Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   26 / 67

75K to 78K   out of 199.9K words

kawai, ko ka gaya wa turaki, na san komai zai zo da sau?i" sauke numfashi ya yi, ya tashi ya fice.

***
Tun da Adam ya fara hawo wa step Win bene, yake jin ?auri, yana hawa falon saman, ya tarar da ya turnu?e da haya?i, kuma haya?in daga kitchen yake fitowa.
A sukwane ya nufi kitchen Win, ya na zuwa ya tarar da rumaisa tana suyar wainar fulawa tana tari, Saboda ?aurin manja.

"Ke meye haka? Me ki ke yi?"

Ta waiwaya ta ce "Girki nake yi"

Da sauri ya ?arasa yana ?o?arin kashe gas Win, dan tuni suka haWa baki da iman, direbanta ya Wuro mata.

Tarewa ta yi ta ce "Girki fa nake yi na iya"

"Matsa, ban ce kar ki kuskura ki ce zaki yi girki ba?" BuWe masa flask ta yi ta ce "Ka ga fa, na iya" wainar fulawa ce ta yi sa?a mai kyau, sai ?amshin attaruhu take.
Ba ?aramin mamaki ta bashi ba, amma a fili ya ce "Idan ki ka yi mini gobara a gida, sai na casaki".

Ta ce "Eh na yadda" ya gyaWa kai ya fice.

Kusan awa guda, ya ma manta da batun rumaisa ya tuna kar ta yi wata aika-aikar, ya le?a falo, ya hangota tana ta suWar baki tana cin yaji.

Ganin tana lafiya, ba wani abu da ya faru, ya sanya ya nemi wuri ya kwanta, dan a gajiye yake sosai.

Sai dai bacci ya gagare shi, tunani daban-daban ya addabi kwanyarsa, ya rungume pillown sa, ya rintse idanunsa, ba ya son tuna yana da tarin matsalolin da ya kasa soloving Win su. Ga wani abu da yake bijiro masa ba gaira babu dalili.

Tashi ya yi ya kunna fitilar Wakinsa, ya tafi kitchen, sai dai ya tarar da rumaisa ba ta yi bacci ba, tana ta gyara abubuwan da ta Sata, tana tsaye a gaban sink tana wanke-wanke.

Bai ce mata uffan ba, ya Wauki heater, ya zuba ruwa ya jona, ita ma ba ta kula shi ba, ta cigaba da aikinta.

A ransa yake yabawa mahaifiyar rumaisa da yayyenta, dan a ?an kwanakin da suka yi, ya fuskanci tana da ?o?arin tsafta.

Tea yake son haWawa, ga ruwa ya tafasa amma sai duru-duru yake yi.

Ta kalleshi ta ce "Rumaisa, dan Allah tun da na ga kin iya girki, dafa mini tea, zan sha. Shi ne abu mai wahala a wurin ka, bari dai na taimaka maka, ai tun da na ga ka Wauko kofi na san shayi zaka sha, a gida ma kusan kullum sai su Yaya Aliyu sun sha shayi da daddare".

Ta taka kujera, ta buWe wata drower, ta Wauko Lipton, da kayan shayi, wanda bai san a in da ta same su ba.

Ta zuba a cikin ruwan zafin, ta sake tafasawa, ta Wauki ?aramin flask ta juye masa, ta haWa masa da kofi a kan tray, sannan ta ce "Gashi nan, kar ka damu ba sai ka yi mini godiya ba, dan na san ba za ka yi ba, muna da irinka a gidanmu. Idan ka gama shan shayin, ga omo da soso, ka wanke kofunan, kar ka bar mini kwanuka wani abun ya bi".

Kamar soko haka yake kallonta, ta Wauki wani Wan bowl, ta zuba uban cabin da madara da sugar, ta fice.

Washegari ta tashi da safe, tana aikace-aikacen ta, barira Waya daga cikin hadimanta, ta kawo abinci ta ce na takawa ne.
Ta karSa ta ajiye masa, dan da baba uwani ta gaya masa rumaisa ta ce a daina kawo abinci, cewa yayi su ?yaleta su cigaba da kaiwa.

?akinsa ta shiga da kayan mopping, ta tarar yana banWaki yana wanka, ta karkaWe masa gadon, ta gyara ta kalli gadon bai gyaru sosai yadda yakamata ba, ta ce "Oho, ni a gidanmu babu gado sai katifa, hakan ma na yi ?o?ari ai".

Idonta ne ya sauka a kan side bed, in da ya sha shayin, nan ya bar kwanukan, "Kam bala'i, Wa ya bar wa kwanukan nan a nan?" Ja ta yi ta tsaya tana jiran fitowarsa.

Rigar wanka ce a jikinsa, sai dai gaban rigar a buWe yake, gashin ?irjinsa ya kwanta saboda ruwa, da sauri ta kawar da kanta gefe.

"Ya aka yi?".

Ba ta kalleshi ba ta ce "Eh kwanukan da na ce idan ka gama shan shayin ka wanke na gani a nan".

Ya ce "Eh, idan kin gama ki fita da su ki wanke"

"Ni na sha maka da zan fita da su in wanke?"

Ya kalleta ya ce "Me ki ka ce?" Ta girgiza kai ta ce 'Bakomai".

"Oya kwashe su ki fita da su, ki je ki wanke, sannan kan na gama karyawa, ki shirya, zamu je gidan turaki".

Ta ji daWi za su fita, amma babban abun da ya bata haushi, bai wuce sakata fita da kwanukan da shi ya mora ba ita ba.

Wata turkey abaya ta saka, blueblack fuskar nan fayau babu ko kwalli, ta yi ta shafa turare, dan akwaisu available a kan mudubinta, dan ko a gida ta saba, dan Abdallah har Sarauniyar turare yake ce mata.

Suna tafe a hanya, tana kallon titi, tana son gane hanya, dan so take wataran ta Salle ta tafi gida.

A gidan turaki suka tarar da Jabir, da shi da Jamil ga kuma Zainab da Mummy, Samha ce ba ta nan.

Rumaisa ta gaishe su, sai dai ba wanda ya amsa mata da mutunci sai Zainab.

Adam ya ce "Zainab nema mana iso wurin mai girma turaki" ba musu Zainab ta tashi.

Rumaisa da sun haWa ido da Jabir take galla masa harara, haka Jamil da yake ta kallonta a wula?ance.

Aka yi musu izinin shiga wurin turaki, turaki yana ganin rumaisa ya fara murmushi.

Ita ma Murmushin ta yi ta ce "Barka da wannan lokaci ranka ya daWe".

"Barkanmu dai ?ar albarka, ya gidan ya ?o?ari?"

Ta amsa da "Alhamdilillah"

Adam har le?a fuskarta yake, ya ga ko ita ce ta nutsu haka.

Shi ma suka gaisa da Adam, Adam ya ce masa sun zo su yi godiya ne, tare da yi musu bangajiya na hidima da aka yi.

Turaki ya yi musu nasiha sosai, mussaman ma Adam, a nasihar rumisa ba komai take fahimta ba, mussaman da ta ga da Adam ake.

Bayan turaki ya gama, yayi musu addu'a sosai, Adam yayi ta godiya, ya ce masa za su je wani wurin daga nan.

Rumaisa ta ce "Babana, yaushe zaka zo gidanmu, na iya abinci in dafa maka duk abun da ka ke so?" Yayi murmushi ya ce "Za a zo ne in sha Allah".

Gudun kar ta fara sakin layi kamar yadda ta saba, ya sanya adam sakata a gaba suka fita, sai dai a wannan karon sai suka fita ta ?ofar da zasu fita haraba kai tsaye, ba tare da bi ta falon gidan ba, sai dai suna fita suka yi kiciSis da Samha!

Ayshercool.
08081012143
*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?




Adam yayi ta maza ya ce "Au dama kina nan? Mun wuce su mama a falo ban ganki ba ai".

Cikin matsanancin takaici ta ce "Meye na borin kunya kuma? Ai ba ka so ka ganni Win ba ne? Tun da har ka shiga ta falo, ka biyo ta nan za ka tafi".

Rumaisa ba ta kula Samha ba, dan ba zata manta fuskar ta ba, ta mayar da hankali wurin tsinkar furanni da ke wurin, sai dai tana jin duk abun da suke faWa.

"Yanzu da ma adam a kan wannan abar ka wula?anta ni, ka ?i ka aureni? Yanzu wannan abar wani abu ta fi ni da shi, yarinyar da ba ta kai a kirata mace ba ma, an ya ka yi mini adalci kenan? Soyayyar da na nuna maka tsawon shekaru shikenan ba ni da wata makoma?"

"To ni idan ba mace ba mace ba ce, namiji ce ni?" Rumaisa ta yi maganar tana ri?e ?ugunta.

Adam ya kalli rumaisa ya ce "Wuce ki je mota ki jirani"

"To saman motar zan hau ko ?ar?ashin tayoyi? Tun da a rufe take".

"Duk in da ya yi miki" kallon banza ta yi wa samha ta wuce.

Samha tana ta tunanin a ina ta san fuskar rumaisa ma, ta kasa tunawa, ta ma fi cika ido a hotunan bikinsu, a zahiri kuwa ?waila ce ta gaske.

"Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta Samha? Da auren wuri aka yi miki, ko baki haifeta ba kin kusa, wannan ai salon ki janyo wa kanki raini ne".

"Ban damu ba adam, ba raini ne a gabana ko akasin haka ba, ni batun soyayyaya ta ce a gabana, wallahi ka cutar da ni Adam".

Adam ya Wan yi shiru, sannan ya ce "Ban cutar da ke ba Samha, abun da nake son ki gane shi ne, komai mu?adarri ne na Allah. Daga haWuwata da rumaisa, zuwa lokacin da na aureta, da zan gaya miki zaki gane aurena da ita ?addarar Allah ce".

"Ba ka son ta kenan?"

"Ba zan ce eh ba, kuma ba zan ce a'a ba, ki yi ha?uri ki cigaba da addu'a, idan da rabo sai in aureki, idan kuma babu ko yi ha?uri, ki auri wani, kar ki ce zaki cigaba da zaman jirana samha".

Rumaisa kuwa ranta a Sace, ta ?arasa in da motarsu take, tana zuwa ta ga Jamil da Jabir a tsaye a wurin suna magana, ba ta kula su ba ta tsaya, tana hura hanci.

Jamil ya ?arewa rumaisa kallo ya ce "Lallai, Adam sai ka ce makaho, dan Allah ina mamora a tare da wannan yarinyar? Me wanna za ta tsinana masa a zaman aure? Yanzu wannan ya zaSa ya bar Samha? Saboda wannan abar?".

Jabir ya ce "Kai ba ka san komai ba ai, ba ta da kunya ne yarinyar nake gaya maka, kai ka ga wahalar da ta din ga bashi, ka san ita ta dawo da jaririn fulani, kan ta faWi fulanin ma ta rasu, sai da aka kai ruwa rana, ba ta da kunya"

Zabura Jamil ya yi ya ce "Kana nufin da gaske wannan yarinyar ce, ta dawo da yaron wurin aisha?".

Jabir ya ce "Tambayeta ka ji"

Juya musu ?eya rumaisa ta yi, tana wasa da ?asa da ?afarta.

"Ke, da gaske kin ga fulani, kin ganta a hannun ?an bindiga, suwaye? Ya aka yi suka kasheta?" Yayi maganar cikin rikicewa yana kallon rumaisa,ya na jin tamkar yanzu A'isha ta rasu.

?aga kai Rumaisa ta yi ta kalleshi, ta yi guntun tsaki.

"Magana nake yi miki, aisha ?anwata ce, jami'in tsaro ne ni, ki gaya mini abun da ya faru, ko kuma ?arya ne kawai haWin baki ne?" Yayi maganar kamar zai kaiwa rumaisa duka.

She?e?e rumaisa ta ce "To mijinta ma shi Adam Win ban gaya masa komai ba, balle wani kai, ba ruwanka da ni kuma, wallahi ka sake ce mini wannan abar, sai na yi maka rashin mutunci, mai na yi muku, ni na ce kar ya auretan? Wannan masifaffiyar matar na na Wauka ma babar wasu ce".

Daga nesa da ya tunkaro su, ya hangi rumaisa tana zazzaga masifa, Jabir ya ri?e hannun Jamil, ya ce kar ya yi magana.

Adam ya ?araso ya ce "Lafiya kuwa?"

Rumaisa ta ce "Ce mini yayi wai wannan abar, ni na ce kar ka auri waccan matar, da za su din ga ce mini wai wannan abar, shi kuma wannan har da ce mini mara kunya, me na yi masa na rashin kunya".

Adam ya buWe motar, ya ce wa rumaisa "Shiga ki jirani"

BuWe motar ta yi ta shiga ta zauna, tana cigaba da tura baki.

Adam ya kalli Jamil ya ce "Sannu Jamil, kirkin ka har ya yi yawa, shikenan ita rayuwa ba za a karSi ?addara ba, ka ?i halartar Waurin aurena, kuma ka ?i yi mini Allah ya sanya alkhairi".

"Allah sanya alkhairi saboda ka auri wannan abar?" Yayi maganar yana nuna motar adam.

Adam ya sauke hannun Jamil ya ce "Ko dan albarkacina, yakamata ka tausasa harshe a kan ta, matata ce, kuma bana son zumuncinmu ya samu matsala saboda son zukatanmu".

Jamil ya ce "Adam ka na da ?warin gwiwar yin wannan maganar? Dama yarinyar nan ita ce ta zo da jaririn aisha, ka ce aisha a hannun 'yan bindiga ta mutu, ya aka yi ita ta kuSuta, wani mataki ka Wauka, na san dole ba za a rasa wani information daga bakinta ba, menene dalilinka na Soye mana?".

Nan da nan Adam ya hasala ya ce "Kai ma kana zargin ni na kashe fulani na yi tsafi da gawarta ko? To na yi, idan wani bayani ka ke da bu?atar ji daga bakinta, ka je ka tambayi mai girma turaki".

Cikin sauri Jabir ya ce "Jamil, bai kamata ka faWi irin wannan maganganun ba, da na san haka abun zai zama, da ban gaya maka ba, takawa dan Allah ka yi ha?uri"

Bai ko tsaya ba, ya wuce mota, ya buWe ya shiga, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi.

Sai da suka Wan yi nisa sannan ya cewa rumaisa me suka ce miki?.

"Su wa?" Kallonta yayi, ta ga alamar babu wasa a idonsa, ta ce "Tambayata yayi, wai ya aka yi na san anty aisha, ni kuma na ce ban sani ba"

Jinjina kai kawai ya yi, ya cigaba da tu?insa.

Wani store yayi parking, ya ce ta fito su shiga. Ta fita ta bishi tana kallon wurin.

Suka je Sangaren jakunkuna ya ce ta zaSi jakar makaranta.
Haushi ne ya kamata, dan ko zancen makaranta ba ta so.

Ya sai mata kayan karatu da rubutu, da takalma, jakar ma uku ya saya mata, sannan ya sakata a mota suka tafi.

Gidajen ?an uwansu ya din ga zagayawa da ita, suna gaishe su, sai dai rumaisa ta ?ule da yadda wasu suke karSarta, tare da nuna ita yarinya ce, ta yi masa ?arama da aure.
Babu wanda ya sake ?ona mata rai, kamar hajiya Lubabatu, wato mahaifiyar Jabir, matar Galadima mai ci a yanzu.

Ban da tana ganin girman matar, ta yi sa'ar mama, da babu abun da zai hana ta zageta, dan ma Adam yana ta kareta, amma matar ta ci zarafinta, duk da bakomai take fahimta ba.

"Ragowar ?an bindiga aka kawo mini kenan, lallai takawa, ka yi jihadi sai fatan Allah ya biya ka".

Adam ya ce "Ba ragowa ba ce ba, kuma aurenta ba ni na yi jihadi ba, ita ta yi, tun da kun san waye Wanku, amma ta amince da aurensa".

Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Yo ba dole ba, ai ko a turu kake Wan mu yana da arziki da sarautar da za a aure shi domin sa, kuma a zauna da shi, kwaWayin abun duniya ne kawai".
Ba dan Ammi ta matsa, lallai ya zagaya da rumaisa, ya nuna mata familynsa ba, ya kuma yi musu bangajiya ba, da babu abun da zai sanya ya zo gidansu Jabir, wurin mahaifiyarsa.

Adam ya ce "To Hajiya, ina ga bari mu koma, akwai in da zamu je".

"Ahh haba dai, na saka a Wora muku girki ai".

"A'a Alhamdilillah, a ?oshe muke".

Hajiya Lubabatu ta ce "Gaskiya ban ji daWin wannan zuwan ba, yakamata a kawo mana ita ta wuni, da haka tana shiga cikinmu, za ta san yadda matan sarakai suke rayuwa, dan na san ba sani ta yi ba".

Adam ya ce "Bakomai ana koya mata"

Wata hadimar Hajiya Lubabatu ta ?araso, ta bawa hajiyar wata leda. Ta karSa ta mi?awa rumaisa ta ce "Amarya ga wannan ba yawa, kya sai tsintsiya, sai na sake kawo ziyara, tun da rabona da gidan, tun washegarin kai ki, mun ce a bamu ?yalle mu tabattar da abun da aka auro mana, an yi mana wala wala".

Rumaisa ta sha kunu, ta ?i karSar ledar.

"Ki karSa mana" rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a"

Hajiya Lubabatu ta ce "Takawa, ba ka gaya mata, masarauta ba ma kyauta ace a'a ba, rayuwar masarauta, ba kamar ta sauran gama garin mutane ba ce".

Ya kalli rumaisa da ke kusa da shi ya ce "Ki karSa, ba a mayar da kyautar matan sarakai".

"Bana so" ta faWa yadda shi kawai zai ji.

Ya saka hannu ya karSi ledar ya ce "Godiya take, kin san amaryat ta wa akwai jan aji, da gudun raini, kyauta ko da ga ni take, sai ta tantance, gaku sarakai, amma ta fi ku sarauta" yayi maganar a baibai, cike da mayarwa da Hajiya Lubabatu martani.

"Ikon Allah, da alama auren haWi zai koma na soyayya, ai labarin zuciya a tambayi fuska takawa".

Adam ya ce "Eh to, ba zan musa miki ba, amma hausawa suka ce Wan hakin da ka raina.."

Murmushi kawai hajiya Lubabatu ta yi, tana yi musu su gaida gida. Rumaisa tuni ta yi waje, dan idan ta cigaba da tsayuwa, matar nan tana washe baki, tana gaya mata magana, ba abun da zai hana ta zageta.

Shi kansa adam mood Win rumaisa ya gani, ya san a ?ule take kamar ta fashe dan takaici, la'asar ta riga ta yi sosai, ya ga idan suka koma gida, shi ficewa zai yi, ya san zama za ta yi, tayi ta ?unci a gidan, dan haka ya wuce da ita da ita gida.

Ammi ba ta nan, sai Nusaiba da Iman, da kuma Sabir, ganin Sabir ya sanya ya manta wani Sangare, na fushin da take yi.

Ba ta fiye shiri da Nusaiba ba, ta fi yi da Iman, dan haka da ita suke ta hirarasu.
Iman ta saka aka kawo musu abinci, nan iman take bata labarin, bayan ta dawo gida mai sunan baba ya kirata, ya ga missed calls Win ta, a lokacin take gaya mata, yadda suka yi da shi, da ta kira shi tana tambayar sa, ina take.

Ruma ta din ga dariya ya ce "Baban mama, sa ba ka dariya sai hamma, kirarin da mama ke yi masa kenan, shi dai kar a raina shi".

Iman ta ce "Anty rumaisa gara haka fa, ina son in ga namiji mai aji, rashin kintsi ko ga namiji bai yi ba ai". Suka cigaba da dariya, iman na nunawa rumaisa hotunan biki.

Nusaiba kuwa kallon iman take, yadda fuskarta take nuna jin daWin hirar mai sunan baba da suke yi.

Nusaiba a ranta ta ce "Iman, wannan ba irin mutumin da ya dace ki so bane, ya fiye zafi, larurarki kuma tausasawa take bu?ata, kuma wata?ila ba zai amince da

26 / 67