro nake ji"

Ya rungumeta ya ce "Ki yi ta Addu'a"

Yayi shiru yana tunanin kenan rumaisa ciki ne da ita? In dai Aisha tayi irin wannan mafarkin, to Sari take yi, amma rumaisa ta ce masa tun a gida take irin mafarkin.

Wata guda da auren su Iman.
Mai sunan baba bai taSa zaton zai iya zagewa ya yi soyayya haka ba, babban abun da yake ?ara masa son Iman bai wuce matu?ar biyayyarta ba, da soyayyar da take yi wa mama, da ?an uwansa ba, dan haka yake ?ara iya ?o?arin sa wurin ganin ya kyautata mata.
Tuni ta cigaba da zuwa makarantar ta, wasu lokutan kan ta dawo ya zo gida ya rage mata aiki, ranar kuwa da zata kai shida a makaranta, har makarantar yake zuwa kai mata abinci babu ruwansa.

?awayenta suna yawan faWa mata, tayi dacen miji mai son ta. Idan za ta tafi makaranta idan ba zai samu kai ta ba, shi ne yake bata kuWin mota.

Tana zaune a falo da daddare tana shige -shigenta a system Win sa, tana typing Win wani assignment, ya fito daga bedroom ya kwanta a kan kujerar da yake, ya Wora ?afafuwansa a kan cinyarta ya ce "Me ki ke nema a computer ta?"

Ta shagwaSe ta ce "Dubawa nake ko zan ga hoton ?an mata"

Dariya yayi ya ce "Ni ina ruwana da wasu ?an mata, ke ma dan kin li?e ne ki ka same ni"

"Ko kuma mun li?e ba" tayi maganar tana tura baki.

Tashi yayi zaune ya rungumota jikinsa ya ce "Na yadda ni na li?e, tun a kallon farko da na ganki, na zata ma da aljana ce za ta aure ni, ashe ?ar autar ammi ce"

Tayi dariya ta ce "Ni fa da tsoro ka ke bani my, i just felt for you, ashe duk fasa aurena da ake a baya rabonka ce ni, Alhamdilillah for having a good husband like you my faruk" tayi maganar tana shafa sajensa

Murmushi yayi yana jin wata annashuwa, da soyayyarta na ratsa shi, ya sake rungumeta ya ce "Deejana, my pretty yellow girl, gaskiya kina so na da yawa".

"To ka ce kana so na nima"

Wata ?ar dariya ta bashi, ya ce "?aukko carbi, ina faWa kina lissafawa, har sai kin ji kin gamsu da ina son ki"

Iman ta sake narke masa ta ce "Ni wa?ar soyayya ma zaka yi mini"

"TaSWijan, ai muryata ba ta wa?a ba ce, ban ma iya ba deeja"

"Muryar ka ta tsorata mutane ce" tayi maganar tana yi masa dariya.

"Eh ai an fi son haka, monster haka ba raini, tashi mu je mu kwanta, zaki school gobe in Allah ya kaimu"

Ta ce "To, bari na kashe system Win"

"Ahh, Baby an yi maka Gmail"

Mai sunan baba ya ce "Ba zaki daina babyn nan ba ko? Baby kamar Wan daudu, gara ki ce mini faruk Win ai".

"Ai a waje ne ake maka kallon monster, ni a wurina babyna ne"

"DaWinta ke ma a da monster ki ke gani ai".

"Eh yanzu kuma baby ba" tayi maganar tana duba Gmail Win.

Message ne a kan ana nemansa a Lagos zai je interview.

Ya ce "Anya wannan message Win nawa ne? Bana tunanin nawa ne"

"To na waye, naka ne mana"

Zai yi magana sai ga message Win Mahmud.

"An kiramu interview lagos, ban sani ba ko ka ga message Win, ranar Sunday zamu tafi, za ayi interview Monday, mun samu aikin nan"

Nunawa Iman yayi yana cigaba da mamakin abun, tamkar dai mafarki.

Iman ta din ga murna, tana addu'a, tamkar

58 / 67